ganin inda mutum ya
daurawa kansa ciwo?" Abba kenan yake wa Mama fada
Nanda nan ta canja da cewa "a'a Alhaji yi hakuri" gani nayi daga dawowarka ko hutawa bakayi ba zata fara hadamu"
"ai ba hadi bane gaskiyane" yace nasha' magani?
Nagir giza, kai, daman aikwai wata durowar ajiye magunguna,
16
RAYUWAR KENAN
ya mike ya dauko magani yace in bude firij, in dauko, ruwa
nasha magani" Sanan nima yabani abin da ya rabawa kowa,
yace inje in kwanta.
Bayan Abba ya raba mana tsaraba yadda ya ba "yarsa
fati haka, nima ya bani. Mama kuwa harda set, din yari da
sarka da awarwaro. Salim kuwa jens, kala kala Yaya na, ba
abarshi a baya ba hatta da su Ramlat, da yan aiki gidan kowa
sai godiya amma, banda Umma da Fati. Idan ka duba
fuskokinsu Sai fishi sukeyi saboda abin da aka bani.
Daga nan sai Abba ya ware kayan Hajiya ta Maiduguri
ya kirawo Yaya, yace mashi
a kamata yasa ranar da zashi maidugurin" sai yace
yawwwaya yatsinke a gindin kaba abokina. Al-Ameen yayo
min wava ran Lahadi daurin auren kanwarsa, zani maiduguri"
sai Abban yace "to ran yau shekenan zaka tafi".
"Ran juma'a Yaya ya bashi amsa
to amma bana son tafiyar mota kaje Bank ka amso
N50,000 ka yanki tiket" Yaya sai murna yana godiya, dan
haka. acikin farin ciki yakammala kin-kin tsawa, sannan yai
kirana mukayi sallama yana cewa, don dale zai tafi ya barni
nace babu komai ina yin murmushi sai yace
"ke baki ma damuba, Yayan naki zai tafi kwana biyu"
muna hada ido sai naji duk kunya ta kamani yana murmushi
yace to ki tanadar mini amsata kafin in dawo inna zuwa sai ki
bani a haka dai mukayi Sallama.
Na kwan ta barci daren da ya tafi amman barcin ya
gagara, in banda tunane tunane babu abin da zuciyata takeyi
can natuno da maganar Magaji data Yaya ko wacce da inda ta
nufa
"oh ni Husna ya zanyi da makircin wannan mutumin
amman Allah yafishi Yaya na kuma insha Allah bazan bashi
kunyaba"
Gari yana wayewa duk sai najini sakaka babu wani
kuza ri, komai nakeyi, sai ya fado sai tunanin shi ya fado min a
17
RAYUWAR KENAN
rai, har ina tuna mganar da mukayi yana cewa inkula da kaina
ya bani a manar kai na, can acikin zuciyata ina cewa mai yake
shirin faruwane?
Bayan Yaya ya sauka atilin jirgin sai ya yiwa babban a
amininsa Al-ameen waya yazo ya tareshi suka rungume juna
yana cewa
"dan mutanen kano yayi wuyar gani"
yadan bugi kafadarsa yana murmushi
"na maiduguri fa?" Yaja hannun sa, su ka nufi gunda
aka tanada don ayi fakin. Tafiyar dasu ka yi bata da yawa sai
yayi fakin akofar katon farin gidan.
Yau kemanin kwana bakwai ke nan da tafiya ga shi
yau lahadi kuma itace ranar da Yaya zai dawo dan haka na
kasa zaune na kasa tsaye abin har mamaki yake bani, can sai
nayi tunani in shiga gidan su Ranlat dan mutattauna.
"Yar halak sai gata ta shigo tana dariya wai tashigo
sukaci karo da Fati, nan take ta fara cewa anzo ayi munafirci,
"to shine kuma na dariya? Na kamo hanunta zoki zauna
daman yanzu nake shirin zuwa gunki"
"to mai kuma ya faru tana zaro ido" shine na fara bata
labarin abubuwan da suka faru tsakanin mu da Yaya, sai tace
"ni dai nasan ba a abota tsakanin mace da namiji.
