Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Ni kuma a iya tunanina banga wanda zuciyata ta aminta in bashi aurenta sama da kai ba. Ko ba wannan ba ma yarinyar ta daɗe tana ƙaunarka. Amma idan baka so bazan tilasta ka ba, domin ba burina bane in aurar da ita inda za ta wulaƙanta. Sai in yiwa ɗan'uwanka Mustapha magana dan ya daɗe yana nuna min sha'awar aurenta ni kuma ina kaucewa zancen tunda na san ita kai take so." Bai san me zaice ba, tsakani da Allah ko da bai sonta zai iya aurenta kuma ya zauna da ita lafiya ko dan darajar Malam. Balle kuma ba shi da takamaimai sani na abinda yake ji game da ita, abinda ya sani dai kawai kuma ya tantance sam yanzu babu ko ɗigo na ƙiyayyarta a zuciyarshi. Yana jin wani ƙauna na musamman a zuciyarsa game da ita, jinta yake kamar wata ƙanwarsa ta jini da suka yi tsananin shaƙuwa. Bai bar cikin falon Malam ba sai da ya amince zai karɓi aurenta da hannu bibiyu, ya fita cikin layin gurin wani mai shago ya siyo katan-katan na ledojin sweet da cakulet wanda za a rarraba ma jama'a gurin ɗaura aure. Ya yi alƙawarin gobe da asubah zai taho da sadakin naira dubu talatin kamar yadda Malam ya yanke mishi in Allah ya yarda kafin a ɗaura auren. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tunanin duk abinda ya faru, ya waiga ya kalli Surayya da take barci a jikinsa hankalinta a kwance. Ya kalli agogon da yake ajiye a jikin gadon, ƙarfe uku da minti biyu na talatainin dare. A hankali ya zare jikinshi daga nata ya rufa mata bargo, ya shige cikin banɗakinsa ya ɗauro alwala, ya zura jallabiya ya tada sallah ya fara jero nafilfili dan neman tabbatuwar abinda yafi zama mafificin alkhairi tsakaninshi da Bilhaƙƙi. Bai tashi daga kan dadduma ba har zuwa ƙarfe huɗu da kwata, yana ta addu'o'i da neman zaɓin Allah. A daidai lokacin ne kuma wani barci mai nauyi yayi nasarar yin awon gaba da shi, bai farka ba sai ƙarfe biyar dai-dai inda kiran sallar farko da Ladan Malam Isiya ya kwaɗa ya dira bisa kunnuwanshi. Miƙa yayi gami da salati, ya yunƙura da bismillah ya miƙe tsaye, zuciyarsa wasai duk wani nauyi yanzu babu. Sai ma wani sihirtaccen farin-ciki da nishaɗi da yake ji yana ratsa gangar jiki da duk wani lungu da saƙo na sassan zuciyarsa. Da wannan dalilin yasa cike da karsashi ya faɗa banɗaki ya tsallo wanka bayan ya wadata ruwan da turarukan wanka kala-kala. A gurguje yake komai, duk da yana da tabbacin idan ya fita yanzu zai iya samun sallar asubah a masallacin Malam. Tunda lokaci ya canza shida saura minti goma ake yin sallar asubahi. Farar shadda ghalila sabuwa kar a ire-iren waɗanda ya ɗinka bai taɓa sakawa ba ya ɗauko ya sa, yana shiryawa shi kaɗai yake sakarwa kansa murmushi kamar anyi mishi bushara da aljannah. A wannan lokacin Surayya ta farka saboda yawan zurga-zurgar da yake yi a cikin ɗakin, idanunta da suke cike da bacci ta ware a hankali take kallonshi. Ta buɗe baki za ta yi magana wani ƙaƙƙarfar hamma ya suɓuce mata dole ta rufe bakin da hannun dama. "Sweetat...? Lafiya kuwa?" "Me kika gani? Wankan ne ya baki mamaki ko mene?" Ya tambaye ta yana fesa