Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tace za ta yi idan ta canza shawarar yi Rose ce take hawa a makwafinta dukda ba a samun abinda ake so kamar Bibin amma tana iya ƙoƙarinta wajen ƙayata abin. Idan ta mutu bata san yadda zata yi ba. Ganin fitowar likita yasa ta sha gabansa da sauri fuskarta na baiyana matsanancin tashin hankali. "Likita yaya? Ya jikin nata?" Tayi maganar da rawar murya, hawaye wasu na korar wasu a fuskarta. Ya goge zufan goshinsa da wani farin hanki da yake riƙe a hannunsa, ya kalleta da ɗan murmushi a fuskarsa. "Is ok! komai ya daidaita. Za ku iya shiga ku ganta, amma banda hayaniya pls" Daga haka bai ƙara komai ba ya wuce ya barta da sassarfa, sauran Noses ɗin suka rufa masa baya a hanzarce. Tsananin damuwa da ruɗanin da take ciki yasa ta manta tare da Bibi suke tsaye, bata ko kalli inda take tsaye kamar mutum mutumi ba ta shige ɗakin da Rose take kwance da sauri dan ganin halin da take ciki, zuciyarta cike da addu'a da fatan samun sauƙi a gare ta. Tunani da saƙe-saƙe kala daban daban ne a ranta har bata san Madam ta shiga ciki ba, wani irin shauƙi take ji a zuciya da gangar jikinta, irin shauƙin da tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin irinsa ba. Tana tuna yadda ya tallabota jikinsa sai taji ƙirjinta yana luguden daka, yanayin ya kasa ɓacewa daga ranta. Babu abinda take ji a ranta tana so a yanzu da take tsaye irin ta sake jin tattausan muryarsa, ta sake tozali da kyakkyawar fuskarsa, ta sake haɗa jiki da tattausan jikinsa mai tsananin ƙamshin daɗi. Ita kawai komai na shi yayi mata, a kallon farko ta ji ya bala'in burgeta. Sai wani yuyu yake mata a duk wani lungu da saƙo na zuciyarta. Runtse ido tayi ta shaƙi daddaɗan ƙamshin jikinsa da ya gauraye da tattausan ƙamshin turaren jikinta. "Waye shi?" Tayi maganar a fili tana huhhurga idanunta lungu da saƙo na harabar gurin kamar za ta sake ganinshi, ko alamunshi bata gani ba, sai noses da masu jinya da suke wuceta lokaci bayan lokaci. Ta daɗe tsaye a gurin tana tunani, daƙyar taja sanyayyun ƙafafunta ta shiga cikin ɗakin dan ganin halin da Rose take ciki, ita bata san ma lokacin da likitan ya fita ba. Saboda yanayin da take ji a jikinta bata jira Madam ba ta karɓi makullin motar da suka taho da ita ta koma gida, sai rawar ɗari take yi kamar wacce zazzaɓi yake neman kamawa. Duk tunaninta ya tattara ne a inda zata sake gano wannan mutumi. ****** ****** Shi kam bai tantance wani yanayi yake ji game da ita ba har ya sai magungunan da aka rubuta masa suka bar cikin asibin. Cikin hikima ta Ubangiji tun kafin yasha magungunan ya nemi ciwon kan ya rasa, ko da ya faɗawa Yusuf kan ya daina ciwo godiya sukai ta yi ga Ubangiji mai yadda yaso a lokacin da ya so. "Amma dai dukda haka kar ka fasa shan maganin." "Eh daman dole zan sha. Ina ga mu koma Otal ɗinnan kawai na ga gaf ake da kiran sallar magrib, idan mun idar sai in kira Alhaji Barazana inji ko ya dawo." Ya ƙarasa maganar yana sake gyara kwanciyarsa a jikin kujeran mai zaman banza, shi kuma Yusuf yana tuƙa motar. Kafin ya amsa shi