Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaba ɗaya, tana fita taga wani mai mashin ta ɗare a kai ta ce ya kaita bakin titi. ******* Duk yadda ta so ta ƙarfafi kanta kar ta sake kuka ta kasa, bata san lokacin da wani ƙaƙƙarfar kuka ya sake ƙwace mata ba. Da saurin gaske ta sa hannu biyu ta toshe bakinta ta rufe fuskarta dan kar hankalin mazauna cikin motar ya dawo gare ta. "Ki yi haƙuri" Ta ji saukar kalmar da ƙaramar murya kamar a tsakiyar kunnenta, a hankali ta ɗago kai dan ganin mai maganar sai tayi arba da kyakkyawar fuskar yarinyar da take zaune kusa da ita. Tsawon minti biyu suna musayar kallo sai yarinyar ta haske ta da tattausan murmushi, ta miƙa mata wani ɗan ƙaramin tsumma. Fahimtar abinda take nufi yasa ta karɓa ta fara share hawayen fuskarta, tana gogewa wasu sabbi na sake gangarowa har ta goge gaba ɗaya bayan ta samu nasarar tsaida kukan da ƙyar. Pure water ta miƙa mata mai sanyi, ba tare da musu ba ta karɓi ruwan ta huda ta fara sha wani sanyi yana kwarara a zuciyarta. "Na gode. Ya sunanki?" "Bibi" Ta amsa a hankali bayan shirun da tayi na second talatin kamar baza ta amsa ba. Dan ma kar ta sake tambayarta sai ta sanya tafukan hannayenta duk biyu ta rufe fuskarta tana tunani kamar mai bacci. 'Maman Ushe ta mutu, Indo ta mutu, Mal Muntari ya mutu, Raliya ta mutu. Ya zama dole ta gudu daga layin mai dubun tsumma in dai tana so ta cigaba da rayuwarta. Ta ji lokacin da aka zo gurin Mal daga gidan hakimi da cewar a tafi da ita ana tuhumar ita mayya ce, tun a lokacin ta yanke wa kanta shawarar abinda zai fisshe ta, da wannan dalilin yasa ta ɓuya can bayan gidan gurin shuke-shuke har sukai kiciɓis da Indo tana fata da mugun alkaba'i a kan Maman Ushe. Ko da Indo ta koma ɗakinta ta faɗi cikin mawuyacin hali bata fito daga maɓoyarta ba, da yake mutan gidan suna cikin tashin hankali shi yasa ma babu wanda ya tuna da ita balle har a neme ta. Indo tun kafin a kaita asibiti ta ce ga garinku nan. Mal Ali da duk wani wanda ya kusance su da al'ummar unguwa sun shiga cikin tashin hankali matsananci, rashin mata biyu a lokaci ɗaya ƙarfin imani da addu'a ne kawai ya hana Malam Ali zaucewa. Cikin dare ta yiwa gidan kallon ƙarshe ta bar kowa da komai na gidan ciki har da sunan Amirah da Maman Ushe ta raɗa mata ta fice daga ita sai kayan makarantan jikinta da naira saba'in a aljihun wandonta. Tafiya kawai take ba tare da sanin inda take jefa ƙafafunta ba ta wayi gari a bakin titi misalin ƙarfe takwas da rabi na safe, motocin Ganjal sai wucewa suke kwandastoci suna ta shelar "Kasuwa... kasuwan bacci." Ba tare da tunanin komai ba tasa hannu ta tsaida motar. "Yarinya ina za ki?" "Kasuwa" Ta amsa shi da sassanyar murya. "Naira hamsin" Ya faɗa mata bayan ya sauka daga kujerar farko ta shige ciki, har motar zata tashi ta hangi mai pure water sai ta sayi guda ɗaya. Sun fara tafiya ba daɗewa Maryam ta tsaida motar ta shiga bayan ta ce ita ma kasuwa za ta...' "Bibi kina bacci ne? mun iso fa." Maryam ta katse mata tunanin da take yi ta hanyar jijjiga ta da ɗan ƙarfi dan ta dawo cikin