take ciki ƙafafu da hannayenta ne suka fara nannaɗewa suna lallauyewa kamar wata mai aljannu, a karo na biyu ta sake yanka ihun da yayi daidai da shigan Madam cikin banɗakin.
Kafin wasu daƙiƙu ta sume.
Murmushi tayi, ta cije leɓen bakinta tana kallon Bibin a wulaƙance.
"Da kyau Oga, aikinka yayi kyau. Maganin shegiyar yarinya mai kunnen ƙashi kenan"
Ficewa tayi da sassarfa ta kwashi jakunkunan kayansu zuwa cikin mota.
Ta kira su Liyat suka yi a tara a tara da Bibin suka kwantar da ita a bayan motar Madam, ta buɗe wani ɗan madaidaicin akwati ta kwashi kuɗaɗe da yawa ta zuba a ƴar ƙaramar jakarta ta hannu, ta ɗebi wasu da yawa ta rarrabawa duk yaran gidan sannan ta faɗa mota ɓangaren mai zaman banza, ɗaya daga cikin direbobinta ya ja a guje suka fice daga gidan suka nufi hanyar kaduna.
****** ******
"Kina ganin za ku iya isowa nan da minti ashirin? ƙarfe biyar muka yi da su zamu haɗu ga shi yanzu huɗu da minti arba'in, kinsan Lion ya tsani a ƙara mishi lokaci ko da minti ɗaya."
"Eh ina ganin haka, yanzun mun shigo refinary junction, za mu ƙaraso yanzu. Pls ki jira ni."
Tsaki ta ja daga can ɓsngaren sannan ta katse wayar.
Bata damu da tsakin ba ta maida wayar ta aje akan cinyarta ta maida kallonta kan direban.
"James ka taka motar nan sosai mu isa da wuri. Mercy tana jira na akwai inda zamu je yanzu."
Bai ce komai ba ya ƙara gudun motar sosai har ɗari da arba'in, lokacin da suka ɗauki hanyar shiga kamazou saboda babu yawaitar cunkoson motoci a hanyar.
Maida idanunta bayan motar tayi tana kallon yadda suka kwantar da Bibin a jirkice, wani ƙaramin murmushi ne ya suɓuce mata. Ta san ba ita kaɗai ke adawa da Bibin ba duk ƴan matan gidan Madam sun tsane ta, ko ɗan yaya suka samu dama a kanta za su gwada mata iyakarta ne, dubi wani kwantar da ita da suka yi a wulaƙance, irin kwanciyar da in banda tana cikin halin suma ne tabbas ba ƙaramin jin jiki zata yi ba.
A minti takwas suka ƙarasa cikin gidan Aunty Mercy. Gudu-gudu sauri sauri Madam ta faɗa cikin falon da ta tarar da tafkeken falon a buɗe, da alamun ƙarasowarta kawai ake jira.
"Yi haƙuri ƙawata, gani na ƙaraso."
Wani matsiyacin takalmi mai masifan tsini ta ɗauka a kusa da ita ta zura siraran ƙafafunta a ciki, tayi far da gashin ido na kantin da ta ƙara a idanunta dan ƙayata kwalliyarta, tayi magana idanunta a kan Marry
"Muje ko?"
"A hakan?"
Tayi maganar tana nuna jikinta da mamaki, duk da doguwar riga ƴar kantin da yake jikinta baiyi datti ba amma ya ɗan yamutse saboda zaman mota, kwalliyar fuskarta ma duk ya ragu ya ɓace. Ta maida idanunta kan Mercy da ta sha kwalliya cikin wani T.shet mai matuƙar kyau da tsada, da wani ɗan ɓingilin sket baƙi kamar wata ma'aikaciyar banki. Fuskarta da bakinta sunsha penti-penti, ta kawo wani gashin doki mai siraran kitso ta ƙwama a kanta duk dan sake ƙawata kwalliyarta.
"Na yi tunanin za ki bari in shirya ko a cikin minti biyu?"
"No babu lokacin hakan Mary, duk abinda za ki buƙata yana cikin nan."
