ba yarinya. Ai tin ranar da kika yi min wulaƙanci a gaban mijinki na shiga bincike akan ki,anan na gano haka halayyar ki take wato wulaƙanta ɗan Adam,tin daga lokacin na yi alƙawarin ba zaki ƙara moruwa ba,sai dai ganin halin da kike ciki ne ya sa na tausaya miki,amma lokaci ya ƙure babu abinda zan iya yi miki,sai dai na ce a guji gaba."
Kuka Hajiya ta saka ta zube a wajen ta na fitar da numfashi da ƙyar,hannunta manuni ta hau nunawa ta na son yin magana amma inaa bakinta ya kasa furta komai,ganin halin da Hajiya ta shiga ne ya sanya Nurse ɗin kare fuskarta ta fita daga ɗakin ta bar asibitin a gaggauce. Layuzah kuka Hajiya kuka. Lamyah ce kawai ke da jarumtar kiran wayar Momma ta sanar da ita duk abinda ya faru,cikin ƙankannin lokaci aka bawa Hajiya taimakon gaggawa kafin su Momma da Abii su iso asibitin,babu ɓata lokaci ya sa aka kai shi ofishin HOD ɗin asibitin,su na zuwa Lamyah ta sake sanar da shi duk abinda ya faru,Abii kuwa ya ɗora da faɗa tare da barazanar zai sa a rufe asibitin gaba ɗaya idan ba su ɗauki mataki ba. Ajiyar zuciya HOD ya sauke kafin ya ce.
"Alhaji babu abinda zan iya cewa da kai sai dai na baka haƙuri akan abinda ya faru,sannan zan taimaka maka na kai ku wajen wani mai magani,da yardar Allah ƴar ka za ta samu lafiya. Mu kammu mun rasa wace macece ke zuwar mana asibitin nan ta na yi mana irin wannan mugayen abubuwan,wannan shine karo na huɗu ana samun irin wannan case ɗin,duk yanda muka so gano wadda ke aikata irin laifin nan mun kasa,amma da yardar Allah idan kere na yawo zabo na yawo,watarana za su haɗu ne."
"To Allah ya kyauta,idan babu damuwa ina so ka sanar dani inda zan samu me maganin da kake magana akai,sannan ina fatan ba boka bane ko?"
Murmushi HOD ya yi sannan ya ce.
"Ah ah ba boka bane Alhaji,baka da matsala malami ne na addinin musulunci mai aiki da ƙur'ani da sunnah. Allah ya bata lafiya."
Sai da ya yi wa Abii kwatance tare da bashi lambar wayar malamin sannan suka yi sallama,ya na tunanin irin matakin da za su ɗauka akam Nurse Jamila da ke yi musu wannan mugun abun,ta na jawowa asibitin su ɓacin suna. Ya yi alƙawari daga wannan karon ba za ta sake yin makamancin abinda ta aikata wa Layuzah ba.
Daga asibiti su Abii wajen mai magani suka zarce,suna zuwa suka tarar da wajen an kunna karatun ruƙya sai tashi yake yi,ga magunguna nan a kwalaye,wajen kamar islamic center haka yake. Abii ne ya yi wa Shaikh ɗin bayanin duk abinda ke faruwa,babu ɓata lokaci ya buƙaci ganin Layuzah,wani ɗakin da yake ganawa da marasa lafiya aka shigar da ita,Abii da Lamyah da Momma tare da Hajiya ne suka shiga suka zauna,suna kallo Shaikh ya hau yi mata addu'o'i a ciwon,sannan ya saka audiga da magunguna ya matse ciwon ya zuba mata magunguna dangin su Habbatussauda zuma da ruwan zamzam ɗin da ya sha ruƙya. Ɗaure wajen ya yi sannan ya basu magungunan da za ta dinga sha,da addu'o'in da za a dinga yi mata,sai da Abii ya sallame shi sannan suka yi masa godiya tare da sallama suka wuce gida.
