ya koma kan wannan tsintacciyar magen ne da kishiyata.
Idan zai yiwu ina so a kaɗa min wannan tsintacciyar can duniya, ta nisance mu, kar ta ƙara waiwayar rayuwarmu. Sannan ina so kishiyata ta zama koma baya a gurin mijinmu, ya zama a duniyar rayuwarshi babu wata mace da zai dinga gani da haske sai ni."
Ko da ta gama saurarenta bata ce komai ba ta ci gaba da kallon kuɗin. Can kuma sai ta kalli Indo ta ƙara maida hankalinta kan kuɗin
"Gaggarumin bala'i nih hango tahe gare ki da iyalinki Indo, ita wagga ɗiya da kika kahwa wa ƙahon zuƙa zata tahi ta barku kamar yadda kika biɗa, amma ba yanzu ba da sauran lokaci, sannan tabbas zata bar wawakeken giɓi ga rayuwarki. Abu ɗai zani ƙara miki ga wagga batu nawa shi ne ki kula sosai, wagga ɗiya da munka yi duba a kanta sosai bata nuhinki da komai sai masifa, kamar yadda a kullun kika nuhinta da sharri.
Gobe ki sayi ƙwarya ta nono kindirmo ga bahillata da ɗaurin huhun goro ki aiko mana da shi. Tashi ki tai mun sallame ki."
A hanyarsu ta komawa gida hankalinta in yayi dubu duk sun tashi, cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka kaɗa jajur! Karime ta sha tsinuwa da Allah ya isa ita da tun farko ta kasance sila ta ɓullowar shaiɗaniyar yarinyar cikin rayuwarsu.
Magajiya dai sai dannarta take yi tana bata baki, da haka har suka ƙarasa bakin titi inda zata hau ƴar ƙumbula zuwa layinsu na mai dubun tsumma.
"Indo kar dai ki manta da Kwaryar nonon da Huhun goron."
Sai kuma tayi sasarai a tsaye
"Magajiya? kin san kuwa da har na manta? to ni ina zan samu kuɗi? siyo kayan nan fa hidima ta wajen dubu biyu da ɗari biyar idan ma basu haura hakan ba..."
"Wannan kuma ai matsalarki ce Indo, tunda kinci ladan kuturu ya zama dole kiyi masa aski. Idan ba haka in suka shanye miki hannu ko ƙafa wallahi babu ruwana, karki kuskura ki faɗi suna na.
Ki bar ganin Mai zobia kamar yarinya manyan baƙaƙen aljanu tamanin da takwas ne a kanta, su suka buɗa mata idanu tana bada maganin duk wani ciwo na duniyar nan. Na ga kanki yana rawa dan haka ki kula, ni kinga tafiyata."
Saboda haushi bata jira ta samu ƴar ƙumbular ba ta tsallaka titi ta koma gidanta, tana tafe a hanya tana ta mita kamar cin ƙwan makauniya.
****** ******
BAYAN KWANA HUƊU da faruwar al'amura a lokacin har Amirah ta ji sauƙi sosai ta fara zuwa makaranta.
Ana tashinsu bata tsaya wasa ba ta nufo gida kai tsaye, turus tayi a tsaye tana kalle-kalle, yadda ta ga mata har huɗu a ɗakin Maman ga Malam tsaye a bakin ƙofar yana ta sharce gumi alamun hankalinsa a tashe yake shi ne abinda ya ɗaga mata hankali, ta sake kallonshi a tsorace jin da tayi ko sallamarta bai samu sararin amsawa ba.
"Abba sannu da gida."
Ta faɗi muryarta a sanyaye.
"Yauwa Amirah, kin dawo? yi maza ki shiga ɗakin Indo ki canza kaya ki ci abinci kinji ko?"
Yayi maganar da sanyin murya, akwai alamun ruɗu da ɗimauta a muryarsa.
"To Abba"
har ta kusa shiga ɗakin Indo sai kuma ta juyo ta kalle shi.
"Mama bata dawo bane?"
Kafin yayi magana Indo ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta tana gantsare-gantsare da ciccije baki, hannunta na hagu riƙe da kwankwasonta.
