Surayya tayi da cusa kanta cikin falon yasa ya tsaida maganar da yake yi, shi kaɗai ya amsa sallamar ita kuwa Rabi ƙara narkewa tayi a jikinsa tana sake ƙwaƙume shi.
Ita kuma ganin yanayin yadda suke yasa ta juya da sauri da nufin komawa inda ta fito, ranta banda tafarfasa babu abinda yake yi saboda tsananin kishi, nan take ta fara saƙe-saƙen da ta san a halin da za ta tarar da su kenan da bata shigo ba.
"Madam bismillah mana, ina za ki je kuma?"
Ya tambayeta bayan ya fahimci abinda take ƙoƙarin yi.
Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi sannan ta juyo ta kalle su, ta kalli fuskarsa ta kalli hannunsa da yake shafa gashin kan Rabi, shi baima san me take kallo ba ya ci gaba da abinda yake yi, bisa ga dukkan alamu sosai yake jin daɗin haka, ita kuwa Rabi tayi luf kamar ƴar kyanwa, har wani lumshe ido take yi dan tsananin jin daɗi, zuciyarta cike fal da farin ciki. Har wani tunani take yi a ranta
'Anya akwai abinda yafi miji ya nuna yana tattalin mace a gaban kishiyarta daɗi?' Rai fes sunan wani zani, a ɓoye sai doka murmushi take yi.
"Ƴallaɓai dama gani nayi ka dawo baka fito ka duba ni ba kamar yadda ka sabawa duk wacce ba ta da girki, shi yasa na shigo in duba Allah yasa dai lafiya."
Ta ƙarasa maganar a hankali, a sace kuwa gallawa Rabi wata muguwar harara tayi kamar idanunta zasu faɗo, tayi ƙwafa a hankali yadda ba wanda zai jiyo ta.
"Lafiya ƙalau ne fa, na shigo ina waya da Yusuf, bayan na gama kuma ƙanwarki ta tsare ni da shagwaɓarta. Afuwan Sweetheart, bari inyi wanka ga ni nan fitowa. Kin yini lafiya ko? ya jikinki?"
"Lfy kalau, da sauƙi, a fito lafiya Yallaɓai. Bari in jira fitowarku a falo..."
"Baby muje in taya ka wankan"
Ta faɗa a shagwaɓe tare da miƙewa tsaye, ta ja hannunsa suka shige cikin ɗaki ɗan ɓingilin sket ɗin jikinta ta ɗagawa, santala-santalan cinyoyin Rabin duk a waje.
Shi kuwa kamar raƙumi da akala yake bin ta a baya, yana tafe yake amsawa Suraiya ba tare da ya waiga ya sake kallonta ba.
"To Madam, sai na fito"
Da sauri ta fice taja ƙofar da ƙarfi ta buga gam dan haushi, a jikin ƙofar ta tsaya dan jiran ko ɗaya daga cikinsu zai biyo jin ba'asin buga ƙofar da tayi sai ta ji shiru, cikin falon ta koma tana ta masifa ita kaɗai kamar taɓaɓɓiya.
"Shegiya, da kwasassun ƙafafu kamar na agwaga, za ki gani in dai ni ce, ramuwar gayya zan miki da ta fi ta gayya zafi. Jarababbiya daga yin faɗa jiya har sun shirya yau dan tsananin fitina."
Taja tsaki, ta sauke wani zazzafar huci ta baki kamar kububuwa, ta riƙe ƙugunta da hannu bibiyu tana safa da marwa a tsakiyar babban falon, daga ƙarshe ta zube kan kujera a kan kujera a kasalance kamar wacce aka naɗawa mugun duka, kishi sai nuƙurƙusarta yake yi, ba abinda take haskowa a ƙoƙon zuciyarta sai hoton miji kuma abin sonta Maheer tare da kishiya kuma maƙiyiyarta Rabi suna tsotse-tsotse da shafe-shafe a cikin bahon wanka.
Lokacin ne taga yayi mata wani mugun tsawo saboda munanan saƙe-saƙen da zuciyarta yake mata. Shiru-shiru basu fito ba ta wuce ɓangarenta zuciya na ƙuna, idanunta ciccike da hawaye ta maida kofar falonta ta datse, har tana danna key saboda ko sun fito kar ma ya neme ta.