A wannan ranar Layuzah ta sha bacci sosai,Hajiya bata koma gida ba a nan ta kwana,Zahrah da Lamyah ne suka dinga jinyar su a tare. Washegari da safe Hajiya ta ji sauƙin jikinta,hankalinta ya dawo jikinta,wata iriyar nadama da danasanin irin mummunar tarbiyyar da ta bawa Layuzah ne suka mamaye ta,hawaye ta dinga sharewa ta na kallon Layuzah kwance ta na bacci. Wanda rabon da ta samu bacci mai daɗi irin haka tun kafin ƙurjin jikinta ya fara ɗurar ruwa me wari.
Haka Lamyah ta dinga kula da Layuzah har ta fara iya yin komai da kanta,ciwon na ta yin saɓa ya na warkewa,sannan ya dena tara rayuwan da yake yi,sai mugun ƙaiƙayi da yake yi mata. Idan ta fara sosawa har wani yawu ke taruwa a bakinta tsinkakke dan daɗi,ta na gamawa zai fara zogi,da ƙyar Lamyah ta hana ta sosawa,bayan ta tsorata ta da cewa idan bata dena ba ciwon zai dawo har ma ya fi na da. Lokacin da maganin ya ƙare Lamyah da kanta ta ɗauke ta suka koma wajen Shaikh ya ƙara musu wasu har da wanda za ta dinga yin hayaƙi da shi,godiya sosai suka yi masa sannan suka koma gida. Cikin sati biyu Layuzah ta warke kamar bata taba yin wani ciwo ba,sai wani mugun tabo baƙi a tsakiyar cikin nata, har kunyar buɗe cikin take yi saboda yanda ya yi mata muni.
Tinda ta buɗe ido ta ga ta samu lafiya sai ta maida hankali sosai wajen gyara alaƙarta da Allah,sannan ta sauke kanta ƙasa sosai suna zaune lafiya da Lamyah,duk abinda Lamyah ta ce za a yi a cikin gidan to fa shi za a yi,ko da sun samu saɓanin ra'ayi akan abu,to Layuzah ta na ɗauke tata buƙatar ta fifita ta Lamyah,wani irin girma take bawa Lamyah kamar ta kwanta mata. Ita kuma Lamyah har kunya take ji idan ta ga Layuzah na bata girma sosai. Haka rayuwarsu ta ke gudana har satin da Aminullahi ya ce musu zai dawo ya zagayo,da dare suna zaune suna kallo suna cin chips da kifi da Lamyah ta gasa musu Aminullahi ya kira wayar Lamyah, ƙin ɗauka ta yi saboda kunyar Layuzah da take ji. Murmushi Layuzah ta yi ta amsa mata kiran ta kara mata a kunnenta sannan ta ɗauki nata kifin ta wuce ɗaki tana dariya kamar babu komai a ranta. Ta na shiga ɗaki ta rufe ƙofar ta durƙushe a wajen ta na kuka. Cikin kuka ta ce.
"Soyayyarka ce ta jefa ni halin da na shiga a baya Yah Amin,ban san cewa duk yanda mutum zai so ɗan'uwansa mutum a duniya ba zai taɓa kaiwa ya Allahn da ya haliccesa ba,tabbas na tafka babban kuskure da na jefa kaina a shirka saboda so,amma na yi alƙawari tsakani na da Allah zan zamo mace ta gari,zan yi koyi da halayen Lamyah ko ma na fi ta. Ba zan damu da dena kula ni da ka yi ba,ko zan rasa raina zan gyara alaƙata da Allah da kuma mutanen da nake tare da su."
Kuka ta ci gaba da yi,kafin daga ƙarshe ta miƙe tsaye ta ajiye plate ɗin a gefen gado ta haye gadon ta rufe idanuwanta ta na tinanin rayuwarta ta baya. Lallai ta yarda wannan mannewa maza da take yi a baya har da shaye-shayen kayan mata barkatai da take yi,da kuma kalle-kallen finanan batsa da karanta littattafan batsa da take yi,yanzu da ta jingine komai ta fuskanci rayuwa bata jin muguwar sha'awar da takan samu kanta a ciki a koda yaushe.
Lamyah kuwa bayan sun gama waya da Aminullahi ta roƙe sa da ya kirawo Layuzah su gaisa,ya ce mata to kawai ya kashe wayarsa. Gaba ɗaya nadamar auren Layuzah yake yi,tare da danasani,cike da ɓacin rai ya ce.
