Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya shanye zafin ya girgije ta ƙara mishi wani marin a ɓangaren dama. Tsananin tsoro da ruɗanin ganin mara-maran da aka saukewa Yarima dukda girman matsayinsa yasa Murja ta ƙara fashewa da kuka, zuciyarta cike da tunanin ita kuma wannan yarinyar wa ce mai girman matsayin ne har ta iya marin Yarima? "Yi haƙuri. Sam ba ni da nufin cutar da ke. faɗa min me yake faruwa kin ji?" Ta tambaye ta a tausashe, bayan ta saka hannuwanta biyu ta miƙar da ita tsaye. "Dan Allah ki yi hakuri ki yi min rai. Wallahi babu ruwana, shi ne yake takura min in zo turakarsa. Yau kuma na faɗa mishi ba ni da lafiya amma ya ƙi yarda..." Zazzafan marin da Yarima Muzaffar ya sauke mata a kunci yasa ta hantsila baya saboda azaba, ta sake fashewa da kuka tana yi tana toshe bakinta dan kar a ji daga nesa. Yayi wani mummunar dariya yana kallonta sama da ƙasa, miyau ya dalalo mishi a baki yasa hannu ya goge. Ƙofar ɗakin ya maida ya datse har da yana saka key. "Ni kika yi kuskuren mari ko? Wallahi sai na yagalgala ki a darennan inga uban da ya tsaya miki a garinnan. Yau za ki san ko wanene Yarima Muzaffar mai jiran gado..." Cikin tsananin fushi da ƙyama ta nuna shi da yatsarta manuniya ta ce! "Au! Akuya kai ne Yarima mai jiran gado a masarautarnan? Madallah! Ni kuma ina yi maka albishir ɗin mummunan tonuwar asirin abinda kake aikatawa akan bayin gidannan. Kai daga yau ma matukar ina raye baza ka sake yunƙurin kusantar wata yarinya a rayuwarka ba. Za mu gani, sai ka cigaba da zaman jiran gadon." Ta buɗe idanunta sosai wasu abubuwa masu tsananin haske da walƙiya suka fito a guje suka daki ƙirjinshi. Ƙam ya tsaya a tsaye kamar mai shirin ɗaukar hoto. Bata ƙara kallonshi ba ta finciki hannun Murja suka fice daga ɗakin. BILHAƘƘI ******* ******* Ba tare da tunanin komai ba ta zauna a gefen faffaɗan gadon irinna masu sarauta, ta janyo kyawawa tausasan ƙafafun ta ɗora a jikinta ta fara mammatsa mata cikin nutsuwa. A haka har sai da ta buɗe idanu ta zuba a kanta. Haɗa idanu suka yi, kamar haɗin baki duk sai suka sakarwa da juna murmushi. Da sauri Bilhaƙƙi ta sauke na ta ƙwayoyin idanun kan ƙafafun tana kallon yadda suke a ɗan kumbure. Tausayinta ne ya ƙara kamata, ita tun jiya a ganin farko da ta yiwa Sarauniyar ta ji wani sassanyar madarar ƙauna da tausayinta yana kwarara a cikin zuciyarta. "Bilhaƙƙi? mun tashi lafiya...?" "Au! yi haƙuri Ranki ya daɗe. Barka da tashi, na katse miki barci ko?" Ta katse ta tana maganar a jejjere cike da kunya. Dariya kawai ta yi tana kallon zallar ƙuruciya a gurin yarinyar. Matar Maheer ɗin ta burge ta, tun jiya da suka isa masarautar idan ta kalle ta tana jin wani abu kaman maganaɗisu yana fisgar tunaninta zuwa tunanin yarinyar, kamar ta taɓa saninta a wani wuri. Amma duk zurfafa tunaninta ta rasa inda ta taɓa ganinta, kuma ta rasa dalilin da yasa tunanin ya ƙi barin zuciyarta. Sakin murmushi ta sake yi tana kallonta. "Ba komai. Lafiya ko? ko akwai abinda kike buƙata?. Haka kike tashi da wuri? Ita Salamatun ta tashi...?" Da sauri ta sake katse ta a karo na biyu "Ranki ya daɗe yanzu na gama yin