Hannayensu sarƙe da juna kafaɗunsu na gogayya suka fito daga cikin ɗakin suna ƙyalƙyala dariya, sanye suke da ƙananun kaya na shan iska duk su biyun saboda yanayin zafi da garin yake ciki. suna zama akan dining table ɗin ya ce
"Je ki yi wa Auntynki magana ta fito muci abinci."
Ɗif ta ɗauke wuta, duk wani fara'ar fuskarta ya ɓace. Ɗan jim tayi kamar baza ta je ba sai kuma ta miƙe dan cika umarnin da yayi mata bayan ta tuna da halinsa na rashin son wargi, yanzunnan idan tayi wasa sai ya saɓa mata ya canza yanayin walwalar da suke ciki.
"Honey?"
Ya kira ta lokacin da har ta kusa ƙarasawa ƙofar ɗakin Surayyan, waigowa kawai tayi tana kallonsa.
"Dawo ki zauna, bari inje da kaina. Na tuna ɗazu ko da na dawo ban shiga na duba halin da take ciki ba."
Tsawon minti uku yana ƙwanƙwasa ƙofar amma ta ƙi buɗewa, kuma tana jinshi tayi biris da shi, da ya gaji sai ya koma ya zauna.
"Ina ga tana banɗaki, mu jira ta minti biyu."
Hira suka ci gaba da yi sama-sama suna zaman jiran fitowarta, ita kuwa tayi bulum-bukwui a cikin ɗaki kaman baza ta fito ba.
"Honey ko inje in sake ƙwanƙwasa mata ƙofar?"
Rabi ta tambaye shi tana kallon agogo ganin lokacin ya ja sosai har an kusa kiran sallah.
Cikin sauri ya dakatar da ita.
"No ƙyale ta kawai, idan na dawo sallah sai mu ci abincin na san zuwa lokacin ta gama abinda take yi."
Sai da ta gama ɓata musu lokaci har aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i a masallatan kusa da su sannan ta fito tana ɗingishi, fuskarta cakuɗe da yanayin ban tausayi, idanunta har da guntun ƙwallah ta ƙarasa kusa da su, ta fara magana a raunane.
"Sweetat..."
Sai kuma tayi shiru hawaye suka ɓalle mata shar-shar kaman an buɗe famfo.
Gabanta ne ya faɗi, bata san me kuma za ta zo da shi ba, ita dai Allah ya sani har tsoron makircin Surayyan take yi. Tagumi tayi kawai tana kallo da saurarenta dan jin da wacce kuma ta zo yau.
Ya kalle ta sama da ƙasa sheƙeƙe, yana ta ƙoƙarin danne ɓacin ranshi dan kar Rabi ta fahimta. Da ya rasa ta cewa sai kawai ya jefa mata tambayar
"Lafiya?"
"Santsi ne ya kwashe ni nayi muguwar zamewa a bayi, ka ga har na gurɗe ƙafata..."
"Allah ya kyauta, sai ki nemi man zafi ki shafa. Idan kinso ki fito muci abinci bayan na dawo masallaci."
Ya faɗa cikin rashin kulawa da ba maganarta muhimmanci, haka kawai yake ji zuciyarsa bai gamsu da gaske ta faɗi ba. Dan ma kar kukanta ya karya mishi zuciya sai ya shige banɗakin falon ya ɗauro alwala.
"Honey na wuce masallaci."
Ya faɗa idanunsa a kan Rabi, da ɗan murmushi a fuskarsa.
"Tam ! A dawo lafiya Honey"
Ta amsa ranta ƙal bayan tayi fari da idanunta, har bakin babban ƙofar falon ta raka shi sannan ta juya ciki dan sauke nata faralin, tana tafe tana karkaɗa ƙugu da satar kallon Surayya da tayi poster a inda take tsaye baki da hanci hangame, fuska duk hawayen makirci kamar mai shirin ɗaukar hoto.
****** ******
Maheer Abdulganiyyu Mai Anini ingarma kuma kyakkyawan matashi mai ji da samartaka ɗan kimanin shekaru talatin da uku.
