daga idanunta,cike da tausayawa da damuwa Afrah ta dafa hannunta ta ce.
"Ki yi haƙuri idan maganganu na sun ɓata ran ki,ina ganin kawai mu bar maganar dawowata nan ɗin,zan dinga leƙo ku muna gaisawa lokaci zuwa lokaci."
Da sauri Lamyah ta jimƙe hannun Afrah,sannan ta ce.
"Sam ba kalaman ki bane suka sanya ni shiga damuwa,na tuna da mahaifina ne wanda ya dage ya yi tsaye tsayin daka har na cimma burina na zama cikakkiyar ƳAR RAWA mai certificate a can ƙasar mu,saboda lokuta da dama shi yake kai ni ajin ɗaukar darasin rawar,idan an tashi ya koma ya ɗakko ni duk da cewa Ammi bata so."
"Allah sarki,Allah Ya yi masa rahama, addu'a za ki dinga yi masa da zarar kin tuna sa,ni ma haka nake yiwa iyayena."
Share hawaye Lamyah ta yi sannan ta ce.
"To yanzu za ki zauna da mu ɗin?"
Ɗaga kai Afrah ta yi,sannan ta ce.
"Zan zauna da ku,daga safe zuwa yamma,da yamma na koma gidana na shirya na wuce hotel ɗin da nake rawa,bana dawowa sai sha ɗayan dare zuwa sha biyu."
Shiru Lamyah ta yi kafin ta ce.
"To shikenan,ni kuma In shaa Allahu zan dinga baki albashin kula da gida da Mubarak duk ƙarshen wata."
"Na gode."
Hira suka ci gaba da yi,har sai da su Lamyah suka kammala cin abinci Afrah ta kwashe kayan wajen,ta gyara duk abinda aka ɓata sannan suka zauna,Lamyah na ta bata labarin shaƙuwar dake tsakaninta da iyayenta,itama Afrah tana bata nata labarin. A haka har aka kira sallar azahar,suna idar da sallah Afrah ta ɗora musu abinci mai daɗi,tana gamawa ta kaiwa Baba Musa da Bala nasu sannan ta dawo suka baje a parlour suka ci suka ƙoshi. Nan da nan Lamyah ta saki ranta ta manta da ƙuncin da take ciki,sai dai lokaci zuwa lokaci takan yi shiru ta hau tinanin iyayenta,da kuma makomar rayuwar su,duk da cewa ta karanta littafin da mahaifinta ya bata,wanda Aminee ce ta fara yin rubutu a cikinsa kafin El-mustapha ya ɗora nasa akai,ya bata labarin yanda ƴan'uwasa suka kafa masa ƙahon zuƙa,sai ATM card dake jikin bangon littafin na bankin Zenith,da kuma maƙudan kuɗin dake cikin jakar da ya bata da takaddun makarantar ta,sai wasu mahimman takardu da ya umarceta ta damƙawa Mus'ab a duk sanda suka haɗu.
Yamma na yi Afrah ta yi musu sallama ta wuce gidanta,sai da ta shiga YouTube ta kunna kiɗa a wayarta ta tiƙi rawa tana koyon sabbin stapes sannan ta shiga wanka ta ƙalƙale jikinta,kaya masu bayyana surar jiki ta sanya sannan ta ɗora abaya a samansu, tana kammala shiri ta fesa turare mai sanyin ƙamshi ta saka takalminta sabo mai tsini da bata taba sanyawa ba,tabarau ta manna a idanunta sannan ta ɗauki jakarta ta kulle gidan. Yaron da ya samar mata aiki a hotel ɗin da take yin rawa ne ya zo ya ɗauke ta suka wuce.........
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA:HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 13.
Muryar Mus'ab na sauka a dodon kunnen El-mustapha sai zuciyarsa ta karye,nan take wasu zafafan hawaye suka hau kwaranya daga idanuwansa,cikin matsanancin kuka ya ce.
"Ɗan'uwana....a yau Allah ya karɓi ran...Aminatu,ta tafi..ta barni da yaranmu da muka ci buri mai...girma akan su"
A kiɗime Mus'ab ya miƙe tsaye,har sai da A'isha sarkin son jiki ta tashi zaune ta na binsa da kallo,tare da tambayar abinda ya gigita shi cikin ƙanƙanin lokaci haka. Barin ɗakin ya yi ya tafi parlour ya samu kujera ya zauna sannan ya dafe kansa,cike da tausayawa ya ce.