"Ke keh lafiya ko? kar ki kuskura ki shiga min ɗaki."
Ta daka mata tsawa ta ƙarasa jikin ƙofar da sauri ta tare bakin ƙofar dan kar Amirah ta shiga cikin ɗakin.
"Haba Indo, me yake damunki? baki ganin halin da Karime take ciki ne...?"
"Dan Allah Malam dakata. Ba fa na ce taje daji kunama ta harbeta ba, kuma ma naga tun kafin tafiyarta jejen ai ta tanadi abincin da ita ƴar gwal ɗin zata ci idan ta dawo makaranta, dan haka ta wuce ɗakin wacce take zamanta ba ni ba"
Wuf ta shige cikin ɗakinta tare da danno ƙofar ɗakin tana haki, hannu bibiyu ta sa ta dafe ƙirjinta zuciyarta cike fal da tunanin maganganun mai zobia.
'Wannan yarinyar tauraruwa ce mai wutsiya, ganinta sam ba alkhairi bane. A yadda take sam baza mu iya cutar da ita ba, amma idan muka bi ta jikin abokiyar zamanki muka raunata ta zaki iya samun cikar burinki na barin yarinyar cikin rayuwarki. Amma fa akwai matsala kafin faruwar hakan, wace irin matsala ce dai bamu sani ba.'
Ba tare da wani zuzzurfar tunani ba ko hangen abinda zai je ya zo kawai ta ce ta amince, ko ma mai zai biyo baya a shirye take.
'Da kyau! ki sa ido ranar laraba, duk abinda ya faru ga abokiyar zamanki mune sila. Makarin aikinki shi ne ki nuna tausayinki ga Karime a ranar larabar, idan kika yi hakan duk aikinki zai lalace, idan hakan ya faru mu kuma babu hannunmu.'
Duk waɗannan maganganun sun yi su ne ranar lahadi da ta je kai musu ƙwaryar nono da huhun goro kamar yadda aka umarce ta, tsabar masifa da son ganin burikanta sun cika ƙaramin gadon da yaranta suke kwana ta ɗaga ta saida a wulaƙance ga wata Dillaliya da take bayan layinsu.
Tayi matuƙar ƙoƙari gurin kiyaye duk sharaɗin aka gindiya mata, ido kawai ta zuba tana jiran ganin biyan buƙata. Tun misalin ƙarfe goma da rabi da aka kwaso Maman Ushe ranga-ranga daga gona kunama ta harbe ta ko kallo na mutunci da tausayi bata yi mata ba duk kuwa da yadda take ta gurmususu tana salati da sallallami dan tsananin azaban da take ji, anyi allurai an bata magungunan gargajiya amma har lokacin dafin bai daina yawo a jikinta yana wahalar da ita ba.
Yayyinta mata biyu ne a kanta sai manyan ƙawayenta guda biyu.
Amirah ko da ta shiga ɗakin ta ga yadda jikin nata yake sai ta fasa kuka, ko abincin ta kasa ci, rakaɓewa tayi a tsakar gida tana kuka da addu'ar Allah ya ba Mama sauƙi.
Suna cikin wannan halin aka aiko daga ƙofar gida wai ana sallama da Malam Ali, a firgice ya fita wajen da takalman ƙafarsa haɗin bauta.
"Malam Ali saƙo ne daga gidan Hakimi, yace lallai a tafi da kai da wannan baƙuwar yarinyar ƴar wajenka wacce mai ɗakinka ta tsinto. Tuhumar *MAITA* har biyu ne a kanta, mun samu labarin duk wanda yayi faɗa da ita a cikin mawuyacin hali yake ƙarewa, a taƙaice ma dai yarinya Raliya da Mal Murtala suna can fadar Hakimi cikin mawuyacin hali sai kiran sunanta suke yi, shi yasa aka bamu umarni lallai mu tafi da kai, ita, da kuma ita mai ɗakin naka da ta tsinto ta. Domin sarkin Mayu na hayin Mal Bello ya tabbatar mana da cewa samun warakarsu Mal Murtala ya rataya ne a wuyan ita wannan tsintacciyar yarinya ta wajenka bayan ta tsallaka su."
