zata kasance dasu da ya sauke girman kai ya ci gaba da neman ta a waya bayan rasuwar Ammin su.
Bayan kwana biyu Mus'ab da Aminullahi suka shirya domin tafiya Nigeria. Sallama suka yi da mutanen gida duka bi jirgi suka tafi Nigeria.
Da isar su Malam Isa ya je Airport ya ɗauke su,gidan El-mustapha da suka saba sauka a duk zuwan da suke yi ya sauke su. Aminullahi na gama gaisawa da Malam Isa sai ya wuce ɗakinsa ya shiga banɗaki ya yi wanka,yana fitowa ya ji koke-koken mutane,nan take ya gane Mahaifinsa ya sanar da su rasuwar mutumin da yake kula da su da iyalan su,rauni zuciyarsa ta yi sosai,tare da jin wani ƙwarin guiwar ci gaba da taimaka musu kamar yanda Baaba ya yi ko ma fiye da haka. Shiryawa ya yi cikin manyan kaya ya shafa mai tare da fesa turare ya fito parlour,kallon su Malam Isa ya yi da Malam Datti suna ta matsar ƙwalla ya ce musu.
"Ku yi haƙuri ku bar kukan haka, addu'a ita Baabana ya fi buƙata a yanzu,Allah Ya jiƙansa ya gafarta masa,kuma In Shaa Allahu zan ci gaba da kula da ku kamar yanda yake yi a baya."
"In Shaa Allahu mun yi alƙawarin yi masa addu'a har ƙarshen rayuwarmu,ba za mu taɓa manta alkhairin Alhaji ba a gare mu."
Daga nan Aminullahi ya yi musu sallama ya ce zai ɗan fita. Kai tsaye hotel ɗin da ya saba zuwa ya tattauna da abokan cinikayyarsu ya nufa,yana zuwa ya kira Faisal a waya ya ce masa ya shigo gari. Bayan sun gama gaisawa ne ya ce.
"Da na kammala da tattaunawar da zan yi da baƙi na zan neme ka mu gaisa da kyau,amma ka sani ba zan zo wajen nan naku ba fa sai dai ka fito waje."
Daga can ɓangaren Faisal dariya ya yi sannan ya ce.
'Kar ka damu,zan fito waje,kai dai kawai da ka kammala ka yi min waya.'
Sallama suka yi,Aminullahi ya wuce kula da baƙin su da suka zo daga Ibadan za su sari kaya a wajen su.
A daidai wannan lokacin kuwa Afrah na can ɗakin da aka tanada domin kwalliya,zaune take a gaba babban madubin da ya kewaye ɗakin wanda aka shaƙe shi da kayan kwalliya kala-kala,mata ne zazzaune da ƴan daudu suna ta hira, tare da yin kwalliya,kasancewar Afrah bata da ƙawa a wajen sai ya zamanto ita ɗaya take harkokin gabanta a wajen,wasu mata ne su biyu da ɗan daudu ɗaya suke gulmar ta,cike da yanga ɗan daudun ya yi ƙas wajen sau huɗu a jere da chewing gum ɗin bakinsa tare da yin fari ya watsa hannu ya ce.
"Kai dan Allah ku rabu da marar rabo,gata siririya fara tass irin yanda wasu manyan mutane ke so amma tana wasa da damar ta,wannan da ace ta bada haɗin kai yanda ya dace kwarmin wuyanta sai ya cike tsaf,tini za ta dena rataya jakar bend down select na sabon gari,ta fara rataya designers,ni daga yau na ma cikin ku duk wadda ta sake maganar ta se na ci uban yarinya."
Taku ya fara yi cike da yanga ya wuce ta gaban Afrah ya na faɗin.
"In banda ma Oga Faisal da yake sanyi ƙalau kamar ƙanƙara,ai irin wannan idan ta hana a nemi kuɗi da kadarar ta watsar da ita zan yi na samo wata,mtsssww aikin banza kawai."
Afrah na jin su bata ce musu komai ba,sai ta saki murmushi ta sake ɗaukan lip glow ta shafa a leɓenta sannan ta miƙe tsaye tana gyara wandon jikinta,Faisal ne ya leƙa yana binta da kallo daga sama har ƙasa,sai da ya tabbatar ta fito fess yanda yake so sannan ya ce.