Saidai in soyayyace tsaka ninsu kai Yaya, ba so yayya
ai ta haka yakeyi miniba in kikace irin ta wadakan wace sai
inyarda can Ramlat tayi shiru komai take tanuni.
"yauwa in haka ne dai mai yasa baya nunawa Fati, ai
itama kanwarsace acikin zuciyata na cewa "shakikiya kuwa,
"amman shawarar da zan baki ki bishi da yadda yake so"
ai bamu rufe baki ba sai mukaji Sallama Yaya ne, ya
shigo sai muka bude baki muna mamaki babu wanda yai
magana Ramlat ce ta gaisheshi ni kuna ya kalleni yace,
"ko, inkoma ne?,
bansan lokacin dana yi farat nace "lah, yi hakuri Yaya
na", Ramlat takalleni tace
18
RAYUWAR KENAN
"munafuka shima ya kelle mu yace "bata da
gaskiyane?" A'a Yaya, ita tasan abin da tayi sai anjiman ku
tana tafiya tana dariya.
Tun ran da Yaya ya dawo bamu sami zamaba ni ina
zirga zirgar makaranta shikuma kullum yana ofis, inya shigo
sai ya tarar ina aiki dan haka bamu ganaba damancan ni, hakan
nakeso wallahi narasa abin da yake da muna ko hada ido
mukayi sai gabana ya fadi balle ina ji maganarsa dan haka inna
ga lokacin shigowarsa yayi sai in sauri in koma daki yau dai
mai zai faru.
中市 ***** ******
una zaune a tsakar gida sai ga yaro yayi sallama, wai
ana kiran Husna, akace injiwa? Wai Mannir ne, na
Mtsaya ina tunanin a ina nasan mai wannan sunan can
Mama ta katsemini tunani da cewa "kai ko Fati aka
ce?" yace
"a'a Husna," na tashi zan fita ta daka min tsawa
ina zakai shasha sha, uwar yan sanbanza daga jin
kira har kinyi kofar gida to Fati, ce zata".
Gamamakin ta ai sai ta ga wata galleliyar mota a fake
kai zuciyarta barazana take mata, bamai wannan motar bane
wata kila abokin Yayane, sai tahau waige waige, sai yazuge
gilas dimotar yace
"yan mata sannun dai, dan Allah, Husna, nake son
gani" ko tananan sai ta yatsine fuska "oho ban saniba,
kodayake ba'a ban garanmi takeba"
ya yi sauran cewa gidan ba daya bane? Dayane ina
nufin tana bangaran yan aiki tana aiki, in sukone ka iya
bayarwa akai mata"
19
RAYUWAR KENAN
tana magana, tana karye karye yace "yanzu kina nufin
bazan sami, damar ganinta ba ko bata nan" kai kacika gaddama
ana kaika kana dawowa"
kafin tarufe baki sai ga Yaya yai fakin suka gaisa yace
nazo induba mutuniyar ne yace babu damuwa ka ganta ne a,a Fati natsaye sororo tana kallansu tana mamaki Yaya aima
yasan shi sai ya katse ta da cewa tayo mishi kiranta ta, tafi
badan rai yaso ba. Don haka, da tashiga balallaine ta fada miniba, can sai ga yaya, yana kallamin kira kafin Mama, tayi
magana yace mutumin daya buge ta kwanaki ne yazo duba ta.
Bai saurari abin da zata ceba yace mini zo muje, tun daga zaure yafara murmushi.
Hajiya, Husna, manya"
"aikune manya mu kananane yakake?
Lafiya, nazo inyi dubiyane, nadanyi murmushi nace lah, ni har.
na manta".
" lallai ashe kin manta da wanda yakasance acikin begen ki, tun lokacin da nadaura idona akan ki nakasa sukuni"
muna hada ido nasaki murmushi ya cigaba "nayi niyar dawowa amma hakan bata samuba dan alokacin sauran kwana biyu na tafi aikin hajji ga zirga zirgar kamfani da jama'a ba dai rai yasoba na tafi banzo nafurta miki abin dayake zuciyata ba
dan haka inadawowa na kasa zama har sai nazo naga gimbiya
dan inji tabakinki dan haka ya kika се?"
