barka da dare"
Sama-sama suka gaisa saboda dare yayi, yayi mata sai da safe ya fice daga ɗakin.
Ko da ya leƙa ɗakin da Surayya take sai ya tarar duk sunyi bacci ita da Inna Lantana, dan haka ya fice daga ɗakin yaja musu ƙofar ya kulle.
Gurin Ummee ya koma yayi mata sai da safe ya fice daga gidan ya hau motarsa a waje ya nufi gidansa.
A wannan daren ko Rabi sai da ta fahimci yana cikin damuwa, yadda ya koma gidan ba haka yanayinsa yake sadda ya bar gidan ba, sam ya kasa walwala.
Tayi tunanin ko jikin Surayya ne sai yace mata ba haka bane, juyin duniya kuma yaƙi faɗa mata abinda yake damunshi dole ta ƙyale shi ta zuba mishi ido.
Ya daɗe baiyi bacci ba sai juye-juye yake yi yana saƙawa yana kwancewa, shi kaɗai yaita jan tsaki zuciyarsa a ƙuntace, har gaf da asubah sannan wani nannauyan ɓarawo bacci yayi nasarar sace shi cike da muggan mafarkai mabanbanta duk a kanshi da Bibi.
****** ******
"Mery..."
Aka ƙwalla kiran sunanta cikin murya mai tsananin ƙarfi da hauhawa wanda yasa duk wani lungu da saƙo na cikin babban ɗakin tsafin amsa kuwwar sunanta. Cikin tsawa da baiyana tsananin fushi aka cigaba da magana da muryoyi mabanbanta daga ko wani bango na ɗakin
"Garkuwa yana daf da yayi mummunar fushi da ke Merry... ki kawo Bibi a cikin ƙanƙanin lokaci matuƙar kina so Garkuwa ya share miki hawaye... Merry... Merry... Merry..."
Aka ci gaba da ƙwalla kiran sunanta cikin sauti mai baiyana ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunne, hakan yasa ta ƙara ruɗewa, tana gurfane gwuiwa bibbiyu a gaban Oga, yafe take da wani jan ƙyalle a jikinta saɓanin sauran ƴan ƙungiya da suke sanye da shuɗayen riguna da jan ƙyalle a kawunansu, wannan jan ƙyallen da ta yafa babban alama ne da yake nuna ita mai laifi ce a ƙungiyar. Ba abinda take yi sai kuka.
"Karki bari fushin Garkuwa ya sauka a kanki dan rayuwarki za ta ɗaiɗaice... rabuwar Bibi da ƙungiya tamkar tarwatsewar rayuwarki da na duk wani makusancinki ne Merry..."
Ɗif sautin muryoyin ya ɓace kamar anyi ruwa an ɗauke, can kuma sai aka ƙyalƙyale da wani matsiyacin dariya da murya mai kama da na gyare, tsawon lokaci kafin dariyar ma ta ɗauke ɗif!
Hannu Oga ya miƙa mata ta kama da sauri, jikinta babu inda baya rawar ɗari.
"Sadaukar da jinin wacce kike tsananin so a zuciyarki dan lallashin Garkuwa ya ƙara miki lokaci."
"Rose"
Ta kira sunan tana kuka, ƙannenta biyu duk ta sadaukar da su a ƙungiyar, a yanzu babu wacce take ji tana so a zuciyarta da ta wuce Rose ɗin, ita ma ga shi yau ta bada jininta.
Runtse ido yayi ya daki bangon yamma na ɗakin sai ga hoton Bibi ya baiyana a kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali, a gefenta Ummee ce take sallar nafila. Ga karatun Alƙur'ani da yake tashi a hankali cikin ɗakin.
"Kinyi sake Merry, kin bari Bibi tayi masauki a muhallin da duk tsafin matsafi sai dai ya zuba mata ido. Matuƙar tana tare da waɗannan iyalan babu wani abu da muka isa mu aika mata daga nan. Aiki ne ja a gabanki, cikin sati biyu ki san duk yadda za kiyi ki rabata da waɗannan mutanen ki dawo da ita cikinmu, suna da matuƙar haɗari a gare mu, ko ma me za kiyi dole ke kiyi in ba haka ba duk abinda Garkuwa ya saukar miki ki kuka da kanki."
