Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah. Mai soron baƙi da ta kai albishir ɗin haihuwar jariran kyautar Raƙumi da doki aka yi mata. Malam da iyalansa kuwa anyi musu kyaututtuka na ban girma, ciki har da wani tamfatsetsen gida na Mai martaba da yake cikin garin kaduna. An ƴanta bayi talatin da biyu a cikin gidan. A wannan ranar dai duk wanda yake cikin masarautar zai shaida wannan gaggarumin abin farin ciki da ake ciki. Masu girke sai dafe-dafe suke yi kala-kala ana sadakar da shi. A wannan ranar ko zaman fada cikin farin ciki da walwala Takawa yake yinsa. Jariran har fada an fitar da su naɗe a gadajensu na jarirai, Hakimai, Galadima, Wambai da duk sauran masu mukami a masarautan sai leƙa fuskokinsu suke yi ana saka musu albarka. Da yamma lis ana gaf da tashi daga zaman fada wani firgitaccen labari da ya firgita duk wani mai rai da ke cikin fadar ya isa kunnensu. Wai ga wani tsohon bafullatani nan da wani matashin dattijo da ya ce shi ne Mustapha ɗan Sarki Abdulfatah. Kafin a ce kwabo Sarki ya bada umarnin ayi gaggawar isa da su cikin fadar don ya ganewa idonsa shin da gaske ne ko ƙarya ne mahassadansa suka yi mishi ture? Don yana da tabbacin in dai Mustapha ɗansa ne duk tsawon shekaru ko da komai na jikinsa ya canza akwai abubuwa da dama da zai iya gane shi da su. "Hattara Matashin dattijo! Nutsu!! shiga cikin taitayinka!!! Gaban Sarkin duniya kake Abdulfatahi na biyu wanda sam baya ɗaukar wargi." Wani Bafade ne ya dakawa Mustapha tsawa ganin yadda ake janshi yana ta turje-turje. Jin an ce a gaban mahaifinshi yake ya sa shi ya ɗaga idanunshi da suke ciccike da hawaye ya zuba a kan fuskar Takawa. Nan take sai hawayen suka gangaro shar... bisa kuncinsa don tsananin ƙunci, kewa, damuwar rashin ahalinsa na tsawon shekarun da bashi da tabbacin iyakarsu. "Abbbuu... bar...ka... da... yamma..." Ya faɗa a rarrabe bakinshi na rawa. Tsam Takawa ya miƙe tsaye daga kan karagar mulkinsa yana nuna Mustapha da ɗan yatsarsa manuniya. 'Tabbas duk da cika da alamun girma da muryar ta ƙara bazai taɓa manta muryar Shalelen ɗansa Mustapha ba. Muryar da ko da basa tare tsawon shekaru kusan kullum sai yayi mafarkinsa yana ce mishi duk daren daɗewa zai koma gare su.? Ta ya zai kasa tantance muryar masoyinsa?' Yana wannan tunanin har ya ƙarasa kusa da Mustapha ya cire hannunsa daga cikin alkyabbar jikinsa ya kama fuskarsa ya ɗaga ya ƙura mishi ido. Har lokacin hawayen idanun Mustapha basu daina zuba ba. Ya saki fuskar ya kamo hannunsa na dama ya ja hannun rigarsa har saman damtsensa. Wani ƙaton tawadar Allah ce da girma yasa ita ma ta ƙara buɗewa a damtsen hannun, yasa yatsarsa ya murje da ƙarfi ta ƙi goguwa. Zuwa wannan lokacin jikin Takawa ya fara kyarma, a hankali ya kama rigar jikin Mustaphan da niyyar cire mishi ita, ganin yadda jikinsa ke rawa yasa Mustaphan ya ƙarasa zare rigar da kansa. Sai ga wannan tambarin na ƙirjinsa wanda alama ce da ake yiwa duk wani jinin sarautar gidan da zai iya hawa karagar mulki. Taga-taga Sarki ya tafi zai faɗi da saurin gaske su