"Wuce mu je,ke kaɗai filin ke jira ta wajena, Allah Ya sa yau ma dawa ta yi nama irin na jiya."
Fari Afrah ta yi sannan ta ce.
"Amin Ya Allah,ai ni dai babu abinda zan ce wa Allah sai godiya,tinda gashi ko da bana sana'ar saida jikina ina samun na kashe buƙatuna."
Nan take yan matan nan suka hayayyako mata da zagi tare da cin mutunci,dariya kawai ta yi musu wadda ta ƙara hasala su kafin ta bi bayan Faisal da ke jiran ta a stage. Afrah na zuwa ta hau rawa tare da juya jikinta kamar tarwaɗa,nan take mazajen da suka ke wajen saboda kashe ƙyayar idanunsu sai suka hau yi mata ɓarin kuɗi,cikin fara'a da farin ciki Faisal ya ci gaba da bata ƙwarin guiwa. Afrah bata bar stage ɗin nan ba har sai da lokacin ta ya cika,cikin sauri masu tara musu kuɗi suka yi kan kuɗin suka kwashe,kai tsaye wani ɗaki suka shiga Afrah ta zauna ta na haki tare da dariyar samun maƙudan kuɗaɗe,nan take ta karɓa ta haɗe kuɗin mazajen biyu na tsaye suna taya ta lissafi,Faisal ne ya shiga wajen ya tsaya har ta kammala ta miƙa masa,yana ƙirgawa ya ga kuɗin sun kai dubu ɗari da saba'in,shewa suka hau yi suna murna,nan take ya kasanfta ya baiwa kowa nashi,cike da farin ciki Afrah ta karɓi kasonta ta koma ɗakin kwalliya ta sanya kayanta tare da rataye jakarta a kafaɗarta. A tare suka fito da Faisal ya na sake yi mata pampo dan ta amince da wani hamshaƙin mai kuɗi da ke ta naci akan ta,cikin marairaicewa Faisal ya ce.
"Ya yi maki alƙawarin mota fa Afrah,kin ga kin huta da zaman jiran a rage maki hanya a maida ke gida,dan Allah ki amince masa ko sau ɗaya ne."
Cike da shaƙiyanci Afrah ta ce.
"Oga Faisal ka dage sai ka ƙarasa lalata marainiyar Allah ko? To ni dai Afrah na yi alƙawarin ba zan taɓa aikata zina ba da hayyaci na,iya wannan zunubin ma da nake kwasa ya isa haka,sai da safe,yau dai ba zan jira a rage min hanya ba,tinda na samu manyan kuɗi,shatar adaidaita zan yi ya kai ni gida,ka ga na huta da gorin ka na yau."
Tafe suke suna hira har ya kawo ta bakin gate ɗin shiga hotel ɗin,wayar sa ce ta yi ƙara,yana dubawa sai ya ga Aminullahi ne ya kira shi,amsawa ya yi tare da sanar da shi yana bakin gate su haɗu anan. Nan take Afrah ta tsuke fuska ta ce.
"Sai da safe,zan matsa ta can na samu abun hawa,dan ba zan tsaya wannan ɗan rainin hankalin abokin naka da be iya hausa ba ya same ni anan."
Dariya sosai Faisal ya yi,sannan ya ce.
"To sai da safe,ni dai ina sake gayyatar ki wannan harkar,ya kamata ki zo ki ci arziƙi ki bar arziƙi a mazauninsa,mai son ka da alheri shi ke yi maka tayin hanyar samo sa."
Murmushi kawai Afrah ta yi ta sawa wani mai adaidaita sahu hannu,a daidai wannan lokacin Aminullahi ya iso,kallonta ya yi ya ja dogon tsaki sannan ya kau da kai,ita ma harara ta zabga masa sannan ta shige ta barsu tsaye a wajen.................
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 18.
