Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya sa ta ƙi sakin hannun Layuzah. Da sauri Layuzah ta zube a saman guiwowinta ta na kuka ta ce. "Don girman Allah mahaliccin ki mahaliccin iyayenki ki sakar mini hannu,wayyoo Allah kin mini targaɗe, wataƙila ma karyewa yatsuna suka yi." "Zan sakar maki hannu,amma da sharaɗi..." Kafin Lamyah ta ƙarasa maganar ta Layuzah ta ce. "Na amince koma wanne irin sharaɗi gare ki na bi,dan Allah Yayata ki sakar min hannu fitsari nake ji." Murmushin mugunta Lamyah ta saki kafin ta haɗe fuskarta ta ce. "Sharaɗi na shine,daga yau sai yau,kar ki kuskura gigin hauka ya sanya ki ki sake tinkara ta da faɗa,domin ni ba karya bace,zaman ibada na zo yi ba zaman hauka ba,kin ji ko ba ki ji ba mu kwana a haka?" "Na rantse da kabarin babana na yarda,don Allah dan iyayen ki ki sakar min yatsu." Sakin hannunta Lamyah ta yi ta na faɗin. "Jahilar banza kawai,ko wa ya faɗa maki ana rantsuwa da wani bayan Allah?" Da ɗingisa ƙafa Layuzah ta bar ɗakin,kai ka ce a ƙafa aka ji mata ciwo,Aminullahi kuwa da sauri ya mara mata baya kamar wani soko,cikin sauri ya kama Layuzah don ya taimaka mata su shiga ɗaki,a harzuƙe ta juya ta kai masa duka da hannunta mai lafiya a ƙirji,wani irin gunjin kuka ta saki sannan ta buɗe ƙofar ɗakinta ta faɗa ta rufe da ƙarfi,tsaye Aminullahi ya yi yana nazarin shin ya shiga ne ko ya tsaya? Ganin bashi da zaɓin da ya wuce na ya barta ne ya sanya shi juyawa ɗakinsa ya rufe kofa,hannunsa da ta ciza har jini ya fara fita ,yarfewa ya yi ya ɗauki spirit ya shafa a wajen,rintse idonsa ya yi yana jin azabar zafi na ratsa shi,a bakin gado ya zauna ya na maida numfashi,a hankali ya furta. "Na shiga uku ni Aminullahi,Allah ka shiga lamura na." Yana nan zaune bacci ya fara fizgarsa sai kawai ya cire takalminsa ya gyara kwanciyarsa babu ko addu'ar bacci. A can ɗakin Lamyah kuwa suna fita ta zauna daɓas a bakin gado ta hau share hawaye,zufar da ke gangaro mata ta goge sannan ta hau matsa hannunta,ta tabbata sai ya yi mata ciwo itama. Ganin zaman ba zai kai ta ko ina ba ne ya sanya ta miƙe wa ta shiga banɗaki,kayanta ta cire ta hau wanka,ta na gamawa ta ɗaura alwala sannan ta fito ɗaure da towel,wajen kayanta ta buɗe ta zaro wata doguwar rigar bacci mai siririn hannu ta sanya,roll on ta fara shafawa sannan ta feshe jikinta da turaruka masu daɗin ƙamshi.Hamibrah face oil ta shafa sannan ta shafa skin oil ɗin,sai ta ɗauki Hair oil ta shafa a ƙasan gashinta da bakin robar,ta na gamawa ta murza sosai ta taje kan ta ɗaure,wata iriyar ni'ima ce ke shigarta bayan ta gama. Abun sallah ta ja ta ɗakko hijabi tana sakawa ta na gode wa Momma da ta siya mata product ɗin HAMIBRAH (09031416423)domin gyaran jikinta Sai da ta yi sallolin ta ta ɗora da addu'o'in da ta saba yi,tare da addu'ar neman zaman lafiya a tsakanin su baki ɗaya sannan ta tashi ta ninke hijabin da abun sallar ta ajiye a saman ƙaramin table ɗin da ta ɗauke su. Rufe ƙofar ɗakin ta yi da makullin dake jiki sannan ta kashe fitila ta zauna a bakin gado, addu'ar bacci ta yi ta shafe jikinta sannan ta kwanta a