Liman da waziri suka tare shi kafin ya kai ƙasa. "Mustapha na ne. Tabbas shi ne wannan..." Kafin ya ƙarasa jijiyoyin sadar da saƙonnin jikinsa suka tsaya ƙyam, ya suma a jikinsu. ******** ******** Zuwa dare gaggarumin abin farin-cikin da ya ƙara samuwa yayi tambari a duk wani lungu da saƙo na cikin garin Bauchi. "Babban ɗan Mai martaba Sarki Abdulfatahi na biyu Yarima Mustapha ya koma gida yau bayan ɓatarsa da shekaru ashirin da takwas." Wannan babban labari ne kuma abin farin ciki ne da ya jijjiga duk wani mai rai da yake rayuwa a cikin garin Bauchi da kewayenta. Ƙawayen masarautar ma sai kiraye-kiraye suke yi suna taya masautar murna. Ga Takawa, Sarauniya Safiyya, Uwar soro, mai babban ɗaki, Mal Abdulganiyyu da iyalansa na barwa masu karatu ku kwatantawa kanku irin kogin farin-cikin da aka tsunduma su a ciki🤣🥰👌🏽. Ƙarfe goma da rabi na dare Mustapha da Yalleru sun gama samun nutsuwa, sunci lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Mustapha yayi wanka ya shirya cikin kaya na alfarma da sarauta. Kasa haƙuri iyayen suka yi suka kulle kansu a turakar Mai martaba aka tasa Mustapha da Baffa Yalleru a gaba yana basu labarin irin gararambar rayuwar da yayi a cikin duniya. Masu saurin kuka a cikin ɗakin sai sharar hawaye suke yi. Tun bayan bayyanar labarin dawowar ɓataccen ɗan Sarki take jinta a cikin wani irin yanayi na faɗuwar gaba da sanyin jiki. Duk da bata samu ganin baƙon ba amma yadda ta ga Sarauniya tana ta murna da kuka tana godiya ga Allah da ya dawo musu da shi yasa ta tabbatar ba ƙaramin ƙauna suke yiwa Mustaphan ba. Shiru tayi a kan gado tana saƙe-saƙe da tunani. Mummy yau da wuri tayi bacci saboda gajiya, don yini suka yi zurga-zurga da hidiman jarirai, tunda ba kowa ake yarda ya ɗauke su saboda gudun abinda ka je ya zo na sharrin mutane. Wani matsanancin kewar Sevgilim ɗinta ne yake ta taso mata tana dannewa. Tun jiya da suka iso gidan bata sake haɗuwa da shi ba sai dai suyi magana ta waya. Da wannan tunanin yasa ta lalubo wayarta a jaka da nufin kiranshi sai ta ga an tura mata saƙonni biyu a fuskar wayar. Ko da ta buɗe saƙonnin ɗaya daga gurinshi ne, ɗayan kuma daga wani baƙon lamba ne da bata san ko ta waye ba. Saƙonshi ta fara buɗewa, zaƙaƙan kalamai ne yana faɗa mata yadda yake tsanani sonta da yadda yake kewarta, har yana ƙorafin shi fa shi yasa a rayuwarsa sam baya son harkar al'amarin gidan sarauta. Ace kai da iyalinka ba halin ku sake kuga juna a lokacin da kuke so? Da yadda ya ƙosa su koma gida a yi bikinsu ta tare a kusa da shi. Yalwataccen murmushin jin daɗi ne kwance a fuskarta, har za ta danna kiranshi sai kuma ta yanke shawarar fara duba ɗayan saƙon da aka tura mata, dan haka ta buɗe. Sunan da ta gani ne da abinda saƙon ya ƙunsa yasa ƙirjinta yayi wani mugun bugawa, kayan cikinta suka cure guri guda. "Bibi. Madam Mary ce. Duba whatsapp ɗinki ki ga wani babban abin mamaki da na tura miki." Da sauri ta wuce saƙon ta shiga whatsapp ɗin da kwata-kwata kwananta huɗu ne da buɗewa. Duk hange da tunaninta ya tafi ne ga tuhumar a ina