haiyacinta. ******* ******* "Mary kwana da yawa? gaskiya mun daɗe bamu haɗu ba, amma bana tunanin wannan ƴarki ce dan naga ba ƙaramar yarinya bace, ko sistan mai gidanki ce?" Taja tsaki fuskanta a ƙuntace, duk da tayi wanka kuma ciwukan jikinta duk anyi dressing ɗinsu ta ci abinci mai rai da lafiya ta sha magunguna har lokacin tsamin da jikinta yayi bai saki ya koma mata dai dai ba. "Mercy daina tuna min batun ɗan iskan nan. Mun rabu da shi gaba ɗaya." Ta maida kallonta kan Bibi da take barci hankalinta kwance, ita ma anyi mata wanka an canja mata kaya da sabbin ƙananun kaya ƴan kanti riga da wando. "Wannan yarinyar a mota muka haɗu, fahimtar da nayi bata san kowa ba kuma bata san inda zata je ba tsawon lokaci tana zaune a gefen titi shi yasa na taho da ita dan kar ta faɗa mugun hannu. Idan ta samu nutsuwa zan tambayi inda iyayenta suke sai in mayar da ita." "Ok ! kin kyauta. Ni zan fita, akwai komai da zaki iya buƙata, idan kuma kina son wani abu ki kira Grace ki yi mata magana. Maybe zan dawo kunyi bacci." Makullan motoci huɗu da suke zube a kan ɗan ƙaramin teburin gilas ta ɗauki guda ɗaya ta nufi hanyar ficewa daga falon, Maryam tana mata fatan dawowa lafiya. 'Tun a hanya da ta tuna yanayin yadda jikinta yake ciki ta yanke shawarar baza ta koma garinsu a wannan halin da take ciki ba. Dole ta nemi inda zata huta ta samu nutsuwa raunin jikinta su warke kafin ta koma gurin mahaifiyarta da ƴan uwanta ta basu haƙuri, tana cikin tunanin ne ƙawarta Mercy Abom ta faɗo mata a rai, tana zaune ne a Kamazou, ta san babu inda zata je ta samu tarba ta mutunci da girmamawa da ya wuce gurin Mercy, dan haka kai tsaye ta yanke shawarar nufan can ita da Bibi. Kamar yadda tayi tsammani kuwa Mercy ta tarbeta da tsananin murna, ta kaisu har cikin tanƙamemen ɗakin barcinta, ta haɗa musu ruwan wanka mai zafi suka gargasa jiki. Ba tare da ɓata lokaci ba ta kira likita ya duba ta ya bata magani, ta bada umarnin a haɗa musu lafiyayyen abinci har saida suka ture. Kafin ta fita tace su shiga duk inda suke so a tangamemen gidan nata su yi duk abinda suke so ta basu dama. A cikin kwanaki goma da suka biyo baya Mary wacce ta daina sallah, kuma ta daina amsa sunan Maryam sunyi shar da su daga ita har Bibi, alamun hutu da jin daɗi ƙarara ya baiyana a jikinsu. Ko a fuska Mercy bata taɓa nuna ta ƙosa da su ba harkokinta kawai take yi tana kashe musu manyan kuɗaɗe ta hanyar sai musu suturu masu tsada kamar bata san zafin kuɗin ba. Mary tun tana magana tana roƙon ta rage kashe musu kuɗi har dai ta gaji ta zuba mata ido. Satin su uku a gidan Mercy ta ɗebi kayanta kala biyu ta nufi kacia dan ganin halin da Mahaifiyarta da ƴan uwanta suke ciki, tayi kyau sosai cikin matsattsiyar rigar da ta saka a jikinta da ɗan ɓingilin sket ɗin jikinta, fuskarta ya sha kwalliya kamar wacce zata je gasar sarauniyar kyau, ta kawo wani faskeken glas ta ƙwama a idanunta. Idan ba sani mutum yayi ba baza a taɓa tunanin ta taɓa zama musulma ba balle har ayi tunanin ita ce Maryam ɗinnan da ta sha matsanancin gwale-gwale a hannun Masa'udu da Mahaifiya da