a kawo mi shi ya ci goron ya duba fuska da
hakoransa turare kuma ya shafa a jikinsa, shi yasa duk inda
babarbare yake ba ka raba su da kamshi, ga tsafta, don haka
muna hsigha gidan karshe na shafa wata humra mai kamshin
gaske ina yabanta nan take matar ta ce dole sai na tafi da itya
har sai data kara min wata har na bar gidan ina yabon karamcin
barebari rana tsaka muka karasa gidan bikin kasancewar
yanayin zafi garin Maiduguri akwai wahalar zama a wajenm
bako jar da ruwan fanfon garin zafi ne da shi muna shiga ta cc,
"ya kamata mu dan watsa ruwa a jikinmu."
Me zai faru? Ai ina tarar ruwa a fanfon bayi, na ji shi da
zafi na zata hita aka kunna, ko da na fito ina fada mata sai ta sa
dariya "Ai mantawa na yi ban fada mi ki cewa ga randuna nan
a tsakar gida ki dibi ruwa a ciki ba."
Daman ina son in tambaye ta, mafi yawanci gidajen da
muka je na ga manyan randuna an haka kasa an birne su sai iya
bakin aka bari, sai ta ce saboda ruwan ya yi sanyi ne.
Yamma na yi dangin amarya suka zo kamun ango shi
kuma yana can abokansa sun 6oye shi har sai da aka ba su
29
kayan
kwalliya
al'adarsu kamar bokiti soso da sabulu manshafawa kayan barkatai da kudi sannan aka kama shi, haka ranar faurin aure sisinan gwal akabayar sadaki, bayan kayan lefe a
nan daurc." na rike baki ina mamaki, "Lallai 'Yan Maiduguri sai an
Ta rike baki, "Ai ba ki ga wata bidi'ar ba ma."
Sai da muka yi kwanaki muna zirga-zirgar zuwa bikin.
Wata rana Yafanna har ta je kasuwa sai ta yi muhimmiyar
mantuwa, ai ta bugo waya cewar in duba waje kazata manta
wasu kudi don Allah in kawo ma ta yanzu don haka ala dolc na
tafi kasuwar ta na gani na ta fara yawwa yarinyar kirki muna
zaunc mu na hira sai ga wata hadaddiyar mota ta faka a gefe,
can wani tsamirmirin mutum ya fito da foodflask rike a
hannunsa, ya na tafc yana yake da ganin motar ba ta dace da
shi ba, ya yi mana sllama ta amsa ta na fadin. "Dan azumi ina
kashiga kwana biyu ku kusa makara."
"Ranki ya dade Yafanna wallahi uwargijiyata ce babu
lafiya, har kwantar da ita aka yi a asitin ASMA'U,yau din nan
muka fito. Ta ce ba ta son cin komai sai wainarkı kin san mai
laulayi."
Yafanna ta na ji ta kwashe da shewa. "Wainar ma ta gero,
kai madalla ai irin wannan cutar muke so. Ya ka gane min idan
gwarzo MUHAMMAD ya sami waje ya zaunc. Ai ba shi uban
gayyar ba, mu kanmu sai mun gwangwajein Allah ya raba
lafiya."
Ta ce, "Amin." Ta yi kirandaya daga dikin masu aikin,
"Maza a karba a zubo waina da miya a zuba mata dan shila
gida shida."
Har ya je gaban motar ya dawo. "Hajiya kin ga zan yi
mantuwa, ta ce don Allah ta na son ganin ki yau din nan idan
kin tashi daga aiki."
"To insha Allahu zan zo, in ce ko dai lafiya?"
30
"Ah, laliya lau."
"To ka mika'min gaisuwa wajen gımbiyar 'yar sarki."
Sai na kelle ta ina mai tamhayar "Yar sarkin ina ce?"
Ta yi min murmushi. "Yar sarkın garin nan ce Gimbiya
Raudat. Yarinyar arziki bata da wulakanta talaka ga girmama
na gaba sai dai kin gan ta ina fatan za ki yi min rakiya."
Cikin fara'a na amsa "Me zai hana in raka ki. Na ji ma ina
son ganin ta tun da tana da kirki."
Bayan mun hada ido ta yi kiran sunana, "Ke Husna wallahi
kuna kama fa ita fa."
