na dan jima"
Hajiya ta bude kenan tafara gani sai muka ji gidan ya
rude hayaniya ashe lokacin da Yaya ya shiga falon sai ya tarar
Fati tana fada musu abin da ya faru ita kuma ta cika jira kawai
take ya shigo shi kuwa gogan naka bai tsaya wata-wata ba ya
tsallake Mama da Aunty Ma'u ya nufi Fati ji kake tas-tas
yadinga hada mata mari dama da hagu mai zai faru sai itama
maman ta tashi ta rufe shi da duka tana cewa
"sai ka fada min abin da Husna take shiga dakinka take
yi?" Yace "a fusace son ta nake kuma auranta zanyi a dai dai
lokacin Hajiya ta shiga tsakaninsu tace Haba sai ta daketa
sannan Aunty dan munafurci da batayi magana ba sai da taga
Hajiyan maidugurin tasa kuka tana cewa tunda Mama ta daki
Nura itama sai tazo ta daketa". Ita Kuma mama sai faman fada
take tana cewa Yaya "ba dai kace Husna ka ke so ba? Wallahi
baka isaba ka yi kadan sai munsa kafar wando daya da kai.
shine akan tsintacciyar mage mara usuli har zaka zo kana
dukan mini 'ya, Kuma auranka da Ladidi kamar anyi angaтa
can.
Hajiya tace wallahi baki isaba kinyi kadan inhar
kinga Nura bai auri Husna ba sai dai m Allah bai yiba amman
aure kamar anyi angama tunda Nura ba mace bane da za'ayi
57
RAYUWAR KENAN
mishi auran dole. ko macece sai ya zabi wanda yake so balle
Shi
ita Kuma aunty ma'u maganar tai mata zafi harda cewa
hajiya ke kaka ce meye nakji aciki? Kibari 'ya'yan su zabar
masa wacce aka san usulinta yar manyan mutane wacce ta gaji
arziki ba gaiyar tsiya ba." Hajiya ta dakatar da ita da hannu
"to uwar shishishigi ba a sa da keba balle ki dauka
yarin ce yace baya so sai dai kiyi hakuri" ita kuma tace aiba ke
çe kike da iko da ubansa ba" hajiya tace "nice kuwa mai iko
dashi tunda ina da iko da ubansa"
Ita kuma mama tace in har ita ta haifesh ba da
yawunta ba in ya aure ta" sai hajiya tace "baki da abin cewa sai
abin da ubansa ya zartar" ta koma kan Fati takare mata tatas,
Kuma tace da a ce Nura ya hukunta ki inhar kinyi ba dai-dai ba
mara kunya fi tsararriya.
Shi kuma yaya duk abin nan da ake yi yana tsugune
yarike kansa da hannu da alamun ciwo yake yi mishi ga idon sa
ya yi jajawur Hajiya ta kamo hannun sa suka fita tana ta
rarrashinsa tare da bashi magana tace ya saurari zuwan
mahaifin sa, suna shiga daki sukai kirana shiru suka tambayi
masu girki akace nafita da gudu, ai sai Yaya shima ya fita da
sauri ya nufi gicansu Ramlat dan aza tonsa can zannu fa, ni
kuwa yadda akayi ina tsakar gida ina sauraran kalamin da kowa
yake yi maganar dai na tabbatar akan yace yana so na ne shine
bayan zagi da cin zarafi iri iri har takai ga dukan sa naji mutun
saurayi kamar Yaya yana kuka, ai nan da nan naji kamar wuta
ake zuba min ajikina zuciyata in ban da tafarfasa babu abin da
take yi na kuma tausaya wa Yaya na kuma tausayawa kaina
domin mina jawo mishi.