hannun damanta bakinta na karanto ƙulhuwallahu ahad,bata samu bacci ba har sai da ta yi goma sannan ta ɗora da tasbihi ga Allah,a haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta,ko tinanin angon nata bata yi ba ballantana ta saka ran ma zai zo gare ta. Layuzah kuwa da alwashin ganin bayan Lamyah ta kwanta bayan ta shiga bayi ta gasa yatsunta da suka kumbura,idonta ɗaya da jini ya kwanta tare da yatsun Aminullahi da suka yi mata zanen goburawa a kunci kuwa da ta kalla sai ta fashe da kuka. Tinda take a rayuwarta babu wanda ya taɓa dukan ta,sai gashi a dare ɗaya mijin da take taƙama da tutiyar ta mallaka ya sharara mata mari,lallai sai ta miƙe tsaye sosai kamar yanda bokanta ya ce mata,idan ba haka ba kuwa lallai ta na ji ta na gani Lamyah za ta raba ta da farincikinta. Washegari da asuba Lamyah na idar da sallah ta gyara ɗakinta ta kwashe kwalaben da bata kwashe ba a jiyan sannan ta saka turaren wuta ta jona,nan da nan ɗakin ya cika da ƙamshi mai sanyaya rai,wanka ta shiga ta tsala sannan ta shafa mai,ita da kanta take kallon madubi saboda yanda kalarta ta fito ta yi kyau,ita ba baƙa ba kuma ita ba fara sosai ba,ga wani irin laushi da santsi tare da sheƙi da take yi,murmushi ta sakarwa kanta ta tsara simple make up sannan ta sanya atampa riga da skirt masu kyau ta kafe ɗauri,parlour ta fito ta ga gidan shiru babu wanda ya fito, kyaɓe baki ta yi ta share kitchen ɗin dan kuwa da alama matar gidan a jiya ta dafa indomie ga ledar nan da ɓawon ƙwai an bari. Ta na gamawa ta hau haɗa abun karyawa,nan take ƙamshi ya game ko ina na gidan. Kamar a mafarki Aminullahi ya ji wani irin ƙamshi mai daɗi na ratsa ɗakin nasa,ƙamshin turaren wuta da na suyar wani abu wanda ba zai iya tantance menene ba,tinda ya auri Layuzah bai taɓa jin irin ƙamshin nan ba a gidan,cikin sauri ya miƙe ya faɗa banɗaki,alwala ya yi ya wanke bakinsa sannan ya fito ya tada sallah,ya na idarwa ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya fito parlourn,ƙamshin da yake ji ne ya ƙaru,nan take yawun bakinsa ya tsinke,a hankali ya taka ya isa kitchen ɗin,tsaye ya tarar da ita ta juya baya tana aikin ta tare da taka rawa a hankali,cike da nishaɗi take bin waƙar da ta kunna a wayarta ta larabci,ya shagala sosai da kallon ta ta juya hannunta riƙe da plate ɗin da ta ɗora abinci akai,ganinsa tsaye ya na ƙarewa bayanta kallo ne ya razana ta,ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi sannan ta ce. "Yah Amee ka tsorata niii." Yanda ta faɗi sunan sa a shagwaɓe ne ya tina masa da rayuwarsu ta baya,cike da shagala ya sakar mata murmushin da bai shirya ba,muryar Layuzah ce ta katse masa hanzari,a ɗan firgice ya juya ya kalli fuskarta da ta yi haushi musamman ta gefen idanunta,ga hannunta da ta riƙe ta na tsiyayar da hawaye,cikin kuka ta ce. "Ina can ina fama da zogi da azaba kana nan ka shagala a wajen amaryarka,ka duba marin da ka yi min yanda ya so nakasa min ido,hannuna kuwa da dikkan alamu sai an duba min shi." Kuka ta sake fashewa da shi,wanda ko kaɗan bai bawa Lamyah tausayi ba,ai so ta yi ita ta nakasa ta a