citta na hada musu jus nayi sallama
akace uwar gida shigo tare da murmushi nashigo bayan
yakarba nadurkusa har kasa na gaishesu, shi Kuma yana
gabatar dasu daya bayan daya can bayan sun gama an kwaso
kwanuka aka turo muzo abokin Yayane Gali ya miko min leda
Kuma yana mai tambayata ina aminiyata Ramlat
69
nace tana
RAYUH AR KENAN
gidansu yace rowarta nakeyi da bazan kirawota agaisa ba nace
"ai mubama rowa sai dai tsada damuke da ita" sai yace ko
nawa aka zai iya tayawa idan za'a sayar gabaki daya muka
kwashe da dariya bayan mun fito tare aka gaigaisa nace Ramlat
Gali ne yake nema ki tace ai gani yaganni ina murmushi yai
kiranta waje daya ana tayi masa tsiya.
Da alamun dai soyyace take shirin kulluwa a
tsakaninsu bayan sunyi sallama yace "yanzu sa idawa sunyi
mana yawa sai na dawo" Yaya yace "garama ka kama kafa da
sa idawar domin sai damu harka zata tafi dai-dai" ya kalleta
yace wai hakane mu dai dariya muke yi bayan tafiyar sa Yaya
bai barni na shigo gida ba muna tare yana tabani labari ina ta
tintsira dariya mai zai faru inuwa kawai muka gani abakin
kofar dakin Mama ce da Fati a tsaye fuskarsu babu rahama.
Gabaki dayanmu kamar mun hada baki muka durkusa "Mama
sannu da zuwa" ta da kamana tsawa "sannunku din banza
sannun kudin wofi marasa kunya naga abin naku so yake ya
wuce gona da iri ta kalleni "waike mai miji, to ko daddawace
sarkin miji daga yau sai yau kar in kara ganinki adakin nan"
Yaya yai saurin daga kai ya kalleta "dan Allah kiyi hakuri
daman bata shigowa sai dai in takawo min abincina" takatse shi
"kaga rufe min baki da baka son lefinta babu yara acikin gida
ne?ta mai da hankalin ta kaina zaki tashi kifita kokuwa sai
nashigo na tumurmusaki na taso zuciyata sai dukan uku-uku
ke yi ina zuwa dai-dai saro muka cikaro da Ladidi ashe tare
suke tawani kalleni ta watsar. A zuciyata nace dole ayi min
wannan wulakanci tunda suna tare da wacce suke son ya aura
ina shiga daki nadira, sana'ar kuka, ashe bi yoni tayi tace min
daga yau kar in kara shiga dakin Yaya tunda ni yar iska ce kar
in lalata mata 'da' kuma har gidan su Ramlat ma hatta, da kofar
gida kar ta kara ganin kafata, waiyo Allah ni Husna bansan
lokacin da wani sabon kuka yace karfina ba. wai nice yar iska
har ana cewa zan bata da namiji kamar Yaya nace ni Husna ina
duniya zata dani? Ina mamakin RAYUWA KENAN FA. shi
70
RAYUW AR KENAN
Kuwa Yaya al'amarin sa kusan ya zarce nawa domin ni na saba
idan yadawo daga aiki baya shigowa sai dai zaman kofar gida
ko zaiga gilmawata amma shiru abin yana bashi mamaki mai
yake hanani fitowa domin yasan ban kin shiga gun Ramlat ba
amman bani ba dalilina. wani lokaci sai dai ya shiga daki yana
kuka yana kuka yana tuna halin da nake ciki gashi yayi zuciya
da shiga gidan in dai ba safiyace ba, acikin wanan halin abokin
sa Gali ya sameshi yake tambayarsa me ayake farauwa, ko ba
shi da lafiya ne ya labarta m ishi halain da muke ciki ya ba shi
hnakauri kuma yace atura akira Ramlat da tace bazata samu
damaba aiki takeyi sukace dan Allah wata magana za'a
tambayeta da kyar akasha kanta ta fito Yayane yake tambayarta
Kwana biyu baya ganinta tace "Mamace ta turawa Ummi cewa
muna haduwa da Husna munayi mata rashin kunya shine aka
hanani shigowa da daimaganganu marasa dadi Yaya ya kalli
Ramlat yace "Baba Sani ya sani? Tace a'a ya girgiza kai idonsa
