faɗa inji me kika ce?"
"Mama"
Ta sake faɗa tana dariya.
Dariyar farin ciki ta tuntsire da shi tana ta jera hamdala Amira tana taya ta da dariyar farin ciki.
Tun daga ranar kuma kamar an buɗe mata bakin magana, a hankali cikin nutsuwa take ci gaba da iya maganar, duk abinda tayi niyyar faɗe sai dai a ji bakinta ya faɗa.
Sati biyu tsakani Malam Ali ya kaita makarantar islamiyar da yaranshi suke zuwa, boko kuma Maman Ushe ta bashi kuɗi ta ce ya saka ta a makarantar private mai sauƙin kuɗi.
******* *******
Maman Ushe da Malam Ali mazauna unguwar mai dubun tsumma ne a cikin rigasa na garin kaduna. Dattijon magidanci managarci, mai wadatacciyar zuciya cike da rufin asiri, matanshi biyu da ƴaƴa takwas.
Indo ita ce amarya kuma ita ce mai yara takwas ɗin, maza huɗu sune manya sai ƙananun mata su huɗu.
Maman Ushe haihuwarta ɗaya ne da Malam Ali, shekarar yarinyar goma sha biyu Allah yayi mata rasuwa. Asalin sunan yarinyar Usaina ne amma Zainabu ƴar gidan Indo da suke sa'anni tun suna yara bata iya cewa Usaina ba sai take ce mata Ushe, a hankali Ushe ya zagaya unguwa sai mata suka fara ce ma Karima Maman Ushe.
Duk da Malam Ali tsayayyen miji ne a gidansa hakan bai hana ƙananun rikice-rikice da kishi ke janyowa tsakanin matansa ba, amma mafiyawancin lokuta Indo ita ce fitinanniya mai yawan tsokanar faɗa da yawan kai ƙorafi, tun Malam bai gane ba har ya gane, shi yasa kullum yake yawan kwaɓe ta da cewa bata son zaman lafiya.
Sana'ar Maman Ushe shi ne saida ganyayyaki da magungunan gargajiya, ita ma ta gaji wannan sana'ar ne a gurin mahaifinta. Mafiyawancin ganyayyaki ita mata suke biya kuɗi ta je daji ta ɗebo musu, kuma idan typhoid ya tasa yaro a gaba cikin hukunci na ubangiji idan ta haɗa magunguna sai ku ga an samu sauƙi, shi yasa har daga wasu unguwannin ana zuwa gurinta karɓar magani, da wannan dalilin yasa a sati tana shiga daji sau biyu, kamar namiji haka take sassaƙo magunguna da saiwoyi da ganyayyaki, kuma Allah yana tsare ta babu wani abin cutarwa da ya taɓa samunta.
****** *******
Shigowar cincirindon yara sanye da kayan makaranta da gudu cikin gidan suna haki da numfarfashi yasa Indo ta fara zaginsu tana zazzaga masifa.
"Wani irin iskanci da rashin tarbiya ne haka za ku shigo mana gida babu ko sallama? iye? ku wuce ku fita tun kafin in ci mutuncinku"
Basu saurareta ba kai tsaye suka nufi gurin Maman Ushe da take tsugunne a ƙofar ɗakinta tana warware himilin magungunan da ta ɗebo a daji.
"Maman Ushe, Maman Ushe, Amira ta sumar da Raliyan mai daddawa a makaranta..."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"
Ta katse su a tsorace hannayenta duk biyu dafe da ƙirjinta, ta juyo tana kallonsu idanunta a bubbuɗe.
"Me ya faru haka? garin yaya har ta sumar da ita?"
Nan yaran duk suka fara ƙoƙarin bata labarin abinda ya faru, amma tsananin ruɗewa yasa ta kasa fahimtar me suke cewa, hijabinta kawai ta ja a jikin ƙofa ta bi bayan yaran zuwa makarantar bokon.
"Hehehehe! Ba na faɗa ance ba haka ba? na farko kenan!"