Ta ƙarasa maganar tare da nuna wani babban leda da yake ajiye kan kujerar kusa da wacce take zaune.
"Muje sai ki shirya a cikin mota."
"Ok ba laifi. Ya za muyi da Bibi? ga ta can kwance a cikin mota..."
"Linda da Agness zasu kula da ita har mu dawo."
Ɗaya daga cikin ƴan matan biyu da suke mata aiki a gidan ne ta ɗauki ledar kayan tana biye da su a baya, ɗayan kuma ta riƙe jakar ƙaramar jakar Aunty Mercy har zuwa gurin danƙareriyar motar da ta sa aka wanke mata tun kafin ƙarasowar Madam Mary, har ta shiga mazaunin direba tayi key ɗin motar sai kuma ta kashe motar ta fito bayan ta yi wani ɗan tunani.
"James?"
Ta ƙwalla kiran direban da ya kawo su Madam, da gudu ya ƙaraso kusa da ita yana kallonta cike da ladabi. Makullin motar ta hurga mishi ya cafe ta buɗe ɓangaren baya na motar ta zauna.
"Shigo ka sauke mu, yanzu yamma ta yi, cikin gari bazai rasa go-slow ba, kuma ina buƙatar muyi saurin isa akan lokaci. Idan munje can sai kayi odar abinci kafin mu fito."
"Ok Ma."
Ta maida kallonta kan su Agness ta ci gaba da magana.
"Bibi tana cikin motar Madam ku shiga da ita ciki, ku kula da ita sosai kafin mu dawo. Ina fatan kun gane?"
"Yes Ma"
Suka amsa bakinsu a haɗe.
Tada motar yayi bayan madam ta shiga ciki mai gadi ya wangale musu get suka fice daga gidan. Ko da ya daidaita motar akan titi a tsiyace yaja motar dan su isa akan lokaci bayan ta faɗa mishi inda za su je.
******* *******
Tana gama gyara mata kwanciyar kanta q kan filon ta juya da nufin barin ɗakin sai ta ji an riƙe hannunta na dama da masifan ƙarfi, jin hakan yasa ta waiga a tsorace tana kallonta, har lokacin tana nan yadda suka kwantar da ita. Abinda ya banbanta ta da ɗazu kawai yanzu ana ganin saukan numfashinta a hankali saɓanin ɗazu da take a sume.
Taja hannunta dan ta ƙwace sai taji riƙon da ta yi mata ba na wasa bane, ƙura mata ido tayi tana karantar yanayinta, sai ta matsa da kunnenta kusa da bakinta sosai lokacin da ta fahimci kamar magana take yi amma ba ta jin abinda take cewa.
"Ku fitar da ni daga nan gidan. Unguwar rimi, Kinshasha road, gida mai lamba ashirin da huɗu, gidan Malam Abdulganiyyu. Can za ku sa a kaini."
Tayi maganar a hankali, yadda take yamutsa fuska tana mommotse baki ya fahimtar da ita cike da matsanancin ƙarfin hali da jin jiki tayi maganar.
Zazzare ido Linda tayi bayan ta gama sauraren abinda Bibi ta ce, ta ƙure ta kallo da kyau sai taga har lokacin idanunta a rufe suke. Kafin ta ce komai Agness ta buɗe ƙofar ɗakin ta leƙo da kanta ciki.
"Me kike yi haka?"
Tayi tambayar idanunta a zazzare bayan ta ga yadda take a durƙushe gaban Bibin.
Hannu tasa ta yafito ta, sai da ta shigo ciki sosai dan jin kiran me take mata sannan ta ce
"Bibi ta ce mu fitar da ita daga gidannan, ta faɗa min wani adress a unguwar rimi wai mu sa a kaita can..."
Tsakin da taja haɗe da banka mata harara yasa tayi shiru bata ƙarasa abinda take cewa ba.
"Ina tunanin kin fara hauka, sai ki fitar da ita daga nan ɗin ni dai ba ruwana a ciki ooo, Idan Aunty Mercy da Madam Mary suka fara Ball da ke kar ki kuskura ki kira sunana."