"Ɗan'uwana ka ce Aminatu ta rasu? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,Allahummaghfirlaha warhamha wa afu anha wa akramha nuzulaha,Allah Ya bamu haƙurin rasa wannan baiwa taSa mai tsananin ibada da kyawawan halaye,Ubangiji Allah Ya sanyaya mana raɗaɗin rashin ta,tabbas rashin Aminatu namu ne baki ɗaya Ɗan'uwana,ina nan tafe yau ɗin nan,gashi ɗan ka baya nan na tura sa Kano duba wasu kayan mu da za su sauka gobe,da ya dawo za mu sake dawowa,kafin nan ka yi haƙuri ka kula da yaran."
Kukan A'isha ne ya sanya Mus'ab saurin juyawa bayansa,daga yanayin ta ya gane ta saurari dika hirar da suke yi,a can ɓangaren kuwa El-mustapha ne ya ce.
"Kar ka zo inda nake Ɗan'uwana,kar ka manta a irin haɗarin da nake ciki ni da iyalina,na tabbata a yanzu haka ƴan'uwana idan suka san ka kai ma ba tsira za ka yi ba daga kaidin su,ina nan dama ina wani shiri,da komai ya kammala zan neme ka."
Cikin tsananin damuwa Mus'ab ya ce.
"Ta ya za ka ce haka bayan ka na buƙata ta a ƙusa da kai?."
Rintse idanu El-mustapha ya yi wasu zafafan hawayen suka sake zuba,cikin sanyin murya ya ce.
"Su ne jinina na,da su ne na haɗa uwa da uba,amma ka fiye min su sau dubu,Allah Ya faranta maka Mus'ab,kai sadiƙina ne,ka yi min alƙawarin ba za ka tako ƙafarka zuwa wajena ba matsawar ba ni ne na neme ka da ka yi hakan ba."
Wani irin nauyi ƙirjin Mus'ab ya yi bai gushe ba har sai da hawaye suka fara ambaliya a kuncinsa shima,cikin dakiya da jarumta ya ce.
"Na yi maka alƙawarin ba zan zo ba,har sai ka neme ni da kan ka,kai ma ka yi min alƙawarin kula da kan ka da su Lamyah,dan Allah ka tattara duk wata dukiya da suke ganin kana da ita a ƙasar nan ka miƙa musu ku dawo Nijer ko Nigeria,Allah Ya tsare min ku Ya kare ku daga sharrin mutum da dikkan abun ƙi,Allah Ya jiƙan Aminatu."
"Na yi maka alƙawari babu jimawa za ka ji daga gare ni,Allah Ya amsa addu'o'in ka Ɗan'uwana,ka lallashi A'ishatu ka bata haƙuri."
Sallama suka yi da El-mustapha, Mus'ab ya tashi da ƙyar ya isa wajen A'isha da ta haɗa hawaye da majina waje guda ta dame kwalliyarta,da ƙyar ya ɗaga ta daga ƙasan da ta baje ya rungume ta yana lallashinta,cikin kuka ta ce.
"Shike nan na rasa ƴar'uwata? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'u,yanzu da wanne ido zan kalli Aminullahi na sanar da shi wannan rashi da muka yi?"
"Yanda mijinta da ƴar da ta tsugunna ta haifa da cikinta za su yi haƙuri,shima haka zai yi haƙuri dole, addu'ar mu ta fi buƙata yanzu ba ya wane zai ji ba idan ya ji labarin rashin ta,ki share hawayen ki,irin wannan kukan da kike yi ne Annabi ya haramta,kin zauna kin fincike ɗanƙwali,kin farka gaban rigar ki,kina ta baza gashi kamar wadda ciwon hauka ya yiwa dirar mikiya,dan Allah ki riƙe kan ki ki sanyawa zuciyarki haƙuri,Allah Ya jiƙan Aminatu."