Nan dadi ya kama ni har da tafa hannu. "Wayyo babu abin
da ke son gani kamar mai kama da ni, sai in ga kamar dan
uwana nc.
Da yamma misalin Karfe shida dan tasin a yake kait
kasuwa ya zo don ya kai mu can gidan, ba tare da bata lokaст
ba mu ka dau hanyar Dambuwa Road', wata shahararriyar
unguwa ce da ta shahara da manyan masu hannu da shuni d
amanyan 'yan boko da ma'aikatan gwamnati unguwar ta tsaru
iya tsaruwogashi tun da muka hau kan titi tsaf babu shara babu
hayaniyar nmulane nan take na fara yabon unguwar direban
motar ya na tsokana ta wai'na ga waje mai kyau ba irin Kano
ba duk shara. Nan take kishin Kano ya kamo ni duk da ba
mahaifatą ba ce, "Ai wallahi kada ka soma hada Kano da
sauran garuruwa saboda ta yi suna ta ko wane 6angare, ba ka ji
an ce Kano tumbin giwa yaro ko da me ka zo an fi ka ba,
bangaran kasuwanci ko dogayen gine-gine, in kuma flat ne
suma ga su-nan idan ka je wata unguwar ma kamar a birnin
Misira ko Madina ka ke, nan dai suka yi ta yi min dariya,
"Magori wasa kanka da kanka!"
A dai dai wani katafaren gida ya yi fakin muka fita ta
tsayar daeshi ya fan dakata mu fito saboda unguwar akwai
wahalar mota kasancewar kowa ya na da abin hawa.
31
Bayan mun shiga harabar gidan gefen dama 6angaren gadi ne, lagu irin rumfunan masu
yi shuke-shukega nan ne naajiyc motoci, tsakiyar an
dan yi tafiya
fitulu rcras an kewaye wajen sannan muka zuwa gana wata baranda da aka yi mata gini irin na
Garden,
kasar Sin, akwai kofofi biyu da suka sa ta a tsakiya daya
mata aiki
daya
a
cikin gidan, it amu ka bi mun tarar da ma su yi
muka
tsakar gidan can muka hango farfajiya irin ginin da
sanyi
baro a baya, muna shiga falon tarc da yin sallama wani da kamshi suka amsa sallama tare da gamewa a jikina
Yafanna
Matar da
ta
muka
na
tarar ta na 'yan gogc-goge ta ambaci sunan yi mata maraba.
iso mana."
"Yauwa Kandc uwar Tuwo a gidan Gimbiya. A yo mana
"Ranki
Nan take ta dau wayar tafi da gidanka ta sa a kunne, shi dade, ga ta ta iso." Bayan ta ajiye kan wayar ta ce mu dan jira, yayin nan idona ya hango min hotuna enlergment guda biyu daya namiji ne da gani shi ne mai gidan daya wata kyakkyawar mace ce ta yi murmushi, da ganin ta na ji tsigar jikina ta tashi, har na ji ba zan iya daurewa ba sai da na dangane kusa da ita, yayin da na Karewa hoton kallo na tsinci kaina ina ajiyar zuciya tare da yin murmushi.Tabas muna yi kama da ita, ai nan take na ji ta shiga zuciyata, ina can na shagala da kallo har ta sauko ita ma kallona ta ke ta na mamakin kamanninmu.
"Ya fanna inakika samo yarinya tubarakalla wallahi na zata kanwata Husaina ceta zo." Yayin da ta zo ta kamo hannuna. "Zo nan mu zauna."
Ni kam kunya ta kama ni. Na rife idona, ina faman nokewa,bayan mun gaisa ne take yi wa Yafanna bayanin abin
da ya sa take nemanta, "Wato Yafanna tun da nasami ciki
nakefama da laulayi, duk abincin da na ci sai na yi amai, shi ne
na ke son ki kawo min yarinyar da za ta ke min 'yan aikaceaikace."
32
Yafanna ta rike baki, "Ke 'yar nan, duk yawan
ma'aikatanki?"
Take ta yi murmushi, "Yafanna kenansu ai aikinsu daban,
wani lokacin sai in ga takura musu nakc yi, suna cikin yin nasu
aikin in kuma katse su gara dai a samo min."
