Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita da Hajiyanta suka kulle gidan suka nufi gidan boka dan sabunta aikin da aka yi wa Aminullahin...... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 27. Duk wata buƙatar da ke ran Layuzah ta zauna ta zayyane wa bokan cike da amincewa tare da sakankancewa babu mai iya biya mata waɗannan buƙatu face shi. Magunguna da sharuɗan yanda za ta yi amfani da maganin ya bata,tare da gargaɗi akan abubuwan da idan ta aikata zai yi tasiri har asirin ya karye,godiya suka yi masa sosai sannan suka ajiye masa maƙudan kuɗaɗen da ya buƙata a wajen su. Sun koma gida ana kiran sallar magariba,dan haka shirin komawa gida ta fara yi, sai da ta tafasa wasu magungunan ta yi wanka da na wanka ta sha na sha,sannan ta tura na turawa a gabanta sannan ta shirya cikin wasu sababbin kayan da ta ke da su a gidan masu kyau,wanda daga baya aka kawo mata ɗinkin su daga wajen tela. Kyawun da ta yi ne ya sanya Hajiya zama ta hau kwarzanta ƴar tata tare da bata wasu shawarwarin duk dan ta samu kan Aminullahi tare da mahaifansa ta yanda za su dinga sake mata bakin aljihu suna yin wadaƙa da dukiyar gidan yanda suke so. Da misalin takwas da minti goma na dare Aminullahi ya isa unguwar su Layuzah,sai da ya tsaya ya yi sallar Isha'i a masallacin unguwar sannan ya isa gidan nasu,waya ya yi mata ya sanar da ita zuwan sa,bata fito a lokacin da ya kira ta ba har sai da ta ɓata mintina sha biyar sannan ta fito,tin daga bakin gate ɗin gidan su ya hango ta saboda hasken fitilar lantarkin da ya haske ta,wani ɗamammen ɗinkin da ya bayyana surar jikinta ya gani ta saka,cikin sauri ya fito jikinsa na rawa ya karɓi kular hannunta da jakarta sannan ya yi sauri ya koma motar ya buɗe baya ya saka su,a jikin motar ta tsaya tana sakar masa wani malalacin murmushin da ya kashe masa jiki, buɗe mata mazaunin gefen direba ya yi sannan ya zagaya ya shiga motar ya kunna suka fara tafiya ba tare da sun tanka wa junan su ba. Zuciyar Aminullahi sai kaiwa da komowa take akan shigar da matarsa ta sauya bayan ba da wannan suturar ta fita ba,ita kuwa tsananin kyawun da ta ga ya yi mata ne ya sa ta mutuwar jiki,burinta da fatan ta bai na wuce su isa gida ba dan ta samu damar yaba kyawun nasa yanda ya kamata. Lokacin da suka isa gida sai ta ga mai gadin da bata san da zuwan sa gidan ba ya buɗe musu gate yana ta washe baki tare da ɗaga musu hannu. Kallon Aminullahi ta yi sannan ta ce. "Yaushe Kailani ya zama mai gadi a gidan nan bani da labari?" Cike da ladabi Aminullahi ya ce mata. "Don Allah ki yi haƙuri ban sanar da ke zan kawo mai gadi ba,na yi zaton idan kika zo ki ka gani za ki yi farin ciki da hakan,shi yasa ban sanar da ke ba." Yanayin yanda Aminullahi ke yi mata magana cike da ladabi da gudun ɓacin ranta ne ya tabbatar mata da maganar Hajiyanta da ta ce. 