Da ƙyar Mus'ab ya samu A'isha ta dena iface-iface da kukan da take yi na rashin Aminee. Da yamma Aminullahi ya kira Mus'ab suka gaisa,bayan sun gaisa ne yake sanar da shi gaba ɗaya wunin ranar ya yi sa ne cikin rashin kuzari da yawan faɗuwar gaba,anan take Mus'ab ya sanar da shi abinda ke faruwa tare da bashi haƙurin rashin da suka yi, addu'o'i ya sanar da shi wanda zai dinga yi saboda ya samu natsuwar zuciya,daga ƙarshe suka yi sallama. Aminullahi ya basu mamaki ƙwarai na yanda ya ɗauki abun da kyakkyawar fahimta,domin kuwa tin da ya yi kuka a wannan lokacin bai sake kokawa ba sai tsananin addu'a da ya dinga yiwa Aminee,tsananin son ganin Lamyah da Mubarak ne suka cika zuciyarsa,har ya so ya saci jiki ya je ya gan su,sai dai kyakkyawan gargaɗin da ya samu daga wajen El-mustapha ne ya hana shi zuwa wajen nasu. Ta ɓangaren Lamyah da Aminullahi kuwa tinda ya yi mata gaisuwa be sake kiranta ba,dan kuwa fushi yake yi da ita,saboda bata kira sa ta sanar da shi rashin Amminsa da suka yi ba,ita ta zama mai surutu mara amfani a cewar sa,tinda za ta iya magana akan komai,amma banda abubuwa masu mahimmanci.
*DUBAI.*
A cikin ƙasa da awanni uku aka gyara gawar Aminee aka sallace ta,wanda ba karamin taron jama'a ta samu ba,saboda karamci da mutuncin El-mustapha, ƴan'uwansa sun zo yi masa ta'aziyya gudun surutun mutane da kunji-kunjin da zai yaɗu a gari. Ana dawowa daga kai gawarta kowa ya watse aka bar El-mustapha shi kaɗai da yaransa a gabansa ya zuba musu idanu yana kallon su cike da tausayawa. Gani ya yi cikin ƙanƙanin lokaci Lamya ta rame sosai,idanuwanta duk sun zurma,hancinta dogo mai ɗan tudu ya sake fitowa,shafa kuncinta ya yi a hankali sannan ya ce.
"Allah Ubangiji ya sanyaya miki zuciyarki,Allah Ya jiƙan Aminatu ya raya mana Mubarak."
Ɗauke ƙwallar da ta zubo masa ya yi kafin ya ɗauki Mubarak da ya fara motsawa yana so ya yi kuka, kitchen ya shiga da yaron ya haɗo masa madara ya zauna yana basa,sai dai sam ya ƙi karɓa sai kuka ya ke,cike da tsananin gajiya da karyewar zuciya El-mustapha ya zauna a ƙasa ya rungume yaron yana sumbatarsa hawaye na zuba a idanunsa. Yana cikin wannan yanayin ne Lamya ta shiga kitchen ɗin ta zauna a gabansa,kallon hannunta ya yi da aka ƙarawa ruwa da allurai,murmushin ƙarfin hali ya sakar mata kafin ya ce.
"Kamata ya yi ace kina hutawa yanzu,haka ma likita ya ce."
"Ka fini buƙatar hutu a wannan lokacin Baaba,kawo shi na bashi abincinsa,dan na fika iyawa."
Murmushi ya yi mai kyau ya kalle ta sannan ya ce.
"Au habaa ? Kin fini iyawa fa ki ka ce? To gashi bismillah."
Cike da rashin ƙwarewa Lamya ta karɓi yaron ta ɗora a saman cinyar ta,ta fara jijjigasa,sannan ta karɓi madarar hannun El-mustapha ta fara bashi,tin yana ƙin karɓa yana kuka har ya cafke bakin fidar ya fara tsotsa a yunwace,kallon su El-mustapha ya hau yi cike da matsanancin tausayi,shi kenan yanzu Lamyan sa ce za ta dinga kula da jaririn ƙaninta,ita kanta tana buƙatar kulawar uwa musamman da take a cikin shekaru na tashen balaga. Cikin sauri ya sumbaci goshin Lamyah ya mike tsaye ya ce mata.
"Idan ya gama sha ki sauya masa pampas,idan kuma ba za ki iya ba ki kira ni,sannan ki tabbata kin ci abinci kin yi sallah kafin ki kwanta."
"To Baaba,ina za ka je?"
"Ina ɗakin karatuna."
