Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
******* A lalace cike da sanyin jiki haka yake tuƙa motar har ya isa gidan. Ko da yayi sallama ya shiga ciki damuwar da yake ciki ne ya hana ya karanci yanayin da fuskokinsu suke ciki. A sakarce duk su biyun suka yi mishi sannu da zuwa, basu jira amsawarshi ba suka ƙara mayar da hankali kan kallon da suke yi. Shi ma yana amsawa ya nufi ɓangarensa, ko da ya shiga ɗakin cike da kasala ya zauna a gefen gado yana jiran shigowar Surayya ta haɗa mishi ruwan wanka, tunda ranar girkinta ne. Ganin shiru bata shigo ba kawai sai ya faɗa banɗaki ba tare da wani damuwa ba. Jikinsa a mace yake, ga wata muguwar kasala da gajiya da take nuƙurƙusarsa. So yake ya kwanta da wuri saboda tafiyar da take gabansu gobe. Yana fitowa ya ga Surayya tsaye ƙyam a tsakar ɗakin, ya kalle ta kawai, ita ma shi ɗin take kallo. Sai a lokacin ya lura da kwantaccen damuwar da ke kan fuskarta, amma saboda bai shirya fuskantar wata damuwar ba bayan wacce yake ciki mazewa yayi. Ya watsa mata taurarin murmushi ya wuce ta ya nufi gefen gado ya zauna, hannunsa riƙe da ƙaramin tawul yana goge ruwan kansa da kafaɗunsa. "Idan ka gama ga abinci can yana jiranka..." "A'a Alhamdulillah! na ƙoshi a gidan Malam." Ƙanƙance idanu tayi cike da masifa, ɓacin ranta sai ƙara hauhawa yake yi, kwanaki biyar kenan tun da ya tsiri tafiya bauchi har yaje ya dawo yana wani wofintar da su a wulaƙance. "Ki shirya min kayan tafiya gobe da su Malam za mu sake komawa Bauchi..." "Bauchi kuma? bayan tafiyar da kuka yi rannan?" Ta tambaye shi cike da gatsali da rashin kunya. "E" Ya amsa ba tare da damuwa da yanayin yadda tayi maganar ba. "Madallah! To muma mu shirya ka tafi da mu ke nan...?" "Ina ɗin? A kan me zan tafi da ku?" Ya tambaye ta yana kallonta da mamaki, zama sosai ya gyara a gefen gadon yana fuskantarta da jiran jin da wacce ta zo. Ya lura da take-takenta tsiya take ji, shi kuwa zai sauke mata duk wani abu da yake damunta. "Can Bauchin, ko kana tunanin bamu san wancan tafiyar da Amaryarka ka tafi ba? Maheer wai me kake nufi da mu ne? Idan ka fara gajiya da mu ne tun kafin Amaryarka ta shigo gidannan ka sanar damu kawai. Ni gaskiya bazan iya zaman wulakanci da bandaro ba. Atoh! Tafiya ce ko dai gobe ka tafi da ni ni mai girki ko kuma kaima ka fasa tafiyar ka zauna a gida ka bani hakkina." Tana zuwa nan a maganganunta kawai sai ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka ta zube a tsakar ɗakin tana rerawa kamar karatu. Shi kuwa kallonta kawai yake yi da mamaki, ashe Surayya ma fitsararriya ce bai sani ba. Lallai ya yarda ko wane gauta ja ne sai dai in bai sha rana ba. Wani ɗan tunani da ya gilma a zuciyarshi yasa shi sakin murmushi, ya fara magana a tausashe "Kina tunanin ko da muka je can ɗin wani hutawa muka yi ni da Tatlim? Hmmm! Rashin sani ya fi dare duhu. Any way! Shi ke nan! Ki faɗawa Rabi ta shirya ke ma ki shirya goben mu tafi gaba ɗaya. Ku shirya da wuri don Malam ya ce tafiyar sassafe za mu yi." A hankali ta ke rage sautin kukan kamar ana control ɗinta da remot