turare a lungu da saƙo na jikinsa. "A'a! Wanka ai kana yi duk asubah. Shigar galleliyar shadda saɓanin ɗaya daga cikin jallabiyoyinka ta zuwa sallar asubah shi ne abinda ya bani mamaki. Ina tunanin akwai dalilin canjin ko?" "Eh ƙwarai kuwa." Ya amsa yana dariya. Ya ajiye turaren a gaban madubi ya ɗauki hularsa ya fara karyawa. "A masallacin Malam zanyi sallar asubah. Idan na fita yanzu bazan dawo gida da wuri ba sai bayan sallar azahar shi yasa kawai na shirya gaba ɗaya." Ya kafa hular a kansa ta zauna cas, ya kalli madubi ya ƙara gyarata sosai. Fuskarsa sai sheƙi take yi kamar wata a daren goma sha huɗu, ya kalle ta ya haske ta da tattausan murmushi. "Ki tashi kiyi sallah. Ki kwantar da hankalinki. Idan na dawo akwai muhimmiyar maganar da zanyi da ku ke da Rabi." Makullin motarsa ya ɗauka ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ita kuwa ta bi shi da kallo baki da hanci buɗe cike da rashin abin cewa. Sai da ya isa bakin ƙofar fita daga ɗakin zuwa falo ya waigo ya kalle ta yana murmushi. "Sweety yau babu ko addu'ar Allah ya tsare?" "A dawo lafiya." Ta faɗa da ƙyar kamar wacce aka tura wa dutse a baki. "Allah yasa haka." Ya amsa tare da rufe ƙofar ɗakin. Tana nan zaune tana saƙe-saƙe ta ji tashin motarsa yana ɗumamata, can kuma ta ji mai gadi ya buɗe mishi get ya ja motar a guje ya fice daga gidaan. Fitarsa yayi dai-dai da wani mugun faɗuwar gaba da tayi, ta runtse ido da sauri kamar aradu ne ya faɗo a ƙirjinta saboda nauyi. Tana ji aka ta da sallar asubahi a masallacin kusa da su, daƙyar ta yunƙura ta miƙe gaɓɓan jikinta sai ciwo suke yi mata kamar wacce aka naɗawa shegen duka. ****** ****** "Gaskiya Gangaran ka tabbata. Wai dan Allah dama da gaske kake yi? Ka san Allah? Wallahi da naga saƙonnan na zaci mafarkinka ne kayi sharing da ni." Ya ƙarasa maganar yana tuntsura dariya. Shi ma dariyar ya kwashe da shi yana sha fa kwantaccen gashin kanshi. "Zauna nan dai Alaji garin kallon ruwa kwaɗo yayi maka ƙafa. Ba dai kai ka maƙale a ɗaya ba? Da gaske ta uku nake faɗa maka Alaji. Ina fatan dai ka fito? ka san da an idar da sallah za a ɗaura auren, ni yanzu haka ma ina ƙofar gidan Malam, Yusuf ma ya ce min ya kusa ƙarasowa." "Abu namu maganin a kwaɓe mu, ai dole ma in himmatu. Ka san na fi Yusuf kusa da su Malam yanzu zan ƙaraso..." "Yauwa! Mukhtar kar ka faɗawa Maman Imam fa. Da yake batun auren ya taso jiya da daddare ne ko su Surayya ban sanarma ba. Kuma na fi so kafin su ji a bakin kowa su fara ji daga bakina." "Ok.. ba damuwa, hakan ma dabbara ce. Sai na iso." Da haka suka ajiye wayoyin a duk ɓangarori biyun, sauri sauri ya gangara kusa da gidan Malam ya gyara fakin ɗin motar ya fita, masallacin ya nufa kai tsaye da sassarfa dan jin har Ladan ya fara tada iƙama. Alƙawari ya cika. Da kyakkyawar niyya da zuciya mai nufin ƙulla alkhairi bayan idar da sallar asubahi Malam ya bada auren Bilhaƙƙi Aliyu(Rashin sanin takamaimai sunan mahaifinta yasa Malam yi mata inkiya da Aliyu, dan gudun ƙananun maganganu. A zuciyarsa yayi tunanin idan yayi mata amfani da sunanshi a matsayin uba zai ɗiga