Ta ƙarasa maganar da ɗage kafaɗunta haɗe da taɓe baki alamun ko a jikinta. Ƙofar fita daga ɗakin ta nufa dan ficewa wani guguwa ya buga ƙofar gam! ya datse.
Gurnanin Bibi ya cika ɗakin kamar mai naƙuda, ta buɗe baki da ƙarfi ta sake cewa
"Kusa a fitar da ni daga gidannan na ce."
Cikin tsawa da murya mai tsananin hargagin da saida lungu da saƙo na gidan yayi amsa kuwwa na maganarta.
Ta saki hannun Linda da ta riƙe, ta buɗe idanunta gaba ɗaya wani farin haske mai tsananin walƙiya ya gilma ta tsakankanin idanunsu, hasken yayi gabas da yamma kudu da arewa na cikin ɗakin a ƙarshe ya daki wani danƙareren madubi da yake maƙale kamar tv a jikin bangon yamma na ɗakin, ratsatsatsatsa ƙarar tarwatsewar madubin ya daki dodon kunnuwansu.
A tsorace cike da sadaƙarwa suka tsuguna ƙasa idanunsu a rufe, hannayensu duk biyu toshe da kunnuwansu. Gaba ɗaya sun gama tsammanin aradu ce zata faɗo a kawunansu saboda mugun rugugin da ya biyo bayan fashewar madubin, sai kuma suka ji ɗif! kamar anyi ruwa an ɗauke komai ya tsaya cak! Can bayan kimanin minti biyu suka ji murya a shasshaƙe tana magana a hankali kamar tsohuwa taci gaba da magiyar susa fitar da ita daga nan gidan.
Sau ɗaya suka yi gigin kallon idanunta bayan sun buɗe nasu idanun a tsorace basu sake marmarin kallonta ba, saboda idanun sunyi ƙuru-ƙuru fari-fari ruwan hazo-hazo babu ko ɗigon baƙi a ciki.
Zubewa suka yi a ƙasa a gaban gadon da suka kwantar da ita a tsorace suka fara bata haƙuri, bata tanka musu ba har suka gaji da tsugunon bata bar magiyar da take yi ba.
Da mugun gudu Agness ta fita daga gidan mai gadi yana tsaida ita bata tsaya ba har taje bakin titi ta samo shatan taxi. Inda Allah ya taimake ta mai motan bahaushe ne ɗan cikin tudun wada, tana faɗin adress ɗin ya ce yasan layin kinshasha amma baisan gidan Malamin ba, sai dai idan sunje yayi tambaya. Suka tsadance akan dubu biyu ta biya shi kuɗin ya ɗauketa suka koma gidan.
Mai gadi sai kallonsu yake yi yana mamaki su kuwa basu san ma yana yi ba. Babban burinsu su aikata abinda take buƙata dan tserar da ransu da lafiyarsu, ranga-ranga suka sake ɗaukota daga cikin gidan suka kwantar da ita a bayan motar yaja daga shi sai ita suka bar unguwar suka miƙe titi dan zuwa unguwar rimi.
Ajiyar zuciya mai nauyi suka sauke a tare duk su biyun. Kafin su ce komai muryar mai gadin ta daki dodon kunnuwansu
"Linda me yake faruwa ne haka? wace wannan da aka tafi da ita?"
A tsorace suka maida kallonsu kanshi cikin rasa abin cewa, tsananin ruɗewa da tashin hankali ma yasa sun manta da mai gadi a gidan.
"Aunty... Aunty... Mercy ce tace a kaita wurin wani Dr."
Tayi maganar a ruɗe tana nuna hanyar da motar ta ɓace da yatsarta manuniya.
Kallon rashin yarda ya bisu da shi har suka shige cikin gidan da sauri basu ƙara sauraren abinda zai ce ba.
"Amma bakya ganin munyi kuskuren ba shi ita ba tare da mun bi su mun ga gidan da zai kaita ba Linda?"
"Wani kuskure kuma kike magana? Thank God mun rabu lafiya ba tare da ta yi mana wani mugun abu ba. Yanzu kawai muyi tunanin abinda zamu ce da su Madam ya faru da ita idan sun dawo."