mafarki naga kin haihu lafiya ba tare da anyi miki aiki ba, shi yasa na kasa daurewa na taho gare ki." Ta maida idanunta kan danƙareren agogon bangon ɗakin, ƙarfe huɗu da minti arba'in na asubah. Ƙasa ta sauke idanunta ta ci gaba da magana " A mafarkin nawa na ga Mummy ce ma ta ke tare da ke har kika haihu. Kin san me kika haifa?" Ta ƙarasa tambayar tana kallonta. Daɗin labarin yasa ta yunƙura a hankali daga kwance ta miƙe zaune tana saurarenta. Biye mata tayi ta girgiza kai alamun bata sani ba, fuskarta cike da murmushi take sauraren daddaɗan labarin mafarkin da take ba ta. A zuciyarta cike da fatan tabbatuwar mafarkin da gasken gaske. A hankali ta ƙara amsa mata ta ƙara da tambayarta. "Ban sani ba Bilhaƙƙi. Me kika ga na haifa?" Maimakon ta ci gaba da faɗa mata mafarkin sai ta yi murmushi, a hankali kuma cikin nutsuwa kamar tana tsoron ji mata ciwo ta sauke mata ƙafafun a kan gadon, ta miƙe tsaye ta nufi inda ta ajiye galan ɗin addu'ar da Malam ya taho wa da Sarauniyar daga kaduna. Kofi ta ɗauka ta tsiyayo ruwan addu'ar ɗan madaidaici ta koma in da ta tashi ta zauna. Ta kara kofin a kusa da bakinta sosai ta fara karanto wasu addu'o'in a hankali. Tsawon lokaci sannan ta tofa addu'a ta nufi bakinta da kofin "Daure ki shanye duka Ranki ya daɗe. Yau ki sha addu'ar nan kafin ki ci komai. In Allah ya yarda za ki ga iko da hukuncin Ubangijin sammai da ƙassai. Dan Allah kar kisha idan zuciyarki na taraddadi, so nake ki sha zuciyarki cike da yarda da sakankancewar lallai Allah mai kowa mai komai ne, kuma shi ne ɗaya mai iko akan komai, mai yin yadda ya so a lokacin da yaso. Da shi kika dogara shi kuma cikin hukuncinsa zai fuskance ki da Rahamarsa. Zai biya miki duk buƙatunki kuma ya share miki hawayen da kika daɗe kina zubarwa na tsawon shekara da shekaru." Tun tana kallon Bilhaƙƙi da murmushi har murmushin ya ɓace a fuskarta, zuciyarta ya cika da tsoro. Amma fa ba tsoron kowa ba sai tsoron Allah shi kaɗai, da tsananin sakankancewar lallai Allah fa shi ne mai amsar addu'ar bayinsa. Wasu hawaye masu rangwamen zafi suka silalo daga idanuwanta, ta lumshe idanu ta buɗe. Haka kawai sai ta ji wani sanyi da ni'ima da yalwataccen farinciki suna sauka a duka sassan jikinta. Hannunta ta ɗora a saman hannun Bilhaƙƙi da yake riƙe da kofin ta buɗe bakinta, hannayensu a tare ta kafa kofin a bakinta ta fara shan ruwan addu'ar a hankali har ta shanye gaba ɗaya. "Na gode Bilhaƙƙi. Allah yayi miki albarka. Kije kiyi sallah ni ma sallar zanyi, bayan kin idar kizo zanyi magana da ke." Murmushi ta yi, ta mayar da kofin ta aje a inda ta ɗauke shi. "Nima na gode Ranki ya daɗe. Zan dawo in Allah ya yarda." Da ido ta rakata fuskarta fal murmushi zuciya cike da ƙauna har ta fice daga turakar ta ja mata ƙofar. Ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya, a hankali ta ture bargon da ta lulluɓe rabin jikinta ta zura ƙafafu ƙasa ta sauka daga kan gadon, wani zillo da ɗan cikinta yayi da ƙarfi yasa ta runtse idanu ta dafe cikin da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta dafe gefen gadon. Bakinta ɗauke da addu'o'i, sai da ta ji motsin ya lafa mata ta nufi banɗaki tana tafiya a hankali dan ta ɗauro alwalar sallar asubahi da ake ta kwaɗa kiran sallar farko. ****** ****** A cikin mugun mafarkin da ta saba yi cikin kwanakin yau hango Shalelenta Yarima Muzaffar tayi cikin wani mugun yanayi na ƙyama da tsangwama daga bayi da kuyangin gidan. A tsorace ta farka ƙirjinta na bugun tara-tara, idanunta a waje take sake tunano abinda ta gani a mafarkin. Ta haɗa zufa tayi sharkaf kamar wacce ta yi tseren gudu a cikin barci. Da taga tunani bazayyi mata ba da sauri ta dira daga kan gadon ta ɗauki jallabiya ta zura akan kayan baccin jikinta. Ko da ta buɗe ƙofar turakar ta fita falo ba ta bi ta kan bayi ukun da taga suna kai kawo ba kai tsaye ta nufi hanyar da zai sada ta da ɓangaren shalelenta bayan ta zura tattausan silifas a ƙafafunta. "Ranki ya daɗe Fulani Taka barka da asubah. Kina buƙatar rakiya ta ne...?" "Ba buƙata." Ta katse ta a hargitse tare da ƙara sauri zuwa inda ta nufa. Ta kusa isa ɓangaren sai ta hangi tahowar Mai Martaba da wasu mutane su huɗu ko biyar a bayansa. Ƙirjinta ne ya buga dam! Bugawar numfashinta ya fara hauhawa daga dai-dai zuwa yanayin da ba a cika buƙata ba a jikin ɗan Adam. 'Me zai kawo Takawa da kansa ɓangaren Yarima da asussubahin nan???' Tunanin zuciyarta ke nan. Da taga tunani da saƙar zuci bazai kaita ba sai kawai ta ƙara ɗaga ƙafa tana sauri dan ta riga su isa ta ga a wane hali Yariman yake ciki. Tana gaf da shiga mai Martaba ya dakatar da ita. "Safra'u?" Ya kira ta da muryarsa mai cike da izza da wani irin kwarjini mai firgita duk wani mare gaskiya. Runtse ido tayi kawai alamun sam bata so haka, ba ta da yadda ta iya dole ta ja ta tsaya cak har ya ƙarasa kusa da ita. "Takawa barka da asubah." Ta gaishe shi da muryar da ke ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin da zuciyarta ke ciki, har da ɗan rusunawarta don nuna ladabi da girmamawa a gare shi. "Yauwa..! Barkanmu dai Safra'u. Me ke tafe da ke ɓangaren Yarima da sassafennan?" Ya ƙarasa tambayar tare da ƙure ta da kallo. "Babu komai Ranka ya daɗe. Kawai a zuciyata ce naji ina buƙatar ganin halin da yake ciki. Shi yasa na yo tattaki da kaina. Ko ga Takawa ma hakan ce ta kasance?" Ta ƙarasa maganar haɗe da sauke idanunta a kan mutanen da suke biye da Mai martaba, sai ta ga Liman, Waziri Umar, Chiroma, sai wani da bata san ko waye ba (Mal Abdulganiyyu ne mahaifin Maheer), da Bala babban Bawan da yake kula da al'amuran ɓangaren Yarima. Saboda biyayya shi Bala yana rakuɓe ne can gefe guda a bayansu. "Safra'u mu kam a gare mu ba hakan bane ta kasance. A ko wane lokaci muna da kyakkyawan tsammanin lafiya ko wane rai da ke ƙarƙashin masarautar nan zai wayi gari. Sai dai yau! Bayan idar da sallar asubah a bakin Bala babban hadimi ga Yarima mun wayi gari da wani mummunan labari, cewar Yarima yana cikin wani jarabta na Ubangiji. Da wannan ƙwaƙƙwaran dalilin yasa muka taho da Malam Liman don ganin halin da yake ciki. Don haka ina ganin ke ki koma ciki duk abinda yake faruwa za ki samu labari daga baya." Idanu ta gwalalo a tsorace haɗe da dafe ƙirjinta da hannu biyu, ba ta saurari umarnin da yayi mata