wa mutane ayar tambaya a zukatansu. Da kyakkyawan niyya yake faɗa ma mutane ƴar ƙaninsa ne, ba dan komai yayi hakan ba sai don ya siya mata mutunci kuma ya kore duk wani zargi ko ƙananun maganganun da zai iya zuwa ya dawo daga gurin mutane.) Ladan Malam Musa mahaifin Surayya shi ya zama waliyyin Maheer Abdulganiyyu wajen karɓa mishi auren akan sadaki naira dubu talatin cif! Lakadan ba ajalan ba. Mutane da ba a iya musu sai mamaki suke yi ganin auren bagatatan babu wani shiri, kuma ɗaura aure da asubah kamar na marassa gaskiya? Babu dai wanda ya kawo kushe sai fatan alkhairi da fatan Allah bada zaman lafiya da ake ta yi ga Maheer. Shi kuwa Ango yana cikin manyan abokansa biyu Yusuf da Mukhtar bakinshi har kunne, fararen haƙoranshi talatin da biyu a waje kamar gonar auduga dan tsabar farin cikin da yake ciki a fili da baɗinin zuciyarsa. Nan da nan aka fara rarraba ɗaurin goro, dabino, sweet da cakulet a manyan ledoji ga duk mutanen da suka shaida ɗaurin auren. Zuwa ƙarfe bakwai da kwata na safe anyi komai an gama mai afkuwa ta afku, Bilhaƙƙi ta zama ta Maheer halak malak. Su Mukhtar suka yi mishi sallama da cewar sai sun gayyato sauran abokansu anjima su zo ganin amarya, dan a lokacin sama da ƙasa sun buga amma ya hana su shiga cikin gidan Malam ɗin balle har su ganar mishi Amarya. Daga nan falon waje na Malam suka yi sallama ya shiga cikin gidan su kuma suka wuce a motocinsu suna tsokanarshi. BILHAƘƘI Daddaɗan ƙamshin turaren jikinsa ne ya fara alamta mata zuwansa, kafin daga bisani ta ji tattausar muryarsa yana doka sallama a ƙofar ɗakin. Dangwarar da kofin tea ɗin da take sha tayi a ƙasa, da sauri ta lulluɓa ta sake tattakurewa a cikin bargo ta ƙudundune guri ɗaya a kan gadon. Wani matsanancin kunyarsa ne yake ratsa ta tun daga babbar ɗan yatsar ƙafarta har zuwa maɗigar kanta. Ƙirjinta sai luguden daka yake yi, da gaske tsoron ganinshi take yi, domin bata san da wani ido ya karɓi aurenta ba. Tunanin yadda auren mai kama da a mafarki yazo mata ta fara yi. 'Da yake jiya ciwo yasa ta yi baccin wahala tare da taimakon allurai shi yasa ƙarfe huɗu da wasu ƴan daƙiƙu na asubah ta farka, a lokacin ciwon ya faɗa mata sosai ba kamar jiya ba. Ummee ta gani zaune akan dadduma tana lazumi, motsin da tai tayi akai-akai yasa Ummin ta maida hankalinta kanta. "Kin tashi? ya jikin naki?" Ta tambaye ta cike da kulawa. "Da sauƙi sosai Ummee." Ta amsa a kasalance. "Allah ya ƙara afuwa. Sa hijabinki bari in kira Malam ya ce akwai maganar da zaiyi da ke." Bata jira amsawarta ba ta fice daga ɗakin. Can bayan wasu daƙiƙu sai suka shigo ita da Malam, bayan tambayarta yanayin jikinta da yadda take ji ne ya faɗa mata shawarar da ya yanke na ɗaura musu aure ita da Maheer, ya bata damar idan bata amince ba kar ta ji kunya ko kuma ta tauye kanta ta faɗa zallar gaskiyar zuciyarta. Shi bazaiyi abinda ba ta so ba. Kunyar Malam ɗin da tsananin ƙaunar waɗannan iyalan ne ya ƙara lulluɓeta, sai ta ja hijabinta ta rufe fuska. Su da ɗansu yake ɗan asali basu ƙi ta ba sai ita da ba a san cikakken asalinta bane za ta ƙi ɗansu? kai