BILHAƘƘI
Haifaffen unguwar rimi ne a cikin garin kaduna. Mahaifinsa Malam Abdulganiyyu da uwargidansa Hajiya Balaraba haifaffun jihar zamfara ne a ƙauyen Maru. Tun duniya na kwance aiki ya dawo da shi garin kaduna a lokacin bai daɗe da yin auren fari ba, dukda iyayensa basu so ba a dole dai suka haƙura ya tattara ya dawo garin kaduna.
Tsawon zama a kaduna da gogayya da zallar hausawa yasa ko cikin maganarsu shi da matarsa sai jefi-jefi ake gane su zamfarawa ne.
Ta ko wani fanni na ilmin boko da islamic gangaran ne, mutum ne da ko wani lokaci hannunsa a buɗe yake. Kuma babban malami ne a nan unguwar rimi da kewayenta. Ga shi da balaga ta iya wa'azi da iya nasiha wa al'umma, cikin hikima yake isar da saƙon Allah da fiyayyen halitta SAW, da waɗannan dalilan yasa al'umma suke matuƙar ƙaunarsa da ganin girmansa.
Shekaransu uku a kaduna Allah ya albarkace su da samun haihuwar Maheer, nan da nan kuma sai haihuwar ta buɗe musu dan shekara ɗaya da rabi tsakani Balaraba ta haifi ƙanwarsa Shafa'atu, Lukman ya biyo bayanta shekara ɗaya da wata takwas tsakani, daga nan kuma sai haihuwar ta tsaya cik!
Ba sa jimawa sosai basu je mahaifarsu sun gaida iyayensu da sauran dangi ba, duk wani abu da zai faru na jaje ko na murna suna tafe shi da iyalansa. Amma sam baya daɗewa saboda aikinsa.
Shekarun Lukman uku a duniya Malam Abdulganiyyu ya ƙara auren wata bazaura mai suna Salamatu, a zahirin gaskiya sadakarta mahaifinta ya ba shi amma ko da wasa bai taɓa furtawa Balaraba sadaka aka bashi ba, ba dan komai yayi hakan ba kuwa sai dan ya kare wa amaryar martabarta a idanun abokiyar zamanta da ƴaƴansa. Da yake tsayayyen namiji ne a tsakanin iyalansa kuma adalin miji da tsananin sa'ar da aka yi duk suna da hankali sai suka haɗe kansu sosai kamar ya da ƙanwa.
Nan kuma haihuwa ta ƙara buɗe ƙofa a gidan suka fara yi a jejjere, Salamatu ta haifi huɗu, Mustapha, Saudat, Fahad, Faruk.
Ita kuma Balaraba ta ƙara yara uku suka zama shida, Badiyya, Asma'u da ɗan auta Yunus.
Tsananin haɗin kan da yake tsakanin iyalan gidan idan ba saninsu sosai aka yi ba babu yadda za a yi a gane ƴaƴan wannan ɗakin da ƴaƴan wancan ɗakin, yaran suna kiran Hajiya Balaraba da Ummee, ita kuma Hajiya Salamatu suna kiranta da Mummy.
Maheer ya taso nutsassten yaro ne mai tsananin ƙwazo da son karatun boko da islamiyya. Mutane da dama a waje suna kiranshi da magajin Malam ne dan duk cikin ƴaƴan gidan shi ne ya ɗebo Malam sak kamar yayi kaki ya tofar.
Kuma a fannin malanta ma shi ne dai ake ganin bisa ga dukkan alamu zai iya biyo Malam ɗin, dan yana shekaru goma sha biyu ya sauke Alƙur'ani mai girma, sauka ta gaske ba karatun zuƙu ba kuma ko a lokacin yana da haddar izufi goma sha biyar a kwanyarsa.
Wani dabara da hikima da Malam ɗin yake yiwa duk yaransa shi ne sai sunyi nisa sosai a karatun addini sannan yake saka su a makarantar boko.