"To yanzu iyayen yara ba su cika bada 'ya'yansu ba wai ana
tauye musu hakki kai ktura naka makaranta nasu suna zaman
bauta, babu na zarnan duniya bare na guzirin lahira, kunbawan
batu karatun dan kama. Kalubale gare ku masu daukar yan aiki
domin su ma 'ya'yane.
Can bayan Yafanna ta yi zurfin tunani sai ta kallo ni.
"Husna ko za ki dan zauna kafin in samo mata?"
Cikin fara'a na yarda, "Ya fanna ba sai kin samo ba ma zan
zauna har Allah ya raba Lafiya..."
Take Gimbiya ta amsa da amin kanwata, wallahi har na ji
kaunarki ta dada shiga zuciyata, bayan ta yi wa Yafanna
tambayoyi a kaina sai ta tambayc ni, na yi karatu. Na ce na
gama sikandare. Ta ce ina son ci gaba?
"Eh." Na amsa.
"Da kyau Husna, zan samo mi ki admission a jami'ar
Maiduguri insha Allahu."
Muna zauneta sani na bude wani karamin fridgc na dauko
mata lemo da ruwan sha kenan muka jiyo ana yi kiran
"Swecty! Swecty!" Wani mutum ya shigo da fara'arsa dogo ne
wankan tarwada kyakkyawa mai kwarjini.
"Swecty missing you." Ya zauna kusa da ita yana kokarin
sumbatarta,ta yi saurin kaucewa, "Honey ka ga fa Yafanna tana
kallon ka."
Yafanna ta tuntsire da dariya, "Ina ruwan Mahmud in dai
halinsa nc ba bakona ba ne."
Take shi ma ya fara fadin, "Yauwa Yafanna, dadina da ke
gancwa. ina laifi dan na duba BABYna kin san abin namu ba
saban ba nc...."
33
"Matar dıreba ta haifi mota." Ta Karashe. "Sai tuki."
ya
Nan ma har da ni ake yin dariyar A nan ya lurada ni bayan
ke,ko
kare
mun
min kallo, "Kai Sweety, kin wata yarinya mai kama da yi baki ne daga Sudan?"
Nan ta zayyane masa komai shi ma take ya yi na'am. Mun koma gida da Yafanna domin in shiryo kayana. Al'amarin Hajja gana kuwa tun da na shaida mata komawata gidan Aunty Raudat sai hankalinta ya tashi haka takwana ta wuni tana kuka har sai da mijinta ya zo ya shaida
mana ni da Yafanna muka je muna ba ta hakuri nadafa kafadarta, "Haba mutuniyar ki yi hakuri tafyata ba mutuwa ba
ce, zan dunga zuwa ina ganinki da Dinina, kuma dududu bai fi
in wata shida ko biyar ba, don Allah ki daina kuka kar nima ki
sani kuka, lokacin da mai tasi ya turo mu fito ai sai na kasa
tabula komai jikina kamar an zare min laka sam ban son
rabuwa dasu lallai na ji dadi shine gari ba na saba ba. Nan na
fara tunanin ya ban ji haka ba lokacin da zan gudu daga Kano
ba? Can wata zuciyar ta ce, "Ba ki ji an ce duk wanda ya tuno
da bara bai ji dadin bana ba? Me za ki tuna a can in banda
rayuwar takura da azaba ıri-iri? Yaya ne kawai yake dauke min
kewa. Masu magana dai sun ce zama lafiya ya fi zama dan
sarki, gashi a nan 'yar rabuwa ce za mu yi ta wucin gadi amma
duk mun damu kanmu har ina jin karmat in ce na fasa. Oh! Ni
Husna rayuwar kenan. Duniyar ta zame min gare-gare, daga in
yi nan sai in yi can yau kuma ga wajen da ta gara ni. Allah Ya
sa na shiga a sa'a, amın.
Har sai da dan tasin ya kawo mu kofar gidan ina zancen
zuci, a haka muka shiga fuskata babu walwala. Auntu tana
hango ni ta tare ni tare da tambayata, "Yau kanwar Aunty me
ke faruwa na gan ki babu fara'a?"