Ya zagi bangon nan take hoton ya ɓace komai ya koma yadda yake kamar wani abu bai taɓa baiyana a gurin ba.
Dungulmin hannunsa ya nuna a jikin bangon kudu yana ƙwalla kiran sunan Rose haɗe da wasu surutai na tsafi da shi kaɗai yasan ma'anar abinda yake faɗe, nan take hoton Rose ya baiyana a jikin bangon kamar a majigi, tana kwance a kan gadon asibiti tana bacci cike da kwanciyar hankali. Alamun sauƙi sosai ya baiyana a jikinta, dan har ta ɗan ƙara kumari saboda hutu da kyakkyawar kulawar da take samu a asibitin.
Kunnenta ya daka nan take jini ya fara ɓulɓulowa daga cikin kunnen kamar an buɗe famfo, da sauri ya tara babban ƙwarya jinin yana zuba a ciki har saida ya cika taf sannan jinin ya daina zuba hoton Rose ya ɓace, ya ɗauko ƙwaryar da hannu biyu ya ɗaga sama ya runtse ido yayi wasu maganganu sai ya sake ƙwaryar, kamar zai faɗo sai kuma ƙwaryar yayi sama a hankali har ya isa saman rufin ɗakin ya tsaya cak.
Nan take masu matsaloli a ƙungiya suka fara zuwa gaban Oga ɗaya bayan ɗaya suna yi mishi sujada sannan su faɗi matsalolinsu shi kuma ya miƙa musu koke a gurin Garkuwa, da haka har suka gama taron duk suka ɓace kowa a cikinsu ya baiyana a makwancinshi.
BILHAƘƘI
"Ki yi haƙuri mana Marry, kiyi shiru haka nan. Is ok! Ni ina ganin kuka da damuwa ba shi ne solution ba. Ki kwanta ki huta gobe sai muyi maganar yadda zamu ɓullowa Malamin nan tunda kina da isasshen time da za ki dawo da ita."
Tayi maganar cikin rarrashi, ta juya mata baya tana ƙara jan bargo, hannu ta miƙa ta ja wani ɗan igiya a gefen gadon nan take ƙwan lantarki mai haske ya ɗauke mai duhu ya baiyana. Rufe idanu tayi alamun ko wane lokaci tana maraba da ɓarawo bacci yayi awon gaba da ita.
Taja wani dogon nishin kuka mai tafe da kakkauran majina, tissue ta ɗauka a gefen gadon ta fyace majinan, sai kuma ta ci gaba da sauke ajiyar zuciya akai-akai, ita kam ta shiga uku sau uku.
Babu abinda yake ƙara ɗaga mata hankali a duk cikin abinda yake faruwa da ita sai idan ta tuno jimlar
'Fushin Garkuwa yana daf da sauka a kanki Merry...'
Da ta zo nan a tunaninta sai wasu sabbin hawayen su sake ɓalle mata shar-shar kamar an buɗe famfo.
Tsawon shekarun da tayi a ƙungiyar mutane biyu kawai ta taɓa ganin fushin Garkuwa ya sauka a kansu. Yadda suka ɗaiɗaice cikin ƙanƙanin lokaci bayan an gama wahalar da su haɗe da gana musu azaba shi ne abinda yake ƙara ɗaga mata hankali.
Na baya-bayan nan da fushin Garkuwa ya sauka a kanshi shi ne Alhaji Zangina.
'Shekaru talatin da biyu suka kwashe shi da matarshi suna yawon neman haihuwa daga wannan ƙasa zuwa wancan ƙasa, basu samu ba sai da suka cika shekaru talatin da biyu cif da aure. Ba zato ba tsammani kwatsam ciki ya ɓulla a jikin matarshi Lailah. Murna a gurinshi faɗe ma ɓata baki ne, har a gurin Garkuwa ya sha neman tabarraki ga ɗan tun kafin ma a haife shi, da fatan matarshi ta sauka lafiya har zuwa lokacin da ta haifo zankaɗeɗen ɗa namiji mai tsananin kama da jinsin larabawa, ga tsananin shiga rai ga duk wanda ya ɗauke shi. Tsabar murna, ɗoki, zakwaɗi, matuƙar farin-cikin haihuwar ɗan Gaske yasa Alhaji Zangina ya dinga ɗiban manyan kuɗaɗe da manyan kadarorinsa yana rarrabawa ga abokai da ƴan'uwansa. Idan ya bada kyauta kalma ɗaya tak yake son ji daga bakin mutum.