Madam ta samu sabon lambar wayarta? Saƙon vidio ne Madam ɗin ta tura mata. Kafin ya buɗe sai jan tsaki take yi ƙasa-ƙasa cike da ƙosawa da son ganin abinda vidion ya ƙunsa. Yana buɗewa ta fara cin karo da fuskar wata tsohuwar mace, tana zaune cikin mawuyacin hali. An ɗaure ta tamau a jikin kujera, kanta fari fat! furfura ce ko wahala ce oho. Wani hannu da bata san ko na waye ba ya damƙi gashin kan matar aka ɗaga fuskarta yadda mai kallon vidion zai iya ganinta sosai. Sautin muryar Madam da ta ji ya biyo bayan ɗaga fuskar yasa ta miƙe tsaye a zabure, hankalinta a tashe, tsananin tashin hankali yasa idanunta ya fara canza launi daga fari da baƙi zuwa ja da kore "Bibi kinga wannan matar? ita ce Mahaifiyarki Rebeccah. Tsawon shekaru goma sha tara tayi a kulle a Coci ana gana mata azaba. Yau mun je mun ƙwato ta a hannun waɗancan da suke tsare da ita, idan kin damu da ita kina son ganinta a raye ki miƙo kanki gare mu, ki dawo cikin ƙungiya ki karɓi muƙaminki. Idan kika yi haka mu kuma munyi miki alƙawarin za mu sake ta lafiya ba tare da wani abu ya faru da ita ba. Kuma kafin ki taho ki tabbatar kin kashe wannan ɗan iskan auren da kika yi, domin a muƙaminki na ƙungiya sam babu aure a rayuwarki." Sai ta sake fashewa da dariya mai tsananin ƙarfi tana ta ƙyaƙyatawa har zuwa ƙarshen vidion. Tsigar jikinta ne ya fara wani irin mimmiƙewa kamar ƙayoyi don tsananin tashin hankali, bata san lokacin da hannunta ya danna amsa kiran wayar da Mustapha yai mata ba sai muryarsa kawai ta ji yana ta "Hello... helloo... Tatlim kina ji na?" "Ka fito yanzun nan ina so mu haɗu." Tayi maganar da wani irin murya da a can ɓangarensa sai da ya cire wayar a kunnensa ya sake kallon sunan da tunanin ko dai ba ita ya kira ba? ganin tabbas sunanta ne kuma lambarta ce yasa ya miƙe zaune da sauri, da jin muryar nan ya tabbatar ba lafiya take ba. Kamar walƙiya tunanin abinda ya faru da ita jiya a hanyarsu ta zuwa ya faɗo masa a rai. "La haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyul azeem. Tatlim kiyi ta maimaitawa gani nan zuwa, ki fito mu haɗu yanzu. La haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyul azeem." Haka yayi ta maimaitawa a wayar tun yana jinta shiru bata amsa shi har ya ji ita ma tana maimaitawa, cikin sauri ya zura rigarsa wayar na maƙale a kunnensa ya fice daga ɓangaren baƙin da aka sauke su. Kai tsaye cikin gidan ya nufa hanyar da zai sada shi da ɓangaren Sarauniya Safiyya. Saboda dare da ya fara yi don lokacin sha ɗaya ta gota jefi-jefi yake haɗuwa da bayi har yayi kiciɓus da ita a hanya, da sanyin jiki take tafe kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Hannunta ya ja da mugun sauri suka koma inda ya fito. Suna shiga cikin ɗakin ya maida ƙofar ya rufe, sannan ya janyo ta tsam ya rungume a ƙirjinsa yana tottofeta da duk wata addu'a da ta zo bakinshi. Ita kuwa sai ƙara riƙe shi take yi a tsorace tana ta sassauke ajiyar zuciya mai nauyi sauri-sauri. Sai da yaga ta ɗan samu nutsuwa ya riƙe ta a jikinsa suka zauna a gefen gadon, sannan ya ɗago fuskarta