Na riga na gigice narasa abin yi sai naja mayafina
nafita da gudu sai gidan su Ramlat ina shiga kuka yaci karfina
duka kansu suna tsakargida har Baba Sani na fada kan cinyar
Ummin Ramlat ina kuka hankalinsu yayi mumunan tashi suna
58
RAYUWAR KENAN
tambayata me ya ke faruwa, da kyar cikin shashshekar kuka
nace
"Yaya ne" ban karasa ba na dada sa kuka Ummi ta
jijjigani "mai Nuran yayi miki? Dukanki yayi? nagirgiza kai a,
a Mamace take dukansa" ta dafa kirji "take dukansa" inji Baba
Sani ya mike yana cewa innalillahi da hanzarinsa, yaunfi kofar
fita a daidai lokocin Yaya shima ya shigo da saurinsa yana
cewa kwallamin kira, sai sukaci karo ya kamo hannunsa
"muje tana ciki" bayan yazauna, Baba Sani yayi shiru
yana mamakin wannan al'amari sannan yace "muyi hakuri har
Allah ya dawo da Abba. Da yake daman yayi tafiya ne yau ko
gobe muke sa ransa. yace
"yanzu idan na koma gida sai tahuce a kaina, ni kuwa
babu irin abin da ban raya a zucigataba, akan abin da ya faru
ina ga bazan amince da aurena dashi ba, saboda tun ba'je ko ina
ba haka ta fara kasancewa balle ace na aure shi gaskiya
hankalina yana kan iyaye na.
Ina ga abin da zai fi dace in tada rigima idan hajiyar
maiduguri zata tafi in bita ko na huta da wannan masifar dana
ke ciki, shima Yayan ya huta kai haka ma zan yi.
zancen zuci yafito fili naji murya a bayana na
tambayata mai za'a yi? Ramlat ce, na warware mata shawarar
dana yanke tace indai sun yarda in bi hajiyar ko yan watanni
nayi sannan idan na huta sai in dawo. Na kale ta ido ackin ido
nace
"lallai ma Ramlat indawo fa kika ce,? bazan iyaba."
A can Kuwa Yaya B.Sani da kuma hajiya suna shawara
cewa a sa mana rana aga ta tsiya.
A wannan ranar ne Abba ya dawo da daddare, ba'a
fada masa komai ba domin abar shi ya huta sai da Allah ya
nuna mana safiya sannan Baba Sani ya shigo suka tura akira
wo Yaya yazo, sannan hajiya ta fara fada masa abubuwan da
yake faruwa har irin magan ganun da Mama da Yayarta suka fada mata.
59
RAYUWAR KENAN
Baba Sani sai hakuri ya ke bata shikuwa Abba bakin
ciki ya hana shi yin magana sannan yace
"hajiya dan Allah kiyi hakuri ki daina kuka insha Allah
karshen wannan rashin mutunci yazo yanzu mai kike ganin
zamu yi?" hajiya ta nisa sannan tace
"abin da yafi ka hada yaran nan aure tunda suna kaunar
juna, in kai haka hankalina zaifi kwanciya, sannan kuma yanzu
a nan za'a yi musu baiko ina nufin a bashi ita tunda kune
waliyan ango da amarya". Baba Sani yace
"Alhamdulillah in akayi haka an kyauta," nan da nan
Abba yai kiran sunan Nura yai saurin amsawa tare da maida
hankalinsa "ka tabbatar kana son Husna tsakani da Allah?"
Ya gyada kai to sai kayi min alkawarin zaka rike ta
amana ba cuta ko cutarwa kai ne uwarta kai ne ubanta, domin
bazan bawa wanda zai wulakanta min ita ba tunda nima amanar
Allah ce na karba."
sai da Yaya ya yi rantsuwa sannan ya kai kallanso
kansu hajiya yace "kun sheda suka ce e mun sheda sannan yace
"na baka ita nan da watan sallah karama sai ayi biki domin yan
zu wata ya kusan mutuwa daga shi sai na azumi dan haka ina
dawowa ma daga umara sai biki." Alhaji Sani yace
"amma ka yi dai-dai haka nake so"
hajiya kuwa sai shimasa albarka take tana, "cewa ka
nuna min cewa kafi karfin gidanka" yace "ina Husna take.
amma na yi wani babban kuskure" gaba daya suka tambayeshi
name? Yace "da nayi saurin yanke hukunci ba tare da naji
tabakinta ba damin na yi alkawarin sai wanda take so zan
bata".
Suka ce indan hakane karkaji komai tana son sa Kuma
zata amince shi dai yace akirawo masa ita dan bata san abin da
aka yanke ba ko tan ada abin cewa kaga ambata nata hakkin
kennan"
Aka tura Salim ya kirawo ni har nayi gaddama Ummi
ta rarrasheni. ina zuwa kai na asun kuye na gaishe dasu sannan
60
RAYUWAR KENAN
Abba yayi mini bayanin ya bawa Yaya ni. Ai sai naji kamar
ancaka min kibiya a zuciyata, sannan ya kara da cewa
"abin da yasa nace ayi kiranki, nayi alkawarin bazan
auar da ke ga wanda ba kya so ba dan haka kin amince kina so?