'Ke Layuzah bakin aljihu fa za ki buɗe,domin shi wannan malamin aikinsa kamar yankan wuƙa ne,dan kuwa shane yanzu magani kuma yanzu yanzu.' Murmushi ta sakarwa Aminullahi sannan ta shafi gefen fuskarsa ta ce. "Kar ka damu mijina ba wai ban ji daɗin ganin Mai gadin bane,kawai dai na yi mamaki ne,to Allah Ya sa ya tsaya a iya aikin da aka saka shi." "Amin Ya Allah." Bayan ya buɗe mata ƙofa ta fita ne,sai ya tsaya ya kwashe duk abinda ya kamata ace ita ce ta kwashe ta shiga da shi ciki,yana kulle motar ya yi wa Kailani sallama ya shige cikin gidan,a tsakar parlour ya ga ta wurgar da mayafinta da ɗankwalinta,yana ajiye kayan hannunsa ta bayyana ta bayansa ta rungume sa ta fara aika masa da zazzafan saƙon da ke cikin ranta,Aminullahi bashi da wani zaɓin da ya wuce ya biye mata,dan haka bai wani jima yana tinanin kazantar da ke gidan ba a ransa ta ja shi suka wuce ɗakin baccin sa da ya fi dama-dama. Tin daga wannan ranar Aminullahi bai sake zuwa gaishe da mahaifiyarsa ba sai da izinin Layuzah,idan zai je kuwa tare suke zuwa,bata taɓa basa dama su keɓe da mahaifyarsa,haka za ta zauna a tsakanin su tana zuba iyayi da surutu,kullum kuma za ta je za ta yi wa Momma alkaki da sauran kayan flour da ta kula Momman na so. Hakan da take yi ba ƙaramin daɗaɗa ran Momma yake yi ba,yana kuma ƙona ran Iya. *NIGERIA.* Kwanan Afrah bakwai tana zuwa wajen rawa ba tare da ta yi wa Lamyah tayin zuwa ba,saboda ta kula gaba ɗaya yarinyar bata da wata natsuwa a tattare da ita,kullum cikin damuwa da kewa take wanda Afrah ta yi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta kawar mata da hakan,amma haƙon ta bai cimma ruwa ba. Dan haka a yau ta yanke shawarar ɗaukan Lamyah ta je da ita wajen rawa ko da ba za ta taka ba,ta dai je kawai ta ga yanda ake rawar wataƙila za ta saki ranta. Da jin shawarar da Afrah ta kawo sai Bala ya ce ah ah,kar su koma duba da abinda ya faru da Lamyah a gidan rawar zuwanta na ƙarshe. Lamyah na jin suna ja in ja a tsakanin su sai ta amince za ta je, jin haka sai Bala ya ja bakin sa ya tsuke,ya koma tsakar gida yana jiran su su gama shiri ya kai su ya ajiye su. Mubarak ma ranar kuka ya sanya musu ya ce dole su je da shi shima ya ga wajen,duk yanda Mama Tani ta dinga lallashin sa akan su zauna a gidan ƙi ya yi,kan dole suka shirya yaron cikin ƙananan kaya suka wuce da shi shahararren hotel ɗin da manyan ƴan kasuwa,ƴan siyasa da attajirai tare da ƴan bariki kala da kala ke ziyarta. A cikin mota Lamyah ta zauna Afrah ta buɗe ta yi musu sallama ta fita,fitar Afrah da kusan minti ashirin ne Mubarak ya gaji da zaman waje ɗaya,sai ya faki idon Lamyah da ta kafe waya da ido ta na ganin rawar da Afrah ta sa Faisal ya ɗakko mata Live ta TikTok ya buɗe motar ya fita,Bala ne ya fara kula da yaron dan haka sai ya kwala masa kira yana ƙoƙarin buɗe mazaunin sa,cike da dariya tare da nisbaɗi Mubarak ya fita yana zagaye Hotel ɗin. Lamyah na ganin haka sai ta ajiye wayarta ta bisa da gudu ta na kira tare da faɗin. "Mubarak ba za ka tsaya ba,idan na kama ka fa zan hukunta ka,ba za ka sake bin mu ko ina ba." Gwalo yaron ya yi mata sannan ya nufi wata hanya da gudu,Lamyah bata ɓata lokaci ba wajen take masa baya da sassarfa saboda idanun mutane da ya dawo kansu,Bala na