spirit din Alheri zai kashe kowa a kauyen nan."
Wani dunkulallen bakin ciki ne ya kawo mishi naushi a kahon zuci, ya so kwarai a ce yau ya shafe babin Rebecca daga doron k'asa. Da ya kalle ta a zuciye sai yaga tana mishi wani murmushi mai kama da na rainin hankali. Ta motsa bakinta a hankali ta ce
*"I'm a Muslim"*
Tsabar rud'ani yasa ya sandare a tsaye a gurin, sauran abokan tafiyarsa kuwa suka fara kwance Rebecca dan cika umarnin Pastor Nuhu.
[12/12, 11:58 PM] Bilhaqqi: *BILHAQQI*
**** ***** ****
Ya kalle ta da wani irin tattausan murmushi, da idanu mai cike da rahama irin wanda tun da aka haife ta bai ta6a kallonta da irinsa ba.
"Rebecca yarinya na"
Ya kira ta a tausashe, bai jira ta amsa ba ya cigaba da jero mata dad'ad'an tausasan kalamai kamar yadda Pastor ya umarce shi.
"Rebecca ! i'm your father. Duk da kike gani kamar mun tsane ki muna son ki sosai, addinin cristianity shi ne asalin addininmu tun iyaye da kakanni. Kina ganin kin kyauta kenan ki bar addininki ki koma wani addini na k'arya? Addininmu shi ne addinin gaskiya, addinin da idan kin mutu Yeso zai daukake ki ki shiga paradise, ki hadu da mahaifiyarki Alheri.
I'm sure ko Alheri yanzu haka da zaki ganta a kabarinta tana fushi da ke, saboda kin bar addininki na cristianity. Ki tuba, ki dawo cikin addininki, ki roki Almasihu ya yafe miki laifukan da kika yi mishi a baya, ki gina sabuwar rayuwa a gaba, Idan kika yi haka mu kuma zamu nuna miki soyayya, za mu baki mukami mai girma a church.
Zidane ma yayi alkawari zai karbe ki as a luvly Sister, zai ji da ke, zai baki kulawa a duk inda kike a kauyen nan.
Pls my dear, ki zàma yarinya mai biyayya, kar kibi zugan wancan shegen mijin naki da ya dad'e da mutuwa, daman bai dace da aurenki ba, he is a muslim, yana kan addinin 6ata ne, shiyasa ko gurin mutuwarsa yayi mummunan mutuwa. Ke kuwa da Yeso yake sonki da shiriya kinga ya tserar da ke, ki dawo kan addinin gaskiya ki bi maganganun littafi mai tsarki."
Yana kaiwa nan a maganarsa yayi shiru yana nazarin yanayinta, zuciyarsa cike da fatan ta amince kuma ta yarda tayi duk abinda ya umarceta. Dukda ba kaunarta yake yi ba sam ba ya fata a ce ta sanadin 'yarshi aka samu gur6acewa a cikin tarihinsu na iyaye da kakanni, dan ko a garin suna daga cikin familyn da aka sansu da tsananin riko da addinin kirista.
A hankali ta dago manyan idanunta da sukai luhu-luhu saboda kuka da tsananin wahala ta kalle shi, ya sake sakar mata wani tattausan murmushi da wafcecen bakinsa.
Ta maida idanunta kan Zidane da yake tsaye a bayan mahaifinsa, idanunsa cike da matsanancin tsanan da yake mata amma yana kokarin boyewa. Fuskarsa dauke da murmushi mai hade da dariya. Gaftara-gaftaran hakoransa suka baiyana a waje kamar zai cinye ta d'anye, amma shi ala dole dariya yake mata.
Ta saukar da idanunta sai suka sauka a kan farantin abincin da suka ajiye mata, farar shinkafa ce k'al da miyan stew, a gefe guda kuma aka zuba mata hadin ganyayyaki da tsokokin nama soyayye manya-manya
"Idan kika bi abinda na ce miki irin wannan delicious din i promise har karshen rayuwarki shi zaki dinga ci..."