Indo ta faɗi hakan tana ƙyalƙyata dariya, dan gulma har tana sake leƙa su ta zauren gidan.
kai tsaye ofishin shugaban makarantar ta nufa inda ta ga Amira an saka ta hawa mashin a tsakar rana, wani malami yana tsaye da zabgegiyar bulala a kusa da ita da ta ɗan tsuguna kaɗan sai ya zabga mata, idanunta sunyi jajur, babu ko ɗigon ƙwallah a idanunta.
"Hajiya akwai damuwa fa, yarinyarki tana cikin babban matsala. A binciken da muka yi na dalilin rikicin mun gano yarinyarki ita take da gaskiya a rikicin da suka yi, amma matsalar da ake ciki shi ne har yanzu ita wancan yarinyar tana asibiti bata farfaɗo ba..."
"Ina Malam Buharin? wallahi Allah bazai yiwu ba, ta ya kuna ji kuna gani za a sabauta min yarinya baku ɗauki mataki ba? ina ita wancan yarinyar? ku bani ita mu tafi asibitin ta yi duk mai yiwuwa ta farfaɗo min da yarinya idan ba haka ba wallahi a station zata kwana, idan ta kasheta ku tabbaci haƙiƙa ita sai na kashe ta."
Mai Daddawa ne ta banka ƙofan ofis ɗin ta shiga tana sababi, ta inda take ba ta nan take fita ba.
*BILHAƘƘI*
"Haba Maman Raliya, ki yi haƙuri a bi komai a sannu mana..."
"Naƙi inyi haƙurin, Karime na ce naƙi inyi haƙurin. Haka kawai za a kashe min ƴar marainiyar Allah a kan wata ƴar tsintuwa can tsintacciyar mage da bata mage? yo wa ya sani ma ko mayya kika tsinto aka jefa ta a cikin yaranmu zatai ta musu ɗauki ɗai-ɗai tana lamushewa?"
Maman Ushe dai shiru tayi ba baka sai kunne, dan idan ta ce zata tanka to tabbas zasu yi ɓatacciya, ta ga abin ya fara zama da cin mutunci, ranta dai yayi mummunar ɓaci zuciyarta cike da mamakin Mai daddawan.
Shugaban makaranta dai sai haƙuri yake bata amma ta ƙi saurarawa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba tana ta zazzaga masifa kamar wata zararriya.
Daga ƙarshe dai da yaga sulhu bazai yiwu a nan cikin makaranta kai tsaye asibitin aka ruguntsuma gaba ɗaya da iyayen yaran.
Isarsu asibitin suka tarar da Raliya ta farfaɗo cikin wani mawuyacin hali, ƙwararrun likitoci biyu ne a kanta amma jini take ta fitarwa ta hanci ta baki, duk iya ƙoƙarinsu sun kasa tsayar da jinin sai zurkuɗa mata allurai ake yi.
Hannu bibiyu mai daddawa ta ɗora a kai ta rushe da kuka mai tsananin ƙarfi, ita ma Maman Ushe kukan take yi zuciyarta cike da fata da addu'ar Allah ya aiko wa Raliya Manzon sauƙi da gaggawa, idan Raliya ta rasu bata san yadda zasu yi ba.
Suna tsaye cirko-cirko har Malam ya je ya tarar da su a asibitin, a lokacin wani ƙanin Mai Daddawa ya ɗauko ɗan sanda, sai masifa suke yi suna faɗin lallai a tafi da Amira a kulle ta har sai Raliya ta farfaɗo, idan ta mutu kuwa itama a kashe ta.
Amma ganin ƙanƙantan Amira yasa basu tafi da ita ko ina ba, ɗan sandan dai ya tsaya a gurin zuwa jimawa su ga abinda hali zaiyi.
"Likita yaya?"
Malam ya tambaya da sauri ganin likitan ya sake fitowa daga ɗakin da aka kwantar da Raliyan.
"Alhamdulillahi, ku kwantar da hankalinku, mun samu jinin ya tsaya. Sai dai har yanzu bata gama dawowa cikin haiyacinta ba."
Yana gama faɗin haka ya kama hanyar barin gurin.