A ƙofar gidanta adaidaita sahu ya ajiye ta, hannunta riƙe da ledojin da ta tsaya a hanya ta siyo kayan maƙulashe. Sallamar sa ta yi da kuɗin da ya zarta wanda ya kamata ta basa,ganin hakan sai ya sanya shi zuba mata godiya kafin ya tuƙa adaidaitansa ya bar wajen. Cike da farin ciki Afrah ta buɗe ƙofar gidanta ta shige,kai tsaye kitchen ta nufa ta ɗakko plate ta juye gasasshiyar kazar da ta siyo leda biyu,zama ta yi ta buɗe lemon kwali ta dinga yagar kazar ta na korawa da lemon har sai da ta ƙoshi,ɗaukan saura ta yi ta ajiye a center table kasancewar bata da fridge,sai ta kifa kwando a sama. Wanka ta shiga ta dirji jikinta sannan ta yi alwala ta koma ɗaki,sai da ta sanya kaya marasa nauyi a jikinta kafin ta tada sallar isha'i da bata yi ba,ta na idarwa ta haye katifarta ta rintse ido,babu jimawa bacci ya kwashe ta.
Washegari Afrah bata farka ba sai ƙarfe bakwai da rabi na safe,a gajiye ta miƙe tana salati tare da istighfari,cikin sauri ta shiga banɗaki ta yi tsarki sannan ta ɗaura alwala,sallar asuba ta yi sannan ta zauna ta yi azkar kafin ta shiga kitchen ta ɗora ruwan shayi,tana gamawa ta yi amfani da gwagwa/matsamin taliya,ta ɗumama kazar nan dika biyun,mazubi mai kyau ta samu ta saka ɗayar da bata taɓa ba,sannan ta ɗauki ragowar ta jiyan da ta ci ta rage ta koma parlour ta zauna ta cinye ta ƙoshi. Tana kammalawa ta zira babban hijabinta ta ɗauki kwanon da wayarta ta kulle gidan ta nufi gidan Lamyah. A bakin gate ta tarar da Baba Musa kamar yanda ya saba zama kullum,gaishe shi ta yi har ƙasa sannan ta miƙa masa kwanon hannunta ta ce.
"Baba ga wannan a sa mana albarka."
Cike da fara'a Baba Musa ya karɓi kwanon ya buɗe,ganin danƙwaleliyar kaza na nason maiƙo ne ya sanya shi sakin murmushi mai sauti,godiya ya yi mata sosai kafin ya miƙe ya shiga ɗakinsa yana cewa
"Bari na ajiye sai masoyin naki Bala ya dawo daga makaranta mu ci tare,dan dai na san wannan na shi ne ba wai domin ni aka kawo ba."
Dariya sosai Afrah ta yi kafin ta ce masa.
"Baba ka yarda da ni domin kai na kawo,ai na riga na san yana makaranta a daidai wannan lokacin."
"Hummm Afrah kenan,kar nake kallon ki fa."
Cike da jin kunyar dattijon ta wuce cikin gida tana dariya,ko da ta shiga sai ta tarar da Lamyah zaune Mubarak na yi mata rikicin yunwa yake ji,ga abincin yara nan ta dama masa ya ce sam shi ba wannan yake so ba,doya yake so ta soya masa ko ta dafa masa abinci,zaune take riƙe da littafinta a hannu ta na kallon shafin da shine ya fi ɗaukar hankalinta a duk lokacin da ta ke karanta littafin da Iyayenta suka yi haɗaka wajen rubutawa,Afrah ce ta zagaya ta saman kanta ta hau karanta shafin da ƙarfi.
-Ko bayan babu raina ina so Aminullahi ya zamo mijin ki,a gani na da iya hange na babu wani namijin da zai riƙe mana ke bisa amana da gaskiya sama da Aminullahi,shi kaɗai ne ya san daraja da mahimmancin ki,shi kaɗai ne zai iya da shagwaɓar ki da duk wata gazawar ki,Baaban ki ya jima da yiwa Aminullahi alƙawarin aura masa ke,Abiin ku da Momma duk sun san da wannan maganar...-
Ɗaga kan ta Lamyah ta yi idanunta na zubar da hawaye ta zuba su a fuskar Afrah,nan take Afrahn ta yi shiru ta dena karantawa,zagayawa ta yi ta zauna a kusa da Lamyah tare da kama hannunta ta ce.