Nidai rufe ido na yi ina murmushi. "Haba gimbiya rashin amsarki zaizame min tashin hankali ya langwabar da kai kitai makeni." Na dankawfar da kaina, nace
to mai zance,"
"amsa zakibani wanda yakamu da ciwan so. Kuma
itace maganin", ya dada rawsayar da kai kamar zaiyi kuka, nan
dan naji tausayinsa yakamani na danyi marmushi tare dace wa "Allah, ya mu tare,"
"yauwa gimbiya ta na jinjina miki kuma kinburge ni kin kuma sani farin cikin da bansan iya karshen shiba na gode
20
RAYUWAR KENAN
da karbar soyayyata hannu biyu dan haka ni zan wuce, sai
yaushe?"".
Gawannan yamika min wata leda wacce da ganin ta
kasan lafiyayyace nadan girgiza kai alamun bazan karbaba yace
ashe ba kya so na ya dai takura min ba, ason rai na ba sabo da
tunanin abinda zai faru gani kaina.
Inna shiga gidan. bayan na shiga gidan kuwa abin da
nake gudun ya faru, nazarce kicin na sameta tana rabon abinci
madurkusa tare da nuna mata
"gashi yabani budawar dazatayi turare kala biyu sai
zobin gwal cikin kwantenarsa. "ye menace gani, ba dake na ke
ba jikina na rawa na kasa magana takama kunnena ta murde na
kwalla wata kara dan Allah, mama, kiyi hakuri.
"sai kin fada min dalilin da yasa ya baki" nace cewa
yayi yana sona dan yana sanki" akwai wata maganar akasa
shegiya mara mutunci don haka, wakika fi bare ki kaishi, masu
usulinma ba akawo musuba sai ke to tashi ki bangu kwalelenki
wannan kayan".
Natasi jikina asanyaye bayan na idar da sallar ne nayi
addu'o aina kamar yadda na saba na mikawa mahallicci na
kukana ya jikai na yakawo mu karshin wannan rayuwar, ina
cikin hakane Yaya, ya turo in kawo mashi abincinsa, shima ya
idar da sallar.
Bayan nayi sallama nadan jira ya shafa addu'a yana
mai kallo na yana ce wa, "Allahumma Ameen".
Ina zaune a kasa ya kira sunnana asanyaye tare da
nuna mini kujera yace
"kanwata har saurayin naki ya tafine? Sai naji wata irin
kunya takamani nace
"haba, yaya",
"to nayi karyane bashi bane irin wannan dadewa,"
"gaisawa kawai mukayi yace bai yarda ba sai na tabe
baki kamar inyi kuka, ya zaro ido yana daga hannu "to
shikenan na yarda hakanne, mu rufe wannan shafin".
21
RAYUWAR KENAN
"Ina alkawarina"?
nayi saurin daga kai "lah, wane alkawari?" Wanne ma
zakice? Sboda baki damu dani ba". Cikin fushi ya cigaba
"ai wannan wulakanci ne muyi magana dake amman
kice kin manta"? nace "Haba Yaya, ya zakace ban damu da kai
ba ko ina walakanta ka inna ga mai wulakanta ka sai inda
karfina ya kare".
Ga mamaki na sai ya daka min tsawa ya dakatar dani
da hanunsa "rufe min baki naga yanzu kika dawo daga gun
wani" naja bakina nayi shiru ina kallon abin mamaki yaci gaba
da magana "saboda kin mai dani dan iska ga alkawarin damuka
yi kice kin manta"
Ina shirin yi masa magana ya daka mintsawa yace
inbashi gu, ainan danan hawaye suka fara zabomin sai gidan su
Ramlat wannan shine rana zafi inuwa kuna.