Yana gama magana sai ya wuce ɗakin karatun sa da yake cikin gidan,wani littafi da yake rubuce-rubuce ya ɗakko ya zauna a saman kujera sannan ya jawo abun rubutu ya hau rubutu,ya jima sosai ya na rubutu ba tare da Lamyah ta kira sa ba,hakan ya tabbatar masa da ta kula da Mubarak kenan yanda ya dace,sai kawai ya hau nemo wasu takardu da passports da duk wani abu mai mahimmanci yana sakawa a cikin wata madaidaiciyar jaka. El-mustapha bai zauna ba sai da ya gama duk abinda zai yi a wannan ɗakin sannan ya ɗauki jakar ya buɗe wata ma'adanar sirri dake ɗakin ya ajiye jakar ya kulle. Ɗakin Aminee ya shiga,kamar yanda ya yi zato kuwa a can ya same su,Lamya na kwance tana kallon sama ta ɗora Mubarak a saman cikinta,fuskar ta ta jiƙe sharkaf da hawaye har sun fara bushewa,sumbatar goshinta ya yi kafin ya ɗauke yaron a hankali daga jikinta,ya kwantar da shi a gefen ta, addu'a ya yi musu sannan ya koma parlour ya ci gaba da ɗauke abubuwan da basu dace a ƙasa ba,sai a lokacin ya koma da tsintsiya da makwashin shara ya kwashe kofin da ya fasa yana zubar da ruwan hawaye.
Yanda El-mustapha ya ga rana haka ya ga dare,domin ya kasa rintsawa. A haka suka yi kwana bakwai suna jimamin rashin Aminee,dangin sa da suka ji labarin rasuwar wasu sun je yi masa ta'aziyya,sai dai babu matar wan shi ɗaya da ta je gaishe shi,balle ta ji ya yaran sa suke,har ma a taimaka musu,gashi yana tsananin tsoron ɗakko mai aiki mace da zata kular masa da yara,sai dai a wannan karon dole ne ya ɗakko mai aiki,ko don karatun Lamyah. Bayan kwana talatin da huɗu da rasuwar Aminee, El-mustapha ya zaunar da Lamyah ya ce.
"Habibty kina lissafi yau kwanaki talatin da huɗu kenan da rashin Ammin ki kuwa? Duk tsawon wannan lokacin baki je makaranta ba saboda Mubarak,dan haka na yanke shawara zaki koma makaranta sai na ɗakko mai kula da shi."
Tsalle Lamya ta yi ta dire ta ce sam ba za a kawo mai aiki gidan ba,tin da rayuwar mahaifiyarta ba a taɓa mai aiki ba bayan Iya da ta taimaka musu,dan haka a yanzu ma ba za a kawo mai aiki ba,cikin hawaye ta kalli mahaifin nata ta ce.
"Baaba baka yarda da yanda nake kula da Mubarak bane? Kana ganin ba zan iya ba na yi ƙanƙanta? Kar ka manta shekara ta sha biyar,babu abinda ba zan iya yi masa ba,da ace ɗana ne fa? Ammi ta ce a Nigeria ana yiwa yara kamar ni aure su haihu,shi yasa ta dage take koya min abubuwa,dan Allah Baaba kar ka raba ni da ƙanina."
Cikin kuka ta sake ƙanƙame yaron da ta yiwa wanka ya ke bacci cikin kwanciyar hankali,yanda take kuka ne ya taɓa zuciyar El-mustapha,dan haka sai ya hau aikin lallashinta,ya ce.
"To ya isa,zan bar maki ƙanin ki,sai dai kuma ki sani,dole ne za ki ci gaba da karatu a gida,dan ba zan bar ki ki zauna babu ilimi ba,kar ki manta da wanene mahaifinki,ina so ki yi ilimi mai yawa ta yanda za ki iya shiga kowacce ƙasa ki yi kasuwanci kamar yanda nake yi,ina so ki zama jaruma tsayayyiya wadda bata jingina da kowa ba,ina so ki cire kan ki daga cikin mata masu rauni,ke ba kasasshiya bace,ke ɗin jinina ce,kuma jinin Jaruma Aminatu."
Wani irin taurin zuciya da izza Lamyah ta ji na shigar ta,a ranta da gangar jikinta take jin za ta iya rayuwa koda a dokar daji ne ita ɗaya kuma ta yi rayuwa mai ƴanci da yalwa,kallon mahaifinta ta yi wanda ya sassauta murya ya ce.