"Ya kamata ki gaggauta nemo wannan ɗan'uwa naki,domin kuwa ina jiye miki yin rayuwa babu wani tsayayyen namiji akan ki,a duk lokacin da mace za ta zauna ita kaɗai ba tare da namiji ba,mutane za su sanya mata idanu ne tare da kiranta da sunaye marasa daɗi,a yanzu ana ɗaga maki ƙafa ne saboda mahaifinki da ya taimaki makarantu da masallatan unguwar nan har ma ya bawa wasu mazajen jari da sauran su,amma da an kwana biyu aka fara ganin gilmawar ki ke kaɗai babu wani tsayayyen muharrami a tare da ke za su fara gulma da ganin ki a matsayin mai zaman kanta,kin ga dai halin da nake ciki da abubuwan da nake fuskanta a unguwar nan."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Lamyah ta sauke kafin ta lumshe idanunta,dogon hancinta mai ɗan kauri ta ja ta goge majinar dake barazanar zubowa da tissue,cikin dakusasshiyar muryar da ta gaji da kuka ta ce.
"Me yasa jiya baki dawo ba? Na yi zaton kema kin barmu ne kamar yanda kowa ya barmu,na jira ki har ƙarfe ɗayan dare,amma baki shigo ba,ƙarshe akan dole Baba ya rufe gate."
"Rashin dawowa ta ne ya sanya ki kuka haka? Haba Lamyah ya kike abu kamar wata ƙaramar yarinya? Idan Mubarak ya ga kina kuka shi kuma ya yi me? Na dawo around 12:30am sai na ga bai kamata na shigo ba,na yi zaton kun yi bacci ma,shi yasa na wuce gida,kar ki sake sakawa a ran ki ni Afrah zan bar ki matsawar kina unguwar nan,to ina nan tare dake. Bari na samar maku da abinda za ku karya."
Tashi ta yi ta na ci gaba da yiwa Lamyah faɗan zama da yunwa,tana shiga kitchen ta hau fere doya,tana gamawa ta yanka ta wanke ta zuba a tukunya ta zuba ɗan gishiri kaɗan da sugar,sai ta rufe ta ɗora a saman gas ɗin da ta kunna,kafin doya ta dahu ta jajjaga ɗan attaruhu da albasa da garlic sai ta zuba curry da kayan ɗanɗano,ƙwai guda bakwai ta fasa akai ta kaɗa. Ajiyewa ta yi ta duba doyar ta,sai taga ta dahu yanda take so,nan take ta sauke ta dora mai ta yanka albasa,ƙamshin dake tashi ne ya jawo hankalin Lamyah ta shiga kitchen ɗin riƙe da hannun Mubarak,a gabanta Afrah ta fara tsoma doyar a ruwan ƙwai tana soyawa,waje ta samu ta zauna ita da Mubarak,da Afrah ta soya sai su hau ci,a haka har suka ƙoshi. Hira suka dinga yi Afrah na ta bata labarin waje da take yin rawa,gaba ɗaya Lamyah ta tattare hankalin ta tana sauraron Afrah cike da sha'awar watarana itama tana so ta je waje dan ta yi rawa,cike da zumuɗi ta ce.
"Yaushe za ki kai ni nima na gwada tawa basirar? Ni ko ba su bani ko sisi ba,ina so kawai na ganni a kan stage ina rawa ana yi min tafi."
Murmushi Afrah ta yi sannan ta ce.
"Ai kuwa in dai kina so zan yiwa Faisal magana,a ware maki rana ta musamman mu je ya gwada ki ya gani,idan za ki iya sai a saka maki lokacin da za ki fita show."
Murna sosai Lamyah ta yi ta rungume Afrah,cike da fara'a ta ɗauki Mubarak ta na yi masa wasa tare da sanar da shi burin ta ya kusan cika a rayuwa,cikin maganarsa irin ta yaran da basu iya hausa ba sosai ya ce.
"Ni ma zan biki na yi rawa."
Dariya ta yi sosai kafin ta ce.