"Daddy !"
Ta katse shi cikin zafin rai, runtse ido tayi dan jin wani azababben zafi da ya ziyarci kumburarren bakinta saboda maganar da ta yi. Saida ta d'an numfasa bakin ya rage zafi ta daga kai ta kalle shi ido cikin ido, fuskarshi na baiyana matsanancin fargabar abinda zai fito daga bakinta, ita kuma idanunta ciccike da hawaye.
"Idan zaku bani duk abinda kuke da shi bazan bar musulunci ba. Ni musulma ce, daga yau sunana ba Rebecca ba, sunana Khadeeja Mustapha..."
Wani gigitaccen tsawa da ya daka mata dole ta hadiye sauran maganar a cikinta, ya daga hannu zai zabga mata mari ya ji an rike hannunsa. Cikin fushi da tsananin mamaki ya juya dan ganin mai karfin halin da ya hana shi tattaka Rebecca, sai yayi ido biyu da Pastor Nuhu.
"Luka calm down. Ka manta abinda na fada maka?"
Bai jira ya amsa ba ya ja daya daga cikin kujerar robobin da suka yi wa falon kawanya ya matsa kusa da Rebecca ya zauna.
"Rebecca, dukda mahaifiyarki mayya ce har ta mutu bata bar addininta na Christianity ba. Kin amince zaki dawo cikin addininki?"
Da kai ta amsa mishi alamun a'a, idanunta ciccike da hawaye.
"Ok ! Thats good. Baza mu kashe ki ba. But zaki yi rayuwa ne tsakanin mutuwa da rayuwa har zuwa karshen rayuwarki. Dakin duhu da yake cikin church a nan zaki zauna har karshen rayuwarki. Kullum za mu baki abinci sau daya dan kar yunwa ta kashe ki. But duk lokacin da kika ji a ranki zaki iya dawowa addinjnki na Christianity za mu baki 'yanci."
Daga haka bai sake ce mata komai ba garadan samari suka cicci6eta kamar kayan wanki suka kaita inda ya basu umarni.
Zuciyar Daddy Luka da Zidane cike da matsanancin bakin ciki, sun so kwarai su samu damar karar da rayuwarta a wannan lokacin.
*****
Sai da ta kalle ta da kyau ta tabbatar tana kallonta, ta yi wani murmushi mai kama da na mugunta, ta mike da tak'ama tinkis tinkis ta isa gaban kulolin abincin.
Faranti ta dauka da luddayin diban abincin ta fara bude kulolin abincin, duk da tashin k'amshin da miyar taushen yake yi yamutsa fuska ta fara yi kamar ta shak'i wari. Wainar da yayi kyau shar kuma yayi tashi su6u su6u ta dauki guda biyu kacal ta zuba a farantin, maimakon ta dibi miyar kawai sai ta d'auki jug din tangaran da yake cike da had'in sassanyar jinja, kamar zata tsiyaya a kofi kawai sai ta saki Jug din da gangar ya fadi a k'asa. Nan take kuwa ya tarwatse.
Ta saki wani k'ayataccen murmushi tana kallonta, ta yamutsa baki da fuska ta ce
"Sai ki dau na annabawa, wannan ma ya bi ayarin 'yan uwansa. Ya riga mu gidan gaskiya..."
"Kan uban can! Uban kuturu ma yayi kadan ballantana na makaho, idan kin isa Allah ya tsine min."
Kamar kububuwa ta tura kujeran teburin cin abincin da take zaune ta mike a fusace ta zagaya ta gurinta. Cikin tsananin masifa ta cigaba da magana bakinta har yana tartsatsin miyau, ko tsoron ta taka fasasshen kwalbar Jug din bata yi.
"Ke Suraiya bari in fada miki, shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne. Na ga alamar sai mun goge raini tsakanina da ke a gidannan, ki bar gani na haka-haka idan zamu kwana mu yini muna ba hammata iska ko kwarzane baki isa ki yi min ba. Wallahi ko ki biya ni dubu biyar din jug dina ko inyi miki magagan dukan kawo wuk'a a gidan nan, in daki banza a banza in daki kud'i na..."