(Wannan wata hikima da baiwa ce irinta Alƙur'ani mai girma. Insha Allah matuƙar yaro ya fara buɗe ƙwaƙwalwa da sanin alƙur'ani sosai kuma ya samu ƙwarewa a karatun Alƙur'anin duk wani karatu da zai biyo bayanta bi'iznillahi za ta zo da mugun sauƙi wa ƙwaƙwalwar yaro ko yarinyar. Wannan kaifiyyan ce an gwada an gani kuma an dace. Allah yasa mu dace)
Yana da shekaru goma sha takwas cif ya amsa sunansa na Mahiru (Gangaran) a fagen karatun Alƙur'ani mai girma, ya haddace ta tsaf kuma yasan tafsirin duk ayoyinta, kuma karatunshi bai tsaya a nan ba sai da ya haɗa da haddar wasu ƙananun littattafan addini. A lokacin ne kuma alƙiblar karatun nasa ya nutsa cikin karatun boko gadan-gadan, a fagen karatun addinin ma ba tsayawa yayi ba, ci gaba yayi da neman ilimi lungu da sako na zaurukan malamai daban-daban, dukda haka dai babban malaminsa Mahaifinsa ne Malam Abdulganiyyu.
A kance taura biyu ba sa taunuwa lokaci ɗaya amma ga Maheer ya haɗe biyun ya taune su tsaf ba tare da ya jigata ko ya galabaitar da haƙoransa ba.
Haka suka ta so har girma shi da ƴan uwansa, kyawawa kuma nutsastsun yara masu cike da tarbiyya ababen koyi ga sauran yara, da rayuwa mai cike da nasara.
Shafa'atu tana kammala secondry Malam ya aurar da ita ga ɗaya daga cikin ɗalibansa Nuhu, daman tun tana ƴar ƙanƙanuwa Nuhu yake son aurenta har ma yayi wa Malam ɗin magana. Aka yi sa'a kuma ita ma Shafan ko da ta girma bata watsa mishi ƙasa a ido ba, tana son shi. Har ta ƙare karatun aka yi auren cikin mutunta juna.
Cike da nasara Maheer ya haɗa digirinsa na farko ya samu aiki a matatar ruwa da yake cikin garin kaduna.
A lokacin kuma sai ƴan mata suka fara kawo mishi cafka ta ko wane ɓangare, a gefe guda kuma manyan aminan Malam guda biyu sun nuna sha'awar son haɗa shi aure da ƴaƴansu mata. Da yake baida wani zaɓi kuma ba shi da wacce yake so sai kawai ya barwa Malam ɗin zaɓin matar da ya ga ta dace da shi.
Lokacin da Malam ya nemi shawaran matansa akan wacce suke ganin tafi dacewa da Maheer a cikin ƴan mata biyun Ummee Balaraba cewa tayi
"Ga Mummynsu nan ita taya ka zaɓe, ni dai nawa addu'a da fatan tabbatuwar abinda ya fi alkhairi."
"Ameen ya Allah. Kin gama magana."
Malam ya amsa yana murmushi, fuskarsa baiyane da tsananin farin cikin furucin da tayi, daman ba ya hasashen samun matsala daga gare ta.
"Ni dai in a son raina ne gaskiya na fi so ya auri Surayya ƴar gidan Malama Hauwa, yarinyar nan ta daɗe tana ƙaunarsa. Duk da kunya da aka san ɗiya mace da ita har ta kai ba ta zuwa gidannan sai ta tabbatar Maheer yana gari, soyayyar da take masa ba kaɗan bane. Kuma na ga tana da nagartattun halayen da ake buƙata ga duk matar aure. Amma dai duk shawarar da ka yanke mu masu biyayya ga umarninka ne Malam. Fatanmu zaɓin alkhairi kamar yadda Ummee ta ce."
"Ma sha Allah ! Wannan ma hange ne mai kyau kika yi. Amma fa Alhaji Ghali shi ne wanda ya fara min maganar in dai Maheer bai tsaida wacce yake so ba yaje su daidaita da ƙanwarsa Rabi'a. Bayan kwana biyu kuma kamar haɗin baki shi ma Malam Hassan ya nemi in dai ba matsala ya ba Maheer sadakar Surayya..."
"To tunda haka ne mai zai hana ya aure su duk su biyun? Namiji ai mijin mata huɗu ne."
Mummy Salamatu ta katse Malam da murmushi fal a fuskarta.