daren ta na farko a gidan miji, ba a barta ta mori auren ba sannan a haɗa ta da jinya,don haka ko ci kanki bata ce ba ta gegare su ta wuce ɗakinta ta na juya manyan mazaunanta da ke shagaltar da Aminullahi. Tsakin da Layuzah ta ja ne ya maida shi cikin hayyacinsa har ya kama ta suka koma ɗakinta ya taya ta sauya kaya suka ɗauki makullin mota suka bar gidan. Lamyah kuwa ta na gama cin abincinta ta fito ta wanke abubuwan da ta ɓata ta gyara wajen sannan ta zauna a parlour ta kunna kallo. Bata jima da zama ba ta ji ana buga ƙofa,izinin shiga ta bayar sai ta ga Zahrah da Afrah da Mubarak,da gudu ta isa wajen su ta rungume Afrah da Mubarak,sannu da zuwa ta yi musu sannan ta kalli Zahrah da ke ɗauke da kayan abinci ta na neman inda za ta ajiye su ta ce. "Aje su a saman dinning table. Gaskiya na ji daɗin zuwan ku sosai,dama ina zaune ni kaɗai kamar mayya ina tinanin ku sai ga ku. Mubarak anya ka yi kewa ta kuwa na ga har wani kumatu ka yi a dare ɗaya." Dariya suka sanya,shi kuwa ya sake lafewa a jikinta ya na murmushin jin daɗi. Hira suka dinga yi har Zahrah ta na basu labarin wacece Layuzah da mahaifiyarta,sai dai har a wannan lokacin Hajiya A'isha bata gano su ba,shi yasa bata ganin laifin Layuzah,jinjina kai Afrah ta yi sannan ta ce. "Allah sarki Iya,ashe shi yasa ta dage da baki shawarwari akan ki riƙe wa addu'o'i wuta banda wasa,ni kaina na koyi abubuwa da dama a abinda ta koya miki,babu wata shawara da zan baki da ta wuce abinda Iya ta koyar dake,don haka tin yanzu za ki fara aikin ki,maza Zahrah ɗakko juice ɗin can ki kawo min ki gani." Ana kawo wa Afrah babban jug ɗin juice ɗin da Zahrah ce ta haɗa shi da kanta sai ta kafa kai a bakin jug ɗin ta hau karanto ayoyin ruƙya kamar haka. *• «بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ * الْحَمْدُ للّهِ رَبّ الْعَالَمِينَ * الرّحْمنِ الرّحِيمِ * مَلِكِ يَوْمِ الدّينِ * إِيّاكَ نَعْبُدُ وإِيّاكَ نَسْتَعِينُ * اهْدِنَا الصّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ * صِرَاطَ الّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِم وَلاَ الضّآلّينَ »* *• « الَمَ * ذَلِكَ الْكِتَابُ لاَ رَيْبَ فِيهِ هُدًى لّلْمُتّقِين * الّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصّلاةَ وَممّا رَزَقْنَاهُمْ يُنْفِقُونَ * والّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَآ أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَآ أُنْزِلَ مِن قَبْلِكَ وَبِالاَخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ * أُوْلَئِكَ عَلَىَ هُدًى مّن رّبّهِمْ وَأُوْلَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ ».* *• «اللّهُ لاَ إِلَهَ إِلاّ هُوَ الْحَيّ الْقَيّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لّهُ مَا فِي السّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأرْضِ مَن ذَا الّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مّنْ عِلْمِهِ إِلاّ بِمَا شَآءَ وَسِعَ كُرْسِيّهُ السّمَاوَاتِ وَالأرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيّ الْعَظِيمُ * لاَ إِكْرَاهَ فِي الدّينِ قَد تّبَيّنَ الرّشْدُ مِنَ الْغَيّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطّاغُوتِ وَيْؤْمِن بِاللّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَىَ لاَ انفِصَامَ لَهَا وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ * اللّهُ وَلِيّ الّذِينَ آمَنُواْ يُخْرِجُهُمْ مّنَ الظّلُمَاتِ إِلَى النّورِ وَالّذِينَ كَفَرُوَاْ أَوْلِيَآؤُهُمُ الطّاغُوتُ يُخْرِجُونَهُمْ مّنَ النّورِ إِلَى الظّلُمَاتِ أُوْلَئِكَ أَصْحَابُ النّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ » [البقرة: 255-258].