dariya ashe dai kina da baki Yaya, yace
"akace muku da ta wasace"
ni dai anan na barsu kashegari da safe kuwa an kafa
cafta akan.cewar Yaya, yana nuna banbanci inji Fati. ita kuma
Ladidi tace agaskiya abincika da kyar in babu soyayya a
tsakaninsu dan abin yayi yawa kinga irin gift din da ya dinga
bata ana daukarsu a hoto kamar irin amarya da ango dan kinsan
idona yana kansu amma bai san ina yi ba" can Mama, tace
"au har kyauta ya bata kefa"?. Fati, tarike baki ni wazai
bani, bakya gani ma kayan da ya dinka mana iri daya yayi
musu shi da ita agaskiya Mama, sai antashi tsaye akan Yaya,
dan ina ga ba haka ta barshi ba".
"kwarai kuwa rannan har bakin ciki yasa na kasa,
magana, to wallai ba za ta sabu ba kuma indai bai rabu da ita
ba sai naci mutuncinsa a dai-dai lokacin Abba ya shigo kuma
ya ji fadan da take yi, sai ya yi kamar bai jiba ya tambayeta mai
yake faruwa tace babu komai.
Bayan na kammala aikace-aikacen dana sabayi da safe
nayi wanka muna dakin Hajiya ni da Yaya, muna bata hakuri
ita kuma sai mita take ta yi tana cewa
"an wulakanta ta agun walima kudu ba yarinyar nan
Fati, kamar bata sanni ba ana cewa tazo mu dau hoto tana
faman guduna daga ita har uwarta sai faman Harare-Harare
44
RAYUW AR KENAN
sukeyi haka duk maganganun da suke fada ina jinsu da yarinyar
nan Husna ta kulasu da ba'asan abin da zasu yi mata ba, kana
ganin kaya ma hanata sakawa akayi:.
ann Yaya, ya cire hannu daga tagumin da ya yi
"kwarai wannan hali na Mama yana bata min rai sai dai
muce Allah ya mana magani kinga tunda naga wannan yan
iskan su Ladidi sunzo ko dakin bansan shiga dan sam basu da
kunya Fatima agunsu ta ke koyan rashin mutunci lokacin da
nake baki give suna tsaye da magaji suna ra hoto nasan zasu kai
gulmarmu kuma su zasu hana Fati sa kayan dane muku".
hajiya tace kwarai da gaske munafukan yara, tun suna
kana nansu sun iya makirei iriri iri Yaya yace
" agun uwarsu suka koya shi yasa babansu ya kori
Hajiyarsu daga gidan' suma kuma da ya ga bazai iyaba, yace su
bita rida-rida, dasu babu mijin aure shine Mama takeso ta lika
min daya daga cikin su ni ko na ki".
Ai da naji ya fadi haka gabana ya yanke ya fadi na
zazzaro ido kamar wacce aka shake ina kallonsa. ya sakar mini
murmushi tare da kanne min ido. Can hankalin mu ya koma
kan hajiya kuka harda hawaye wai ita ammai da ita banza ba
girma ba mutunci tunda Mama bata ganin girmanta haka
Fatima, tunda tazo gidan nan babu abin da yake hadata dasu sai
gaisuwa.
"jiya agun walima har habaici ake mata ita kuma
uwarta sai faman kunbura take tana batsewa ni bansan abin
dana yi musu ba.
Yaya, ya kalleni yana nuna alamun murarrasheta nace
"haba hajiyarmu kiyi hakuri ba'asan manya da karaya ba inki
lura kai da kaya duk mallakar wiya ne, ke mai yanke hukunci
ce, akan duk wani na cikin gidannan kuma habaice-habaicen ba
da ke suke ba".
