cike da zaƙaƙan mafarkai ya kwashe su duk su biyun.
BILHAƘƘI
Karfe shida da minti hamsin dai-dai Bilhaƙƙi ta farka. A lokacin har an idar da sallar magrib, motsin da tayi shi ya farkar da Maheer daga daddaɗan barcin da yake yi.
"Babe ya aka yi?"
Yayi maganar a hankali, har lokacin idanunsa suna lumshe.
"Kalli lokaci ka ga, kamar ma an idar da sallah fa."
A hankali ya buɗe ƙwayoyin idanunsa da har lokacin suke cike da barci ya zube su a kanta, suka yi kallon-kallo da murmushi a fuskokinsu. Sai kuma ya kauda fuskarsa ya maida kan agogon bango.
"Subhanallahi."
Ya faɗa cikin sauri. Za ta miƙe ya riƙe ta a jikinsa. Ya tashi daga kwancen suka miƙe zaune gaba-ɗaya.
"Muje inyi miki wanka, sai muyi alwala muyi sallah."
Dariya tayi kawai, ta sake sunne kanta a ƙirjinsa cike da kunya.
"Je ka fara yi, idan ka fito nima sai inyi."
Murmushi yayi, ya shafi gashin kanta, ya ɗago fuskarta ya sumbace ta a goshi. Ya ɗauko rigarta da ke ajiye a gefensa ya sa mata. Ya sauke ta a gefe sannan ya sauka ya nufi banɗakin. Sharp-sharp ya watsa ruwa, ya ɗauro alwala ya fito sai ta shiga. Ita ma nan da nan ta gama ta shirya cikin kayanta da ta fito da su daga gida ya ja musu jam'in sallar magrib.
Ta so su tafi bayan sun idar da sallah ganin dare yana ƙara nisa ya ce shi yunwa yake ji, dole ta jira yayi musu odar abinci. Hankalinta gaba ɗaya yayi gida shi yasa tsattsakurar abincin kawai ta yi, shi ma ba wani sosai ya ci ba suka harhaɗa kayansu suka fito.
"Me kike so in siya miki?"
Suna hanyar komawa gida yake tambayarta haka.
"Bayan duk waɗannan siyayyar?"
"Eh mana. Za muyi tafiya gobe da Malam, bana so bayan na tafi kafin in dawo ki nemi wani abu."
"Ni dai bani da buƙatar komai. Ina za ku je?"
Tayi tambayar idanunta yana kanshi.
"Bauchi."
Ya amsa a taƙaice.
A ƙofar Ostrich backery ya faka motar ya ce ta jira shi minti biyu. Bai daɗe da shiga ba ya fito hannunshi riƙe da ledoji masu tambarin backery ɗin. Ya shiga ciki ya aje ledojin a kujerun baya na motar, ya ja suka ci gaba da tafiya.
"Amaryar sarkin Bauchi Abdulfah na biyu ƙanwar Hajiya mahaifiyar Malam ce. Ita ce zamu je gaisarwa, gobe zamu yi sammakon tafiya saboda mu isa da wuri kar dare yayi mana a hanya, ni da Malam da Mummy."
"Allah ya kaiku lafiya."
"Ameen ya Allah."
Ya amsa fuskarsa na baiyana jin daɗin addu'ar da tayi musu.
Haka kawai ta ji a ranta tana mararin zuwa bauchin, hannunta ta kai ta dafa hannunshi guda ɗaya kalle ta.
"Bir tanem ko za ku je da ni...?"
"No ki haƙura kawai Tatlim. Tafiyar akwai nisa bana so ki wahala, muma kwana biyu kawai za muyi. Kuma Malam ya ce idan mun dawo weekend na sama za ayi biki ki tare a ɗakinki."
Ya kalle ta da murmushi ya ci gaba da cewa
"Kinga ko a irin wannan lokacin da nake gab da gurzar angwanci duk wani abu da zai jigatar min da ke bazan yadda ya kusanto ki ba."