na komawa cikin gida ba ta buɗe ƙofar da sauri ta afka ciki, bata tsaya a falon ba kai tsaye ɗaya daga cikin ɗakunan baccinsa ta nufa inda take jiyo wani ƙaƙƙarfar gurnani kaman na doki da wani kuka-kuka yana tashi a cikin ɗakin. Tana shiga su Mai martaba suka rufa mata baya, basu ganshi a tsakar ɗakin ba. Yana rakuɓe can saƙon tsakankanin gado da lokokin gadon yana kuka mai haɗe da gurnani, idanunsa jajur, bakinsa sai dalalar da yawu yake yi. Yana zaune ya naɗe hannayensa a ƙirji, babu riga a jikinsa daga shi sai gajeren wando. Yana haɗa idanu da Mahaifiyarsa ya miƙe a zabure ya nufi gurinta da mugun sauri yana waige-waige da raɓe-raɓe, kamar dai yana tsoron wani abu da yake gani a idanunsa. Yana ƙarasa kusa da ita ya rirriƙe hannayenta a tsorace ya fara maganganu kaman wanda notocin kansa suka kwakkwance. "Umma... Umma... ki ɓoye ni... ta ko ina ita nake gani za ta kashe ni... ta faɗa min daga jiya bazan sake iya haiƙewa wata baiwa ba... kin ganta can ko...?" Ya fara nuna jikin bango da yatsarsa yana ƙara rirriƙe mahaifiyarsa a tsorace, yayi wani ƙaƙƙarfar gurnani a lokaci guda kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi ya ci gaba da magana. "Wai fa kawai dan ta ce min tana haila na ce ban yarda ba shi ne take neman kashe ni... ki gudu da ni Umma... wayyo... wayyo... wayyyo.... ga ta nan ta biyo ni da wuƙa..." Ya ruƙunƙume ta da ƙarfi yana nuna ƙunzugu mai ɗauke da jinin da Murja ta yar a tsakar ɗakin lokacin da ya kimtsa mata zazzafar marin da ya sa ra hantsila. Tsananin tashin hankali, ruɗani, firgici, da tsoron yadda Shalelenta ya buɗe baki yana tona asirin irin tsiyar da ya daɗe yana tsulawa akan duk wata saffa-saffar baiwa mai jini a jika yasa ta rungume shi a jikinta haɗe da sakin wani ƙaƙƙarfar kuka. Mai martaba da ya rasa na yi hannu ya naɗe kawai yana kallon ikon Allah yana sauraren saɗara-saɗarar abinda Muzaffar yake cewa. Mal Liman da Mal Abdulganiyyu sai jan ta'aweezi da a'uziyya suke yi. Shi kuwa Chiroma can gefe guda ya rakuɓe cike da tsoron kar maganganun tonuwar asirin da Muzaffar yake yi yayi kuskuren ambato sunanshi. Bala kuwa baki da hanci buɗe ya sake yana sauraren duk abinda yake faruwa. Ko da Mal Abdulganiyyu ya ga lokaci na ƙara tafiya, maganganun bakin Yarima sunƙi tsayawa kamar an kunna radio mai jini, ga wani zabura da yake yi yana mimmiƙewa kamar ana tsikarinshi da allura kusa da Mai martaba ya matsa cikin ladabi da tausasan kalamai ya ankarar da shi abinda ya kamata a yi. Daƙyar Takawa ya samu nasarar ɓamɓare Yarima daga jikin Sarauniya Safra'u. Tana kuka da turjewa yasa aka fice da ita daga cikin ɗakin shi kuma Yarima aka kulle shi a cikin turakar kafin isowar likitoci. A can ɓangaren Sarauniya Safiyya kuwa cikin hukunci na Allah SWT tana idar da sallar asubahi naƙuda mai ƙarfi ya taso mata. Wannan ruwan addu'a da Bilhaƙƙi tayi mata tasha shi ya zama kamar ruwan naƙuda da allurar naƙuda aka zurkuɗa mata a jikinta. Ko da Bilhaƙƙi ta koma turakar kamar yadda ta umarce ta bayan ta idar da sallah tana ganin halin da take ciki ta fara sharar ƙwallah don tsananin tausayin ganin yadda take salati