tsaye ta ce ta amince...' "Ka shiga ciki mana Magaji. Kila bacci ne ya sake ɗaukarta." Muryar Mummy da taji tana faɗin haka yasa tayi saurin katse tunanin da take yi, da mugun sauri ta sake curewa guri ɗaya. Yana shiga sai yaga tana ta mutsu-mutsu a cikin bargo. Nan da nan kuwa ya harbo jirginta. Ya saki wannan tattausan murmushi ya tsaya ƙyam! a guri ɗaya, ya ci gaba da kallonta yana karantar yanayinta. Ita kuma jin shiru yasa ta buɗe rufar kaɗan, a hankali ta leƙo da kanta waje. Karaf suka haɗa ido, cike da matsananciyar kunya da sauri ta sake ɓoye kanta tana murmushi. "Yarinya na ganki fa." Ko kafin ta ce komai ya haye kan gadon gaba-ɗaya ya ɗagata ita da abin rufar ya haɗa ya rungume a ƙirjinsa. Tsawon wasu daƙiƙu yana sauke ajiyar zuciya, daga can ƙasan ransa farin cikinsa yana ƙara ninkuwa. Ita ma luf tayi idanunta a rufe take sauke sassanyar ajiyar zuciya, mai alamta kwanciyar hankali da farincikin zuciya ta samu abinda ta daɗe tana muradi. A hankali kuma cike da wani irin nutsuwa mai tafe da daddaɗan shauƙi yake warware bargon daga jikinta, har ya buɗe ta gaba ɗaya ya tattare bargon ya ajiye a gefe. A nutse ya fara ƙare mata kallo tun daga kan kyakkyawar fuskarta zuwa ƙasa, sanye take da kayan bacci masu ɗan kauri riga da wando. Har lokacin idanuwanta suna lumshe, ƙirjinta sai luguden daka yake yi. Tana jin kaifafan idanuwansa masu kama da maganaɗisu a gare ta suna kara-kaina da zagayawa a duk wani sassan jikinta. Can ƙasan mararta ne ya sake tsirga mata da wani matsanancin ciwo, da sauri ta ware idanunta gaba ɗaya ta buɗe su tare da yamutsa fuska. "Menene... uhmmm...?" Ko kafin ya rufe baki ta kai mishi wani mugun riƙo tana tattakure jikinta a cikin nashi, tana ƙara riƙe shi sosai. Cike da raki da jin raɗaɗi ta ce "Asssshhhhh... Gangaran, Marata..." Sai kuma hawaye shar-shar kamar an buɗe famfo. Sai juye-juye take yi tana ƙara ruƙunƙume shi cike da azaban ciwo. Hankalinshi ne ya ɗugunzuma, zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta. Da alamun ya manta ma a inda suke, ɗago ta yayi daga jikinsa ya ɗage rigarta ta ƙasa yasa hannu a ƙasan cibiyarta, da tunanin ko nan ɗin ne yake mata ciwo "Sannu, Nan ne yake ciwon?" Yayi maganar kamar yana mata raɗa. "A'a ƙasa fa" Ta amsa cike da shagwaɓa, wasu sabbin hawayen suna sake ɓalle mata. A hankali ya ƙara ƙasa kaɗan da hannunsa yana shafa mata mara sai kuma ya cire hannunsa da sauri kamar wanda shocking ya ja. Duk da sanyin da ake yi a garin shi zufa yake yi, ya ja ta jikinsa ya rungume tsam-tsam a ƙirjinsa yana bubbuga mata baya alamun rarrashi. "Baya na... cinyoyina ciwo... dan Allah ka danna min..." Ta faɗa cikin matsanancin kuka da magagin ciwo. Abin dariya abin tausayi, Bilhaƙƙi ke ciwon Maheer ke zufa da jin raɗaɗin a jikinsa, gaba ɗaya ma kamar a ruɗe yake, ya ruɗe ya susuce kamar wanda bai taɓa aure ba, shi bai taɓa ganin irin wannan ciwon a gurin matansa ba. Shi kuwa ciwon mara kamar ana ƙara tunkuɗoshi sai gurmususu take mishi a jiki tana kuka, gaba ɗaya ta gama yamutsa gallalliyar shaddar da take jikinshi. Jin yadda