Dariya suka yi duk su biyun. Haka suka ci gaba da hira cikin nishaɗi da ƙoƙarin fayyacewa juna duk yadda suke ji a zukatansu har suka isa gidan Malam. Bai wani jima ba bayan ya sauke ta ya shiga mata da duk siyayyar da yayi mata cikin gidan. Sama-sama suka yi magana da Malan ya bar gidan da cewa sai ya zo gobe da safe.
****** ******
Kallonta yake yi yana ta doka murmushi har ta ƙarasa kusa da shi ta zube a gabansa, kanta a ƙasa ta fara gaishe shi yana amsa mata a tausashe. A ko wane lokaci idan ya kalleta yana jin wani ƙauna ta musamman a zuciyarsa game da ita, har yau ya rasa gane dalilin da yasa haka. Yadda yake jinta kamar wata ƴarsa da ta fito daga tsatsonsa, balle yanzu da sanadin da zaisa ta ci gaba da dauwama a ƙarƙashin iyalansa ya auku ba ƙaramin murna yake ji ba.
"Bilhaƙƙi an maimaita haddar jiya ko?"
"Eh na maimaita Malam, na iya ma. In biya maka ka ji?"
Ta ƙarasa maganar tana kallonshi da murmushi.
"A'a ki biyawa Umminku. Yau ita za ta ƙara miki karatun. Yanzu wanka zan shiga, akwai tafiyar da za muyi da maigidanki da safennan."
"Bauchi ko? na manta ya faɗa min jiya. Allah ya kaiku lafiya ya dawo mana da ku lafiya."
"Ameen ya Allah. Allah ya miki albarka."
"Ameen."
Harta kai bakin ƙofar falon za ta fita sai kuma ta koma ciki ta zauna a inda ta tashi.
"Malam ko za kuje da ni? Na ji ya ce har da Mummy za ku tafi."
"Kina son zuwa ne Bilhaƙƙi?"
"Eh ina so. Har ma nayi mishi maganar ya ce in haƙura garin akwai nisa."
"Eh da nisa kam."
Shiru yayi kamar shi ma zai ce ta haƙura da son zuwan, sai kuma ya ce.
"Ki shirya tunda kina son zuwa, zan nemar miki izini a wajensa."
Murna kamar me a zuciyarta har ya gaza ɓoyuwa a fuskarta.
"Tam! na gode Malam. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana."
"Ameen."
Ya amsa addu'ar shi ma yana dariya. Da idanu ya raka ta har ta fice daga falon. Girgiza kai kawai yayi ya yunkura da Bismillah ya tashi ya nufi banɗaki don yin wanka.
A can cikin gidan ita ma cike da ɗoki ta faɗawa Ummee da ita za a je, Malam ya ce ta shirya su tafi tare. Wanka ta faɗa cikin ƙanƙanin lokaci ta fito ta fara shiryawa, tana shirin tana harhaɗa kayan sawarta da duk wani abu da ta san za ta buƙata a cikin kwanaki biyun da za su yi. Ganin har da ita za aje Saudat da Asma'u suka ce suma za su Malam ya ce a'a. Sai dariya da gwalo take musu tana tsokanarsu.
Ko da Maheer ya isa gidan ya ganta cikin shiri bai ce mata komai ba, don Malam ya kira shi a waya kafin ya isa yayi mishi maganar. Bai wani so tafiyar da ita ba amma tunda Malam yasa baki ba shi da ta cewa, ko da ta gaishe shi bai nuna mata komai ba ya amsa. A tsaitsaye suka karya sannan suka miƙi hanya bayan sun ja addu'oin da fiyayyen halitta SAW yayi umarnin yi ga duk wani matafiyi. Ita da Mummy suna zaune a kujerun baya na motar, Maheer shi ne direba. Shi kuma Malam yana zaune a kujeran mai zaman banza. Suna barin kaduna an fara miƙar hanya sosai Malam ya kunna radion suna sauraren labarun duniya, jefi-jefi kuma suna hira kan abinda suka ji an taɓo a labarun duniyar.