har ta ɗauke sautin kukan gaba ɗaya. Ta miƙe tsaye bakinta a gaba ta fice daga ɗakin tana gunguni "Oho dai! Idanma tsananin wahala kuke sha a can ɗin muma a je damu mu sha tare." Shi dai ya raka ta da idanu har ta fice daga ɗakin gaba ɗaya. Murmushi ne ya sake kuɓuce mishi. "Mata? Hmmm! Sai a barsu da halinsu." Shiryawa ya ci gaba da yi har ya gama shirin bacci gaba ɗaya ya bi lafiyar gado, yayi mamaki da har ya kwanta bata shigo ba. Da yake yana tare da gajiya bai bari yayi zurfi a tunanin ba nannauyan bacci yayi awon gaba da shi. A can babban falo kuwa Surayya da Rabi sun daɗe suna shirya yadda idan aka yi tafiyar za su haɗu su cusgunawa Billhaƙƙi. "Ki ƙyale shegiyar yarinyar nan, da ƙafafunta sirara kamar ragowar amai da gudawa. Har fa yana wani ce min ba daɗi suke ji a can ɗin ba. Kila ko yana tunanin bamu san ƙanwar kakansu ita ce matar sarkin bauchin ba. Don Allah ina wata wahala da za a sha a kaiwa matar sarki ziyara?" "Ke ma dai Surayya kamar baki san rainin wayau na ɗa namiji ba? Ai tsabar dabara ce yake neman shirya miki. Yayi tunanin ko za ki ce mun hakura da tafiyar. Ai yau kam kin gama burgeni, aikinki yayi kyau, daman ke ce kike mishi lakwa-lakwa yana taka mu yadda yake so. Tuntuni da mun haɗa kai ai wallahi da ba haka ba..." "Ai yanzu duk wani batun rikici a tsakaninmu ya ƙare Rabi. Tunda an kawo wata rikicin me za muyi? mu haɗa kai mu kore ta tukunna sai mu cigaba da bugawa a tsakaninmu." Dariya suka kwashe da shi gaba ɗaya, suna tuna yadda da suke yawan faɗa a tsakaninsu kamar masu ganin hanjin juna. "Ke muje fa mu shirya kayanmu mu kwanta, dan ya ce gobe tafiyar sassafe za a yi inji Malam." Daga nan suka yiwa juna sai da safe ko wacce ta nufi ɓangarenta, zukatansu cike fal da farin ciki. ******* ******* Sauri-sauri ta shirya saboda kusan duk an gama shiryawa ita ake jira, ba wani kwalliya mai yawa ta yi a fuskarta ba, ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ya sai mata kwanakin baya ta zura ta naɗe mayafin. Sosai ƴar doguwar fuskarta tayi kyau, dukda dai ta ɗanyi fayau alamun ramewa saboda rashin lafiyar da ta yi, don har lokacin wuyanta da kafaɗanta basu gama warkewa ba. Tana fita falon tayi turus ta tsaya tana kallonsu, suma ɗin ita suke kallo tunda fuskokinsu na saitin ɗakin da ta fito ne. Wani ɗan murmushi tayi da sassarfa ta nufi gurin Aisha matar Luƙman. "Aunty Aisha ina kwananku? kun ƙaraso ashe? Sam banji shigowarku ba." Da fara'a Aishar ta ke amsa mata gaisuwar, su kuwa fuskewa suka yi ko wacce ta ɗauki wayarta tana daddannawa, sun sha kwalliya na ƙure adaka kamar masu shirin halartar gasar zaɓen sarauniyar kyau. Sai yatsune-yatsune suke yi alamu dai na tsananin wulaƙanci. Ita ma da yake ta fi su gigi suna gama gaisawa da Aisha bata ƙara kallonsu ba ta wuce ɗayan Bedroom ɗin Ummee inda Mamanta ta ke. Ganin yadda Rebeccah tayi kyau cikin doguwar rigar atamfa ba ƙaramin daɗi ya tsunduma zuciyar Bilhaƙƙi a ciki ba. Duk wannan tsufa da lalacewar da ta yi kashi talatin da biyar sun ragu cikin ɗari. Ta ƙarasa cikin ɗakin da sassarfa ta