take ta ƙara maimaita bayanta da cinyoyinta ciwo suke yi yasa shi miƙar da ƙafafunsa akan gadon ya kwantar da ita rub da ciki akan cinyoyinsa kamar wata ƴar bebi, ya yaye rigarta sama sosai ya fara danna mata bayan a hankali da hannayensa biyu haɗe da ɗan bubbugawa kamar yana lallaɓa jaririya tayi bacci. Cikin sa'a kuwa lokaci kaɗan sai ta fara sauke ajiyar zuciya, da alamun sosai take jin daɗin abinda yake mata. Ya leƙa fuskarta yaga har lokacin idanunta a rufe suke, sai dabbara-dabbarar hawaye a kumatunta. "Ciwon ya daina?" "Ya yi sauƙi dai." Ta faɗa a shagwaɓe kamar za ta sake fashewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke, ya kalli bayanta da yake buɗe, sai a lokacin idanunshi suka kai kan maɓallin bra ɗinta mai ruwan madara. Yayi kamar zai kai hannu ya ɓalle sai ya kwaɓi kanshi, ya maida idanunshi kan gadon bayanta. Fatan jikinta irin mai kyau ɗinnan ne ga sheƙi, ita ba baƙa ba ita ba fara ba. Karaf idanunshi suka gangara har zuwa kan mazaunanta da tudunsu ya ɗago a wandon baccinta. Saurin watsar da wannan tunanin yayi a lokacin da yaji tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa, a kunyace ta saukar da idanunta ƙasa ba ta yarda sun haɗa ido da shi ba, ta janye jikinta ta matsa daga kusa da shi. Hannunta ta ɗaga za ta saukar da rigarta ta baya da sauri yasa hannunshi ya saukar mata da rigar. "Na gode" Ta faɗa da muryarta ƙasa-ƙasa. "Keeee godiyar miye? aikina ne fa." Yayi maganar fuskarsa fal da murmushi, ƙoƙarin haɗa ido yake yi da ita ta ƙi ba shi damar hakan, sai ya matsa kusa da ita, ita ma ta matsa baya. A haka ya matso ta matsa har suka ƙure ƙarshen gadon. Sai kawai ta takure kanta a cikin cinyoyinta tana murmushi. Shi baisan duk kunya yake bata ba. Kanshi ya cusa kusa da nata cikin raɗa ya fara magana. "Da gaskiya amaryar Gangaran kinyi farin ciki kuwa? Wani tukwuici za ki bani yau da zai tabbatar min kina taya ni farin-cikin da zuciyata take ciki?" "Kai Maheer... wani tukwuici kuma...?" Tayi maganar cikin sakalci da wani irin wawuyar shagwaɓar da tayi mugun tafiya da ɗan sauran nutsuwarsa. Kamar zai sake janyota zuwa jikinshi dan samun sauƙi-sauƙi sai kuma ya maze. Ya fara hurga idanunshi lungu da saƙo na cikin ɗakin yana ƙare mishi kallo, sai kuma yayi murmushi. A zuciyarsa ya ce 'Gaskiya cikin iyayenshi mata biyu duk wacce tayi tunanin mayar da Bilhaƙƙi ɗakin ƴanmatan gidan a safiyar nan da ta tabbata halaliyarshi ba ƙaramin taimaka mishi tayi ba. Shi kam da ya zai iya fita da wannan yamutsattsen kayan na jikinshi? Amma yanzu zai fita salin-salin ba tare da an ganshi ba tunda ɗakin yana can ta ƙarshen gidan ne, kuma akwai siririyar hanya ta baya da zai iya bi wacce in ba rashin sa'a yayi ba zai wahala iyayen su ga fitarshi.' "Yanzu haka za ki ta fama da wannan ciwon har sai baƙon ya tafi? kwana nawa ne yake yi?" Ya tambayeta da fuskarsa mai baiyana zallar tausayinta, alamun ya tuno irin azabar da ta gama sha ɗazun. Wayyo Allah... ina ma ƙasa ta tsage ta shige don kunya, can gefe ta maida kanta da jikinta tana ƙara ɓoye kanta tsakanin cinyoyinta. 