"Lamyahn Baaba,ina so ki ɗaukar min alƙawari,duk rintsi,duk wahala ba zaki taɓa rabuwa da ƙanin ki ba,ki yi min alƙawari komai daren daɗewa zaki nemi Abiin ku Mus'ab ki yi rayuwa da su, Lamya...."
A gigice Lamyah ta kalle shi ta ce,
"Baaba wai me yasa ka ke so ka tarwatsa min ƙwaƙwalwa da waɗannan kalamai naka masu kama da bankwana? Kar ka sake ka bar ni umarni nake baka ba shawara ba,kar ka sake ka rabu da ni Baaba,ka kasance da ni da Mubarak har tsufan mu,ina so ka sa a ran ka muna nan tare da junan mu har abada babu mai raba mu,ina son ka Baaba."
Cikin kuka ta ƙarasa maganarta tare da faɗawa jikin El-mustapha ta fashe da kuka,shi kanshi hawaye yake ƙoƙarin mayarwa dan baya so ta ga rauninsa,sai dai duk ƙoƙarin da ya yi sai da guda ɗaya ya sauko mai tsananin zafi, cikin sauri ya ɗauke hannunsa da ya rungume su da shi ya share hawayen sannan ya ɗaga ta suna fuskantar juna ya ce.
"Ba zan taɓa rabuwa da ku ba Lamyah,ina nan tare da ku har abada,ina son ku,Allah Ya raya min ku Ya albarkace ku."
Murmushin ƙarfin hali ta sakar masa sannan ta sake komawa jikinsa ta kwanta riƙe da Mubarak a hannunta guda ɗaya.
Haka suka ci gaba da rayuwa cike da maraici da kaɗaici,tare da kewar Aminee,suna da kuɗi da duk wata rayuwar jin daɗi,amma sam ba sa jin daɗin su saboda zuƙatan su cike suke da baƙin ciki,a ganin su ma masu aiki a ƙarkashin su sun fi su more dukiyar da suke da ita. Mai koyarwa na musamman El-mustapha ya ɗakko yake yiwa Lamyah karatu a gida, cikin ikon Allah kuma tana gane komai daidai gwargwado. Mubrak na da shekara ɗaya a duniya El-mustapha ya sake sauyawa Lamyah mai koyarwa,wanda a wannan lokacin Lamyah na da shekaru sha shida a duniya daidai. Ta ƙara girma da kyau,fatar ta ta sake gogewa,ta ɗauki girma ta ɗorawa kanta dan hatta da fita da Mubarak wajen shaƙatawa da Baaban nasu ke yi ta karɓe ita ta ke yi,a duk sanda bata da karatu. A shekarar da take gab da kammala karatun ta matakin sakandire ne ta nemi da a samo mata mai koyar da Rawa,domin kuwa a kullum tana jin tsumin ta na taso mata,dannewa kawai take yi,ba tare da ɓata rai ko damuwa ba El-mustapha ya samo mata wata mata matashiya,dan ko auren fari bata yi ba,tsananin kyawun matar ne ya sanya Lamyah ƙin amincewa da matar ta koyar da ita rawa,sai ta dage ita bata son matar ta fiya faɗa,haka El-mustapha ya sauya mata ita ba dan ya yarda da uzirinta ba. Cikin sa'a ya samu wani mutumi da zai kai shekaru arba'in a duniya mai suna Idris. Idris irin ƴan daudun nan masu koyar da ado da kwalliya tare da rawa ne,Lamyah na ganin sa sai ta yi murna da farin cikin samun sa a matsayin malamin ta na koyon rawa.
A duk sanda ya zo haka zai ta bin mazan dake aiki a gidan suna hira,cike da kwarkwasa da karairaya,su kuwa dariya yake basu saboda yanda yake abu kamar mace,a haka Idris ya saba da kowa na gidan,abu kamar wasa tun Idris na koyar da Lamya rawa kawai,sai gashi ya koma koya mata yanda ake kwalliya,da girki da duk wani abu na mata. Sosai El-mustapha ya sake masa yake shiga ko ina na gidan,Lamyah kuwa ta saki jiki da shi sosai har tana iya bari ya ɗauki Mubarak ya yi masa wasa. Wata iriyar shaƙuwa ce ta shiga tsakanin su sosai,a haka suka kai shekaru biyu da haɗuwa da Idris,lokacin da Idris ya samu labarin Lamyah zata cika shekaru sha takwas a duniya,a wannan ranar ne Idris ya yi nufin su yi wata ƙwarya-ƙwaryar walima a gidan dan taya Lamyah murnar zagayowar ranar haihuwarta, shirye-shirye suka fara yi tin ana sauran kwana biyu birthday party ɗin,da kansa ya yi snacks ya haɗa cake,banda washe baki da rangwaɗa babu abinda Idris yake yi. Lamya da El-mustapha kuwa sai farin ciki suke yi,dan kuwa ba a taɓa yin irin wannan bidi'ar ba a gidan.
