An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
RAYUWAR KENANHAJIYA JAMEELA HALLIRU BRIGADE
AUNTY)
RAYUWAR KENAN
NA
HAJIYA JAMEELA Y. DANKAKА
BRIGADE
COPY RIGHT © 2005
1
RAYUWAR KENAN
KACAN CANCI YABO
Maigidana Nakaina Alhaji Halliru Jibril Gama
Domin bata lokacin da kayi na duba littafina tare da bani
kwarun gwiwa nagode, Allah ya karo budio ya kareka da ga
sharrin mahassada
BAZAN MANTA DAKUBА АBOKAN ZAMANA
H Dada A Halliru
Binta A Halliru k/jaba
Al hamdu lillah
RAYUWAR KENAN!
Goron Sallahne
Hajiya Jameela Y. Dankaka Brigade
Mrs Halliru Jibril Gama k/jaba galabarwayataran mata kawai
GSM 08043263572
942519
GODIYA
Dukkan godiya tatabbata ga Allah madaukakin Sarki da ya bani
iko tare da basira rubuta wannan littafi, tsira da aminci sukara
tabbata ga fiyayyan talikai.
SADAUKARWA
Nasadau kar da wannan littafi ga mahaifina
Alh. Y. dankaka da yan uwan Alh. Idris dankaka- Rabiu
Dankaka birged tare da fatan Allah yajikansu tare da kulluhum
musulmi Amin.
GARGADI
Banyarda ayi amfani da wani bangare na littafina ba aki ya ye
Gaisuwa mai tarin yawa ga family dina Dankaka Yahuza
Birged
Dalhatu Muhamud Zango
2
RAYUWAR KENAN
Muhammad Borodo family
JIN JINA AGAREKU YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI
Aunty Maryam Mrs. Rabi'u
Aunty Hadiza Dankkaka Kandala
Hidaya
Halima
Amina
Mrs Auwal
Mrs Usman
Mrs Nura
Yahanas Borodo Mrs Sani
Zainab inya Zango
Hajiya Umma Ado Dandawaki Mrs Nalami
Hajiya Nana Asma'u Gusau
Aunty Maryan (MAMA) Mrs Aminu Sifetor
Aunty Fatima Ibrahim
H. Baraka Ali Mrs Auwalu
H. Ashsha Muhammed
H. Sadiya Dauda Mrs Hussaini
H. Asiya Baba Mrs Aminu
Aunty Rakiya Ado
Jinjina Hauwa Ali Dodo
Baturiya Uba
Atine Usman (Mommy)
Aunty Baby Sulaiman Yan Awaki Mailittafin (Huda)
Aunty zainab Lawan Birged (Maza basuda tabbas)
Aunty Siyama Ado Bayero Alkawarin Allah).
CARE BABYS
Bilksu Isiyaku Mrs. Bashir
Binta Hamisu Mrs. Rabi'u
Amina (Yadikko)
Safiyya (Lamimi)
Samira Dalhatu Zango
Samira Haliru Jibril
Kadija Halliru Ummi
3
Lawisa Halliru
Zuwaira Uba
Nazifa Haliru
Zainab Kasim Musa
Baby Kasim Musa
Yahanasu Kasim Musa
Farida Halliru.
Hadiza Zubairu Tabawa
YABO GARE KI KAKAТА
Hajiya Hadiza Borodo
Allah ya kara miki lafiya amin
TSARAWA A COMPUTER DA BUGAWA
Kausar Comp. Kwanar/Jaba 080-26918425 Kano
4
RAYUWAR KENAN
RAYUWAR KENAN
ari yayi shiru bakajin motsin kowa sai kudarar ubangiji Gkawai, adai dai lokacinne kuma ya amsa sunan sa na
dare mahutar bawa asannan ne Husna!
Na farka daga barawon barci da yasaceni na kai kallona ga
agogo na ga karfe biyu da rabi nadare, nafara tuna irin
abubuwan da suka faru dani ayammacin wannan ranar, ai nan
da nan wasu za fafafen hawaye da wani kuka mai bantausayi ga
dukkan wanda yaji shi. A lokaci guda kuma na tuna babu mai
bani hakuri bare mai rarrashina, na kara fadawa cikin tunanin
halin da rayuwa ta fada na rashin iyayena ko wasu yan uwana,
sannan uwa uba natuna dacewa munfa rabu kenan in ba wani
tsananin hukunci na, Allah ba. Kuma shine masani ko suna
raye ko sun mace? Wanda adalilin rashinsune na tsinci kaina
acikin kuncin rayuwa, ake gana min ukuba iri-iri hakan kuma
yasa ake yimin gori da cewa wai ni shegiyace mara usuli 'yar
tsuntuwa.