"Dr zamu iya shiga mu ganta?"
Mai daddawa ta tambaya muryarta na rawa, idanunta sun tasa luhu-luhu saboda kuka.
"Eh zaku iya shiga ku ganta, amma kar kuyi hayaniya sosai."
Su Maman Ushe basu samu sauƙi da rangwamen hantaran da ake musu ba sai da Alhaji Kabiru mahaifin Mai daddawa ya isa gurin, kakan Raliya. Ya nuna matsanancin ɓacin rai akan abinda su Mai Daddawa suka yi.
"Yau idan mutuwa Raliya tayi lokacinta ne yayi sanadi ne kawai wannan yarinyar ta zama, haba ! sai kace baku yarda da Allah ɗaya ba? ina imaninku ya tafi Habiba? To wannan yana daga cikin ƙaddara mara kyau, Ubangiji ya jarabce ki ne dan yaga cikar imaninki. Kinsan kuma yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau yana daga cikin rukunan imani.
Kai kuma Ibrahim tsalo-tsalo da kai ka biye wa Yayarka har kana ɗauko jami'an tsaro, sai kaje ka sallame su.
Habiba ca nake ke da Karime ƙawaye ne tun na yarinta? Tare kuka yi ƴanmatanci, dan da zumunci da kara Raliya ai ɗiyarta ce, bai kamata ku titsiye su har haka ba. Sam banji daɗin abinda kuka yi ba."
Da ya gama faɗa ya ƙara ba su Malam haƙuri sosai kamar zai ari baki, sannan ya ce idan zasu gida suna iya tafiya, su kwantar da hankalinsu in Allah ya yarda komai zai zo da sauƙi.
****** ******
"Wallahi Abba ba laifi na bane, dan Allah kuyi haƙuri. Kullum Raliya sai sun tsokane ni ita da Jamila suna ce min tsintacciyar mage, to ban taɓa damuwa ba sam bana tanka musu, yau kawai zan wuce sai ta shaƙo min hijabi ta baya ta yar da ni a ƙasa yara sukai ta min dariya. Shi ne naji haushi da na tashi na tunkuɗeta ta faɗi a ƙasa, daga haka ban sake mata komai ba har na kusa fita daga makaranta aka kamo ni wai na sumar da ita."
Ta ƙarasa bayanin cikin kuka, tana ta jan majina da sauke ajiyar zuciya.
"Kai ! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! ya Allah kai mana maganin masifa. Dan Allah dan Annabi Amirah ki kiyaye karki kuskura ki sake yin faɗa da ko wace yarinya kinji ko? ita kuma Jamila zan ɗauki mummunar mataki a kanta kinji ko?"
"To Abba. Bazan sake ba"
Saboda mugun dukan da ta sha sai da ta kwana biyu Maman Ushe tana gasa mata jiki da ruwan zafi sannan ta bi ta shafe mata jiki da Mantaleta, daga bisani kuma ta haɗa mata da maganin gaɓoɓi, cikin hukunci na Ubangiji sai ga shi ta warke tsab ta cigaba da zuwa makaranta, bayan matsanancin jan kunne da gargaɗin da aka yi mata.
****** ******
"Mal Murtana na zo karɓar canjin jiya ne"
Nan da nan ya haɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk, ya kalleta yana zazzare idanu alamun rashin gaskiya ƙuru-ƙuru.
"Ke karki kawo min zancen banza da na wofi, wani canji zan baki bayan wanda kika amsa da magriba."
"Ko dai ka manta ne Mal Murtala? baka bani canji na ba fa. Yanzu ma Mama ce ta turo ni in amsa in siyo mata shinkafa kwano ɗaya..."
"Amirah idan baki bar nan ba wallahi zan mare ki, ni zaki kawo wa rainin wayau? sau nawa zan baki canjin ne? ku ji min yara da rashin gaskiya, cuta ta zaki yi? ko sata zaki min? ki bar nan tun kafin in saɓa miki."
Yanda yake ta masifa da tada jijiyar wuya a ƙofar shagon yasa mutane suka fara taruwa, daman kuma an fito sallar la'asar kenan ba daɗewa.