ƴan'uwansa ba. Bata ji daɗin labarin da ta samu na mutuwar mahaifiyarta watanni huɗu da suka wuce ba, ta ci kuka sosai tayi mata addu'a a jikin kabarinta da yake cikin gidan, ƴan'uwanta kuma duk da basa cikin wahala rayuwa suke irinta cikakkun karuwai masu zaman kansu, da wannan dalilin yasa a daddafe ta kwana biyu ta tattara ta koma gidan Mercy bayan sunyi musayan lambobin waya da ƴan uwanta, sunyi murna sosai da ta sanar da su ta bar musulunci, har suka ƙara da ce mata barinta musulunci daɗaɗɗan buri ne da mahaifiyarsu ta daɗe tana addu'a a kai, sunsan ko yanzu tana can tana murna a kabari. "Mercy ina tunanin zamana ya isa haka nan. Ina so in kama sana'a ko wani abu da kuɗi zasu dinga shigo min." Ta kalle ta fuskarta na baiyana rashin jin daɗin maganarta, ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi. "Mary akwai wani abu da kike so ki siya ne ko ki siyawa Bibi baki faɗa min ba shi yasa kike so ki kama business?" "No wallahi ba haka bane, kin ɗauke nauyin duk wani abu da muke buƙata har ma da wanda bamu nema ba. Amma a zaman da nayi cikin hausawa na ƙaru da wani magana da suke cewa da a ba mutum kifi gara a koya mishi yadda ake kamun kifin, kin gane? just kawai zaman haka ya ishe ni, kuma ina so inga nima ina walwala da kuɗaɗe na ko dan in rage miki wasu ɗawainiyan, kinga ga nauyin Bibi ma da har yanzu bata tuna da inda iyayenta suke ba. Ni ko a cikin business ɗinki ki sama min wani abu da zan dinga taya ki da shi..." Dariyar da Mercy ta kwashe dashi shi ya katse Mary daga maganganun da take yi, tsawon lokaci tana ƙyaƙyatawa kamar taɓaɓɓiya kafin ta tsagaita ta ce "Za ki iya yin irin sana'a ta?" "Why not? in dai kin iya jurewa nima ai zan iya." Ta amsa da ƙwarin gwuiwa. "Ok ! yau da daddare zan kaiki gurin Oga. Amma fa indai muka je dole ki amshi duk abinda zai ce miki in ba haka ba zaki mutu. Kin yadda?" "Eh !" Ta amsa ba tare da zurfafa tunani ba. ****** Misalin ƙarfe uku na dare tana gurfane gwuiyawunta a ƙasa gaban ƙaton mutumin da yake zaune a kan wani danƙareren kujera da yake ta walwali yana ɗaukar ido, wasu mutane maza da mata sanye da shuɗayen dogayen riguna sun jeru a gabanshi kamar masu assembly, a kansu ɗaure da jajayen ƙyalle, Mercy tana cikinsu. Da ta hurga idanu lungu da saƙo na cikin gurin sai taga manyan tulu masu kama da tulun giya suna yawo a mabantan gurare su ba a ƙasa ba su ba a sama ba, kuma bata ga wanda yake riƙe da su ba. A matsayinta na sabuwar zuwa ce aka gurfanar da ita gaban Oga dan a karanta mata dokokin ƙungiya kuma a sa mata albarka. "Ba fita har mutuwa... hukuncin kisa mafi muni idan kika yi yunƙurin tona asirin ƙungiya..., za ki yi sadaukarwar jini... kuma duk inda kika shiga a faɗin duniya idanunmu na kanki... Za ki samu duk abinda kike so a duniya, za ki yi fice, za ki yi suna..., amma duk sadda ƙungiya ta nemi abu a gurinki komai wahala za ki bada..." Sautin ƙatuwar muryar da ta karaɗe gurin kenan ba tare da taga wanda yayi maganar ba, tsananin tsoro da fargaba ne ya kamata, mararta ya ƙulle dam da fitsari. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara rawar ɗari, haƙoranta sai haɗuwa suke gaf-gaf. Wani ƙwarya ta gani a gabanta yana yawo shi ba a ƙasa ba shi ba a sama ba. "Ɗauki ki sha dan zama cikakkiyar ƴar ƙungiya." Ƙatuwar muryar ta sake faɗa cikin tsawa. Da sauri ta damƙi ƙoƙon mai ɗauke da wani baƙin abu mai tsananin kauri da wari, da ɗoyi ta kafa a bakinta bayan ta runtse idanunta ta fara kwankwaɗa. "Hhhhhhhhh.... Barka da shigowa cikin ƙungiya Mary... Barka da zama cikakkiyar ƴar ƙungiya Mary..." Abinda ake ta maimaitawa kenan da mabanbantan muryoyi ana ƙyalƙyala dariya. Can kuma muryar ta ɗauke ɗif kamar anyi ruwa an ɗauke. Wannan ƙaton mutumin da take durƙushe a gabanshi ne ya miƙa mata hannunsa da yatsun suke a dunƙule irin na kutare da sauri ta miƙa hannunta ta riƙe nashi hannun. "Kuɗi, mulki, ko suna a duniya?" Ya tambaye ta da siririyar zazzaƙar muryarshi mai kama da ta ƙananun yara. "Kuɗi." Ta amsa da rawar murya. "A cikin seconds biyu ki faɗi sunan wanda za ki sadaukarwa ƙungiya..." "Baba Lauratu." Ta amsa da sauri tun kafin ya rufe baki. "Arzikinki yana tare da ke, wannan yarinyar Bibi ita ce hanyar arzikinki, ita ce zata samar miki suna da ɗaukaka da mulki. Amma sai kin jure, dan zata baki wahala. Duk tsananin wuya kar ki kuskura ki rabu da ita." Yana gama maganar ya sakar mata hannu ya juya bayansa yana wasu surutai masu kama da na tsafi, minti biyu tsakani ya fara ƙwala kiran sunan "Lauratu... Lauratu... Lauratu..." Sai ya haska tafin dungulmin hannunshi a bango. Nan take hoton Baba Lauratu ya baiyana a jikin bangon, tana kwance a kan yar karamar katifarta tana bacci, sai soshe soshe take yi da alamun sauro ne suke damunta. Ta jikin bango ya miƙa dogon hannunshi ya kama agarar ƙafarta ya cisgo da tsananin ƙarfi, nan take ya finciko jijiya da ƙashin gurin ya tara wani ƙaton ƙoƙo ta ƙarƙashin ƙafar jini yana ɓulɓula a ciki.. BILHAƘƘI Tana hakimce a kan wata ƴar ƙaramar kujera da take fuskantarsa, saɓanin duk wasu sabbin shigowa ƙungiyar da ake gurfanar da su gwuiwa bibiyu a gaban Oga ita a zaune take. kuma babu wasu dokoki da aka karanta mata, kai tsaye ya miƙa mata hannunshi duk biyun da nufin ta kama, ƙin kamawa ta yi, a maimakon haka ma sai ta sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannayenta. Bai daddara ba ya sake matsawa kusa da ita sosai ya tura mata hannayenshi jikin nata hannayen, ta ɗago kai a fusace ta kalle shi idanunta jajur, minti ɗaya suna musayar kallo sai kuma ta sake sadda kai ƙasa ta ja wani dogon tsaki kamar bakinta zai taɓa ƙasa. Hannu yasa ya ɗago fuskarta da yake ƙasa suna haɗa idanu wani kakkaifar walƙiya ya fito daga idanunta ya maka shi da jikin bango, da yake shi ma a shirye yake bai bari an watsar da shi ba ya tsaya da ƙafafunsa. Wani ƙaƙƙarfar huci yayi ya kamo ɗaya daga cikin tulunan da suke ta zagaye tsakar gurin ya wanke fuskarsa da baƙin ruwan ciki, yana sakin tulun ya ci gaba da zagaye kamar yadda yake yi da farko shi kuma ya nufe ta gadan-gadan. Hannayenshi duk biyu yasa ya damƙo gashin kanta ta ɗaga ido ido tana kallonshi da idanunta da suke