"Wai ni me nake tunani ne ma har na auri wannan yarinyar? Ina hankali na yake a lokacin da na amince da auren ta?"
Cike da damuwa ya ci gaba da haɗa kayan sa. Washegari da sassafe jirginsu ya taso daga Nigeria zuwa Niger.
Tin da asuba Lamyah da Layuzah ke shirin tarbon mijin nasu,daga can gidan Momma ma ta sa an yi masa snacks masu daɗi ta aiko Zahrah da shi,anan ne Layuzah ta samu damar neman afuwar Zahrah,ita kuma ta yafe mata sannan ta taya su ƙarasa aikin gidan suka wuce wanka. Kwalliya suka yi ta fitina kamar mutum ya sace su ya gudu,sai dai suna fitowa Layuzah ta ji ta yi mugun raina kanta a gaban Lamyah,saboda yanda ta ga tsantsar kyau da yalwar gashin da Lamyah ke da shi. Ga wani sihirtaccen ƙamshi na tashi a jikinta,wani yawu ta haɗiya ta na karanto a'uziyya a cikin ranta,domin kuwa wani irin kishi ta ji yana taso mata yana neman rufe mata zuciya. A hankali ta fara samun salamar ruhi har suka zauna suna ƙarasa jera abinda Zahrah bata jera ba a saman dinning.
Suna kammalawa suka koma tsakiyar parlour suka zauna,Lamyah ce ta ɗakko turaren wutar da Iya ta aiko mata na musamman ta zuba a abun ƙona tiraren wuta ta jona,nan da nan ƙamshi ya fara karaɗe gidan,ɗakinta ta shiga ta zuba turaren wutan sannan ta tsaya akai ya na ratsa jikinta. Ta nan tsaye ta ji ƙarar buɗe gate,wani irin tsallan murna zuciyarta ke yi,ji take yi kamar ta kwasa da gudu ta isa wajen Yah Amee ɗin nata,sai dai kuma ba za ta so ta ƙuntata wa Layuzah ba,dan haka sai ta yanke shawarar jira har ya iso wajenta da kansa.
Layuzah kuwa zama ta yi a parlour ta na washe baki tare da fatan Allah Ya sa Yah Amin kar ya wulaƙanta ta,za ta zube har ƙasa ta nemi gafararsa akan duk abinda ta yi masa,fatan ta ko da ba zai so ta kamar yanda yake son Lamyah ba su zauna lafiya.
Ya na shiga gidan ya shaƙi ƙamshin da Lamyah ta fara sabar masa da shi,lumshe idanunsa ya yi sannan ya saki murmushi ya na faɗin.
"Assalamu alaikum."
Cike da yanga da rangwaɗa Layuzah ta ce.
"Wa'alaikumussalam amintaccen Allah,barka da dawowa."
Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce.
"Na same ku lafiya?"
Wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyar Layuzah,cikin ƙwarin guiwa ta isa gabansa ta karɓi jakar hannunsa da akwatin da yake ja ta ce.
"Lafiya kalou alhamdu Lillah."
"Na ga alama ai tinda ga ki tsaye ƙyam kamar ba ke ce kika yi ta fama da ciwo ba,to Allah ya kiyaye gaba ya sa kuma kin koyi darasi a jinyar da kika yi."
Kanta ta saukar ƙasa cike da jin kunyarsa ta ce.
"Amin Ya Allah. Don Allah ka yafe min duk abubuwan da na yi maka,wanda ka sani da wanda baka sani ba,In Sha Allahu ba zan sake ba."
"Ki gode wa Lamyah da a kullum take tausa ta tare da bani haƙuri akan abubuwan da kika yi,tabbas da yanzu haka kina can gidan ku,domin ban zaci zan iya yafe miki laifukan ki ba,sai dai na duba na ga muma ƴan adam muna yi wa Allah manyan laifuka kuma mu nemi yafiyarsa ya yafe mana,to ni me zai hana na yafe miki? Wataƙila Allah ma ya yafe miki laifin da kika yi masa,ni to a su wa da ba zan yafe miki ba?"