Ta faɗa a hankali tare da ɗosana mazaunanta a kan kujera, jikinta a sanyaye.
"Me kuwa za mu faɗa musu da ya wuce gaskiyar abinda ya faru? kinsan matuƙar muka faɗa musu ƙarya a cikin ƙanƙanin lokaci za su binciko gaskiyar abinda ya faru."
Tana gama maganar ta fita ta ɗauko tsintsiya da abin kwashe shara ta shige ɗakin da suka kwantar da Bibi dan tattara madubin da ya tarwatse, ta bar Agness zaune da tagumi hannu bibiyu.
***** *****
"Malam dan Allah nan ne gidan Malam Abdulganiyyu?"
Ya tambayi wani dattijo da ya gani tsuguno a jikin famfon masallaci yana alwala, ya nuna gidan da ɗan yatsarsa manuniya, idonsa yana kan lambar gidan ashirin da huɗu da aka rubuta da manyan baƙi a wani ɗan ƙaramin allo aka manna a jikin bangon ƙofar gidan da yake kusa da masallacin.
Sama da ƙasa dattijon ya kalle shi sannan ya maida idanunsa kan kwararraɓaɓɓiyar motar da ya zo da ita.
"Eh nan ne, lafiya?"
"Eh to lafiya ƙalau. Daman wata mare lafiya ce aka ce in kawo ta wajenshi."
"To Madallah! Allah ya bata lafiya, Malam ga shi can yana jan sallah. Sai ka jira shi a nan har a idar ko kuma kayi alwala ka shiga sallar dan ka samu jam'i."
Bai jira cewarsa ba ya shige cikin masallacin da sauri.
BILHAƘƘI
Jikin motarsa ya koma ya jingina yana jiran a idar da sallar, zuciyarsa cike da saƙe-saƙen gara ya bar sallar idan ya koma gida sai yayi.
Lokaci bayan lokaci yana leƙa kansa ta glass ɗin motar dan ganin a wane hali take ciki? sai yaga har lokacin tana nan kwance cikin fita haiyaci kamar yadda ya ɗaukota.
"Assalamu alaikum."
Malam ya faɗa a tausashe sannan ya miƙa mishi hannu suka yi gaisuwa irinta addinin musulunci.
"Malam lafiya dai ko? yanzu mun idar da sallah aka sanar da ni kana jira na a waje."
Nan ya faɗa mishi duk yadda suka yi da su Agness sannan ya buɗe mishi bayan motar dan ya ga mara lafiyar. Gabanshi ne ya faɗi, nan da nan fuskar yarinyar cikin mafarkin da yake yawanyi a cikin kwanakin nan ya faɗo mishi a rai
'kamar ita?'
Ya tambayi kansa a zuciyarsa. Sai kuma ya rufe ƙofar motar da sauri ya kalli direban, ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu ya ce.
"Bari mai gadi ya buɗe get ka shiga da motar sai mata a cikin gida su sauketa. Babu wani ƙarin bayani da suka yi maka kawai cewa suka yi ka kawo ta nan gidan?"
Ya tambaye shi fuskarsa cike fal da mamaki.
"Eh Akaramakallahu."
Ya amsa yana sussunkuyar da kai.
"To madallah. Ba laifi. Allah ya bata lafiya. Juyo da motar bari inyi magana da mai gadi ya buɗe maka ƙofa."
Ya nufi cikin gidan da sauri shi kuma direban ya shiga motar dan juyo da ita ya shiga gidan kamar yadda Malam ya umarceshi.
****** *******
Danƙareren agogon bangon falon ya kalla, fuskarsa baiyane da matsanancin mamaki bayan ya ajiye wayar da ya amsa kiran Hajiya Shafa, ƙarfe goma saura kwata na dare.
'Wasu baƙi mata ne za su zo ganina a wannan lokacin baza su jira gari ya waye ba?'
Ya tambayi kansa da kansa a zuciyarsa, amma da yayi tunanin ƙila ƙaƙƙarfar uzuri ne da baza a iya jiran wayewar gari ba sai ya zura takalmansa ya nufi cikin gidan ɓangaren Hajiya Shafa inda baƙin suke.