Nan Yafanna take shaida mata ita da maigidanta cewa
kukan rabuwa da Dini da uwarsa nake yi. Aunty ta kamo ni,
34
2
"Haba kanwata, ata za mu raba ki da su Dini ba, na yi
alkawarin duk sati zan sa kai ki ki wuni kin ji ko?"
"Ya ban ga ki na fara'a ba Ba kya son zama da Aunty?"
Me gidan ne ya tambaya, don haka take ya ban dariya, "Yauwa
har na ga kamannin ya Kara bayyana." Take ya duba agogon
hannunsa, "Bari dai in je gida in gaida su yau. Hidimar Bebi ta
hana ni fita da wuri, sai wahalar da mu ya ke yi, bayan mun sha
fama kafin ya zo ya yi jinkiri yau shckara uku kenan muna
dakunsa."
Yafanna ta rike baki, "Oh! 'Ya'yan zamani kenan mutanen
da har shekara fiye da goma suna yi ba su damu ba, amman ku
daga shekara uku."
Ya ce, "Watlahi na so a ce lokacin da muka yi aure wata
daya mu je yawon duniya wata na biyu mu zauna a gida, mu ci
amarcinmu wata na uku duniya ta san amaryata ta sami
Karuwa."
"LA ILAHA'ILLALLAHU MUHAMMADUR
RASULILLAHI!" Yafanna ta hau tafa hannu, mu kuma mu na
ta dariya yayin da shi kuwa tuni ya fice da gudu.
Kafin mu rabu sai da ta yi min fadan zaman lafiya sannan
ta ce "Husna kamar yadda na sanki da ladabi da rikon addini ki
ci gaba da yi. Ke kuma Rauda ga amanar Husna kamar inda ni
ma na karbi amanarta."
Yau da gobe ta sa na fahımci wace ce Raudat da asalinta
kamar haka: Mahaifinta sunansa Sarki MUSA YAKUDIMA
babarbare ne dan asalin Kasar Maiduguri, ya gaji sarautar
mahaifinsa bayan ya rasu halin rayuwa da yawan zirga-zirga
zuwa kasashen waje ya sa ya hakura da sarauta ya bar wa
Kaninsa Isa Yakudima sarautar, a halin yanzu ya zama
Ambassador na Kasa yana da mata guda daya ta haifar masa
'yaya uku Al'amin, Aunty Raudat sai Asma'u ta rasu.Bayan
rasuwar Asma, ba dadowa Hajiya Salwa ita ma ta rasų, wato
uwar gidan nashi,bayan wasu shakaru yaran suka nuna damuwarsu akan ya yi aure, an.man abin ya faskara saboda tsananin son da yake yi ma ta gani yake ba zai iya zama da wata macen ba. Su kuma yaran zamansa haka ya na damunsu
cewar ai abin kunya ne ya zauna haka a shigo katafaren gidan Sarki babu mace si bayi.Ko da suka takura masa sai ya basu izini su nemo masa mata in dai zabinsu ne zai amince.
Ana cikin haka kwatsam sai mijin kanwar mahaifiyarsu ya
mutu, ta na fita takaba ta cika idda sai suka je har Sudan suka
kai kukansu gun kakarsu maman Sudan, nan ta ce ta ji ta gani,
Batula ki yarda ko don ki rike 'ya'yan 'yaruwarki, haka kuwa
aka yi, cikin ikon Allah cikin shekarar ta haifo 'yan biyu
Hassana da Hussaina a halin yanzu sun girma suna daf da gama
secondary, yaran sun shaku da Aunty kamar inda Momy
Batulla ba ta nuna banbanci yawancin weckend suna zuwa
gidan Aunty su kwana. Shikuwa Yaya Al'amin yana can Sudan
uana yin course yana dawowa, za fara aiki,shi ma suna sa ransa
karshen shekarar nan. Shi kuwa Yaya Mahmud mahaifinsa
kwamishinan 'yan sanda ne yana aiki a can Abuja e iyalinsa
suna zaune a nan Maiduguri matansa biyu mahaifiyarsa ce
uwar gida su kadai tahaifa sai amaryarsa Hajiya Karama, ta na
da yara biyar biyu mata uku maza matan ne manya Jamila da
Sakina yaran ga tsiwa da rashin ganin girman nagaba, haka
uwar su ma ba ta ragawa uwar gidanta Hajiyar Mahmud. Sau
da taru suma su kan zo weekend gidan Aunty amman saboda
suna tsoron Yaya shi ya sa ba sa yi mata rashin kunya ita ma ba
ta cika wasa da su ba, ta kama kanta, haka duk abin da suke so
a wajen sa sai sun biyo ta wajen ta suke samu suk da ta na jin
zafin rashin girmamawar da mahaifiuyarsu ke yı wa tasa hakan
bai sa ta hana shi yi mu su alheri ba. Sai dai kara mi shi kwarin
gwiwa a kan ya yi zumunciya rike Kannensa, saboda shi ns
babba kum Allah ya hore masa Hajiyarsa kuwa duk da hidimar
ttahakan bai hana ta dafairin abin da ta ga ta na da yake yi ma
36
so ta kai mata ba kamar abincinmu na gargajiya, in kuwa aka
kai ta dunga shi mata albarka itada mijin. Shi kuwa kullum
godiya ya ke ga Allah ya da ya ba shi mtar da za ta kai shi
Aljanna. Ga shi ya na yi da ita kamar kwai a hannu. Kowa na
shakkar 6ata mata rai. Gimbiya kenan ta gidan Yarima
Mahmud.