rungumeta tana dariya "Mamata kinyi kyau sosai wallahi, kamar ba ke ba. Anya ma idan Babana ya ganki zai gane ki kuwa?" Zare idanu ta yi tana dariyar ita ma, ta ɗago fuskar Bilhaƙƙi suna kallon juna da murmushi a fuskokinsu, sai kuma idanun Rebeccah ya cicciko da hawaye "Baby Billhaƙƙ a wancan lokacin da Babanki ya aure ni kamar ke nake, kyau da dirin jiki, gayu da kwalliyar sosai ni kika biyo. Idanunki da bakinki ne kawai irin na babanki. Amma exactly ke kamar ni ce da nake yarinya. Ko a yanzu ma Babanki zai sake so na a karo na biyu? kila ma yayi aurenshi ya auri hausawa yarinya ba kamar ni da na tsufa ba." Sai hawaye suka zubo mata shar! Gwanin ban tausayi. "Oh noo! Kar kiyi kuka Mamana. Malam ya faɗa min har yanzu Babana yana tsananin son ki. Har fa sun saka anje can ƙauye nemanki, da ba'a same ki ba har yanzu yana can yana ta damuwa da addu'ar Allah ya baiyana mu ni da ke. Wannan ai babban alamu na soyayya ce ko?" "Eh Baby ta." Ta amsa zuciyarta cike da jin daɗin maganganun. Ummee ce tayi sallama ta shiga cikin ɗakin hannunta riƙe da kofi ta haɗo kakkauran tea a ciki, ɗayan hannun kuma riƙe da plate an zuba soyyyen dankalin turawa da ƙwai a ciki "Ummu Bilhaƙƙi ga tea ki sha. Kinsan fa mikakkiyar tafiya ce a gabanmu. Malam ya ce kowa ya karya kafin a ɗauki hanya." "Na gode Hajiya, Allah ya saka da alkhairi." Bata saurari godiyar ba ta maida idanunta kan Billhaƙƙi da murmushi a fuskarta. "Kije ku haɗa tea ke da Saudat, kwai da irish yana nan na ajiye muku a kicin." "Tam! Sannu da aiki Ummee. Shi ne yau ma baki kira ni na taya ki ba?" Tayi maganar a shagwaɓe. "To yi hakuri, ai kullum indai lafiya kike tare muke yi. Har yanzu baki gama jin sauki ba shi yasa na barki ki huta. Je ki maza ku karya kar mu makara." "Tam!" Ta amsa a ladabce da murmushi a fuskarta, ta fice daga ɗakin da sassarfa. Tana fita falon ta hange Maheer da Luƙman zaune a kan dining suna karin kumallo. Su kuma matan suna kan kafet sun shimfiɗa ledan cin abinci suna karyawa. Kusa da su ta ƙarasa fuskanta na kan Luƙman ta fara gaishe su. "Ya Luƙman ina kwana? Ya Maheer barka da safe." Da fara'a suka amsa mata. Maheer sai laluben fuskarta yake yi dan su haɗa idanu amma ko kallon ɓangaren da yake zaune ta ƙi yi. Suna gama gaisawa ta wuce da nufin shiga kicin. "Keeee!" Daga can tsakiyar falon Surayya ta kira ta a wulaƙance kamar bata san sunanta ba. Dukda faɗuwar da gabanta yayi, da yadda ranta ya ƙara ɓaci bata tsaya ba, balle kuma har ta juya. Tafiyarta bai canza ba daga inda ta nufa, sai da taji daga can Surayya ta sake cewa cikin fushi. "Ke Bilhaƙƙi baki ji ina kiranki bane?" Kamar baza ta tsaya ba sai ta tsaya, ta runtse idanunta, addu'oi take ta ja a zuciyarta sannan ta juya ta nufi gurin Surayyan. "Aunty Keee fa naki ji kina cewa ni kuwa ko Ummee bata ce min keee. Ga ni." Sai da taja wani dogon tsaki ta bita da mugun kallo cike da muzanci, ta nuna mata kofin da ta gama shan tea da yatsarta manuniya. "Ɗauke wannan kofin ki kai kicin." Duk mutanen falon basu ji daɗin yadda Surayyan ta yi wa Bilhaƙƙi ba, ba ma