kiran waya ya shigo cikin wayarsa, da yake wayar tana aljihun gaban rigarsa ne sai ya rage gudun motar ya zaro wayar. "Kaga Alhajin ne ma yake kira na, kila ya nemi lambarka bata shiga ba." Ya ƙarasa maganar tare da danna madannin amsa kira ganin yana gaf da tsinkewa, buɗe sipikar wayar yayi dan duk su biyun suji abinda zai faɗa daga can ɓangaren. "Ka faɗawa Alhaji Maheer don Allah yayi haƙuri, duk yadda naso in shigo yau bazan samu shigowa ba. Amma in Allah ya yarda gobe zan shigo da yamma, wani muhimmin al'amari ne ya taso min a nan ɗin wallahi. Na kira wayarsa in bashi haƙuri kuma wata yarinya ce ta ɗauka." Ƙit kiran ya katse daga can ɓangaren ba tare da an jira amsawar shi ba. "Kash ! Amma na so ƙwarai gobe inyi sammakon komawa gida wallahi, amma ba damuwa, Allah ya kaimu goben. Ubangiji yasa hakan shi yafi alkhairi." Ya faɗa yana lumshe idanunsa. "Ameen Yallaɓai..." "Ji nayi kamar ya ce ya kira wayata wata yarinya ta ɗauka ko?" Ya tambayi Yusuf fuskarsa cike da mamaki sannan ya zaro wayarsa a aljihu. Kirjinshi ne ya buga dam! a kallon farko ya gane wannan sam ba wayarsa bace, irin tasa ce dai sak amma ita wannan an saka mata riga mai masifar kyau da ɗaukar hankali irin na mata. Jujjuya wayar ya ci gaba da yi yana tunanin aɗan fitar nan da suka yi zuwa asibiti a ina ne har yayi canjin waya da wata? "Wannan ai ba wayata ba ce." Ya faɗa hankalinsa akan Yusuf kamar mai neman ƙarin bayani. "Tooo... subhanallahi. Ta ya akayi hakan ta faru Yallaɓai? Ashe da gaske an kira lambar taka wata ta ɗauka. To ina ga wacce kuka yi musaya da ita ne." Yayi maganar tare da gangarawa da motar gefen titi, kashewa yayi kafin su yanke shawarar abinyi tsakanin juyawa inda suka fito dan cigiyar mai wayar ko kuma ci gaba da tafiya zuwa inda suka nufa? Shiru yayi zuciyarsa cike da tunanin inda aka haihu a ragaya. Da ya rasa tunawa sai kawai ya danna madannin kunna wayar, sai a lokacin ya fahimci wayar ma a kashe take. Bayan tsawon minti ɗaya da kunna wayar ɗanɗasheshen hotonta ne ya baiyana a fuskar wayar tana dariya. Tayi kyau sosai kamar wata zara a cikin taurari, ga tsananin ɗaukuwa da hoton yayi kamar a kirata ta amsa, zallar ƙuruciyarta baiyane a fuskarta ta cikin hoton. "Zillaziyya" Yusuf yayi maganar a zuci ba tare da sanin a fili yayi ba, da ya ƙara kallonta sai kuma ya sauke wani nannauyar ajiyar zuciya yana yabawa Ubangiji sarkin ƙawata halitta. "Sunanta kenan?" Ya tambaye shi yana wani basarwa, idanunshi na kan hoton shi ma yana sake ƙare mata kallo. "Wa ɗin?" "Ita na jikin hoton mana, na ji kace Zilliya-zilliya" "A'a ni bansan sunanta ba, zallar kyau dai na gani da ƙuruciya, shi yasa na kira ta da hakan." Yusuf ya amsa da murmushi a fuskarsa. Ya taɓe baki, har lokacin idonsa na kan hoton, da hasken wayar ya ɗauke sai ya danna ya ci gaba da ƙare mata kallo. "Muje kawai, ka ji can nesa ana kiran sallah. Na gane yarinyar, ɗazu a ofis ɗin likitan nan muka yi karo da ita. Na san ita ma za ta kira dan ta karɓi wayarta, gobe in Allah ya kaimu sai ka kai mata ka amso min tawa wayar." Da wannan maganar yaja motar suka ci gaba da tafiya zuwa masaukinsu. A can ɓangarenta lokacin da ta fahimci sunyi canjen waya ba tare da saninsu ba wani sakaran murmushi ne ya suɓuce mata. "Waww!" Ta faɗa a fili kamar taɓaɓɓiya kuma sai ta fara ƙyalƙyala dariya tana madungure a kan gadon dan tsabar murna. Da ta gaji wayar ta tasa a gaba ta zurawa ido, hannayenta duk biyun dafe da ƙuncinta, fuskarta cike da murmushi. 