Allah Ya bada zaman lafiya da kwanciyar hankali Allah
ya sa mu ga na 'yan baya wadanda ba su da............ AllahYa ba su
na gari amin. A maimakon dukkannin FAMILY of ALHАI
HALLIRU JIRBRIL GAMA (HAL-JIB)
Shiryawa da bugawa da yadawa
Madaba'ar IYA RUWA
08065566690 - 07028117773
4
MATASHIYA
Ma su karatu in har ba ku manta ba na tsaya a dai dai inda
Husna ta suma umat Ramlat da Ummita sun zata mutuwa ta yi.
1
K
o da suka ga sun yayyafa mata ruwa tare da yin iya bakin
kokarinsu ba ta farfado ba, take suka dada shiga halin
damuwa da kidima suna kuka tare da yin salatin ANNABІ
MUHAMMAD (SAW) suna rokon Allah kamar haka; "Ya
Allah kada ka dau ran wannan yarinya ba tare da ka nuna mata
iyayenta ba in kuma kwananta ya kare to Allah ka yi mata
rahama ka sa bakin wahalar kenan. Da kyar Ummi ta mike ta
nufi falo ta rarumi kan waya domin ta sanar da maigidanta
halin da ake ciki nan da nan shi ma cikin kidima ya ba su izinin
maza a sami taksi a kai ta asibitin Sir Sunusi shi ma ga shi nan
zuwa. Da ya ke asibitin ya na kusa da su ne cikin 'yan mintuna
sai ga su har sun isa bayan direba ya yi parking suna sanarwa
da ma'aikatan aka kawo irin gadon nan na daukar ma'aikatan
gawa aka dora ta suka tura ta zuwa emergency, ummi da
Ramlat su na biye da su suna kuka daya daga cikin likitocin da
suke gewate a kanta ya kalle su ya na tambayarsu "Hajiya
accident ne?"
Maimakon su bada amsa sai Ummi ta dada zabura "Likita
ta mutu ko?"
Cikin tausayi ya jinjina kai tare da daga mata hannu.
"Kwantar da hankalinku, ba ta mutu ba, sai dai ta na cikin
wahala ina so in sani ne domin ba ma karba sai da jami'an tsaro."
Cikin wannan yanayi Baba Sani ya iso ya na tambayar "Ina
Husna ta ke?" Ya na ganinta ya fara fadin "Wa'iyazu billah! Ya
aka yi haka ta faru?" A nan take suka shaida masa halin da
suka gan ta ta shigo gida har lokacin da ta suma take shi ma ya
matsa ya na taba ta likita ya kama hannunta tare da tashi
5
"Kwantar da hankalinka Alhaji da alamar motsin rai e intu
insha Allahu nan da an jima za ta farfado dogon suma ta yi ne.
Bayan sun yi mata taimakon gaggawa kamar wanke ido da
raunikan fuskarta tare da sa bandeji sai aka tura ta zuwa Room
5 don kwantar da ita tare da sa mata ruwa sannan likitan ya
bawa B. Sani takardun magani den a siyo har ya juya zai fita
Ummi ta bi bayansa, ta na sanar da shi cewa kada ya sake Nura
ya gan shi kuma ya ja kunnen ragowar mutanen gidan kada su
shaidawa kowa halin da ake ciki, nan ya jinjina maganar ya na
fadin "Ki ce Nuran bai san halin da ake ciki ba? Lallai dole ne
mu yi taka-tsantsan saboda rigimarsa daga nan ta lissafa masa
abubuwan da zai taho mu su da su daga gida. Ummi ta na
komawa ta sami Ramlat rike da hannun Husna ta zuba mata
ido ta na kuka ta dafa kanta. "IHaba Ramlat, har yanzu kukan ne
edai? Ki yi hakuri tare da ci gaba da yi mata addu'ar Allah Ya
ba ta lafiya ya kuma kufutar da ita daga sharrin da zalincin
wadannan bayin nashi"
Ramlat ta ja ajiyar zuciya tare da kailon mahaifiyarta
"Haba Ummi duba fa ki ga halin da Husna take ciki tun farkon
rayuwarta har zuwa wannan ranar ita mama ba ta tuna ranar da
za ta sadu da ubangijinta ne ko ta manta akwai hisabi tsakanin
da da mahaifi ne? Ballantana shi Allah bai barin hakkin wani a
tsakanin wani balle Husna marainiya wacce ko da iyayenta
-suna da rai in ta gan su ba za ta gane su ba. Shi ya sa nake dada
jin tausayinta."