Sai nasa kuka ina cewa
"a'a bazan iya ba" sai hajiya ta hau salati tana tafa
hannu yannan haka zakiyi mana" Abba ya dakatar da ita tsaya
hajiya abita asannu. Baba Sani yace kinga daina kuka ki
saurara sosai daman can bakya son sa ko yanzu kika sake
shawara?
"Ina son sa, amma ba da aure ba" ai yaya yan jin haka
sai ya yi zumbar ya mike kamar wanda aka tsakura "karya take
wallahi karya ne kina so na."
Abba ya daka mishi tsawa yana cewa "me ye haka
baka da hankali ne ko antaba so dole?" Baba Sani sai
rarrashinsa yake, amma ina fuw ya fice ya barsu nan.
Gu ya hargitse hajiya ranta yai mummunan baci Abba
cewa yake "in rai ya baci hankali ba ya bata ita ma Husna 'Ya
ce dolene akan mu mu bata hakkinta dan haka banga lefinta ba
Kuma banji Haushin ta ba" yace sai dai ayi hukuri Baba Sani
yace "in Kuma kin sake shawara kinzo gida ki sameni dan haka
kiyi tunani sosai ai in kika yi haka sai ayi miki dariya".
Shi Kuwa Yaya daki ya nufa ya fada kan katifarsa yana
ta sharbar kuka kamar mace haka ya muni da ya ga dare yayi
ma yana sallar isha'i ya kulle dakin sa dan kar azata ma yana
ciki ya kashe fitila nan da nan ciwon kai da zazzabi ciman kirji
suka yo mishi sallama. Daman ciwan kai al'adar sace inya tashi
sai kowa na gidan ya firgita, domin baya masa ta dadi haka yau
ma bakin cikine, yatayar dashi, dan haka ya kwana, har kusan
karfe goma bai fitaba. Ni kuwa tsakanina da Hajiya babu badi
dan zaman doya da manja. Mukeyi innayi mata, magana taki
kulani naci kuka na na koshi ko kallona bata yi, sai mita tana
cewa "ma izan ce miki ke da kika ki jikana, dan haka ko
kasheni za.ayi agidan nan, ta daina magana, tunda bansan
61
RAYUWAR KENAN
muntunci ba, dan anaso akwatar min yanci ina wulakan ta
mutane, to kaina na wulakanta kuma sai Allah ya saka musu".
nidai kuka nake ina rokan Allah ya fiddani daga zargi
da kankin bakin ciki.
bayan Abba ya fito ya shigo gun Hajiya dan su gaisa.
sai tace ina Nura kwata kwata yau ban ganshiba? Shima yace
bai shigo ba! Daya shigo zai gaisheni, amman ina fita zan duba
ingani".
yana karasawa kofar dakin a kulle ya kwan kwasa tare
da kiran suna shiru yafita waje yana tambayar su Magaji sukace
bai fitaba a nan Baba Sani shima yazo daga gida yaji ana
cigiyarsa ga baki dayan su suka shiga zauran ana ta bu gawa,.
Nura kuwa bugun da akeyi yanaji amman bazai iya taso wa,
yabude musa ba saboda ciwon yaci karfinsa daman idan ciwon
kansa kansa ya tashi ko gani bayayi dan haka Abba ya hassala
yace Magaji ya kirawo maza suballa kofar.
dukan karfi suka dinga yima kofar har ta balle mai zasu
gani male male cikin amai jikinsa sai tsatstsafar gumi ya keyi
dan haka agigice yaga dan da yake takama da shi kuma mai
biyayya yana neman mutuwa cewa yake A. Sani ku kama shi
mota ina zuwa" yana shigowa gun mahaifiyarsa ya nufa ya
shaida mata ta saka kuka yace" ba kuka zakiyi ba dauko
mayafi mu kaishi asibiti".
suka yi waje na bisu abaya har na kai soron kofar gidan
sai na ja, na tsaya, can cikin zuciya ta anayi min gargadi "me
zaki je kiyi ke da kika ce ba kya son sa?"
Duk halin da ya shiga ke ki ka jawo masa" nan take sai
nasa kuka ina ganin motar ta tashi har da daga mishi hannu.