* *• «يَكَادُ الْبَرْقُ يَخْطَفُ أَبْصَارَهُمْ كُلَّمَا أَضَاءَ لَهُم مَّشَوْا فِيهِ وَإِذَا أَظْلَمَ عَلَيْهِمْ قَامُوا وَلَوْ شَاءَ اللَّـهُ لَذَهَبَ بِسَمْعِهِمْ وَأَبْصَارِهِمْ إِنَّ اللَّـهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ».* *• «وَاتّبَعُواْ مَا تَتْلُواْ الشّيَاطِينُ عَلَىَ مُلْكِ سُلَيْمَانَ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَكِنّ الشّيْاطِينَ كَفَرُواْ يُعَلّمُونَ النّاسَ السّحْرَ وَمَآ أُنْزِلَ عَلَى الْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَارُوتَ وَمَارُوتَ وَمَا يُعَلّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتّىَ يَقُولاَ إِنّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلاَ تَكْفُرْ فَيَتَعَلّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرّقُونَ بِهِ بَيْنَ الْمَرْءِ وَزَوْجِهِ وَمَا هُم بِضَآرّينَ بِهِ مِنْ أَحَدٍ إِلاّ بِإِذْنِ اللّهِ وَيَتَعَلّمُونَ مَا يَضُرّهُمْ وَلاَ يَنفَعُهُمْ وَلَقَدْ عَلِمُواْ لَمَنِ اشْتَرَاهُ مَا لَهُ فِي الاَخِرَةِ مِنْ خَلاَقٍ وَلَبِئْسَ مَا شَرَوْاْ بِهِ أَنْفُسَهُمْ لَوْ كَانُواْ يَعْلَمُونَ» [البقرة :102].* *• « وَأَوْحَيْنَآ إِلَىَ مُوسَىَ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ * فَوَقَعَ الْحَقّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ * فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَانقَلَبُواْ صَاغِرِينَ * وَأُلْقِيَ السّحَرَةُ سَاجِدِينَ * قَالُوَاْ آمَنّا بِرَبّ الْعَالَمِينَ * رَبّ مُوسَىَ وَهَارُونَ » [الأعراف:117 –122].* *• « وَقَالَ فِرْعَوْنُ ائْتُونِي بِكُلّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ * فَلَمّا جَآءَ السّحَرَةُ قَالَ لَهُمْ مّوسَىَ أَلْقُواْ مَآ أَنتُمْ مّلْقُونَ * فَلَمّآ أَلْقُواْ قَالَ مُوسَىَ مَا جِئْتُمْ بِهِ السّحْرُ إِنّ اللّهَ سَيُبْطِلُهُ إِنّ اللّهَ لاَ يُصْلِحُ عَمَلَ الْمُفْسِدِينَ * وَيُحِقّ اللّهُ الْحَقّ بِكَلِمَاتِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْمُجْرِمُونَ » [يونس:79-81]* *• « قَالُواْ يَمُوسَىَ إِمّآ أَن تُلْقِيَ وَإِمّآ أَن نّكُونَ أَوّلَ مَنْ أَلْقَىَ * قَالَ بَلْ أَلْقُواْ فَإِذَا حِبَالُهُمْ وَعِصِيّهُمْ يُخَيّلُ إِلَيْهِ مِن سِحْرِهِمْ أَنّهَا تَسْعَىَ * فَأَوْجَسَ فِي نَفْسِهِ خِيفَةً مّوسَىَ* قُلْنَا لاَ تَخَفْ إِنّكَ أَنتَ الأعْلَىَ * وَأَلْقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلْقَفْ مَا صَنَعُوَاْ إِنّمَا صَنَعُواْ كَيْدُ سَاحِرٍ وَلاَ يُفْلِحُ السّاحِرُ حَيْثُ أَتَىَ » [طه:65-69].* *• « قُلْ هُوَ اللّهُ أَحَدٌ * اللّهُ الصّمَدُ * لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ * وَلَمْ يَكُنْ لّهُ كُفُوًا أَحَدٌ » سورة الإخلاص.* *• « قُلْ أَعُوذُ بِرَبّ الْفَلَقِ * مِن شَرّ مَا خَلَقَ * وَمِن شَرّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ * وَمِن شَرّ النّفّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ * وَمِن شَرّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ» سورة الفلق.