'Ashe dai zan sake ganinsa? Oh my God wannan gayen ya haɗu wallahi, ohh Allah ni ina son shi ma... wallahi ina son shi. Kai !? wai da gaske sonshi nake yi? tabbas wannan so ne duk da ban taɓa yin so ba ina gani a fina-finai.' Ita da zuciyarta take ta zancen zuci tana dariya. Daga ƙarshe ma falo ta koma ta ƙure sauti sosai cikin waƙar Me and you again ta fara taka rawa tana lanƙwasa kamar zata karye. Sauran ƴan mata da ma'aikatan gidan da sun leƙo falon dan yin masifan sautin da aka ƙure bayan jimamin da suke ciki na halin da marassa lafiyarsu suke ciki suna haɗa ido da ita sum-sum suke juyawa zuwa ɗakunansu. Gaba ma da gabanta ai, Madam ma kanta lallaɓa Bibi take yi balle su karan kaɗa miya, yanzunnan in ta sa ma mutum ido sai duniyar warwala da jin daɗinsa ta dagule. Sai da ta gama sharafi da nishaɗinta ta gaji sannan ta tattara ta koma ɗakin Madam a sama, tayi ɗaiɗai a kan gadon ta zubawa wayar idanu, zuciyarta cike da tunaninsa. Ƙarfe goma sha ɗaya dai-dai na dare kira ya shigo cikin wayar, da sauri ta kaiwa wayar raruma kamar shi ne a gabanta ba wayar ba. Bata tsaya duba lambar ba ta danna madannin amsa kiran ta kara a kunnenta, shiru tayi tana sauke numfashi a hankali bata yi magana ba, a can ɓangaren shi ma sai yayi shiru yana saurarenta. Ɗan gyaran murya yayi ita kuma a hankali ta buɗe baki ta ce "Na'am" "Me kika ce?" Ya tambayeta da mamaki. "Oh sai naji kamar ka kira sunana." Ta faɗa a hankali. Sake gyara kwanciyarsa yayi a kan gadon, ya lumshe idanunsa. Wani iri yake ta ji a jikinsa kamar ana mishi tafiyar tsutsa. "Na kira sunanki na ce me?" Yayi maganar yana sake ƙasa da muryarsa kamar wanda ya fara bacci. "Ji nayi kamar ka ce Bi....bi" Tayi maganar da wani irin salo mai kama da na shagwaɓaɓɓun yara. "Uhmmm!" Yaja ajiyar zuciya ya sauke. Bai jira cewarta ba ya ci gaba "Kawai ɗazu kuma sai kika ɗauken wayata ko?" "Laaaah... ni ce ma na ɗauke maka taka wayar? kaine fa ka fara ɗaukar tawa baka sani ba" Ta faɗa a sanyaye, sai yaji kamar ma zatayi kuka. Haka kawai yaji yana son janta da hira, ya kuma rasa dalilin da yasa hakan. "To yanzu dai ya za a yi? kinga dai ni baƙo ne a garin. Ya za ayi ki bani wayata?" "Kai kana ina ne? Sai in kawo maka ko yanzu in kana so" Agogon bangon da yake maƙale a sama ya kalla, sha ɗaya da minti goma. "Ke yanzu zaki iya fitowa a darennan?" "Eh mana. Ai dare bai wani yi ba" Ta amsa kai tsaye, a muryarta ya gane zallar gaskiya ce a maganarta. "Kuma har sai a barki ki fito a gida?" Yayi mata tambayar muryarsa na baiyana zallar mamaki. "Eh mana. Kana ina ne?" "Ina Garuje hotel, ɗaki na 102" Yana gama faɗa mata ƙit ya katse wayar yana dariyar