sai addua takeyi tana cewa kar in butur
cemishi.
Kashe gari aka hada da kayan da Abba ya siyo mata
Yaya ya kaita iyafot, sai Maiduguri ni kuma muna kuka muka
rabu, ina karanta inna lillahi, sabo da tunanin halin da zan shiga
bayan tafiyarta haka kuwa akayi na kama kangin bota da takura
iri iri ta kamani tayi mun duka wai da Hajiya tazo mun shirya
mata makirci kuma da saurayina yazo ban nuna masa itaba sai
na gabatar da Hajiya, kuma tunda tazo na gujesu abinci ma da
ita nake ci sai ta kulleni adaki tace inci ragowar munafunci da
take koyamin haka na wuni ina kuka ina dada kokawa har sai
da Yaya ya dawo daga aiki sannan ta bude ni.
Makarantar da muke zuwa a garejin gidan ranar
banjeba saboda bani da kwarin jiki yunwa taci karfina a haka
na ci gaba da rayuwata daman lokacin da Hajiya ta tafi shima
Abba yayi tafiya ta sati daya bayan ya dawo ne nima nashi ga
sahun yaran gida kashe gari da safe muna karyawa akan dani
tibil. kowa yayi shiru Abba da Yaya ne kawo suke hirar
kasuwancinsu can Abba ya kalleni yace
"Husna yau ba Hajiya kina cin abinci damu, kaka, mai
dadi" nasa dariya nace "wallahi da ta tafi banji dadi ba" karaf.
Mama tace "ai sai ki tashi ki bita" uwar yan shishshigi ba inji
Fati" Abba ya kalleta yace "dan uwarki shishshigin me tayi?"
kafin yakarasa jikake tas!!! Yaya, ya kifa mata mari yana cewa
"da ke ake magana ita da kakarta" Mama, itama tai caras ta
karba "ah taje tanemi kakarta acan duniya yar tsintuwar wacce
31
RAYUWAR KENAN
baasan uslintaba kafin yace wani abin Abba, ya daka mata
Isawa yana mai nunata da hannu
"ki. kiyayeni ki kuma nutsu kisan duk abin da kike
yiwa yarinyar nan bawai bansani bane?" To kinyi na farko
kinyi na karshe, ko labari naji sai nadau mummunan mataki
akanki".
"kema dan uwarki mahauciya ba daga sama aka
jehotaba. ke da uwarki mahaukaciya mara rabo alahira da
duniyar, ta ya ya Allah zai bamu amana ki dinda, wulakanta
wa. kiji tsoron gamuwarki da Ubangijinki, ko dan da kika
Haifa acikin kine kika takura mishi sai ya saka masa,
ballantana wanda aka baki amanarsa".
Ran kowa abace ni kuwa nayi shiru na kasa motsi
zuciya tace kaucin take bugama da karfi kukan ma, yaki zuma
Allah, ne kadai, Allah ne kadai yasan halin da nake ciki Abba.
ne, ya katseni, da kiran suna na, "kiyi hakuri kinji duk abin da
kike so kidinga tambayata in bana nan ga Nura nan Allah ya
miki albarka tashi ki tafi makaranta.
Misalin daya da rabi nadare natashi fir gigit daga
mafarkin da nake yi, na tashi zaune ina salati ina cewa ya
Allah, kacika min burina dan fiyayan talikai can sai nasaka
kuka nadubi halin dana ke ciki na ce wani mafarki yana zama
gaskiya musamman a'irin yana yin dana ga matar da nayi
mafarki da ita "wai ina cikin tafiya na wahala ga yunwa can sai
nafada wata gona mai yalwatatciyar fire da korayen ciyawa ga
yunwa ina ji sai naga wani abinci mara kyau na dauka zanci
kenan sai ga wata mata da fararan tufafi ajikinta fara gashin ta
har gadan baya tana kirana, bayan naje gareta ta kwace wannan
abincin mara kyau ta yar ta kawo mini wani kwano mai kyau
tace inci abincin ciki kuma tace ta dade tana ne mana Allah bai
nufaba mun haduba, amma tana me yimin nasiha in rike addini
na in bautawa Allah shi daya na cigaba da hakuri tare da
addu'a, bayan wuya sai dadi sai tabace".