* *• « قُلْ أَعُوذُ بِرَبّ النّاسِ * مَلِكِ النّاسِ * إِلَهِ النّاسِ * مِن شَرّ الْوَسْوَاسِ الْخَنّاسِ * الّذِى يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النّاسِ * مِنَ الْجِنّةِ وَالنّاسِ »* *• «مَّا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَلَا الْمُشْرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْكُم مِّنْ خَيْرٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَاللَّـهُ يَخْتَصُّ بِرَحْمَتِهِ مَن يَشَاءُ وَاللَّـهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ».* *• «وَدَّ كَثِيرٌ مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَوْ يَرُدُّونَكُم مِّن بَعْدِ إِيمَانِكُمْ كُفَّارًا حَسَدًا مِّنْ عِندِ أَنفُسِهِم مِّن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ الْحَقُّ فَاعْفُوا وَاصْفَحُوا حَتَّىٰ يَأْتِيَ اللَّـهُ بِأَمْرِهِ إِنَّ اللَّـهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ».* *• «فَإِنْ آمَنُوا بِمِثْلِ مَا آمَنتُم بِهِ فَقَدِ اهْتَدَوا وَّإِن تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا هُمْ فِي شِقَاقٍ فَسَيَكْفِيكَهُمُ اللَّـهُ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ*صِبْغَةَ اللَّـهِ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّـهِ صِبْغَةً وَنَحْنُ لَهُ عَابِدُونَ».* *• «وَإِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَاحِدٌ لَّا إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ الرَّحْمَـٰنُ الرَّحِيمُ*إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَالْفُلْكِ الَّتِي تَجْرِي فِي الْبَحْرِ بِمَا يَنفَعُ النَّاسَ وَمَا أَنزَلَ اللَّـهُ مِنَ السَّمَاءِ مِن مَّاءٍ فَأَحْيَا بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَابَّةٍ وَتَصْرِيفِ الرِّيَاحِ وَالسَّحَابِ الْمُسَخَّرِ بَيْنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ».* *• «آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّـهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ*لَا يُكَلِّفُ اللَّـهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنتَ مَوْلَانَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ».* *• «قُلِ اللَّـهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَن تَشَاءُ وَتَنزِعُ الْمُلْكَ مِمَّن تَشَاءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَاءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَاءُ بِيَدِكَ الْخَيْرُ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ*تُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَتُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَتُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَتُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَتَرْزُقُ مَن تَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ». Afrah na kammalawa ta miƙa wa Zahrah ta mayar sannan ta kalli Lamyah ta ce. "Haka za ki dinga yi kullum,ko a ruwan shan sa,ko a abincinsa ko a ruwan da za ki yi girki,ki dinga ayoyin ruƙya ciki,ko ki karanta Fatiha x7,Iklas x7,Falaƙi x7,Nasi x7. Ko uku-uku ma za ki iya yi,abinda ake so kawai shi ne,ki yi da kyakkyawar niyya da imani tare da yaƙinin Allah zai amsa komai daren daɗewa. Wannan shawarar da Iya ta