"nasan dani suke ta share hawaye ta dago takalle ni.
toke uban mai kika tsare musu? Badan kina da hakuri da
45
RATUWAR KENAY
hankali da nutsuwa ba. da ba aizaman lafiya dake ba ta kalli
Yzya
kai kuma kamar bana mijiba, idan shi Abban naka, ba
ayi akan idonsa ai kai kasan komai yadan yi ajiyar zuciya
yace nidai babu abin da zance sai dai ayi hakuri fadan da yafi
karfinka sai kamai dashi wasa saboda ina da zuciya sosai, dan
haka, nake dan kwada kaina, innayi magana, tace zatayi min
baki amman wannan matsala tagidanan tana damuna in raina
yayi dubu sai ya baci adai-dai nan muka ji sallamar Abba, duk
hankalinmu ahar gitse bayan yazauna an gaisa sai yace
wai mai yake faruwa ne can ita da Yayan ta sai surutai
suke ku kuma kunsa Hajiya agaba kuna ta surutu wai abin da
aka yine agun walimar? mude shiru mukayi muna shirin
boyewa can sai muka ji Hajiya ta fara zaiyana masa irin
wulakancin da ake mata da dai duk irin abin da akayi agun
walima har tana cewa ita tafiya zatayi tabar musu gidan Abba
idon sa ya kada dagani zuciyar maza ta baci
"wallahi basu isa akansu kibar gidan nanba, sai dai su
subar gidan yace da Yaya kai don me yasa ba ka dau hukunci
akan Fatin ba? ko tsoranta ka keji? Yadan girgiza kai
"a'a ba haka bane idan nayi magana musamman akan
Husna sai kaga ran Mama, yabaci tana cewa ina nuna banbanci
atsakaninsu, ta kamani da fada tana ta fadan wasu kalamai
marasa kyau, shi yasa kaga bana fada maka dan idan na fada
abin sai yafi haka"
hajiya ta kara da cewa kaga har da kayan da aka
dinka musu hanata sakawa tayi sai yarannan ne ta nuna Yaya
ya kawo musu wani suka sa ba dan haka ba da sai dai tayi
walimar a haka."
Abba ransa yai mummunan baci to. me ye dalilın
hanata saka kayan naga ba ita ta dinka mata ba? Amma dan
Allah Hajiya kiyi hakuri nasan matakin da zan dauka, kema
Husna kiyi hakuri kinji, komai na duniya mai wucewane".
46
RAYUWAR KENAN
Ya fita Yaya suka cigaba tana cewa ni banga abin da
wanan yarinya ta tsarewa wani ba ya kamata a riketa tsakani da
Allah narasa abinda yake damun uwarka, ita batasan 'da' da
dukiya ba'a muguntarsu ba, domin ba'a san maimorarsu ba sai
Allah. Kuma kowa kaga ni, da baiwar da Allah yayi mishi balle
Husna tunda aka kawo ta da ganinta babu wahala tare da ita
daga ganin irin yanayin kayan jikinta da yadda take aiwatar da
halayan ta ba daga karamin gida tafito ba, duk da dai alokacin
batafi shekara biyar ba".
da jin haka nan da nan na daga kaina idona cike da kwalla na
kalleta, shi kuwa Yaya, matsawa yayi ya dawo kusa da ita tace
To sarkin zumudi"
yace "ai ya zama dole inyi saboda nadade ina son inji labarin
yadda akayi muka hadu da mai tayani rayuwa"
tayi dan murmushi fuskarta na annuri yace wato har
yan zu baki mantaba?"
"haba ina zan manta har da hoto a hannunta ita da ko
yar uwartace ajikin bayan hoton akwai sunansu ajiki Yaya,
yace "to waye ya kawo muku ita?"
"Nidai ina zaune ina damawa mallam fura ya yi baki
da yake bama rabo da baki haka matafiya suka tsaya a kofar
gidan dan suyi sallah sudan huta sai gashi ya shigo da ita a
hannu tana ta kuka yace
"wasu mutane ne suka kawo mishi ita yanzu suma
sunzo wucewa suka ganta agefen titi tana kuka tana waige
waige. Bayan sun yi cigiya da tambayar yan uwanta duk an
sami wanda yasanta ba, sai a kace su kawo ta nan gidan liman
tun da idan irin haka ya faru nan ake kawowa kuma ana samun
dace to alokacin babanka yana gari abin ya faru da yaga an
shafe sati babu labarin iyayanta ko wani wanda ya santa sai ya
nuna yana son ta ita ma kuma ta shaku dashi, daga yashigo zata
tafi da gudu tana murma nan da nan ya dagata sama yana yimata
wasa dan abin da ya riko mata ya bata kuma ba fitar da zai yi
sai sayo mata yar riguna yan kanti ta kalma kayan wasa iri ini
47
RAYUWAR KENAN
abun mamaki yarinya sai ta daina rigima ta saba da kowa
saboda haka sai yayi mini magana akan yana so yatafi da
Husna, nace da ganin sarkin fawa sai miya tai zaki kaima kasan
ba haka ake yi ba, kabari sai andebi lokaci mai tsaho in ba aga
iyayenta ba a haka dai da taimako Alhajin har gidan Redio da
T.V. aka kai cigiya amman shiru ba labari.