riƙe da wayar Lamyah yana kallon yanda Afrah ke rawa ƙarti na kallon ta,wani irin kishinta ne yake ratsa zuciyarsa,fatansa bai wuce yanda zai tara kuɗi ya aure ta ba tin kafin sauran mutuncinta da yake gani a idanunsa ya gama ficewa. Caraf aka ɗaga Mubarak sama kamar wani tsinke, Lamyah na shiga wajen da yaron ya nufa a guje ta tsaya ƙiƙam tana ƙarewa mutumin kallo tin daga ƙasan ƙafarsa har zuwa fuskar sa,hannun bawan Allah'n nan rawa ya fara yi a daidai lokacin da ya ƙure fuskar Mubarak da kallo,mutanen dake bayan sa ne suka ce. "Lafiya dai ko Alhaji? Alhaji ka na lafiya kuwa?" Cikin wata iriyar murya mutumin ya ce. "Ɗan'uwana.... El-mustapha Ɗan'uwana...lallai wannan...wannan jinin Ɗan'uwana El-mustapha ne." Kukan da ya ƙwacewa Lamyah ne ya sake jan hankalin Abii da ke riƙe da Mubarak,da wani irin gudu Lamyah ta fito daga babban ɗakin taron da mafi yawanci ƴan siyasa da manyan attajiran ƴan kasuwa ke yin taro a cikin sa, babu ɓata lokaci Abii ya ƙanƙame Mubarak a jikinsa ya na sumbatarsa,tabbas wannan yaron El-mustaphansa ne da Lamyah,lallai Allah yana yin yanda ya so ne a lokacin duk da ya so,idan ba iko na Allah ba ta yaya zai haɗu da Lamyah a wajen da bai taɓa zato ko tsammani ba. Lamyah kuwa na zuwa wajen motar su sai ta tarar da Bala da Afrah suna ta sa'insa a tsakanin su,Afrah banda faɗa babu abinda take yi wa Bala,cike da masifa ta ce. "Idan wani abu ya same su Bala ka sa a ranka daga yau babu ni babu kai har abada." Riƙon da Lamyah ta yi mata ta baya tana gunjin kuka ne ya sanya Afrah juyawa cikin sauri ta sake rungumeta a jikinta kamar za ta saka ta a cikinta,cike da tashin hankali ta ce. "Wanne ɗan iskan ne ya taɓa ki yau kuma? Ki yi shiru ki sanar da ni abinda ya same ki,na rantse da...." "Abiii." Shine sunan da Lamyah ta iya furtawa kenan,cike da rashin fahimta Afrah ta ce. "Ki na kewar Abii ne? Ki yi haƙuri to,mu je gida ina Mubarak ɗin? Da na san damuwar dake ran ki ba za ta ragu ba da bamu zo ba." Afrah na shirin shigar da Lamyah mota ta koma neman Mubarak sai ta hango wani kamilin mutum na ɗauke da Mubarak suna tunkaro su,da sauri ta saki hannun Lamyah ta isa gaban dattijon ta karɓe Mubarak,cike da nuna janwuyanci ta ce. "Malam me yasa za ka ɗauke min ƙani bayan baka yi kama da mugayen mutane ba? To bari ka ji na faɗa maka,idan ma rigar mutunci ka shiga ka ke son aikata zalunci ni nan maganin ka zan yi,babu wanda zai taɓa min ƴan'uwa ba tare da na ɗauki mummunan mataki akan sa ba." Murmushi Abii ya yi wanda ya bayyana tsantsar kamanninsa da Aminullahi,jikin Afrah ne ya yi sanyi a lokacin da ta ga ya yi mata kama da wanda ta sani,sai dai ko za a ɗora mata bakin bindiga a wannan lokacin ba za ta iya faɗar sunan shi ba,cike da fara'a Abii ya ce. "Ke ce Afrah da Mubarak ke bani labari yanzu? Lallai ya yi gaskiya you are overprotective indeed,da kyau haka ake son ƴar'uwa ta gari,ni suna na Mus'ab wato Abiin su Lamyah." Kallon Lamyah da ta rakuɓe a jikin mota tana satar kallon Abii ta yi,babu abinda ke damun zuciyarta a yanzu da ya wuce