Daga wannan zancen kamar wasa auren zuƙa-zuƙan ƴan matan biyu ya tabbata ga Maheer cikin ƙanƙanin lokaci, amma fa duk su biyun babu wacce taso hakan, sosai kishi ke cin zukatansu. Dan Maheer zankaɗeɗen saurayi ne na nunawa tsara, irin mijin da duk wata mace zata so mallakarshi ita kaɗai.
A dole dai duk suka danne kishinsu dan Maheer ya faɗa wa ko waccensu duk wacce baza ta iya zama da ƴar'uwarta sai dai ta haƙura da shi, duk su biyun sunyi mishi kuma su biyun zai aura.
Aurenshi da Surayya aka fara ɗaurawa, bayan sati biyu aka ɗaura aurenshi da Rabi'a.
Wani irin zama mai cike da drama suke bugawa a gidan domin an samu saɓanin halaye a tsakanin matan biyu, ita Surayya irin matan nan ne masu siffar munafurci da tsananin kissa da kisisina. A mafiyawancin lokuta da waɗannan halayen nata take gasawa Rabi gyaɗa a hannu, a gurin Maheer kuwa da yake ya fahimceta a baibai kallon mace mai tsananin ladabi da haƙuri yake yi mata, cikin hikima da waɗannan halayen take zurma Rabi a rami ita kuma ta ke ƙara siyo wa kanta martaba a gurinsa, ga tausayinta da yake yi dan mahaifinta malami ne mai ƙaramin ƙarfi saɓanin mahaifin Rabi da yake da arziki sosai.
Ita kuwa Rabi zawayi ce, sam bata da haƙuri, in dai abu ya ɓata mata rai komai ƙanƙantarsa bata iya ɓoyewa sai ta baiyana. Ga zallar tsiya da masifa a cikinta kamar mai aljannu, sam bata iya munafurci da ɓoye-ɓoye ba. Waɗannan halayen nata yasa Maheer yake kallonta a mace fitinanniya mai tsananin mitar tsiya, wacce bata cika son zaman lafiya ba. Shi yasa a mafiyawancin lokuta idan suka yi rikici da Surayya kai tsaye ita yake ba laifi.
Duk da waɗannan halayen nasu jajurtaccen namiji ne kuma tsayayye a gidansa, yana matuƙar ƙoƙarin sauke hakkin ko wacce daga cikinsu, ba ya taɓa fifita ɗaya akan ɗaya. Yana gwada musu soyayya sosai kamar auren soyayya ne a tsakaninsu ba auren haɗin iyaye ba.
A bayan aikin gwamnati da yake yi Maheer babban ɗan kasuwa ne, bai dogara da aikinsa kaɗai ba, yana sha'awar kasuwanci sosai tun yana ƙaraminsa.
Manyan shaguna biyu gare shi a kasuwar central da yake cikin garin kaduna, kayayyakin abinci irin na gida ake saidawa buhu-buhu, sosai kasuwancin ke gara mishi, yana samun alkhairi sosai fiye da yadda yake zato. Shi yasa duk yaran da suke mishi hidiman shagunan sosai yake fitar musu da hakkinsu, bai zama cinye du ba. Kamar wasa wata shekara da citta ya faɗi rugu-rugu babban yaronshi kuma abokinshi Yusuf ya bashi shawarar ko zasu siya su ajiye ne? bai ki shawararshi ba kuwa suka sai buhu ɗari biyu suka ajiye, ƴan watanni kaɗan aka nemi cittan aka rasa a kasuwa, suka saida akan farashi mai rahusa, dukda sauƙin da suka yi sun samu riba sosai da har ya kusa kamo uwar kuɗin. A wannan shekarar ya biya wa Malam da Ummee kujeran makka, da alƙawarin in dai yana raye bi'iznillahi shekara na zagayowa zai biya su tafi shi da Mummynsa.
Tun daga wannan lokacin ya zama dilar saida citta, lungu da saƙo na garuruwan kudancin kaduna irinsu kachia, kubacca, walijo, maraban walijo da sauran kasuwannin ƙauyaku yake tura yaranshi su saro mishi buhunhunan citta. Tun manyan dillalan citta a kudancin kaduna basu san sunanshi ba har suka sanshi, ko bai tura yara ba za a aiko mishi da kaya gangariya yawan yadda yake buƙata har shagunanshi na kasuwa, shi kuma ya tura musu da kuɗaɗensu ta banki.