da gurmususu. Ɗakin da aka sauke su ta koma wanda ɗaya ne daga cikin ɗakunan da yake ɓangaren Sarauniya Safiyya, kiran Mummy Salamatu tayi suka koma can turakar Sarauniyar da sauri. Ruwan addu'ar ta sake tsiyayowa ta ba Mummy ta ce ta bata ta sha sannan ta fice ta ja musu ƙofar. A nan falon ta hakimce tana dakatar da duk baiwar da ta yi yunƙurin zuwa turakar Sarauniya Safiyyar. "Barci take yi. Kuma ta ce bata buƙatar a dame ta har sai ta fito da kanta." Amsar da take ta basu ke nan wanda yasa dole suka dakata tunda sun ji umarni ne daga ita kanta Fulanin. A can lungu da saƙo na sassan cikin gidan kuwa abinku da gidan sarauta da ba a raba su da tsegumi. Cikin ƙanƙanin lokaci wannan faɗawa wancan, wancan tseguntawa wannan nan da nan zancen halin da Yarima yake ciki da irin maganganun da yake yi ya karaɗe lungu da saƙo na gidan. Sai hum-hum-hum ake yi da zancen ana tsoron Fulani Taka ta tsinci ana tauna maganar. Bayan isowar likitoci cikin gidan duk yadda aka so a fitar da Yarima daga ɗakinsa ƙiyawa yayi, sai zambarma yake yi yana zabura da jifan likitoci da mutanen ɗakin da duk abinda yake kusa da shi. Har lokacin kuma bai fasa irin surutun da yake yi yana zabura haɗe da cewa ga tanan za ta kashe shi ba. Dole dai likitocin biyu suka koma asibiti suka kwaso wasu ƙananun kayayyakin aikin da za su buƙata suka koma gidan. Mai martaba ne ya rirriƙe shi da taimakon su Mal Abdulganiyyu da ƙyar aka samu nasarar zurkuɗa mishi alluran barci mai ƙarfi. Minti goma tsakani barci ya ɗauke shi sannan likitocin suka samu damar fara binciken abinda yake damunshi, daga ƙarshe dai dole sai kwasarsa aka yi zuwa babban asibitin cikin garin Bauchi don a binciki halin da ƙwaƙwalwarsa ta ke ciki. Ita kuwa Fulani Taka kulle kanta tayi a cikin turakarta ta hana kowa shiga gurinta. A cikin ɗakin sai safa da marwa take yi kamar wacce ta haɗiyi taɓarya. Tana kuka da majina tana tsinewa tauraruwa mai wutsiya, don ta tabbata wannan mummunan al'amarin da yake faruwa da Muzaffar aikinta ne. A can ɓangaren Sarauniya Safiyya kuwa bayan awa biyu da minti goma tana gurmususu da jan ayar Summas sabeela yassara Allah ya kawo mata haihuwa lafiya da taimakon Mummy Salamatu, farar jaririya mai kama da turawa ce ta fara kunno kai bayan fitowarta da daƙiƙu ashirin kyakkyawan jariri mai kama da larabawa ya biyo bayanta. Kukan da suke ta tsalawa mai bayyana alamun lafiya suke shi ya fara tona asirin abinda yake faruwa a cikin ɗakin. Nan da nan jikin bayi da kuyangin ɓangaren ya fara kyarma don tsananin murnar wannan daddaɗan haihuwa ta bazata a lokacin da ba a taɓa tsammani ba. Guɗa suka fara rangaɗawa suna taka rawa da godiya ga Allah. Bilhaƙƙi ma baki ya ƙi rufuwa don tsananin murna, duk yadda take ta bubbuga ƙofar da son Mummy ta buɗe mata don ta ga abinda aka haifa ƙin buɗewa Mummy ta yi har sai da uwa ta biya. Bayan ta yanke ma jariran cibi a jikin Sarauniya da take ta zubda hawaye ta kwantar da su. Banɗaki ta shige ta haɗa mata ruwa mai zafi-zafi ta kama ta zuwa bayin, ta ce kukan ya isa haka ta daure ta tsarkake jikinta. Sai a lokacin ta buɗewa Bilhaƙƙi ƙofa tana shiga suka