Bayan 'yan kwanaki kadan aka samo min ci gaban karatuna
a University of Maiduguri. Kullum direba ne ke kai ni, kuma
ya dauko ni, ga shakuwar da muka yi da Aunty ba ta kauna in
matsa daga kusa da ita, makarantar ma don ta zama dole ne in
son samu ne ta gan ni tare muna ta yin hira aikin bai wuce
"Husna dauko wannan Husna gyara wancan, kin ji an yi kaza
ko? Har ta bawa kanta dariya "Kai bari dai in saurara kiran
haka kar sunan kanwar tawa ya kare ko?"
Dakunanta kuwa babu inda ba na shiga har samanta babu
inda ba na gyarawa, in share tas, akwai wata rana ta je unguwa
Dan'azumi ya kawo mata kayan wanki na bude wardrobe dinta
na shirya mata su na feshe su da turare na gyara ko ina dakin
yaya ne kawai ba na shiga, shi ma ina yin takatsantsan saboda
na ga tun da ta na da kishi.
Ta na dawowa ta yo wanka, kanta tabude don ta sami kaya
marasa nauyi ta sa, it akanta abin ya ba ta sha'awa, inda ta ga
komai a shirye ta kira ni. "Husna an kawo wanki ne na ga sif
din tsaf?"
Na bata amsa "eye."
Cikin jin dadi ta fara yabon kulawar da nake nunawa a
kanta da kayanya, take ta dauko min turmin atamfa Super
Holand ta miko min."An jima ki dau Dan Azumi ya kai ki
wajen tela."
Nan fana fara odiya tadab dafa kafada ta "Haba Husna ki
ke fa a matsayin kanwata na dauke ki, don haka kar ki yi
shayin komai duk abin da kike so ko ya dame ki ki same ni ki
sauar da ni."
37
२
domin
Idona
shi
ya
kansa
cika
da hawaye. "Ai Aunty dole ne in yi уа, Mahaliccinmu ya na son bayinsa masu godiya."
A kwan a tashi baby wuya a wajen Allah, yau ne sadakar arba'in din mahaifiyar Uwale, na shirya tsaf ta sa dircba ya kai ni kai tsaye na zarce dan don na san iya Yafanna ta na can, muna ganin juna ni da uwalc muka rike juna don murna ta kare min kallo. "Husna kin sami lafiya."
Na cafe, "Sauran kwanciyar hankali."
"Ma sha Allahu 'yar gidan Yafanna, kin ga kuwa inda kyawunki ya dada fitowa?"
Nan dài na zauna ina ba ta labarin komawata gidan AUnty
da irin rikon da take yi min. Ta nuna farin cikinta kwarai daga
nan na tafi gidansu Dini can na wuni sai magriba an zo dauka
ta mutumina kuwa Dini kamar yadda muka saba da kuka mu ka
rabu. Bayan kwana biyu lokacin tafiyar Uwale ya yi Yafanna ta
kawo ta don mu yi ma ta sallama tare da yi wa Aunty godiya.