Shi kuwa YAYA NURA karfe biyar da rabi na yamma ya
dawo daga ofis bayan ya yi wanka ya hade cikin tsadadden
boyal green colour haka takalmi da hula da agogon hannunsa
fararc sannan ya feshe jikinsa da tsadadden turare mai dadin
kamshi yana dukan shi, ganin abin kaunar shi kai tsaye ya
shiga cikin gidan dan dauko mata alkawarin da ya yi zai ba ta
in ya dawo ga shi kuma nan da sati ya ke sa ran za ta zama
ta
amaryarsa bayan sallama da ya yi ta kwadawa Baon wallDP ÁR
ji bare ya amsa kai tsaye ya yi shigewarsa ba su ankara ba sai
ganinsa suka yi durkushe a gaban mahaifiyarsa ya na gaishe
don haka cikin firgita kowace ta daidaita sahunta suka yi shiru
da barin hayaniyar da suka zurfafa a cikinta. Ko kallo ba su
ishe shi ba ya ci gaba da magana "Mama ina dan key din nan,
Abba nake san duba wani abu."
Nan ta bawa Fati Kanwarsa izinin ta dauko masa ya na
karba ya nufi dakin nan da nan Aunty Ma'u yayarta ta zaro ido
"Kar dai a ce ya ji hirar da muke yi dan na ga yau fuskar nan ba
yabo ba fallasa."
Mama ta dan yi murmushi. "Haba dai, wa zai fada masa ko
bai gan ta ba ba zai yı zargin wani abin ba, kin san shi abin
bakin cikin bai 6oyuwa a fuskarsa haka ma na farin ciki."
Bayan ya dauko ALBUM tare da dauko hoton da ya ke
manne ya kura mata ido ita da 'yar uwarta da ke jiki ya
sumbace shi, tare da kiran sunanta. "Husna! Husna!! Ya ji ba ta
amsa ba take ya saki murmushi ya nagodewa Allah da ya ba shi
ita a matsayin uwar 'ya'yansa sannan ya yi fatan Allah ya sa ya
dauko hoton a sa'a ya zama shi ne sanadin gano iyaye da 'yan
uwanta, amin.
Ya zo wucewa Aunty ta kira sunansa, "Ango na amarya, ka
sha kamshi tun da ka dawo daga Saudiyya na ke zuba ido ko
'yar tsarabar ma ban gani ba, balle 'yar uwarka Ladidi ta sa rai."
Take ya hade fuska. "Ni ban yo wa kowa tsaraba ba in
banda kayan lefen anaryata da na siyo....."
"To mara kunya tuin kafin ka yi auren ka fara nunawa 'yan
uwanka mace ta fi su?" In ji Mama. "Macen ma wacce ba a san
iyaycnta ba bare usulinta tsintacciyar mage wata kila ma
mayyace.
Wai! Turkashi! Ai tun kafin ta karasa ya daga hannu ya na
mai daka mata tsawa da karajinsa "Ya isa! Ya isa! na kuma
cewa ya ishe ki haka, ke wace ce da za ki dunga fada min
7
m ia laud ita ma ke kike zuga ta. 'Yarki ce ban so na ce akai kasuwa, ko ana yi dole ne?" Lai saurari me zai biyo baya ba ya yi ficewarsa rai a 6ace. A zaure
ne suka hadu da kaninsa Salim bayan ya gaishe shi ya ke tambayarsa.
"Yaya lafiya na ga ranka a bacc?"