"da dai Mallam yaga tafiya tayi nisa sai aka bawa
Alhaji amman sai da aka hada da offishin yan sanda da mai
unguwa yasa hannu aka bashi damar yaci gaba da rikonta,
amman akan sharadin zai dinga bullowa akai akai koza'a
dace".
" kaji labarin inda ka samu Husna Yaya, idon sa cike
da kwalla ya kalleni tare da kiran sunana kidaina kuka insha
Allah kin sami maishare miki hawaye kuma zantai maka akan
neman iyayanki inhar ina raye insha Allah namai da hankali
kan hajiya yanzu ina hoton da aka gani a hannunta yana gun
Alhaji hatta da kayan da yake jikinta sai daya taho dasu kuma
takara dacewa suma suna nan suna dada yin bincike".
hira tayi dadi daga kai na ke da wuya karfe daya ta gota
na tabashi tare dayi mishi nuni da hannu muka yi sallama ya
tafi yana tsokana shidai sai yaga nayi dariya sai kuwa da na dan
murmusa
"take care kinji" Yaya ya fada yana kallonan. Hajiya
kuwa har ta fara gyangyadi Yaya, kenan agskiya yana bergeni,
komai nashi yana ban sha'awa gashi babu ruwansa da duniya
kamar ba dan zamani ba yarone amman mai halin manya, ni dai
a haka cikin zancan zuci da kyar nayi addu'a barci ya daukeni.
Kashe gari kamar yadda muka saba bayan na kammala
komai dan hantsi ya daga a hada daba a dukin Mama, harda
magaji saboda ina ga Abba, ya yi mata maganar da Hajiya tayi
mishi daman tun da gari ya waye naga alamun yau ba mutunci
a fuskarta dan haka Allah-Alah nake in kammala komai in
shige gun Hajiya.
48
RAYUWAR KENAN
Mama ita da makarraben ta sunata, nanata abin da akayi tana faman fada da fadar maganganu marasa dadi akai na
da Hajiya har Abban bata barshiba mai zai faru na fito tsakar
gida ke nan sai ga Abba ya yi mantuwar wasu mahimman ta
kardu yadawo dauka ina ganinsa nace la..Abba lafiya sai ya
nuna mun da hannu inyi shiru kunnen sa kuwa yana gun hirar
su. A sannu ya karasa falon daidai inda take cewa bajurinsu
sharriba, to mune tsumma makullin sharri.
Kuma bayan ya tsinci kadan daga maganganun da
sukeyi ana dariya ana shewa tana cewa "kowa ya yi min kan
kara sai nai mishi na itace" yana karasa shiga ya ba ta amsa da
cewa
"ke kuma ayi miki na rodi"
dukkan su dif, suka yi kamar ruwa ya cinyesu kowa
bakinsa abude, domin basu zata zai dawo dai-dai, wannan
lokacin ba, dan haka, sun saki jiki ya kalle su tare da gyada kai
ya nuna magaji da yatsa kai kuma mai kakeyi acikinsu?
Shasha, sha, na mata na mata ya dada daka mishi tsawa banza
Mashi mara mutunci"
ya saurin sunkuyar da kai "Alhaji dan Allah ayi hakuri
nima yanzu na shigo karbar wankine..." "kaga da kata banasan
dogon bayani daga yau karka kara shigo min gida idan wanki
ya taru a dinga kai maka waje".