Kamar wasa sai ya zamana daga lungu da saƙo na manyan jihohin arewacin nigeria ana zuwa siyan citta a gurinshi, dan ko ta yi wuya a kasuwa ba a rasa ta a gurinsu, kuma daidai gwargwado ba ya tsawwala riba, yana bada cittan akan farashin da wanda ya siya zai ji daɗi ya koma gobe. Da wannan dalilin yasa Allah yake saka mishi albarka a kasuwancinshi.
A wancan shekaran da ta gabata citta ya faɗi warwas a kasuwa tun daga watan ɗaya har zuwa watan goma da sha ɗaya lokacin da ake haƙo sabuwar citta, ganin har lokacin darajar cittan bai ɗaga ba yasa manyan dillalan suka yi miting, dan wancan shekarar ba ƙaramar asara suka yi ba. Dokar ta ɓaci suka sanya a kan duk wanda aka kama ya fitar da citta ba tare da farashin ya ɗaga zuwa yadda suke so ba zai biya tara mai tsananin yawa, ɓoye ta suka yi daga tsohuwar har sabuwar aka neme ta ɓat aka rasa a kasuwa.
Wannan dalilin ne yasa Maheer yin takakkiya da kanshi tun daga kaduna har garin kachia dan ya gana da manyan dillalan ko zasu rangwanta mishi farashin su bashi kaya yadda shi ma zai saida ya samu rabonshi.
Ashe ƙaddara ce ta cillo shi kachia...
***** ****** ******
"Ƴallabai ciwon kan ne har yanzu?"
Tsaki yayi ƙasa-ƙasa, ya sake lumshe idanunsa da suka ɗan canza launi kaɗan zuwa jajaye.
"Wallahi kuwa Yusuf. Ka san tun ɗazu da na kwanta da niyyar baccin sam na kasa yi? daman tun shekaran jiya da yamma naji kan ya fara sara min amma baiyi tsananin haka ba, da na yi barci ma sai na daina jin ciwon kan. Ina ga yau dan ya haɗu da doguwar tafiyar da nayi ne"
"To ko dai zamu je kaga likita? tunda Alhaji Barazanan ya ce sai zuwa dare zai shigo."
"Ok ! ina ganin dole hakan za a yi, bari in ɗan watsa ruwa tukunna, sai mu sha iska ma daga can."
Yana shirin shiga banɗakin kira ya shigo cikin wayarsa, a hankali ya duba fuskar wayar dan ganin mai kiran, Surayya ce. Bai ɗauka ba ya shige bayin ya bar wayar a kan gadon.
Yusuf ma fita yayi zuwa gurin sauran abokan tafiyarsa dan ya bashi damar shiryawa a nutse.
Kafin ya fito daga wankan a jejjere saƙonni har huɗu Surayya ta tura mishi duk na ban haƙuri, da addu'ar Allah ya huci zuciyarsa. Ta gane kuskurenta, in Allah ya yarda baza ta sake ba. Yadda ya karanta haka ya aje wayar ko reply ɗaya baiyi mata ba, ya canza shiga cikin wani yadi ruwan madara mai tsananin kyau, ɗinkin tinibu da aka yiwa yadin ya ƙara fito da kyan kayan a jikinshi, sosai kayan ya ƙara fito da kyawunshi kamar ɗan ashirin da biyar. Ya miƙawa Yusuf makullin motar suka fice daga ɗakin.
Nan da nan suka isa asibitin da yake ba nisa sosai da ɗakin Otal ɗin da suka yi masauki, babban asibiti ne na gwamnati. Babu laifi ko wane lokaci ba a rasa likita a asibitin, da yake yamma ne mutane sunyi sauki bayan sun yanki kati mutane uku suka jira kafin layi ya zo kansu.
A daidai wannan lokacin kuma Bibi da Madam Mary suna tsaye kan gadon da aka kwantar da Rose, tana ta jan numfarfashi sama-sama cikin mawuyacin hali, sai sannu suke jera mata kamar za su ari baki.
"Bibi kinga har yanzu numfashinta bai daidaita ba kamar yadda nose ɗinnan ta ce, yi sauri ki kira likita kawai kar ki saurari nose ɗinnan."