tsattsafar jini a maimakon ruwan hawaye, hannunta ɗaya ya sa a cikin nashi hannun yana ci gaba da kallon ƙwayar idanunta dan neman abinda yake son gani. Tsafi gaskiyar mai shi, wannan magana tabbas haka take. Nan take a cikin ƙwayar idanunta ya ga hoton wata kyakkyawar matashiya a cikin tsakiyar dare, a tsakiyar dokar daji tana ta gudu, a bayanta goye da jaririyar da take ta tsala kuka cikin fita haiyaci. Saida tayi gudu mai tsanani sannan ta cimma wani bukka ƙwallin ƙwal a dokar daji, a bakin bukkar ta tsaya tana haki da sauke zazzafar numfashi, second goma tsakani sai kuma ta fara waige-waige kamar tana tunanin an biyota daga bisani kuma ta afka cikin bukkar da sauri tana ƙoƙarin sauke goyon bayanta. Bata tsaya a ko ina ba sai a gaban wata yanƙwananniyar tsohuwa da take zaune a kan wani gadon kara, tana zaune daga ita sai ɗaurin ƙirji da wani baƙin zanin saƙi, wuyanta kuwa ƙashi ne ƙwara-ƙwara kamar ta shekara biyar tana jinya, gashin kanta fari fat, idanunta ƙulu-ƙulu masu barazar firgita ƙaramin yaro, aje a gabanta wasu manya-manyan sarƙoƙi ne zube da matuƙar yawa masu kama da murjani, gefe da gefenta kuma duma ne a ajiye da wasu luddan duma a kansu an jingina su sun fuskanci gabas. "Re...bec...ca..." Tsohuwar ta kira sunanta a rarrabe fuskarta na baiyana matsanancin mamakin ganinta a daidai irin wannan lokacin. Bata jira komai ba ta aje jaririyar a jikin tsohuwar sannan ta zube a gabanta gwuiyawunta a ƙasa ta haɗa hannuwanta duk biyu alamar roƙo ta fara magana cikin kuka. "Mama Vero ita wannan ƴata ce... ita ce rabon da kika tabbatar min akwaita a tsakanina da Musty. kin daɗe kina bibiyata akan in faɗi abinda nake so ko menene kiyi min saboda Mummy na ta taimake ki, duk tsawon wannan lokacin duk da matsanancin halin ƙuncin da nake ciki a ƙauyen nan ban taɓa roƙonki komai ba. Yau ga ni ina neman abu a gurinki, Pls ki tsare min ita, ki kare ta, ki ɗaukakata a duk inda ta shiga, karki ba wani mutum ikon ya cutar da ita, ki kaita duk inda ɗaukakarta yake, za ki iya, na tabbatar za ki iya, shi yasa na kawo ta gare ki..." Bata ƙarasa aje numfashin maganar ba ta sake tashi ta fice ta runtuma a guje dan komawa inda ta fito... Tsohuwar da aka kira Mama Vero kuwa yarinyar ta rungume a ƙirjinta tana mata wasu irin maganganu da ba a gane me take cewa a cikin kunnenta, wani abin ban mamaki nan da nan kukanta ya fara yin ƙasa har daga ƙarshe tayi shiru sai sauke ajiyar zuwa take yi. Zanin da aka naɗe yarinyar ta warware tana ƙare mata kallo, can kuma sai ta shimfiɗar da yarinyar a kan gadon ta buɗe bakinta tasa yatsarta can ciki ta ɗago ɗan ƙanƙanin harshen yarinyar ta haske da tocila mai tsananin haske, wani tafkeken baƙi ne a jikin harshen yarinyar, minti ɗaya tsakani ta gwale idanun yarinyar tana kallon ƙwayoyin idanun ta cikin madaidaicin haske, wani saɓulallen murmushi ne ya suɓuce mata, ta ɗaga ƙafafun yarinyar sama kanta yana kallon ƙasa ta fara wujijjigata. "Alheri...? welcome back." Tsohuwar ta faɗa cikin ɗaga murya fuskarta cike da murmushi, sai kuma ta ɓarke da wata ƙaƙƙarfar dariya muryarta