shirmenta a ransa, bai taɓa ɗaukar da gaske take za ta iya fitowa a wannan daren ta kawo masa wayar ba, sai da yaji ana kiran wayar tarhon da yake cikin ɗakin. "Oga kana da baƙuwa fa, sunanta Bibi. Ka san da zuwanta?" "Eh." Ya amsa a mamakance. Ko kafin ya ƙara wata magana har an ajiye wayar daga can ɓangaren. Rigarsa ya saka yana ƙoƙarin sauka ƙasa ya tare ta kawai yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, yana buɗewa kyakkyawan murmushinta ne ya fara mishi maraba. "Hi" Ta faɗa da zazzaƙar muryarta haɗe da karkaɗa mishi yatsu biyu. Yana ta tattare hanya dan kar ta shiga ɗakin ganin irin shigar da yake jikinta na kayan barci, ita kuma sai cusa kanta take yi dole ya kauce ya bata guri ta shiga ciki. "Daman da gaske kike yi?" "ƙarewar gaskiya ga tabbaci ka gani" Jinjina kai kawai yayi alamun hakane. Kan gadon ya ƙarasa ya ɗauko wayarta ya miƙa mata. "Ga wayarki, bani tawa kiyi hanzarin tafiya gida. Ke ko tsoro ma bakya ji? ki fito a tsakar daren nan ba tare da rakiyar wani ba?" Sai kuma yaja tsaki, ya ɗaure fuska tamau alamun lamarin ya ɓata mishi rai. Ya galla mata harara ya ci gaba da masifa. "Ji wani banzan shiga da kika yi kamar wata shashasha. Bani ki ɓace min daga nan" Ya karasa maganar haɗe da daka mata tsawa. Jikinta na rawa ta miƙa masa wayarsa ta karɓi nata, idanunta ciccike da hawaye ta fice daga ɗakin. Ko kafin ta isa gida sha biyu da minti uku na dare, ko gama daidaita fakin ɗin motar bata yi ba ta shige cikin falon hankalinta a tashe, har lokacin tunaninsa da kyakkyawar surarsa na maƙale a zuciyarta. A wannan daren duk iya ƙwarewar sarkin ɓarayi bacci baiyi nasarar sace ta ba. Washe gari da sassafe bata san yadda aka yi ba kawai zuciyarta ta dinga tunzurata haka ta sake ɗaukar makullin ɗaya daga cikin motocin Madam ta koma gurinsa, a lokacin ko tashi baiyi ba. "Me ya kawo ki?" Ya tambaye ta a tsorace, yana tsaye ya babbake ƙofar ya hana ta shiga. "Just kawai... na zo ganinka ne" Ta amsa tana narai-narai da idanu ciccike da hawaye. "Jiya ka hana ni bacci..." Ko kafin ta ƙarasa magana Ruf ya maida ƙofar ya kulle ya saka key ta ciki, haka ta gaji da kwankwasa kofar taja sanyayyun ƙafafunta ta koma gida. Bata gaji ba da rana ta ɗanɗasa wanka tayi kwalliya cikin wani figigin sket da guntuwar riga ta sake komawa gurinsa. ɗakin a rufe yake, duk yadda take ta ƙwanƙwasawa bata ji alamun yana nan ba, dan haka ta koma reception zaman jiransa. ****** ******* A cikin kwanaki biyun da yayi a garin ta zame masa wata maƙale masa komai lilo, kusan duk inda yasa ƙafa tana biye da shi. Tun yana ganinta da marmari har ya fara mata kallon tsoro. Da daddare da ta je ɗakinsa bagatatan zuru yayi yana kallonta kawai cikin rashin abin cewa, a zuciyarsa sai jan ta'aweezi yake yi yana neman tsari da wannan hatsabibiyar yarinyar da ta addabi rayuwarsa cikin kwanaki biyu kacal. "Maheer...!" Ta sake furta sunanshi cikin wani irin salo mai kiɗimarwa. Ganin ya ƙi kallonta yasa ta sake cusa mishi jikinta kamar za ta faɗa masa duk da ta san baya so tana kusantarsa, kusan rabin ƙirjinta suka