Allah ya raya Ɗan Gaske.
Kwanan jinjirin huɗu a duniya da tsakar daddare suna zaman meeting na ƙungiya kamar yadda suka saba Garkuwa yazo da buƙatar da ta jijjiga hanjin duk wani member na ƙungiyar, buƙatar shi ne dole Alhaji Zangina ya sadaukar da jinin wannan jaririn a gare shi, Oga ya ƙara da cewa barin jaririn ya girma babban masifa ne kuma barazana ne ga ƙungiyarsu da shi kanshi Alhaji Zangina. Kawar da shi tun yanzu kuwa arziki da ƙarin buɗi da samun babban shugabanci a ƙasar nan ne ga mahaifinsa.
Nan Alhaji yayi tsalle ya dire hankalinshi a tashe, idanunshi a rufe da alamun ya mance a inda yake ya ce babu uban da ya isa ya sha jinin jaririnshi, ko da girman jaririn zai zama ajalinshi da ajalin kowa na cikin ƙungiyar.
Ƙwaryar tsafin da yake a mazaunin kamar ruhin Alhaji Zangina cikin fushi Oga ya kunna wuta da dungulmin hannunshi, naman jikin Alhajin ne ya fara zaizayewa yana narkewa a hankali kamar kitse, sai ihu yake yi yana make-make da buge-buge, sai da ya wahala sosai daƙyar yake iya motsi sannan Oga ya kashe wutan.
Nuni yayi a bango sai ga hoton jinjirin kwance a tsadadden gadonshi na jarirai yana bacci hankali kwance, Da ƙarfin tsafi Oga ya zuƙe jinin jinjirin ta babbar yatsar ƙafarsa a gaban idanun Alhaji Zangina, matarsa Laila da ta kasance cikon farin-cikinsa tunda duk ya gama sadaukar da iyayensa ga Garkuwa ita ma tana bacci a makeken gadonta aka zuƙe jinin jikinta ta agarar ƙafarta.
Ganin wannan babban abin baƙin-ciki da ɗaga hankali yasa shi yanka wani mahaukacin ihu ya fara fiffisga yana mimmiƙewa kamar sabon shiga a hauka, ya zura a guje zai kaiwa zakaran wuyan Oga cafka ayi mutuwar kasko da sauri Oga ya nuna shi da yatsar ƙafarsa nan take ya zama ƙatoton alade. Tun da Oga ya shafi kan aladen ya ɓace ɓat har yau da aka doshi shekaru biyar da faruwan al'amarin basu sake jin ɗuriyar Alhaji Zangina ko wani abu da ya shafe shi ba.'
Tana zuwa nan a tunaninta ta sake fashewa da wani matsiyacin kuka tana surutai haɗe da tsinewa Bibi da su Agness da suka yi sanadin barinta gidan.
"Oh my God ! Merry gaskiya zan barki kiji da damuwarki ke kaɗai in dai baza ki barni inyi bacci ba. Na gaji sosai ina buƙatar hutu, mun fita tun yamma muna gurin Lion har dare, mun dawo bamu huta ba saboda gudun da Bibi tayi kin ce dole muyi shigar muslims muje mu dawo da ita a gidan Malamin nan, bamu daɗe da dawowa ba mun shiga meeting yanzu kuma mun dawo kin hana mu huta me yasa hakan?"
Ta ƙarasa maganar cikin fushi idanunta a ƙanƙance, sosai bacci yake a idanunta amma sukur-sukur da shessheƙar kukan Merry ya hana ta samu baccin a cikin nutsuwa.
"Yi haƙuri Mercy, pls gobe za ki sake rakani gidan Malamin nan...?"
"A'a!"
Ta faɗa kai tsaye tare da sake juya mata baya tana jan wani dogon tsaki.
"Abbeg in baki shirya yin bacci ba ki koma ɗayan bedroom ɗin ina so in huta."