Hawaye ta share sannan ta durƙusa har ƙasa ta ce.
"Na gode Baby Allah Ya saka da alkhairi,Allah Ya bani ikon kiyaye duk abinda zai ɓata muku rai."
Murmushi ya sakar mata sannan ya ce.
"Amma dai wannan ɗinkin sabo ne ko?"
Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi sannan ta wuce ɗakinsa ta ajiye masa kayansa ta fito, ɗakinta ta wuce kai tsaye ta na jin daɗin yanda komai ya zo mata da sauƙi ba yanda ta zata ba,ita da kanta ta san A'isha Lamyah ta gama yi mata komai a rayuwa,bata kuma da abinda za ta biya ta da shi da ya wuce ta dinga yi wa iyayenta addu'a sannan ta zauna da ita lafiya.
Aminullahi na ɗakinsa ya na baza ido ya ga ta inda Lamyah za ta fito,ita kuwa tinda ta ji shigarsa gidan ta sake lafewa a ɗakin,jin shiru bai shiga ɗakinta bane ya sanya ta fitowa,sai ta ji yana cewa Layuzah.
'Amma dai wannan ɗinkin sabo ne ko?'
Wani irin kishi ta ji ya daki zuciyarta,sai ta koma baya a hankali ta shige ɗakinta,a ranta take ayyana.
'Ohh namiji ɗan babansa,kullum fa sai ta lallashe shi akan ya daidaita da Layuzah ya dena wulaƙanta ta,amma wai shine daga dawowarsa har da yabon ɗinkinta,wa ma ya sani sai da suka gama cin soyayyar su na fito. '
Ajiyar zuciya ta sauke ta na jin jikinta ya mutu murus, hawaye ne masu ɗumi suka hau gangarowa a idanunta,bata share su ba sai ta basu damar zubowa. Ta sani tana da kyawawan halayen zama da mutane lafiya,amma ta na da zafin kishi sosai,duk abinda take yi daurewa take yi,ta na tina lahirar ta ita ce gaba da komai,ba domin haka ba wani abun ma ba za ta iya aikata shi ba. A kullum idan Abii da Momma da Iya suna sanya mata albarka,sai ta ga ai yin kyakkyawan hali ya biya ta,tinda kullum albarka ake sanya mata. Ga kuma uwa uba albarkar mijinta da soyayyar da yake nuna mata. Hannunsa ta ji a saman fuskarta ya dangwalo hawayen idanunta ya kai bakinsa ya na ɗanɗanawa,kallonta ya yi ya ce.
"Hawaye kuma ? Taso ki sanar dani abinda zai sanya ki zubar min da precious hawayen ki."
Ɗaukan ta ya yi cak ya ɗora a saman cinyarsa ya na shafata tare da sunsunarta,narkewa ta sake yi a jikinsa ta fashe da kukan shagwaɓa. Babu ɓata lokaci Aminullahi ya hargitsa kwalliyar da bai gama ganin kalarta ba.
Sai da komai ya wanaka a tsakanin ma'auratan suna manne da junansu Aminullahi ya ce.
"To yanzu sai ki sanar da ni abinda ya sanya min ke kuka ko? Dan gaskiya ba zan yarda da kalmar babu komai ba,dole akwai dalilin zubar hawayen ki."
Sumbatar ƙirjinsa ta yi wanda kanta ke kwance akai,kafin ta ce.
"Soyayyar ka ce ta sanya ni zubar hawaye,Yah Amee ina son ka fiye da yanda nake son kai na,ina tinanin yanda rayuwa za ta kasance min ne idan babu kai a cikinta,na hanga na hango na gama gane ni da kai ruhinmu ɗaya ne jiki kowa da nasa. Don Allah kar ka guje ni,kar ka yi nisa da ni nisan da zan yi kukan rashinka a gareni."
Kuka ne ya ci ƙarfin ta wanda ya sanya ta yin shirun dole,wani irin taratsatsin son Lamyah ne ke ƙona zuciyar Aminullahi,rungumeta ya yi tsam a ƙirjinsa kamar zai tsaga ta shige ciki ya ɗinke,a hankali ya furta.