32
RAYUWAR KENAN
Nayi addua ain da akeyi in anyi mafarki, na yiwa lyaye
na addu'a nace in amace suke Allah ya kai musu kabarinsu
haka na tashi da safe jikina asanyaye ina tuna nin wazan
fadawa mafarkin nan, abin yana ta cina aria
Wata rana muna hira da Yaya sai na bashi labarin
mafarkin danayi ga mamaki na sai naga yayi shiru shima
jikinsa ya yi sanyi idanunsa sun kawo kwalla kamar zata zubo
ina kallon sa da kyar ya shanye yana gudun in ta zubo nima zan
tayar da hankalina nace
"Yaya, me ye naga kayi shiru, sai yayi murmushin
karfin hali sannan yace "Husna a gaskiya mafarkin akwai alheri
aciki ina gani Allah ya kusa yanke wannan wahalar in sha
Allah, kwanan nan zakiga iyayanki" nayi dariya na tafa hannu
na tashi ina tsalle yacе
"to tsaya kiji yanzu abin da zamuyi sadaka zamuyi
amman dan kar kowa yasani zan kai kudi gidan masu waina
suyi mana sadakar acan. Kuma zanbawa mai kosai a bakin titi
kudi itama ta rabawa yara Allah ya tabbatar da Alhairi". nace
Amin Yaya na, yace
" kuma Allah ya cikawa Yaya naki nashi burin" na ce
Amin. oho bansan, abin da yake nufiba a haka muka rabu,
akwana a tashi babu wuya agun Allah.
Yau munyi saukar Qur'ani kowa sai murna da farin
ciki da walwala dan haka Abba, ya sai raguna guda uku ni da
fati da Ramlat, akayi mana sadaka amma, sai aka dakatar da
walima sai nan da wata biyu dai dai lokaci zamuyi Kandi
(Candy), sai a hada da bikin gaba daya. amma agaskiya Fati.
bata mai da hankali sai wasa daga yawan biki sai na fati wata
rana ma tana gida tana kale kale taki binmu makaranta mu dai
Alhamdu Lillah, dan haka Yaya da Abba da Baban Ramlat sun
yaba mana kwarai da gaske kuma sun bamu kyaututtuka masu
yawa Fati kuma tasha fada kuma har Abba, yana cemata in bata
maida han kaliba ba ruwan sa da ita sai dai taga yana yimana
33
RAYUWAR KENAN
abin duniya rainta dai yayi mummunan baci daga ita har
uwarta.
Mudai mungode wa Allah, haka kuma munci gaba da
tulawar Qur'ani tare da wasu muhimman littafai har dai hutun
mu yakare muka koma makaranta.
A daidai wannan lokacin soyayyarmu da abin kaunata,
Mannir, dada habbaka take har yafara sheda min muna gama
makaranta zai turo magabatansa, haka, kuma samari sunyi min
cah, domin nagirma kyauna ya da da fitowa sosai shikuma
Yaya Nura, abinsa yakan daure minkai ba dama yaganni da
wani a tsaye sai yakoreni Mannir, ma ko kwarjini yakeyi masa
nidai bansaniba sauda yauwa ina fadawa Ramlat, cewa abin
yana damuna zan tambaye shi dalilin da yasa yake yimin haka
sai tace indan saurara.
Bangaran Mama kuwa ta tsani ta ganni da farcen susa
duk irin kyau tuttukar da samari suke yimin sai da ta kwace, ta
bai wa Yarta ina ji ina gani akwai wata rana Mannir yake
cemin yakamata muje zango ko Sahad ko muje Welcare yadan
yimin siyayyar kayan shafe shafe maimakon inyi murna sai
idaniya ta ce take kokarin zubda hawaye cikin gigita ye kira
suna na, "Husna, daga wannan maganar sai rai yabaci, to kiyi
hakuri in bakyaso kibari sai insiyo inkawo miki" sai na samsa
ina kuka, ina girgiza kai alamar banaso, yace sai na fadi dalili
nadai nuna masa babu can yadan yi shiru da alamun abinne
yake damun sa ko mamaki yake bashi oho, dago kan da zanyi
muka hada ido dashi hawayene kawai afuskata
"haba my sweet idan nabata mikine kiyi hakuri na dada
girgiza kai, to menene,?" ya ada yin jugun can yai saurin daga
kai ni kuwa "Husna bari in tambayeki dan Allah zaki fada min
na daga kai, yacigaba
"anya, kuwa Maman su Fati, itace ta haife ki?"
ai dajin wannan tambaya sai zuciya ta ta kama bugawa bakina
sai rawa yake na kasa bashi amsa sai kuka a haka dai muka
rabu, ban nuna masa cewar ba itace ta haifeniba agaskiya
34
RAYUWAR KENAN
natau sayawa kaina domin komai, daran da dewa sai ya gane
domin zancan duniya, baya buya.