sunkada sunyi jawur atsorace Ramlat ta kalleshi tace "dan
Allah Yaya banfada maka wannan magana dan ka tgayar da
hankalin ka ba,"
"yace shi bawani abu bane, yake damun saba sai ta
kura min da akeyi yace so ake akashe Husna ko ita ba mutum
bace gaskiya ta kurawar tayi yawa ya sa kuka yanzuma
wayasan halin da take ciki, insha Allahu sai nakar bar mata
yancinta Kuma duk da uwata ce sai na fadawa Abba halin da
tasa husna kuma yan zuma na fara santa Yaya dai kamar wani
zararre su Gali sai rarra shinsa sukeyi. Abinci kuwa kullum
Ladidi ce take kai mishi in zata tafi kwalliya iri iri ta fesa
turare kala kala sai tazo dai dai inda nake zata kwallawa Fati
kira tace tazo su kaiwa mai gida abinci aran gada shewa wani
lokaci har gwalo suke yimin.
Bayan Ramlat) ta koma gida ummin su take tambaya
kiran mai ake yi mata ta kawashe duk yadda akayi ta sheda
mata ummi tanuna alamum tausayi tace wannan al'amari da
ban tausayi yake ta се "Mama tana bata mamaki in ban da
71
RAFUWAR LENAN
abinta abin da Allah yayi wani mutum bai isa yahana ba heka
kawai duk tabi ta tsangwami yara sai faman rama sukeyi bayan
ga abin yiwa fada nan agaban ta yau agan ta da wannan gabe da
wancan saurayi.
Bayan abba yadawo domin duk irim wannan iskancin.
ba ayi sai baya gari to Allah yadawo dashi lafiya bayan ya huta
Yaya ya kwashe duk halin da suke ciki ya fada masa ransa yai
mummunan baci yakuma tzusayawa dan nasa domin da ganin
sa kasan hankalinsa ba'a kwance yake ba, ya rarashe shi yacе
ya dinga daurewa zuciyarsa, domin ana son namiji da juriya da
dakiya sai Yaya ya sunkuyar da kansa yana sosa keya yave "ai
saboda Husna Abba bana so arabasu da Ramlat domin tana
dauke mata kewa a dai-dai likacin da Abba yashigo ma cikin
daki ina karatum qur ani ya leko da kansa yace Husna in kin
gama ina son ganinki a falo" bayan nayi sallama an amsa kaina
tsaye naje gaban Abba na dur kusa na gaisheshi sannan ya
kalleni yace "damme yasa kika dai na shiga gidan Allahji Sani
sai naji zuciyata tayi ras na dan isaya ina inda inda saboda ta
kamai me banace ga dalili ba kafin ince wani abin Mama tan
gani yin magana da ocwa ni na hanata a fusace yace mata
saboda me? Inwani lefi tayi kibari in dawo in yanke hukunci da
kaina ta sassau ta murya kamar zatayi kuka haba Allaji amaапа
daya take innaci amanarka sai Allah ya tambayeni abin da yasa
na hanata fita dankar ta janyo mana abin kunya" ya zaro ido
wana irin abin kunya tanunani da yatsa gata nan yawan banza,
takeyi in ta ga bakowa wata ranma bata kwana a gidan ya mike
tsaye wai haka Husna? Amma kinban kunya" ina shirin yin
magana ya hanani nasa kuka ina cewa wallahi Abba bansan
wannan maganarta ku ima Ramlat da Yaya suna sheda ta bana
yawo" sai tace "daman ko kisa kika yi agabansu baza su fadi
gaskiya ba Abba ya kare min tas sannan yace abin da Mamа
tayi ta yi dai-dai amman tabami inci gaba da zuwa gidan su
Ramia) amman duk ranar da aka tura ba' a same ni ba afada
masa ni kuma sai rera wani kuka nake mai ban tausayi ga Abba
72
RAYUWAR KENAN
baya san ya ganni ina kuka duk sai tausayina ya kamashi taga
hakanta bai cimma ruwaba, sai tace "sambata yarda in dinga
shiga gidan su Ramlat ba, ai tare muke zuwa yawon tace in
baka mantaba nadabe ina fada maka dan haka dolene muyi taka
tsantsan, yace to sai yayi shawara amman hakan da tayi tayi dai
dai ni kuma na tafi na bashi gu.