Ko kafin ta rufe baki ta fice daga ɗakin da sassarfa dan kiran likita kamar yadda Madam ta umarceta.
"Ke ke ina zaki je?"
Ɗaya daga cikin noses ɗin ta tare ta da sauri tana tambayarta ganin ta nufi ofishin likita gadan-gadan.
Wani kallon ke a suwa ta watsa mata, ta buɗe baki daƙyar kamar anyi mata dole ta ce
"Dr. zan kira..."
"Ki ɗan jira shi minti biyu, yanzu yana wani mare lafiyan ne..."
Ko kafin ta gama maganar cikin laƙaiƙaita da yanga Bibi har ta kai ƙofar ofis ɗin likitan, ta murɗa handle ɗin ƙofar tana niyyar cusa kai cikin ofis ɗin take magana cikin masifa
"Ta mu mare lafiyar tana cikin wani yanayi kike min zancen wani? ciwo ai baifi ciwo ba..."
Kamar wacce lantarki ya ja ko kuma wacce ta taka ɓawon ayaba ba zato ba tsammani ta tafi suu sai a kan ƙirjinshi a daidai lokacin da shi ma yake ƙoƙarin fitowa daga ofis ɗin, hannunshi riƙe da wayarshi ƙirar Samsung. Kirjinshi ne ya buga dam ! ya sake wayar a ƙasa da sauri ya tallafeta ganin tana ƙoƙarin zamewa ta faɗi ƙasa warwas!
"Subhanallahi ! hankali dai, ba kya gani ne?"
Tattausan muryarsa da yake fita a hankali ya daki dodon kunnenta.
A zabure cike da tsoro ta ɗaga kanta daga jikinsa ta ja da baya a ɗimauce. Ta sake kallonsa a gigice, abu ne da bai taɓa faruwa da ita ba kwanciya a jikin wani namiji. Wasu ababe masu kama da kibau ne suka fito daga cikin kyawawan idanunsa suka cake ta a ƙahon zuci dai-dai saitin ɓangaren dama.
"Sorry... I'm very sorry pls."
Ta faɗa cikin rawar murya.
Shi ma a ruɗen yake, idanunshi na kanta ya tsugunna ƙasa dan ɗaukar wayarsa, a daidai lokacin ita ma tayi ƙasa dan ɗaukar tata wayar da ƙaramar jakarta da suka zube a ƙasa. Hannayensu ne suka sake gogar na juna sai suka janye da saurin gaske kamar shokin ne ya jasu, idanunsu na cikin na juna.
Yana samun nasarar ɗaukar wayarsa da sauri ya zagaye Nose ɗin da ta biyo bayan Bibi dan dakatar da ita ya fice daga ofis ɗin, bai sake yarda ya haɗa ido da ita ba.
Itama gurin likitan ta ƙarasa da sassarfa da ya saki baki da hanci buɗe yana abinda yake faruwa kamar a fim ta fara magana cikin rawar murya, ƙirjinta sai bugun tara-tara yake yi.
"Dr. Rose tana cikin wani hali, numfarfashi take yi sama-sama..."
Bai ce komai ba, ko kafin ta aje numfashi kayan aikinshi kawai ya kwasa ya fice da sauri suka bi bayanshi ita da Nose ɗin.
Tsawon wasu mintuna likita da Noses uku ne a kan Rose suna ta iya ƙoƙarinsu dan daidaita numfashinta.
BILHAƘƘI
Daƙyar suka samu nasarar daidaita al'amarin, numfashinta ya koma yana sauka kamar yadda ake buƙata. Suka sake gyara zaman ƙarin ruwan da yake ɗaure a hannunta, sannan suka fice daga ɗakin likitan ya haɗa zufa sharkaf.
Madam Mary da take tsaye a ƙofar ɗakin hannayenta naɗe a ƙirji babu abinda take yi sai tsiyayar hawaye. Duk cikin yaranta tana bala'in son Rose, ƴar uwarta ce, mahaifiyar Rose ƙanwar mamanta ce.
Sosai take yi mata biyayya da aikata duk abinda take so, shi yasa take matukar jin daɗin aiki da ita. Duk cikin ƴan matan gidan bayan Bibi Rose ce ta ba muƙami kamar shugabansu, duk abinda Bibi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 25