ganinta da ya yi a hotel,da wace manufa zai fassara ganinta a hotel da ya yi yanzu? Wannan dalilin ne ya kashe mata jiki har ta kasa sakin jiki ta fitar da tsananin murna tare da farincikin ganin Abiin nasu da ke ranta. Durƙusawa Afrah ta yi ta na ɗaga hannayenta sama tana godewa Allah, cike da zumuɗi ta ce. "Lamyahna kin ga ikon Allah ko? Yau ƙarshen wahalar ki da neman Abiin ki ya ƙare,Allah mun gode maka." Bala ma durkusa wa ya yi ya kwashi gaisuwa,a hankali Abii ga buɗe wa Lamyah hannayensa alamar ta je gare shi,cikin sassarfa ta isa gare shi ta na hawaye,da sauri ya kulle hannunsa ya haɗe ta da Mubarak ya rungume yana jin tsananin kewar El-mustapha,ji yake yi kamar a lokacin aka sanar da shi rasuwar Ɗan'uwansa,hawaye masu zafi ne suka dinga zuba daga idanunsu. Suna cikin wannan halin ne Faisal ya zo da gudu ba tare da ya kula da su Lamyah ba,miƙawa Afrah maƙudan kuɗaɗen ta ya yi ya na faɗin. "Ya za ki gudu ba ki kammala abinda kike yi ba,anyway ga wannan wani Alhaji ya ce a baki saboda ya yaba da aikin yau,dan Allah ki lallaɓa ƙanwar nan taki gobe itama ta dawo bakin aiki,mutane na ta son ta yi ko da sau ɗaya ne,dan Allah ki zo gobe kin......" Maganarsa ce ta maƙale a lokacin da ya ga Abii rungume da Lamyah,cikin in-ina ya hau gaishe da Abii tare da faɗin. "Yaushe ka zo Alhaji? Ya aboki na,kwana biyu? Sannu da zuwa." Murmushi kawai Abii ya sakar masa sannan ya juya wajen su Afrah,babu jimawa Faisal ya danna layar zana ya ɓace a wajen,dan kuwa ba ƙaramar kunya ya ji ta kama shi ba,tinda ya fara aiki a wajen ya san su Aminullahi da ya ga Abii ɓoyewa ya ke yi, duk da cewa ya san Abii ya san yana aiki a wajen,ya kuma san wanne irin aiki yake yi,amma kunyar bawan Allah'n yake ji sosai. To su kuma Afrah me ya haɗa su da shi? Ɗaga kafaɗa ya yi ya wuce cikin club ɗin ya ci gaba da hidimar gabansa. Abii kuwa motarsa ya nufa Malam Isa na ganin sa ya taso ya buɗe masa,a lokacin ne Abii ke sanar da Malam Isa abinda ke faruwa,farin ciki ya dinga yi tare da godewa Allah akan bayyana su Lamyah da ya yi cikin sauƙi,Mubarak Abii ya ɗakko ya saka a gefen sa Malam Isa ya tada mota suka bi bayan Bala da ya ja motar da su Afrah ke ciki ya yi gaba dan ya yi wa Abii jagora zuwa gidan su. Ko da suka je Abii ya ga wajen da su Lamyah ke da zama sai ya yi hamdala sannan ya yi musu alƙawarin zuwa a cikin satin su wuce Niger da zarar ya kammala abinda yake yi. Godiya sosai Afrah ta dinga yi masa har ya shiga motarsa zai koma gidan sa. Wannan rana rana ce mai ɗinbin tarihi mai cike da farinciki a wajen Lamyah da Mubarak,a gefe ɗaya kuma rana ce mai cike da baƙin ciki da tsantsar damuwa tare da tsoron rabuwa da masoyi a wajen Afrah,bayan ta gama taya Lamyah murna sai ta ce kanta na ciwo da jikinta,bari ta je ta watsa ruwa ta sha magani ta ɗan kwanta ko za ta ji daɗin jikinta,ba tare da Lamyah ta gane komai ba ta yi mata fatan samun sauƙi ta raka ta har ɗaki sannan ta koma parlour,rasa wanda za ta kirawo ta sanar da shi abun farincikin da ya sameta ta yi,ji ta yi ina ma Handsome ɗinta ya san da zaman ta,sun ƙulla kyakkyawar alaƙa tabbas da shi za ta kira ta sanarwa da wannan abun farin ciki da ya same ta......