Ina shiga nayi sa'a ba kowa a tsakar gidan akwance
akan gado na sameta tana karanta wani littafi mai suna NANA
BILKISU na H. Kilima gani na tayi nafada kusa da ita ina
faman kuka, nan da nan tayi wurgi da littafin sai faman
tambayata take mai ya faru? Ina na kasa bata amsa sai sautin
kuka ne mai ban tausayi yake fitowa, sai da naci kuka na iya
sanrai sannan na tashi naga ashe itama kukan takeyi, na dafata
tare da kiran sunan ta kiyi hakuri nace da ita.
Ta dago kanta tace dani nima inyi hakuri dan Allah ki
daina sa bacin rai indai halin Mama ne, inda sabo kin saba tun
kina yar karamarki dan haka wataran sai labari.
Hawaye masu zafi suka kwaranyo min nace
"haba, Ramlat, dole, abin duniya yayi min yawa, yau
Yaya ne ya yi min abin da bai taba yi minba dole hankalina ya
tashi" sannan nabata labarin abin da ya faru tun daga zuwan
Mannir, har shigata da kiran da yayi mun. Amman mai zai faru
sai naga tana dariya, abin dai na ga ya wuce tunanina sai nayi
sororo ina kallanta sai cewa tayi
22
RAVUBAR KENAA
"to albishirinki. yar uwa wallahi duk. abinda yayi
kishin ki ne yasa" nace "wane irin kishi bafa cewa yayi yana so
na ba cewa yayi mukulla abota"
"lallai Husna, ke yarinyace man kaza. inkin tuna
nadade ina sheda miki irin kaunar da yake nuna miki tana da
nasaba, da soyayya kuma komai da ran dadewa zainuna miki
dan haka karki fiddarai da rahamar ubangiji, kamar littafin nan
danake karantawa farkon rayuwar yarinyar tasha wuya, amman
karshe Allah, ya daukakata, dan haka, kema ina yi miki fatan
fiye da haka amin".
Na katseta da cewa "amma maganar Yaya, indai hakan
ta dosa bazan aminceba tunda yanzu yafara yimin haka Ramlat
ita dai abin dariya kawai yake bata daga nan mukayi sallama
sai mun hadu a makaranta.
Kamar yadda muka saba duk ranar litinin mukan tsaya
a gaban asambilet, bayan munyin salatin Annabi, an bude da
addua, sannan prinsipal dinmu tayi mana gargadi akan saka
kanan hijabi da wasu dalibai suke sawa. Sannan tacigaba da
sanar mana dacewa zamu shiga hutun eister Monday da good
friday sannan ga asabar da lahadi takuma umarcemu da kada
muyi wadan nan kwanaki, aban za, mu dage da karatun don
kuwa muna dawowa zamu fara jarabawa.
Bayan mun tashine a hanya Ramlat, take tambayata ko
mun sasanta da Yayan? Nace matá wallahi haryan zu duk
narasa abin dayake yimin dadi sai rama nakeyi nakasa taransa
da maganar muna hada ido sai inji nakasa ta buka komai, ta
girgiza kai sannan tace in daure insame shi adakinsa in bashi
hakuri-nace "haba Raınlat, kin manta har koroni yayi daga
dakin sannan kice inje, sai kace mara zuciya inna koma duk.
abin da yace min nina janyowa kai na"
tsaya Husna, ko kinsan duk, abinda kikayi mishi baki
fadi ba. domin Yaya, ba abin yadawa ne ba". can nadan nisa
sannan nace hakane zan bashi hakuri amma ba a dakin sa ba" ta
yomin gwalo, tace
23
RAYUWAR KENAN
"amman zaki shiga na aurenku a haka muka karasa
gida, ina shiga natarar munyi bakuwa Hajiyan maiduguri
mahaifiyar Abba. tazo tayi mana yan kwanaki kamar yadda ta
saba dan ita acan take da zama bayan mahaifin Abba ya rasu
tunyana karami Yayi aure acan yagirma dan haka, har, yanzu
suna tare da mai gidanta.