"Mal me yake faruwa ne? subhanallahi."
Wani daga cikin mutanen ya fara tambayarsa ganin har Amirah ta fara kuka, kuma ta cije a ƙofar shagon tace baza ta tafi ba sai ya bata canjinta.
"Tun jiya da yamma tazo da dubu ɗaya na bata suger rabin mudu, wallahi Mal Liman ba a yi minti ashirin ba ta dawo na bata canjin ɗari bakwai da hamsin..."
"Wallahi ƙarya yake yi ban dawo na karɓi canji na ba."
Ta katse shi da faɗin haka cikin ihun kuka.
"Baki da tarbiya ko? da girma na ni nake miki ƙarya?"
Ya tambaye ta cikin fushi da zuciya, ko kafin Liman da sauran jama'a su tanka ya ɗaga zabgegen hannunsa ya kai mata ƙaƙƙarfar mari da hannunsa na hagu.
Cikin sa a kuwa ya same ta da kyau, ta daddage ta kwalla ihu a ɗimauce ta fara diri-diri a gurin tsananin ruɗewa sai da Liman ya riƙo ta.
"Assha ! Assha !! haba Mal Murtala? duk da ta yi rashin kunya wannan marin da ka yi mata baka kyauta ba, ka shiga babin zalunci kuma..."
"Allah ya isa, mugu, azzalumi. Wallahi sai Allah ya saka min, kuma sai ka bani canji na."
Ya miƙa hannu zai sake cafko ta dan shi mutum ne mai tsananin zuciya da sauri Liman ya janye ta, sauran mutane suka fara ba Mal Murtala haƙuri shi kuma Liman ya ja ta zuwa gidansu, yana zuwa ƙofar gidan kuwa yayi kiciɓis da Malam Ali ya dawo kasuwa dan haka ya damƙa mishi ita bayan ya kora mishi bayanin duk abinda ya faru.
Godiya sosai yayi wa Liman ya ja hannunta suka shige cikin gida ɓangaren dama na fuskarta sashin yatsu ruɗu-ruɗu, cike da tausayinta shi kuma Liman ya wuce gurin nashi harkokin.
"Me ya faru Malam? Subhanallahi, Amirah? wa ya duke ki haka?"
Maman Ushe ta saki butar hannunta tayi kan Amirah tana duba yadda fuskarta ya kumbura sosai lokaci ɗaya.
A tsaitsaye a nan tsakar gidan ya kora mata bayanin abinda ya faru kamar yadda Liman ya faɗa mishi, ya kalli Amirah da take ta sauke ajiyar zuciyar kuka akai akai yace
"Amirah ko dai kin karɓi canjin kin manta ne?"
"Haba Malam ! idan da ta karɓo canjin ta ya zan sake tura ta ta karɓo min canjin? wallahi bata karɓa ba. Jiya tun da ta karɓo suger yace ba canji taje ta dawo tana nan tana aikin makarantar da aka bata, bata gama ba ma aka kira sallar magariba, kuma ka san ka hana aiken ƴaƴa mata bayan magriba. Yau kuma tun safe tana makaranta ko da ta dawo ta ci abinci bacci tayi sai yanzu da tayi sallah na ce ta amso min canjin.
Kila dai shi ne ya manta ko kuma cuwa-cuwar da ya daɗe yana gwadawa ne yau zai gwada ta a kaina..."
"Karime kenan ! Ba dai a shaidar ɗan yau. Kika sani ko ta karɓi canjin ta kashe a makaranta?"
Indo ta faɗa haka tana dariyar ƙeta.
"Ko cikin ƴaƴa dubu zanyi shaidar Amirah, banyi mata tarbiyar karɓar abu har ta kashe ba tare da ta tambaye ni ba."
Tana ba ta wannan amsar ta ja hannunta suka shige ɗaki zuciyarta yana tuƙuƙi.
Malam Ali buta ya ɗauka a ɗakin Indo ya shige bayi dan kuwa girkinta ne, ita kuwa Indo ta ja tsaki ta ci gaba da tankaɗen garin tuwo tana waƙa tana yaɓa habaici.