Ya dafa kafadarsa ya na murmushi. "Babu komai my brother, in ka shiga ka turo min Husna."
Jim kadan ya fito ya shaida mi shi, "Ba ta nan, amma bari in duba ta a gidan B. Sani."
Cikin jin dadi ya amsa "Yauwa kanina."
Nan ma aka ce ba ta nan. Ya dan cije yatsa ya na tunanin
ko inma suka je? Daga nan ya yanke shawarar ya shiga don ya tambayi Ummi ina suka tafi. Fitarsa ke da wuya ya hango B. Sani ya fito daga cikin gidan da kaya a hannunsa ya doso shi
nan take ya karbe shi ya na tambayarsa "Wane ne a asibiti na
gan ka da tabarma da filo ga kwanikan abinci?" Kafin ya ba shi amsa nan da nan ya diririce, zuciyarsa sai lugudan tara-tara take yi zuru zuru kamar ya yi wa sarki karya, shi dai ba abin ya yi masa karya ba, domin komai daran dadewa zai gane kuma zai dunga ganinsa a matsayin makaryaci, kunga girma ya zube nan dai Nuraya ci gaba da fadin, "Daman yanzu zan shiga ciki in tambayi Ummi Husna
suna tarc da Ramlat na turo ba sa nan." Nan dai ya daure ya
sanar da shi cewar ita ma Ummin ba ta nan ya sake tambayar "Ko suna tare nc?" Ba dai a san rai ya amsa da "c" ba. Nura cikin fargaba ya sake tambayar "Ko wanene a cikinsu babu lafiya?"
Baba Sani ya fan saki fuskarsa "Lafiya suke, sun je duba 'yar abokina ne da ta ke kwance a can asibiti."
Cikın hanzari ya bude motar ya na fadin "Ai sai mu je ní ma in duba ta."
8
Nan suka fara gardama kan ya yi zamansa, ya san halinsa
bai iya ganin abin tausayiba, yanzu sai ya rikice nan ya rantse
wallahi zan daure baba ya ce sai ka yi alkawari babu abin da
zai faru bayan ya yi ba dai a san ransa ba ya bi shi sai da suka
fara zuwa PHARMACY tukuna suka sayo allurai da
magunguna. Nan ma tun da Nura ya gan su da yawan kudin da
aka kashe ya fara jinjinawa "Lallai wannan mara lafiya da gani
yana jin jiki.'
B. Sani ya kalle shi, "Kaga don haka na ce ka zauna."
Shi dai tun daga nan ya tsuke bakinsa har suka shiga cikin
asibitin suka yi parking wajen da aka tanada don ajiye motoci
nan ya ce da Nura ya tsyawa ya mikaca likitan magani sannan
ya zo suka nufi dakin. Shi dai B. Sani zuciyarsa cike da
zulumin abin da zai faru ya murda mirikin kofar suka shiga
tare da yin sallama su kan su na dakin da uska gan shi tsurutsuru suka yi Nura ya durkusa ya gai da Ummi tare da
tambayar ya me jiki? Kana ya matso gaban gadon ya na kallon
mara lafiyar, tarc da jerowa Ramlat tambayar "Ya mai jikin, na
je gida ina tambayar Husna ashe kuna tare."
Ita kuwa ta na jin haka ta nuna masa ita, "Ga ta nan ai jikin
da sauki..."
SUBHANALLAHI! Me zan gani? Dama ita ce mara
lafiyar ka ke boye min Baba?" Nan ya tafi gabanta ya durkusa
kamar me neman gafara yanzu Husna ke ce kamanninki zuka
canja wa ya yı mi ki haka kjo da ya ji shiru ba ta yi motsi ba sai
ya fara taßa jıkinta, "tashi Husnata ga ni na zo ki fada miyn
anda ya taba min ke." Dakyar B. Sani ya jawo shi. "Yi hakuri
Nura tun farko shi yasa na yi kokarin boye maka har sai ta
sami sauki tukuna, maganar a fadi ma wanda ya yi mata bai
taso ba don abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu ce Allah
shi kiyayc gaba."