A haka na cigaba da rayuwata cikin wahala, takura har
Allah, ya kaimu ranar firatikal, san nan muka zana jarabawar.
karshe dan haka yau ranar farin ciki ce agun dalibai da
lyayansu, kowa kagani sai murna, ga kuma kyau tuttuka da
akayi mana ni da Ramlat da sauran yan guruf dinmu ambamu
kyautar littai tafai masu amfani wanda bayan mun dawo gida
zasu ci gaba da taimaka mana, kuma ko munci gaba da
makaranta basai mun nema ba. Bayan angama bamu kyauta sai
muka fara daukar hotuna da kawayanmu kuma muka bawa juna
adireshi, wasu na kuka wasu na farin ciki haka muka rabu.
Bayan mun huta sai Yaya, ya yi kiranmu mu uku dan
ita ma Fatin ta gama, lokacin yace mana musa ranar da
mukeso aiyi mana walima dan yayi wa Hajiyar Maiduguri
alkawari, in lokacin yayi zai je, su taho tare anan dai muka
yanke shawarar sati biyu masu zuwa kuma ranar lahadi ta sama
kenan bayan anbuga kati sannan yayi shirin yin tafiya. Ni
kuwa aduk lokacin da yace zai tafi sai hankalina yatashi ahaka
dai yararrashe ni da cewa, in yadawo zai zomin da wani
albishiri da yai shekara da shekaru yana son fada mini, ai nan
da nan na fara tsalle ina murna, yana daga min hannu muka
rabu gaskiya babu abin da zance sai godiyar mahallicinmu da
ya ban basira ilimi, hazaka, duk, da galllazawar da akemin da
nuna halin ko inkula da ake yimin bai hanani kula da kaina da
tarbiya da hali nagari da addini da tarbiya mai kyauba.
Dan haka, dole in godewa Allah mai shiryar da wanda
yaso gashi malamanmu mutanen gari dana unguwa sai yabo
na, ake ana tayani murna domin in mun fita mu ukun akasarin
mutane nida Ramlat suke yima murna wacce kuwa ake so yar
lele, wasu har shagube sukeyi mata saboda hakan ta daina
binmu.
Daman haka, bahaushe yace ka ki naka duniya ta soshi
in kuwa ka soshi duniyar ta kishi. Kwana biyu Yaya yayi sai
35
RAYUWAR KENAN
gasu tare da Hajiya. Abba, ya taramu adakin da mahaifiyarsa
take sauka yayi godiya ga Allah sannan yace mu lissafa abin da
muke bukata bayan mungama ne kuma kowacce yabata turmi
kala shida tare da N10;000 duk, mutun daya, shikuma Yaya,
cewa yake
"gaskya Abba. kana shagwaba kannan nan nawa"
Abba, yana dariya yace "ban da abinka duk abin da akayi ba
afadi ba saboda sun nuna hazaka kwarai da gaske"
"nima ina da tawa gudunmawar" sai Fati, tace mai za
kayi mana, yace nadau nauyin robobi sitika kalanda tare da duk
kanin abin da za'aci" kafin ya karasa mun hau tafa hannu dan
murna sallamar Baba Sani ce ta katsemu yana cewa lallai yara
duniya, tayi dadi Abba, yace "shigo ayi dakai kafin su gaisa da
Hajiya ya mikawa yaya mukullin mota ka bude but ka kwaso
kwalaye guda biyu ka dauko. Bayan yara sun shigo dashi sai ya
kallemu yace tawa gudunmmawar wannan kajine guda ashirin
da hudu sannan ya fito da wata leda ya mikawa Hajiya yace
kibasu set daya daya" ai sai muka zazzaro ido ingilish gwalne
yari da sarka muna murna Hajiya sai godiya takeyi can yace ina
Mamane akace tana falo Abba, yace Salim yai kiranta bayan
sun gaisa da B. Sani tana yimishi tsiya tana cewa
"ka hada kan iyali a kulla mai kyau" shi kuma yace
"mata kishiyace dai kike tsoro dan haka ki saurari zuwanta"
tace in da dadi a aika ta gidan ka mana"
yace to dai tunda kin tsorata ayi shiru da zancan"
mudai farin ciki ya ishemu bayan an nuna mata abubuwan da
aka bamu tayi godiya amma iya fuskarta kawai.