kamar Maheer da ya tsaya cak da cin dankalin da yake yi yana kallon Bilhaƙƙi har tazo ta wuce ta kusa da su hannunta riƙe da kofin, shi kaɗai ya ga yadda idanunta suka tara ruwa. Ummee ma da ta fito tun sadda ta ji keee ɗin tana tsaye a bakin ƙofar ɗakinta tana ji tana ganin duk abinda yake faruwa ranta a ɓace. Wucewar Bilhaƙƙi yasa ita ma ta fito zuwa ɗayan ɗakinta inda Bilhaƙƙi take kwana. Sai a lokacin matan suka lura da tsayuwarta, tsuuuu suka yi musamman Surayya da ta yi rashin mutuncin. Shi kuwa Maheer bai ma lura da Ummee ba, da sauri ya ture kujeran da yake zaune a kai ya bi bayanta zuwa kicin ɗin. Tana shiga ciki ta dangwarar da kofin hannunta a saman cabinet, ta dafa cabinet ɗin ta ƙurawa kofin idanu zuciyarta na tuƙuƙi. Sai ga hawaye shar! Ita a rayuwarta ta tsani a wulakanta ta a cikin mutane. A dai-dai lokacin shi kuma ya shiga cikin kicin ɗin, tana jin motsi a bayanta tayi saurin share hawayen amma bata san ya riga ya gani ba. Ƙugunta ya riƙe ta baya ya juyo da ita yana tambayarta "Kukan na miye?" "Ba komai!" Ta amsa a cushe tare da fisge jikinta, tana kyarma ta matsa kusa da gwangwanin madara da bounvita ta fara ambulawa a kofi ba tare da lura da zubarwar da take yi ba. Kusa da ita ya sake matsawa ya riƙe hannunta, yana ƙoƙarin kallon cikin idanunta "Idan babu komai shi kuma ɓacin ran na menene?" "Ba komai!" Cikin fushi ta amsa tare da watsa mishi wani birkitaccen kallo. Ta fisge hannunta ta haɗa hannu biyu alamar roƙo. "Dan girman Allah Malam ka fita daga harkata." Hanyar fita daga kicin ɗin ta nufa, shi kuwa a sukwane ya janyo gefen rigarta. "Idan za mu tafi fa motata za ki hau..." "Baza ta hau motarka ba." Ya ji muryar Ummee kwatsam ba tare da ya ga sadda ta shiga kicin ɗin ba. Sansarai yayi a tsaye, jikinsa yayi mugun sanyi. Fuskanta a ɗaure ta ƙarasa shiga kicin ɗin, hannunshi ta nuna da yake riƙe da gefen rigar Bilhaƙƙi. "Sakar mata riga ka fice min a nan." Da sauri ya sake ta ya nufi hanyar fita, yana zuwa daf da ita cikin murya mai baiyana ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunne ta ce "Ka jawa fitsararriyar matarka kunne. Idan kai wasa daga kai har matan naka babu inda za kuje Wallahi." "Ummee dan girman Allah kiyi haƙuri..." "Ka ɓace min da gani na ce ko?" Da sauri ya cikawa rigarsa iska zuciyarsa cike da takaicin Surayya. Daman ya san tunda ta tada ballin sai ya je da su tabbas sai ta jaza mishi wani tsiyar. A maimakon ya koma cikin falon kawai sai ya fita waje. Ta kalli Bilhaƙƙi ta yi murmushi, ta ja hannunta suka matsa gaban kayan tea ta fara haɗa mata "Wai kishiyar kike wa hawaye? Wannan fa alamun jin tsoronta ne tun kafin ki shiga gidan?" Ta tura baki tana murmushi "Ba fa tsoro bane Ummee, kawai ni bana son a disgani a cikin mutane ne." "Eh lallai ba daɗi kam! Amma ki manta da ita kawai, ko ba yau ba kar ki ƙara yadda suyi miki wani abu ki nuna musu ranki ya ɓaci kinji ko?" "To Ummee na, in Allah ya yarda." "Yauwa Baben Yayanta, ungo maza je ki zauna ki cinye tas kuma ki shanye tea ɗin. Ki cewa Saudat idan bata fito ba da alama