"Ni... Wace ni in had'a jiki da kishiya? Baki da labarin hakan tsiya yake janyo wa? Ke dai da kike matsiyaciya kije can ki nemi dai-dai da ke amma ni na fi karfinki."
Ta fada hankalinta a kwance, sai karkad'e-karkad'en kafad'u take yi kamar tana ji fitsari.
Haushi, takaici, wani dunkulallen bakin ciki da suka hade guri daya suka kawo mata naushi a kahon zuci yasa tayi kukan kura ta mika hannu biyu da nufin ta cakumo Surayyan sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Da mugun sauri ta ja baya, hakan da tayi yasa ta taka wani fasasshen kwalba dukda akwai tattausan silifas a kafafunta saida ya huda takalmin ya ratsa kafafunta.
"Ahhhhh !"
Ta fada cikin jin zafi ta durkushe a gurin tana kokarin kamo kafar ta duba. Ba tare da ta lura ba ta sake dafa hannunta daya a kan wani kwalbar, kwalla kara ta yi ta dago a zuciye ta kalle ta.
"Rabi baki da hankali ko? kina so ki hallakani ne?"
kafin ta amsa mata ta ji shigowar motar mai gidan, kwafa tayi tana murmushin jin zafi,
"Zaki gani, tabbas zaki biya wannan"
Tana jin ya kashe motar ta bude baki da matsanancin sauri ta kwallah ihu mai tsananin karan da yake barazanar fasa dodon kunne.
Ita kuwa Rabi sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, dukda ta san Surayya gwana ce gurin makirci bata zaci abin nata ya kai haka ba, da ta kalli fuskarta sai taga har ta jika shi da ruwan hawaye.
A daidai lokacin ya sanyo kai cikin falon da sassarfa bakinshi dauke da sallama, hankalinshi yana kan Surayya da take durkushe a kasa tana kuka, ko da Rabi ta nufe shi tana kwarkwasa da yi mishi sannu da zuwa sakar mata jaka da ledojin hannunshi kawai yayi bai kalle ta ba ya nufi Surayya.
"Menene? me ya faru?"
Yana ganin fasassun kwalaben yaja da baya da sauri
"Subhanallahi, me ya faru haka?"
Yayi tambayar yana kallon Rabi da manyan idanunsa masu cike da tuhuma.
Ranta a ɓace, fuskarta a cunkushe, zuciyarta a ƙuntace da irin wannan cin mutuncin da yake gwada mata a gaban kishiyarta. Ta dai daure ta cije tayi ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta, ta buɗe baki zata yi magana Surayya ta riga ta fara magana cikin kuka
"Sweetat wai fa kawai dan na ture mata jug ban sani ba ya fashe shi ne tace sai na biya ta. Na fara bata hakuri da gangar ta hankaɗa ni cikin fasassun kwalaben, ka ga har na huda ƙafa da tafin hannuna..."
Ta ƙara fashewa da kuka tana nuna mishi hannun da yake ta tsattsafar jini.
Mugun kallo ya watsa wa Rabi, a hankali cikin takatsantsan ya ƙarasa gurinta ya ɗaga ta tsaye, cikin hila ta langaɓe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa.
"Ki tabbatar kin gyara gurin nan kafin in kaita asibiti in dawo."
Bai ƙara kallonta ba yaja ta a hankali suka nufi dakinta, minti biyu tsakani suka fito yana riƙe da ita a kafaɗunsa a hankali suka nufi hanyar fita daga falon. Ita kuwa poster tayi tana kallonsu fuskarta cike da hawaye, zuciyarta sai lugude take yi kamar zata faso ta fito fili.
Sai da suka kusa fita daga falon ta waigo ta kashe mata ido ɗaya ta yi mata gwalo. Ta sake rukunkume shi tana faɗin
"Wash ! Sweetat zafi"
Nan ya sake tarairayota jikinsa yana jera mata sannu kaman zai ari baki.