"Waw... wane irin magana kake min haka??? Amirar ce mayya? nawa take da har za a mata wannan ƙazafin?"
Mal yayi maganar cikin rawar murya da ɗimaucewa, sai sharce gumi yake yi kamar ya haɗiyi gatari.
Ko kafin ɗan aiken ya amsa mishi Inna Talatuwa ta fito a ruɗe tana hawaye
"Malam ka zo ka ga halin da Yaya karime take ciki..."
Da saurin gaske ta koma cikin gidan jin muryar Inna Asabe babbar yayarsu tana kwantsama salati mai tafe da ƙaƙƙarfar kuka.
"Dan Allah ayi min afuwa, a halin da ake ciki yanzu bazan samu amsa kira ba. Mai ɗakina wacce ta tsinto wannan yarinyar da kake magana ita ce a cikin mawuyacin hali na rai kwakwai-kwakwai. Ita kuma yarinyar tana makarantar boko bata dawo ba"
Bai jira amsawarshi ya faɗa cikin gidan da sauri dan ganin a wane hali ake ciki.
'Matsiyaciya, Annoba. Da zata mutu ma da an rage mugun iri...'
Haɗa idanun da tayi da Amirah yasa gabanta ya buga dam! Duk da idanun yarinyar ciccike yake da ruwan hawaye hakan bai ɓoye canja launin da ƙwayoyin idanunta suka yi ba.
Ta balla mata harara, da masifa ta ce
"kallon me kike min haka?"
Bata yi magana ba, tsawon wasu daƙiƙu suna musayar kallo sai kuma Amirah ta fara matsawa kusa da ita, daman suna tsaye ta can bayan banɗakin gidan ne inda aka shuka rama da zogale. Indo tana tsinkar rama ne ta jiyo salatin da Inna Asabe tayi shi ne take zancen zuci da fatan Maman Ushe ta mutu ba tare da sanin zancen zucinta ya fito fili ba.
Idanunta sun rufe da tsananin son cikar burinta ba ta da masaniyar Amirah tana rakuɓe a can gefe guda inda in ba tsananin lura mutum yayi ba ba lallai ya ganta a gurin ba.
Ta tsorata sosai da yadda ta ga yarinyar ta nufo ta amma sai ta maze ta tsaya ƙyam dan ta ga abinda zai faru, a duke dai ta san baza ta doku ba.
"Fata kike yi Mama ta rasu ko? to ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, burinki zai cika. Amma fa ke ma zaki mutu, idan kuma za ki zauna gadin duniyar ne to ga ki ga ta nan."
Bata ƙara cewa komai a kan haka ba ta fice daga gurin, ta barta a tsaye ƙiƙam kamar wacce aka zare wa laka.
Wani abin mamaki kuma sai jikinta yayi mugun sanyi, zuciyarta ya cika da wasu tunane-tunane marassa amfani. Tsananin tsoro da fargaba ya kama ta, ramar da bata ƙarasa tsinka ba kenan a saluɓe ta bar kwanon da ta fara zuba wanda ta tsinka a ciki ta kama hanyar komawa ɗakinta.
Kamar ta leƙa ta ga halin da Karime ke ciki sai kuma ta fasa shiga ɗakin.
Tana daf da shiga ɗakinta taci wani mugun tuntuɓe da dandamalin ƙofar ɗakinta ta kifa ciki, ƙwalla ihu tayi a gigice nan da nan jini ya ɓalle mata ta hanci ta baki.
A wannan lokacin su Malam suna zagaye da Maman Ushe da jikinta ya saki gaba ɗaya, alamun mutuwa ya baiyana a jikinta ƙuru-ƙuru, da ganin haka ba ɓata lokaci Malam ya fara biya mata kalmar shahada tana maimaitawa a hankali cikin shaƙewar murya, matan kuma sai kuka suke yi zuciyarsu na ƙara cika da tsananin tsoron Allah, lallai mai rai ba a bakin komai yake ba.