"Lamyah da ace akwai inda ake zuwa a yi wa mutum aiki a sanya gangar jikin wani a cikin ta wani,to tabbas da na sanya ki a jikina domin mu dawwama manne da junan mu,kin ga ta haka ne kawai za ki dena jin tsoron watarana zan rabu da ke. Ina so ki sanya a ranki,a duk sanda na rabu dake,to bana duniyar nan. Ina son ki Lamyah,ina son ki soyayyar da baki ba zai taɓa bayyana irinta ba."
Nan da nan Lamyah ta sake birkita wa Yah Amee ɗin ta lissafi,ta susuta shi da salon soyayyarta,Aminullahi kuwa ji yake yi duk duniya babu wanda ya kai shi sa'a da dacen aure. Haka suka lalace suna musayar soyayya a tsakanin su har magariba. A tare suka yi wanka Aminullahi ya wuce masallaci,Lamyah kuma ta saka wasu fitinannun ƙananan kaya ta ɗora ƙaton hijabi akai,sallah ta gabatar kafin ta je parlour. Wayam ta samu parlourn babu kowa sai TV da ke aiki, zama ta yi ta na kallon Sunnah TV har Aminullahi ya dawo,ya na shigowa ya ce.
"Taimaka min da abici gaba ɗaya kin yasashe ɗan abincin da na ci a jirgi."
Tura baki ta yi tana yi masa shagwaɓa ta ce.
"Lallai ma Yah Amee ɗin nan,haka ma za ka ce? Da ka samu na taimaka maka?"
Dariya suka kwashe da ita,nan da nan Aminullahi ya tina ranar su ta farko,wani irin shauƙin son Lamyah ne ya ɗebe shi har ya kai shi ga rungume ta ya na sumbata a tsakiyar parlourn,Layuzah da ta fito cin abincin dare ce ta gansu a haka,cikin sauri ta juya za ta bar parlourn,da sauri Lamyah ta ƙwace jikinta ta ce.
"Bismillah zo mu ci abinci dama ke muke jira."
Cike da yaƙe Layuzah ta dawo,kanta a ƙasa ta hau kujera a saman dinning ta fara ɗiban abinci. Nesa da kujerar da Aminullahi ya zauna Lamyah ta zauna bayan ta zuba masa abinci,cikin ranta ta ƙudiri aniyar kiyaye yin duk wani abu da zai motsa kishin Layuzah saboda a zauna lafiya,tinda itama idan aka yi mata irin abinda suka yi ɗazu ba za ta ji daɗi ba.
Su na kammala cin abinci Aminullahi ya shiga ɗakinsa ya ɗakko musu tsarabar su,sannan ya bawa Lamyah saƙon Afrah,godiya suka dinga yi masa suka zauna a parlour suna kallo suna hira,a wannan rana ne Aminullahi ya raba musu kwana,zai dinga yi wa kowaccen su kwana bibbiyu,sannan kuma be yarda da bin ɗaki ɗaki ba,duk me girki ita ce za ta je ɗakinsa ta same shi,ya ƙarasa maganarsa ya na kallon Lamyah,sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta na murmushi. Sai da Layuzah ta fara jin idanunta na rufewa saboda bacci sannan ta ɗauki tsarabarta ta yi musu sallama ta koma ɗakinta.
Bayan watanni biyar da daidaituwar lamuran gidan Aminullahi suka haɗu suka je duba Hajiyan Layuzah da jiki. Aminullahi ya kawo mata atampopi da shadda wanda za ta dinga siyarwa ta na samun taro da sisi,tinda dama ita mace ce me neman na kai sosai bata zaman banza,ga kuma sana'arta ta alkaki da dubulan bata dena ba,sai dai ta samu wasu dattijai biyu suna taya ta suya,saboda hawan jinin da take fama da shi ba a so tana zama a bakin wuta.