Tana jin tashin motarsa ta ɗora hannu biyu a kai ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka, kamar mahaukaciya ta fara watsi da ƙananun kofunan da Surayya ta fasa jug dinsu.
**** **** ****
"Ke ! har kin isa ince ga abinda zanyi ki ce min ga abinda kike ga ya kamata inyi?"
Tayi mata tambayar cikin mamaki tare da zazzare mata idanu. Bata ba ta damar kare kanta ba ta ci gaba da zazzaga mata ruwan masifa tana hakimce akan kujera mazaunin mutum biyu ta dora kafa daya kan daya. Sai jijjiga kafar take yi alamun jira take yi a taɓa ta tayi bindiga.
"Ke wacece ? yaushe kika zo gidannan? to kashaidi na farko kuma na ƙarshe kar in sake yin magana a gidannan ki tsoma min zumɓutun bakinki, a gidannan da kika ganni zaman kaina nake yi. Ko Madam Mary bata isa ince ga abinda nake da ra'ayin yi ta hana ni ba balle ku ƙananun ƴan iska. Idan kunne ya ji rayuwarki ta tsira. Ina fatan kin fahimce ni?"
Da sauri ta dinga ɗaga kai alamar ta ji, da rawar murya ta dinga jera mata kalaman ban hakuri kamar me fadanci.
"Ki yi hakuri Bibi, Allah ya huci zuciyarki. Ki yafe ni, in Allah ya yarda bazan sake ba. Allah ya baki hakuri."
"Dallah ɓace min da gani shashasha kawai, kina wani sussunkwi da kai siffar tsoffin munafukai."
Ko kafin ta rufe baki ma har Nafsi ta kusa shigewa cikin ɗakinta. Ta bi ta da harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa, tsawon wasu daƙiƙu ta kauda kanta ta dawo da kallonta ga sauran mutanen cikin falon, ganin kowa yana harkar gabansa yasa ta ja wani dogon tsaki, ta yi ƙwafa, sannan ta maida hankalinta kan wayar da yake hannunta.
Madam Mary da duk abinda yake faruwa tana zaune a gurin amma ta yi kamar bata a gurin, zuciyarta ne ya ƙara cika da tumbatsa da tsananin tsanar Bibi, amma da yake gogaggiyar ƴar duniya ce kuma mace mai tsananin wayau ko kaɗan bata bari hakan ya baiyana a fuskarta ba.
Ta kalli wasu saffa-saffan ƴan mata da suke zaune su huɗu suna buga karta ta ce.
"Rose ku je ku shirya mana lokacin fa yana tafiya."
"To Madam !"
Suka amsa cike da ladabi. Suka tattara katunan suka shige cikin wani ɗaki da Bello makeover yake cancaɗa musu kwalliya su dawo ƴan cararas kamar sabbin ƴan matan da aka ƙyanƙyaso daga leda.
Madam ta maida hankalinta kan Bibi fuskarta yalwace fal da murmushi.
"Umm na ce Bibi..."
Ta ɗago a lalace tana kallon Madam ɗin, ganin ta kasa ci gaba da magana yasa ta ce
"Ina jinki Madam"
"Ina ga ya kamata ki daina faɗen irin wannan maganar a gaban yaran nan, kar girma na ya zube a gabansu."
"Wace magana ke nan?"
Tayi tambayar da alamun rashin ba maganar muhimmanci, sai ma ta cigaba da daddanna wayarta.
"Cewar da kike yi ko ni ban isa in hana ki abinda kika yi niyya a gidannan b..."
"ƙarya na faɗa ke nan?"
Ta tambaye ta bayan ta ƙure ta da kallo.
"A'a ! ba ƙarya kika faɗa ba"
Ta amsa tana ɗage kafaɗu sama, alamun maganganun basu ɓata mata rai ba. Ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.