****** ******
Washe gari unguwar suka tashi da gaggarumin gobarar da ya lashe shagon Mal Murtala tas da duk wani kayan da yake ciki, tsinke ba a fita da shi ba. Kuma wani abin mamaki da tashin gobarar ko kaɗan bata shafi gidan da shagon yake ba balle har ta shafi sauran gidajen da suke makwaftaka da shagon.
Da saurin gaske aka garzaya gidan Malam Murtala dan sanar da shi abinda yake faruwa sai aka tarar da iyalinshi cikin wani mugun tashin hankalin, yana kwance baisan halin da yake ciki ba aman jini kawai yake yi ta hanci ta baki.
Nan kuma sai jimamin ya zama biyu, a gurguje aka idar da sallah sannan makwafta suka taimaka aka kwashe shi zuwa asibiti.
BILHAƘƘI
"Amirah ya jikin naki?"
Maman Ushe ta tambaye ta tana ƙoƙarin zama kusa da ita, ta sa bayan hannunta ta taɓa goshinta taji har lokacin zafi rau.
Ta ɗago idanunta da sukai mata nauyi a wahalce ta kalleta, ta buɗe baki da kyar ta ce
"Mama kaina ciwo, nauyi yake min kamar zai faɗi."
"Sannu Amirah, zai faɗa in Allah ya yarda, bari in sake shafa miki maganin."
Da sauri ta ɗauko wani roba da ta mutsittsika ganyayyaki ta tsiyayi ruwan ta shafa mata a kai tun daga goshi har ƙeya, sai wash wash take yi ita kuma tana jera mata sannu kamar ta amshi ciwon kan ta maida shi jikinta, zuciyarta cike da matsanancin tausayinta.
Tun jiya da daddare da zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, ta haɗiye kwayar paracetamol tun cikin daren amma har lokacin bai faɗa ba, shi yasa ta juya yi mata magungunan da ta fi ƙwarewa na ganyayyaki.
Tana gama shafe ta da magungunan ta kama kan ta karanta fatiha ƙafa bakwai ta tottofe ta da shi, cikin hukunci na Ubangiji kuwa nan da nan bacci mai nauyi ya kwashe ta, nishe-nishen da take yi yai sauƙi sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara haɗa zufa alamun zazzaɓin ya sauka, sai a lokacin hankalin Maman Ushe ya fara kwanciya.
***** *****
"Uhmmm! Wato Mal Hadi mutane suna raina girman Allah da buwayarsa. Ban san me yake damun mutanenmu ba da har suke iya danne gaskiya su take ta ƙiri-ƙiri kuma suyi ta zabgo rantsuwa a kan ƙarya.
Jiya zaka sha mamaki idan kaga yadda Murtala ya fututtuke yana ta masifan cewa ya ba yarinyar nan canjinta. Da ta ce mishi ƙarya yake yi ya shammace mu ya zabga mata wani wawan mari da duk saida muka ji a jikinmu.
Ita kuwa tai ta zabga mishi Allah ya isa da cewar sai Allah ya saka mata, tabbas da gaske ne Allah yana saurin amsa addu'ar wanda aka zalunta, sai dai wani lokacin sakaiyar tana daɗewa kafin baiyanarta.
Idan kayi tunani dakyau ba komai ne yake ɗawainiya da Murtala ba face hakkin wannan yarinyar, yanzu fisabilillahi dubi yadda shagonshi ya ƙone ƙurmus an ce ko tsinke ba'a fitar da shi ba, shi kuma yana can ya yini a asibiti har yanzu da yammacinnan an tabbatar mana baisan wanene yake kanshi ba."
"Wannan gaskiya ne, tabbas gaskiya ka faɗa Mal Liman. Kuma ka san shi Murtala an daɗe ana mishi raɗe-raɗin riƙe wa yara canji, tun jiyan na ji mata suna ta surutun shi ne baida gaskiya."