baki kar ki sake ki yi wasa da ita,domin ni kaina na fara yarda bayan wulaƙacin Handsome akwai surkulle a kan sa. Suna nan suna hira Aimanah ta zo itama,sai Zahrah ta yi musu sallama ta koma gida. Hira suka dinga yi ƙarshe dai Lamyah ta shiga ɗaki ta sauya kayan jikinta ta na mitar sun yi mata nauyi. Kayan da Afrah ta yo mata tsarabar su ta saka ta fito,ihu su Afrah da Aimanah suka sanya suna yabon kyan da kayan suka yi mata. Ana haka Zee cinema suka sako waƙar india zazzafa,nan take Afrah ta yi wurgi da after dress ɗinta ta miƙe ta kama hannun Lamyah ta ce. "Ƴar'uwa taho mu tina baya." Noƙe kafaɗa Lamyah ta yi sannan ta ce. "Kin manta wa'azin Iya ko? Ta ce a haƙura da RAWA da waƙa babu kyau,sannan idan ina yawan jin su a koda yaushe addu'o'in da nake yi ma ba za su karɓu ba,domin shaiɗanun aljanu da mala'iku ba za su yi gogayya a waje guda ba,dole ne ɗaya ya tafi ya bar ɗaya." "Hakane kuma,Allah mun tuba ka yafe mu,rawa da waƙar ne Lamyah akwai daɗi,sai an jure,yanzu haka ji na nake kamar na haukace idan ban taka ba." Aimahan ce ta ce. "Ni ma zan so na ga irin rawar da kuke yi a baya,don Allah ku yi mana ko kaɗan ne." Da surutu tare da daɗin baki su Afrah suka ja ra'ayin Lamyah ta hau yin rawa kamar wata macijiya,yanda take lanƙwasa jikinta fatarta da ta sha gyara tana walƙiya da ɗaukan ido ma kawai abun burgewa ne,suna can sun shagala da rawar da suke yi su Aminullahi suka dawo,hannunsa riƙe da ledar magunguna,Layuzah an shafe mata hannu da magani sai ajiyar zuciya take yi,da dikkan alamu jan yatsan aka yi ta ci kuka ta gode Allah. Tsayawa Aminullahi ya yi ya saki baki ya na kallon yanda Lamyah ke karkaɗa ƙugu rigar ta na ɗagawa cikinta na buɗewa,idan ta girgiza ƙirjinta sai ta yi baya kamar za ta kwanta sai ta ɗago,gashin nan sai yarari yake yi kamar ba nata ba. Aimanah ce ta kula da yanda Layuzah da Aminullahi ke kallon Lamyah,sai ta yi shiru ta ƙi yin magana,Layuzah na tsaye kishi kamar zai fasa mata zuciya,cikin jin haushi ta isa wajen makashin talabijin ɗin ta kashe,shirun da su Lamyah suka ji ne babu kiɗan ya sanya su kallon juna suna maida numfashi suna dariya,Afrah ce ta ce. "Shegu ƴan wuta sun ɗauke abarsu." A hasale Layuzah ta ce. "Ko kuma masu gidan suka kashe kayan dujal ba,ke malama wa kike da suna? Ki ja tarkacen ƙawayen ki ku koma can ɗakin ki ku yi haukan naku,dan ba za ku zo cikin gidana ku dinga yi min hauka ba." Dariya Lamyah ta ƙunshe sannan ta kai hannu za ta taɓa fuskar Layuzah,a gigice Layuzah ta yi bayan Aminullahi ta na faɗin. "Kar ki sake ki taɓa ni azzaluma kawai,ku tattara ku bar min parlour matsiyatan banza." Afrah ce ta ce. "To kujerun na uban ki ne da za mu tattara mu bar maki parlourn? Ko uwar ki ce ta siyo ta zuba miki su?" Lamyah ce ta yi saurin riƙo Afrah da ke tsalle kamar za ta kai duka ta ce. "Yi haƙuri kar ki karasa gawar da ba taki ba,mu je ɗaki na anjima mu fito mu ci abinci dan na fara jin yunwa." Yawu Layuzah ta haɗiya da ta ji kalmar abinci,dan kuwa wata matsiyaciyar yunwa ta dawo da ita,shi kanshi uban gayyar yunwa yake ji,sai dai ganin Lamyah