Sallama yayi a ƙofar ɗakin ya jira aka amsa daga ciki kafin ya cusa kanshi cikin falon idanunshi cikin na maiɗakinsa.
"Malam barka da shigowa"
Hajiyar ta faɗa a ladabce, saida ya amsa sannan ta nuna mishi baƙi matan da suke son ganinshi.
Ya kalle su a karo na farko yana karantar yanayinsu a cikin hasken ƙwayayen lantarkin da suka haske ɗakin kamar rana, sun sako dogayen riguna baƙaƙe har ƙasa, sun naɗe kawunansu da gyalen rigunan kamar wasu zuri'ar larabawa.
A karo na farko suka gaishe shi idanunsu a ƙasa, kujerar kusa da Hajiya Shafa ya zauna sannan ya amsa gaisuwarsu a mutunce.
"Madallah. Bayin Allah daga ina kuke? Ban shaida fuskokin ba."
Kafin su ce komai ɗaya daga cikinsu ta fara shessheƙar kuka tana jan hanci, sannan ta fara magana da rawar murya
"Malam ni sunana Maryam, ita kuma wannan ƴar'uwata ce sunanta Aisha. Ɗazu mun fita siyayya kasuwa da muka dawo sai bamu tarar da ƙanwarmu da bata da lafiya a gida ba. Ko da muka tambayi masu aikin da suke tare da ita sai suka ce wai an kawo ta nan gidan. Shi ne muka zo mu tafi da ita."
Shiru yayi yana karantar yanayinta, baisan me yasa ba haka kawai yake ji a ransa bai yarda da su ba. Tun ɗazu da aka kawo mare lafiyar yasa su Hajiya Shafa suka yi mata wanka da ruwan magani, suka saka mata kaya na mutunci, ko da ya ƙare mata kallo da kyau ya fahimci tabbas ita ce yarinyar da yake mafarki tana neman taimakonsu. Rayuwa take a tsakankanin matsafa ko daga ina take bai san wane dalili ne yasa Ubangiji ya turo ta gurinsa ba, dan haka zaiyi iya bincike sosai har sai ya gamsu da gaskiyarsu kafin ya basu ita, ko zai basu ita ma sai ta samu lafiya sosai ya ji daga bakinta tabbas waɗannan ɗin yayyinta ne kamar yadda suka faɗa sannan zai damƙa musu ita.
"Amma abin da mamaki, kika ce ita ɗin ƙanwarku ce?"
Ya tambayi wacce ta kira kanta Maryam yana tsattsare ta da idanunsa masu cike da kwarjini.
Majinar kuka ta sake ja ta ɗago jajayen idanunta karaf suka haɗa ido, saukar da nata idanun tayi ƙasa jikinta babu inda baya rawa
"E ! Eh wallahi da gaske nake yi. Aisha kiyi mishi bayani mana."
Ta ƙarasa maganar tare da zungurin cinyar abokiyar tafiyarta.
Cike da taraddadi da maganarta mai baiyana alamar ita yare ce dukda hausan ya zauna a bakinta ita ma tace
"Malam ka taimaka ka bamu ita, idan muka koma gida ba da ita ba wallahi iyayenmu zasu yi fushi da mu..."
"Ma sha Allahu! Tunda iyayenku suna raye gobe in Allah ya kaimu ku dawo tare da su. Akwai wasu ƴan tambayoyi da zanyi musu idan na gamsu da amsoshin salin-alin zan baku ita ku tafi."
Yayi maganar da dakakkiyar muryarsa tare da miƙewa tsaye alamun ya gama saurarensu.
Tsam suka yi da ransu, cikin su biyun an rasa wacce zata sake cewa komai. Kawunansu a ƙasa alamu ƙarara ba hakan suka so ji daga bakinsa ba. Maryam ta sake fashewa da ƙaƙƙarfar kuka ta zube daga kan kujeran gwuiwoyinta a ƙasa.
"Dan Allah Malam kayi haƙuri karka jefa mu cikin bala'i, wallahi idan muka koma gida ba tare da Bibi ba zamu shiga cikin mummunan masifa..."