za a tafi a barta. Ni ma bari inje mu ƙarasa shiryawa ni da Mamanki." "To Ummeena." Da murmushi a fuskarta ta bar kicin ɗin. Ta ma manta da babin wata Suraiya. Ummee tana shiga falon ta kalli surukan da ɗaurarriyar fuska, irin kallon da take watsawa Surayyan yasa duk ta ji ta muzanta. "Ku zo ku gaida Mahaifiyar Bilhaƙƙi." A sanyaye duk suka bi bayanta zuwa ɗakin. Zukatansu cike da mamakin ko yaushe mahaifiyarta taje gidan? Haka dai suka gaishe ta a ladabce suka fice daga ɗakin. A wannan ranar dai haka aka yi tafiyar zuciyar Maheer babu daɗi, yana ji yana gani Bilhaƙƙi ta hau ƙatuwar jeap ɗin Luƙman, Malam ne a gaba, ita, Ummee, Mamanta a bayan motar. Shi kuma matansa biyu ya ɗauka, Aisha matar Lukman, sai Saudat. A gidan Malam dai ƴan samarin ƴaƴansa kawai aka bari da jiran gida. ******* ******* A can Masarautar Bauchi kuwa gaggarumin taro uku ne ake shiryawa, bikin sunan Ƴan biyun Gimbiya Safiyya, bikin murnar baiyanar Mustapha da iyalansa (Don Malam ya sanar da su ganin Rebeccah da ƴarta) Sai bikin naɗin Mustapha a matsayin tabbataccen Yarima mai jiran gado. Shi Takawa ma tun lokacin ya so yayi murabus ya sauka a naɗa Mustaphan amma yaƙi yarda, shi Mustaphan ya nemi alfarmar a ɗaga mishi ƙafa ya ƙara hutawa ya koma cikin nutsuwarsa sosai, kuma ya samu damar karantar harkar mulki da yadda ake gudanar da shi. Ta ko ina manyan baƙi masu sarauta, ƴan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa sai tuttuɗawa masarauta suke yi. Tun ana gobe sunan algaita da bushe-bushe suka fara tashi a masarautar. Gaggarumin biki ne da aka daɗe ba'ayi irinsa ba a masarautar, kowa so yake ya kashe ƙwarƙwatan idanunsa. BILHAƘƘI Da yake a wannan karon an kawar da matsalar su Oga, Na shuri ma babu maganarshi. Lafiyar Allah suka yi tafiyar cike da kwanciyar hankali da nutsuwa ba tare da wani mummunan abu ya faru da Bilhaƙƙi ba. Ta daɗe tana sharɓan bacci a jikin Mamanta, sallah da cin abinci kawai ke tada ita. Sai da suka kusa shiga cikin garin sannan Rebeccah ta tashe ta, ta ce ta zauna da kyau ta wartsake an ce sun kusa isa gurin Babanta. Da yake wannan karon gudu suke yi ba na wasa ba, kuma basuyi tsaye tsaye a hanya ba, ƙarfe biyar saura suka isa cikin masarauta. Nan fa aka sake kacamewa da gaggarumin murna na bayyanar iyalan Yarima Mustapha, Jakadiya ƙarama da aka mayar da ita matsayin Jakadiya Babba tattakura ta yi ta kama hanci ta rangaɗa zazzaƙar guɗa mai tsananin ƙara da fitar sauti, ko minti biyu bata yi ba Uwar Soro ta karɓe da nata zazzaƙar guɗan. Wannan watan gaba ɗaya sun raɗa mishi suna WATAN FARIN CIKI. Sarauniya Safiyya da ta ga Bilhaƙƙi tsaye a gabanta matsayin jikanyarta, halastacciyar ƴa ga gudan jininta na farko suman zaune ta yi, kafin daga baya ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka mai baiyana tsananin farin cikin da zuciyarta take ciki. Rebeccah sai ina za'a saka da ita ake yi. Babu kunya ba kara Sarauniya ta rungume ta a cikin mutane, uwar Soro da Umma sai tsokanarta suke yi irin na jika da kaka, wai ta tafi da zuciyar mai gidansu Mustapha gaba ɗaya