"Ayyo... na zaci ƙarya na yi yanzu in tabbatar miki da gaskiya"
Tana gama faɗin haka ta yunƙura ta miƙe tsaye ta fara takawa kamar wahainiya, sassan jikinta suna motsawa a hankali kamar wahainiya.
"Amma ni ma na shinshini ƙamshin gaskiya a maganar Nafsi, waƙar da kika zaɓa tsohon yayi ne da aka fara mantawa da shi, ga sabbin waƙoƙi nan zafafa da aka yi su a cikin kwanakin nan ina ga za su fi ɗaukar hankalin Mazaje..."
"Na fasa casun, ki nemi wata a cikin ƴan matanki ta hau role ɗina"
Tana gama faɗin haka ta fara cire sarƙoƙin gwalalan da aka maƙala mata a kyawawan ƙafafunta da kunnuwanta tana watsi da su a tsakar tangamemen falon, wani abin ban mamaki shi ne fuskarta cike yake fal da murmushi take aikata hakan.
"Madam lokaci yayi fa, tunda babu african time ya kamata Bibi tana can yanzu. Yau an samu masu siyan tickets sosai jin Bibi ce zata yi rawa, mun daɗe bamu samu customers irin haka ba."
Jamus ya faɗa wa Madam yana tsaye daga bakin ƙofa, ganin da yayi Madam bata amsa shi ba ta yi suman zaune yasa ya maida hankalinshi inda take kallo, sai a lokacin ya lura da abinda yake faruwa.
"Bibi me yake faruwa ne haka? kar dai kice min yau ma yarfa mu zaki yi...?"
"ƙwarai ! hakan nake nufi"
Ta katse shi har lokacin bata daina murmushi ba.
Da sauri ya shiga cikin falon ya tsaya kusa da Madam ya fara magana fuskarsa cike da damuwa.
"Haba Bibi wannan ba girmanki bane fa. Ban sanki da magana biyu ba karki fara daga yau.
Duk masu siyan tickets babu wanda ya siya ƙasa da dubu biyar saɓanin mu da mukai niyyar saidawa dubu biyu. Minista Yugi dubu hamsin ya ca ke mana kuɗin tickets dan kawai ya ji ke ce zaki yi rawa"
Ya jero jimlolin cikin tashin hankali bakinshi yana karkarwa, shi kaɗai yasan lagwadar da yake sharɓa a gurin manyan Mazaje masu ƙumban susa duk ranar da Bibi tayi rawa, mutuwar sonta suke yi ita kuma tana yanƙwana su, da shi ne kawai idan aka yi kamun ƙafa ake samun damar ganawa da ita na ƴan wasu daƙiƙu ƙalilan.
"Ba ka da damuwa Jamus, Rose zata hau matsayina. Ta iya duk wani girgiza da zanyi ƙila ma ta fini ƙwarewa. Ku shirya komai da Madam ni bari in shiga ciki."
Tana gama maganar ta hurga mishi belt din da ta ɗaura a saman ɓingilin sket ɗin da yake jikinta shi kuma ya ca fe, santala-santalan cinyoyinta duk a waje ta fara hawa matattakalar benen tana ƴan waƙe-waƙenta zuciyarta cike da nishaɗi.
Da sauri ya zunguri Madam Mary da take zaune kamar mutum-mutumi, ranta a ɓace, ya ƙale mata ido ɗaya yayi mata alamun ta yi wa Bibi magana in ba haka ba asara zasu yi.
"Bibi...!"
"Kar ki ce komai Madam. Kiyi shiru kawai."
ta katse ta tana riƙe da ƙarfen benen. Ta juyo tana kallonsu amma bata sauko ba, a wannan lokacin fuskarta a ɗaure ne tamau, idanunta har sun fara canja launi.
"Yau fa ina tabbatar miki Galar taki baza ta yi armashi ba, casun ma baza a yi ba. Rikici sosai za a yi, dan haka yi ta kanki tun kafin a yi kisa a gidanki"
Bata ƙara kallonsu ba ta haye saman ta shige ɗakin Madam tayi kwance ɗai-ɗai a makeken gadon da ya mamayi fiye da rabin ɗakin.