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 28. A cikin kwanaki tara da Abii ya yi bai dawo ɗaukan su Lamyah ba,ta rame ta zama wata iriyar shiru da ita,daga kuka sai tagumi. Lamyah ta cire ran zai dawo ɗaukan su,cikin kuka ta ce da Afrah. "Shikenan Afrah last hope ɗin mu ya kuɓuce mana,na tabbata ganin mu a hotel kaɗai ya isa ya yi masa katanga da mu,wanne irin rashin sa'a da baƙin jini ke bibiyar rayuwarmu? Dangin mahaifin mu sun yi sanadiyyar barin ƙasar mu ta haihuwa,dangin mahaifiyar mu sun ƙi karɓar mu,ga kuma aminin mahaifina wanda na yi zaton uwa ɗaya Uba ɗaya suke ba dan sun sanar da ni cikakkiyar alaƙar dake tsakanin su ba shi ma ya gudu." Kukan da take yi yana taɓa zuciyar Afrah sosai da sosai,cikin sigar lallashi Afrah ta ce. "Lallai wannan abubuwa da suka faru a rayuwar ku ba masu sauƙin ɗauka bane a zuciya,amma kuma a duk sanda kika shiga damuwa ki dinga godewa Allah akan ni'imomi masu tarin yawa da ya yi muku wanda bai yi wa wasu ba,kin dinga tina cewa wani tin yana jariri yake rabuwa da nasa iyayen da dangi baki ɗaya,sannan baya taɓa haɗuwa da iyayen riƙo nagartattu,ga talauci da ya yi wa rayuwar su rumfa ko ta wanne fanni. Sannan ki dinga tinawa kina da ni ga Bala,Baba Musa da Mama Tani,gaba ɗayan mu muna buƙatar junan mu tinda duk damuwa ɗaya ce a cikin zuƙatan mu, sannan Uwa Uba muna son ki muna ƙaunar ki kamar yanda ƴan'uwa na jini suke son junan su ko ma fiye da haka." Tinda Afrah ta fara magana Lamyah ta kwantar da kanta a saman cinyar ta ta yi lamo tana sauraron ta,ganin haka sai Afrah ta ci gaba da kwantar mata da hankali har ta samu bacci mai nauyin gaske irin wanda ta jima bata yi irinsa ba ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Afrah ta sauke tare da alƙawarin za ta je club yau ta tuntuɓi Faisal ko ya san inda za ta samu Abii,daga nan za ta je har inda yake ta cinye masa mutuncinsa tass tinda ya nuna bashi da riƙon amana kamar yanda ta yi zato. Haka suka wuni har yamma Lamyah bata saki jikinta yanda ya kamata ba bayan ta tashi daga bacci,da ta yi sallar la'asar ma sai ta yi zamanta a wajen da ta yi sallar ta takure waje ɗaya tare da ɗora kanta a saman guiwowinta. Ta ɓangaren Abii kuwa tin kwanaki biyar da rabuwar su ya kammala duk abinda zai yi a Nigeria,sai ya wuce Rijiyar Lemo dan ya ji dalilin da ya sa basu kira sun sanar da shi Lamyah ta je wajen su ta jima ba kamar yanda ta sanar da shi a mota da suna komawa gidan su. Ransa ya ɓaci sosai da jin irin abubuwan da aka yi musu,dan kuwa bai taɓa zaton haka daga gare su ba,musamman Malam Abubakar da yake aminin mahaifin Aminee da sukai zama na amana. Malam Isa na tsayar da mota a ƙofar fadar Mai Unguwa Abii ya fita daga motar fuskar sa a ɗaure,kai tsaye wajen Mai Unguwa ya nufa ya zauna a tabarma kamar yanda ya tarar da mutane,washe baki Mai Unguwa ya yi cike da jin nauyin Mus'ab,domin kuwa da ganin fuskarsa ya fahimci