tana rawa ko ina na motsawa ya girgiza duniyarsa,bai san hankalinsa baya jikinsa ba sai da ya ga ta juya ita da su Afrah za su bar parlourn,kafe bayanta ya yi da ido,ita kuwa kamar ta san ya na kallon ta ta sake narkewa ta na kaɗa jiki suka shige ɗakin ta. Layuzah kuwa saman dinning ta wuce ta zauna,a shagwaɓe ta kalli Aminullahi da ke haɗiyar yawu idanunsa sun kaɗa sun yi jawur ta ce. "Baby ka zo ka bani abinci yunwa nake jii." Haɗiye wani abu ya yi mai ƙarfi kafin ya fara takawa zuwa inda take kamar wani ɗan maye,zama ya yi ya buɗe abincin sai ya ji sam bai masa ba,saboda ba shi ya ga Lamyah ta yi ba, wannan da gani daga gida aka kawo. Jiki babu ƙwari ya hau zuba wa Layuzah ya na bata,ita kuwa wage baki ta yi ta ci ta ƙoshi ta kora da juice,ta na gamawa ta saki wata ƙatuwar gyatsa sannan ta miƙe ta wuce ɗakinta ba tare da ta damu da ya ci ko be ci ba. Yunwar da ta addabe sa ce ta sanya shi zuba abincin kaɗan ya fara ci,ya na gamawa ya hau shan juice, daɗin da ya yi masa ne ya sanya shi ɗaukan jug ɗin ya koma parlour ya zauna saitin ƙofar Lamyah,ta yanda ta na buɗe wa za su haɗa idanu,a hankali ya ke shan juice ɗin ya na lumshe idanuwa, gajiya ya yi da jiran tsammani sai ya tashi ya shiga ɗakinsa ya kwanta yana kallon sama,siffar jikin Lamyah ce ke yi masa gizo,a hankali ya furta. "Ga mace iya mace,sai dai ta gama rabawa mazan waje jikin nata gaba ɗaya. Mtsssww Allah ka tsare ni kai kaina ga hallaka." Su Lamyah kuwa basu fito ba sai da suka yi sallar azahar,sallama Afrah ta yi mata suka tafi gida. Lamyah kuwa suna tafiya ta yi murmushi domin ta shirya fito na fito da Layuzah akan Aminullahi,fatan ta ta samu nasarar samun soyayyarsa ba tare da ta wahala ba. *Wanne fata za ku yi wa Lamyahn ku? Don Allah kar ku manta ku zabga min addu'a Allah Ya ƙara min lafiya da dikkan musulmi.* [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 38. DUBAI. Babban parlour ne wanda ya sha shimfiɗu na alfarma,banda ƙamshin abinci da shayin gahwa tare da turaren wuta babu abinda ke tashi a parlourn. Kewaye suke a saman babban farantin da aka dafa shinkafa da banƙararren rago,cike da nishaɗi suke cin abincin nasu kamar basu da wata damuwa a duniya. Sun ɗauki tsawon awa guda su na cin abincin kafin su kammala kowa ya goge hannunsa da tissue,wasu karan sigari suka ɗakko suka hau kunnawa suna zuƙa,wasun su kuwa shisha suke busawa tare da yin hira sama-sama. Sun shagaltu da jin daɗin rayuwa suka ji ƙarar glass cup da spoon,hankalinsu suka tattare suka mayar wajen Noor wanda yake babban ɗa ne a wajen Baffan su El-mustapha. Sai da kowa ya nutsu ya bashi hankalinsa,sannan ya yi musu nuni da mazaunin Muhammad,hankalin su suka mayar wajensa gaba ɗaya. Cike da ƙasaita da izza ya ke kallon ƴan'uwan nasa kafin ya buɗe baki ya ce. "Kamar yanda kuka riga kuka sani,mun taru ne anan wajen saboda mu kawo ƙarshen abinda ke damun mu na shekara da shekaru. Sanin kan ku ne kafin mutuwar El-mustapha akwai ragowar dukiyarsa da bai bamu ba,wadda muna kyautata zaton ya damƙa ta ne a hannun yaransa sannan ya tura su Nigeria. Ni da