A wani ƙauye suka tsaya yin sallar azahar da la'asar, suka ci abincin da Mummy ta yi musu guzuri sannan suka sake ɗaukar miƙaƙƙiyar hanyar tafiya, sun fara tafiya ba daɗewa wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Bai fi saura minti talatin su isa cikin garin Bauchi ba ta fara wani irin mummunan mafarki mai cike da ababen tsoro.
"Karki kuskura ki ce za ki shigo cikin garinnan... babu dai-dai da ke a masarauta... Mai wutsiya ki koma inda kika fito ko kuma in hallaka ki..."
Yanƙwanannen tsohon mai ɗauke da jajayen idanu da zaƙo-zaƙon haƙora ne yake mata wannan kashedin yana nuna ta da wani dogon sanda. Ya bugi ƙasa da sandar nan take wasu ƙananun halittu masu kama da kwaɗi suka fara fitowa ta ƙarƙashin ƙasa kusa da inda yake tsaye, ita ya nuna musu da sandar hannunshi yana wasu irin surutai nan take suka yi kanta da gudu kamar tarin ƙudaje saboda yawansu suna yi mata feshin wani abu mai kama da dafi.
Tsananin tsoro da firgici ya sa ta yanka wani ƙaƙƙarfar ihu ta fara cure jikinta a guri ɗaya tana dunƙulewa haɗe da tattakure ƙafafunta a cikin motar, duk yadda ta so ta buɗe idanunta ta kasa buɗewa. Kamar daga sama ta ji muryar Oga yana mata magana a cikin ƙwaƙwalwar kanta.
'Bibi... Karki shiga wancan garin... ki dawo gare mu... har yanzu muna jiran ki dawo gare mu... matsayinki a cikin ƙungiya yana nan yana jiranki... Ki dawo kafin Garkuwa ya saukar miki da mummunan bala'i a kanki...'
Suffar shi ne ya baiyana tsaye a gabanta cikin mummunan shigarsu ta ƙungiyar tsafi yana jifanta da mummunan murmushi. Hannunshi ɗauke da wani ƙaton ƙoƙo da bata san ko miye a ciki ba. ƙananun halittun suna ƙarasawa kusa da ita ya fara watsa musu wani baƙin abu da yake cikin ƙoƙon, duk wanda baƙin abun ya sauka a kan shi sai yayi bindiga ya tarwatse a gurin.
"Ku ƙyale ni... na barku har abada... Yanzu ni matar wani ce...ku ƙyale ni na ce..."
Ta faɗa cikin ƙaraji da murya mai matuƙar amo da sauti, lokacin ne kuma ta samu nasarar buɗe idanunta gaba ɗaya tana kallon Oga fuskarta na baiyana matsanancin fushi.
Wannan tsohon yana ganin Oga ya ɓace daga inda yake tsaye. Wani abin mamaki kuma sai
motar ta fara jijjiga tana layi da su a kan titin kamar za ta kifar da su. Gaba ɗayansu sun shiga cikin ɗimuwa da ruɗewa sai salati suke yi da sallallami tare da jan duk wata addu'a da tazo bakinsu. Duk yadda Maheer ya so ya dakatar da motar ya kasa sai da Malam ya fara janyo karatun alƙur'ani mai girma farkon suratul baƙara, duk su biyun sai suka ɗauki karatun da ƙarfi. A hankali motar ta fara rage gudu da hajijiyar da take yi har ya samu damar faka motar a can gefen titi.
Ihu ta sake ƙwallawa a karo na biyu ta ƙara wage manyan idanunta da suke fari ƙal babu ko ɗigon baƙi a ciki. Oga take gani zaune a gefenta yana ƙoƙarin zuba mata wani farin abu a jikinta. Cikin fushi ta kai mishi wani mugun shaƙa a wuya da hunnunta duk biyu tana magana da murya mai tsananin amo
"Na ce ku ƙyale ni inyi rayuwata ko...? Baza ku barni ba...? Me yasa dole sai da ni a ƙungiyar...?"
Wani kakkaifar walƙiya ne ya fito daga idanunta ya daki jikin Oga nan take shi ma ya ɓace.