Ta sake jan tsaki haɗe da jan bargo ta rufe har saman kanta.
Tana jin sadda Merry ta fice a ɗakin, kanzil bata ce mata ba sai ma ta rakata da harara. Nan da nan kuwa bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.
******* ******
Cikin hukunci da ƙudura irinta Ubangijin sammai da ƙassai mai kowa mai komai SWT da sassafe Bibi ta farka lafiyarta ƙalau, kamar ba ita ce jiya ta yini ta kwana a cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai ba.
Babu abinda yake tashi a bakunan Malam da iyalinsa sai ma sha Allah Alhamdulillah, fuskokinsu ɗauke da matsanancin farin-ciki.
Sai da ta rama duk sallolin da suke kanta, tayi wanka da ruwa mai zafi-zafi ta gargasa jikinta. Ummee ta haɗa mata tea mai kauri ta sha hanjinta ya warware. Ko da aka ce a kawo mata abinci mai nauyi ta karya da shi a kunyace idanunta a ƙasa ta ce ta ƙoshi da tea ɗin, a bar abincin sai anjima.
Malam ne ya kira ta falonshi da matansa biyu sannan ya umarce ta da ta faɗa mishi gaskiyar ita wacece? Daga ina take? Wa ya bata kwatancen gidanshi? ya ƙarasa maganar da yi mata gargaɗin kar ta kuskura tayi mishi ƙarya, domin matuƙar ya gano tayi mishi ƙarya a cikin labarinta zai ɗauki mummunan mataki a kanta.
Kafin ta ce komai Maheer ya cusa kanshi cikin falon bayan yayi sallama an amsa mishi. Ganinta a zaune digirgir a gaban su Malam abin ya bashi mamaki ƙwarai, jinjina kai kawai yayi, zuciyarsa cike da mamakin ƙwarewarta a makirci. A tsaitsaye ya gaida su Malam ya juya da nufin ficewa daga falon sai Malam ya tsaida shi.
"Nemi guri ka zauna"
Runtse ido yayi duk ransa a ƙuntace ya nemi guri a kan kafet ya zauna kusa da ƙafafun Malam, ita ma tana zaune a ƙasa ne kusa da ƙafafun Ummee, tunda ya shiga cikin falon idanunta ƙyam a kanshi zuciyarta cike da farin-cikin ganinsa har fuskarta ya gagara ɓoye hakan, shi kuwa sam ya ƙi yarda ko da wasa ya haɗa ido da ita.
"Yarinya ke muke saurare"
Mummy ta faɗa tare da dafa kanta dan dawo da hankalinta kansu.
Idanunta ta sauke ƙasa, ta haɗe hannayenta biyu tana matsawa a hankali.
"A haƙiƙanin gaskiya ni kaina bansan ko ni wacece ba."
Da sauri duk suka ɗaga kai suna kallonta fuskokinsu baiyane da matsanancin mamaki, Maheer kuwa tsaki yaja a zuciyarsa dan tuni ya daɗe fahimtar ita ƙwararriya ce a fagen rainin wayau.
Bata damu da irin kallon da suke bin ta da shi ba a sanyaye ta ci gaba da cewa.
"Abinda zan iya tunawa kawai tun ina ƴar ƙanƙanuwa na rayu a mabanbantan gurare a hannun mabanbantan mutane. Waɗanda ƙarancin shekaru na a wancan lokacin bazan iya tuna su ko inda suke a yanzu ba. Sama-sama wacce nake iya zaman da nayi a gurinta wata baiwar Allah ce Maman Ushe. Bayan rasuwarta ne na haɗu da Madam Merry wacce har zuwa na nan gidan ina tare da ita."
Cikin nutsuwa da kwantar da kai ta ci gaba da basu labarin duk wani abu da ta iya tunawa dangane da zamanta da Madam Merry har zuwa haɗuwanta da Maheer, da yadda tayi ta binshi da soyayya yana gwasaleta, haɗuwarta da Yusuf har ya bata adress ɗin gidan Malam. Da irin yadda Madam ta shiga tashin hankali bayan ta faɗa mata ta faɗa soyayya har zuwa kiran da Oga yake yi mata ta fice daga haiyacinta, har zuwanta nan gidan. Ta baiyana musu komai iya yadda ta sani.