Na kara kecewa da kuka kamar wata "yar jinjiniya,
zuwa wani lokaci sai na tuna cewa ashefa dare ne kuma a dadai wannan lokaci, lokaci ne na karbar addu'a dan haka sai
kawai na share hawayen dake zuba daga ido na, na dauki buta
nayi alwala.
Nan take na canza wasu kaya masu tsabta tare da jero
nafiloli. Bayan na idar sai na dauki carbi nayo salati ga
fiyayyen talikai, tare da istigfari da hailala, sannan nayo
wuridin ayatul kursiyu adadinta 7,77. na kuma hada da wannan
addu'ar wadda take fitar da mutum daga kunci kamar haka:
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN
ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA'AKLIFNI KHAIRAN
MINHA"
na kara samun nutsuwa akan wannan addu'ar dana
karanta saboda, Manzon (saw) yace dukkan wanda ya sami
kansa cikin wani matsi da musibar rayuwa in in har yakaranta
wannan Addu'a to Allah zai kubutar dashi.
5
RAYUWAR KENAN
Bayan nan na daga hannuna sama ina mai langwabar
da kai tare da rera sabon kuka hade kirari gun mai jinkaina ina
mai cewa
"ya Ubangiji ya mahaliccin samai da kassai ya
ubangijin Annabi Muhammad, gareka nake neman taimako
gareka na dogara. Ya mijibincin rayuwata ina neman
taimakonka da ka neman taimakanka da ka bayyana min
iyayena da yar uwa ta wacce nake so da gani, kuma ka ceci
rayuwata daga kangin bakin ciki".
Ina cikin wannan hali ban ankaraba najiyo ana kwada
kiraye kirayan assalatu na mike nayo raka'a tainil fijir ina
zaune ina lazimi har aka tada sallar bayan na idar na cigaba da
lazimin dana sabayi sannan na godewa Allah da ya bani ikon
bauta masa aduk irin hali dana tsinci kaina, haka kuma bana
mantawa shine ya kaddara min kowacca irin kaddara tasamenm
ako yaushe ina cikin gode masa domin ni baiwarsa ce.
Bayan gari yayi haske namike nanufi kicin domin bani
da hutu ko zama, na daura, girke girken, dana sabayi domin
Karin kumallon safe. Ba wai rashin masu girkabane ya sa nake
yi ba aa' sai don atakura minnc, bayan na kammala na kai kan
dani tebel, najera nassanar da mama) nagama. Nayi sauri na
debi ruwa na watsa kar na makara wajen zuwa makaranta,
domin kullum hakan ce take faruma nashiga falon tare dayin
sallama, mamace azaune da 'ya'ya Nura, Salim da Fati, suna
yin karin kumallo duk da sallamar dana yi amma mutum daya
ne ya amsa sallamar tawa.
Bayan na gaisheta ta amsa da kyar 'ya'ya kuwa cikin
fara;a muka gaisa. Ita kuwa Fati. Kallo ma ban isheta ba
nakoma jikin ban go, na, rakabe ma sauraraan abani nawa, duk
da cewa kuwa ni na dafa ban isa nadiba da kai naba sai anci
anrage, wataramma bana samu haka nake tafiya da yinwata,
dukkansu abincin suke ci, amman wani abin mamaki shi yaya
Nura ya yi tagumi kallona kawai yakeyi in, za'a gane hakan ne
6
RAYUWAR KENAN
kawai da irin kallon da yake yi min da ka kalli kwayar idon sa
babu tambaya alamun tausayi ne a tare da shi.
Ga dukkannin alamu abin da yake damun shi kenan, ga
dai abinci agabansa amma yakasaci ita kuma fati ta lura da abin
da yake faru wa, duk da haka sai faman. Harare Harare take yi
tana faman tsaki da dai shima ya lura mahaifiyar ta sa ma tana
son gano halin da yake `ciki sa yai saurin kai, kallon sa ga
agogon hannunsa tare da mikewa tsaye yana musu nuni dasu
tashi lokaci zaikure yaya) dai abincin dabai cibakenan mama)
ranta abace ya kalleni yace "kinzo kin samu agaba sai kace
mayya, sai kitattara wanda akarage kici azuci yata nace
"Yau kuma har mayya ake ce min," ina hadawa ina
kuka azuciyata nace dan yinwa ba aimata lahaula dana hakura
da abincin fitata kenan naci karoda su Ramlat) suna kokarin
biyomin mutafi 'Ya'yan Aminin Abbane summa zama yan
uwan juna. Domin wanda ma bai sani ba cewa ake wada kanine
Alh. Nasir da Alh Sani Allah yahada jininsu domin tasu tazo
daya, domin Abba, ya amince da shi, yakuma jashi ajikinsa
sosai shine lokacin da Abba yake kokarin sani amakaranta
primary yace ga 'Ya'yansa zai samu tare dan haka makaran
tarmu daya shine muke tafiya tare.
Wannan ne ma yasa muka shaku dani da Ramlat
domin kammu daya tun ma shekara biyar har ga shi, yanzu
muna sakandire a haka rayumar taci gaba, domin bansan
mahaifana ba sai shi Alhaji Nasir. Wanda muke kiransa da
Abba. Asalinsa dan jahar Kano ne amman yagir mane a
Maiduguri haka kuma shararran dan kasuwaane yakanyi tafiyetafiye domin neman arzikinsa haka duk da arziokin da Allah ya
bashi bai sa yana wulakanta "yan'uwa da abokan arziki ba, ga
kuma Uba lyayensu dan haka ya kasance kullum acikin godiyar
Allah yake, domin yana ganin cigaba a rayuwarsa yana yawan
zuwa Maiduguri domin acan yayi karatu kuma mahaifiyarsa ma
tana can tana aure.
7
RAYUWAR KENAN
Gidan sa yana uguwar yan kaba. gidan tsararrene
kamar yadda ginin zamini yake dai-dai gawar gwado.
Matarsa daya Ya'yansa uku biyu maza mace daya
haihumar ta tsayawa matar tasane saboda yawan shaye shayen
maganin tsarin iyali da takeyi kuma Allah ya karbi fatanta.
Amman shi dai Abban ya rasa abin da yake yimishi dadi domin
yana da bukatar yaga yara dayawa agabansa Allah shine
masani.
Bayan kwana biyu gidan babu walwala domin Yaya
ransa abace yake. kowa yashigo ba mai ganin dariyarsa, sai ni
nima din sai in mun kasance tare, domin agaskiya duk gidan
babu mai farantamin rai kumar Yaya da Abba, dan ko ganina
yayi cikin bacinrai Yaya haka zakaga yana jana da wasa,
harsai ya tabbatar babu sauran. bacin rai a tare da ni ko wata
damuwa
Wani lokaci ya kan kanne Idonsa daya yace ko ina
sanwani abunne? Sai nagirgiza kai nayi dariya, haka kuma tun
mahaifiyarsa, tanayin fada akan yadda yakan yi wasa dani har
ta agaji ta kyaleshi sai dai nuna fishi.
******* *******
ata rana mama ta, aike ni kasuwar yan Kaba inyo W
cefane, bayan nayi wanka nadau kwalliya ta nataje
gashina na hade na matse da ribon na kalli kai na a
midubi na godewa Allah domin yayi min halitta mai kyau ga
milk colar ga Idona saiszi) baki na dai-dai misali, nadanyi
murmushi tare da fadar wata kalma a zuciyata. Karkice na koda
kaina sau da yawa mutane kance wai ni irin shuwa arab din nan
ce. Ni dai nakan yi murmushi domin bana cewa komai.
Bayan ta bani kudin cefanen ne tace in tafi ni kadai na
mamaki matuka domin ko wane lokaci zani kasuwa ni da
8
RAVUWAR KENAN
Magaji mai wanki take aikenmu amma yau kuma ba haka
lamarin yake ba
Gun mai kayan miya na fara zuwa sannan na wuce na
karasa yin cefanen. Leda uku ce rike a hannu na niki-niki ga
rana da gajiya uwa uba ga yunwa tana damuna, ina kokarin
tsallaka titi ne al'amarin ya fanu Domin kuwa ina shirin
tsallaka titin da zai maida ni hanyar zuwa gida, can sai ga wata
mota aguje yayin da ni kuma na karasa tsakiyar titin ji kake
kuww! Ya taka birkin motar kamar ransa zai fita
Tuni nakai kasa ledodin da suke hanuna kuwa sukaа
tarwatse c an waje daya Hakika Allah dai- shine ya cece ni
domin kuwa mdumin ma yana da zafin nama da tuni ya take
ni. Ka fin kace me wurin ya dinke da mautane. bayan ya fito
daga motarsa yana salati waman bai hana mutane su yiwo ca
akan sa ba, kowa yana fadin albarkacin bakinsa
Wasu na cewa "Alhaji a kaita asibiti, wasu kuwa zagin
sa sukeyi. Ni dai da naga haka nayi kokarin mikewa anayimin
sannu shi kuma sai yasha gabana yana tambayata. ko naji
ciwo?
kudi
Nace a a
Ya ci gaba da abi hakuri, can wani ya zaburo yacе
ke baki da wayo ki langwabe ki ce kinji ciwo yana da
na dan yi murmushi nace babu damuwa nidai na dawo
haiyaci na nidai hada ledodin cefane nakeyi sai mai motar
yace
ki yi hakuri muje a duba kafarki dan naga kina yin
dingishi
ni dai nariga na dawo haiyaci na na koma hanyata na
barsu nan can sai ya biyo bayana yana yimin maganar in tsaya
ya kaini gida yaga da kyar nake takawa
na juyo nace dashi mi fa ko taba ni fa bakayi ba, hakam
ma da ka ga guiwoyi na ne suka yi sanyi
9
RAYUWAR KENAN
ya dai takura min da cewa bai kamata ya barni intafi
gida ni kadai ba "in nayi hakan banyi miki adalciba"
nidai nasa gaddama domin ina tunani inyakaini mai zai
faru? Haka dai yarin jayoni yabude mini gaba, nace a'a nabude
gidan baya nashiga nayi jugun. ya yakalleni ta mudubi yace
yan mata sai kidin ga nuna mini hanyar da zan bi ko, a haka har
ya shawo kunar layinmu, yayi fakin adaidai kofar gida gabana
ya fadi yace ras ai nan da nan jikina ya daurawa, Magaji mai
wankine muka fara yin ido, hudu dashi yabude bakinsa da
alamun mamakin ya ganni a wata motar. Daga gefe kuwa Yaya
Nura ne tsaye ransa shima abace ni kuma ina ciki inata gigin ta
nafito, duk nakidime domin abinda nake gudune yake shirin
faruwa, nanufi inda yake atasaye ina karasawa na fashe da kuka
sannan mai motar yaka raso dai dai lokacin da ne yake tambaya
ta ya ya ga jiki na, duk kasa, kuma kukan inai nake yi? Sai yayi
mishi sallama sukayi Musbaha yana cewa sunana Mannir
Ahamed ina aikine akan fanin jiragen sama.
"Na san zaka yi mamakin ganin ta dare dani; to wani
tsatsayine yafaru da ita, tazo tsallaka titine ni kuma nataho. Ban
Ankara ba, nakusa takata, anan tafadi kan kwalta, Allah neya
kiyaye, ai nandanan Yaya yazazzaro ido kabugeta shi kuma da
ya ga idonsa ya canja sai ya saurin cewa a'a, ban taba ta ba
domin bataji ciwoba, shine naga ya dace na kawo ta dan na
bada hakuri, Yaya kenan da ya juyo muka hada ido yaga nayi
munnushi sai shima yasaki fuska sannan ya mai da kallonsa
gun Mannir to babu damuwa tun da ba ta ji ciwo ba ko?
Nagyada kaina sai muka saki dariya ga ba dayan mu Mannir
yasake mika mishi hannu yana dada godiya shi kuma yana
cewa babu damuwa sai ya kalleni yace sai dai banji sunan
malamarba, Yaya kamar shi, a ka tambiya yai farat yace
sunanta HUSNA kai sunan maidadi yace to HUSNA) Allah ya
sawwake ki sai nadawo dubaki.
Yaya har bakin motar yarakashi yana budewa yace af!!
gakayan afanin mun manta, ya mika mishi.
10
RAYUWAR KENAN
Can cikin gida kuwa muryar Mamace take tashi tana ta
faman fada tana cewa,
"kullawa sukayi, daman shege baya fasahalinsa da
nasan yawan iskanci ta zata, da ban aiketaba shi kuma muna
fiki daya kai labarin, ya na cewa abin nawa ya bunkasa har
anfara kawoni a mota.". ai ina jin haka sai nafara ja. dabaya
Ya'ya yakalleni muka hada ido dashi yace
"shige muje" kirjina sai dukan uku-uku yake
"salamu alaikum mama ai Allah ne ya kiyaye da sai
dai muji mummunan labari domin motace ta bugeta, shine
mutumin ya kawo ta dan ya ba da hakuri"
ta daka mishi tsawa tare da, dakatar dashi da hannu,
to Sarkin tsari rufe minbaki daman ba ka son laifinta
shine zaka sakota agaba kana kareta" yace
amma ita ce kuma dole ne a fade gaskiya daya
ta" tace "uaan tunda kana daure mata gindin tayi abin da ta ga
dama, ai halittane dan tsintatciyar mage bata mage!"
Nikuwa hawayene kawai yake żuba, a idanu na, cikin
halin kuka nadur kusa gabanta nace
"wallahi Mama duk abin da 'Ya'ya ya fada haka akayi
dan Allah kiyi hakuri ta daka min tsawa "inyi hakuri? "To
kayane saiki nada gammo, ki dauka, Allah ya dawo da Alhaji
Lafiya dan shine ya dauko mini wannan garyar tsiyar"
Yaya ransa abace yace haba, Mama, mutumfa
rahamane kowa kuma da irin baiwar da Allah yayi mishi" rufe
min baki" in baso kake inbatar makaba mara kunya"
ta, tsahi tana huci kamar wani kumurci zuwa wani
lokaci kadan Yaya ya waigo ya kalleni tare da girgiza kai
alamar inyi hakuri yakira suna na yace in tashi inyi Sallah na
kuma canja kayan jikina nace' to..
Musalin biyu da kusan mintina ashirin na kammala
kintsawa na nuti kicin, a sannan masu aikin sunkamalla hada
abinci nadebo nakai kan dani table najerasu kamar yadda
nasaba na koma guri daya na tsuguna cikina inbanda kugi da
11
RAYUWAR KENAN
kiran ciroma ba, abinda yakeyi, sai ga Fati tazo gabana tana
faman yatsina da hararata tace inje inkwashe kwanukan in
tattara wanda aka rage dan babu sauran abinci da sauri na nufi
falon natarar bawani maiyawa suka rageba sai na nufi kici ina
kankarar kanzo ina hawaye, domin ba yadda na iya da kaina
saboda matsananciar yunwa dake dukan kokon cikina.
Kuka da wani sauti na sheshshekar kuka mai ban
tausayi suke fita. A zuciyata ina cewa
ko almajiri mai dan kanzo aka, ajiye baza ayi mishi irin
wannan, wula kanciba, ina cikin wannan halin sai ya Magaji ya shigo da kwanan da yaci.abincinsa muka hada ido yayi dariya
"hajiya Husna; kenan daman na dade ina son ganin ki saboda
wata magana, nace da shi to ai yanzu gani, yadanyi dariyar da
babu gaskiya acikinta,
ya ci gaba "idan kika yarda da abin dazan fada miki, to dukkan matso lolin da kike fuskanta agidan nan sunkare"
sai nayi saurin daga kai na kalleshi dan ya sosa min inda yake
min kai kayi yacigaba, yana sosa keya "innace ba" kace m?
Ina sauraranka"
"husna ki yarda in aureki sai inkai ki kauyanmu shi
kenan kinga kinhuta nayi miki gata inba hakaba, baki yarda da
kin aure ni ba to keda jindadin zaman gidan nan har, abada".
ina jin haka sai na mike tsaye "baka isaba daman da
haka kake yi min sharri iri iri to bana sonka ban kaunar mai
sanka,"
"ke dakata, dan ance ana sonki harda wani fiffike wa
idan namurda kanbuna dolene ayi dani" magaji mai wamki ya fada yana dariyar mugunta
nace dashi ta Allah ba taka ba" nawuce nabarshi anan
yana cije yatsa.
Yau ranar lahadice haka kuma su Mana sun tafi
unguwa shi kuma Yaya, bayan zuwa aiki masu aiki, suna can
bangaren kicin sai ni a tsakar gida na debo kayana ina
12
RAYUWAR KENAN
wankewa sai naji an yi min sannu na juyo naga Yaya atsaye
yana kallona na ce dashi
wanke"
"sannu da zuwa"
"kema sannu da wanki ga karona nace to kawo in
nan da nan yayi murmushi "Allah sarki kanwata da
wasa nake yi wannan ma da da hali da bazaki shi ba" na
kalleshi nace
"haba Yaya inbanyi ba mai zanyi"?
sai na ga ya girgiza kansa to idan kingama ina da
magana, ki taho mun da abinci na.
Bayan na kamala komai na nufi dakinsa tare da sallama
na ajiye foot filas akan tebil yana kallon tashar ALJAZIRA, kai
na asunkuye domin tunda na shiga idonsa yana kaina nadaga
kai domin ingaisheshi amma abun mamaki sai na kasa don
kallon nasa ya canja bakamar yadda na saba gani ba.
Nace "Yaya, gani ai, ina har yan zun bai dawo daga
duniyar da ya tafiba, nasake yin magana amma ina, sai nace
"ko bakajin dadine in kawo maka magani?"
Aiban tsaya jin amsaba abin yawuce tunani na juya
wata ke da wuya, sai naji yaruko hannuna a tsorace na kalleshi
yace "ina zaki?"
nace "magani zankawo maka"
"akace miki bani da lafiya?
aimuna dada hada ido sai kunya takamani, na sunkuyar
da kaina sannan nace "gani nayi- "kika ga me?"
"wallahi tunanin mani abokina dana rasa nakeyi
munshaku da juna muna kaunar juna, kuma nake neman mai
irin halinsa amman narasa shine abin yake damuna,"
sai jikina yayi sanyi nace da shi,
"mutuwa yayi?" yace e, nace "Allah yajikansa ya baka
wani mai kamar halinsa, nagari dadai yaga na shiga sosai sai
yakwashe dada riya, yace aiya bani kamiuli managarai
maisauri muka hada ido nace
13
RAYUWAR KENAN
"lah, Yaya, a ina. Sai yanunani. abin sai ya ban
mamaki, sai nace dashi a ina kaga an taba abota mace da
?
n
"ana yi mana" "a'a ni dai ban taba ji ba"
to yau zaki gani Husna dan haka amincewarki nake
nema in baso kike yayan naki ya higa wani hali ba"
acan cikain zuciya ta kuwa maganar nake ta juyawa k
mai yuwuce? Can zuwa wani lokaci naji ya kira sunana wanda
shine ya katseni daga kogin tunanin da na fada ya ci gaba da
amagana "ya naga kin yi shiru?"
na ce dashi "shawara nake yi"
"dawa" nace "da zuciyata mana" shima sai yayi shiru
yana sauraron mai zan yanke. Can ya mike tsaye to kanwata bari in baki lokaci abin da kika shawarta nanda rana ita yau kin
fada min shiga gida.
mana
anihsi aine kaga anayi abata mace da namiji? Anayi
Acan kasa mai tsarki kuwa, Alhazai sun kammala aikin
Haji lafiya kowa sai kokarin komawa kasarshi yake haka
Abbanmu wato mai gidan dana nake zaune yayi wo waya gida
ranar talata azo iyafot din Mallam Aminu Kano, adau koshi,
dan haka, kowa sai farin ciki Mama sai hidimą, ta keyi maigida
zai dawo a kasa su Magaji wanke gida ni kuma goge-goge ko
ina mun tsaftaceshi.
Ran talata ta shedawa Yaya ya dauko sabuwar motar
Abba. Ya debi yara suje filin jirgi. Bayan angama harhada
kayan abinci muka yi sallah ishsha sai kowa yadau kwaliya
haka itama uwar gida tayi kwalliyar taran maigida sai na dubi
kaina nikadai ce, dakin datti ina son ni ma inyi kwalliya kamar
yadda kowa yayi amma ina tsoronyi ace saboda me.