Tashin hankalin da suke ciki yasa ba wanda ya bi ta kan ihun da Indo tayi, daman duk suna cike da ita ganin yadda take nunawa a fili ciwon Maman Ushe bai dame ta ba. Ta biya kalmar shahada sau huɗu a na biyar mala'ikan mutuwa ya zare ranta.
BILHAƘƘI
Ta sake shan gabanshi cikin matsanancin kuka, zazzafar marin da ya kimtsa mata ma shanyewa tayi ta girgije kamar ba ita ya mara ba, ita kam ta gaji, ta kai maƙura gurin gajiya da mugayen halayensa da na ƴan'uwansa. Yau gara a yi ta ta ƙare a tsakaninsu. Ta cigaba da magana a hargitse cikin kuka.
"Masa'udu ya kake so inyi maka ? so kake in dinga bauta maka? to bari ka ji, duk yadda kake ganina kamar wulaƙantacciya wacce bata da wani makomar da ta wuce ta inuwarka da nake a ƙarƙashinta bazan zauna da ƙuruciyata ka ƙarasa kashe min rayuwa ba. Kar ka manta na canza abubuwa da dama saboda kai, na rabu da ƴan uwana da iyaye na duk saboda makahon son da nake maka, na rabu da addinina na shigo naka saboda tsananin son da nake maka. Amma saboda kai butulu ne duk waɗannan sadaukarwar da nayi dan kai baka kalle su a matsayin abinda zaisa ka mutuntani ba? A shekarunmu na biyar da aure ban tsinci komai da zan iya ƙararwa na jin daɗin rayuwa ba a gurinka da azzaluman ƴanuwa da mahaifiyarka..."
Kafin ta rufe baki ya kai mata wani ɓarin makauniya nan take tayi juyin masa a tsakar ɗakin.
Ƙaƙƙarfar ihu ta ƙwalla a gigice dan tsananin azaba ta sake tashi gadan-gadan tayi kanshi da dambe tana yaƙushinshi haɗe da cizo duk ta inda ta samu dama, shi kuwa ya ware ƙwanji sai narkarta yake yi ta ko ina kamar Allah ne ya aiko shi, ita kuwa duk da tsananin azaban da jikinta ke karɓa sam bakinta yaƙi mutuwa kuma taƙi saduda, bama-baman zagi take ta ɗura mishi kamar tsohuwar bamagujiya tana jifanshi da duk muggan maganganun da suka zo bakinta.
"Wallahi yau sai dai ka kashe ni ko in kashe ka, mugu, azzalumi, maciyin amana. Abinci ne bazan daina saidawa a bakin titi ba tunda dai baka ɗauke min nauyin da musulunci ya ɗora maka ba. Musuluncinka bai ƙare ka da komai ba sai zalunci da butulci, in Allah ya yarda ko ka mutu wuta ne makomarka..."
Saukar ƙatuwar sanda ta ji a gadon bayanta ba zato ba tsammani, nan ta gantsare ta sake ƙwalla ihu ta juya a gigice dan ganin wanda ya aikata mata haka, ido biyu sukai da sarkuwarta Baba Lauratu, zubewa tayi a tsakar ɗakin zuciyarta a ƙuntace ta sake fashewa da wani matsiyacin kuka tana sauraren baƙaƙen maganganun da take yaɓa mata.
"Muguwa mai baƙar aniya, tubabbiyar banza da wofi. Bakinki ya sari ɗanyen kashi azzaluma, in Allah ya yarda ke ce zaki ƙarke a jahannama a wutar ma kina can ƙasan ƙoli, kafira kawai."
Ta maida kallonta kanshi cikin masifa tana nuna shi da tsinin sandar hannunta ta ci gaba da zazzaga ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
"Masa'udu indai na isa da kai kuma ka haifu a cikina a yanzunnan ba sai anjima ba ka sau auren wannan tubabbiyar, kuma saki uku nake so kayi mata ta yadda baza ta sake maƙale maka ba, idan ba haka ba yanzunnan zan ɗaga maka nono Wallahi."