"Assha ! ka ji irinta ba? Allah ya kyauta. Tsakanin arha da tsada kaɗan ne fa amma mutane sun gwammace su ringa ɗaɗɗakawa cikinsu haramun. Allah ya tsare mana imaninmu."
"Ameen ya Allah"
Da waɗannan surutan suka isa ƙofar gidajensu kasancewarsu maƙwaftan juna, nan suka rabu kowa ya shige gidansa.
***** ****** *****
Ta sake gyara zama sosai ta kalli Magajiya, hannunta na dama riƙe da haɓarta ta ji zancen da ya shige ta, fuskarta cike da matsanancin mamaki.
"Magajiya anya da gaske kike yi? na sanki da shafawa fa idan kika ji sanyin waje."
Nan take ta ɗaure fuska tayi murtuk, ta ƙara ƙanƙance mitsi-mitsin idanunta ta kalle ta cikin fushi.
"Indo ke fa baki da mutunci, daɗi na da ke ƙwaƙwalwar kifi gare ki, shi yasa kullu yaumin a doɗe kike."
Ita ma ɓata fuskar tayi, zagin ya shige ta, har ta buɗe baki zata yaɓa mata baƙaƙirin sai ta maze, da tayi wani tunani kuma sai ta saki fuskarta ta fara dariya.
"Yi haƙuri aminiyas, wai dan girman Allah da gaske kike yi?"
"Wallahi Allah da gaske nake miki, idan kuma kina tantama ki tashi muje gidan Harisatu ki tabbatar da gaskiyar zance na."
"Ki bari dan Manzo?"
Ta sake tambayarta cikin tantama zuciyarta cike taf da wasi-wasi da shakkar abinda Magajiyar ta faɗa mata.
"Ah ! Zancen kike so Indo, ai kuma sai kiyi."
Ta juya mata baya ta janyo matankaɗin da yake ajiye can gefe ɗaya ta fara rairaye tsakin masara.
"Haba mana ƙawalli, ke da zaki rakani gidan mai zobian ya kuma za ki tatago aiki? yi haƙuri zo muje mu dawo tun da kince nan layin bayan ku ne, kamar na san zan tadda harkar arzikin nan yau duk ƴan kuɗaɗe na hansin hansin ne."
"Yanzu na ji batu, haba! Da ana nuna miki ga Annabi kina kaucewa, dan ma kin samu za a taimaka miki? Na yi wa mutane hanya gurin mai zobia sunfi mata hamsin, duk cikinsu banji wacce ta kawo ƙorafin buƙata bata biya ba."
Nan ta janyo wani tsumman gyale a cikin ɗaki ta yafa a kai suka kama hanyar ficewa daga gidan, sai kuma ta buɗe ƙaton muryarta tana magana da wacce suke zaman haya tare a gidan.
"Kuluwa ga sanwar fate na nan a wuta ki dinga duba min kar ruwan ya ƙone, yanzu zan dawo. Idan Baban khalifa ya dawo a ce mishi na je amso daddawa maƙwafta."
Bata jira amsawarta ba suka fice daga gidan, suna tafe tana ƙara ƙarfafawa Indo gwuiwar tabbas buƙatarta zata biya.
"Ni fa daman ba komai yasa kika ga ina zizzillewa ba kinsan abinda baka yi farkon yinshi ba yana da wahalar farawa lokaci ɗaya, har ga Allah ban taɓa bin gidan malamai ba balle har in kai sunan Karime, a duk wani abu na zamantakewarmu baki na yake ƙwatata a gurinta da gurin Malam."
"Kar ki damu Indo, ba saɓo fa zaki aikata ba. Na ji malamai da yawa suna faɗin babu laifi mace ta nemi taimako a kan miji ko kishiyarta matuƙar taga a zamantakewar nasu ana cutar da ita."
"Uhmmm! Magajiya ke nan!"
Ta sake faɗin haka zuciyarta cike da kokwanto da rashin yadda da abinda Magajiyan ta ce.
Sun isa ƙofar gidan ta sake jan tunga ta tsaya hannayenta duk biyu riƙe da ƙugunta.