Ban koma gidan ba na shiga Baba Sani muna zaune ana ta
jimamin rashin lafiya. Ita Kuma Mama basu san abin da yake
faruwa ba sai Magaji ne yake tsegunta musu.
Asibitin Warsh Haruna dake dakata, suka kaishi, nan
da nan likita ya duba shi ya tabbatar musu cewa zuciyarsa bata
buga wa sosai, Kuma jininsa ya hau dan haka za'a bashi
62
RALWAR KENAN
kwanciya nan da nan aka sa masa ruwa akayi masa allurai
hardai ya samu barci. Bayan ruwan ya kare aka dada sa masa
wani sannan ya farka daga barci yana kirana wai in bashi ruwa
idan ina sonsa. sai Hajiya tasa kuka fadi take
"yarinyar nan ta cuceni da ta yarda da haka bata faru
ba" Abba yace Husna bata nan ungo ruwan sha" ya girgiza kai
alamun bai zai shaba sai hawaye ne suke zubowa. A na cikin
wannan hali ne wayar A. Sani tayi ringin, bayan gaisuwa ashe
Mama ce take tambayar sa a wane asibitin suke?. Abba ya daga
hannun alamun wa yake magana yace uwar gida ce take
tambayar asibiti, sai yace
"kar ka fada mata", sai yace "haba Alhaji ba a haka, ba
ruwan ka, ran Abba abace yace mai zata yi mishi in ta zo? Yace
nace ba ruwanka. Bayan ya sheda mata sukayi sallama, can
bayan anyi anyi Yaya ya karbi ruwa yaki, sai ga Mama da Fati
sunyi sallama suna hada ido taga in yadda danta ya rame ya fita
daga haiyacin sa sai tasa kuka Fati ma haka Abba yace "kunga
bama san shashanci, duk ke ce sanadi". Bayan wani kankanin
lokaci su Abba suka tafi aka bar su Mama agun Yaya.
Can Yaya ya da da farkawa da sunana ya farka sai ace
yanzu zanzo a haka har sai daya kwana biyu ban sami ganinsa
ba. Duk ko da cewa nima ina son ganinsa amma narasa ta Inda
zan ganshi. Ranan naji ummi tana cewa zata je duba shi nida
Ramlat muka bita muna shiga ta sha kunu kamar baza ta amsa
gaisuwar Ummin ba, ni dai na takure gu daya sai hawayene
yake kwarara na kasa karasawa ko da jikin gadon ma.
Kamar an sanar da shi nazo sai ya farka yana cewa
"Husna in kina so na ki bani ruwa"
sai nayi wata irin anyar zuciya, nayi sauri nararumi
robar ruwa ina shirin mika mishi Mama ta warce tace "bani nan
uwar shishshigi" sai yasa kuka yana cewa Abba ya bani ita
amana ita zan aura, maganganu dai barkatai wasuma ba dai-dai
yake fadaba, sai hajiya tace
63
RAYUWAR KENAN
"kin ga likita yace duk abin da yace yana so ayi mishi
in ana aga daidai mai zai hana ta bashi ruwan, tun da muka zo
asibitin nan yau kwana biyu yaki karbar komai sai ita yake
kira"
Ummi ma tasa baki ina kuka Ramlat ta miko min na
bashi sannan na hada masa ruwan Tea shima ya karba yana
mur mushi kowa sai murna ana barka ana samu yadan sa wani
abu abakin sa.
Muna wannan halin ne likitan ya shigao baki a bude
yana cewa "Mallam Nura madan ta zone?" Ya nuna ni da yatsa
kaganta kaganta sannan yace "ai sai ki zauna da shi saboda
yana bukatar zamanki kusa dashi". Yau dai wuni guda acikin
nisahdi suka yi dan sai da aka yi mishi allurar barci sannan
Ummi tace zamu tafi. "amma ina ganin gara mubar Husna a
nan, sabo da samun kwanciyar hankali". Hajiya har ta yarda
Mama tace a'a nima dai azahiri naïf son tafiya ta kuma ta ce
idan na kara zuwa sai taci mutuncina, hajiya bata yi koda musu
ba domin itama haushina take ji. Kuka na keyi har muka isa
gida.
Ummi da Ramlat suna bani hakuri tare da yi min
nasiha, na shiga kuncin rayuwa, har narasa mai zanyi inje inda
yake, can cikin zuciya ta kuwa ai yane ai yane take yimin!