Da ita da take kukan, da shi da yake tsaye kamar zaki dan tsananin fusata yana ta sauke numfashi ɗif suka yi kamar ruwa ya cinye su, a take kuma sai jikinshi yayi mugun sanyi, nadama mai tsananin gaske ya rufe shi. Sai kuma zuciyarsa ta cilla da shi tunanin shekaru biyar baya da ya maƙalƙalewa Mary Barnabas har ya samu nasarar cusa mata matsananciyar soyayyarsa a duk wani lungu da saƙo na zuciyarsa, tun a lokacin ita Mary so tayi su ringa watsewarsu ba tare da zancen aure ya shigo ba a matsayinsa na musulmi ita kuma mabiyiyar addinin kirista amma sam yaƙi yarda da hakan.
Sau ɗaya ya taɓa gwada yunƙurin kusantarta amma tunda ya fahimci ita budurwa ce dal a leda ya fasa mugun nufinshi, ya sha tsananin wahala kafin ya iya yaƙin shaiɗan ɗin da yake ta ƙawata masa ya keta rigar mutuncinta. Daga lokacin iyakar rungume-rungume da tsotse ke shiga tsakaninsu ba ya taɓa bari su keta iyaka.
Daga baya kuma sai ya fara kwaɗaita mata batun su yi aure, tun tana noƙewa tana turjewa har dai ta amince da gaske zata aure shi, amma da sharaɗin bazai tursasata shiga addininsa ba, ya ce ya yarda.
Ko da ya jewa da iyayensa batun aurenta sai sukayi tsalle suka dire kan cewar sam bai isa ya kawo musu Ahlul kitabi cikin zuri'arsu ba.
A nata ɓangaren ita ma mahaifiyarta tace sam bazata auri musulmi ba, akan maganar aurennan sau goma sha biyar ana tale ta a zaneta a coci amma duk ta jure ta shanye tace in ba Masa'udu ba sai rijiya mai kwalabe.
Da taga ma bai dawo garin Kacia ba daga zuwa sanar da iyayensa zaunannun hayin rigasa kawai sai ta tattara ƴan kayanta ta bar ƙannenta biyu mata da mahaifiyarta dan mahaifinta Barnabas ya dade da mutuwa ta gudu gurinsa, daman tana da cikakken adireshinsu shi da abokinsa Umar da suke zuwa cirani a garin kacia.
Ko da taji halin da yake ciki da iyayensa sai tace in dai musulunta zaisa iyayensa su amince ya aureta ta amince za ta musulunta, amma tana so ya ɗaukar mata alƙawarin duk runtsi, duk wuya, komai wahala da juyin juya hali na rayuwa kar ya taɓa wulaƙanta ta.
Ba tare da tunanin komai ba ya ɗau mata wannan alƙawarin sannan ya ƙara da cewar duk wani daɗi na duniya zaiyi iya ƙoƙarinsa wajen jiyar da ita ko da shi zai ƙuntata kansa da tasa rayuwar. Ba tare da ɓata lokacin komai ba suka je gurin wani limami ya musuluntar da ita, ko da suka yi mishi bayanin halin da suke ciki ya tausaya musu ƙwarai, bayan kwana biyu ya ɗaura musu aure akan sadaki naira dubu goma bisa shaidar abokan mahaifinsa biyu ba tare da sani ko yardar mahaifiyarsa da ƴan uwansa ba.
Jagora yayi wa Limamin har gida yayi wa mahaifiyarsa zazzafar nasiha, ya jawo mata ayoyi da hadithai masu nuni akan cikar imani ta hanyar yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau, ya nusar da ita ɗimbin lada da romon da bawa yake sharɓa a wajen ubangiji idan yayi sanadiyyar musuluntan mutum ɗaya a ƙarshe ya dire da faɗa mata ɗaura auren Mary wacce musuluntan da tayi ya maida ita Maryam da Masa'udu ƙwallin ƙwal ɗin yaronta namiji a cikin ƴanuwansa mata bakwai, yaron da ta gama tattalinsa da ɗora burin duniya a kansa tana ganin nan gaba kaɗan shi ne zai zama Ɗangwaten hayin rigasa gaba ɗaya.