a tausashe ya fara tambayarta abinda ya ɗaga mata hankali. "Tatlim! kinsan bana son damuwarki ko? Ummm?! Faɗa min! Wa ya taɓa min ke? Menene abinda ya ɗaga miki hankali?" Sai a lokacin ta ji wani ƙaƙƙarfan kuka ya taho mata, karo na biyu ta sake kwantar da kanta a ƙirjinsa ta fara rera kukan a nutse kamar karatu. Shi kuwa bai katse ta ba sai shafa bayanta yake yi yana ɗan bubbuga ta alamar rarrashi har saida ta samu nutsuwa don kanta ta ɗago tana kallonsa ta fara magana a muryarta baiyane ƙarara da tashin hankali. "Sevgilim! Sun kama Mahaifiyata... ashe duk wannan gararambar da nake yi a duniya mahaifiyar da ta haifeni tana raye a can tsare a hannun wasu azzaluman mutane. Yanzu su Oga sun kamo ta, sun ce in dai ban koma cikinsu ba za su kashe min ita. Sevgilim ita Ummata ce wacce ta tsugunna ta haife ni, ya zama dole in miƙa musu tawa rayuwar don in cece tata rayuwar. Duk da ban taɓa ganinta a ido biyu ba na ji a raina ina tsananin son ta, sun faɗa min shekarunta goma sha tara tana cikin uƙuba a hannun waɗancan mutanen. Don tabbatuwar cika ta ƴar halas ya zama dole in zame mata silar jin daɗi. Ko bayan ba raina kai da Malam dan Allah ku riƙe min ita Sevgilim, ka jiyar da ita daɗin duniyan da ta daɗe ba ta ji ba. Idan kayi min haka ka gama min komai Masoyi." A karo na uku ta sake kwantar da kanta a ƙirjinsa wasu zafafan hawaye suna tsiyaya daga idanunta. BILHAƘƘI Shiru yayi yana saƙe-saƙe da jujjuya maganganunta. Kamar ya fahimta amma kuma bai gama fahimtar inda maganganunta suka dosa ba. Har sai da ya tambaye ta "Babe nutsu pls, ta ina ne suka faɗa miki sun kamo Mahaifiyarki?" Wayarta ta nuna mishi da take yashe a can gefen gadon. Zai tashi ya ɗauko ta hana shi ta hanyar sake ƙanƙame shi. Dole ya koma ya zauna ya ci gaba da shafa bayanta. Tsawon lokaci suna a wannan yanayin har yaji yanayin saukar numfashinta ya canza, alamun ta samu barci. Bai yi ƙwaƙƙwaran motsi ba sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sosai, ya zame jikinsa a hankali ya kwantar da ita a kan gadon, ya zare hijabin jikinta ya gyara mata kwanciyar sannan ya ɗauki wayar ya matsa can gefe ya fara dudduba saƙonnin cikin wayar. Dukda yana namiji al'amarin ya jijjiga shi, tsawon lokaci yana ta saƙe-saƙe da tunanin hanyar da zai bi ya taimake ta amma ya rasa na yi. Sai jan Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un yake yi. Vidion ya sake kunnawa ya kure fuskar matar sosai da kallo, tabbas tana tsananin kama da Bilhaƙƙi. Babu tantama wannan matar ko ba mahaifiyarta ba ce to tabbas sun haɗa dangantaka ta jini a tsakaninsu. Kamannin yayi yawa. Aje wayar yayi ya yakice tunanin komai a ransa ya shige banɗaki ya ɗauro alwala, nafilfili yayi ya haɗa da addu'o'i sosai a kan Allah ya kawo musu mafita da gaggawa. Cikin hukunci na Ubangiji kuwa bai tashi a kan sallayar ba sai da yaji zuciyarsa ta tsayar mishi da ƙwaƙƙwaran shawara na hanyar da ya kamata su bi. Hamdala yayi ta yi yana godiya ga Allah har ya tashi ya ɗauko wayarsa. Ƙaninsa Luƙman mai bi masa a haihuwa ya kira