Take ya yi zumbur ya mike da nufin fita ya na fadin "Bari
in je yanzu za dawo." Nan take suka fahimci inda za shi, B.
Mama
Sanı ya kamo shi "Ka ga inn buyagın naka ko, in ce. ne, ko 'yar uwana?
da
Ya na faman zulle-zulle, "Wallahi odere Maa 'yarta shi yasa na same su sunz ta asa to wallatı akan Husna ba zan ragawa kowa ba ko da va ga babu halin tafiya inda ya yi niya, sai ya sa kuka anda duk wanda ya ji sas ya tausaya mi shi daga nan sai ya fara hada qonı ga azababben ciwon kansa ya na neman ya tashi nan da nan ya fara birgime "Wayyo kaina!"
Hankalin kowa ya yi mummunan tashi, B. Sani ya zuba da gudu zuwa ofis dion likitan ba a jimaba sai ga shi nan sun shiogo da likita suka dora shi a bisa daya gadon kana ya yi mi shi allurar barci, sannan hankalinse ya dawo wajensu, Ummi yana tambayar daman yana da irin wannan ciwon kan?
"Yana da shi tun ya na karai amman bai fiye tashi ba sai dai in har ransa ya mummunan басі."
Likitan yace, "To Alhaji tun da kun fahumci hakan sai ku
dinga yin taking careda fadin abin da vai tada hankalinsa."
Nan dai B. Sani ya ke fada mi shi irin taka-tsantsan da suke yi duk don kar ya sani, bayan kamar mintt aslurin da biyar ne, ni Itusna na farka a firgice cikin kidima, ina fadin "Na tuba
mama, ba ni na dawo ba, kawo ni aka yi waiyo Allah, ka cece ni ban da kowa sai kai..."
Yayin da su Ummi suka nufo inda nake suka rike ni tare da kiran sunana. "Husna Ummi ce ga Ramlat. Ki kwantar da hankalinki, ki bude idonki sosai ga ma yayanki ya zo."
Nan na dade rintse ido don ji nake sam ba na son ganinsa a
takaice sai da na baiwa kowa tausayi ana cikin haka sai shi ma
ya farka ya na fadin ina Husna?" 'Yan wajen kowa kallonsa ya ke tare da mamakin shin wai wane irin so ya ke yi wa Husna ne?
A takaice dai a ranar akai-aka yi ya tafi gida ya ki a zaune
ya kwana Ummi ta tafi gida ta bar shi tare da Ramlat daga na yi
10
cin wani motsi zai dinga tambayata me ke damuna ko ina son
abu ne alhalin ga take away kala-kala mun kasa ci shi kuwa
Likitan duk lokacin da ya ga yaya sai ya tsokane shi me ciwon
so' ka kwanantar da hankalinka insha Allahu sai kun haifi 'yan
biyu sau hudu Kullum sai an wanke min ido da ruwan magani
sannan akwai wanda ake diga min duk da na fara sami sauki a
jikina amman ni kadai na san irin azabar da radadin da nake ji
a jikina da zuciyata raina ya kasa samun sukuni saboda ban
manta abin da ka yi min musamman in na bude idona ga Yaya
Nura sai in ji duk na tsane shi saboda a kansa ne na shiga
warnan halin wani lokacin kuma ya kan bantausayi in na ga
irin damuwar da ya shiga a kaina, ya kasa zaune ya kasa tsayc,
saboda ni, har sai da ya yi fashin zuwa wajen aiki a yanzu ma
ba ya tafiya sai sha dayan dare d yamma kuwa ya na tasowa
wajena zai z0, ammamn ba ya birge ni musamman in na tuna
ranar da zu mamansa suka yi min azaba da barkono take
dariyarsu da maganganun da mama ta ke fada min a lokacin
suka fado min kamar haka: "Daga yau karyar bin maza ta kare,
na yi miki gargadin kar ki kara kula NURA kin ki har
sammako kike yi ki je wurinsa, to daga yau taki ta karc sai dai
ki je ki auri dan iska irin ki ki kuma tattara kayanki ki bar
gidan nan. "Na kwalla kara sannan na saki sautin kukana mai
ban tausayi su Ramlat suka yi ta ban hakuri shi kuwa Yaya in
ya na nan shi ma kukan ya ke yi.