"Lala kai makaranta zan saka ka,ka fara karatu ni kuma in dinga zuwa ina yin rawa,idan lokacin tashi ya yi sai na ɗakko ka,ko Bala ka ke so ya dinga ɗakko ka?"
Ɗaga mata kai ya yi kawai ba tare da ya bata cikakkiyar amsa ba,da wannan hirar suka kammala abinda suke yi suka tattara suka koma parlour,Afrah sai ta ɗauki abinci ta kai wa Baba Musa,tana komawa sai ta gyara gidan sannan ta yiwa Mubarak wanka ta sauya masa kaya. Kallon Lamyah ta yi ta ce.
"To ni zan wuce gida,saboda ina so na ɗan tattaka kafin lokacin fita ya yi,ko akwai wani abu da kike so na yi maki?"
"Ah ah babu komai,na gode,amma me zai hana ki yi anan? Ko baki so na ga yanda kike yin rawar ne?"
"Ah ah ba haka bane,na ga cewa har yanzu kina jimamin rashin mahaifinki shi yasa,bai kamata a lokacin da yafi buƙatar addu'ar ki ba ki shagala ki manta da shi."
Ajiyar zuciya Lamyah ta sauke kafin ta ce.
"Babu komai Afrah za ki iya yin duk abinda kike so anan,ni dai bana so a barni ni kaɗai,kaɗaici na yi min yawa, addu'a kuma ai kema kin san a koda yaushe cikin yiwa iyayena nake ko?"
"Kar su Baba su ga rashin hankali na Lamyah."
Hannun Afrah Lamyah ta kama ta amshe wayarta da mayafinta ta ajiye mata su a gefe,sai ta tashi da kanta ta kunna TV ta kai tashar da ake raye-raye da kaɗe-kaɗe,tun Afrah na jin babu daɗi sai ta ga Lamyah ta miƙe ta na rawar da ta sanya ta sakin baki tsabar ganin ƙwarewarta,ashe dai ita harigido kawai take yi bata sani ba? Wannan ai idan suka je club ɗin da take aiki babu mai sake barin ta ta taka rawa. Zama ta yi ta dinga koyon duk wani taku da Lamyah ke yi,ganin haka ne ya sanya Lamyah koya mata rawa irin ta larabawa mai ban sha'awa. Haka suka lalace wajen rawa har sai da suka gaji dan kan su suka zube a kujera su na maida numfashi.
**********************
Mus'ab da Aminullahi tare da Malam Isa ne gurfane a gaban Mai unguwar Rijiyar lemo da muƙarrabansa,kusan duk wanda yake wajen sai da ya zubar da hawayen jin rasuwar Aminee da El-mustapha. Malam Abubakar kuwa abun haɗe masa ya yi,domin kuwa yana cikin kaɗaicin rashin iyalinsa sai wannan mummunan labarin ya riske shi. Mai Unguwa ne ya yi gyaran murya cike da jarumta ya ce.
"Kai Malam Haladu a je a kirawo mana ƴan'uwan Malam Muhammadu da suka yi saura da su Habibu,saboda su san halin da ake ciki,tinda su ne ƴan'uwan Aminatu na jini ko ba haka ba?"
Nan waje ya ɗauka da faɗin.
"Haka ne Allah Ya taimake ka."
Babu jimawa Malam Haladu ya bi dika gidajen ƴan'uwan Malam Muhammadu guda uku ya sanar da du Mai Unguwa na kiran su,duk wanda ya tambaya akan me yasa ake kiran sa,ya ji cewar game da rashin Aminatu da aka yi ne sai ya zuƙe tare da faɗin.
"Allah Ya jiƙanta,muka rasa ubanta ma muka yi haƙuri balle ita? Yanzu uziri ne da ni a gabana,idan na dawo na samu lokaci zan zo har fadar na miƙa gaisuwata."
Haka Malam Haladu ya gama karaɗe kaf dangin Malam Muhammad ba a sami guda ɗaya da ya bi shi zuwa wajen mai gari ba,Delu kuwa da ta samu labari sai ta kada baki ta ce.