Bayan nakoma daki barci sam ya kaurace mini zazzabi
da ciwon kai sukayi min sallama zuciyata ta shiga nadama da
Kuma dana sanin kula Yaya, domin duk wannan sharrance
sharrancen da ukuba iri iri sabo da shi ake yimin dan haka can
cikin zuciya ta naji ana yi mini gargadi da cewa ke Husna ki
rabu da Nura ki Kuma san auranku ba zai yi wu ba" nasa kuka
ina kiran sunayen Allah natuna halin da nake ayanzu da kuma
da Ubana na kusa da ban shiga ba, can sai Yaya ya dada fado
min azuciya tare da wasu kallaman da yake yawan fada mini
musamman idan ya ganni a irin wannan halin.
"Husna nine Uwarki nine Ubanki inhar muna raye ba
zaki taba tozarta ba haka Kuma in duniya gabaki daya sun kiki
ni ina sonki dan haka sonki da kaunarki sun zame mini dole
domin lafiya suka karamin" nace Allah sarki Yaya kana so na
amman uwarka da yan uwanta basa so na, na dada rushewa da
kuka.
Akwan a tashi babu wuya watan tafiyar alhazai ya
tsaya har amfara tashi Abba ma gabe zai tafi domin sune
nafarko Kuma yana da bukatar yin kusan wata guda acan su
kuwa Yaya sai karshe dan haka Abba ya tara mu afalo har
Yaya bayan mun nutsu yakalleni yace "ke Husna kije kice
Ramlat tazo maza kuzo yanzu nafita duk, sai naji bawai saboda
nakai fiye da sati biyu ban fitaba Yayama sai dai in yashigo da
safe in mun hadu mugaisa. Bayan mun shigo yace, "duk yaji
abin da yake faruwa Kuma yace duk abin dayake gudana acikin
gidan nan yana sane shiru kawai yake ya kalli Fati yace "kafin
ya dawo acikin masu sonta ta tsayar da daya baya son ganin
samari barkatai, ke Kuma Husna ki yi takatsantsam bana son
73
RAYUWAR KENAN
yawo daga gidan Alhaji Sani ban yarda kije ko ina ba" nace to
"kema Ramlatu haka saboda yanzu mutum ake kiwo ba dabba
ba, dan haka na bar komai kuke bukata kutambayi mamanku
Kuma in sha Allah inna dawo zamuje maiduguri tare kafin biki
sai mu taho da hajiya anan nayi murmushi sai naga shima Yaya
yayi yana tsokanata "un, kaga an ambaci mai duguri har tayi
fara'a" yace "to Nura kai kace sai karshe" yace e, bukin dai sati
biyuma zanyi yace dan shashanci kai da baka taba zuwaba ina
lefin sati kaga daga nan sai ka hado lefenka" ya washe baki, to
shike nan ayi hakan" Mama kuwa tacika ta batse "haba Alhaji
lefenma dan dorewa karya gindi ba za'a hada ananba sai anje
har wata kasa dan wahala, yace aiba wahala bace lokacin abu
ayishi sai tamike agaskiya banyarda ba yace kamar me? Ya auri
wannan lalatacciyar yarinyar sai tasa kuka bayan ga halin da
take ciki kariga kasani amman ga yarinya yar mutunci waccе
akasan asalinta tana mututar sonsa", sai yace wace, ce? Tanuna
Ladidi kanta asunkuye a she duk hirar da akeyi zubda hawaye
takeyi saboda tsabagen kishi kafin Abba) ya farga shima Yayan
ya mike yana cewa bana sonta bazan aure taba akai kasuwa
Abba yamai da nunfashi yace "AlhamduLillah daman tamba
yarsa zanyi sai Kuma ga amsa tafito daga bakin sa" ita dai ta
inda tashiga bata nan take fitaba yace "kya yi kyagama auren
Nura da Husna sai baya rai na ahaka duk muka watse muka
barta ita da yayanta.