Abinda bata sani ba Mummy ta shaƙe wa wuya domin ita Oga take gani, nan da nan Mummy ta fara jiyo ƙamshin barzahu, nan take ta fara kakari, duk yadda take ta ƙoƙarin ɓamɓare hannun Bilhaƙƙi daga wuyanta ta kasa, wani mugun ƙarfi ne ta ke da shi kamar ta shaƙe ta da rodi haka ta ji hannayenta.
Tsakanin Malam da Maheer har rige-rigen zuwa bayan motar suka yi don kai wa Mummy ɗauki kafin ta hallaka ta.
Malam ya fara jan Mummy ganin haka sai Maheer ya fara ƙoƙarin ɓamɓare hannayen Bilhaƙƙi a wuyanta.
A fusace ta ɗago kai za ta yi magana ƙwayoyin idanunsu yana haɗuwa sai tayi laƙwas, jikinta ya saki, ƙarfin nan da take ji duk ya tafi. Lauuu ta yi za ta zube da sauri ya tare ta ta zube a jikinsa.
Malam matarsa ya ja suka koma gaban motar yana ta jera mata sannu, gorar ruwan swan ya ɗauko ya buɗe ya kafa mata a baki. Kaɗan ta sha ta cire goran a bakinta, idanunta jajur, sai haki take yi tana sauke numfashi akai-akai. Inda Allah ya taimake su hanyar babu cunkoson motoci sosai, motoci biyu ne suka tsaya don basu taimakon gaggawa ganin kuma al'amarin yazo da sauƙi sun samu nasarar tsayar da motar ba tare da an samu hatsari ba sai suka yi musu fatan alkhairi da addu'ar kiyaye gaba suka wuce.
"Magajin Malam ka kula da matarka a nan. Ni bari in lallaɓa in tuƙa motar mu isa cikin gari. Kafin mu isa gidan sai mu fara zuwa asibiti a duba su ita da Salamatu."
Plate ɗin karatun Alƙur'ani ya kunna ya buɗe volume sosai sannan yayi addu'a ya zauna a mazaunin direba ya ja motar suka bar gurin.
Tunda ta zube a jikin Maheer bayan wasu daƙiƙu ta fara dawowa cikin hayyacinta. Ƙam ta rirriƙe shi zuciyarta cike da tsoro tana tunanin ababen da ta gaggani su ba a mafarki ba kuma ba a ido biyu ba.
A haka dai har Allah yasa suka isa cikin garin Bauchi lafiya. Za su nemi asibiti Mummy ta ce in dai don ita ne su wuce masauta kawai, ta ji sauƙi. Ita ma Bilhaƙƙi ta ce ba ta buƙatar wani likita, ta ji sauƙi gajiya kawai yake damunta. Don haka kai tsaye suka nufi masautar bauchi fadar mai martaba Sarki Abdulfatahi na biyu.
******* ********
Tana hakimce a kishingiɗe tana zuba mulki a tsakiyar bayi da kuyangin da suke mata hidima kawai ta ji ƙirjinta yayi wani mummunan bugawa. Rabon da tayi irin wannan faɗuwar gaban tun shekaru aru-aru da suka gabata, lokacin da Jakadiya ta zo mata da labarin Safiyya amaryar mai martaba tayi ɓatan wata. Masokiya ce mai tsini kamar mashi ta sake taso mata tun daga tsakiyar ƙwaƙwalwarta ta cake ta har zuwa kan babban ɗan yatsar ƙafarta.
Da saurin gaske ta runtse idanu saboda zafin jiki da na zuciya, nan wani zazzafan gumi ya fara antayo mata daga duk wani kafan gashi na jikinta, duk da A.C har uku ne suke fidda daddaɗan iska daga ko wace kusurwa na tafkeken falon. Ƙarin hutu da mulki kuma wasu bayi har biyu ne tsaye ƙiƙam a kanta kamar dogarai suna yi mata firfita da mafici irin na Sarakai.