Wayarta ta janyo a zabure ta danna kiran wata lamba, sai huci take yi kamar kububuwa tana ta jan tsaki akai-akai.
"Madam lokaci ya cik..."
"Jamus dan Allah ka barni inji da abinda yake damuna. Baka ji abinda Bibi ta ce bane? kasan duk abinda tayi hasashen zai faru tabbas sai ya faru. Kaje ka sallami mutane kafin ta janyo mana wani bala'in."
Ta ƙarasa maganar cikin tsawa da hargagi.
"Yanzu Madam duk kuɗaɗen da muka karɓa..."
"Ka wuce ka mayar musu da kuɗaɗensu ka sallami kowa na ce..."
A daidai lokacin kuma kiran wayan da take yi ya shiga, aka ɗauka daga can ɓangaren, bata jira an fara magana ba ta fara magana cikin ɗimauta.
"Oga ! Bibi tana so ta janyo min masifa. yanzunnan ka bani makarin duk wata masifa da yake shirin tunkaro Gala ta a yau..."
"Ki bata haƙuri, ki saka ta dariya, ki bata farin ciki duk a lokaci ɗaya. Yanzunnan fa kafin lokaci ya ƙure miki."
ƙit ya kashe wayar ba tare da ya sake saurarenta ba.
'Bibi ! Bibi !! Bibi !!!? Amma anyi ƴar iskar yarinya shaiɗaniya, wallahi in banda Oga ya tabbatar min haske na yana jingine da wannan yarinyar da tuni na daɗe da turɓuna hancinta a cikin ƙasa. amma ba komai, lokacinki ne yarinya, ki yi komai ba komai, akwai ranar ƙin dillanci."
Ta ƙarasa zancen zucin da yin ƙwafa, ta ja wani ƙaramin tsaki, da sassarfa kuma sai ta fara hawa matattakalar benen dan zuwa gurin Bibi.
"Oh ni Jamus ! ko me yasa Madam take tsoron Bibi?"
Yayi maganar a fili yana ƙara leƙen Madam Mary da ta kusa ƙule wa ganinsa, ya mele baki guri ɗaya kamar mace, tunda ta haura a zafafen nan ya san rarrashinta zata je yi.
Daman tunda ta kora shi da cewar yaje ya sallami mutanen da suka sai tickets ya maƙale a jikin tangamemen ƙofar falon yana tufka da warwara da tunanin waƙar farawa.
'Mutane sunfi ɗari da suka sai tickets da manyan kuɗaɗe ta ina zai fara mayar musu da kuɗaɗensu...'
Hayaniyar da ya ji yana tashi sama-sama daga can cikin gurin rawar yasa ya zura da gudu dan ganin abinda yake faruwa, ƙirjinshi sai bugun tara-tara yake yi.
Kiciɓis mugun gamo yayi da tantirin ɗan sara sukan nan Yusuf Guba da tawagarsa suna ta farfasa kwalaben giyan da aka jera a gurin karɓar kayan shaye-shaye suna jifa kan mai uwa da wabi.
Mutane da ma'aikatan gurin sai guje-guje suke yi suna neman matsera, ga tangamemen ƙofar shiga gurin a buɗe amma ruɗu da ɗimauta yasa sai zagaye suke yi a guri ɗaya da ɓuya a ƙarƙashin kujeru sun kasa ficewa waje.
Wata makekiyar fasasshiyar kwalba da aka kawo jifa tush kake ji a goshin Rose da ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar da suke shiga ta ciki ta yadda zasu ɓulla a gaban jama'a cikin tsinanniyar shigar kwata sutura rabi da kwata tsiraici, tana yaye ƙayataccen labulen da ya hana mutane ganin ƙofa ne ta samu nata rabon.
"Ahhhh !"
Ta ƙwalla wani gigitaccen ƙara ta zube a gurin a sume. ƴan matan da suke biye da ita a baya da mugun gudu suka koma ta ƙofar da suka zuwa cikin falon suna iface-iface.