'Ita yana bata kunya wallahi, bata taɓa tsammanin akwai lokacin da zai zo da za ta dinga jin kunyarshi har haka ba. Ita yayi ya tafi ma kar Ummee ko Mummy wata a cikinsu ta shigo a gansu a yanayin da suke ciki.' Da ya fahimci manufarta sai yayi dariya kawai, ya kwanta a kan gadon. "Kinga yarinya gara ma ki faɗa min, idan ba haka nan yini nan kwana saboda idan ciwon ya motsa in dinga miki matsa miki baya da cinyoyi..." "Wayyo Maheer ciwon na jiya da yau ne fa kawai. Ka ga ni na ma ji sauƙi, ka tafi in samu inyi wanka inje gurin Ummee." Ta ƙarasa maganar idanunta a nannarke take kallonshi, kamar za ta saka kuka. Da zallar gaskiyarsa ya ce "Kinga muje kawai in taya ki wankan tunda baki gama jin ƙarfin jikinki ba..." "Ni dai a'a!" Ta katse shi da sauri tana wawware ido a tsorace. "Ka bari zan iya yi da kaina. ka ga ni na warke ma gaba ɗaya dan Allah ka tafi." Ya ɓata fuska kamar ya shaƙa "Kora ta kike yi ko?" Tayi narai-narai da ido ta matsa kusa da shi sosai "Yi haƙuri ba fa haka bane Allah..." "To yaya ne?" Ya tambaye ta murya a tsaitsaye yana sake tamke giran sama da ƙasa. Tsoro ne ya fara kamata, lokaci ɗaya yana neman koma mata wancan murɗaɗɗen Maheer ɗin da ta sani a farko wanda sam baya ƙaunarta. Idanunta a ƙasa take mummurɗa yatsun hannayenta "Kawai... kawai... ina jin tsoron kar su Mummy su shigo. Ka yi haƙuri dan Allah..." Wawan rungumar da ya kai mata ba tare da ta ankara ba yasa ta kasa aje numfashin maganarta dai-dai "I'm sorry Babe. Da wasa nake miki tsawa." Ya raɗa mata a kunnenta yana dariya ƙasa-ƙasa. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta runtse ido, ƙara ƙanƙame shi tayi tana jin wani irin baƙon yanayi yana ratsa ƙashi da ɓargon jikinta. "Je kiyi wankan anjima zan dawo kinji?" Ɗaga kai kawai tayi alamar ta ji, bakinta nauyi yayi mata ta kasa amsawa. Raɗan da yake yi mata a kunne a jikinta ji take yi kamar yana mata tafiyar tsutsa. "Me zan taho miki da shi?" Ya sake raɗa mata da wani rikitacciyar murya, domin ba ita kaɗai take karɓar saƙon ba shi ma yana ji a jikinsa. Ƙanƙameshi ta sake yi kamar za ta tsaga ƙirjinsa ta shige, ko kuma tana tsoron kar a raba jikinta da nashi. Da ƙyar ta yi ƙumajin buɗe tsukakken bakinta da yayi mata nauyi ta ce "Bana buƙatar komai" "Ba komai fa kika ce Babe ki tuna dai." Yayi maganar yana dariya ƙasa-ƙasa. Nauyayan idanunta da suka ƙara ƙasa-ƙasa ta sauke su a kanshi, ta tura baki gaba "Ni dai ba komai..." "Har Pad bakya buƙata?" Ƙwace jikinta tayi da sauri ta dira daga kan gadon ta faɗa banɗaki ta danno ƙofar cike da matsananciyar kunyarsa. Dariya yayi mai isarsa kafin ya ɗan gyaggyara rigarsa ya ɗauki hula, makullin motarsa, ƙaramar wayarsa ya fice daga ɗakin. Ta baya ya bi, yana tafe saɗaf-saɗaf yana waige-waige kamar mare gaskiya har ya fice daga gidan ba tare da ya haɗu da ɗaya daga cikin iyayen na shi ba. ***** ****** "Da girman kujerarki Sarauniya. Amarya a gurin mai martaba Sarki Abdulfatah na biyu. Ranki ya daɗe Innata ta kaina. Allah ya ja zamaninki ki daɗe kina yi ki ƙare da kyakkyawan cikawa." "Ameen ya Allah." Ta amsa