Kinga Husna ki gudu keji ki nemi iyayanki sune gatanki duk
fa duk irin halin bakin cikin da kike shiga rashin sune ya jawo
miki.
can nayi ajiyar zuciya zancan zuci yafito fili nace ina
tafi Yaya wane irin hali zai shiga ina cikin zance ni kadai
Ramlat tazo kaina ta tsaya amma ban kula ba, sai da ta kai
hannu ta dafa kafada ta, tare da kiran sunana tana girgiza kai
alamun tausayi tace "Husna kar ki sa wannan abu a zuciyarki
kizo ciwo ya kamaki ciwon da baya jin magani ga shi dai kina
ganin halin da Yaya yake ciki akan ki ni dai shawarar da zan
baki, ki amince masa zaki aure shi na tabbata ba zai bari wani
ya wulakanta ki ba. Ta nisa sann ta ci gaba da magaba
64
RAYIWAR KENAN
"gashi Abba da Hajiya sun amince dari bisa dari Kuma
in har kika ki ba kiyi masa adalci ba ki tuna fa tun baki kai
haka ba yake kaunar ki baya son bacin ranki uwarsa taki jinin
taga yana kulaki amma haka bai hana shi kula da ke ba..."
da shashshekar kuka na dakatar da ita nace "Ramlat
kema kinsan ina son Yaya fiye da yadda baki zato, haka Kuma
na haki kancewa kaina shine ginshikin rayuwata tunda mutane
da yawa sun gujeni akan rashin sanin usulina amma, shi yaji ya
gani, ba wani abu bane nace bazan aureshi ba sai saboda irin
kiyayyar da mahaifiyarsa take yimin inaga inna aure shi sai tafi
haka, sannan idan muka samu zuria.
Kiyayyar da take nuna min har su zatayi wa, shine na
yanke shawara akan in hakura badan bana soba". itama ta
girgiza kai ta yi tana kwalla tace "lallai hakane amma ba da ita
zaki zauna ba". Ta yi ta bani hakuri da shawarwari masu
amfani, daga karshe muka yanke shawarar zata asibiti ta bashi
hakuri bayan na koma gida kenan ko mintuna biyar ban yiba
Mama ta shigo masu aiki suka tareta da sannu da zuwa tare da
tambayar jikin Yaya tace "jikin da sauki yan zuma a zaune ta
baroshi yana shan tea shine nace bari na zo gida gobe na koma"
nima na fito kaina asun kuye nayi mata sannu da zuwa
ko amsawa batayi ba sai zagi da hantara da suka buyo baya. Ina
shiga daki da niyar yin barci sam sai ya gagareni na kasa zaune
na kasa tsaye zuciyata sai faman bugawa take yi naji babu abin
da yake min dadi a ruyuwa ta domin duniyar gabaki dayan ta
tayi min zafi in banda Yayana babu wanda nake son gani. A ha
lin yanzu kawai sai na mike na nufi tsakar gida na tabbatar
babu wanda yaganni sai nayi waje na mike ina ta sauri kamar
wacce zata tashi sama, tafiya nake ba kakkautawa. daga
wannam titi in tsallaka wancan titin nice har dakata na bulla a
sibitin Warsh Haruna cikin ikon Allah sau daya da muka je
amma na gane natura kofar dakin sai shi kadai yana kwance
dakin ba kowa surutun da na ji yanayi ne ya dakatar dani daga
65
RAYUWAR KENAN
ganin sa dai barci yake dan haka ga dukkan alamu irin
mafarkin nan ne wanda idan ana yi yake fitowa sarari.