ta hana shi nutsuwa saboda rashinta (idan baku manta ba su kakannin Mustapha ne). Ita dai ba baka sai kunne, sai sussunne kai ƙasa take yi saboda kunya da rashin sabo. A wani babban falo na musamman da yake ɓangaren Sarauniya Safiyya aka tarbe su da kalolin abinci na gani na faɗa na alfarma, sunci sunsha sunyi hani'an sai godiya ga Allah suke yi. Nama kala-kala sunci sun ture ciki har da na ɗawisu. Kai wani kalan naman ma basu san ko na wace dabbar bace su dai kawai ci suke yi suna tanɗe hannu, kunnuwansu kamar zai tsinke saboda tsananin daɗi. Tun daga nan su Surayya suka fara zubar da makaman yaƙinsu bayan sun fahimci abinda yake faruwa. Tsananin takaici da bakin cikin wannan al'amari na ɗaukakar Bilhaƙƙi lokaci ɗaya Surayya sai da ta shige banɗaki ta shaƙi kuka kamar ranta zai fita. 'Yanzu duk matan Maheer ita ce koma baya kenan? Daga ƴar sarki sai ƴar Alhaji ita ce ƴar Ladani? Ita wallahi da ta ma san abinda za ta gani kenan da bata zo ba.' Tana zuwa nan a tunaninta wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata shar! shar!! kamar an buɗe famfo. Haka ta shaƙi kukanta ta fita tana yaƙe a cikin mutane. Ga dangin Maheer daga Maru sunje sosai, saboda sha'ani ne da aka daɗe ana cin burin lokacin zuwanshi. Duk ƙwaƙwar Musty da yadda ya ci burin son ganin Rebeccah da yadda ita ma ta ci burin ganinsa a karon farko da isarsu basu samu damar haɗuwa da juna ba sai da aka idar da sallar magrib. A lokacin ne Takawa ya bada umarnin a kira duk wasu dangi makusanta na jiki-jiki don a gabatar da Bilhaƙƙi da Mahaifiyarta. A wannan lokacin ne haɗuwar masoyan biyu ta kasance, dukda an raba su da juna na tsawon shekaru goma sha tara zuciyoyinsu na tare da juna. Sun ba kowa na cikin falon tausayi, duk wani mai rai da yake cikin falon nan sai da ya zubar da ƙwallar tausayin waɗannan masoya biyu. Lallai da gaske ne soyayya ba ta tsufa sai dai masoyan su tsufa, haɗuwa ce da duk su biyun suka daɗe da fitarda tsammanin yin irinta, idanunsu rufewa yayi ruf! basa ji basa ganin kowa a falon sai su biyun nan. A tsakiyar falon suka haɗe idanunsu na cikin na juna suna zubar da hawaye, hannuwansu na riƙe da na juna. Jikkunansu sai kyarma suke yi, lallaɓansu sai mazari suke yi. Kamar haɗin baki a tare suka kai gwuiyawunsu ƙasa har lokacin basu daina kallon juna ba. Rebeccah ce ta fara katse shirun da suka yi da magana cikin muryar matsanancin kuka da ciwon zuciya "Musty nah... Tsawon shekarun nan suna gana min azaba... kullum sai Zidane ya zane ni saboda na ƙi sakin kalmar da ka laƙaba min a baki kafin ka tafi... sun alƙawarta min dukiya mai yawa amma na ƙi ƙarɓa... sunyi min alƙawarin muƙami mai girma a coci na ce bana so... har Jerusalam sun ce za su kaini na ce bana so... Ka san saboda menene suka yi min haka? wai in bar musuluncin da na shiga a gurinka. Wai in daina kiran la'ilaha illallahu muhammadur rasulillah... Amma har yau ban bar Musuluncin ba Musty, ban bari ba. Na rantse maka ban bari ba... kullum sai na ce La'ilaha illallah atleast sau talatin... Amma duk tsawon lokacin nan bana yin