"Wa'iyazubillahi! sai kace ba musulmai ba? wane irin masifa kuma ana zaune ƙalau? anya ma maganganun da kuka faɗa min gaskiya ne? Ban ga alamun gaskiya a tattare da ku ba. Shafa'atu kira min Lukman yazo da yaransa su bincika min waɗannan mutanen ban yarda da su ba."
Da sauri suka miƙe tsaye jin ƙarshen maganarsa, sum-sum suka nufi hanyar ficewa daga falon ba tare da sun sake cewa komai ba.
"Ku tsaya mana idan ku yayyinta ne da gaske..?"
"Za muje mu taho da iyayenmu ne."
Maryam ta faɗa cikin zafin rai tana zura takalminta da yake ajiye a ƙofar ɗakin, ita kuwa Aisha har ta kusa ficewa daga gidan zuciyarta cike da tsoron tsohon Malamin mai masifaffen wayau da saurin fahimta.
Tana fita ta ƙaramin ƙofar gidan Maheer yana sanyo kanshi zai shiga gidan, kaucewa yayi har saida ta wuce sannan ya shiga yana waigenta. A zuciyarsa yake tunanin su kuma waɗannan me ya kawo su gurin Malam a daren nan? Dan ya ga Aisha jingine da motar da suka zo da ita tana jiran fitowar Maryam daga cikin gidan.
Ko da ya shiga cikin gidan kai tsaye ɗakin Mahaifiyarsa ya nufa nan ya tarar da su suna kakabin maganar.
"Gara da kayi musu haka Malam, kana ganin waɗannan matan ka ga tsofaffin kwanti-kwan. Fuskarsu ta sha bilicin da ganinsu ba mutanen arziki bane. Idan ka gama binciken in da gaske ƙanwar tasu ce a basu ita daga baya amma ba a wannan halin da take ciki ba."
"Ni duk ba ma wannan ba Shafa'atu. Ɗazu direban nan yace min ƴanmatan da suka ce ya kawo ta nan gidan sun faɗa mishi ita tace su kawota nan ɗin kuma ita ta bada kwatancen nan gidan. Dole ina buƙatar yi mata wasu ƴan tambayoyi bayan ta warke kinga batun in basu ita ma bai taso ba."
Ya maida hankalinsa kan Maheer yana amsa gaisuwarsa sannan ya ce
"Yauwa Magaji, zo ka gani."
Ya ja shi har zuwa ɗakin baccin Ummee inda aka kwantar da Bibi akan gadonta, dukda akwai hasken ƙwanlantarki a ɗakin sai da ya sake haska mishi fuskarta dan ya ganta sosai.
"Ko kasan wannan yarinyar?"
Gabanshi ne yayi mugun faɗuwa, cikin ƙanƙanin lokacin walwalarsa ta ɓace ransa yayi mummunar ɓaci. Tsaf ya gane ta, yo ai dole ne ma ya gane ta, duk da tsananin tsanar da yayi mata da kuma ko a mugun mafarki baison ya ga fuskarta ba'a ɗauki dogon lokacin da zai ganta ya ce ya kasa shaida ta ba.
'Yanzu wannan mayyar yarinyar har nan gidan iyayenshi ta biyo shi kenan?'
Kamar zai ce wa Malam bai santa ba amma da yake ƙarya ba halinshi bane sai kawai ya ɗaga kai, alamun eh ya santa.
Cike da ɗoki Malam ya dafa kafaɗarsa fuskarsa fal da murmushi ya sake maimaita tambayar
"Da gaske ka santa Magaji?"
"E na santa Malam, amma ba a garinnan na santa ba."
Ya amsa muryarsa a cuccushe.
Hannunsa kawai Malam yaja suka fice daga ɗakin zuwa ɓangarensa, Hajiya Shafa ma da tayi niyyar biyo su dan jin inda aka haihu a ragaya dakatar da ita Malam yayi yace ta koma ta kunna wa mare lafiyar karatun Alƙur'ani mai girma ta jira dawowarsu.