sake baiyana a fili. Hannu ta miƙa da nufin ta dago fuskarsa dan ya kalle ta da sauri ya sake ja da baya. Ya sake galla mata wata muguwar harara a karo na barkatai mai baiyana tsananin tsanar da yake mata. Ita kuwa ko a jikinta, tayi wata dariya mai ban sha'awa. Daman burinta ya kalleta, kuma ya kalle tan, dan haka burinta ya cika. Ta sauke ajiyar zuciya, ta karkaɗa idanunta tayi fari da ido, ta nuna shi da yatsarta manuniya tana taune gefen bakinta na dama, ta kashe idonta na hagu. "Gangaran ! Ina son ka! Ka daina ja min aji fa, bai dace da kai ba. Sam bai dace da kai ba. Ka huta, anjima da daddare zan dawo in taya ka hira. Ya kamata kaima ka ji kana so na fa, cikin kwanaki biyun nan duk ka hana zuciyata sukuni..." "Bana sonki, kuma kar ki kuskura ki dawo anjima" Ya katse ta cikin masifa. Bai jira ta amsa ba ya ci gaba. "Wai ke wace irin maiya ce? Anya kuwa akwai zuciya a kirjinki?" "Kirjina dai Gangaran? Barin zo ka duba. Amma dai ina da tabbacin tun daga ranar da idanuna sukai tozali da kai na daina jin bugawar zuciyata a kirjina." Tana gama faɗin haka ta fara kici-kicin cire 'yar yaloluwar rigar da ke sanye a jikinta. "Nooo..." Ya faɗa cikin tsawa tare da runtse idanunsa duk biyu. Da hannu ya nuna mata hanyar ficewa daga d'akin. A maimakon ta fita sai ta koma cikin ɗakin sosai ta zauna a kan kwallin kujeran da yake ajiye a ɗakin, ta zauna ɗai-ɗai ta ɗora ƙafa daya kan daya tana ƙare mishi kallo, zuciyarta na sake tumbatsa da tsananin so da kaunarshi. "Au! Baki tafi ba?" Ya tambaye ta da zallar mamaki a fuskarsa bayan ya buɗe idanu, shi kam ya haɗu da alaƙaƙai. "Me kike jira?" "Yau a nan zan kwana" Ta amsa hankalinta a kwance, tana jifansa da tattausan murmushi. Kiran da ya shigo cikin wayarsa ya hana shi bata kyawawan marukan da zai sa ta fice masa daga ɗaki. Surayya ce, tun kafin ya amsa kiran ya fara sakin tattausan murmushi kamar tana gabansa, tsawon kwanaki biyun bata taɓa gajiya da bibiyarshi ta waya tana bashi haƙuri ba, ya yafe mata. A taƙaice ma dai sun shirya, daman tsakanin mata da miji sai Allah. Ire-iren zaƙaƙan kalaman da taji yana furtawa wacce suke waya ne yasa ranta yayi mummunar ɓaci, abinda ya ƙara tunzura ta shi ne ganin yadda ya ma manta da ita a cikin ɗakin. Ta mik'e tsaye ta fuskanci jikin bango, a hankali kyawawan dara-daran idanunta suke canzawa daga farare tas zuwa jajaye, ƙwayar baƙin cikin idon kuma ya koma launin ruwan bula. Taja rigar jikinta sama-sama sosai cikinta ya baiyana a fili, kawai sai ta durk'ushe a ƙasa ta fara motsawa tana kanannaɗewa kamar mai aljannu. Da wani irin tafiya kamar tsohuwa mai k'usumbi ta nufi hanyar fita daga d'akin. Jini yana d'id'd'iga daga cikin idanunta a maimakon hawaye. Daga can 6angaren Suraiya ta yanka ihu ta zube k'asa sumammiya, wani irin ruwa bakikirin mai yauki yana fita daga bakinta. ****** ****** BILHAƘƘI Suna tsaye su biyu a bakin wata tsohuwar rijiya mai matuƙar zurfi da mugun faɗin baki, da ganin rijiyar irin tsoffin rijiyoyin nan ne masu daɗaɗɗen tarihi. Gugan da yake ajiye a gefe duk yayi ƙura alamun