ya warware masa duk abinda yake faruwa. Maganganu mai tsawo suka yi sannan suka yi sallama kowa ya katse wayar. Fita yayi ya ja ƙofar ya kulle ta waje, ya nufi ɗakin da Malam ya kwana jiya wanda yake kusa da nasa ɗakin dan ya ga ko Malam ɗin ya dawo daga turakar Takawa inda suke ganawa. Sai ya iske ya dawo sallah ma yake yi. Ganin haka sai ya nemi guri ya zauna yana jiran ya idar da sallar. "Magajin Malam? lafiya a darennan? Na yi tsammanin tuntuni ka yi barci?" Tambayoyin da Malam ɗin ya fara jera mishi kenan bayan ya idar da sallar. "Lafiya ƙalau Malam. Barka da dare." "Yauwa barkanmu dai Magaji. Me yake faruwa?" Ya sake tambayarshi cikin zaƙuwa, dan ya ga alamun maganganu ne a bakin Maheer ɗin. "Malam daman kira ne mai muhimmanci aka yi min daga gurin aikinmu. Sun buƙaci lallai idan zai yiwu in koma kaduna gobe. Shi yasa daman na zo inji yaushe ne ka shirya za mu koma gida?" "Eh to nima da a niyyata mu koma gida gobe ko don saboda aikin naka. Amma a darennan Mai martaba ya zo min da buƙatar da bazan iya musa mishi ba. Ya ce akwai muhimmin al'amari dangane da Yarima Mustapha da zai kaisu can wani ƙauye a jihar kaduna. Ya buƙaci ko zan koma gida in bari muyi wannan tafiyar mu dawo, in yaso ma ni sai in tsaya a kaduna idan sun gama su sai su dawo nan ɗin." Shiru suka yi duk suna saƙe-saƙe, sai Malam ɗin ya ci gaba da cewa "Ina ga abinda za a yi gobe idan Allah ya kaimu kai ka koma gurin aikinka. Ni sai na iso kawai. Daman tun kafin bayyanar Mustapha Innah ta buƙaci in bar Salamatu da Bilhaƙƙi a nan har sai bayan an gama shagalin suna sai su bi tawagar masu zuwa daga maru su sauka a kaduna. Idan duk hakanma bai yiwu ba za ta sa a mayar da su har gida." Da 'To' kawai ya amsawa Malam wacce bahaushe yake kira da ba ta karya wuya. Amma ya san tafiyarshi ya bar Bilhaƙƙi a nan ko da lafiya ƙalau ne ba abinda ke faruwa ba abu ne da zai iya jurewa ba. Balle kuma ga gaggarumin tashin hankalin da ya ɓullo musu. Ya san ko ya hana Bilhaƙƙi tafiya ga mahaifiyarta tabbas za ta tafi, shi yasa da ta bi motar haya ba tare da saninsa ba gara shi ya kaita da kanshi. Ya zaɓi ya ɓoyewa Malam gaskiyar halin da ake ciki ne saboda ya san yana iya shiga cikin matsanancin tashin hankali da damuwa. Sallama yayi mishi da fatan tashi lafiya bayan ya sanar da shi gobe ana idar da sallar asubah zai ɗauki hanya. Ya fice daga ɗakin ya koma ɗakinsa gurinta. Ya tarar da ita har lokacin tana barci, shirin bacci yayi ya hau gadon ya janyota jikinsa ya rungume, yayi musu addu'ar barci gaba ɗaya ya shafe musu jiki ya ja musu bargo. A wannan ranar nan gurinsa ta kwana, kiran sallar farko ya tashe ta tayi wanka. Tana fitowa shi ma ya shiga ko kafin ya fito har ta maida kayan jikinta, har lokacin fuskarta danƙare take da damuwa. Shi ma bai yi ƙoƙarin damunta ba saboda ya san lamarin babu sauƙi, addu'a ya umarci tayi sosai idan ta idar da sallah sannan ya fice zuwa masallaci. Ana idar da sallah kafin jama'a su fara fitowa ya fice daga masallacin, sauri-sauri ya kira ta ta shige motar ya ja a sukwane