maida ƙofar aka datse, cikin zafin nama Mummy ta tsaftace gurin ƙal ta goge da klin da dettol kamar ba'ayi haihuwa a ɗakin ba. Ita kuma Bilhaƙƙi tana zaune akan gado tana aikin gogewa jariran jikinsu da dettol, abinku da wacce bata saba ba har saida Mummy ta gama ta amshe ta, bayan ta gama ta naɗe su a cikin kayan sanyi kafin ayi musu wanka. A lokacin ne mai Soron baƙi ta isa ɗakin da kanta ba aike ba don ganewa idanunta tabbacin abinda yake faruwa ba jita-jita ba. Kyawawan jariran da aka damƙa mata a hannunta yasa ta fashe da kuka don tsananin farin-ciki, daga bisani kuma ta fashe da dariya ta tattakura ta kama hanci ta rangaɗa ƙaƙƙarfar guɗar da ya karaɗe ɓangaren Sarauniya Safiyya gaba ɗaya. Su Mummy da Fulani sai murmushi suke yi cike da tsananin farin-ciki. Kwantar da jariran ta yi akan gado ta fita dan ta riga kowa kaiwa Takawa wannan kyakkyawan albishir ɗin, tana da tabbacin za ta samu gwaggwaɓan tukwuicin da zai jijjiga nutsuwarta. Duk wanda ta ci karo da shi a hanya umarni take badawa kan a shiga lungu da saƙo na cikin gidan a sanar da Sarauniya Safiyya ta haifo kyakkyawar Gimbiya da sabon balarabe Yariman Bauchi. Nan fa labarin ya sake fantsama a lungu da saƙo na cikin gidan. Haka Allah yake ikonsa, idan ya so sai ya haɗa wa bawa farin-ciki da baƙin ciki duk a lokaci guda. Hakan ce ta kasance ga Takawa, ga farin-cikin haihuwar Safiyya ga baƙin cikin abinda yake faruwa da Muzaffar. Da kanshi yay tattaki har zuwa ɓangaren Safiyya don ganin sanyin idanunsa. A karo na tara cikin kyarma da rawan jiki Jakadiya ta sake ƙwanƙwasa ƙofar turakar Fulani Taka, amma har lokacin ko alamun za a buɗe mata ƙofar bata ji ba. Kanta ta kwantar a jikin kofar ta buɗe murya sosai yadda za ta iya jiyo ta ta ciki "Ranki ya daɗe Jakadiya babba ce. Jaje haɗe da gwaggwaɓar albishir na taho inyi miki. Jajen akan abinda ya faru da Yarimanmu ne, albishir ɗin kuwa yanzunnan na samu labarin Fulani ta sauka lafiya, ta haifi ƴaƴa tagwaye lafiyayyu ƙosassu, da ita da jariran duk suna lafiya..." Ihun da taji an yanka ta can cikin ɗakin tare da jin rijib! alamun faɗuwar wani abu yasa ta kasa ƙarasa maganar da take yi, daga nan kuma ɗif ake ji. BILHAƘƘI Duk da jikinta yana bata wannan ƙarar da ta ji daga cikin ɗakin da alamun faɗuwar wani abu ba na lafiya bane. Amma don ta ƙara tabbatarwa sai ta sake kara kanta a jikin ƙofar tana kiranta. "Ranki ya daɗe Fulani? kina ji na? Allah yaja zamaninki ki daɗe kina yi a masarautar bauchi. Dan girman Allah ki taimake ni ki buɗe ƙofar nan." Shiru ne nan ma ya sake ba ta amsa. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma. Tana nan tsaye ita da bayin ɓangaren sunyi cirko-cirko da tunanin waƙar farawa sai ga shigowar Chiroma buguzum-buguzum yana baza babbar riga. Nan da nan duk suka dare suka bashi guri, kowa ya zube a ƙasa yana kwasar gaisuwa. Ko amsa musu ya kasa yi saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki. Haihuwar Fulani lafiya ba tare da samun labarin mutuwarta gurin haihuwar ba shi ne babban abinda ya sashi ya zuge ya ƙare a lokaci ɗaya. Daman ga damuwar ciwon sambatu da ya kama Muzaffar