a buɗe zaƙi cau kamar ta matashiya ƴar ashirin da biyar. Ludayin duman nan ta ɗauki guda ɗaya tayi wani magana ta tofa miyau ta manna a ƙirjin yarinyar inda Mustapha ya tsattsaga da reza, haka taitayi tana maimaitawa har sau uku, da ta haska gurin sai na ga ya dausashe ya bada wani tabo mai kyau alamu na tsohon ciwo. Aje yarinyar ta sake yi a kan gadon karan ta fita waje cikin daren ta zagaya ta can bayan bukkarta ta tatso madarar shanu a jikin wata saniya da take ɗaure ƙwallin ƙwal a gurin ta dawo ciki ta ɗiga wa yarinyar sau uku a baki, zanin da aka naɗe ta da shi ta yayyaga ta ɗaurawa yarinyar a ƙirji kamar yadda ita ma zanin saƙi ne kaɗai ɗaure a ƙirjinta. ****** ****** Sake gyara zamanta tayi a kan ɗan kututturen icen tana kallon yarinyar ƴar kimanin shekara biyu da take ta wasa da wasu tarin dutsuna farare tas, a fili idan aka kalli tsohuwar za a ga kamar yarinyar take kallo amma haƙiƙanin gaskiya idanunta ne kawai a kanta zuciyarta ta cilla ne cikin zuzzufar tunani. 'A tsawon shekaru biyun da tayi tana renon Alheri kamar yadda take kiranta tayi su ne cikin tsuma ta da ɗura mata duk wasu sirrikan tsafi da ta sani, lamarin yarinyar ne yayi mata daidai har ma fiye da yadda take buƙata. A karan kanta ita yarinyar ƴar baiwa ce da aka haife ta da wasu sirrika na tsafi kamar yadda aka haifi kakarta Alheri mahaifiyar Rebecca. Da wannan dalilin yasa ƴan ƙauyen suke ce wa Alheri mayya har daga ƙarshe suka yi gangamin ƙona ta da ranta a lokacin Mama Vero bata nan. Ita Mama Vero ta zame wa mutanen ƙauyen tamkar ƙadangaren bakin tulu ne, a karta a kar tulu a barta ta ɓata ruwa. Matsafiya ce ta gasken gaske wacce da farkon yarintarta ta fara ne da bada magunguna, duk ciwon da ya gagara indai har aka je gare ta ta bada magani cikin hukuncin Allah sai ciwon ya warke, daga nan kuma sai mutane suka lura ai Mama Vero tamkar wata ƴar baiwa ce domin duk abinda tayi hasashen zai faru tabbas komai daren daɗewa zai faru, ta ba mutane magunguna da dama musamman masu neman haihuwa, har daga ƙauyukan da suke nesa da su ana zuwa gurinta karɓar magani kuma a cikin farashi ƙalilan. Wani abin mamaki daga cikin aikinta idan ta kalli mace in zata haihu tana faɗin ta ga haihuwa a tare da ita, idan kuma bazata haihu ba kai tsaye zata faɗa mata kuma ta ƙara da cewar idan zata zagaya duniya tana neman magani baza ta taɓa haihuwa ba. Da wannan dalilin sai mutanen ƙauyen suka maida ita kamar ta biyun abin bautarsu duk abinda zasuyi sai sun nemi amincewarta, idan suka bijirewa umarninta kuwa tana amfani da alƙaluman tsafinta ta tura musu masifu kala daban-daban, kamar fari na abinci, ko cutar amai da gudawa manya da yara suyi ta mutuwa, ko kuma ta lalata duk noman da suka yi a shekarar amfanin gonar sam yaƙi yin kyau ko da kuwa an samu ruwan sama yadda ake buƙata. Akwai aminci mai ƙarfi tsakaninta da Alheri mahaifiyar Rebecca tunma kafin a haifi Rebecca, wata rana Mama Vero tana cikin daji tana tsafe-tsafenta aka sami wani baƙon iskar maciji da ba zaunannen cikin dajin bane ya sare ta, ko kafin tayi wani yunƙuri