"sai Hajiya tace to akwai sauran rina akaba tunda duk
wanan hakin da iyaye yakamata subawa yayansu sun bamu
saura da me kowace ta fito da mijin aure" Abba, ya kalli Yaya,
yace har kai ba kana wani soshe soshen kai ba" su Baba. Sani
sukace kwarai Hajiya kinyi daidai daman akwai maganar a
zuciyar mu" wai Allah ji nayi zuciyata tana bugawa kamar zata
fado kasa domin nasan Ramalat da Fati, suna da wadan da suke
36
☑
RAYUWAR KENAN
sonsu da aure ni kuwa mannir ne, amma yau kusan watansa
daya rabona dashi bansan dalili kin zuwansa ba abin duniya
yataru yayi min yawa.
Can akai kiran sunana tunanin me ki ke yi Yaya,"
kenan hankalinsa yana kaina murmushin karfin hali "babu
komai" "to sai kushirya mu je fagge don dinkuna" Bayan
munje ne kowaccen mu, tazabi irin dinkunan da takeso ya biya
daga nan muka shiga kofar wambai siyan robobi san nan muka
shiga cikin gari muka ba da kwangilar kek, cincin metfey,
sambusa, dadai sauransu, bayan mundawo gidane har munkai
zaure ya kwalla min, kira na juyo idan kin shiga ki kawo min
abinci na nace to bayan na dauko kayan abinci sai na tsaya
bakin kofar ina kwada sallama sai na ji yace "firem came in"
maganar ta bani mamaki tare da dariya dan haka, ina murmushi
na shiga tare da kallona yace "wallahi kinyi mini kyau
musamman da kika shigo da fara, a" na sunkuyar da kaina
domin nidai irin wannan kallan na Yaya, yana firgitani, haka
dai cikin jin kunyarsa na gaisheshi namike zan tafi, yai saurin
kiran sunana
tsaya mana alkawarin da nace zanfada miki wani
albaishir" kafin ya karasa nace "yauwa sai kabani na sani wuri
na zauna da farko dai yafara da cemin congratulations on
poulur'anic Graduation muka hada ido tare dayin godiya,.
Husna; ina fatan za'a gaiyace ni, walimar kuma in
kasance babban bako agun"
nace "Haba, ai kaine uban taro domin kai mai gaiyatar
wasu ne" da "gaske kike karfa Mannir, yazo yahanani rawar
gaban hantisi?" Ai yana fadar haka na canja fuska yana nunani
da yatsa "kinga har kinbata rai, saboda na taba na hannun
damarki in kuma ba haka bane maganar da zuce, ta fado min
zuciya tacewar mufito da miji ai kuwa nan da nan naji wani irin
damauwa acikin raina. Ya katseni da cewa
"tunanin me kike" a dai dai lokacin kuma idanuna sun
ciko da kwalla, babu damar inmai da ita nan danan sai kuka
37
RAYUWAR KENAN
kafin kace kwabo Yaya ya gigice yana rarra shina yana cewa in
yafe masa in ya fada mini abin daya batan rai, ya kasa zaune ya
kasa tsaye daga karshe har durkusa wa yayi abin mamaki
shima sai yasa kuka "ko baki fada ba nasan maganar mannir ce
ko inec samarinki kina ganin kamar na tauye miki hakkinki na
rabaki da su, alhali sam ba haka ba ne" muka hada ido nayi
saurin dauke kaina.
yaci gaba da zudda hawaye tare da wata iri shashshe ka, wanda
bazan iya kwatan ta yadda nake ji a cikin zuciyataba..
"Husna ....banyi haka dan in cuceki ba na yine dan
kafa wata ginshi ki rayuwa kuma mafi dacewa tsakanina dake
ina fatan ba zaki zargeni ba, tunba yanzu ba, naso in furta miki
abin da yake zuciyata, amma sai na ga cewa biki gama
mallakar hankalin badan haka na biyo miki ta wata sigar dan
kulla wata mu'amalar da zata sa mukara shakuwa kafin rana iri
ta yau ta zo nace miki mukulla abota, amma a zahiri ba haka ne
azuciyata ba, Husna, ba wani abu bane azuciyata illah So, da
kaunarki nakeyi miki kuma tun kina karamarki Allah ya
jarabce ni dan haka, ba tun yanzu nake kishin inganki da wani
kuna zance ba"
yaja wani dogon numfashi sannan yaci gaba
"Haka, kuma in kika lura duk samarin da suke zuwa
gunki, basa dawowa ninake kararsu" sannan ya danyi shiru
kana ya dago ya yi kirana oh ni dai azaune nake kawai nazama
kamar mutum mutumi can sai ga wasu sababbin hawayen suna
faman zabari a fuskata wanda na kasa tantancewa na dadi ne
ko, na bakin cikin da zan kasance akan abin da yake furtawa.