Tunda Abba) yatafi na dada shiga cikin sabuwar
takura, bani da katabus, dama Allah) ya tai maka Abba yaban
izinin shiga gidan su Ramlat Kuma ina fita ina ganin Yaya
Kuma muna tsayawa mu gaisa yayi in shiga dakinshi nace
Allah ya tsareni tun yana jin haushi har ya hakura. Kamar
yadda aka saba yauma anty Yayar Mama) tazo taji sharrin da
suka hada min yayi tasiri amman daga baya ga hukuncin da
Abba) ya yanke dan haka da har tafara murna, Kuma bakin
cikin cewar Nura yace bazai auri yartaba ya tsaya mata, ta hau
kutuntumamun ashar ina jigata, gabana sai dakan uku uku yake
74
MAYUWAR KENAN
ina karanto innaillahi wa, inna ilaihirraji'un can sai naji an
kwallamin kira nashiga tare da sallama ta daka min tsawa tare
da nunani da yatsa "ke dan ubanki dan uwarki idan baki
sunshigo bakya yi musu sannu da zuwa bare kizo ki gaishe
su? Nace "kiyi hakuri wallahi ban san kin zoba" kafin in
karasa sai saukar kyakkyawan mari naji a ku matu na, "rashin
muncin zakiyi min saboda kin mallake mana da, to bari kiji
inbaki rabu dashi ba sai kinyi dana sani domin Nura basa an'
uran ki bane dan haka kwaraya tabi kwarya kinji yan mata,
Kuma in baki fita hanyar sa ba ni da kene kinji ko ba kijiba
nace naji" na mike ina shafa inda a kamare ni, bayan na isa
aki na yi sallah na kai kukana gun mai share min hawaye tare
neman sauki yakuma yaye min wannan bawa nasa da a ke
on hallakani akansa, haka Kuma shima na nema mishi sauki
domin wani hadisi na Manzon Allah (SAW) yana cewa
"KU SOMA YAN UWANKU ABIN DA KUKE SOWA
KANKU YAU" Sauran kwana uku Yaya ya tafi amman yarasa
mai yake faruwa domin kwanan na ina yawan shareshi ko mur
asa naji yashigo sai nayi sauri in shiga daki idan Kuma fita
zanyi sai na tabbatar baya kofar gida in Kuma mun hadu sai
nasha kunu, dan haka yasami Ramlat yana sheda mata halin
dana canja Kuma tare da tambayarta ko wani abin akayi mini
tace bata saniba yadanyi shiru can yace mata to yanzu yana
son ganina dan sauran kwana uku su tashi tace zata fada min
atsakar gida kuwa yam mata Mamane suke ta sha aninsu wai
suna rubuta wa Yaya irin abubuwan da zai siyo musu sannan
anata yi mishi soye soye za'a kai mishi, idan ankalle ni asa
dariya ni dai har sai da ya rage ana gobe zai tafi na yarda muka
zauna shima sai da Ramlat) ta shidawa Ummi tace ina
walakanta Yaya gashi zaiyi tafiya yana so muyi sallama naki
sannan akayi kiransa gida ina zaune yashigo da fara'arsa yana
cewa "ran ginbiya shi dade mai ke faruwa ne?" na sunkuyar da
kaina nace "babu komai" "Haba Husna kin sani acikin
matsananci hali ko kindena so na ne" nayi shiru "nida zan tafi
75
RAYUWAR KENAN
maimakon murabu muna kuka nai saurin dago kai "ai ba
munrabu kenan ba zaka dawo" ya kanne ido daya "kika sani ko
zaki yi takaba" Ramlat tace "ah Yaya ba yanzuba, yace ai gani
nayi tun yanzu ta tsaneni a haka dai fuskata ba yabo ba fallasa
mukayi sallama nayi mishi kyakkya wan addu'a.