Mubarak ya fara zuwa makaranta,direba na musamman Abii ya samar masa yake kai shi yana dawowa da shi,wani irin gata Momma ke nuna masa wanda ya sanya Iya jan hankalinta domin ta dinga kula kar ya sanya shi fanɗarewa,bata kuwa ɓata lokaci ba wajen ɗaukan gyaran da Iya ta yi mata,dan ta san ita ɗin babbar masoyiyarsu ce,ba za ta bata shawara mara kyau ba. Nunawa yaro mungun so har ka kasa hana shi yin abinda be dace ba,ba soyayya bace.
Lokacin da Afrah ta sanar da Lamyah cewar ta kusan haihuwa kuwa rigima ta sanya wa Yah Amee ɗin nata akan sai ya kai ta Nigeria,ƙin amincewa ya yi ya ce ba za ta je ta jijjiga masa nasa babyn ba,akan haihuwar wata. Ta na kuka ta shiga mota bayan ya fita ta kai ƙararsa wajen Abii. Abii kuwa sai ya kama haɓa ya ce.
"Wai wai waiii lallai dole a hukunta Yah Amee,ina shi ina hana ki zuwa Nigeria wajen Afrahn ki?"
Cike da sangarta ta ce.
"Kuma fa wai Araf Yah Amee ke kira da wata kamar be san matsayinta a waje na ba."
Momma ma dariya ta gimtse kamar yanda ta ga Abii yana ta yi,sannan ta ce.
"Rabu da shi ki fara shiri abunki,ai kamar kin je Nigeria ne kin gama."
"Kwarai da gaske,tafiya ta zama dole,kin ga daga nan ma sai mu sake leƙa dangin Ammiin ku,domin shi zumunci na Allah ne,Allah da manzon sa ne suka wajabta shi,kuma wanda ya yanke shi ya yanke hanyar shigarsa aljannah,dan haka nima zan shirya da ni za a je Nigeria."
Momma ce ta ce.
"To nima dai kifin rijiya bana ina so a je dani,ina so na je na ga wannan Nigeriar da mutanen cikinta."
Nan fa hira ta ɓarke tsakanin Momma da Lamyah,Lamyah na bawa Momma labarin Nigeria ita kuma ta na jin kwaɗayin zuwa na ƙara kama ta . A haka Aminullahi ya zo gidan Abii ya sa shi a gaba har sai da ya amince za su je Nigeria gaba ɗayan su......
Mutanen Nija a shirya karɓar baƙi. A yi min afuwa akan ji na shiru da ba a yi ba. Masu tambaya kuma daga farko don Allah ku yi min adalci mana,mun kusan fa gamawa,ina kuke lokacin da na fara posting daga farko? Sai yanzu ana gaf da gamawa ku ce a baku daga farko? Sannan amfanin attaching da link ɗin channel kenan,ku shiga ku karanta a can. Idan baku samu ba ku bi link ɗin wattpad da nake sharing shima. Na gode.
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 45. LAST PAGE.
Duk yanda Afrah ta so ta hana Mama Tani zuwa taya ta aiki,bata samu haɗin kanta ba. Domin kuwa Baba Musa na fita kasuwa Mama Tani ta ƙarasa ayyukanta ta kulle gidan ta wuce gidansu Afran,ta na zuwa ta tarar da Afrah ta ci ƙarfin aikin sosai,banda nishi babu abinda take yi. Murmushi suka yi wa junan su,Afrah ta jingina a jikin gini riƙe da mopper ta ce.
"Barka da safiya Hajiyan Baba,irin wannan kyau haka? Amma dai ba aiki kika zo taya ni ba ko?"
Kaɗa kai kawai Mama Tani ta yi tana dariya ta ce.
"Ke kam dai babu abinda zan ce akan ki sai fatan shiriya. Yanzu ke kika yi dika ayyukan nan?"
Gyaɗa kai Afrah ta yi sannan ta ce.
"Ƙwarai da gaske ni na yi komai,sai ɗan abinda ba a rasa ba ne dai Bala ya taya ni."
"Lallai kin yi ƙoƙari sosai gaskiya,bari mu ƙarasa mu shiga kitchen kuma a ga me za a rage."
"Tin yanzu Mama Tani? Lamyah ta ce min fa sai nan da kwanaki biyu za su zo in ji uban ƴan iyayi."