Kiran sunana yake yana kara wa "ki tai makeni ki amsa
soyayyata hannu biyu ni dai ka sake nayi har da wani
murmushi da bansan ko nameye bane domin abin da yake
faruwane, nake ganin kamar a mafarki murmushin da yaga nayi shima sai kuka yakoma murmushi ni, kuma garin haka, har
mun hada ido sai nayi sauri na kare da kau da nawa ai sai ya gigice cewa yake "Husna Ki kalleni mana kar zuciyar Yayan
38
RAYUW AR KENAN
naki ta fashe, domin ta dade dai jan ruwa fashewa kawai take
jira kinji my love dan Allah kidan kalloni"
nan da nan naisaurin rufe idona da tafin hanuna, dan
wata irin kunyace naji ta kamani can cikin zuciyata kuwa amsa
kuwa take tayi tana cemishi nima ina sonka ina sonka amma
bakina yaka sa, furta hakan can wata zuciya naso baki na ya
hana Allah mai yadda yaso a takaice dai bansan lokacin dana
amsa mishiba da Yayana I LOVE YOU ina gama fada kuma
na kwasa da gudu ne gidansu Ramlat akwance take na fada
kusa da ita na riketa ina cewa
""yar uwa albishirin ki, goro na tashi tare da mika mata
hannu ban kisha labari", ita kuwa sai zumudi take tace ke ban
halinki nan in kinga ana son jin labari daga gunki sai kin ja wa
mutum rai, dan Allah, ji wata irin murna da kike yi kamar
wacce aka bawa kyautar duniya".
na karkada hannu "ai wannan yafi duniya da abin
cikinta dadi aguna amma dai bari in fada miki wato magnar
kice ta ba, tabbata Yaya Nura ya furta na kwashe duk yadda
mukayi na sheda mata dan murna kamani tayi Allah, ya
tabbatar da alheri sai dai kuma ana dara ga dare yayi muka
hada ido nace Mamansa ko? nadanyi shiru ina tunanin abin da
zai taniina ta sani.
Kwalla ce ta fara zubowa, Ramlat tace to zaki fara
kuua no nace "haba Ramlat ai ya zama dole dan kuwa
ina cikin tashin hankali domin ina bukatar iyayena kuma a
nemi aure na a gaban su zai fi daraja da mutumci duk da nasan
babu matsala agun Abba, amma uwarsa da danginsa fa?
Gaskiya bazan yarda ayi mun aure ba tare da naga iyayena ba."
Dan haka duk dan halak yake neman iyayensa na dau alkawari
insha Allah duk inda suke sai na nemesu can kuka na ya
tsananta itama kukan take yi muna cikin wannan halin
Ummansu ta shigo tana salati "ya'yannan mai zangani haka sai
ta zauna "Husna me akayi muku? Ko ke da maman taki ce? na
39
RAYUWAR KENAN
girgiza kai to me ya faru? Ko dadi ne yayi muku yawa?"
Ramlat ba tambayar ku nake yi ba.
Da yake bama boyemata komai ita babu ruwanta sai
mu zauna da ita ana hira ana dariya dan haka, Ramla ce ta fede
mata biri har witsiyarsa itama tana ji sai ta nisa tace in kwantar
da hankalina babu yadda su Mama, za suyi dani domin idan
Abba, ya amince to anyi angama saboda yafi karfin gidansa
nidai shawarar da zan baki karki sake kinuna masa afili dan in
suka gane da wuri za afuskanci matsalą, watakilama kafin
yakai maganar gun manya uwar tasa ta bi ta karkashin kasa ta
wargza lamarin domin ita a nata tsarin akwai yarinyar da ta
keso ya aura Yar yayar ta Ladidi, dan haka, kikwantar da
hankaliki kici gaba da rokun ubangijinki ya zaba mana mafi
alkairi dan haka, ku gyara fuskarku karma kununa mashi wani
bacin rai".