Nan Liman ya cigaba da ƴan nasihohinsa da fatan alkhairi wa auren amma abinda bai sani ba tun da ya faɗi tabbatuwar auren ta daina fahimtar abinda yake cewa har ya kwashi tsumman ƙafufunsa ya ƙara gaba.
Kamar gaske ta basu ɗaki guda a cikin gidan da cewar su zauna amma zuciyarta cike da alwashi kala daban-daban na yiwa tubabbiyar gashin ƙuma a tafin hannu har sai azaba yasa ta bar gidan da ƙafafunta.
Tabbas tayi nasarar hakan, a hankali da zuga da makirci da sharrin abinda bata yi ba tace ta yi saida ta sa Maryam ta fice daga zuciyar Masa'udu, duk abinda yayi niyyar yi dan ya kyautata mata sai Baba lauratu tayi fiti-fiti ta hana, ta ƙara da ce masa ita mace ba a gwada mata tsananin daɗi in ba haka ba sai ta lalace, balle ma ita tubabbiya ai sun saba da wahala, matan kirista su suke noma su ciyar da mazajensu.
A hankali har ya sangarce ya ci gaba da neman matan banza a waje dukda kuwa tsananin ladabi da biyayyar da Maryam take masa, tana iya ƙoƙarinta gurin shanye duk wulaƙancin da suke mata bango da bango, ba ga uwar ba ba ga ƴan'uwansa mata da shi kansa ba.
Sana'a iri-iri tayi dan ta rufawa kanta asiri, gorin haihuwa kuwa da yana fitowa a jiki da ya fito mata dan tsananin gorin da suke mata, amma a gefe guda Baba Lauratu murna take yi da rashin haihuwar dan ta ce Allah ya kyauta ta haɗa jini da tubabbiya.
A gurinsa ta ƙara gogewa da hausa ƙwarai kamar jakar kano, daman kuma ko a kacia suna cikin hausawa ne, tana ji sosai, a yanzu kam idan ba faɗa aka yi ba babu wanda zaice ba asalin bahaushiya ba ce.
A lokuta da dama idan ta zauna tana kuka tana yawan tunanin wai dama haka musulunci da musulmai suke? Ita dai bata tsinci komai a musuluncin ba sai baƙin ciki da takaici da ɗumbin da na sanin shiga cikinsa.
(Wa'iyazu billah. Ta haɗu da baragurbin musulmai😢😢)
Abinda ya zafafa rikicinsu a kwanakin shi ne saida shinkafa da miya da ta fara yi a bakin titi kusa da shagon wani mai saida miniras, Allah ya sa mata albarka sosai take ciniki a gurin, shiga ta mutunci take yi kuma bata yarda wani maganar banza ya shiga tsakaninta da maza, tana da almajirai biyu da suke mata wanke-wanke da miƙa abinci.
Ganin rayuwarta ya fara canzawa tana cikin walwala sai ƴan uwansa da Baba suke ta zuga shi da lallai ya hana ta saida abincin in ba haka ba zata kwaso cikin da ba nashi ba ta kawo mishi, dan duk unguwa an san bin mazanta take yi tana fakewa da sunan sayar da abinci...
"Dan ubanka tunanin me kake yi? Za ka sauta ko sai na tsine maka?"
Ta katse mishi zuzzurfar tunanin da yake yi cikin masifa da ɗaga murya.
Ya kalle ta a hankali, ita ma shi take kallo, idanunta cike maƙil da hawaye, amma a hakan ƙoƙarin murmushi take yi dan ta nuna mishi ko ya sake ta bata da asara, fuskarta dama da hagu sashin yatsunsa ne kwance, bakinta a fashe, ya aune ya kumbura suntum, kyakkyawar halittarta duk ya canza zuwa mummuna dan tsananin dukan da ta sha, wani matsanancin tausayi da ƙaunarta da ya daɗe baiji irinsa ba ya tsirga a filin zuciyarsa.
Ya maida kallonsa kan Baba Lauratu, a sanyaye kuma cike da ladabi ya fara magana.