Suna shiga ya maida ƙofar falon ya rufe, ya zaunar da Maheer akan kujera shi ma ya zauna a gefensa kamar wasu abokai.
"Magaji faɗa min inda kasan yarinyar nan ka ji? kar ka kuskura ka ɓoye min komai nima akwai abinda zan faɗa maka game da ita."
Nan da nan Maheer ya warwarewa mahaifinsa inda ya santa da duk abubuwan da suka faru tsakaninshi da ita, yana maganar shi kuwa Malam murmushi kawai yake yi yana jinjina girman hikima da iko irin na Ubangijin sammai da ƙassai mai kowa mai komai.
'Yana nan yana ta addu'ar Allah ya bata kariya a duk inda take ashe ta taɓa haɗuwa da ɗansa wanda a mafarki take kira garkuwarta harta faɗa cikin matsanancin soyayarsa.
Ko da ya fahimci Maheer ya gama ba shi labarin sai shima ya fara warware mishi bayanin duk irin yadda yake ganinta a cikin mafarki da yadda take neman taimakonsu. Ya ƙarƙare maganarsa da cewa
"Da wannan dalilin yasa ko da na dawo Semina naga halin da Surayya take ciki ba wani ci gaba a asibiti shi yasa nace a sallame ta, kuma kaga cikin hukuncin Allah yanzu an samu ci gaba sosai tana mommotsa jikinta kaɗan-kaɗan, babbar matsalar kawai a yanzu maganar da bata iya yi sai dai tayi ta bin mutane da kallo."
Kanshi ne ya buga, ransa ya ƙara ɓaci, zuciyarsa ta sake cika da matsananciyar tsanarta, babu abinda ya fahimta a maganganun Malam sai ciwon da Surayya take yi da sa hannun Bibi a ciki. Shi kam ko da matan duniya sun ƙare me zaiyi da wannan ƴar iskar yarinyar? yarinya ƙarama amma tun bata tafasa ba tana neman ƙonewa...
"Magaji tunanin me kake yi haka ina ta magana ka yi shiru?"
Malam ya katse mishi tunani ta hanyar girgiza kafaɗarshi da sauri.
"E... na'am?"
Ya faɗa a ruɗe, ganin irin kallon da Malam yake mishi sai yayi ƙoƙarin daidaita kanshi cikin nutsuwa ya sake cewa
"Ni abinda ban fahimta ba zaman me zata yi a gidannan Malam? yarinyar nan tun a garinsu na fahimci ba ƴar arziki bace ko daga irin kayan da take sawa masu baiyana tsiraicinta. Ni ina ga idan sun zo gobe kawai ka basu ita su tafi da ita can su ƙarata, idan akwai abinda zamu taimaka mata da shi bai wuce addu'a ba. Amma ni dai ban goyi bayan zamanta a gidannan nan ba..."
"Gidanka ko gida na?"
Malam ya katse shi cikin fushi fuskarsa a tamke, ashe tunda Maheer ya fara magana yanayin fuskarsa ya canza amma bai lura ba sai da ya dire.
"Ka yi hakuri Malam, Allah ya huci zuciyarka. Duk yadda ka ce haka za a yi."
Ya faɗa a ladabce hankalinsa a tashe.
"Babu komai Magaji, je kaga iyalinka ka wuce gida, sai gobe idan Allah ya kaimu."
Yana gama faɗin haka ya shige ɗakin barcinsa ya barshi nan a tsugune.
Gwuiyawunshi a saɓe ya miƙe ya fice daga falon, gurin Mahaifiyarsa ya koma sai ya tarar da ita tana sallar shafa'i da wuturi, daga can cikin ɗakinta kuma inda Bibi ke kwance karatun Alƙur'ani mai girma ne yake tashi a hankali cikin zazzaƙar muryar Alaramma Abdullahi Abba, cikin suratul Baƙara aya ta ɗari da biyu.
Ɗakin Mummy ya shiga ya tarar da ita da casbaha a hannunta, da alamun ita ma sallar ta idar.
"Magajin Malam ne a daren nan?"
"Ni ne Mummy,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 25