El-Hassan da Hussein tare da Zaid mun yanke shawarar ƙwato dukiyarsa ta Nigeria mu dawo da ita ƙarƙashin kulawar mu,sannan mu ɗakko yaransa mu dawo da su cikin mu. Noor ya zo domin a yi wannan tafiyar da shi,idan da wanda yake da wata maganar ko wata shawara bismillah." Mutum uku ne suka ɗaga hannayen su,wanda tin a shekarun baya duk abinda ake yi basu taɓa saka baki ba,saboda yanda suke tsananin yi wa Muhammad biyayya,da kuma tsoron saɓa ra'ayi da shi ya illata su,cikin dakewa da ƙwarin guiwa Misbah ya ce. "A gaskiya wannan karon ma ni bana tare da shirin nan naku,ba dan komai ba sai dan na riga na san cewa dukiyar El-mustapha ba tawa bace mallakinsa da iyalansa ce,mu na da arziƙi daidai misali babu talaka a cikin mu,me ya sa za mu biye wa son zuciya mu dage sai mun raba yaransa da dukiyar da suka gada a wajen mahaifin su? Na zaci ma za ku ce a nemo su saboda mu riƙe su mu kula da rayuwarsu,amma sai..." Tsawa Muhammad ya daka wa mutum ukun nan da ke neman bijirewa shirin su da suka ɗauki lokaci mai tsawo suna yi. Rai a matuƙar ɓace ya ce. "Ku tashi ku tafi to tinda ku kun nuna babu ruwan ku a cikin shirin mu,sai dai ina mai gargaɗin ku akan buɗe baki ku yi surutun da zai zamo ajalin ku." Cikin rawar jiki suka tashi suka bar parlourn,su na fita su Zaid suka dinga zuga shi,shi kuwa sai hawa yake ta yi ya na nuna ɓacin ransa tare da cin alwashin cimma burin su akan su Lamyah da dukiyar da mahaifinsu ya bar musu. Bayan doguwar tattaunawa ne suka ware mutum uku a cikin su wato El-Hassan da Hussein da Zaid su ne za su je Nigeria domin nemo su Lamyah a duk inda suke. Sai dai kafin nan suna buƙatar sanin ina ne ma Nigerian da ɗan'uwan nasu ke yawan zuwa har ya auro ƴar ƙasar? **************************** Kwanan amarya Lamyah goma takwas a gidan Yah Amee ɗinta ko hanya bata sake haɗa ta da shi ba,domin kuwa Layuzah ta tsaya tsayin daka dan ganin babu wata alaƙa da ta ƙullu a tsakanin su ballantana ya bata kulawa a matsayinta na matarsa. Hannun Layuzah ya yi sauƙi sosai kamar babu abinda ya taɓa samunta a yatsun.Tsananin kishin Lamyah da take ji a ranta ke sanya ta jin kamar ta buɗe ido ta ji an ce yau wani mugun abun ya samu Lamyah ko kuma ta ma mutu gaba ɗaya. A cikin kwanakin nan kuwa Lamyah babu abinda take yi da ya wuce maida lamuranta zuwa ga Allah,tare da kewar Afrah da suka tafi da wuri,dan kuwa ta so ƙwarai su zauna su ɗan jima tinda har yanzu Bala bai fara zuwa kasuwar ba. Amma Abii ya goyi bayan su ya siya musu tikiti suka koma. Yau ma kamar ko da yaushe bayan ta kammala duk wani abu da ta saba yi da safe,sai ta shirya cikin riga mara nauyi,wadda take shara-shara da ta tsaya a iya cinyoyinta,babu abinda ta saka a ciki kasancewar an fara zafi sosai,gashin kanta ta raba biyu ta kitse saboda ta samu iska ta ratsa cikin kan nata. Wayarta ta riƙo ta na dannawa ta fito zuwa parlour dan ta shiga kitchen ta samawa kanta abinda za ta ci,lokaci ta kalla a wayarta ta ga ƙarfe sha biyu na rana,mamakin irin nannauyan baccin da ya ɗauketa bayan kammala sallar asuba ta yi. A haka ta

Chapter 23 of 30