farat ɗaya. Daga samun labarin haihuwar zuwa yanzu ya zaga bayi sau shida. Duk gwuiyawunsa a sake suke saboda rashin ƙarfin jiki. Fulani Taka yayarsa ce, tonuwar asirinta a masarautar nan tabbas babban tonuwar asirinsa ne. Domin duk wani tuggu da makirci da asire-asire tare da shi take ƙullawa, a taƙaice ma shi ne jakadan amsowa da isar da duk wani saƙo ko magani a gurin malamai da bokayenta. Da wannan dalilin yasa yazo tun da wuri kafin wankin hula ya kaisu dare, gara su san na kwatanci su nemawa kansu mafita da hanya mai ɓullewa. Ya kalle su shakaka da baki sannan ya daka musu tsawa dan kawo ƙarshen gaishe-gaishen da suke ta mishi. "Kai dallah ku saurara min! Ina ita Fulanin ta ke?" Jakadiya ce ta gyara tsuguno ta kora mishi bayanin duk abinda ya faru. A diririce ya matsa kusa da ƙofar shi ma yayi kirari, yayi magiya, yayi roƙo amma shiru ya ke ji, babu ma alamun za ta amsa balle har ya saka ran za ta buɗe ƙofar. Hankali a tashe ya kwashi jiki zuwa gurin Mai Martaba don ya sanar da shi halin da ake ciki. Mai soron baƙi ne ta tare shi da cewar baya nan ya shiga cikin gida gurin Mai Babban ɗaki (Mahaifiyar Sarki). Haka ya sake kwasan jiki zuwa ɓangaren Mai babban ɗaki bayan ya nemi iso anyi mishi izinin shiga ciki, ya tarar da lafiyayyiyar tsohuwar mai kyawun jiki an zuba mata jariran a gabanta tana tottofe su da zafafan addu'o'i. Takawa yana zaune a gefe yana kallon yaran da mahaifiyarsa fuskarsa cike da farin ciki. "Chiroma lafiya kuwa? Me yake faruwa da har aka gaza jira mu fito har sai an biyo mu nan gurin Umma?" Ƙasa ya sake kwantar da kanshi yana neman afuwa "Tuba nake Ranka ya daɗe. Tuba nake, Allah ya huci zuciyarka. Haƙiƙa ba lafiya ba, tunda Fulani taga halin da Yarima yake ciki ta bar sashen cikin tashin hankali da damuwa har yanzu bamu san a wane hali take ciki ba. Ta kulle kanta a turakarta ko motsinta ba a ji, munyi magana munyi magiya shiru har yanzu bata buɗe ƙofar ba. Tsoro muke ko tana cikin wani mummunan hali shi yasa nayi gaggawar zuwa in sanar da Takawa. Tuba nake Ranka ya daɗe." "Subhanallahi! Abdulfahi ayi gaggawar ba da umarnin a buɗe ƙofar ko ta wane hali don a ga yanayin da take ciki." "To Umma. An gama!" Ya amsa ma umarninta cike da ladabi da biyayya a muryarsa. Sai kuma ya maida idanunsa kan Chiroma. "Ayi gaggawar sanar da Badaru halin da ake ciki, idan ta kama ma a ɓalla ƙofar. Gamu nan fitowa." "A fito lafiya Ranka ya daɗe. Allah ya huta gajiya. Ranki ya daɗe a huta lafiya, Allah ya raya mana Gimbiya da Yarima ƙarami, Allah yayi musu albarka." Haka yayi ta surutai yana satar kallon kyawawan yaran har ya fice daga sasan gaba ɗaya. Ko da aka ɓalle ƙofar turakar Fulani a sume aka tarar da ita. Shi yasa ba tare da wani ɓata lokaci ba itama aka kwashe ta zuwa babban asibitin cikin gari, inda a can ne aka kwantar da Shalelenta. ****** ******** An kira babbar likita har gida ta duba Sarauniya Safiyya da jariran ta tabbatar da lafiyarsu ta ba Safiyya magunguna, Mai martaba yayi mata sha tara na arziki sannan ya sallameta. A wannan ranar Takawa kyaututtuka yake ta yi na bajinta da nuna godiyarsa ga

Chapter 19 of 25