Ko da ta yunƙura za ta miƙe zaune sai taji kamar an saka wani nannauyan dutse an danne ta.
'Tauraruwa mai wutsiya...'
Kamar walƙiya wannan tunanin ya gilma a duk wani lungu da saƙo na zuciyarta sai kuma ya ɓace ɓat! A tsorace ta fara waige-waige kamar za ta ganta a gabanta, sai kuma ta sauke idanunta a kan ɗaya daga cikin bayin da suke gurfane a gabanta suna bata daɗaɗan labarai don saka ta cikin nishaɗi.
"Laraba anyi wasu baƙi yanzu a masaurautar nan ne?"
"Baƙi kuma Ranki ya daɗe? Gaskiya ba ni da labarin haka. Sai dai kuma a fita a tattambaya ko wane sassa na gidan nan."
"A je ayi hakan. Daga nan a isarwa da Jakadiya Babba saƙon ina son ganinta da gaggawa."
"An gama Ranki ya daɗe."
Ta tashi da hanzari don cika umarni.
Ko da Jakadiya ta isa ta sake tabbatar mata lallai fa babu wasu baƙi da aka yi da magaribar farin nan.
"Lafiya kuwa Fulani Taka?"
Wani zazzafan huci ta ja ta fesar, ta kalli Jakadiyan a ɗimauce
"Me yasa kika tambaye ni haka Jakadiya?"
"Allah ya huci zuciyar Fulani ni ganinki nayi duk a ɗimauce kamar wacce ta haɗiyi kunama. Yo ba ma ni ba ai duk wanda ya kalle ki a yanayin da kike ciki yanzu kallo ɗaya zai fahimci kina cikin gaggarumin tashin hankali."
Gefe da gefe ta waiga ta tabbatar duk baƙin da ta sallama sun fice daga falon sannan ta sake gwada yunƙurawa ta tashi zaune karo na biyu. Wani abin mamaki gare ta yanzu duk nauyin nan babu lafiya kalau ta zauna. Ta yafito Jakadiyar ta matsa sosai kusa da ita, sai ta fara mata magana cikin raɗa muryarta baiyane da tashin hankali.
"Ta iso Jakadiya. Tauraruwa mai wutsiya ta iso. Wallahi na ji isowarta a jikina kamar yadda Na shuri ya tabbatar min zan ji da zarar ta iso. Amma nayi mamaki, rannan da kika ziyarce shi ba kin ce min ya ce zai hallaka ta kafin ta iso nan ba...?"
"A'a Ranki ya daɗe mantawa dai kika yi. Ce miki nayi ya ce zayyi duk mai yiwuwa ya dakatar ita kafin ta iso. Idan tayi taurin kai ma zai iya hallaka ta in ya samu dama a kanta. Yo tunda kika ji ta iso kila shi ma tafi ƙarfinsa ne. Yanzu dai sai ki san mai yiwuwa daman tun farko ya sanar da ke wannan yaƙin naki ne ke kaɗai."
Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin saƙa da tunanin da yake yi a ransa. Jakadiya ce ta sake katse shirun da cewa
"Ni kam Ranki ya daɗe wai tauraruwar nan mutum ce ko aljana?"
"Nima bani da masaniyar daga wane jinsin halittu ta fito Jakadiya. In kika bibiya ma dabba ce, dan na kwana biyu ina mafarkin gani a tsakiyar dokar jeje ina tiƙar dambe da wata ƙatuwar zakanya."
Ta ƙarasa maganar a sanyaye.
Laraba ce ta ƙwanƙwasa ƙofar ta jira aka bata izinin shiga sannan ta shiga ta zube a gaban duk su biyun.
"Ranki ya daɗe Raliya ce ta iso, ta ce a sanar miki akwai labari da ɗumi-ɗumi."
Jin haka da sauri ta bada umarnin a shigo da ita, daga ita har Jakadiyar fatansu Allah yasa labarin ya shafi zancen da suke son ji na game da Tauraruwa.
"Ranki ya daɗe barka da hutawa. Baƙin Fulani sun iso daga kaduna, maza biyu mata biyu. A halin da ake ciki ma har an kaisu masauki suna hutawa..."