A can cikin gidan kuwa tun da wannan sa'insar ta faru
tsakanin Aunty da Nura bai kara shiga giodan ba, abincin ma
bai ci in dai aka kai haka za a dauko shi in ya fita tun safe sai
lokacin kwanciya zai dawo dakin barcinsa, ganinsa ya yi wa
kowa wuya abin duniya ya yi wa Mama yawa nan ta tura
Magaji mai wanki ya kirawo mata yayarta don su tattauna
saboda tana zargin ko Nura ya san abin da ya faru. Ko shi ya sa ba ya shigowa, don ba karamin aikinsa ba ne ya bi ta tun da ta
11
shanye shi. bayan Aunty ta zo ne take yi mata wannan bayanin, Aunty ta dan yi ajiyar zuciya, "Hauka ya ke yi zai bi ta? Yanzu dai abin da za mu yi mu turta a kirawo mana kawarta kila ta san wani abın bayan dan aiken ya dawo an ce ba ta nan sai suka yanke shawarar su shiga da kansu sun fi yarda sun shiga tare da sallama.
namu?"
"Lale ku karasa daga ciki, yau Aunty Ma'u ce a gidan
Ta wani yatsine fuska ta na cika ta na batsewa, ta amsa. "Yau ma dalili ne ya kawo mu, mun zo cigiyar 'yar gidan ne da kuka daurewa gindi ta ke yi wa mutane rashin kunya daga ta yi laifi an yi mata fada ta gudu yawon iskancinta yau kwana uku.
Ummi ta dakatar da ita, "Kin ga ban san surutan banza ko Ramlat ban yarda ta ci mutuncin wani ba ballantana Husna 'yar
amana, duk wanda ya ci amanarta sai Allah ya ci tasa ban san inda takeba, sai ku je can ku nemo ta."
"Ba zamu nemo ta ba, ta yi gaban gobe." "Oho, can ta matse mu ku ni dai na san zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi." A Rarshe dai baran-baran suka rabu.
Nayan ta gama hada abincin ta kawo mana da yamma ne
na ji ita da 'B. Sani sun sa yaya a gaba suna fada masa suka cе, "Tun da babu wanda ya san Husna tana nan za mu roki likitan
ya bar ta a nan har sai lokacin da A. Nasir ya dawo daga kasa
maı tsarki ka gasai mu san matakin da za mu dauka mu dai abin da muke so da kai ka ci gaba da yin hakuri."
Kashc gari da ya ke weekend ne muna zaune ni da yaya ya
ga na yi tagumi ina ta zancen zuci ya taso daga inda yake ya
durkusa a gabana "Uwagidana abin alfaharina me kike tunani
bayan ga ni a gabanki?"
Nan na saki tsaki tare da dauke kai, nan dai ya yi ta zolaya
ta da maganganun ban dariya kamar dai yadda ya saba yi min
12
in ya gan ni cikin irin wannan halin har sai da na yi dariya,
Ramlat ta & fitowa daga toilet ta fara tafa hannu, "сус, Hиna
sauki ya samu."
Na cc, Sauran kwanciyar hankali."
Yaya ya langwabar da kai ya na ban hakuri da baki "Husna
tun da ga ni kin sami kwanciyar hankali na yi alkawarin zan
zama madadin iyayc sannan sai kin yi alfaharin samin miji
nagari."
Ramlat ta kare masa kallo, "Ah, yaya dube ka duk ka rame
kamar kai ne mara lafiyar."
"Ah." Ya bude baki. "Ba ki san ciwon ne a jikinla b.
amman zafin da radadin suna jiki da zuciyata."
Ta yi murmushi, "Allah dai ya nuna mana ranar da za ku
zama mata da miji."