***** *****
*本本本
ayan tafiyar yaya) sannan nasan cewar ni mare niyace Bbani da kowa domin duk jikina yayi san yi kamar an zare
min laka haka kuma babu irin tuna nin da ban yiba da
dana sanin canja masa fuska dana yi amman duk da haka bana
yawan tunashi har abin yazo yana irin damuna dinnan nasan
addua a bata faduwa kasa banza tuna nina daya Allah) yasa
yaje asa'a ya dawo asa'a kuma ya musanya mana da mafi
alheri. Ranar sallah bayan ansakko daga masallacin idi Yaya ya
yo waya bayan sun gaisa da Mama da Fati yace, abaiwa Husna)
sai tace bata nan ga Ladidi tana wata irin magana kai kace
agaban sa take ko mai yace sai naga ta hade fuska ta mikawa
Fati. Ita mama tana tana cewa nace maka tana gidansu Ramlat
babu yaro can ta katse sallama damuka jine han kulam mu
yakoma kan mai maganar Ramlat ce "kizo Yayane yake
nemanki awaya" ina shirin yi mata gaddama tasa kama
hannuna muka fita da saurin mu "Hello my sweet I miss you"
na danyi murmushi yace ko da ban gani ba murmushin yayi
kyau" nace "nagode" "wai kina inane ina nemanki" nace
"lokacin da kuke magana ina wajan bata ga damar bani bane"
yace to mun gama azo iyafot atare ni" nace "Haba dai kabari
kutaho da Abba, mana" ya ce "bazan iya ba ina son ganin my
sweety ki fadawa Mama"
Bayan Yaya ya dawo Kuma lokacin bikinmu yamatso
dan baifi sauran kwana ashirin da biyar ba, Yaya ya kasa
sukuni kullum suna, tare da abokai ana tashirye shiryen biki ni
kuwa anawa bangaran har yanzu ya kasa gane kaina domin shi
76
RAYUWAR KENAN
kadai yake sha'a ninsa, ni kwata-kwatama banason ganinsa
wani zubin ko muryarsa na ji sai gaba na ya fadi amma a daidai wannan lokacin ma naga yana Haukan sona, ana sauran
kwana uku Abba Yaya ya shigo da katin darin auremmu ashe
daman tun acan saudiya ya bugoshi ina tsakar gida yami kamin
da ya yawuce kansa tsaye falo yana kallawa Mama kira yana yi
mata bayani ina ji ta kamashi da fada "sarkin doki kabari uban
naka yazo ko kai zaka daurawa kanka auran" yace "ai shiyasa
ma aka buga" tace wato kai inda kasan bakin maye haka kake
abin danake so baza kayi ba ko to ayi mu gani" yafito afusace
nikuwa ina duba abin dake jikin katin naji hantar cikina ta kada
nan da nan gumi yayi sallama ajikina ina rawar dari na karasa
daki nakwan ta zuciyata tana ta yi min aiyane aiyane yanzu da
gaskene wannan katin daurin aure nane da Nura? Wanda ya
yarda dani ya yarda da kaddara ya amince zai aureni batare da
ya san Usulina ko tushe naba, wanda ya tallafi rayuwa ta tun
ina yar ficiciyata, can naji wata tambaya awani bangaran.