Nan Aunty tayi mata halin girma ta hada ma ta sha tara ta
arziki. Uwale ta durkusa tana ta yi mata godiya. Da muka rako
ta bakin get ne ta ce Yafanna ta dau wani abin take ta girgiza
kai "Sam rike kayanki in dai alherin Raudat ne in har gida ya
ke samun mu."
Nan ta fara kasafi, "Kun ga na hada da gadona in bawa
malam jari."
Mu ka amsa da ya yi dai dai."
Abin da yake gudana tsakanina da masu yi mata aiki kuwa
shi ne, ganin na samu daukaka da kauna wajen masu gida sai
suka dau karan tsana suka aza min, da na yi magana sai su
hantare ni, musamman ma Kande komai na yi ban iya ba, ta yi
ta kai kushe da sarana gun Aunty har ta kai ga su ma kannan
Maígidan sun fara nuna min kiyayya a fili daga dan abu Kalilan
saí gori. Haka wata rana na dawo daga aiken da Aunty ta yi
38
min, na same su tare da 'yan aikin gidanatsakar gida suna yi ina
ta kwada sallama kowa ya yi min shiru sai kallon banza suke yi
min, ni kam da na ga haka sai na wuce Kande ta na bude
bakinta sai cewa ta yi, "Kin fi kannen maigidanne kina wani
takaw dai dai, awai da dai ba mu san asalin ungulu ba sai ta ce
'yar sarkin Masar ce."
Nan ko suka saki shewa suna dariya Sakina ta cafe, "Haka
ne Kande, shi ne za a yi mana yangar kwalba babu man
shafawa. Mu dai mun fi son a yi zuciya a nemi iyaye, don babu
mai auren tsintacciyar mage."
Ina jin haka na yiniyar shigewa wajen Aunty sai na fasa na
nufi dakin da muka kwana na fada kan katifar kwanciyata na
dinga kukan maraici da bakin cikin rayuwa. "Oh! Ni Husna
ashe ban rabu da Bukar ba na haifi Habu." Nan dai na nutse
cikin tunanin halin rayuwar da na ke gani a duniya, nan takc na
jiyo kiran sallar azahar, na dauro alwala na yi sallar, sannan na
ci gaba da kukana ina rokon "Ya Ubangijina ka fi ni sanin
halin da nake cikin, sannan kai ne masanin komai, sannan kai
ne ka ce Ya ku bayina ku roke ni ni kuma zan amsa mu ku. Ya
Mahaliccina na san ka fi ni sanin iyayena, ko da ina tare da su,
sai yadda a tsara min rayuwa zan yi, ko mai dadi ko mara dadi,
gare ka na dogara daga gunka nake neman taimako, na kuma
yarda da kaddara ina rkokonka in har suna rayc ka yi gagawar
hada ni da su, idan babu.rabon ganawa da su ka yi min gafara
tare da su ka tashe mu a tutar Muhammadur Rasulillahi
Birahmatika Ya Arrahamanir Rahim." A nan barci ya dauke ni
sai lokacin sallar la'asar na farka bayan na idar na fita Kande ta
na hango ni ta fara fadin "Kar ma ki soma zuwa ban raba
abinci da ke ba."
Na dauke kaina zuwa inda na nufa. Aunty ta na falon kasa
ta maida hankalinta gaban T.V. ta na kallon tashar Larabawa.
Na durkusa na gaishe ta ta amsa tare da tambayar "Ina kika
shiga ina ta jiran ki?" 39
Na sunkuyar da kai ina wasa da yatsana. "Dago mu gani."
Na dago na kalle ta. "Ai kamar ma kuka kika yi?"
ga
Na girgiza kai tare da ba ta amsa. "Barci na yi shi ya sa ki haka, tun dazu ina daki."
Cikin mamaki ta ce "Da kina gidan amman na tambayi Kande ta ce ba ki dawo ba." Ta gyada kai. "To ga abinci can a
cikin filas ki zuba ki ci."
Bayan na gama nadauko littattafaina ina duba wa, abin da ban gane ba ina tambayarta ta koya min.