Wani dogon tsaki da ta ja shi ya gwaɓarwa da Raliyan gwuiyawu. Ta fara magana cikin fushi.
"Saboda ke dabba ce wannan ne wani labari mai muhimmanci da har za ki raɗa mishi da ɗumi-ɗumi? maza ki koma bakin aikinki karki sake zuwar min da banzan labari irin wannan."
"Tuba nake Ranki ya daɗe, godiya nake. Allah ya huci zuciyarki."
A sace ta fice daga falon cikin sauri tana haɗa hanya.
Jakadiya ta buɗe baki za tayi magana da sauri ta ɗaga mata hannu alamar ta dakata.
"Jakadiya bana son jin komai daga gare ki. Je ki sai na neme ki."
BILHAƘƘI
A fakaice ta kyaɓe baki, alamun ko a jikinta. Ciki-ciki ta yi magana.
"Shi ke nan! Allah ya huci zuciyarki mai babban ɗaki ta gobe a masaurautar Bauchi, ki huta lafiya."
"Jakadiya?"
Ta kira sunanta a lokacin har ta kai bakin ƙofa za ta fita.
Waiwayowa kawai ta yi ba tare da ta dawo ba ta amsa kiran
"Na'am Ranki ya daɗe."
"A nema min ison ganawa da Mai martaba a gurin mai Soron baƙi. Yanzu!"
"To Ranki ya daɗe. Angama!"
Tana hanyar zuwa gurin mai soron baƙi take dariya a zuciyarta.
'Lallai al'amarin mai wutsiya ba ƙaramin girgiza Sarauniya yayi ba. Da da ne yadda ta amsa kiran nan daga ƙofa kuma ta tsaya ƙiƙam a gurin bata koma ta zube a gabanta ba ƙaramin masifa za ta sha akan hakan ba. A hakan ma don dai Jakadiyar ce da a ɗaya daga cikin bayi ne tayi hakan sai tasa an hukunta ta. A ƙalla ta karɓi hukuncin zafafan bulalai talatin. Amsa kira daga tsaye ba tare da zubewa a ƙasa ba babban alama ce ta raini da fitsara ga duk wanda/wacce aka yiwa a Masautar.'
Tana wannan tunanin har ta ƙarasa ɓangaren Mai soron baƙi da yake kusa da ɓangaren Mai martaba. Ƙara shiga cikin nutsuwarta tayi bayan ta nemi iso a ɓangaren an yi mata umarnin shiga.
Tana shiga ta zube a gabanta cike da ladabi ta fara zuba mata kirari. Ita kuwa Mai soron baƙi babbar mace hakima tana zaune ta mimmiƙe ƙafafunta aka lallausan kafet ɗin da ya malaye tsakar ɗakin tana ta sakin murmushi, kanta sai ƙara kumbura yake yi da jin irin kirari da yabon da Jakadiya take jera mata.
"Ranki ya daɗe. Barka da dare, sannu da hutawa. Allah ya ja zamanin tsani kuma ja gaba wajen neman izinin ganin Takawa. Sai kin so ake ganinshi idan baki so ba duk masarautar nan babu wanda ya isa ya ga Takawa. Allah ya ƙara wa Takawa lafiya da nisan kwana."
"Ameen ya Rahmanu. Jakadiya? Me ke tafe da ke a daren nan?"
Ta jefa mata tambayar har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba.
"Ranki ya daɗe Fulani Taka ce ta turo ni in faɗa miki tana neman iso za ta gana da Mai martaba akan wani muhimmin al'amari yanzu..."
"A sanar da ita bazai yiwu ba Jakadiya. Yau ba ita ce da Mai martaba ba, a bayan haka ma Takawa yana da manyan baƙin da zai gana da su a darennan daga Birnin kaduna."
Ta katse ta tun kafin ta ƙarasa aje numfashin maganarta.