aikuma duk wani da namiji yana son samarwa yayansa uwa
tagari mai usuli ko addinin ta ko dukiyarta ko kyanta ko? can
kuma da wata babbar muryar akace Husan!!! Abu na farko da
ya wajaba kiyi karbarwa kanki yanci yanci kuwa baizai samuba
sai kin gano iyayenki adai-dai nan nayanke shawarar kafin
Abba ya dawo zanbar gidan amman Kuma sauran mai? Hoto
nafa? Taya zanyi in sameshi? Domin kona tafi neman iyayena
bani da wata hujja da zan dogara da ita wajan nuna wa, dan
nemansu tunda ba sunansu na saniba. can natuna Yaya yasan
inda hoton yake dan haka Allah ya kaimu gobe nasan dabarar
da zanyi yadau komini
Kashe gari da sassafe nafaki ido na nufi dakinshi, yana
kan sallaya da carbi ahannun sa, bayan ya idar yashafa shima
abin ya bashi mamaki yace "Husna lafiya naganki da saasafe
adakin nan? Alhamdulillah Allah majibudda awat) yau kece, a
dakinnan ina fatan kin huce? Nadai saki fuskata, yaci gaba da
surutunsa "Husna kin hunce duk dadai basan lefin da nayi miki
77
RAYUWAR KENAN
ba dan Allah) kiyi hakuri ki amince muyi aure kinga lokaci ya.
gabato bai kamata haka tana faruwa atsakanin muba ina so ki
amince nine mai kaunarki kuma bazan batulce mikiba duk irin
halin da kika sami kanki kiyarda dani" Allah sarki Yaya muna
hada ido ya bani tausayi natuna kallmar da take cewa so hana
ganin lifi domin du irin abin danake yi mishi sam babu
alamunsa afuskar sa, na dai yi karfin hali nace "Yaya
kakwantar da hankalinka babu wani abu da kayi min duk abin
duk abin da kaga yafaru mukaddarine Kuma matar mutum
kabarinsa dan haka Allah yazaba mana mafi alkairi" yace
Ameen baya mun danyi shiru na wani lokaci kadan nace
"daman wata babar kawatace tazo daga maiduguri shine ana
hirar iyayena, tace in kawo mata Hoto na wanda muke tareda
yayata ajiki tagani shine nace tunda gobe zata tafi gashi Abba
bai dawoba in nasheda maka saika dauko min in nuna mata kila
ko adace", yace kwarai kuwa ai wannan Hoto yana da amfani
in sha Allah) shine sanadin gano yan uwanki, hakan yayi daidai
domin duk mai-nema yana tare da samu" dan haka bamu
rabuba sai da yayi mini alkawarin in ya dawo da yamma zai
daukomin, ina fitowa mukaci karo da Magaji yana kokarin
shigowa soro nai saurin dafe kirjina tare da innalillah) domin
kirjina dukan tara tara yakeyi ni ba abin in komaba domin ya
ganni, sai cewa yayi Allah) yakamaki munafika, har sammako
kikeyi kifaki ido kizo to yau Allah) ya tona asirinki". na
marerece ina bashi hakuri ya daka min tsawa wallahi tunda
nace ina sonki kika kini, sai nafadawa Mama wato ke sai dan
masu gidako? Ina tabbatar miki dace wa idan baki amince kin
aureni ba to asirinki yau yagama tonuwa" naji zuciyata ta dake
yana fada nima ina mayar masa nace ta Allah ba takaba kuma
sharrin ka babu inda zai kai ni domin narigaka nace Allah."
nabarshi nan bayan rana ta daga sai ga Magajin da Aunty sun
shigo har cikin gidan da alaman turoshi tayi yakira wata bayan
sun zauna ana ta shirya makirci iri iri domin sun rasa abin
dayake yimusu dadi dan tunda Ladidi tazo gidan bata isheshi
78
RAYUWAR KENAN
kalloba, domin bata birgeshi saboda itama baya shigowa gidan
sosai akace gara ayi sanadin dazan bargidan gaba ki da inba
rabamu dashi akayi ba abin da ake gudu ne zaifaru domin baifi
sati biyu daurin aurenba, tace ga maganganun da magaji yafada
mata kinga koda tabar gidan idan Alhaji yadawo sai ace bin
maza take yi saboda anyi mata ragana shine tashiga duniya
tare da shewa suna darya can Anty tace "ranafa tanayi kar
wankin hula ya kaimu dare gashi Nura karfe biyar yake
dawowa ya kamata kafin yadawo ankammala komai" ladidi da
fati sukace abarsu suyi min duka sukoreni sai Anti tace duk, ai
anyi mata mai sauki kisan mummuke zanyi mata ga masifa ga
radadi ga nauyi furtawa wani yaji sai mu da mukasan
muhmmancinsa sai ta radawa Mama tace "ahaiyye yar uwa
kinbirgeni takalli Fati tace "ina yajin da mukaci dan wake jiya
dauko minshi", Aunty takarba tace ku biyoni". Ni kuwa daidai
lokacin ina kwance zazzabi da ciwon kai sun rufeni ina fama
numfashi sama sama babu irin abin da bai da menba a rayuwata
ba nidai Allah Allah nake yaya yadawo ya daukomin Hotona
dare nayi zakara yabani sa'a idona a rufe yake sai naji kamar
motsin alamun shigowa daki amma jin haka baisa nabude ido
na ba dan banyi zato akwai mai shugowaba sai dai ko Ramlat.