daƙyar, muryarta baiyane da ƙasaita da matsanancin mulki. Ta sake gyara kishingiɗar da tayi a kan tuntum ɗin sarautar, ta gyara riƙon wayar a kunnenta tana jan fasali kamar baza ta ƙara tankawa ba. Har sai da daga can ɓangarenshi ya ce "Ina jinki Fulani." "Abdulganiyyu ya iyalanka?" "Duk lafiya ƙalau suke Fulani. Da fatan ku ma haka? Ya jikinki?" "Jiki mun gode Allah Abdulganiyyu. Gamu nan har yanzu muna turawa." "Ubangiji Allah ya raba ku lafiya Innata." Yayi mata addu'ar muryarsa na baiyana tsananin tausayinta. Daga can ɓangarenta hannu ta ɗaga ta shafi turtsetse cikin da ya turo sosai a cikin alkyabbar da yake jikinta, sannan ta amsa addu'ar a kasalance. Kafin ya ce wani abu ta ci gaba da magana jikinta a sanyaye, bisa ga dukkan alamu tana cikin tsananin damuwa amma fuska da muryarta na ƙoƙarin ɓoyewa. "Abdulganiyyu ka san mun shiga wata na goma sha huɗu, har yanzu kuma ba wani motsi. Mai martaba ya fitar da ranar da likitocinsa zasu yi min aiki, nan da sati biyu za a fitar da cikin in dai har zuwa lokacin haihuwar bata zo ba. Ina jin tsoro Abdulganiyyu, da gaske ina matuƙar jin tsoro. Ban sani ba ko wannan cikin shi ne zai zama silar ajali na... Idan zai yiwu ina son ganinka kafin lokacin." "Karki damu Ranki ya daɗe, babu komai da zai faru in Allah ya yarda sai alkhairi. Muna addu'a, kuma za mu ci gaba da bada ƙaimi, Ubangiji maji roƙon bawa ne. Na tabbata bai manta da halin da kike ciki ba, in Allah ya yarda addu'a ta karɓu sai dai jinkirin biyan buƙata. Ki kwantar da hankalinki kinji?" "Insha Allah. Na gode Abdulganiyyu. Allah ya maka albarka." "Ameen Inna. Na gode." Ya amsa cikin jin daɗi, kafin ta ƙara cewa komai ya ci gaba da cewa "Kamar yaushe kike buƙatar in zo?" "Kar ya gaza nan da sati ɗaya. Idan ka yi jinkiri da yawa kuma nan da kwanaki goma." "Tom In Allah ya yarda bazan wuce lokacin ba. Allah ya ƙara miki lafiya Ranki ya daɗe." "Ameen ya Allah. Ka taho min da Magajin Malam, shi ma ya kwana biyu bai zo ba sai a waya yake gaishe mu." "To za mu taho tare da shi. Sai mun iso." Da haka suka ajiye wayoyin a duk ɓangarorin guda biyu. Sa ke motsawa tayi cike da ƙasaita ta yunƙura daƙyar ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi, nan take bayin da suke zagaye da ita wasu suna firfita wasu suna mammatsa mata ƙafafu suka fara jera mata sannu, haɗe da addu'ar Allah ya raba ta da cikin jikinta lafiya, Allah ya ja zamaninta. Ta kalli Amintacciya kuma Shugabar bayinta mai suna Lantana ta yi ɗan murmushi ta ce "Na gode Lantana, ku bani guri. Ina buƙatar in huta." "Hutawarki lafiya Fulani, baya goya marayu. Allah yaja zamaninki ki daɗe kina yi a zuciyar mai martaba. Allah ya raba ki da cikin Yarima lafiya." Tattausan murmushin da bai cika ɓacewa daga fuskarta ba ta sake sakar musu. A zuciyarta ta amsa kyawawan addu'o'insu. Ta yunƙura da ƙyar ta miƙe suna ta jera mata sannu, cike da nutsuwa take tafiya a hankali har ta shige can cikin turakarta. Ta daɗe a tsugunne kanta a ƙasa kamar an manta da ita. Tun tana jero kirari Babbar baiwar da take gefenta tana amsawa har ta

Chapter 14 of 25