Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dinga godiya sosai,Malam Abubakar ne ya yi musu jagora suka shiga mota suka nufi gidan su Aminee,suna isa suka tarar da su Lado a bakin ƙofa domin kuwa zuwan su kenan ko sallamawa ba su yi ba, ɗauke kai suka yi daga barin kallon su El-mustapha suna ta wani cin magani,Malam Abubakar bai bi ta kansu ba ya kwaɗa sallama ya na kiran Aminee. Aminee dake bakin rijiya ta na jan ruwa tana jiyo muryar abokin Abbahnta sai ta ajiye guga a gefe ta zari hijabi ta fita waje,ta na zuwa sai ta yi turus ganin mutane da yawa a wajen,sallama ta yi musu sannan ta raɓe ta tsugunna a gefe,kafin wani a wajen ya ce wani abu,Delu ta fito tana yafa mayafin atampar da ta yayimo a jikin katanga,turus ta yi ganin mutane da yawa a tsaye a ƙofar gidan nata,cikin dafe ƙirji ta ce. "Kai Lado me zan gani haka? Kar dai ka ce min har an ɗaura?" Mere baki Lado ya yi kamar wata mace sannan ya ce. "Yo me za a fasa,mutuwa ko hisabi? Ai wannan ɗan anacen ya nace sai da aka ɗaura,gashi nan sadaki dubu talatin ya cake suna hannun Malam." