da ke ba
Husna."
Na amsa "Ba sonsa ne ba na yi ba."
"To mc ye na kukan? Ni dai ban ga abin ki tare da shi bа,
Yarinma ga kyau ga usili, ilimi ta kowanc 6angare ke da za ki
yi murna, da samin miji nagari, ni kuma abin da ya sa na amsa
na riga na ce ke 'yar uwata cc, kin ga bai kamata ya nemi wani
abin a guna in hana shi ba, balle har ga shi na ce ke kanwata
ce."
Cikin matsanancin kuka na ke magana. "Ni abin ikonki ce,
na yarda da duk hukuncin da kika yanke a kaina, sai dai ina
fargabar abin da ya faru a kaina a can baya, yanzu ma sai na ga
iyayena domin an ce ranar wanka ba a boyon cibi, ban manta
irin halin da na shiga a baya ba, daa nan na fara ba ta labarina
tun daga fara soyayyata da Yaya Nura har kawo azabar
barkonon da aka yi min, duk don ya ce ya ji ya gani zai aure ni,
kawo kwanciyata a cikin asibiti, har lokacin da na gudo ana
sauran sati daurin aurena. Ni dai tsakanina da ita ban san
42
wanda ya fi wani kuka ba, "Taho Husna ." Ta rike ni a jikinta
ta na rarrashi da goge min hawaye, "A gaskiya Husna ba
Karamar wahala kika sha a rayuwarki ba amman na vi alkawari
cewar insha Allahu ta zo karshe, sai Allah ya saka mi ki don
shi ba azzalumin Sarki ba nc, kuma bna dau alkawarin ni zan
share mi ki hawayenki. Haba 'yar uwata, yanzu don babu iyayс
sai ki ta zama haka babu aure? Ki sani shi Allah ba ayi mi shi
dole, don haka ni ce uwark. ni ce ubanki, don haka ki kwantar
da hankalinki ki kuma ban hadin kanki insha Allahu ba za ki
tozarta ba balle ki ji kunya zan shaida wa Dady da Momy
Batula maman Sudan da sauran 'yan uwana ke'na thatar in
har aka fadawa Yarima gaskiya ba zai musa ba, saboda ga
ya makance akan ki, ki share hawayenki kin ji 'yar gidan Aunty
don Allah dan yi murmushi in gani."
Nan dai Aunty ta ba ni dariya.
Akwai watarana, da hantsi bayan Yaya M. ya fita ta ce,
"Kanwata don Allah dan samo min abu mai dan sanyi na sha."
Nan na bude fridge na jero fresh milk, mango juice a bisa
karamin tire na ajiye a gabanta bayan ta kare masa kallo ta dan
yatsina fuska, "Ba ni son dangin madara kin san ina sha amai
suke sa ni gara dai lemon 'nice'."
"Lah Aunty kinkwana biyu ma ba ki yi aman ba."
"Kwarai daman likitan dama ya ce idan ya yi kwari zan
daina:"
Na dan yi murmushi. "Allah ya sauke ki lafiya, mu sha
shagalin suna."
Ta dafa ni, "Amin kanwata maza kirawo min su Kande."
Na je kusa da su na yi sallama babu wanda ya amsa, nan na
idar da sakon Aunty. "Aunty ta na son ganin ku yanzu." Na
juya na yi tafiya ta, na shiga babau dadewa ragowar suka shigo
ita kuwa Kande sai da ta jika tamula sai ga ta ta na wani
43
!
yamutsa. Aunty ta Kare mata kallo, "Ran uwar tuwo shi dade, me e faruwa ne?"
Take ta durkusa ta na gaishe ta, "lafiya kalau uwar gijiyata." Ta kalle ni. "Ki je dakina ki dauko min jakar da yayanki ya shigo da ita jiya."
Na amsa da "To." Jim kadan na kawo, ta na budewa ta
fiddo da daman kudi Kande ta na ganin masu gidan rana ta fara fara'a.
Aunty ta tambaya, "Yau mu na karshen watan biyu ko" То
lokacin biyanku kudin aikin ya yi, dama ku kuka ce sai wata na
biyu za ake biyanku ko?" Nan ta bada amsa har tana gyara
zama tana leka cikin jakar. Daya bayan daya ta baiwa kowa har
maigadi da dan'azumi, sannan ta miko min "Ke ma ga naki
Husna."
Ai tun kafin in ce wani abu idona ya cika da kwalla, ina
girgiza kai, "Wallahi ba zan karôa ba ni ba don ki biya ni na ke
zaune da ke ba."
Nan fa gardama takacame a tsakaninmu sai Kande ta hau
lakace min hanci "Munafukar banka kina so kina kai wa
kasuwa, ranki shi dade ba mu in bata so, daman ke bai kamata
ki karba ba, tun da ki naikrarin ke 'yar gidan ce, mune bare an
zo an fi mu shiga."
Ta dakatar da ita, "Kin ga Kande, ba na son rashin mutunci
a gabana kike fada mata haka? Don me ya sa ke ba kya son
zaman lafiya ne? To ki shiga taitayinki, ku tashi ku ban waje."
Haka ta tashi jiki babu laka, har ta je bakin kofa ta yi kiran ta,
"Ina so ki dama fura a bulandar nan, an jima muna da baki."
Ta dawo ta durkusa, "Ranki shi dade na dade rabon da in
ga bulandar nan.'
Take ta tambayc ta, "Wai shin don me ya sa sau tari in na
tambyac ki abu a gidan nan sai ki ce ba a gan shi ba?"
44
"Ehm...." Ta rike baki, "Ni na fada ta gudu, a barta ta
lalace, a kyale ta ta nemi mazau jama'a." Cikin bacin rai ta се,
"In gaskiya ne ki fada min mana."
Ta sunkuya u kai, "To ki yi min aikin gafara, uwar ſaki,
wallahi tun dayanyar nan Husna ta zo gidan nan ake yi mana
'yan sacc-sacc, rabona da ganin bulandar nan tun ranar da
iyayen gidanta su Yafanna suka zo ta dama mu su fura, ban
kara ganin ta ba, don haka ku tuhume ta, Allah Ya hada mu da
6cra..."
Ai tun ma kafin ta Karasa na zunduma ihu, nan fa hankalin
Aunty ya kara tashi, ta hau Kande da fada ta inda ta shiga ba ta
nan ta kc fita ba, "Ki rasa sharrin da za ki yi mata sai na sata, to
ni na riga na san halinta ba barauniya ba ce tun daga dakina za
ta fara dabarauniya ce, a dai nemi 6arawon ko a ina ya ke,
amman ba dai Husna ba, saboda haka kihada kayanki ki bar
min gida akan Husna zan bata da kowa."
Ko sauraren hakurin da magiyar da take yi ba ta yi ba, ta
hayc sama ta bar mu nan."
Kusan la'asar sakaliya yaya M. ya dawo ya hau sama ya
sami gimbiyarsa ita ma ta ci kuka fusar nan babu walwala, don
kuwa ko irin tarar nan da take yi mishi bai samu ba. Cikin
sanda ya tsaya a bayanta tare da kare mata kallo, bayan ya
fahimci akwai wani abin. Cikin nutsuwa ya kira sunanta, tare
da tambayar ta, "Me ke faruwa?"
Ta zaiyane masa abin da yake faruwa, take cikin bacin ya
tambaya, "Yanzu ina take?"
"In ba ka gan ta a falo ba watakila tana dakinsu."
"Ki ka ce kin sallami Kanden, amman na gan ta a tsakar
gidan? Taso mu je."
Ta biyo bayansa har zuwa inda na ke a kwance, ina faman
kuka, suka tsaya a kaina ya kira sunana, na dago káina muka
hada ıdo, "Kin ga in da ıdanuwanki suka yi ja suka kumbura
kuwa? Haba Husna me ya yi zafi haka za kı damu kanki a
45
kwan wata Kande. To wallahi sai na đau mataki a kai, zu mu je."
kira,
Ya
"Kande!
shige
Ke
muka bi shi a baya, yana faman kwalla tva ta Kande!"
dade."Cikin kidima ta fito ta durkusa gabansa, "Ga ni ranka ya
hada
Ya daka mata tasawa, "Kin ga ban son dogon zance maza kayanki ki bar gidan nan tun ranki bai 6aci ba. Ko yanzu na sa 'yansanda su yi akon gaba da kc."
gijiyata."
Take ta rike Kafar Aunty "Na tuba na bi ki ya uwar
Aunty ta janye Kafarta, "Kin ga babu ruwana. Husna da maigidan za ki bawa hakuri ni na yi iya nawa tun da ba ki yarda ba shikenan."
Ta na wajen a durkushe ya nufe ta da bel suka kasa tsere har sai da ya raka ta bakin get, daga nan gidansu ta je wajen Hajiyarsa, ta na kukja da koron ta ba mu hakuri muna zaune sun sani a gaba suna rarrashina tare da tambayata me ус dalıhna na kin karbar kudin sun yi min kafan ne a kara min? Na girgiza kai, wasu zafafan hawayc na bin kumatuna, "Ga ni na yi ban da bukatar su, dukkanin wani nauyi nawa kun dauke min, ci da sha, da dawainiyar karatuna, kula da rayuwata wanda ko da a gaban iyaye na na ke iyakaci kenan, watakila
ma in ba masu hali ba ne ba zan samu kamar haka ba, duk wani abu na samu a rayuwa banda abu daya."
Nan take suka zaburi, "Mene ne shi mu yi mi ki?" "Iyayena."
Kallo na suke yı cikin tausayawa har da ajiyar zuciya, "To Husna wannan al'amari sai dai mu ci gaba da shaidawa Allah
domin shi maji du'ai ne."
Mu na zauna Kanin Yaya ya shigo bayan sun gaisa sai ya
sanar mi shi Hajiyarsa ta na nemansa yanzu. Ya mike tsaye yа
na fadcin, "To Husna ni fa ba zan bar nan ba sai kin sakı ranki,
kin yı murmushi, amaryar yarima."
46
Aunty ta ce, "Da ya ke babu kari, in kuwa ba ki yi ba zan yi fushi ko ni ma in yi kukan."
Shi ma take ya fara murza idanu, "Tun Ja kika sa swectyna kuka ni ma sai na yi. Habawa, nan take abin ya ban dariya har da kyakyatawa, gaba dayansu suka fara faſin "Yawwa ko ke fa."
Sai ga shi ya dawo rai a бacc ya na ta fanab tsaki, da muka tambayc shi lafiya, sai ya ce Hajiya ce ta ce ya yi hakuri Kande
ta dawo in ta sake duk matakin da muka dauka babu ruwanta,
"Amman fa na ce sai ta bawa Husna hakuri tukuna." Ya kwalla
kira, "Ki na ina mara mutunci, zo ki ba ta hakurin mana." Ta shigo jiki a sabule ta durkusa tana "Don Allah Husna ki yi hakuri ki yafe min."
Na kalle ta, ina yin murmushi, "Na hakura komai ya wuce Kande."
Muna zaunc har kusan sha biyun dare suna yi wa yarima kamfen, wai lalai sai na amsa ina sonsa kuma in ba shi izini
gobe ya zo zance, kai sai da na ba da amsa sannan hankalinsu
ya kwanta kashe gari da la'asar ya zozo ba nanan Aunty ta aike ni
tarc da shaida min in dawo da wuri, saboda zuwan nashi,
amman ina sane na je na yi zamana sai kusan biyar da rabi na
dawo na same shi zaine a falo su na hira da ita na durkusa zan
gaishe shi, ya yi saurin kauda kai, "Ni dai na yi fushi, ba zan
amsa ba, domin na ga alamun tun ba a je ko ina ba na zama mijin-tace. Allah-Sarki ni Yarima."
Na kalli Auntu, muka sa dariya, na shige daki da gudu don ajiyc sakon hannuna, AUnty ta biyo ni, "Husna me kike yi ne
tun dazu ga Yarima ya na lambu yana jiranki?"
Take na bi na diririce na rasa anin da yake min dadi. Shin kwarjini yake yi min ko tsoronsa nake ji ne? A zaune na same
shi bisa kan kujerar roba na yi sallama, ya amsa tare da nuna
min kujera kusa da shi ina zama ya gyara tashi yana kallo na.
"Ranki shi dade Husna,ina fatan kin ji sakona na dade ina
sauraren amsarki shiru ko me ya sa, ko ban yi mı ki ba ne?"
Na yi shiru tare da dukar da kaina.
"Ina son ki ba ni amsa, saboda in son in kai magana wajen
manya."
Ina jin haka na ba shi amsa, "A gaskiya ba yanzu zan yi
aurcba."
"Sai yaushe?"
Nan ma na yi shiru.
A hasale ya fara yin magana, "Kc dakata, kar fa ki ga don
na ce ina son ki ki nemi wulakanta ni, ban rasa wacce nake so
ko suke so na ba." Ya mike tsaye, "Kin ga dakata, kin kuwa
san ko ni wanc nc?"
Ai ina jin haka na ji sam na tsane shi, ban san ganinsa a
kusa da ni, wai har matsayinsa yake nema in sani, nan take
kuwa na yi tunani, tunda ya na tunkaho da asali, ni kuyma in
har ya ji nawa a ya zai kalle ni? nan take na taka mishi birki,
"Ka gani ban nemi jin ko kai wane ne ba, don haka ni din nan
talaka ce, sai ka je ka nemi dai dai kai." Kawai sai na bi hanya
na yi tafiyata na bar shi nan. Tun daga nan na san tamu ba za ta
daya ba, na ga alamun yana da jiji-da-kai da nuna isa.
Safiyar Juma'a an tashi da hazo sakamakon sururun sanyin
da ake yi, don haka kowa yana daka, in ba da gaske mutum ya
yi ba ba za ka ankara ba za ka ga rana ta yi kamar su Aunty tun
da suka koma barci bayan sun sallar asubahi, ba su farka ba sai
bayan sha daya har na fara yin tunanin lafiya yau Yaya bai tafi
wajen aiki ba, to ko kiransu zan yi ta wayar starcomms ne?
Ashc a dai dai lokacin ciwo ya tashi Aunty tun tana zirgazirgar zuwa toiltel ita kadai har ta gagara fitowa take ta ga wani
irin ruwa mai yauki yana bin cinyarta, nan ta fara kiran
"Honcy! Honcy wayyo Allah zan mutu!"
48
Ina shi kam sharara minshari ya ke ko da ta ga haka sai ta
dauko soson waka ta jefe shi da sh a fuska, firgigit ya farku
yana fadin, "Me ke faruwa?"
Fadi ta ke, "Ciwie ka zo ka cire min."
A gigice ya nuic ta tarc da tararirayarta, "Taso mu je
asibiti, haihuwa ce kin ji my swect."
Nan take ya yi wa Dan azumi izinin ya fito da mota kusa
sannan ni ma ya kira ni maza in hawo a dai dai matattakala
muka haďu ni ma cikin kidima na taya shi muka kai ta mota, ya
kalle ni "Maza ki je ki hado kayan da ki ka san za a yi amfani
da su."
Na shiga da gudu, tun dana hau saman nake ta bilayi na ma
rasa mc zan dauko, sai diri-diri nakc yi saboda tsabar gigıcewa
da kyar na sami kaina ashe ma ta riga ta hada kayanta a cikin
jaka, ina fitowa na tarar da Dan Azumi ya dawo jirana kawai
yake yi ina zuwa na tarar har sun shiga, na tarar har sun shiga
da ita dakin haihuwa sai Yaya yana ta faman zirga-zirga da
waya a hannunsa ya na sanar da 'yan uwa don haka kafin dan
wani lokaci wajen ya cika hatta da Hajiyarsa yau ta ajiye kunya
ta yi saboda ta na murnar ganin jikanta muna zaunc mun yi
ngum kowa addu'ar Allah ya raba lafiya yake yi can sai ga
wata nas ta leko ya na ganin ta ya nufe ta, "Ya aka yi ne Nas?"
"Yallabai congratulations!"
Cikin zumudi duk muka taso a na tambayar me aka samu?
Abin ya bawa Nas din dariya ta ce ina tukuicin fadar albishir.
Take ya zura hannusa a cikin aljihu ya kwakuso iiahirin kayan
da ke cikin, waya, carbi, kudi da sauransu ya ce ga su.
"Na gode Yallabai, ina yi maka albishir an sami BABY GIRL."
Nan take ya kutsa kai ya shiga fakin ya same ta bisa gadon
haihuwar ta na faman numfashi, ya isa gare ta ya tsaya yana duban ta cike da tausayi "Sannu my sweety ina beauty BABY GIRL din da ki ka hatfar tmin ?"
49
Ta nuna da hannu, "Honey ina ka tafi ina ta kiran sunana,
cikin shagwaba take yin magana.
"Ga ni sweetyna."
Can suka jt an ce, "A'a, yallabai, wa ya ba ka izinin
shigowa ba ka san ba a shigowa ba musammam maza."
Ya kalle ta, "A gaskiya ba zan fita ba, sai da Beina." Ya na
tsayc ana thrigarda da shi har sai da aka yi mata wanka aka ba
shi tare da tura Auniy dakin hutu, gaba daya mu ka bi su dakin
tun da ya dau 'yat yake ta faman kallon ta ya na yi mata addu'a
nan fa aka dunga rige-rigen faukarta da murna da shewa gaba
daya waya nas fadi ta ke "Lallai yau Ambasado Yakudima ya
yi amarya."
Momy batulu ta ce "Ina gidana ya fi karfinta sai dai gidan
kwamıishina. Ga Hajiya Karama nan ta zumburo ba ki in dai za
ta shiga kicin ta yi wanke-wanke bisimillah."
Nan fa muka yo caa ni da su Hassana da kannen yaya "Ina,
ai wannan ta sha gabanku haka dai nas din suka yi ta shigowa
daya bayan daya suna taya murna da ya ke asibitin na gida ne
sun san kowa suman Asibitin Asma'u Memorial an samo sunan
ne saboda sunan Ranwarsa Asma'u da ta bata daga baya aka
kawo mu su labarin ta rasu, shi ne saboda tsananin kaunar da
mahaifinsu Dady yake yt mata ya bude asibitin da sunanta, ya
dauko kwararrun likitoci va sa a ciki don kawai su taimakawa
dan gida wadanda suka da bukata kyauta daga nan musu ya
kaure tsakanin Kannen yaya da Kannen Aunty mu muna cewa
yarinyar ta fi kama da mu su masuna cewa kama da su ta yı,
muna cikin wannan hayaniyar sai ga Yarima ya shigo bayan ya
gai da kowa ya kuro min ido, "Husna rowar ta ki za kı yi min
ne"
Cikin kunya zan mika mishi Usaina ta shige gabanmu,
"Aunty Husna kar ki ba shi sai ya biya kudi tun da bai zo da -
wuri ba."
50
Ya hararc ta da dunkujea hannu zai kai ma ta naushi. t3
zulle daga nan ya shaida mana, "Daga Airper na ke na je taro
dan Sudan, jirgin bai zo ba sai ranar Laraba. Na fada mi shi an
yi hailuwa shi ne ya ce zai tsaya tukun su taho da maman
sudan, nan fa su Hassanar suka fara tsalle da murnar dawowar
yayansu Al'amin, da kuma kakarsu ta wajen uwa, Ambasada da
Kwamishina kuwa dukkansu ba sa gari aka yi haihuwar amman
babu wanda bai ji ba, kuma dukkansu sun yo waya suna murna
musamman dady, kamar ya yi tsıntsu daga Senegal ya taho.
A ranar da aka yi sallama tun da tahaihu lafiya kuma babu
wata matsala bayan kwana biyu Kwamishina da kansa ya zo ya
ga jikansa cikin ladabi da girmamawa Aunty ta gaishe'a na
kallonta ya na kallon jaririyar, "Sannu kin ji Raudat, Allah ye
kara lafiya kin ji." Ya na ta yabonta shi ma, yayan ya zo
gabansa, "Yallabai ni fa?"
Ya kalli yan wajen, "Kun ji fa kishi, to kai ma haka."
Gaba dayanmu muka kwashe da dariya, babbam mutum da
shi amman sai wasansa yake da kowa babu ruwansa da girman
kai, haka shi ma dady yana dawowa a sukwane ya taho don
murna kamar ya maida Aunty da yarinyar ciki, sannan ya hado
shatara ta arziki abin dai sai wanda ya gani, su Hajjagana kuwa
suna ganina aka fara tambayar "Ta haihu? Haka dai muka
kasance cikin farin ciki gidan kuwa baya daukewa da jama'a
har sai mun rufe shi, in dare ya yi ni kuwa tun da aka yi
haihuwar ba ni da zama daga zuwa kasuwa sai wajen teloli
kaya ktuwa ba na iya irga adadinsu.
Wata rana na dawo Aunty take fada min "Husna yanzu mu
ka gama waya da rigimammiyar tsohuwar nan."
Na tambaye ta, "Wace ce fa?"
"Mamam Sudan mana. Ki na ji fa aka ce sai ranar Laraba
za su taho,to yanzu ta na can ta na yi musu rigima sai ta taho,
shi ne ta yo min waya wai in shaida wa dady ya je su taho
tare."
51
Na rikc baki, "Shi kuma Yaya Al'amin fa?" "Oho, ita ta sani ni abinda ya ke ban mamaki shi ne tun da
mamanmu ta rasu ta tsani ta zo Nijeriya sai dai mu mu je
saboda wai in ta zo gani take yi kamar za ta ganta, kin ga rabon
ta da nan tun bikina amman Al'amin yayo waya ta dame shi
nan dai muka ta yi dariya, na cc "Allah Sarki mama yar tsohuwa, wallahi har na matsu ni ma in gan ta."
Ranar da Aunty ta cika kwana biyar da haihuwa ranar ne su
Maman Sudan za su dira a garin maiduguri, gaba daya jikokin
suna gidan Aunty saboda nan za ta sauka cikin masu taro ta har
da daddy misalin karfe uku na yamma ina daka ina shirya
kayan da aka samu na BABY na jiyo tsalle da murna ni ma na
yi maza na yo falon gaba dayan jikokin momy da Aunty wasu
sun rike ta wasu sun rikc Yaya Al'amin ana ta faman maraba
da lalc, yaya da Yafanna fadi su ke "Kar fa ki yar da ita ni kam
ina wajc daya ina kallonsu kawai yayin da muka hada ido da
ita kuwa takc ta bi ta diririce ta nufo ni ta rungume tana fadin
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN Raudat yaushc aka
ga Asma ba ku sanar da ni ba, nan fa ta fashe da kuka gaba
daua wajc aka zuba mana ido kowa jikinsa a sanyayc AUnty ta
dafa ta "Haba mama, duk tsufa ne haka? Wannan ba Asmaun
ki ba cc, sunanta Husna, 'ya ce wajen Yafanna, ta kawo ta mu
zauna tare shi kansa Al'amin kallona ya ke ya na kara
jimamawa, "Kai ban yarda ba, naka naka ne, abina ko dikin
dubu ya shiga si na gane shi."
Gaba daya ta basu dariya, 'yar autanta mai suna Asi fadi ta
kc, "Haba mamata, in dai ba kwacc za ki yi wa iyayenta ba.
Aunty ta ce "So ta ke ta zama hankaka mai da dan wani
naka: Su dai nan suka sa ta a gaba suna dariya ga shi ba ta fasa
fidda hawayc ba, ba ta kuma cika ni ba, ni ma ganin haka
tausayinta da ni kaina ya sani hawaye, domin ina jikinta ina jin
mai da numfashin da ajiyar zuciyarta, nan dai cikin rarrashi
52
4
Aunty ta kawo mu s" Iemo da fresh milk, ta sha ni ma ta takura
sai na bude bakina ta bu ni.
Tun da lokacin kwaya ya yi Aunty Rauda ta kasa yin
barci sai tunanin abin daya faru da yamma ta ke. "Anya kuwa
in an bi ta 6arawo ba za a bi ta ma bi sawu ba? nan take labarin
da na ba ta na cewar iyayena na fito nema ya dawo mata sabo
haka ni ma Husna tun da na kwanta sarn na nemi barci na rasa
sai juyi na ke tare da tunanin cewar anya kuwa ba ni ce 'yar
uwar Aunty da aka ce ta mutu ba? Ai ita 6ata ta yi daga baya
aka ce ta mutu ni ma kuma tun ina karama aka tsince ni an cе
an tsince ni a Maiduguri ne, sannan duk bakan da aka yi sai ya
tambayc ta, ni kanwar ta ce saboda ganin kamar mu daya
sannan ga babban abin al'ajabin da ya faru na dazu lallai ina
shakkar dakyar ni in ba kanwar Aunty Raudat ba сс.
Can na ji ana yi min gargadi a wani bangare na cikin
zuciyata, "Ke Husna kar ki fa yaudari kanki domin in kin fada
ma ragowar ba yarda za su yi ba, ba ki ji lokacin da maman ta
ce idan su Aunty da Al'amin sun yarda lokacin da ta bata ai ita
Batula da wayonta ba sai ta ce wallahi ba za ta tantance ba
domin wani in ya girma kamanninsa canzawa su ke, to tun da
ba su yarda da zancen ba ke, sunanki Husna ita kuma Asma'u
take. Na tuna da suratul IIASHARI wacce kullum sai mun yi a
gaban assembly a makaranta, kamar haka, Bismillahi Rahmanir
Rabim, Huwallahu Kalikul bari Ulmusawwur lahul asma'ul
Husna. AllahuAkbar! Ni Husna na gode wa Allah.
Zumbur na mikc na shiga toilet na yo alwala na fara jero
nafila tare da godc wa Allah mahaliccina da ya nuna min
wannan rana. Sauran bayyana ta kawai nake jira Allah Ya
ganar da su, ya sa karshen wahalar ce ta zo amin. Ina zaune
ban san lokacin da Sarkin 6arayi wato barci ya dauke ni ba,
cikin barcina na yi mafarkin wannan matar da na saba gani a
mafarkin da fararen kaya, t nui ni fuska cike da annuri ta na
53
yin murmushi, ta miko min manyan goro fararc kal, ta na min albishir kafin in yi ma ta magana ta bace na yi firgigit na farka na yi juyi ina yin salati wani abin al'ajabi ina juyawa ne na yi ido biyu da maman Sudan, tana tsaye a kaina ta na zubar da hawayc, na tambaye ta "Mama lafiya?"
Nan ta ga hawayc, "Daman zuwa na yi in tashc ki ki yi sallar asuba, ashe ma kin yi, na gan ki kan sallaya."
Na mittsike idanuna, "Wallahi yau na makara, wannan shimfidar tun tajiya се."
Nan ta ce, "To shì ne na ce ki zo mu kwana da ki ga na yi barci ki ka gudo ko?"
Na dan yi murmushi, "Ki yi hakuri yau tare za mu kwana Mamata."
Ta dafa ni, "Na hakura maza ki yo alwalarki kin ji Asma." Haka ta ke kira na tun da ta zo tun ba na amsawa har na ke
amsawar, musamman yau da da kwarin gwiwa na amsa. Nan da nan mu ka shaku da ita ko abinci za ta ci sai ta neme ni im
ma anguwa za ta je tare mu ke zuwa, yaya da jikokinta su yi ta tsokanar ta.
Ranar suna aka rada wa yarinyar suna Hajiyar Yaya
Muhamud amma Yusrah mu ke kiran ta, gidan ya cika 'yan
uwa da abokan arziki kamar su Yafanna, da jama'arta, Uwalc
Maijego daga kasa kasa har da yayar 'yar Yarima Aunty
Bilkisu da take aure a Birnin Tarayya Abuja Aunty tayi kirana
ta na shaida min ga Aunty Bilki ta na son gani na, ashc Yarima
ya je ya yi ma ta maganar ki, don haka maza ki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 13