macijin ya silale ya ɓace daga gurin, tayi duk dabarar da ta sani na magani dafin ya ƙi tsayuwa guri ɗaya, a bincikenta dole sai ta kashe wannan macijin sannan zata samu damar fitar da dafin daga jikinta ga shi tayi neman duniya bata ganshi ba. Har ta fara galabaita sai ga Alheri da macijin riƙe a hannunta ta shaƙe wuyanshi tana ƙoƙarin kashe shi, a gaban Mama Vero ta kashe shi, ba tare da jin tsoron komai ba ta durƙusa ta sa bakinta a inda ya sari Mama Vero ta zuƙo wani kakkauran jini ta zubar, ta yanki naman bindin macijin ta manna a gurin. "Sannu Maa ! ciwon zai warke, zafin zai tafi." Tayi maganar a hankali tana murmushi. Ita ta kama Mama Vero ta raka ta har cikin bukkarta hannunta riƙe da mushen macijin, da zata tafi ta aje mata macijin ta ce kullum ta yanki tsokar jikinshi ta manna a gurin ciwon zaiyi saurin warkewa. "Yarinyata mene sunanki?" Ta tambaye ta tana bin ta da kallon ƙauna da yabawa ƙoƙarin da ta yi mata. "Alheri" Ta amsa a lokacin da take daf da ficewa daga cikin bukkar. A wannan lokacin Alheri tana amarya lamarin ya faru ko cikin Rebecca bata da shi, tun daga wannan lokacin jefi-jefi tana zuwa gurin Mama Vero har ma tana taya ta da wasu aiyukan harhaɗa magani dan ita ma tana da nata baiwar, ko da Mama Vero ta nemi da ta taimakawa Alheri gurin ninka mata ƙarfin baiwar da take da shi ƙin yadda ta yi, ta ce bata so. Istifanus shi ne mahaifin Luka, mijin Alheri, mahaifiyar Rebecca. Ciwo ne mai tsanani ya kama shi tun ranar auren Alheri da Luka, tun a ranar wasu daga cikin mutanen ƙauyen suka fara surutun amaryar mayya ce tunda an auro ta ne daga wani ƙauye da yake nesa da Rimau, sunan ƙauyen gefe, tafiyar mashin ce miƙaƙƙiya daga Rimau har sai an haye ruwa sannan a isa gefe, kuma mutane suna ta hasashen akwai mayu a garin. An yi maganin amma sam ba a dace ba, Mama Vero kuma ta ƙi ba shi magani wanda hakan da ta yi babban alamu ne da yake nuna musu Istifanus mutuwa zai yi. Sai da ya shekara cur yana jinya a ranar da Alheri ta haifi Rebecca a ranar shi kuma ya mutu, abinda ya ƙara dasa wa mutane yarda da cewar Alheri maiya ce kafin ya mutu yana ta kiran sunanta yana mimmiƙewa a zabure har ya tunkuyi burji. Sai kuma suka cigaba da cewa ai Lidiya mahaifiyar su Zidane ma ita ta cinye ta tunda anyi aurensu ba daɗewa ta mutu. Nan fa gaba ɗaya ƙauyen ya ɗauki ƙananun maganganu ita kuwa tana gida rungume da jaririyarta bata da masaniyar abinda yake faruwa har sai da Luka ya koma gidan afujajan yana tuhumarta. "Alheri ki faɗa min gaskiya, ke mayya ce?" Luka ya tambaye ta da jajayen idanunsa cikin fushi da tashin hankali. Matsanancin firgita ne ya kamata, har saura ƙiris ta suɓutar da yarinyar a ƙasa saboda jin tambayar tayi tamkar saukar aradu, bakinta na rawa ta ce "Luka kana cikin hankalinka kuwa? me kake cewa haka?" Ta mayar mishi da tambayoyin tana kallonshi a tsorace, fuskarta ɗauke da matsanancin mamakin maganganunsa. "Daga yadda kika yi da na faɗi maganar nan ya tabbatar min da zargina gaskiya ne, amma baki min adalci ba Alheri. Menene bana yi miki a gidannan?

Chapter 6 of 25