bayan fitar sa sai yamai da hankalinsa kan su Ladidi da
Fati da kanwarta,
"ku kuma ta taraku tana yi muku hudubar banza, haka
zaku gidan mazajanku babu tarbiya ba kamun kai musamman
ke Fati, duk irin abin da ki keyi agidan nan ina da labari sai
kinci kaneyarki tashi kuban guri"
haryana kaimata duka da hannu tana kuka suka nufi
tsakar gida "ke kuma tamuce ni dake" ransa abace ya wuce
taiwani irin yamutsa tuska lallai da aiki agaban maza sai dai ka
yiwa Yayan ka" ko, kallan ta bai yiba yasan inya tsaya lokaci
zai kure mishi baryi abin daya kawo shi ba bayan ya sakko
49
RAYUWAR KENAN
daga saman inda yabarta tana mita haka ya dawo ya tarar da
iata tana cewa
"haka kawai daga shigowa zaka kama fadan bagaira ba
dalili aiba sai kayi haka ba za'a san anzugaka.." "waye zai
zugani ? "kai kasani ta shige dakint a. Shidai ransa abace, ya
ficce bayan kwana biyu zuciyar Abba, babu dadi kullum yazo
gaishe da hajiya tai taimishi nashiha tana cewa "kayi hakuri wanan ina wata jarabawa ce da ubangiji
yake yimaka duk wani bawa ba ta inda Allah baya jarrabar
imaninsa dan yaga yadda zaka yi.
kagani dai ya baka ilimi ya baka yaya ya rufa maka
asiri amman ta bangaran matar ka, baka jin dadin zama da ita
sai kai tai mata addu'a Allah yashiryeta. Haka Yaya. mai da
yaji ransa ya baci sosai har yake tunanin ina ma ba ita ta haife
shiba. yayi zurfi cikin tunani daga baya dai yayanke shawarar
in safiya, tayi yaje gaisheta yayi mata dn nasiha ko zataji.
Da gari ya waye Kafin azauna gun cin abinci yashiga
dakin ya sameta bayan sun gaisa tace mishi "ina zaka je kayi
wannan sammakon" yace "bako ina. nazo gunki da wasu
mahimman maganganu" bai jira tace wani abin ba ya cigaba
gaskiya mama ke ce ya kamata kiyi wa yayanki fada kuma abin
da babba ya hango yaro koya hau Dala ba zai han gaba,
ammam tunda ansani sabanin haka naga ya dace a matsaa yina
nada, agunki ya zama dole in fada miki gaskiya abin da kike
yiwa Abba bai kamata ba yana matsayin miji agunki kuma
uban yayanki ya zama dole ki guji bacin ransa kibishi sau da
kafa, sannan Hajiya mahaifiyarsa ce kigirmamata, kamar ita
tahaifeki domin bin nagaba bin Allah ya daga kai yana
kallonta yaga dai akwai face. Sannan yatabo bangaren da tafi
tsana a rayuwarta, haka zalika akan yarin yarnan Huss... sabo
da tsoro ya kasa karasa sunan banga abin da ta keyi narashin
ladabi ba ya kamata kidai na bambanta ta damu ki sani
amanace Allah) ya baku sai ku riketa tsakani da Allah..." ba
50
RAYUWAR KENAN
zato ba tsammani ta mike tare da daka masa tsawa maifir
gitarwa kana ta nuno shi da yatsa tace
"dakata uban yan tsari wato anhado baki da kai dan
acuceni daman ance makashin ka na gindinka" Yaya yana jin
kalaminta ya tashi ya matsa kusa da ita ya durkusa yana bata
hakuri yana cewa idan ya fadi wani abu da ya bata mata rai to
tayi hakuri ta yafeshi, shidai yasan d uk wani mai sonta yabi
bayanshi.
Ta tureshi ta wuce tana yi mishi gargadin cewa yayi
nafarko yayi nakarshe, shima ransa abace ya ficewar sa daga
dakin ta.
Bayan ya dawo daga ofis ya turo a kira ni ina shiga na
san ba lafiya domin bayadda nasaba ganin sa ciki farin ciki da
walwala nagan shiba gashi babu irin surutun nan da yake yimin
nikuna ga kunya tana son hanani tambayar sa domin yana da
wata baiwa da bako wane namiji yake da itaba idan har yana
gabana sai inji kamar babu kowa a duniyar sai mu Kuma in har
yakalleni, sai inji kamar ansaukar min da wani wahayi ajikina
haka yanzuma in banda kallona babu abin da yake yi amman da
ganin fuskar sa za'a gane akwai abin da yake damunsa, dan na
dade da karantar sa, bakin ciki ko farin ciki basa boyuwa a
fuskar sa.
can natuna da cewa inban faran ta mishi rai ba to me ye
amfanin kaunar dana keyi mishi? koma ba haka ba, Yaya
bamutumin banza bane, nasaurin cire hannunsa daga ta gumi
ina mai tambayarsa da ccwa Yayana) mai yake damunka?