duk yanda akai fushi yake yi akan rashin kiransa da ba su yi ba su bashi wani bayani akan Lamyah,zuciyar Mai Unguwa har ta raya masa kawai ya zabga ƙarya ya ce har wannan lokacin ba su ga Lamyah ba,sai wata zuciyar ta ƙwabe shi,a matsayinsa na shugaba ƙarya bata kamace sa ba,cikin borin kunya dan tinawa da yanda Lamyah ta bar gida ya hau gaishe da Mus'ab wanda ke gaisawa da mutanen dake wajen. "Malam Buzu yau kai ne a unguwar tamu? Maraba lale,ai mun jima muna neman lambar wayar da ka bamu domin mu sanar da kai cewar yarinya dai ta kawo kanta har wajen mu,sannan in sanar da kai duk wani abu da ya faru da ita a wannan unguwa tamu mai albarka. Dangin Mahaifiyarta sun ƙi karɓarta sam,babu abinda ban yi ba dan ganin sun karɓe ta,sai daga baya na gane tafiyar ta inda ta fito shi ne kwanciyar hankalinta,abinda ban ji daɗi ba shine yanda iyalina suka azabtar da ita ba tare da sanina ba,sai bayan abubuwa sun faru ta bar gidan mun dawo daga jana'iza na samu mummunan labarin barin ta gidan." Ajiyar zuciya Mus'ab ya sauke,yana jinjina irin rashin imanin wasu mutanen. Sun jima suna tattaunawa da mutanen Rijiyar Lemo kafin Abii ya yi musu sallama da ihisani kamar yanda suka saba yi shi da El-mustapha a duk sanda ya zo,sannan ya koma gidan sa. Da yamma ya tafi gidan su Faisal dan jin abinda ya haɗa shi da su Lamyah har yake basu kuɗi tare da roƙon Lamyah ta zo washegari. Ba ƙaramin faɗuwar gaba Faisal ya samu ba a lokacin da ya fito ƙofar gidan su ya ga Abii tsaye yana jiran sa,cike da ladabi ya durƙusa ya gaishe shi,bayan sun gaisa ne Abii ya tambaye shi alaƙarsa da su Lamyah,cikin tsakanin ladabi Faisal ya ce. "Alhaji babu wata alaƙa dake tsakanina da su da ta wuce ta aiki,suna zuwa club ɗina ita da ƙawarta su yi rawa ni kuma na basu kuɗin sallama." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, rawa kuma? A club? Maza na kallon su?" Sosa kai Faisal ya yi yana ta rarraba ido,a sanyaye Abii ya ce. "Bayan rawa kuma akwai wani abu da suke yi? Kar ka sake ka ɓoye min dan zan tsananta bincike akan wannan lamarin,idan na gano akwai wani abu bayan wanda ka sanar dani zamu samu mummunar matsala da kai Faisal." Nan da nan Faisal ya hau rantsuwa tare da yi wa Abii bayani game da irin rayuwar da su Lamyah suke gudanarwa,jin cewa iya rawa suke yi,babu wani abu bayan wannan sai ya kwantar masa da hankali. Daga wajen Faisal hotel Abii ya koma ya sake tambayar mutanen wajen halayyar su Afrah da Lamyah,amsar da Faisal ya bashi ita mutane suka bashi,mutane ƙalilan ne suka yi ɓatanci akan Afrah saboda suna jin haushin taƙi amincewa da su su yi lalata da ita. Da wannan bayanan da Abii ya tattara ya koma gida. Washegari da misalin biyar na yamma ya ɗau wanka ya shiga cikin gari da kansa,sai da ya je Sahad store ya yi wa su Lamyah siyayyar kayan maƙulashe sannan ya nufi gidan. Ya na zuwa ya tarar da Afrah tsaye a waje ita da Bala suna hira,da alama ran Afrah a ɓace yake,murmushi ya sakar mata wanda ya fitar da kwarjininsa da kamalarsa,sunkuyar da kai ƙasa Afrah ta yi ta nemi