Jikina asanyaye na karasa kansa na kura masa ido
tausayinsa tare da son sa suka kara ratsa zaciya ta nan da nan
sai hawaye wasu suna bin wasu, banyi zatan akan fuskarsa
yake zuba ba, tare da daga hannuna sama ina rokon mai kowa
mai komai in cewa
"ya ubangijin talikai ya masanin sirin boye kafini sanin
halin da muka shiga haka Kuma kafimu san kammu da kammu
domin idan, nufinmu akan niyarmu ta alheri ka zaba mana mafi
alheri ka bawa wannan bawa naka lafiya domin darajar Annabi
Muhammad S.A.W kafin ina karasa sai naji anri ke hannuna
tare da kiran sunana Husna, kukan mai kike nagirgiza kai yace
"bana san inga kina kuka yana kokarin tashi zaune na tai maka
masa ya zauna, yanuna min gefen gadon yace
"zauna" nace a'a tafiya, zanyi yace ke dawa kuka zo
kafin in bashi amsa naga an bude kofar dakin Hajiyan
Maiduguri tafito sai na ga ta bude baki alamu mamaki a
fuskarta na durkusa na gaida ta ta amsa ciki-ciki na mike
zantafi yayi zumbur ya yiriko mayafina muka hada ido yace
"tambayar ki nake Husna? Nace ki da waye ki ka yi shiru
Kuma a wannan daran zaki tafi to wallahi ba zaki tafi kibar ni
ba sai dai ki kwana" na sun kuyar da kaina kasa ina magana
cikin sanyin jiki da sanyin murya wanda tayi daidai da marayan.
da ba uwa ba uba, gazo bara dan ya samu uwar daki
"Yayana kayi hakuri ka yafe min abisa akasin da aka
samu domin duk halin da kashiga nice najawo maka ina
tabbatar maka da cewa ina cikin kuncin rayuwa da ganin jafa'i
iri-iri akan ka ina Kuma tausayawa rayuwata idan natuna da
cewar duk rashin iyayena ne, yajanyo min shiga halin dana
shiga nadan, tsaya tare da ajiyur zuciya na ci gaba "gara kabarni in tafi domin babu wanda yasan na fito yanzu ma."
A dai-dai lokacin da muka hada ido da shi har Hajiya hawaye ne ke zuba a idanunsu, babu zato ba tsammani naji
66
あたり
RAYUWAR KENAN
Hajiya ta taso tare da kamani ta zaunar dani tana bani hakuri
tana rarrashina tana cewa komai yawuce Allah yayi miki
albarka amma ki zauna ki kwana " nace "ina gudun bavin ran
Mama tace da sassafe kin tafi Kuma babu wanda yasan kin
kvana anan nace to Allah shi kaimu.
Bayan kwana biyu Yaya Nura ya sami sauki sosai aka
sallameshi ya dawongida mukaci gaba da soyayyarmu acikin
nutsuwa daman boye-boye da fargabar kar aji muke kuma anjí
sai dai muce Allah) ya tabbatar da alleri Ameen.
Hajiya ta kusa tafiya to ta tara su Abba tace tana so
kafin ta tafi asa ranar bikin mu tunda taga na sakko, dan haka
Abba yace sai da izini na akai kirana ya tambayeni tsakanina da
Allah ina son Nura? Nayi shiru ni dai harga Allah ina son sa
amma ina gudun wulakanci dan haka tun farko naki amin cewa
dan haka ni dai nayi shiru babu yadda zanyi gudun abin da ya
faru baya yasa naki cewa a'a Kuma da kunya a gaban
mahaifinsa da kakarsa in ki amincewa dan haka ko banaso dole
na amsa dan murabu lafiya. An sa mana ranar bikin mu watan
dawowar Alhazai karshen sa sabo adai-dai lokacin Abba ya
dawo daga Hajji Kuma shima Yayan za shi:
Awannan lokacin idan kaga Yaya Kowa yasan yana
cikin farin ciki kamar yadda aka saba, Abba ya hadowa hajiya
sha tara ta arziki ta gama shiryawa tsaf sannan ta yi sallama da
kowa Yaya yace ta fito su tafi wannan karan tiket Yayan
karmata, don haka iyafot (Airport) za'a kai ta Hajiyar Abba
kenan yar gatan Abba ba komai dole ya shagwabata shi kadai
ta Haifa, Kuma ga Allah ya hore mishi dai-dai gwargwado
dolene yayi mata in yana son Albarka. Bayan mun gama koke
koken mu dan bamason tafiyarta domin tana tafiya zan koma
cikin kunci da takura daman duk wani abin da ake raga min
ganin idon tane yasa yanzu kuwa ta tafi zan yabawa aya
zakinta, wai yo ni Hasna Allah, kai mana maganin abin da yafi
karfin mu.