an matuƙar daɗewa ba'a ɗebi ruwa da gugan ba, harabar gurin ma a bushe yake ƙamas duk rairayi. Matsanancin ƙishin ruwa ke damun duk su biyun, amma suna ta muhawara akan su janyo ruwan ko kar su janyo? Shi Maheer ya dage akan kar su janyo dan kila ruwan bazai rasa datti da ƙwayoyin cuta ba tunda alamu sun nuna an daɗe ba'a ɗibi ruwan rijiyar ba. Shi kuma Malam ya dage akan su janyo ruwan, babu wani ciwo da zai kama su sai abinda Allah ya ƙaddara zai faru da su. Daga ƙarshe dai Malam ne ya haƙura yabi ra'ayin Maheer da yace su tafi kawai sa ɗibi ruwan a rijiyan da yake can gaba wacce bata kai wannan zurfi, haɗari da faɗin baki ba. "Maheeeeer...!" Suka ji an ƙwalla kiran sunan da murya mai matuƙar amo da hargagi daga can cikin rijiyar. A tsorace suka dawo da baya suka leƙa kawunansu cikin rijiyar, da farko basu ga komai ba sai tsananin duhu saboda tsananin nisan ruwan, minti ɗaya tsakani sai wani matsanancin haske ya baiyana, da sauri suka kare idanunsu dan kar hasken yayi musu illah. "...Ga hannuna... ku taimaka min... za su hallaka ni..." Aka sake faɗa da rawar murya daga can cikin rijiyan. A tare suka sake leƙawa a karo na biyu bayan sun buɗe fuskokinsu, yanzu kam babu hasken nan mai yunƙurin cutar da idanu. Wani abin mamaki da ban tsoro kuma sai ruwan rijiyar ya ɗago sama sosai suna ganin cikin ruwan garai-garai kamar a sa ƙoƙo a ɗiba a sha. Minti ɗaya tsakani ruwan ya rikiɗe ya zama jini ja jajur, zara-zaran yatsu suka fara bayyana a saman jinin, daga haka hannun ya ɗago sama sosai har zuwa kafaɗa "Ku taimaka min..." Ta sake faɗa a karo na biyu tana miƙa musu hannun, kanta da gangan jikinta suka taso sama gaba-ɗaya daga cikin jinin, wasu hannuwa ne zasu kai goma daga can cikin rijiyar suka riƙe ƙafafunta tana ƙoƙarin ƙwacewa suna yunƙurin janyeta su dulmiyar da ita can ƙasa cikin jinin. "Ku taimaka min, so suke su hallaka ni wai dan zan bar cikinsu." Ta faɗa cikin raurawar murya tana ci gaba da miƙa musu hannunta ɗaya, kallonsu take yi da idanunta fari ƙal babu ko ɗigon baƙi a ciki, hawayen jini na zuba daga cikinsu, gashin kanta duk yawanshi a tsattsaye yake kamar kibiyoyi, fuskanta yayi fari fat kamar ba daga cikin jini ta fito ba. Cike da jarumta da rashin tsoro Malam da Maheer suka miƙa hannuwansu da nufin su janyota waje, kafin su ankara wani guguwa mai matuƙar ƙarfi da tururin zafi ya fito daga can cikin rijiyar ya watsar da su gefe ɗaya. Duk da buguwar da suka yi shanyewa yayi da saurin gaske ya yunƙura da ƙyar ya riga Malam miƙewa tsaye, ya sake nufar rijiyan gadan-gadan da nufin ya janyo hannunta, dan har lokacin tana ihun su taimaka mata. "Maheer..? Ka dakata kar kaje" Ya ji an ƙwallah kiran sunanshi daga can baya ana dakatar da shi, muryar kamar ta wacce ya sani. "Ku taimake ni... ku taimake ni mana... za su komar da ni cikinsu." Ta sake faɗa a galabaice daga can cikin rijiyar cikin kuka. Daga bayansa ana ta ƙwallah mishi kira, ana dakatar da shi, daga cikin rijiyar kuma tana ta roƙon su taimake ta. Ruɗewa yayi ya rasa gaba zaiyi ko baya, daga ƙarshe kawai sai ya