Ya mike tsaye yana mai daga hannu. "Amin summa amin."
Muna cikin hira da dariya ne nurse din da ta saba yi min
allura ta shigo ta na kwarkwasa ta na magana ta na fari, tuni na
lura da ita musamman sai ta ga yaya take yi ta kalle ni, "Yau
patient na ga alamun fara'a kike ji."
Yaya farat ya amshc, "Ai dole ne ta yi tana kusa da
masoyinta."
Ta kalle shi ta na murmushi, "To yau allura biyu zan yi
mata, in kuma kana son daya ne to."
Ya dan yi murmushi, "Gabaki daya ma nakc so, don ni ma
patient din ne." Ya kalle ni tare da yi min murmushi, "Ko ba
haka ba gimbiyar?"
Take na watsa masa harara saboda wani irin kishi da na ji
ya turnike ni, tun shigowarta ni dai a ranarban bari ta yi min
allurar ba, duk da ta kasance ta karshe, bayan sallar magriba ne
Yaya ya miko min ambulan, "Ga sakonki." Ya dauko udi, "Ko
za ku bukaci wani abin saboda yau da wuri zan tafi kin san yau
madaurin aurenmu zai dawo ko ya kika cc?"
Na kauda kai, "Sai ya dawo."
13
Ya zauna, "Ban ga ta fita ba, na fasa zuwa an ort fin tun da Gimbiya ta ki yi min magana, har gabana ya durkusa, "Wallahi ba zan tafi ba sai kin yi murmuishi." Ya Kura min ido har sai da mu ka kwashe da dariya yana dagon hannu ni ma
hannu,
haka domin
ni da
shi
da
biyu
sai
nake yi na san tuin da na sami hotona a
har abada, don
wani jikon, in ba wata Raddara ba ni da shi
aure babu fashi
ba zan bari Abba ya dawo ya same ni ba, na san
mijina da
gara in je in nemi iyayera tun yanzu uwar
aure shi ba
danginsa suna gana min irin wannan azabar balle na ni ba yayana ma sai sun fuskanci matsala. Da irin wadannan shawarwarin tashi na yi sallahr na kwana safiya na yi na
tashi
asuba tare da yin wanka na, tsaf sannan na Ramlat ta rike baki ta na mamaki, "Har kın yi me?"
70."
"Har na yi wanka, kin san yau babu aiki da wuri yaya zai
abin
Ramlat ta shiga wanka saida na bari ta fara yi na tattara
na samu
da na san zanyi amdani da shi na yi ficewa ta ina zuwa get 'yan acaba sun jeru suna jiran mai tafiya, na matsa kusa
Maiduguri,
da daya, "Don Allah Malam tashar da ake shiga motar za ka kaini."
Ya tayar da mahsin fin. "Hajiya hau mu je." Cikin 'yan dakiku sai ga mu a cikin tashar bnayan ya sauke ni na fara tambayar 'yan kamasho inda zan sami motar cikin sa'a kuwa wajen mutu biyu motar ta cika ina shiga sauran mutun daya dan kamasho ya ci gaba da shela "Maiduguri
mutun daya" Ba tarc da 6ata lokaci ba sai ga mutum biyu mata da miji sun zo, dan kamasho ya sanar da su "Malam sai dai ka shiga ta baya wajen mutum daya ne sai na ga ya kalli matar, da tun da suka tsaya faman kuka take yi, "Uwale ki yi hakuri mu shiga ta baya." Ta dada fashewa da kuka. "Haba malam mu yi
maleji idan muka shiga waccan yaushe za mu je?"
"Gani na yi da mu je da wuri da kar mu je da wuri ba za
mu dawo mata da ran nan ba. Sannu ba ta hana zuwa."
14
Ai kuwa ina jin haka, sai tausayınsu ya Kara kama ni, nan
da nan na fito ina cewa "Baba ku slaga."
Ya ce "Yarinya kin fasa tafiya ne?"
Na pirgida kai. "a'a, na tamaka ne saboda na ji shigen
matsalarmu daya ne."