"Ai ni dama na zare Aminee a cikin zuri'ar gidan nan,tunda aka nuna min iko akan ta,to me ya sa za a zo ana faɗa min rasuwar ta? Ni kaina yanzu abar a jajanta min ce tunda ban san inda ɗana Hamzah yake ba shekara da shekaru."
Kafin Delu ta koma cikin gida jikarta Sajidah ta dawo hannunta riƙe da bokitin talla,fuskar nan ta sha kwalliya raɗau kamar me shirin zuwa biki,sai taunar chewing gum take yi tana ƙwai tare da fari,ko gaishe da Malam Haladu bata yi ba ta wuce buguzum-buguzum cikin gidan tana waƙe-waƙen batsa a bakinta. Girgiza kai Malam Haladu ya yi jiki a matuƙar mace ya koma fada,Mai unguwa da mutanen wajen sai kallon bayansa suke yi amma basu ga kowa na biye da shi ba,cike da damuwa Malam Haladu ya fashe da kuka,sai da ya yi mai isar sa sannan ya labartawa mutane abinda ya faru,cike da matsananciyar damuwa Mus'ab da Aminullahi suke kallon mutanen wajen. Hankali a tashe Aminullahi ya ce.
"Waɗannan waɗanne irin mutane ne haka? Anya akwai ɗigon imani a zuƙatan su kuwa? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,Abii idan Lamyah ta zo nan kana ganin za su karɓe ta ma kuwa?"
Ajiyar zuciya Mus'ab ya sauke mai ƙarfi,cike da damuwa ya ce.
"Na so ace mun same ta anan mu ɗauke ta mu koma da ita wajen Momman ku,sai dai kashh bata zo nan ɗin ba,ina kuma fatan Allah kar ya sa ta iso wajen waɗannan mutanen da babu ɗigon imani a ƙirazan su."
Nan da nan fada ta gauraye da labarai marasa daɗi akan zuri'ar,wanda suka sake ɗaga hankalin Mus'ab da Aminullahi,lallai Malam Muhammadu ne kaɗai ya fito a mutumin kirki a cikin su in dai haka suke. Mai gari ne ya nisa ya ce.
"Yanzu haka tsabar shaye-shaye ba a san inda Hamzah ya nausa ba,dan kuwa shi ko auren fari be yi ba ya fara ɗauke-ɗauke da haura gidajen mutane kwartanci,idan aka kai wa uwar ƙara sai ta tsani mutum ta shiga ta fita gidan bokaye ta yiwa mutum mummunan sihiri. Shi kuma Habibu da ake tinanin shine na Allah'n tinda ya yi aure har ya haihu kafin matar ta gudu ta bar gidan saboda baƙin halin Delu, watan can da ya gabata aka gano fyaɗen da ake yiwa kananan yara mata da maza ashe duk shi ne,to ka ga fisabillahi ta ina za ka tsammaci ɗigon rahama a wajen waɗannan mutanen?"
Cike da jimanta lamarin Mus'ab da su Aminullahi suka yiwa mutanen Rijiyar lemo sallama suka koma gida. Nan da nan Mus'ab ya baza sanarwar neman su Lamyah,rashin hoton su da za a bayyana wa mutane ya kawo babban cikas a neman su. A haka Mus'ab ya share watanni biyu a kano ƙarshe Aminullahi ne ya lallaɓasa ya ce ya koma bakin aikinsa shi zai ci gaba da neman ta,ba dan ya so ba haka ya haƙura ya koma Niger ya koma bakin aikin sa, A'isha ta yi baƙin cikin rashin ganin Lamyah da ba a yi ba sosai,wanda har kokawa ta dinga yi tana addu'ar Allah Ya bayyana ta a duk inda take.
***********************
Yau ce rana ta farko da Lamyah ta shirya za ta bi Afrah hotel ɗin da take aiki,Faisal ya gwada ta ya gano idan ta fara rawa a wajen ba ƙananan kuɗaɗe zai samu ba,dan haka da kansa ya shiga kasuwa ya siyo musu sababbin kayan da za su yi amfani da shi,dan kuwa Lamyah bata da irin kayan da ake sakawa a je rawa da su,gaba ɗaya kayan ta dogayen riguna ne,sai ƙananan riguna na zaman gida da dogayen wanduna.