gamamakina kai ka ce, wata almara ce ta saukar min sai naji an
danneni har nakasa motsawa bude idona keda wuya nagansu
sun dan danne ni kafin inbude bakina an tura min zani anrufe
kofar dakin sai ga Ladidi da Fati da wani kofi a hannunsu sai
naji Mama tana cewa "ku cika min aiki", can sai naji suna
kokarin cire min diros, can sai naji wani irin radadi agabana
domin azatona yajine suka zubamin suna dariya suna shewa
Mama cewa take daga yau karyar bin maza takare Kuma nayi
miki gargadin karki kara kula Nura kinki har sammako kikeyi
kije dakinsa ta dagayau karyarki ta kare sai dai kije ki auri dan
iska irinki badai Nura ba domin yayi miki nisa yanzu yanzun
nan ki tatara kayanki kibar gidan nan, inba hakaba karshen
rayuwar ki tazo". ina shirin mikewa na koma jabar sai su ladidi
79
RAYUWAR KENAN
suka dada bada min yajin a ido na waiyo Allah) ainan danan
narikice nagigice na dada kidimewa ina cewa waiyo Allah
kubani ruwa suna ihu suna dariya, sai naji rabo abakina nazata
ruwa ne ashe rabar yajince suka zuba mata ruwa sai mun
kasheki ina tafe ido arufe ina tuntube ina bugewa da bango ina
faduwa ina tashi a haka duk nafasa bakina da goshina duk jini,
cikin taimakon ubangiji har nafita sai nayi tunanin inna tafi a
haka ina zani dan haka sai nafada gidansu Ramlat) adaidai
zauren naji an sa ihu tare da salati an rikeni tana mai zangani na
nuna mata alamun ruwa ruwa Ummi da Ramlat suka kaini
gindin famfo suka sakar min ruwa suna tayani muna wankewa
da kar nabude ido yayi jawur kamar gawta. Su kuma sai kuka
sukeyi adai dai lokacin danaji kamar karamin wani radadi akeyi
bude bukina keda wiya sai numfashina ya dauke kwata kwata
bana motsawa bare numfashi suna salati suna cewa na mutu,
kash mai karatu anan zan tsaya sai kunemi littafin.
RAYUWARYAR KE NAN! NA BIYU
Dan Jin karshe labarin HUSNA?
Taku mai kaunarku
Hajiya Jameelah Y. dankaka (Brigade)
(Mrs) Halliru Jibril Gama (Aunty Mami)
80
Madaba'ar IYA RUWA
08029418426, 08065566690
RAYUNAR KEYANHAJIYA JAMEELA HALLIRU BRIGADE
AUNTY
RAYUWAR KENAN
2
he
Haj. Jameelah Halliru Birgade
(Aunty Mamee)
1
HakKın Mallaka (M) Haj. Jamila Halliru Brigad
Shekarar Bugu: 2008
"Afuwa makaranta littattafaina."