Uwale ta ce "Ke ma mutuwar ce?"
Na ji ajiyar zuciya, "Gara ku ma ni na fata ne, tun ina
karama yanzu zan tafi neman su ne ban san ko suna raye tun da
suka ji haka Malam ya ce da ni "Uwale mu zauna kan kujera
shi ko a maneji. Haka kuwa aka yi, nan da nan mota ta dau titin
Madugun, muna tafe muna hira da Malam muna kuma bawa
Uwale hakuri a haka muka saba da su.
Al'amarin Ramlat kuwa yaym da ta fito daga wanka,
maimakon ta gan m sai ta ga tyaventa zaune su ma abin ya
basu mamaki, kasancewar ba n Husna su ka gani ba ba na suka
fara tambayar ina patient din ta shiga? Ita ma tambaya ta ke,
"Au da kuka shigo ba ku same ta ba? Amma bari mu duba waje
ko ta dan zagaya waje."
Bayan B Sani ya yı yawo bat gan ni ba, ya dawo ya na
fadin na je har wajen nas da dakin likita sun ce yau ba sa yin
sallama, bayan dan wani lokaci nas din suka shiga suna
tambayar sun gan nı? Suka ce a'a sai dai aje gida a gani nam
ma B. Sani ya dawo ya ce ba ta nan daga' nan aka yi wa babban
likita waya aka shaida masa halin da ake ciki ba tare da bata
lokaci ba sai ga shi ya zo nan aka fara yi wa Ramlat tambayoyi
kamar haka, "Ke ce mai kwana da ina, ya aka yi ta fita?"
Ta amsa "Ni dai ta yi wanka sannan ta tashe ni ni ma in yi
wankan."
"Kafin ai hakan ba ta shaida miki za ta je unguwa ba?" "Eye." Ta daga kai.
Tambayoyi dai barkatar har sai da suka kusa kure ta, nan
ya koma kan B. Sani "Alhaji kana ganin matsalar da take ciki ba za ta sa ta gudu ba?"
15
Ya jinjina "Kwarai ni ma kai na abin da nake tunawa kenan."
Likita ya ce, "Saboda hhakan ba za mu bar ku ku tafi ba sai
mu je wajen hukuma tukun."
Nan ma tun da suka je ake yi mu su tambayoyi daga karshe dai suka yi wa D.P.O bayani ya tausayatarc da fadin "Babu mamaki ta gudu amman insha Allahu za mu yi tsattsauran bincike a wajen nemanta daga nan suka yi sallama, suka koma gidan giwa a sanyaye, al'amarin yaya kuwa kamar yadda ya saba yin hidima, sai ga shi niki-niki da kaya a hannunsa, ya nufi dakin da mu ke, shigar nan da zai yi ya ga wayam, sunan wani mawaki, ya tasho yana mamakin ko an sallame su ne? Nan ya ci karo da wannan nurse din ta nufo shi ta na murmushi "Ranka shi dade tun da ka yi parking na hango ka."
"Eh wallahi, an yi sallama ne na hsiga dakin ban gansu ba."
Ta rike baki da alamun ba daga gida kakc ba ko?" "Kwarai tun safe, ina can neman kayan Abbana da yau da jiya shi ya sa."
Daga nan ta fara bashi labarin neman da aka yi nawa aka
rasa, tun daga farko har karshe, yaya dai saboda kidima bai san
lokacin da ya yarda ledojin hannunsa ba ya n fadin "Yanzu
haka Husna za ta yi min? Sai da lokacin aurenmu ya gabato za
ta gudu ta bar ni? Amma in ta yi haka ta cuci rayuwata, haka
dai ya fara tafiya ya na surutai kamar zararre ita kuwa nurse ta
na biye da shi har sai da ta sami damar yi mishi tambayar
"Kana nufin Husna ba matarka ba ce nan gaba ne za ku yi
aure?"
Ya juyo ya ba ta amsa.
Tun da ta ga ta sami shiga sai ta fara fadin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 13