Yadan kau da damuwar zuwa murmushi a dan firgice yace lah,
Husna babu komai nace
"Haba Yaya agaskiya ban yarda ba bayan tunda na
shigo baka yi min maganaba kayi shiru, kuma ni ba haka
nasaba gani ba"
yace haba uwar gidana karki samu damuwa nidai
burina in mallake ki", nace
51
RAYUWAR KENAN
"shine yake damun ka? ya danyi min sigina tare da
kanne ido sai nadan tabe baki tare da alamun shagwaba nasa
kuka dan Allah) Yaya ka fada min meya ke faruwa? Da yaga
zanyi kuka ya yi saurin dakatar dani da hannu
"to tsaya tsaya nace, miki, sai yadan sha kunu ni kuma
hankalina yana kansa, sannan ya fara fada mini abin daya faru
tsakanin sa da mahaifiyarsa yana zuiwa kan maganata yasa wani
dogon numfashi sai naga kwalla na kokarin zubawa hawaye na
kokarin zubowa daga idanunsa ai nan da nan nima naji nawa
idon ya kawo hawaye.
Kaina asun kuye nace "in ce ko ba maganar.. ban sami
damar karasawa ba ya tari numfashi na "kina nufin maganar
auranmu? ba ita ba ce"
sai nayi ajiyar zuciya tare da dafa kirji gara da baka yi
ba yace saboda me?
"Ai itama zan yine ko yau ko gabe" nace "dan Allah)
Yaya ka rufa min asir"i ya zaro ido "ke kin taba ganin anyi
soyayya da wasa?""To ni auranki zanyi kuma nasan ina
fadawa Abba anyi angama tunda dai kina so na shike nan insha
Allah nida ke Allah ya kusa yanke mana bakin ciki dan haka
sai muyi ta addu'a Allah ya tabbatar mana da alheri".
Na yi shiru yace "kanwata bakice amin ba? Nadanyi
mur mushi natashi ina shirni guduwa yace sai nace Ameen zan
fita sai ko danace tare da dariya da farin ciki muka rabu nayi
gidan su babbar aminiyata Ramlat.
Haka dai mukaci gaba da zama gida babu badi dan
kowa zuciyarsa babu dadi haduwar da akeyi agun cin abinci
ma an daina dan Abba da Yaya basa zaunawa, da man ko ni tun
da Hajiyar maiduguri ta zo na dai na shiga cikinsu kamar yadda
na saba.
Yauma kamar yadda na saba kaiwa Yaya abinci in
yadawo daga ofis haka yauma ya turo nazo daman na fito daga
wanka kenan salim ya shigo ya fada min.
52
RAYUWAR KENAN
bayan dan bata lokaci gun shafe shafe na saka atamfa koriya duk da dai ba wata babba bace nasan tama yirmini kyau musamma,dayake ina da farar fata, nadan fisa turare, ashe duk.
abin danákeyi Hajiya tana lura dani har ma tana yi min tsiya
kenan amlat ta shigo tace Yaya yace kibar abincin yanzu
shima 2ai shigo.
Tana zama ke nan sai gashi ya shigo yana yi mata tsiya
da cewa Ramlat kina nan kwana biyu bana ganinki tace "lah
Yaya kullum fa sai na shigo haduwa ne bamayi"
yace ban yarda ba dana ganki, ta kalleni tace Husna)
itama yanzu sai muyi kwanaki bamu ganta ba"
ah ramawa kenan kika yi aa gani nayi kullum tana
nanike da kai tun yanzu ka fara kullen ta ya kama haba wane
ni"
Kana yanuna Hajiya tunda yar tsohuwar nan tazo
shike nan babu shiga, bafi ta, amman nima nasan abin da zanyi
mata turldatHajiyar takusa tafiya sai inci gaba da kulleta nace
"lallai sai kabari sai kayi aure Ramlat muna dariya gaba dayan
mu "Hajiyptace banda abinki Husna ke ce kaza da zakaran zai
sa a 'a kurki domin akan ki yake yawan cara, don naga shishshigin ya yi yawa akan ki" nace a'a Hajiya yana da wacce
ya keso açan wata unguwar".