suka fice daga gidan. Suna hawa titi ya ƙure ƙarar karatun alƙur'ani mai girma ƙira'ar Sudais. Sosai yake ba motar wuta duk da nisan tafiyar so yake su isa kaduna a cikin taƙaitaccen lokaci. ****** ******* Duk zamanta a gidan baifi a ƙirga ba da ta taɓa haɗuwa da shi, tunda shi ba mazaunin jihar kaduna bane. Tsananin ƙwazo da himmar aiki haɗe da tsage gaskiya yasa a cikin ƙananun shekarunsa aka ba shi muƙamin D.P.O na ƴan sanda. Shi yasa yau a cilla shi wannan jihar gobe a cilla shi wancan jihar don share tsagerun da suka addabi garuruwa. Bai fi sati biyu ba baya da aka yi mishi transfer zuwa jiharshi ta kaduna, yana tsaka da aiki Maheer ya kira shi yana faɗa mishi wannan sarƙaƙƙen al'amarin na Bilhaƙƙi. Shi ya bada shawarar duk yadda ya kamata suyi kuma Maheer ya gamsu ɗari bisa ɗari. A karo na barkatai ya sake kallonta da manyan idanunsa, shi mamaki ma yake yi ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar ita da babban al'amari. Da gaske in banda Yayanshi ne ya tare shi da case ɗin kai tsaye zai ƙaryata duk wanda ya faɗa mishi labarinta. "Amma ƙanwata kina ga mu barki ki tafi gurinsu ke ɗaya shi ne abinda ya fi? Ko dai in haɗa ki da jami'an da zasu taimaka miki a tarwatsa ƙungiyar..." "A'a! A'a Ya Luƙman. Dan Allah kar kayi haka." Ta katse shi da sauri jikinta na rawa, sai kuma hawaye shar... ta ci gaba da magana cikin kuka "Wallahi ba imani ne da su ba idan aka bi bayana na tabbata za su iya kashe min mahaifiyata. Idan kuwa hakan ta faru bazan taɓa yafewa kaina ba." Ɗage kafaɗa yayi alamun shi kenan tunda hakan ta zaɓa, ya sake tura kwalin lemun exotic da kofi a gabanta. Kisha kafin Yayan ya dawo sai ku wuce..." Buɗe ƙofar da aka yi tare da shigowar Maheer yasa shi yayi shiru, kallon juna suka yi, Maheer yayi wa Lukman wani alama da ido da na rasa gane ko me yake nufi. Gyaɗa kai yayi tare da ce masa "Ka dawo?" "Eh na dawo." Ya ajiye wani leda a gabanta ya ɗago haɓarta da hannunsa yana kallonta cikin ido. Kujera ya janyo ya zauna a kusa da ita har gwuiwoyinsu na gogar na juna "Babe kukan ne har yanzu?" Kafin ta yi magana Luƙman ya ce "Ina ga idan ta sha lemun za ku iya wucewa. Ta ce bata buƙatar mu bi ta, za ta iya zuwa ita kaɗai." Yana gama maganar ya fice daga Ofis ɗin sannan ya ja musu ƙofar. Hannayenta ya rirriƙe duk biyun fuskarsa baibaye da damuwa "Kin tabbata barinki ki tafi ke kaɗai shi zai sa su sake ta lafiya ba tare da sun cutar da ita ba?" Ɗaga mishi kai kawai ta yi alamun eh! "Babe kiyi min alƙawarin kema za ki dawo gare ni, wallahi ina tsananin sonki. Bazan iya rayuwa idan baki a kusa da ni ba." "Gaskiya banyi maka alƙawari ba Sevglim. Amma zanyi ƙoƙarin dawowa idan na samu dama in Allah ya yarda." Ta amsa tana ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ma kanta gwuiwa. Janyo ta jikinsa yayi ya riƙe ta tsam a ƙirjinsa, sai sassauke ajiyar zuciya suke yi a tare, tsawon lokaci sannan ya kai hannu ya buɗe kwalin lemun ya tsiyaya a kofi. Ya ɗauko kofin ya nufo bakinta da shi, kauda kai ta yi, murya ƙasa-ƙasa ta ce "Bana jin