yanke shawarar waigawa baya dan ganin wacce take dakatar da shi. Ido biyu yayi da Surayya, wani farin haske mai kama da hazo zagaye da inda take zaune, an ɗaureta jikin wani ƙaton bishiya, hannayenta da ƙafafunta duk an ɗaure ta baya da wani dogon kaca mai matuƙar tsaho da ya kasa hango ƙarshensa. "Kar kaje gurinta, mayya ce. Muguwa ce azzaluma, ka ga ita ta ɗaure min kurwa tana so ta hallaka ni. Idan ka ciro ta daga ciki mutuwa zanyi" Tayi maganar cikin gunjin kuka mai baiyana fita haiyaci. ƙafafu da hannayenta inda aka ɗaure sai tsattsafar da jini suke yi dan tsananin azaba. Da mugun gudu ya nufi gurinta dan ya taimaka mata ya kwance ta daga mugun ɗaurin da aka yi mata, duk da ihun kiran sunanshi da ake yi cikin murya mai amo da amsa kuwwa daga can cikin rijiyar sam bai waiga ba har ya isa gurin Surayya. A daidai wannan lokacin Malam ya yunƙura da ƙyar ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya leƙa, ko da ya miƙa hannunsa dan ya janyota sai yaga waɗancan hannuwan da suke jan ƙafafunta ta can ciki har sun kusa janyeta zuwa cikin jinin. "Kai mahaɗi ne, shi ne jigon da za ku iya haɗa hannu da yaddar Allah ku fitar da ni a halin da nake ciki... shi ne zai iya zama garkuwata a duk lokacin da suka tunkaroni da mugun nufinsu... ku taimaka min..." Ɗif muryar ta ɗauke, ruwan jinin ya ɓace ɓat kamar bai taɓa wanzuwa a cikin rijiyar ba, kusa da ruwan ya ɗago sai ya koma can nesa kamar yadda yake a da, hasken da ya baiyana ya ɓace matsanancin duhu ya baiyana. Firgigit Malam ya farka daga nannauyan barcin da ya ɗauke shi mai cike da hargitsattsun mafarkai, bakinshi ɗauke da salati da hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Shiru yayi yana tunanin mafarkin da yayi tiryan-tiryan a zuciyarsa. Matsanancin tsoro ne da fargaba ya kama shi, bai cika yin mafarki ba a rayuwarsa, amma duk lokacin da yayi mafarkin wani abu in Allah ya yarda mafarkin ko akasin abinda ya gani zai tabbata. Ɗai-ɗai ne mafarkan da yayi basu tabbata ba. Fuskar yarinyar mai siffar ban tsoro sam ya ƙi ɓacewa daga idanuwansa, har lokacin bai daina jin amsa kuwwar muryarta tana ihun su taimaka mata ba. Ko da ya kalli agogo sai yaga ƙarfe biyu da minti goma sha biyu na dare, addu'o'i yayi ya sake maida haƙarƙarinsa kan katifa ya fuskanci gabas, da nufin gyangyaɗawa zuwa ƙarfe uku da rabi. Amma sam ya kasa barci, da ya rufe ido ita yake gani tana miƙo masa hannu kamar yadda ya faru a cikin mafarkin. Sai juye-juye yake yi, daga bisani sai ya miƙe ya shiga bayi ya ɗauro alwala ya fara jero nafilfili kamar yadda ya saba ko wane dare. Amma yau akalar addu'o'insa gaba ɗaya ya tattara ne ga roƙon Allah ya tsare yarinyar nan ta cikin mafarkinsa, Ubangiji ya kawo mata ɗauki aduk halin da take ciki kuma a duk inda take a faɗin duniya. ****** ****** "Bibi wai me yake damunki ne? kwana biyun nan gaba ɗaya na rasa gane kanki da inda kika dosa. Faɗa min me yake faruwa? ina kike yawan zuwa a ƴan kwanakin nan bayan kuma na san yawo ba halinki bane" Shiru tayi kamar ba da ita take magana ba, idanunta

Chapter 9 of 25