Da Musalin tara da rabi na dare Yaya, yashigo yayi
kwalliya mai kayatarwa dan kuwa tayi yi mishi kyau sosai sai
kamshine yake tashi ya kalleni ya hada rai ke maiyasa baki
shiryaba. Koba za kibane? Nace zani to sai kiyi sauri, ciki
14
RAYUWAR KENAN
hanzari nashiryatsaf yace mufito su Fati suna gaba ina baya
dasu sai ga, Magaji, munci karo dashi
"a'a 'ya'yan Mama har da ku za'aje ne? yakai kallon
kaina yace "amman dai ke ba binsu zakiyiba?
Nace bin su zanyi mana" ina tafiya ina, bashi amsa,
sai naji Mama tana kwallamin kira' ina zaki uwar shishigi?
Nace yayane yace nima mutafi"
"ku tafi gidan ubanki, ai ba irin kune suke zuwa iyafot
dinba suma Ubansu zasu taro, in kuma kinyi zuciya kine mo,
naki uban".
Wayyo ni Husna (Allah) kanuna mini iyayena nan take
kwalla tafara kwararowa daga idanuna. A Can kofar gidan
Yaya sai hon yake tayi da yaga ban fitoba sai ya turo Salim in
zamu mu tafi" lokaci yana kurewa cikin daka tsawa da daga
murya tace
"Au da baku tafi ba? E, Husna, muke jira" to kace
injini ba zataba, mai zai faru sai, ga, Yaya, haba Mama, ni nace
itama tazo muje yazaki hanata" gaskiya sai dai dukkansu suyi
zamansu"
Tace "iye haka kace daniyar masu gida bazataba gayar
gwal ko? to me idan kace ba zaka, dauko shiba Yayi daidai
shikuma muna fikin sai cewa yayi
"Nura kabi maganar mahaifiyar ka, ita inaga aiki zatayi
ai nan ya daga masa hannu tare da wata irin tsawa rufe mana
baki muna fiki"
ya juya afusace can sai muka jiyo kukan Fati, ya korata ya
tafi da salim, mazai faru sai kawai sai Maman tayo kaina
tarufeni da duka tana faman zagina tana cewa narabata da dan
uwanta baya santa saini, sukuma, sai dada zaugata suke mama,
cewa take yanzu tafiya yayi ya barki saboda wannan shegiyar
kara mata" dan ubanta, har tana cewa
"ungo takalmi, kar hannunki yayi zafi
15
RAYUWAR KENAN
niko a tsugune nake ina ihu ina bata hakuri da kyar yan aiki suka karbeni. Mama, cewa take akyale ni ta koya min han
kali, ai wannan kadan nagani.
Na nufi dakin da na ke kwana, ina zuwa nayi Ruf da
ciki kan dagargajajjiyar katifata ina kurshe ken kuka ina cewa
ya Allah) ka hadani da iyayena koda a marfarki ne can sai naji
ana kici-kicin shigo da kaya kofar gidan da kuma cikin gida ya
cika da haya naji ana ta barka da zuwa Alhaji..
Bayan ya, shigo sittin room dinsa haka kowa da kowa
hatta yaran gidan su Ramlat suna gun kowa yana gai da Abba,
yana tambayarsu anyi Salla lafiya ya karatu kai harda masu aiki
ba abarsu a baya ba.
Sannan yadau ko wata jaka yafito da tuffa da sweet
yaba kowa bayan ya dan nutsu sai yafara waige waige
"ina Husna" ya tambaya kowa yaya shiru sai Yaya
yace "ko tayi barcine"
"Salim jeka ka gani" ya dawo da gudп
"Abba gatanan ba barci take ba kuka take yi"
"Sallamu Alaikum" na durkusa tare dayi mishi sannu
da zauwa" "haba Husna, nayi fishi da idan ki biyu, amman kina jin, dawowata bakizo ba ko wani abin akayi mikine"
"a'a bani da lafiyane" shine kike kuka? "Maiyake
damunki,"? "ciwon kai da zazzabi" ina daga kaina mukayi ido
biyu da Mama, na sunkuyar da kai.
Tace "munafuka kin sunkiyar dakai tun da ciwon
karya kike,"
"ah, dan maiyasa bakya jin maganane, nadade ina nuna miki cewar yarinyar nan fa amana ce, kiriketa tsakani da
(Allah) amman kin kasa ganewa ki taba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 13