RAYUWAR KENAN
Su Mamakuwa tunda aka samana rana bata da
kwanciyan hankali ta kasa tsaye ta kasa zaune yau tana gun
wancan bokaduk tarasa inda zata saranta tana tsoron tabani
saboda abinıda zai biyo baya dan haka sai Aunty Ya'yarta ta
bata shawara subi abin ahankali har su, sami abin da suke so, ni
kuwa in ban da rama babu abin da nake yi. Akwai wata rana
dana shiga gidansu Ramlat Ummi) tai kirana tace Husna) mai
yake damun ki ne? Sai rama kike Kamar dabbar data hadiyi
allura na sunkuyar da kaina kasa hawaye na zuba nace "Ummi
ni dai bana ce ga abin da da yake damuna ba." tace "babu wani
gu da yake miki ciwo ajikin ki?" nace babu "amma zuciyata
tana yawan yimin zafi da radadi wani lokaci kums har jikina".
Anan dai jikin ta yayi sanyi ta dago kanta muka hada ido tare
da jawo ni jikinta da kalamai masu sanyaya zuciya sannan
tabani Addu'ol masu amfani Kuma tace akwai wani maganin
sammu zata abaniindinga wanka dashi har tsawankwanaan
bakwai naceNnagode Ummi Allah ya saka miki da alheri" tace
"babu komai Husna duk abin danayi miki ban fadiba ke da
Ramlatnduk daya na dau keku dan haka nasha fada miki duk
irin. abin da kike so ki fada mini" Kuma kamar yadda nasaba
sallolin nafilfili babu kakkautwa tare da karatun Alkur'ani main
girma ina nemawa kaima sauki da mafita agun mahallicinam
haka Kuma kullum soyayyarmu da Yaya karuwa take.yiekamam
yadda nasaba in dai ya dawo daga ofis zai turoe in kawo mishiна
abincinsanhaka nacingaba Kuma ko naki zamasai ya takura ar
mininna zauna munyi hira a kullum hirarısa bata wuce Allahlita
yanuna mana lokacin auran mu.
A kwana a tashi babu wuya a gun Allah gashi wannan
watanya kusa mutuwa zamu shiga Zulkidah dan haka hankali
su Mamanyayi mummunan tashi, domin bin bokaye bai yi tasiri
ba anyi abuwa kala-kala dan Yaya yaji kwata kwata nafita daga
ransanyaceuyafasa.amman shiru kakeji dan kullum soyayya
dada: karuwa take Kuma ba'a taba jin kammu ba, dan haka yau
Mama da kanta ta tafi gidan Yayarta dan ta sheda mata cewa.innn.
68
RAYH AR KENAN
dara taki sai akoma cacah tace mata hanata fita zakiyi ko ina
hatta da kai masa abincin da take yi dakinsa in yaso baga idanta
abude yake kar ta lalatashi inyaso ba ga yar uwarsa nan ba
ladidi sai in turota ta dinga kai masa kinga idan baya yawan
ganinta abin yayi sauki." Mama ta mika mata hannutare da
shewa tana cewa "yauwa Aunty wallahi shi yasa kike burge ni
ko dan iya hada makirci".
Ita Kuma sai hura hanciu take wai amfasa mata kai.
sannan ta waisayo tace 'kinga in Alhaji ya tambayi dalili rashin
fitarta sai kice yawan banza takeyi wata ranama bata kwana
agidan" suka dada rangwada buda sannan sukayi sallama akan
cewa nana da kwana uku zata zo taji yadda sukayi.
Anan kuwa gidan bayan nayi wanka na shiga gidan su
Ramlat ta yarfamin kananan kitso abinka da mai gashi kamar
na larabawa, jelar kitson ya kwatomin agadon bayana daman
tun kafin mugama Yaya yake tayo aike inzo nace bamu gama
ba yan zuma nataso kenan dan aike ya shigo Ramlat ce ta
dakatar dashi tanamai rike hannuna "kace mashi angama amma
sai ya bada kudin kitso zambar ta tazo". Ya juya ni kuma
dariya nake can sai ga Salim da sababbin kudi yan naira ishirin
ishirin na N1000 da Sweet kala kala akawo mata wai ta barni
inzo sai murna tana nunawa Ummi tana cewa "lallai yaya ba
karamin so yake yima Husna ba" ina fita gogan naka yana
kofar gida cewa yake yawwa mai ruwan larabawa amman kinyi
kyau yi sauri wallahi abokai na ne sukazo nake so ki hado
mana abinci". Na dan zumbara baki nace "maimakon ga
mutane acikin gidan katura abaka amman kabar su da yinwa?
na gama hada abincin cuscus da miya na bude firji na dauko
abarba namarkada da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13