"Hey ! Ko a fito min da babban maƙiyi na Ɗan filulu da na samu labarin shigowarsa cikin galar nan minti talatin da suka wuce ko kuma in farke cikin kowa da yake nan gurin. Kowa ya tsaya a gurin da yake..!!"
Ya ƙarasa maganar cikin wata gigitacciyat tsaww da ƙatuwar muryarsa mai kama da an tada babban injin markaɗe.
Cike da mugun tsoro kowa ya ƙame a gurin da yake, masu raunanniyar zuciya kuwa nan take suka fara sakin fitsari a wando. Can na hangi Jamus da wasu mutane kwance cikin jini suna gurmususun azaba.
Yadda Madam ta ga idanun Bibi a rufe amma tana far-far da su kamar mai shirin buɗe su yasa ta san aiki ya kwana, wani irin ƙaƙƙarfar numfashi take ja kamar mai sauke ajiyar zuciya yasa ta cije baki cikin takaici, wannan alama ce da yake nuna Bibi tayi mugun nisa a cikin barci kuma tashinta wani gaggarumin matsala ne. A zuciyarta tayi ƙwafa, ta kai wawura kamar zata shaƙo wuyan Bibi wani tunani mai walƙiya da ya gilma a zuciyarta yasa ta kaiwa filon da yake ajiye a gefen Bibi raruma.
Ihun da Rose ta ƙwalla ta jiyo sama-sama dan haka ta fita a guje ko nauyin jikinta bata ji.
"Nafsi, Liyat lafiya? me yake faruwa ne yau a gidan galar Madam?"
Ta riƙe ƴan matan biyu tana tambayarsu a ruɗe.
Ko kafin su amsa mata ta jiyo ƙwaƙƙarar muryar Yusuf Guba yana sauke musu zazzafar kashedi, daga bisani ta ji ƙarar watsewar kayayyaki ratsatsa a cikin gurin sannan aka karci bango da wani kakkaifar wuƙan da ko da bata gani ba ta tabbatar gayawa jini na wuce ne.
Wani wawan sufa sukayi a tsorace sai ga su a bayan kushin sun dunƙule guri ɗaya suna makyarkyata.
"Akwai waya a jikinku?"
Madam ta tambayesu cikin raɗa tana kallon yadda tsabar gudu da rige-rige yasa ɗan kamfan jikin Nafsi ya baiyana.
Kamar ƙadangaru suka ɗaga mata kai alamun babu.
Aljihun ɗamammen wandon jikinta ta fara lalubawa cikin sa a kuwa ta ji wayarta a ciki, da sauri ta rarumo ta fara kiran lambar da duk hannunta ya sauka a kai, jimlar magana ɗaya kawai take nanatawa da an ɗauki wayar.
"Taimako !!! daga gidan Galar Madam Mary ne. Ku kira mana ƴan sanda Yusuf Guba ya rutsa mu a ciki zai hallaka mu"
*BILHAƘƘI*
Cikin mintunan da basu wuce goma ba jiniyar motocin ƴan sanda har guda uku suka cika unguwar zame wando na garin Kachia local govt.
Kai tsaye gidan Galar Madam Mary suka nufa da yake ba ɓoyayye bane a unguwar.
A lokacin Yusuf Guba ya gama bincike duk mutanen cikin gurin amma bai samu Ɗan Filulu ko ɗaya daga cikin yaransa ba.
"Duk ku kwanta a ƙar ɗaya bayan ɗaya zamu biku da yankan rago. Na san wani munafukin ne a cikinku ya faɗa masa ina cin hanyar zuwa shi yasa har ya samu nasarar samfewa ban kama shi ba, to a jikinku"
Ya ƙarasa maganar cikin fushi da hargagi, nan ya ba yaransa umarni suka farfasa duk wasu sauran kayayyaki masu amfani a cikin gurin, suka kwashe kuɗaɗen da aka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 25