"Ke wato ba zaki dena yi wa Alhaji Aminu tsiya ba ko? Bari ya zo ya tsare ki da idanuwan nasa da kike tsoro,zaki maimaita abinda kika faɗa yanzu a gabansa."
Zama Afrah ta yi ta na dariya ta ce.
"Kuma kin san me Mama Tani? Ba ƙaramin tsoron idan bawan Allah'n nan nake ba fa,kawai dai ƙarfin hali nake yi nake aika masa da tawa hararar domin fa kin san maza idan kana ƙyale su suna taka ka,sai su raina ka."
"Humm Afrah kenan,kin ga tashi mu yi mu kammala gyaran gidan mu yi abinda ya sawwaƙa na snacks,idan ya so sai a saka a fridge ranar da za su iso sai a soya, ko ya kika gani?"
"Hakan ma shawara ce me kyau."
Babu ɓata lokaci suka hau ƙarasa gyara gidan. Da misalin sha biyu na rana suka kammala komai,suka kulle ɗakunan da baƙin nasu za su sauka a ciki. Kitchen suka shiga Afrah ta taya Mama Tani haɗa duk kalar snacks ɗin gargajiya da na baturen da ta iya,suna kammalawa suka soya na soya wa a lokacin,wanda za su iya ajiyewa har ranar da su Lamyah za su zo kuma suka ajiye. Bayan Afrah ta dawo daga yin sallar azahar Mama Tani ta tafi ta gabatar da tata,sai suka dafa abincin rana har zuwa dare. A manyan kuloli Afrah ta zuba wa Mama Tani wanda za ta tafi da shi gidan,sannan ta zuba musu suka ci suka ƙoshi. Bala na dawowa Mama Tani ta ɗauki komatsanta ta wuce gida,domin kuwa ta san nata mijin na hanya shima ko kuma ya dawo ma. Ile kuwa ta na zuwa gida sai ta tarar da ya dawo har ya shiga wanka. Plate da cup ta ɗakko ta zuba masa abinci da abun shan da suka dafa ita da Afrah,sannan ta zauna ta na jiransa ya fito ya ci. Baba Musa be fito ba sai da ya shirya tsaf sannan ya isa parlourn,gaishe shi Mama Tani ta yi tare da yi masa sannu da dawowa,bayan ya amsa ta ne ya fara cin abincinsa yana santi,sai da ya kusan cinyewa ne sannan ya tsaya fuskarsa a haɗe da alamun damuwa ya ce.
"Tani ina so na yi miki wata magana,sai dai ina tinani akai,dan ban san ya zaki ɗauki lamarin ba."
Cikin murmushi Mama Tani ta ce.
"Na kula dama akwai magana a bakin nan naka Malam,sai dai bana so na katse maka jin daɗin abincin da na kula ya yi maka daɗi sosai. Kar ka damu za ka iya sanar dani duk abinda ke cikin ranka,In Sha Allahu zan yi masa Kyakkyawar Fahimta(Labarin Jiddah da Muiɗo Ɗan ta'adda 500 ne kacal,mai so ta yi min magana 09031416423 har da wasu zafafan labarai masu ƙayatarwa akan farashi mai sauƙi)"
Gyara zama sosai Baba Musa ya yi suna fuskantar juna da matar tasa da ya ke jin ƙaunarta sama da kowacce mace a duniya,cikin sanyin murya ya ce.
"Bana so ki samu labarin an ganni ko ana gani na da Kulu a wani wajen,ki yi zargin wani abu ne a tsakani na da ita. Babu wata alaƙa a tsakanin mu da ta wuce ta yaro ɗaya da Allah ya bamu,wanda kuwa yaron nan ba na goye bane ballantana na ce za ta karɓe sa ta shayar. Matsalar da aka samu Kulu ta sake kashe auren ta da zummar na mayar da ita ɗakinta,ni kuma na ce mata bata da wani ɗaki da ya rage mata a gida na,to shine har yanzu bata haƙura ba take ta bi na duk inda ta san za ta same ni,ta yi roƙon Bala ya sa baki har ta gaji,ya nuna mata har abada baya buƙatar ta a rayuwarsa,iyakarsa ya kyautata mata a matsayinta na uwa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 30