zan iya shan wani abu yanzu." Shiru yayi bai amsa ta ba, ko da ta kalli fuskarsa sai ta ga yanayinsa ya canza, kamar bai ji daɗin ƙin shan da tayi ba. Kawai sai ta karɓi kofin ta kafa a baki ta fara sha, saboda sanyinshi yasa ta shanye gaba ɗaya ta aje kofin a kan tebur. Ajiyar zuciyar da ya sauke yasa ta kalle shi, sai ya sakar mata murmushi kaɗan. Miƙewa tayi daga jikinshi "Ya kamata in tafi, lokaci yana ƙara tafiya." "Tam! Ɗan jira ni minti biyu bari inga Luƙman a waje." Ko kafin ta amsa har ya fice daga ofis ɗin. Minti biyu, huɗu bai dawo ba, nauyin da ta ji kanta yayi mata yasa ta ɗan kifa kai a kan tebur ɗin kafin ya dawo. Nan fa wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita. Minti takwas yayi da fita sannan ya koma cikin Ofis ɗin, ganin ta yi barci yasa shi sakin murmushi ya koma ya sanar da Luƙman, sannan ya kira Dr. Bilyaminu da yake zaune a wani ɗan ƙaramin Ofis suka koma ofishin Luƙman duk su ukun. ******** ******** "Madam ! kamar yadda na sanar da ku a shirye nake in koma cikin ƙungiya dan in cece rayuwar Mahaifiyata. Lokacin yayi, ga ni yanzu na fito daga gidan Malam. A ina zamu haɗu...?" "Ki rufe min baki Bibi!" Ta daka mata tsawa daga can ɓangaren, cikin masifa ta ci gaba da cewa "Me kika maida ni? Wacce ba ta da wayau ko me? karki manta duk iskancinki da wayon da kike ganin kina da shi a ƙarƙashi na kike. Ko kin manta kina ƴar ƙanƙanuwar yarinya na tsince ki? Ki ajiye wayar hannunki da duk wani abu da kike riƙe da shi a ƙofar gidan ki hawo titi ki ci gaba da tafiya kawai." Wani dogon tsaki ta ja sannan ta katse wayar. Daman wayar ce kawai a hannunta, jikinta a sanyaye ta aje wayar a ƙofar gidan ta ci gaba da tafiya cikin sauri tana waige-waige. Ko da ta isa kan titin tsayawa tayi tana tunani don bata san ina ya kamata ta bi ba. Gabas ko yamma, kudu ko arewa? kawai sai tayi shahadar ƙuda ta miƙe titin yamma samɓal tana ta tafiya. Ta jigata ƙwarai, domin ta shafe minti arba'in tana tafe da sassarfa kafin wata baƙar mota ta ci burki mai ƙarfi a gefenta, ko kafin ta waiwaya ta gama gane kalar motan an buɗe ƙofar da sauri aka fincike ta zuwa cikin motar, aka ƙara figar motar a guje aka harba titi. Basu barta ta gama nutsuwa daga firgitan janye ta da suka yi ba aka shaƙa mata wani hoda a hancinta. Daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba har suka isa wani babban gida a sabon tasha. Wani ƙato a cikinsu ne ya saɓa ta a kafaɗa kamar ya ɗauki sillan kara ya shige gidan da ita, wani ɗaki ya kaita ya shimfiɗar a kan gado. Minti biyu tsakani wasu ƴan mata biyu suka shiga ɗakin suka caje ta gaba ɗaya bayan sun cire kayan jikinta tas! ɗaya daga cikinsu ce ta kira Madam a waya ta yi mata bayani "Madam! babu komai a jikinta. Sosai mun duba ta ko ina a jikinta bamu samu komai ba." "Ok! ku saka mata kayan nan da na ba Moses ya kawo muku." "Ok ma!" Wani doguwar riga shuɗi suka saka mata a jikinta saɓanin riga da zane na atamfar da suka cire mata. Suka ɗaure gashin kanta da wani jan ƙyalle mai ɗan faɗi. Garjejen ƙaton

Chapter 20 of 25