ya kalleni makar yaçiya ya mai da kallan sa kani Hajiya,
a she daiskingane bakin/zaren? Tacet haba danrnangganizai ya
kori frenida sai naji kunya duk ta kamani na tashi nal fitarnabar
Yaya sal zunudi yake yana ta surutu an sosa mishirinda yake
mishi gikayi sai faman zuba yake Ramlat tana ddadartayyashi
anan datrHajiya ta yanke magana kan in Abba ya cdawozza tayi
masa mauana, tace abu yayi mata dadi shikermanttuwo na maiya
na nayi farin ciki da kasancewar haka Allah yashi muku
albarka dan kullum buri na baya wuce inga kunyi aure.
takuwa mama abu yayi mata yawa domin yau kusan
wata biyt kenan Abba ya juya mata baya ko wani abin take so babu fuşka bare ta tambayeshi hatta da kudin cefane sai dai ya
53
RAYUWAR KENAN
bawa Salim ya kai mata in ta gai sheshi da kar yake amsawa
dan haka ta canja wata shawara da cewa gara ta aika magaji
gun yayarta uwar su Ladidi kenan dan asan ta inda za'a
bullowa lamarin bayan yaje unguwar dakata ya sanar da Hajiya
Ma'u duk halin da ake çiki sannan ya sanar mata tana san ganin
ta, da gaggawa, tace mishi yau kaduna zata kan lamarin siyasa
amman gabe da yamma tana nan tafe.
Hajiya Ma'u irin matanan ne da suka goge da yawo
kuma sukan bi yan siyasa suyi masu canfen dan haka babu
tarbiya tagari ga yayanta kowa yake abin da yaga dama yayanta
sai yawan bin samari gidajan fati dan haka daman masu
magana, suna cewa zama da madaukin kanwa shike kawo farin
kai, fatima, ta dau irin wannan al'adar tasu.
Ranar da Hajiya Ma'u tazo sun kule a daka ba ajin
duriyarsu tana fada mata irin halin datake ciki tana kuka babu
kuma wanda bata fada mataba musam man akai na tace
shegiyar yariyar nan tana so ta zame mana kadan garan bakin
tulu domin naga alamun tasha gaban Nura dan baya san laifinta
ko kadan gashi alamu yana nunawa sonta yake yi Aunty da
haka take kiranta.
Tai saurin dukan kirji "mai kika ce? Kina nufin auran
zumunci da muke san hadawa yana neman shan ruwa? To
wallahi baza ta sabuba sai dai inbabu malamai agarin nan ita
dim me? Husnan banza" Mama tace yawwa Aunty haka nake
so' yan zu ya kike ganin zamuyi? ta danyi tunani ai rabasu za
ayi yaji samta ya fita daga zuciyarsa har maigidan kida uwarsa
duk ara ba kaw u nan su".
Sai tace a.a ba haka za'a yiba wannan muna fukar
tsohuwar ba sha sbato za'ayi mata kwata kwata ta dena zuwa
tace kwarai da gaske dan sai tazo ake tada tsirfa iri iri Mama
tace kwarai da gaske fun da ya shigo gidan nan sai tsirfa iri.iri
tace wannap tace wancan dan haka abin da za muyi kenan.
Ita, kuma wannan karamar alhakin ki tashi a tsaye
masifa da bala, i iri iri ma ya isheta kuma a hanata kulashi ni
54
RAYUWAR KENAN
Kumi ai zan turo Ladidi ta zauna dan su hadu dan da ya fara
zuwa da kike ta kura masa in ma yazo sai yayi hira da ni ko
kanwar ta, har ya tafi gaisuwace kawai take hadasu, tace
"kinji ko ai wallali ba haka aka bar shiba ga shi baya
ganin mutuncin kowa tace Nuran? Shifa laile kinyi sake za ki
ayi miki sakiyar da babu kuma dan haka yan zu ki fara ba da
kafin muji ba yani?". Ya kawo amman dai kinsan arha bata
ado? Ta dan karyar da wiya Aunty kici ka in basu isa ba kinsan
yanzu fishi ya keyi bawani kudi nake samu ba sai na cefane ko
in karyar bani da lafiya ya ban kudi yauwa suka tafa ashe kina,
da da bara ni kuma a dai dai lokaci nafito zan kaiwa Yaya
ruwa da juis da yace in hada masa na taho mukaci karo da Fati
zata shigo gida tai wani ban gajeni, na wai ga tare da danyin
murmushi na dan cigaba da tafiya tai kiran sunana na amsa tare
da dada juyowa sai cewa tayi
"banza uwar yan shishshigi mara zuciya har lemo kike
kawo wa Yaya wato kin hada da rubutu dan ki mallakeshi dan
ba haka kika bar shiba kina san kiraba shidsa uwarsa da mu, to
wallahi munfi karfinki kina ganin mai zai yi da ke mara usuli.