Bayan mun fito yana tsaye akofar gida muna hada ido
muka kwashe da dariya shima dariyar yake yace "daga nin ku
baku da gaskiya Ramlat, tace "haba, yaya, mai kagani ku yo
kiran fati, mutafi karbo dinki da sauran abubuwan da zamuyi
amfani da su. Haka dai mukai ta zirga ziga har ana gabe
walimar ma tunda muka fita bamu dawo ba sai kusan magariba
mai zai faru muna shigowa da kaya ahannuna mukai ido biyu
da Ladidi, da kanwarta da fara'arta ina shirin yi mata, magana
ita kuma tana kokarin taro Fati ta wani banga jeni,ko waiwayo
wa, batayi ba, balle tace wani abin nasan tana sane domin da
biyu, tayi Ramlatce, ta jahannuna, muka karasa cikin gidan
kuwa da gidan su Ramlat babba, da yaro, kowa kagani farin
ciki yakeyi.
Amma ban da mutum, daya kamar ba abin alheri ne,
yasamu yar taba, sai faman hade fuska take dan dai babu damar
yace kar afasane saboda ni da amfasa nidai kullum acikin dari
dari, nake da su, kullum addu'a ta ayi taro lafiya agama lafiya,
da safe kowa kagani yayi wanka yayi kwalliya ni kuwa tasa
kani aikace, aikacen da bagaira ba dalili dana gama wannan ace
40
RAYUHAR KENAN
inyi wannan har kawayen mu suka fara taruwa sai Hajiyan maidugurice tai kirana tace ni hazan yi kwalliyarba? Nace aiki
aka sani tace inbar aikin inje inshirya in ta yi magana ince ita ta sani.
Daya daga cikin kayan da aka dinka mana nasa Ramlat,
ma irin nawa tasa bayan na fita mukaci gaba da harkoki
camara man da mai daukar Hoto sunfara aiki amma agun
babu fati sai su Ladidi, can akace Mama tana kirana nashi ga.
da fara'ata, dan a zatona yau ba ranar bakin ciki bace aikuwa
muna hada ido nasan babu mutunci tare da ita gabana sai dakan
uku yake nayi saurin cewa innalillah, ta daka min tsaya da
cewa
"waya baki izin saka kayan jikinki batare da
kintambayi Fati ba, wani za'a fara sawaba?"
"Gani nayi ta rigani shiryawa"
"ke dakata ki ji na jikinta nice na dinka mata wannan
kuma ubantane yayi muku, ko dan an karaki an yi dake shine
zakifi masu uban zakewa to tunmuna sheda juna kije ki cire sai
taga ma, saka kala shidan da nayi mata sannan kufara sa wa
tare"
Su Ladidi, kuma sai dariya suke yi. Bayan na tube,
kayan na sawo doguwar riga nasa jikina asanyaye na fito kamar
anzare min laka, ina hango Ramlat tana ta dawainiya da jama,
ta daga min hannu alamun tambaya. Hajiyama tana cikin 'yan
uwanta da abokan arziki ta bude baki tana shirin kirana can
kuma su Fatine, da kawayenta sai shewa sukeyi raina inyai
dubu yabaci domin da basu fadawa kowa abin da akai minba da
zan iya daurewa, in shiga cikin jama'a amma ina sai na zama
saniyar ware.
Can sai ga babban bakonan yashigo les fari ajikinsa da
hula irin ta yarbawa akansa, da fara'arsa da kwarjinin sa yana
waige waige nasan ni yakesan gani, ni kuma na shagala da
kallon abin farin cikin idon yan mata kuma cah, akansa tun ba
41
RAYUWAR KENAN
Ladidi ba sai wani irin kalo take mishi shikuwa bai san tana
nan ba.
Ramlat, ya kwallawa kira yana tambayarta da hannu
ina ina nake, ta nuno mishi ni muna hada ido sai naga
Kamanninsa sun canja yana kara sowa yace in biyo shi dakin
hajiya ya yan na gan ki haka? Ko baki da lafiyane?".
Tambayar tasa kamar ya murdomin ruwan hamaye, da
leda a hannunsa, sai na gaya saketa ya karaso guna yana cewa
haba sahibata nasanki da hakuri tare da jurewla ko wane irin
al'amari dan haka yau ran farin ciki ce agunmu bai kamata duk.
irin abin da za'a miki kiyi bakin cikiba ungo wannan".