"Amma Magajiya kina ganin idan na je zan samu maganin matsalolina?"
Wani dogon tsaki ta ja ranta a ɓace, cikin faɗa ta fara magana
"Kinga Indo in dai kina kokwanto zuciyarki bata bada gaskiya akan aikin mai zobia ba daga nan kawai ki wuce gidanki nima in wuce gida na, dan Billahillazi in akwai rashin yadda ko tayi miki aiki bazai ci ba."
"Maganar bai kai haka ba, yi haƙuri mu je."
Ta faɗa cikin sadaƙarwa da miƙa wuya.
"Kin yadda?"
"eh"
"Kin miƙa wuya?"
A wannan karon kai kawai ta gyaɗa kamar ƙadanguruwa, alamar da ke nuna ta miƙa wuya.
"To ki sa a ranki wannan tsintacciyar magen ta gidanku kamar ta ƙara gaba cikin duniyar ne, ita kuma Karime ki ɗauketa a matsayin bandaro ko kuma ince koma bayan-baya a gurin Malam Ali. Babu wacce zai dinga gani da haske kamar fitila da tsananin ƙyalli kamar tauraruwa sai ke Indo. Bani hannunki nan"
Ta damƙi hannunta da sauri suka faɗa gidan mai zobia da ƙarfin jiki da na zuciya.
Da yake ita sananniya ce kuma tsohuwar customer ce da take kawo mata da yawa masu zuwa ayi musu aiki kai tsaye ɗakin mai zobian ta shiga dukda ta ga wasu mata kusan su takwas a zaune a benci suna zaman jiran layi ya zo kansu. Nan take kuwa aka ba Indo umarnin ta shiga ciki bayan an sallami matar da take cikin ɗakin.
"Ki shiga, zan jira ki a nan. Kar kiji tsoron komai kiyi mata bayanin duk abinda kike buƙata."
Magajiya ta faɗi hakan tana kallon Indo, sai da taga ta shiga cikin ɗakin sannan ta nemi guri can gefe guda ta zauna tana jiran fitowarta.
Indo na shiga ta ga wani abin mamaki, bisa ga yadda Magajiya taita bata labarin Mai zobia a zatonta tsohuwar mace za ta gani, saɓanin tunaninta sai ta ga matashiyar mace ce, a ƙiyasce ma baza ta haura shekaru ashirin da biyar ba zuwa ashirin da bakwai. Kyakkyawa da ita, alamar hutu baiyane ƙarara a jikinta. Duk da baƙa ce amma baƙinta irin mai kyau ɗinnan ne da sheƙi, ɗakin kuma a gyare tsaf-tsaf babu tarkace, an malaye tsakar ɗakin da tattausan kafet ita kuma mai Zobia tana zaune a gefen wani ƙaramin gado na bono da wasu kwanduna a gabanta...
"Ba a kalle-kalle a nan, idan baki da matsala kina iya fita ta gaba ta shigo"
Mai Zobia ta faɗa bayan ta zabgawa Indo harara da juyayyun idanunta masu matuƙar ban tsoro.
Ba shiri ta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa, sai inda-inda take yi cikin ɗimauta.
Hannu ta ɗaga mata alamar dakatarwa ba tare da ta amsa mata gaisuwar ba.
"Ina Zobia?"
Da saurin gaske ta warware ƙullin kuɗi a haɓar zaninta ta zaro gudan naira hamsin sabuwa fil ta miƙa mata.
Da hannu biyu ta buɗe kuɗin ta ƙura ma hamsin ɗin idanu kamar tana karantar wani abu a ciki, minti biyu tsakani sai ta fara wani surutai shi ba hausa ba shi ba larabci ba.
"Indo..? Ige ke tare da ke mi'am matsalarki?"
Mai Zobia ta tambayi Indo da hausar zamfaranci.
"Ƴar kishiya ta ita ce babban matsala ta a yanzu, ba ƴarta bace ta cikinta tsinto ta tayi a daji watanni huɗu da suka wuce, yarinyar nan ta zame min alaƙaƙai. Hankalin mijina gaba ɗaya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 25