Washegari da safe ta kama ranar shagalin zagayowar haihuwar Lamyah......
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 17:
Mus'ab bai tashi sanin rasuwar El-mustapha ba sai da ya rasu da kwana biyu, yana zaune a ofishinsa dake Zinder ya kira layinsa ya ji shiru baya shiga,sai kawai ya yanke shawarar kiran wani amintacce kuma ma'aikacin El-mustapha dake ƙasar Dubai,anan ne yake sanar da shi duk abinda ya faru da El-mustapha. Nan take Mus'ab da ya miƙe tsaye saboda tashin hankali ya yanke jiki ya faɗi ba tare da kowa ya san da hakan ba,sai da lokacin tashi daga aiki ya yi ma'aikatansa suka ji shiru bai fito ba, Aminullahi wanda ya biyo mahaifin nasa dan ganin yanda suke gudanar da kasuwancin su na Nijer ne ya leƙa dan ya ga ko lafiya mahaifin nasa ya jima bai fito ba? Yana leƙawa sai ya gan shi kwance a ƙasa kamar matacce,cike da tashin hankali ya nufe shi yana kiran sunan sa,ganin baya ko da motsi ne ya sanya shi fita da gudu waje ya sanar da sauran abokan aikin mahaifin nasa,rige-rigen shiga office ɗin suka hau yi,mutum ɗaya aka samu ya yi hikimar ɗaukan ruwan roba daga fridge ya kwara masa a fuska,nan take Mus'ab ya sauke numfashi mai nauyi,idanunsa da suka yi masa nauyi ya buɗe da ƙyar yana bin mutanen wajen da kallo,akan Aminullahi ya tsayar da kallonsa,nan take wata ƙwalla mai zafi da ƙona maganai ta taru a idanunsa,cikin muryar da ke cike da tashin hankali da damuwa ya ce.
"Aminullahi na rasa Ɗan'uwana,shi kenan sun kashe Baaban ku, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un."
Sakin baki Aminullahi ya yi yana kallon mahaifin nasa da ke kwaranyar da hawaye bayan ya miƙe tsaye,hannun Aminullahi Mus'ab ya kamo ya ce.
"Yanzu na kira waya dan na ji me yake faruwa bana samun sa,gashi birthday ɗin Lamya ya gabata ban taya ta murna ba,sai kawai nake samun mummunan labarin rasuwar Baaban ka,mu yi haƙuri, Allah'n da ya bamu shi ya fi mu son sa,shi yasa ya karɓe shi,Allah Ya jiƙan Ɗan'uwana,Allah Ya yi masa afuwa."
Nan take idanun Aminullahi suka kaɗa suka yi wani irin jan da Mus'ab bai taɓa gani ba a rayuwar sa,ga wata ajiyar zuciya mai ƙarfi da ɗan nasa ke saukewa,ya tabbata da shi aka bawa labarin yanda mutuwar ta kasance,to fa tabbas da sai ya fi haka shiga tashin hankali,dan haka cike da dabara ya dinga lallashin Aminullahi har suka tafi gida,Aminullahi bai tashi yin kuka ba sai da ya yi ido huɗu da mahaifiyarsa, wani irin kuka ya saki mai cin rai,ya jima yana yinsa kafin ya tashi ya wuce ɗakin sa, A'isha da ta ji labarin rasuwar El-mustapha a bakin Mus'ab itama kuka ta ke yi,gaba ɗaya gida sai ya rikice da baƙin ciki,girkin da ta sa akai wa Mus'ab da Aminullahi kuwa masu aiki ta kira ta ce su kwashe su je su ci kar ya lalace,wanda za a iya sakawa a fridge kuma a saka.
Sanda labari ya riski Iya gigicewa ta yi ta na kuka da nemawa su Aminee Rahamar Allah,fatan ta shine Mus'ab ya je ya ɗakko musu Lamyah da kanin ta,cike da damuwa Mus'ab ya ce.