Gidan yayi tsit kamar ba, uwar maigidan ce tazo ba
don Mama, ba'a son ranta take zuwa ba dan gani take kamar
kwada yin wani abune yake kawota ko zata tsare mata wani
abin.
irin wannan hali na Mama kowa yasanta da shi ahalinyanzuma suna daki tunda suka gaisa basu kara fitowa ba ina
ganinta nahau tsalle ina oyoyo ga Hajiya itama da mumarta
tana cewa ga yar garinmu ga Husna, wanan sunan da take fada
min ya samo usiline daga can maidugurin aka tsince ni. dan
haka, inta yasamo usiline daga can maidugurin akak tsince ni.
dan haka, inta fada dadi nakeji ai, ina zuwa na fada kan
cinyarta adaidai lokacin da yaya, yashigo yace
"a'a mai zan gani sai kin karasata aba, ba kwariba"
nace "tsahon kashi ya fi'naka kwari" nai amfani da
wannan damar nayi masa magana daman kafa nake nema sai
muka sa dariya yaci gabada cewa
"Wallahi ki dagata murabu lafiya kar talangwabe
mana", nace "im bari intashi dan kiris take jira muka dada
kwashewa da dariya cikin dakin da take sauka muka wuni
muna ta tsokanar ta har Abba, ya dawo shima da fara'arsa.
Dan haka, kullum da safe zaishiga suyi hira haka in ya
dawo. Ni kuwa nasamu yancin kaina da safe inna gama hada
abinci na kai sai inzo gun hajiya na daina saura ran sidi,
nakuma samu lafiya, don wanan masifar da hantarar yayi sauki
sai dai aiki, shikuma ba abin kibane dan nariga nasaba in banyi
bama banajin dadin.
Yau lahadi kowa hutu vake Abba da Yaya basu fita ba,
muna gun hajiya muna tahira abin gwanin ban sha'awa.
24
RAYUWAR KENAN
Lokacin cin abinci yayi Mama. ta turo fati Abba yazo
yaci abinci yace a kawo mishi dakin Hajiya anan zaici. Bayan
an kammala akwashe kayan tsab, sai aka, kawo na mahaifiyarsa, aroba mai murfi ana ajiyewa sai Yaya, ya kalleni
nima hakan kafin mu Ankara Abba sai yayi sauri yadau abinci
yana kwallawa Mama, kira yayin da ita kuma Hajiya take kokarin dakatar dashi, amma ina har yakai kofar falon sukaci
karo
dan wulakanci da rashin mutunta na gaba ki rasa
kwanan da zaki zuba wa Hajiya abinci sai wannan" in uwarki
ce zaki bata anan"
amma ina kamar bada ita yake ba cingan nema abokinta tana wani girgiza tana tauna shi kokarin da katar dashi
da hannun ta, take "ka gama? daman tunda wannan matar tazo kake wani take take iri -iri baka shigowa sai bayan sha daya
wai hira kake" ka fin ta karasa ji kake tas!!! Ya bata kyawawan
mari hagu da dama, nan danan muka yo tsakar gidan Hajiya
tana yimishi, fada tana cewa.
"idan ya kara marin matarsa akanta bata yafe ba ita. ko, ame aka bata abincin ci zatayi dan ba. bakuwar zafi bace"
Shima Yaya, yana ta Abba. hakuri dan gaskıya nsa
yayi munmunar baci dan nì dai kasa hada ido nayi dashe yayr
ficewarsa daga gidan.
Fati kuwa ban faman kunkuni ba abin da take a
zuciyata, nace bakiyi sa'ar uwa ba, dan halinsu daya abin da
mama, ta suka shizata girba.
Bayan ankwana biyune Hajiya tace mushirya zamu
raka ta gidan wani dan uwanta a hotoro ta riga ta sanarwa da
Abba, yace Yaya yakaimu bayan nayi kwalleyata tsaf. nasaki
gashin kaina, duk, da bawata kyakkawar kulawa yake samuba.
duk da haka, bana sake da gyara shi na dauko daya daga cikin
rigunan da Abba ya kawo mana na sa. gaskiya ba yabon kai ba
nayi kyau kamar a indiya, ita dai Fati. ba'asan ranta zata ba
25
RAYUWAR KENAN
saboda abin da yafaru kuma, tana ganin tafi karfin tajero dani
a takaice dai dolece tasa ta bimu.