"Baba kiyi haƙuri, idan na sake ta zata iya komawa ruwa cikin addininta na kirista..."
"To ta koma mana dan Ubanta. Ai daman ko yanzu ba musulma bace tunda bata shekara arba'in a cikin musuluncin ba, manyan malamai sun tabbatar da hakan. Maza sakatta mu yarda ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda."
Ya zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta da niyyar fara mata magiya.
"Baba..."
Ta katse shi da sauri ta hanyar fincike ƙafafunta ta ɗaga murya ta fara addu'ar cikin sauri
"Ya Allah ka tsi..."
"Baba zan sake ta, dan Allah karki ƙarasa"
Ya katse ta da faɗan haka cikin gunjin kuka kamar mace.
Jikinsa na kyarma ya rarrafa kusa da ita ya haɗa hannayensa biyu alamar roƙo, sai kuma ya miƙa hannu kamar zai ruƙo nata hannun da sauri ta ja da baya kamar ta ga kumurcin maciji.
Bai damu ba ya fara magana sauri-sauri murya da jikinsa babu inda ba ya rawa.
"Maryam ! ki yi haƙuri. Ban taɓa tunanin a nan kusa zanyi da na sanin irin abubuwan da na daɗe ina miki ba, a yau da Allah ya fargar da ni sai kuma na rasa damar da zanbi gurin gyara kuskure na. Duk da nasan zaiyi wahala ki iya yafe min amma dai bazan gaji da roƙon ki yafe min ba. Maryam dan girman Allah ki yafe min, ina roƙonki ko da kin tafi dan Allah karki koma cikin addinin kirista... Na sake ki ! Saki uku!!"
Yana ƙarasa sakin ya zube wanwar a gurin yana jan numfashi sama-sama kamar mai cutan asma.
Suman wucin gadi ta yi, Allah ya sani ta so Masa'udu so mai tsanani, duk da irin azabtar da ita da yake yi bata taɓa tsannanin akwai saki a tsakaninsu ba, yanzu da sakin ya afku sai tayi tsam da ranta jijiyoyin shige da fice wajen kai saƙonni a ƙwaƙwalwarta suka tsaya da aiki na wucin gadi.
Ƙaƙƙarfar guɗar da Baba Lauratu ta daddage ta rangaɗa shi yayi nasarar dawo da ita cikin haiyacinta, bakin ta kamar gonar auduga, burinta ya cika. Yau dai Allah yayi sun rabu da alaƙaƙai.
"Zaman me kike yi? ai sai ki yunƙura ki fice mana daga gida tunda igiyoyin da suka sarƙafa mana sun tsittsinke..."
"Dakata Baba Laurata !"
Tayi ƙarfin halin dakatar da ita cikin tsawa tare da ɗaga mata hannu. ɗan ragowar jarumtar da ya rage mata ta tattaro ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta babu inda ba ya mata ciwo.
"Ta fi nono fari, ɗanki ga shi nan ki jiƙa shi ki sha. Idan kinso ki aure shi ƙarewar hana shi auren tubabbiya..."
"Keeee karki kawo min iskanci da zancen banza irin naku na kafurai"
Ta katse ta cikin zafin rai ta ɗaga sandar hannunta da nufin sake kwaɗa mata.
Caraf ta riƙe sandar tana gwalalo ido waje
"Wallahi kika sake duka na saina zubar da ke a nan gurin, matsiyaciya wacce bata san Allah da ikonsa ba."
Yarɓar da sandan tayi Baba ta tafi taga-taga kamar zata faɗi ta yi ƙoƙarin tsayawa.
Bata sake kallonsu ba ta nufi ma'ajiyar kayanta ta ɗauki doguwar riga ta canza riga da zanin jikinta da suka yayyage. Ta ɗauki wani siririn gyale ta rufa a kanta ta ɗauki jakar hannu inda take tara ƴan kuɗaɗenta ta nufi hanyar ficewa daga ɗakin hannunta jaye da akwatin kayanta.
"Masa'udu na barka har abada, kamar yadda na bar maka addininka har abada."
Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta fice daga ɗakin ta bar gidan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 25