"Na tambayi Hadimin gidan nasa ya ce min ba a gan su ba,an neme su an rasa,hatta da hukumar ƙasar sai da ta shiga case ɗin amma har yanzu ba a gano waɗanda suka aikata hakan ba,dan kuwa ƴan'uwasa da nake zargi da aikata wannan mummunan aikin sun shiga sun fita ana ta neman wanda ya aikata laifin da su."
Kuka Iya ta fashe da shi, cike da tausayin yaran ta ce.
"Allah Ya tsinewa duk mai hannu a wannan lamari,Allah Ya bayyana mana yaran nan kar su tagayyara."
"Amin Ya Allah Iya,ki dena kukan haka ya isa,kin ga ba isasshiyar lafiya gare ki ba kwana biyu."
"Dole ne na koka Alhaji,ni kaɗai na san irin karamcin da mutanen nan suka yi min,Alhaji El-mustapha ne ya yi wa jikata kayan ɗaki har ma da jarin da za ta juya saboda kar ta zauna haka,banda kula da magunguna na da ci na da sha na,ya ɗauke ni kamar mahaifiyarsa,bai taɓa gaishe ni a tsaye ƙiƙam ba duk arziƙin sa,ka ga kuwa dole na koka Alhaji."
A'isha ce ta fyace majina a tissue,sannan ta ce.
"Yau sai rasuwar Aminee ta dawo min sabuwa a cikin raina."
Kuka ta sake fashewa da shi mai tsanani,haka suka kwana suna jimanta lamarin. Babbar damuwar Mus'ab shine inda zai ga su Lamyah,dan haka a daren ya siyi tikitin tafiya Dubai ta online,yana so ya je ya duba yaran da kansa.
Lokacin da ya sanar da A'isha abinda ya aikata kuka ta dinga yi tana birgima tare da rantsuwar babu inda za shi,tinda har El-mustapha ya gargaɗe shi akan kar ya bari ƴan'uwansa su san shi,to fa babu inda zai je,cikin kuka ta ce.
"Mutanen da suka kashe jininsu da hannun su kana tinanin za su ƙyale ka ne? Na tabbata yanzu neman ka suke yi ido rufe ko dan su ƙwace duk wata dukiyar ɗan'uwansu dake hannun ka,wadda sun san cewa basu da gadonta ta su Lamyah ce,ina laifin ka je Nigeria tinda ka taɓa bani labari ya ce zai maida yaran dangin mahaifiyarsu."
Shiru Mus'ab ya yi yana nazarin maganar A'isha,duk da haka zuciyarsa ta fi amince masa akan ya je Dubai wataƙila yaran na can,cikin murya mai cike da rauni Mus'ab ya ce.
"Na riga da na siyi tikitin tafiya,haƙuri kawai za ki yi,dan ba zan yi asarar kuɗina ba."
"Zan iya biyan ka kuɗin da za ka yi asara akan na rasa ka gaba ɗaya,idan kuma ka dage sai ka je Dubai ka sa a ran ka kafin ka dawo na kashe kai na !"
A'isha na gama faɗar haka ta fita daga ɗakin tana kuka,kai tsaye ɗakin Aminullahi ta nufa tana bugawa ta na kuka kamar ƙaramar yarinyar dake jiran a lallasheta,ba tare da ta jira ya buɗe mata ƙofa ba ta hau zayyane masa abinda ke faruwa,cike da damuwa Aminullah ya buɗe mata ƙofar,rungumeta ya yi a ƙirjin sa ya na lallashinta,cike da damuwa ta ce.
"Ka sanar da mahaifin ka,da a zo a sanar da ni gawar sa gwanda ni ya binne ni,idan ya dawo da ran nasa kenan."
Da ƙyar Mus'ab ya janye tafiyar da ya ƙwallafawa rai,tare da yanke shawarar neman su Lamyah a Nigeria kamar yanda El-mustapha ya sanar da shi zai tura su can. Aminullahi na jin haka ya ce shi ma ba za a barsa a baya ba,tare za su je neman su Lamyah tinda dama shi ya fi zama a can yana kula da kasuwancin su na can. Tsananin danasanin ƙin ci gaba da sada zumunci da yarinyar ne ya fi tada masa da hankali,da ya san haka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 30