Tunda ta fara faɗan sarƙaƙan abubuwa masu matuƙar rikitarwa da ɗaure kai game da tarihin rayuwanta jinjina kai kawai suke yi, cike da mamaki har zuwa sadda tayi shiru alamun ta gama. Ummee da Mummy kallonta kawai suke yi suna mamakin ƴar ƙanƙanuwan yarinya ɗauke da manyan al'amura a cikin rayuwanta.
Shi kuwa Maheer kanshi a ƙasa yake jujjuya maganganun a zuciyarsa, idan wani sashe na zuciyarsa ya ƙaryata labarin da ta basu sai wani sashen ya gasgata ta, dan tun a haɗuwarsu ta farko ya haƙƙaƙe bata da wani tsayayyen mai faɗa aji a rayuwarta, duba da yadda tayi ta liƙe masa kuma tana ziyartarsa a duk sadda ta so, ba tare da duba tsawon dare, sassafe ko tsakar rana ba. Da waɗannan tunane-tunanen da saƙe-saƙen sai zuciyarsa ta tsaya cak a guri ɗaya, shi kanshi bazai ce ga ainahin abinda yake ji game da ita ba. Tausayinta yake ji ko kuwa haushinta ya kamata ya ji?
Ga Malam kuwa ya samu gamsassun amsoshin cukurkuɗaɗɗun tambayoyin da yake son ji game da ita. Da yawa daga cikin abinda suke ɓoye a cikin mafarkin da yake yawan yi da ita yanzu idonshi ya buɗe ya fahimce kusan komai. A karo na barkatai ya sake sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kallonta. Kamar ya rasa ta cewa sai kuma ya daure cike da taraddadi ya ce
"Bibi za ki iya barin Madam Merry ki dawo da zama ƙarƙashin kulawata da ta iyalaina?"
"E zan iya!"
Ta amsa kai tsaye ba tare da tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo ba. Haka kawai take jin wani saukakken nutsuwa a cikin rayuwarta tun bayan dawowarta cikin hayyacinta, ta na ji a ranta zata iya ƙarƙare rayuwarta tare da Malam da iyalinsa da suke da wani girman matsayi na musamman a zuciyarta. A gefe guda kuma ga ta ga Gangaran ɓarinta, cikon farinciki da walwalarta. Ko da wasa baza ta taɓa yarda tayi sake da damar da yazo mata ba, waɗannan dalilan su suka tattaru suka sa tayi saurin amincewa buƙatar Malam.
"Madallah! To daga yau ki ɗauke ni a matsayin mahaifinki, su kuma a matsayin iyayenki mata. Ina fatan zaki dage kiyi watsi da duk wani mummunan turba da mugun hali da Madam ta ɗora ki a kai? ki buɗe ƙwaƙwalwarki kiyi mata sabon zubi na kyakkyawan tarbiya da cikakkiyar rayuwa irinta addinin islama da za muyi iya ƙoƙarinmu wurin ɗora ki a kai. Kin gane?"
"Eh na fahimta."
Ta amsa a sace tana kallon Maheer duk da sam bata fahimci abinda maganganun Malam ɗin suke nufi ba.
"Sunan Bibi ba shi da wata cikakkiyar ma'ana a musulunce, dan haka idan akwai sunan da kike so na hausawa mai asali ki faɗa mu dinga kiranki da shi kin ji?"
Shiru tayi tana tunani, da kamar za ta ce Malam ɗin ya zaɓa mata sunan da ya dace sai kuma wani tunani ya gilma a can ƙasan zuciyarta.
"Idan ina barci wani farin mutumi dogo yana yawan zuwa min da hawaye a fuskarsa, yai ta ce min in bar irin wannan rayuwar bai da ce da ni ba, yana kira na da wani suna mai daɗi amma yanzu na manta sunan."
"Allah sarki. In Allah ya yarda yanzu ne za kiyi irin rayuwar da mutumin yake fata kiyi. Amma tunda kin manta sunan za mu dinga kiranki da Fatima. Idan kin tuna da wancan suna mai daɗin idan yana da ma'ana sai mu dinga kiranki da shi. Kin ji ko?"
"Eh! Na gode Malam."
Ya maida idununshi kan su Ummee.