Hankicine fari kal na karba na share hawayena, ina
kayanki nace
"mama ta hana ni sawa saboda me? Nayi shiru to shi
kenan ungo wannan kisa zan turo su Fati da Ramlat ankone
nayi mana ki yi sauri ki fito ina jiranki".
nidai kasa magana nayi, dana bude ledar les ne, fari
irin na jikinsa, anyi buba, can Ramlat, ta shigo tana tambayata
mai ke faruwa har nayi kwalliyar na cire? Kafin ince wani abu
Fati, ta shigo suna bude nasu les din kore da milk sai Fati, tai
saurin daukar koren tace Allah ya kiyaye ne anko da shege,
Ramlat, tace
"haba, agaskiya abin da kike yi bakya kyautawa"
"ke kinga babu ruwanki in kuma so kike ayi dake to'
Ramlat tace to wayake tsoranki nikin san in kika
yimin sai na rama shashasha, wallahi ba tasan abin da take yi
ba".
ta jani muka fita muka barta atsaye ah ni Husna na
godewa Allah Suttura itace mutun, ai ina zuwa kan cinyar
Hajiya na fada mai hoto ya dauke mu can sai ga Yaya ya shigo
da give a hannunsa ya mikamin aka dauka na mikawa Ramlat,
aka sake dauka ya dada miko min aka dada dauka sannan na
sake mika mata a haka sai da ya miko sau bakwai.
42
A
RAYUWAR KENAN
Haka kuma mun dau hotuna ni dashi babu adadi, fati,
kuma tana fitowa falon mamanta, ta shige ta saka mata kuka
tare da labarta mata irin abubuwan da suka faru can sai ga
sunan, tare da tawagar kawayen ta da Yayarta da dai sauransu,
muna hada ido suka bini da muguwar harara amman babu
damar bala'i, saboda muna tare da Yaya ga kuma Hajiyan maiduguri, sukai kiran mai hoto da camara man akai ta
haskasu ana kuma daukar Hoto tare da habaice habaice iri iri
Fati kuma kamar za'a mai da ita ciki sai kallo ya koma kansu
amma ba tai kara tsaka nina da Ramlat, muzo mu dau hoto da
ita ba.
ko Hajiya ma kallonsu take kawai kamar ba kakarsu
ba. can Yaya, Nura, yace Fati kuzo mu dau hoton tarihi da
hajiya sai taki uwar tana kallo maimakon tayi mata magana sai
ta kawda ido. Yaya kuwa sai haba haba ya ke yi da ni da
Ramlat,.
Can sai ga wani camara man da mai hoto tare da
tawagar gidan su Ramlat har da Umminta inda ake harkar
arziki tsiya bata zuwa. Ummi, tana shigowa da fara'ar ta ta
gaida su Mama ta kuma hadamu gu daya muka dau hotuna
babu adadi takuma, bamu gift din Qur'an kowaccan mu, ta
kuma bamu wasu tace murarraba wa kawayen mu har da su
Dala'ilu da dai sauransu haka kuma kawayenmu sunyi rawar
gani domin karatu sukai tayi babu sassautawa.
Su Fati kuwa sai kallo da ido ni dai tun anan na godewa Allah
da yasa na kasance mai kama kaina da kishin addinina a haka
dai taro ya tashi lafiya kowa ya tafi gidansa.
ayan na idar da sallar ishsha Yaya ya turo inzo suna da Byawa acikin dakinsa dan haka abakin kofar na tsaya ina
yin sallama, bayan amsa sallamar akace "M. Husna,
43
RAYUWAR KENAN
shigo nan duk daliban kine" ina murmushi na shiga ina basu
amsa da cewa
"haba sai dai almajiran malam" bayan gaishe gaishe
suka tayani murna sai wani ana ce mishi Gali yace
" munji wani abin alheri da ya ke faruwa ke da Yayan
naki Allah ya sanya Alheri" ni dai kunya bata bari na dago
kaina kale su ba shi kuwa gogan naka idonsa ya kura akai na
yaci gaba "tun da kunyar mu ki ke ji to ga wannan suka bani
kaya acikin leda bansan ko meye aciki ba, nayi godiya.
Bayan na mike to amarya sai mun hadu asiyan baki"
nace "ah, mai kuke ci na baka na zuba" gaba dayansu suka
kwashe da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 13