Bala baya son Lamyah ta faɗa wannan harkar ta rawa,amma bashi da iko ko ƴancin hanawa tinda a ƙarƙashin ta suke,sai dai ya bata shawara,amma masoyiyarsa Afrah ta ture shawarar ta hanyar sanar da shi,itama Lamyah na da ra'ayin yin rawa tin kafin zuwanta Nigeria,dan kuwa iyayenta har wajen koyon rawa suka saka ta ta samo satifiket. Da wannan maganar ta ɗinke bakinsa har ya ɗauke su ya kai su Hotel ɗin da kansa,a bakin ƙofar shiga club ya ajiye su. A waje suka tarar da Faisal yana ta kaiwa da komowa yana jiran zuwan su,ya na ganin Lamyah ya washe baki sosai,jiki na rawa ya isa gare su ya ce.
"Sannun ki da zuwa sarauniyar kyau."
Hararar sa Afrah ta yi kafin ta ce.
"Matsala ta da ɗan bariki butulci,mu kuma da muni ya yiwa yawa sai a nemi bolar zubar da mu a watsa."
Dariya sosai Bala ya yi kafin ya yi musu sallama ya tafi dan yana so ya yi karatun exam da ta ke tunkarar sa. Haƙuri Faisal ya bawa Afrah sannan suka shiga ɗakin kwalliya dan su gyara jikin su su sauya kaya kafin lokacin hawan su stage ya yi........
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 19.
Kayan da suka tarar a ajiye sun kashewa Lamyah jiki har dai ta gaji da jujjuya su a hannunta ta kalli Afrah dake murnar ganin kayan ta ce.
"Sister yanzu sai mu saka kayan nan mu fita gaban mutane mu yi rawa? Kar ki manta fa maza ne a wajen bana jin akwai mata ƴan'uwan mu."
"Kin ga My sister rintse ido za mu yi mu bawa zuciyarmu abinda take muradi,ai ba dawwama za mu yi da su a jikin mu ba,ga wannan ƙyallen da shi za ki rufe fuskar ki daga hancin ki zuwa bakin ki,idan ki ka yi haka wa zai san ke ce? Babu kuma wanda zai gane ki ko bayan mun bar nan."
Kallon wani ƙyalle Lamyah tayi wanda yake shara-shara ruwan zinare,sai walwali yake yi,ganin suna ɓata lokaci ne ya sanya Afrah soma saka kayanta,Lamyah ma bata sake yin musu ba ta sauya nata,da kallo Afrah ta bita ta na zabga uban murmushi,cike da farin ciki ta ce.
"Dole ne mu samo manyan kuɗi yau Sister."
"Kema kin san i am not after the money,ina so kawai na cika burin dake cikin zuciyata ne na zamowa ƳAR RAWA tun ina ƙarama."
"Ni kam kuɗin nake so,dan haka mu jeee."
Afrah ta faɗa ta na ƙarasa gyara skirt ɗin jikinta da ke da wata muguwar tsaga,dika-dika rigar jikin su da kaɗan ta wuce ƙirjin su,sai wani skirt mai baza da wasu stones masu walwali golden color a jiki,dogon takalmin da ke ƙafafun su ne ya ƙarawa kwalliyar tasu kyau,suna fita karuwai da ƴan daudun dake jin mugun takaicin su sai suka bi Lamyah da kallo baki sake,duk wata hassada da baƙin cikin da suke ji akan su sai ya sake fitowa fili,nan da nan wasu suka hau tsaki tare da harar su har suka wuce stage,waƙar india ta LAILAH aka saka,babu ɓata lokaci Lamyah da Afrah suka fara takawa suna juya jikin su kamar waɗanda aka haifa a teku,wata iriyar rawa suke yi kamar babu ƙashi a jikin su,banda ihu da shewar matasa tare da manyan alhazawan dake wajen babu abinda ke tashi. Faisal kuwa tini ya fara jin manyan kuɗi na shiga account ɗinsa mutane na ta yin kamun Lamyah da Afrah,babu ɓata lokaci yake sanar da su su ɗin ƳAN RAWA ne kawai ba karuwanci suka fito yi ba,wasu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 30