Kusan duk weekend,yaya da Aunty suna zama a cikin hadadden lambunsu don shakatawa, ko in ce nishadi yau ma
kamar yadda suka saba, suna can zaune a gefen swimming pool, suna wasa da ruwa tsuntsaye kamar dawisu, jimina, talo- talo, kunkuru, agwagi sunata wanka cikin nasu kwamin, abin
gwanin ban sha'awa ga wanda ya gani. Ga daukewa masoya
kewa in banda kukan tsuntsaye babu abin da ake ji. A dai dai
lokacin ni ma na nufo wajen rike da irin karemin basiket da ke dauke da kayan marmari a ciki ina karasawa na yi mus u
sallama snnan na ajiye a gabansu. "Yauwa kanwar Aunty, shi yasa kike birge ta."
Na rufe ido ina yin murmushi.
Muka ji an yi mana sallala, juyawar da zan yi muka hada
ido da wani hadaďden gaye, dogo ne fari kal kamar shi ya yi
kanshi, sanye yake da kayan farauta jikinsa, ya kalle shi cikin
zolaya, "Ranku ya dade na shiga cikin gidan aka ce kuna
lambun soyayya." Ya mika mi shi hannu. "Yarima ya san
ranka?"
"Raina fari kal, don ni ma na zo lambun a sa'a." Ya kalle
ni. Aunty ta fahimci abin da yake nufi. "Yaya kenan, ba ka da
dama." Yanuna hannun damarsa "Ina dai ita ma." Ya sake kallo
ni ko ban yi dai dai ba yarinya yanzune kyau? Ni dai ban tanka
40
ba na fara jeta kauan marmarin da na kawo hisa kan karamin
tir na mike kenan zan tafi saboda kallon da ya kc min ya yi
yawa,ya yi magana "Kin ga."
Najiyo.
"Don Allah ruwan sha za ki sam mini."
Na amsa, "To bariin kawo maka." Ina tafiya ya tambayi
Aunty, "In cc ko daga Sudan ta zo?"
Ta amsa da "e."
"Gaskiya kuna yi kama sosai, a gaskiya na yaba da
nutsuwarta, ki taimaka ki ba ni ita."
Ta yi murmushi. "Yaya Yarima kenan ke ncmi so a
wajenta in har ta amince ni kuma zan yi jagora da taimakon
Allah."
Yaya Mahmud shi ma ya ce, "Ko ni ma in da gaske ka ke
zan daure maka gindi."
Yana shirin yin magana na iso, hannuna rike da robar
SWAN WATER, na durkusa tare da ajiyc mi shí a gabansa. na
bude murfin na tsiyaya a kofi. Har na mike zan tafi ya kirani.
"Mai kyau."
Na jiyo. "Husna sunana."
"Kai beautiful name. Husna karasa ladanki ki miko min."
Cikinjin kunya na ba shi.
"In son samu ne ma a ba ni a baki."
"Kada fa ka wuce gona da iri mana." In ji Yaya M. Ina
jiyowa na ga kowa kallona ya ke, take kunya ta dada kama ni,
na yi cikin gida da gudu, ya na kıran "yaki, yaki, kun ga kun
korar min budurwata ko?"
Ina jiyo dariyarsu. Suna fita tare da Yaya M. Aunty ta yi
kira na, ta wayar starcoms, wai in zo in taya ta hira na makę kafada, "Gaskiya kunyar bakonku na ke yi........"
Ta katse ni. "Kc ba bako ba ne, dan uwana ne, sun ma fita da Honey."
41
Na karasa kusa da ita na zauna ta juya ta na kallona "Husna kin san yadda mu ke da na dazu?"
Na girgiza kai.
"To na san kina jin labarin kanin Daddy Sarki me ci yanzu."
Na ce, "Kwarai."
"To shi ne babban dansa, Yariman kenan, don haka ya gan ki kin yi masa y ana son ki da aure."
Nan na yi saurin dafa kirji. "Aure fa kika ce Aunty?"
"Zan mi ki wasa ne, ko zan bari ya yaudare ki, tun da har
ya furta babu wasa domin shi ba ya kula 'yanmata, amman ya
na ganin ki ya gigice. Ko ya kika ce, ya ne kanwata?"
Kina sunkuye dago habata ke da wuya ta ga hawaye na
faman zuba wani na bin wani. Nan take ta gigice ta na tambaya
ta. "Me ya yi zafi nake yin kuka, in har ba kya son sa babu dole
ni dai na san ba zan kawo mi ki abin da zai cutar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13