sallah Musty, basu bani damar da zan fita cikin musulmai ba balle in koya yadda zanyi... har yau ban canza sunana daga Rebeccah zuwa sunan musulmai ba Musty... kana ganin musuluncina har yanzu yana nan Musty???" Jikinsa ne ya ƙara sanyi da ɗaukar matsanancin rawa kaman bugun zazzaɓi, hannuwanta duk biyun ya damƙe a ƙirjinsa kamar mai ƙoƙarin janta ta shige cikin jikinsa, cikin kuka shi ma ya fara magana da ya fahimci amsoshinshi take jira "Musuluncinki yana nan Rebeccah... Tabbas har yanzu ke cikakkiyar musulma Ummu Bilhaƙƙi... Addininmu mai adalci ne. Ubangijinmu mai jin ƙan bayinsa ne. Bazai taɓa kama ki da laifin da aka tilastaki gurin aikata shi ba... idan kuma kina tantama zo kiji daga bakin babban limaminmu." Tsananin tashin hankali yasa da rarrafe ya ja ta har gaban Malam Liman da shi ma ya sadda kai ƙasa yana ta sharan ƙwallah "Liman dan Allah ka faɗa mata. Ina ce har yanzu ita musulma ce ko? ka faɗa mata ko hankalinta zai kwanta. Matata ce ita da har yanzu nake tsananin son ta, ta sadaukar da abubuwa masu girma saboda ni da farinciki na. Don Allah ka faɗa mata, sam bana son tashin hankalinta. Har yanzu ita musulma ce ko?" "Ƙwarai kuwa Mustapha. Har yanzu ita musulma ce." A tare suka sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, suka haɗa idanu ga kuka ga murmushin farin-ciki. A wannan lokacin dai sam sun kasa nutsuwa, tsananin tausayinsu kuma da ya cika zukatan mazauna gurin duk sun kasa magana. Liman ne kawai yayi dogon nasiha mai ratsa zuciya, a ciki ya nusar da kowa wannan tafiya da Mustapha yayi dukda akwai sila rubutaccen ƙaddara ne da aka rubuta zayyi tun kafin a haifesa. Ya ƙara da cewa ta wani fannin tafiyar ta haifar da alkhairai da dama, ciki har da jihadi na musuluntar da wata Ahlul kitabi. Wannan babban abin farin ciki da godiya ga Allah ne. Sannan ya maida akalar nasihan kan Rebeccah yana faɗa mata irin gwaggwaɓar lagwadar da duk bawan da ya mutu a matsayin cikakken musulmi mai imani zai sharɓa a gurin Allah SWT. Ya kuma gode haɗe da shi mata albarka na yadda tsananin wahalan da tasha a hannun ƴan'uwanta bai sa ta fita a musulunci ba. Ya sake janyo hankalin duk dangi da iyayen Mustapha kan su tsananta kyautata kamar yadda addininmu ya koyar da mu, ta yadda ko a mummunan tunani baza ta taɓa yin dana sanin shigowa musulunci ba. Daga nan ya bata damar zaɓen sunan da take so na musulunci ita kuma ta ce ta ba Mustapha wannan daman, yana daga cikin abinda take jira idan sun haɗu a aljannah ya raɗa mata. A nan kam sai da taba kowa dariya da tausayi. "Nana Khadeeja. Malam Liman na raɗa mata sunan Nana Khadeeja." Mustapha ya faɗa da sanyin murya. Nan gaba ɗaya falon ya kaure da kabbara. A nan sai Malam Abdulganiyyu ya karɓi bayanin, inda ya bada taƙaitacce tarihin Nana khadeeja da irin gudummuwarta ga addinin musulunci. Nanma wata kabbarar aka sake ɓarkewa da ita. A nutse ya ci gaba da bada labarin duk yadda aka yi Bilhakki taje hannunshi, har zuwa ɗaura mata aure da yayi, da yadda su Maheer suka samu nasarar karɓo Rebeccah. Bai ɓoye

Chapter 23 of 25