A sace Jakadiya ta ɗaga kai ta kalle ta sai taga wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta, fuskarta ɗaure tamau. Cike da mamaki tayi mata sallama ta fice daga gurinta ta nufi gurin Sarauniya don isar mata da saƙo, tunani take ta yi a zuciyarta.
'Ta rasa dalilin da yasa tsakanin Mai soron baƙi da Fulani Taka sam basa ga maciji. Abinda ta lura da shi kamar duk sun zamewa juna dole ne, ga ko wannensu sun zama ƙadangarun bakin tulu. Ita Sarauniya Safara'u uwargidan Sarki ce. Ita kuwa Mai Soron baƙi Inna Laminde ƙanwar gyatumar Mai martaba ce. Tana tsananin ƙaunar Takawa tana ƙaunar duk abinda yake so, ita da kanta ta nemi ya bata wannan muƙamin yadda duk wani abu da zai isa gurin Takawa sai ya fara isa gurinta ta tantance tsaftarsa da halaccinsa saboda gudun a kai mishi abinda zai cutar da shi. Hatta matansa biyu sai sun bi ta gurinta suke samun isa gare shi ko da kuwa ranar girkin mace ne. Ta matsa lamba sosai a masarautar, ta tare gaba ta tare baya. Jajurtacciya ce kuma tsayayyiyar mace da sam bata ɗaukar wargi ko raini ga kowa a masarautar. Wani abin mamaki a yanzu Mai Soron baƙi tana tsananin ƙaunar Safiyya da duk abinda ya shafe ta, saɓanin da da tafi ƙaunar Safara'u akan Safiyya.'
"Ina ga akwai wani ƙwaƙƙwaran dalili da ya juyar da akalar wannan ƙauna da ƙiyayyar, ko ma menene dai ma ji ma gani."
Tayi maganar a fili da murya ƙasa-ƙasa tana murmushi.
A hanya ta ci karo da Sarauniya Safiyya tare da baƙinta biyu (Mummy da Bilhaƙƙi) bayi da kuyangi suna take musu baya. Da alamun kai tsaye ɓangaren gurin Mai martaba suka nufa.
Har ƙasa ta zube cike da ladabi da girmamawa ta fara kwasar gaisuwa ga Sarauniya. A mutunce ta amsa mata suka wuce zuwa inda suka nufa, sai da suka ɓacewa ganinta sannan ta daina kallonsu ta nufi ɓangaren Fulani Taka cikin sauri kamar za ta kifa.
"Inji ita Mai soron baƙin ne ta ce a faɗa min yau ba kwana na bane?"
Ta sake maimaita tambayar cikin tsananin fushi.
"Ƙwarai kuwa Ranki ya daɗe. Ta ce yana da manyan baƙi kuma ni da idanuna naga Fulani da baƙinta mata biyu sun nufi ɓangarensa. Kinga ke nan su ne manyan baƙin."
Ƙwafa tayi, ta cije gefen bakinta na dama alamun mugunta, ta ci gaba da ƙanƙance idanu cike da masifa.
"Safiyya da wasu banzayen baƙinta har sun isa su fini muƙamin ganawa da Takawa?"
"E to ga zahiri kin gani? ai ke kuma kin saka ƙafa a jarka tunda kika yi saken da mai wutsiya ta shigo masautar nan."
Jakadiya ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda baza ta abinda ta ce ba.
"Magana kike Jakadiya?"
"A'a cewa nayi Allah ya huci zuciyarki. Amma fa ke kika yi saken da Mai soron baƙi take kawo miki wargi."
"Gaskiya kika faɗa Jakadiya. Bari inje da kaina in gani idan ta isa ta hana ni shiga gurin Takawa in gani."
Ta miƙe a fusace za ta fita da sauri Jakadiya ta dakatar da ita.
Ta rage murya ƙasa-ƙasa ta ce
"Ranki ya daɗe a halin da ake ciki faɗa ko tayar da jijiyar wuya ba naki bane. Ki kawo sulallan gwal a kaita gurin Na shuri ya cika mata aiki kawai."
"Shi kenan Jakadiya. Ya kamata saisaita mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 25