"Balaraba baki ce komai ba?"
Murmushi tayi ta shafa kan Bibi, tana ƙara jin wani nutsuwa da tausayin yarinyar yana kwaranya a zuciyarta.
"Bani da ta cewa Malam, sai addu'a da fatan Allah ya taya mu riƙo. Ko ba haka ba Mummy?"
"Kin gama magana Ummee. Allah ya ƙara mana ƙwarin gwuiwa da haɗin kai a tsakaninmu."
"Ameen ya Allah."
Suka amsa gaba ɗaya.
"Magajin Malam kana da abin cewa ne? Na ga kamar bakinka yana ta motsi tun ɗazu."
Sosa ƙeyarshi yayi da makullin motarsa, yayi ɗan murmushi.
"Ba komai Malam. Allah ya taya ku riƙo. In Allah ya yarda duk abinda take buƙata kamar sauran ƙannina kar ta ji shakkar faɗa min, zanyi iyakar ƙoƙarina gurin biya mata buƙatar duk abinda take so."
Da alamun duk sun ji daɗin maganganun da yayi, sai zabga murmushi suke yi suna sa mishi albarka.
"To kuje kai da ƙanwar taka ta gaida iyalinka. Ga mu nan fitowa. Fatima bi Yayanki kuje ki gaida maiɗakinsa da bata da lafiya."
Ya ƙare maganar da sauke idanunshi a kan Bibi, hakan ya fahimtar da ita yake yi. Dan haka ta miƙe ta bi bayan Maheer suka nufi hanyar ficewa daga ɗakin.
"Yauwa Malam na tuna sunan. BILHAƘƘI yake ce min."
Ta faɗa da sauri ta juyo tana kallon Malam lokacin da take gaf da ficewa daga falon.
"BILHAƘƘI?"
Ya maimaita yana mamaki.
"Eh! haka yake yawan ce min cikin kuka. BILHAƘƘI wannan rayuwar sam bai dace da ke ba. Tuntuni na ji ina son sunan"
Ta ƙarasa maganar tare da sauke ƙwayoyin idanunta a ƙasa, a zuciyarta tana ƙoƙarin tuno yanayin damuwar da take gani danƙare da fuskar mutumin a duk lokacin da yazo mata a cikin barci.
"Kinsan menene fassarar sunan?"
"A'a!"
Ta amsa haɗe da girgiza kai.
"Da gaskiya."
kallonshi tayi fuskarta da alamun rashin gane abinda yake nufi.
"Sunan ne na fassara miki. Da gaskiya shi ne fassarar Bilhaƙƙi. Kalma ce mai kyau, babu laifi a sunan."
Farare talatin da biyu ta buɗe su gaba ɗaya tana sakin tattausan murmushi mai haɗe da dariya.
"Daga yanzu sunana Bilhaƙƙi ko Malam?."
Dariya suka yi gaba ɗaya har da Maheer da yake tsaye a bakin ƙofar falon.
"Ƙwarai kuwa Bilhaƙƙi."
Ummee ta amsa tana dariya.
Tafiyar kurame suka yi a tsakaninsu har suka ƙarasa ƙofar ɗakin, duk yadda take ta ƙoƙarin ta haɗa ido da shi ya ƙi bata damar hakan har suka shiga ɗakin da Surayya take jinya bayan an amsa sallamarsu. Da sauri suka koma da baya suka fice daga ɗakin ganin Inna Lantana tana sa mata kaya, da alamun wanka aka yi mata.
Kamar haɗin baki duk sai suka nufi ɗakin Ummee.
"Wash Allah na..."
Ta faɗa a marairaice tare da zubewa ƙasa da hanzari ta kama babbar yatsar ƙafarta da hannu ɗaya hannu ɗaya kuma tana shusshushun zafi, nan da nan idanunta suka cicciko da hawaye.
Da sauri ya ƙarasa gurinta cike da kulawa yake ƙoƙarin kamo ƙafar da ta riƙe
"Ke me ya faru? Sannu. Mu ga ƙafar?"
Sai ta sakar mishi ƙafar gaba ɗaya tana hawaye da rurin wayyo zafi.
Ya gama dube-dube da jujjuya tattausar ƙafar haɗe da ɗaɗɗaga yatsar bai ga alamun komai ba.