Muna fitowa kofar gida Yaya yana zaune a kan mota
yana murmushi yace
"yar tsohuwa ina zaki kaimin kannen nawa?"
"Af kamanta ma zaka kaini gaisuwa gidan kanina.
tunjiya a kafada maka" yace
"ba mantawa nayiba na zata sai da daddare" cikin
harara "aka ce maka ni matar kulle ce tun banje gidanba" Sai
muka kwashe da dariya.
A dai-dai lokacin da muka shiga zauran gidan su
Ramlat bayan an amsa Sallama umminsu ta tareta da murna
da fara ar ta tana cewa,
"lale maraba" suka shiga falon mu kuma muka zarce
dakinsu Ramlat. Shigarmu ke da wuya Ramlat tace
"Hajiya Fati, talaka nagainku?" tana wani yatsine ta
bata amsa "ah, sai maikudi mai kudimma malti muloniya".
"A lallai kice mudage da nema, in muna so mu ganki"
muka kwashe da dariya tace, "Husna, ya hutu tunda Hajiya tazo
baki lekoba nace
umma ta"
"yan zuma zamu rakata Hotoro zamu yi ta yi gaisuwa".
"wazai kai ku," nace "Yaya ne".
"don Allah ki dauko gyalenki muje tace saina tambayi,
Fati tace "sai ki tambaya ai zata barki tace Hajiya ai
bani ce da kaina ba" can sai mukaji Yaya ya shigo ya na cewa
to sarakan surutu ku fito mutafi kar lokaci ya kure"
ya kalli Ramlat "ke ko kema za kiyi rakiyar"
to bari intambayo" tashi ga "au ummi Hajiya har ta
fita ne?", yanzu Yaya ya shigo yayi kiransu, tace ai inkun hadu
ba kwason rabuwa, sannan tace
"ummi sunce inzo mu tafi shine nace su tsaya intam
bayeki", ta danyi murmushi yayi kyau yar gidan ummi, adawo
lafiya".
26
RAYUWAR KENAN
Hajiya tana gaba mu uku muna baya tunda muka hau
kan kwaltar yankaba babu wanda yayi magana can Yaya ne ya
kauda shirun da saka kaset din music, irin na kasar turai yako
ware redio ananfa ya tabo Hajiya ta toshe kunne tana cewa
kai ba "dan Allah ka cire mana wannan gulalantun
yaran kaba" mu kuwa dariya muke musu shi kuma sai faman
gyada kai yake yi ta sake cewa gwara Hausa imma zaginmu
sukeyi muna ji,"sai Ramlat tace ai yasan abin suke cewa Hajiya
tace gwaran cin yammna? Tasake cewa turancine, nidai bana so
gwara yasa na, waazi Yaya, yace kunji dan mai gidanki malami
ne to saiki bari in mun koma gida mu saka miki tuni takai
mishi duka mukuwa, sai dariya muke musu fati, tace duk kuyi
shiru asamata wa'azin mala'ikan mutuwa, sai muka yi shiru
dan duk, rigimar ta, tana jin ance mutuwa zata bari dariya muke
muna dada kyakya cewa munkafe bakinta. Batare da bata
lokaciba har mun hau saban titin nan wanda zai kaika hotoro
wato ringi raod titin gwanin bansha'awa ga fitilu sunyi reras,
anan ne, nayi magana nace
"a gaskiya titin nan yana birgeni domin ya tsaru gashi
zai kaika unguwanni da yawa, wannan gwamnnati babu abin da
za'a ce sai Allah yai mata jagora" can yaya. yace "ai wannan
kadan ki ka gani sai kin shiga soko-sako kinga irin cigaban da
ake samu nagyaran hanyoyin mugudane, gaskiya balefi".