ɓacin ran da take ciki ta rasa,domin kuwa kafin zuwan Abiin shawara take nema wajen Bala akan za ta je wajen Faisal ta nemo adireshinsa ta je har gida ta ci masa mutunci,shi kuma Bala haƙuri yake ta bata ya ce ta bari su cike kwana goma idan be dawo ba sai su je neman sa,tinda da kansa ya ce zai dawo idan ya kammala abinda yake yi a gari. Muryar Bala ta jiyo yana gaishe da Abii cike da girmamawa,amsawa ya yi sannan ya tambayi lafiyar su,Afrah ma duƙawa ta yi har ƙasa ta gaishe sa,gate Bala ya ɓude wa Abii ya shigar da motar sa sannan suma suka mara masa baya,yana fitowa daga motar Afrah ta kwasa da gudu ta shige cikin gida,a zaune ta tarar da Lamyah ta na ta shessheƙar kuka,ƙugu ta kama sannan ta ce mata. "To ɓaure sarkin kuka sai ki taso ki zo kin yi baƙo." Da sauri Lamyah ta ɗaga kai tana kallon Afrah,murmushi Afrah ta sakar mata idanunta cike da ƙwalla ta ɗaga wa Lamyah kai,hanya ta bata tare da miƙar da hannayenta tana yi mata nuni da hanyar,a guje Lamyah ta fita daga parlour tana kuka. Tsaye ta ga Abii ya na kallon hanyar da Afrah ta bi da kallo,wani irin tsallen murna ta daka ta faɗa jikinsa ta na sake rushewa da wani sabon kukan, riƙe ta Abii ya yi a jikinsa da kyau ya na bubbuga bayan ta da sigar lallashi,Mubarak dake yawo a motar sa ta wasa ne ya hango Lamyah rungume a jikin Abii, cikin sauri ya buɗe murfin motar ya fito ya nufe su da gudu ya na ƙara irin ta yara idan sun ga abun farinciki. Da sauri Abii ya maida Lamyah gefe ya ɗauki Mubarak ya wurga shi sama, ihun murna ya dinga yi kamar ya daɗe da sanin Abii,a tare suka shiga cikin gidan suka zauna,Lamyah na maƙale da hannunsa na dama Mubarak na zaune a cinyarsa ta hagu,banda surutu da tambayoyi akan abinda ya hana shi dawowa gare su babu abinda Abii ke amsawa daga yaran nasa,sai dai ya ɓoye musu yanda ya tsaya ya yi bincike game da rayuwarsu kafin ya zo gare su. Cikin tsananin farin ciki Lamyah ta ce. "Abii yaushe za mu je ka kai ni wajen Momma da Yah Amee?" "Jibi nake so mu tafi Lamyah,yau idan zan tafi ki bani paspo ɗin ku na wuce da shi. Sai kuma maganar yayar taki da su za mu tafi ko ya abun zai kasance?" Cikin sauri Bala wanda tin da ya biyo bayan su yana washe baki saboda taya su murna bai koma waje ba ya ce. "Ai Alhaji ina gama jarabawa za a ɗaura mana aure da ita Afrahn,ina ga sai dai ku yi gaba mun kawo muku ziyara daga baya." Cike da jin kunya Afrah ta sunkuyar da kai tana dariya ƙasa-ƙasa,murmushi Abii ya yi sannan ya ce. "Ah masha Allahu,yaushe ne za ka gama jarabawar kenan?" "Gobe ne zan rubuta ta karshe idan Allah ya kaimu." "To Allah Ya kai mu da rai da lafiya,idan haka ne ba zan tafi ba har sai an ɗaura auren ku da masoyiyar ka,ni zan ɗauki nauyin duk wani abu da za a gudanar a bikin naku,ina fatan dai za ku ci gaba da zama anan gidan tinda su za su koma wajena da zama ne, ko ya kika ce Ƴar Abii?" Cike da jin daɗi Lamyah ta ce. "Yauwa Abii gwanda da ka faɗa musu da kan ka,domin da na yi musu maganar zama anan cewa suka yi sam ba za su zauna a nan ba,za su

Chapter 16 of 30