"Wai bigewa kika yi ko menene?"
Ya tambayeta a tausashe yake kallonta, da yake ta riga shi shiga cikin ɗakin.
"Ni ji nayi kamar wani ƙwaro ya cije ni."
Tayi maganar cikin shagwaɓa tana tura baki gaba, ta kalle shi suka haɗa idanu tana mutsuttsuke ido da hannu ɗaya. Sai kuma tayi murmushin da yasa ya ramfo ta.
"Ƙarya ko?"
Ya tambayeta a hankali idanunsu cikin na juna.
"A'a! to ba kaine ba duk ka wani ƙi kallona."
Ta faɗa da wani irin salon magana da yasa shi yin shiru na wasu seconds yana ƙara kallonta. Sai kuma ya miƙe tsaye ya kama hanyar ficewa daga ɗakin bai ƙara yarda sun haɗa ba.
"Sannu Aunty, Allah ya baki lafiya."
Ya ji muryarta daga bayansa tana yiwa Surayya addu'a, sai a sannan ma yasan ta biyo bayanshi.
Ya ɗago ya saci kallonta a hankali, yana jin wani abu da ya rasa gane ko menene yana tsungulinshi a ranshi game da ita.
Karaf a idanun Surayya da tun shigowarsu cikin ɗakin idonta ke kan Maheer, duk sai taji ranta ya sosu.
Da ta kalli Bilhaƙƙi sai taji ƙirjinta yayi wani mugun bugawa, kauda ido tayi daga kanta zuwa gefe ɓacin ranta yana ƙara ninkuwa.
Ba komai ya ɗaga mata hankali ba sai zallar kyaun da ta gani da ɗanyen ƙuruciya, ga wani kwarjini na musamman da ta gani a fuskar yarinyar. Haka kawai a kallon farko taji ta tsane ta. Ta ɗaure fuska kuwa tayi katamau, ko ɗan murmushin da take yawan yi idan Maheer ya zo ganinta yau ta kasa yi.
"Ayya... Sannu Aunty. Me yake damunta haka Gangaran?"
Tayi masa tambayar fuskarta narke da tsananin tausayinta.
Kallonta yayi tana naniƙe kusa da shi, ƙiris ya rage jikinsu su dinga gogan juna. Cikin hikima ya zagaya can gefen gadon kusa da Surayya ya zauna.
"Cuta ce kawai daga Allah, amma da sauki sosai ma Alhamdulillah."
Ita ma ƙara matsawa kusa da Surayya tayi ta kamo tafin hannunta na dama ta riƙe ta ƙura ido kamar tana karantar wani abu daga ciki.
Ran Surayya in yayi dubu duk sun ɓaci, da ɗan ƙarfin jikinta da ta fara samu take ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Bilhaƙƙi, ita kuwa taƙi sakewa, sai tayi ma kamar bata fahimci me take ƙoƙarin yi ba.
"Za ki warke soon. Sannu Aunty."
Ta faɗa har lokacin yanayin tausayin bai bar fuskarta ba, idonta yana kan hannun.
"Allah yasa hakan. Sake mata hannu na ga kamar ta gaji."
Ya faɗa tare da amsar hannun Surayya ya sauke a kan katifan da take kwance.
Duk sai suka yi shiru daga haka, ita Bilhaƙƙi ta maƙale ta ƙi fita shi kuma Maheer ya ƙi cewa ta fita. Hakan ya ƙara ɗugunzuma ran Surayya, da takaici ya ishe ta ga shi babu bakin ƙorafi kawai sai ta runtse ido kamar mai bacci.
BILHAƘƘI
BAYAN WATA SHIDA
"Ummee ban ganta ba fa."
Ya faɗa muryarsa a buɗe yana sake buɗe labulen falon sosai yadda zai iya ganin komai na ciki, tare da leƙa kansa ciki yana kalle-kalle.
"To kila tana cikin ɗaki, ni dai yanzu nan na barta a falo tana kwance kitso."
Ko kafin ta ƙarasa maganar ma har ya cire takalmansa ya shiga cikin falon, a bakin ƙofar shiga cikin bedroom ɗin ya tsaya yana ta doka sallama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 25