sai Fati, itama tace kaji Husna, ke wata gwamnati kika
sani? Muda muke tare da ya'yan manyan kasannan
amakaranta muke ganin abin da ake. shukawa yanzu kowa
yahau kan mulki kansa yake so wannan titinan mada ake
gyarawa dan sunsan hanyace ta wucewar manya, in abin
gaskiyane a gyara titinan sabon gari da 'yan kura mana".
sai Yaya, yace "ai komai sai a hankali, daidai lokacin
da yaya, yasha kwanan Hajiya tace ashe baka manta gidan ba".
yace ah, nida gidan zuwa na, su Fati ne, dai nake tsammani
basu taba zuwa ba"
27
RAYUWAR KENAN
tai saurin cewa "e, wallahi, Abba, bai taba kawo muba
rufe mana baki mara zuminci uwar kice ya kamata ta nuna
miki, in dangin tane kinsan gida gida ta zunburo baki dan ta
tsani aiyi mata fada babu wanda ya sa, baki gaba ki dayan mu
han killanmu yana kan kofar gidan da yake kokarin yin fakin
get ne da Masallaci mutane suna fitowa da alamun an, idar da
Sallar la asar, sai ga Alhaji Mallam dan uwan Hajiyan da
fara'arsa ya taremu yana yi mana sannu da zuwa
"Hajiya saukar yaushe? Yakai kallonsa kanmu ah aha,
da amare aka zo?
"e gasunan sai ka zaba in kuma su Hajiya suka fasa
muku kwuna shike nan mukuwa sai dariya muke.
Bayan mun shiga ne aka taremu da gara iri-iri gabaki
dayan mu muna zaune ne afalonsa yaran gidan su ka shigo
daya bayan daya suna gaishemu bayan gama gaishe-gashe tare
dayi musu gaisuwa can saiga samari subiyu sun shigo bayan
sun makawa Yaya, hannu muma, mun gai sa, suka
ta'tambayarmu, wace makaranta mukeyi a haka hira tai:tsawo
ina kallan yaya, sai faman hararata yakeyi ni kuwa ina sane sai
surutu nake tayi Ramlat ashe. itama ta lura, sai shurina take da
kafarta ko da yaga daya daga cikin su mai suna Musbahu yana
nema yawuce gona da iri sai mukaga ya mike yace mu same
shi, a waje ai gabaki daya suma suka kai kallo gareshi ya ya zaka fita yakalli agogo tare da murmushin karfin hali.
"ah yakamata mu tafine kar lokaci yakure" mukuwa dariya muke domin mundago yawar.
Tashinsa ke da wuya sai Musbahu ya dawo kujerar daya daga kujerun da Yaya ya tashi yana cemin
"Husna, dariyar me kukeyi?" nace "babu ko mai" yana tambayata yana wani kashe mini ido mai yana so yazo gida muyi hira nace bayan wadda mukeyi yanzu yace ai, wannan daban take nadai nuna mishi bani da lokaci yadai dage. Can su Hajiya banyan sun gama hirar zumuncinsu tace mutafi, matan gidan suka hada mana goma ta arziki,
28
RAYUH AR AENAN
Tunda muka fito yaya. ya haderai ya ki yi mana
magana har abin yafara damuna a zuciyata ina cewa ba dama
muyi hira da wani sai ya hau fushi wannan abu nashi yana bani
mamaki dan da ba haka yake yimin ba, a haka dai har muka zo
gida yanayin paking, sai gawata ta faru.
motar Mannir muka gani yana jiranmu yana ganinımu yafito
yana washe baki "gimbiya sannunku da zuwa" nima da fara'a
ta nace amma ka sha jirako?
"Wallahi kakarmuce da tazo muka raka unguwa",
yausauri yakarasa ya gaisheta sannan shima Yaya yamika mishi
hannu duk dai da ya sanshi kuma inda sabo sun saba amma
wannan lokacin bai sakar mishi fuska ba.
Itadai Hajiya har tsokanarsa take irin wasan jika da
kaka, nakuma gabatar da Ramlat tare da matsayinta Fati, kuwa
ko kallo bamu ishetaba tai shigewar ta gida nima bayan mun
danyi hira yace zai dawo suyi Sallama da Hajiya sannan
mukayi Sallama nashiga gida.