yar tsuntuwa ka marki"
Nan take nace
"bari in gaya miki babu wanda yafi wani, agun ubangiji
sai mai tsoronsa, kuma ni ma 'ya ce domin ba daga sama aka
jehoni ba kune ku ke jayayya da ikon Allah na wuce wata, tana
kallo har na shiga dakin Yaya na da alamun amsar da na bata ta
tashigeta. haka nima jikina a sanyaye nayi sallama a kofar
dakin a kace uwar gida ana maraba cikin murmushi da
annashuwa ya tareni tare da karbar dan tiren hannuna bayan na
gaisheshi sama sama.
"Husna mai yake faruwa ban saba ganin ki cikin bacin
rai ba". nace
"kamawa tai ka ganni hakan tare da nura damuwa a
fuskarsa ya yambayeni mai kuma yafaru? Bai shafekaba "babu
wani abin da zai dame ki kice bai dameni ba sai dai in babu so
55
RAYUWAR KENAN
da kauna" sai da naga yana neman bata rai sosai sai nace haba
Yayana wallahi bansan ranka ya baci ko kadan" yace
"zancan yaushe kuma ai tuntuni ya ce nadaga hannu to
yi hakuri abin da yasa bansar sanar dakai, nasan sai kayi
magana kuma abin bacin rai ne."
"Keda waye sai kayi mini alkawarin baza kace komai
ba yace nayi sai nace wata yar maganace ta hadamu da Fati
dan haka taga shigowata ma bari in koma cikin gidan"
nan da nan ya bata rai ya sha kunu tare da cewa to sai
me? in ta ga shigowarki, dan kar tace ta ganki a dakina? Na
kada kai ya tuntsire da dariya yana cewa
"ai ni, haka nake so, ni dai a tsorace nake cewa nake ni
dai muyi maganar da takawoni" ya miko min album) na kalle
shi ma tambaya na meye, tare da kanne ido yace bude kiga
amarya da angonta.
shafin farko hoto ni da shi lokacin da ya ke mikamin gift na biyu ma haka amman mun sake salo sai dana bude rabin
alban din duk da gani sai shi sannan nida Ramlat da Hajiya daidai sauran kawayam mu, gashi ajikin hotonan mu ni dashi
anrurrubuta wasu kalaman soyayya sai dana gama karantawa
nazo karshen albun din na dago kaina na kalleshi nace
"ah Yaya ba ka da dama yanzu idan aka ga wadannan
rubutun sai fa ankaranta
ya kuro min ido tare da cewa to ina lefin mai so dan
yayi bege? Sai naji wani irin dadi yalillibeni harsai dana
murmusa, shiMa murmushin yake yana nuna ni da yatsa sannan
yai kiran sunana daga can cikin mako gwaransa tare da wasu
kalamai masu dadi sauraro nace maikake cewa ya fada cikin
rada
"wallahi murmushinki yakan sani farin ciki da anna
shuwa, dan haka ina son kullum inga kina fara'a" na gyada kai
irin haka sai dai ina tare da kai nanuna shi in Kuma babu kai
babu farin ciki---a---Fati ce a tsaye akofar dakin tana kallan
mu, ayatsine kazo inji mama" tare da harara. yace mata "shine
56
RAYUHAR KENAN
zaki shigowa mutane daki ko sallama babu" ba tsammani sai
cewa tayi "kayi hakuri kai ya kamata in yiwa sallama amman
banda wannan karyar"
ta juya ta fice aikuwa sai yatashi da sauri yana huci ya
bita dan magana ma ya kasa ina kokarin dakatar dashi, amman
ina har ya kai soron cikin gidan ni Kuma jikina a sanyaye nabi
bayan sa saboda nasan kiran da akeyi mishi bana dadi bane.
Shigarsa ke da wuya yafara kalla mata kira shiru bata amsaba.
kansa tsaye ya nufi falon ni kuma dakin hajiya na zarce tarike
haba
"oh 'ya'yan nan harna manta dake" nace kin ga" tare
da mika mata albun nace kallan Hatunan walimar mu, na tsaya
yi dan haka kika ga
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13