Assalamu alaikum warahmatullah.
bayan gaisuwa irin ta adinin musulinci gare ku, na ke so in yi amfani da wannan dmaar in ba ku hakuri bisa yawan korafe- korafenku da na ke samu ta hanyar wayar sadarwa ko wasika,
wasu ma har takanas suke zuwa saboda rashin fitowar littafina
RAYUWAR KE NAN '2', har jama'a sun fara cewa wai bazan
yi ba, to masu magana dai sun ce rana bata karya, sai dai uwar
diya ta ji kunya, kasancewar yau xusan shckara da rabi da bada aikin, Allah ya hada ni da wani macuci ya 6ata min labari
kuma ya fito da shi ana siyarwa ba tare da izinina ba. Don haka
za ku gan shi da hotan Shamsiyya Habib Kansakali, ba shi ne
aihinin littafin RAYUWAR KENAN ba, ga shi Allah ya nufa
na fidda na biyu da na ukun lokaci daya za ku ga hoton
shararriyar sabuwar 'yar wasan nan wato ZAINAB ADAM
(Zec) a maimakon hoton Shamsiyya Kansakali da ke bangon
wancan, a kula makaranta! Na gode.
Sako daga marubuciyar
H. Jamecla DAN KAKA Birgade
(Mrs Halliru Jibril Gama)
Allah Ya sa mu dace amin
Godiya
Dukkannin godiya ta tabbata ga Ubangiji madaukakin sarki
mai kowa mai komai tsira da aminci su kara rtabbata ga
Annabi Muhammad da Ahlinsa da sahabbansa har ila yaumul
Kiyamati.
2
(Gargadi
Ba a yarda wani ko wata su yi amfanı da wani fangare ko
salo na cikin wannan littatin ba sai da izinin marubuciyar a
kiyaye. Ga lamnar wayan nan banda maza sai dai mata kawai.
07038416535
A.
Maigidana!
Har abada ban manta da maigida abin alfaharina ba, wato
Halliru Jibril K/Jaba.
Allah ya ja zamani ya Kara kiyaye ka da kiyayewarsa.
Sameera Dalfat
Lawesat Halliru
Ina kara yabawa 'Yayana
Sadeya Shehu Lamixo
Umma'aiman Sabo Yaro Kaduna
Zannura Sabo Yaro Zainab Ahmad Tijjani Usman
Haj. Halima Sani Brigade (Uwani)
Muhammad Lawal Barista
Jinjina ga
Saboda da kokari da jajircewarka wajen ganin fitar wannan
littafi. Na gode, Allah Ya yi maka jagora akan dukkan
lamarinka, na alkhairi.
Allah Ya bar zumunci
Aunty Amina Dan Kaka Mrs Nura
Hajiya Zulai Jibrin Mrs Abdullah
Hajiya MurjaJibril Mrs Muktar
Aunty Suwaiba Jibril Brigade
Hajiya Asma'u Mrs Aminu Goro
Hajiya Maryam Mrs M. Kafi karfin yarо
Aunty Jamila Mrs Jamilu Dankaka
Aunty Sakina Mrs Kabir Dankaka
3
Aunty Sadiya Mrs Nura Dankaka Aunty Lantana Mrs Iawan Dankaka Aunty Amina Mrs Lawa Brigade Aunty Hajiya M. Iya Dansmogal Haj. Jamila Malam Yaya Ruqayya Auwal Mrs. Bashir. Hadiza Halliru Angaje
Haj. Habiba Mrs. A. Abbа
Aunty Maryam Mrs. Umar Dankaka Aunty Kaltume Mrs. Abbakar
Sai 'Yan mutunci
Hajiya Asıma'u Ibrahim
Hajiya Binta Inuwa Jos Hajiya Hafsat Maman BABY
Hajiya Izzatu Mrs Nafi'u Haj. Uinma Ashsha A. ('Yan Matan Jami'a) Aunty Hadiza S. Sharif (So) Aunty Sadiya Lawan
Marsiyya Uba K/Mata
Shamsiyya Idris K/Jaba
Congratulation!
Ina taya 'ya'yana murnar bikinsu
SAMEERA HALLIRU MRS FATUHU
FAREEDA HALLIRU MRS YUSUF
KHADIZA HALLIRU MRS UMAR MATARE
Ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 13