Bayan mun kammala jarabawar shiga aji shidane,
watarana muna dakin Hajiya tare da Ramlat tana ta jammu da
hirarsu ta mutanda, can sai ga Fati, ta shigo akaci gabada hira ta
ce mana acikin satin nan zata koma Maiduguri nan da nan na
dau bata rai na kalleta.
"Haba, Hajiya, yanzu tafiya zakiyi? Ki barımu dan
Allah tunda hutu mukeyi zanbiki" sai ta dan dafani
"ki yi hakuri, sai na dauwo kinga inna tafi dake zan
katse miki karatun Qur'anin da kukeyi naji Alhaji yana cewa.
in kun sauka kafin ku gama makaranta sai a hada ayi muku
walima tare da bikin gama makarantarku ta boko, in kuma kan
lokacin kun gama ruwan ido kun tsayar da miji kunga har aure
kenan".
sai Fati, tazun buro baki tace "tirkashi wallahi baza
aimin aure yanzuba sai naga karshen biro" ta kalleta tace
29
RAYUWAR KENAN
"ai ba kace da kankiba ke kuma Ramlatu fa."? na yi
farat nace "ai ita jirantama akeyi dan matakine da tuni munsha
biki" muka tafa
"akace mai surutunfa" nayi dariya nace
"sai dai ki barmin tsohon mijinki kinga sai in koma
garinmu da zama" dakin ya hargitse da surutu, sai ga Abba, da
Baba Sani, ya kallemu yace
"shakiyen ya ran nan bakwa barinta ta huta" Abba ya
kara da cewa "balle Husna indai kana so kaga walwalarta sai
agaban Hajiya" anan muka barsu mukuma muka fita adai dai
soro mukaci karo da Yaya, yana kallona naji tsigar jikina tayi
yar muka gaisa yace "sarakan surutu ina zaku?" nidai kai a
sunkuye sai Ramlat ce, take bashi amsa, ya ciga da cewa
"ko yauma samarin nakune suka zo"
na yi saurin dago kai muka hada ido yace abinda
zanfada muku yanzu ba lokacin wasa bane ku dage da karatu
ana komawa makaranta ajin karshe, zaku shiga sannan ku bada
himma akan Qur'ani ku samu saka mako mai kyau daman
nasan kuda kokari" Yaya na kenan kamar yasan hirar da muka
gama kenan.
Ana, gobe Hajiya zata tafi Mannir ya turo yana
gaisheta kuma yace yazo ne suyi sallama, yanzu kowa ya
sanshi hatta da Abba, ya san matsayinsa dan haka Abba yace da
Salim ya bude mishi kofar sitin room ta waje ya shigo hajiya ta
dauko mayafi, ina zaune atsakar gida ta kalleni tana tsokanata
"na tafi gun angona ko zakiraka nine?" Mama tana
zaune inban da harararmu ba'abin da takeyi bayan sun gaisa
tare da hira mai tsaho aka turo inzo yana ganina ya sakar min
murmushi wanda ba kowane namijine ya iyashi ina sanshi idan
naganshi har wani sanyi nakeji azuciyata dan haka ban san
lokacin da namai da martaniba Hajiya dai mikewa tayi tana
tsoka narmu ya kawo 10,000 yace in bata sam taki kar ba, ai.
Bayan mun gama hira yace da Salim abude but din
motarsa adauko kaya na Hajiya ne. na kalleshi nace "haba
30
RAYUWAR KENAN
Mannir baka gajiya?" shima ya kwai-kwayeni sai na rufe ido
dan kunya yace "Husna ina sonki kuma a rayuwata ina son
mace mai kunya" nace
"nagode Allah ya saka". Bayan ya tafi nashiga gida
antaru akan kayan daya kawo ana ta surutu Hajiya tana cewa
amayar sunyi yawa sai Salim, yace ya tafi nima yabani N1000
Abba. yace "ai yaran dan mutuncine daga ganinsa dan manyan
mutane ne" Hajiya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 13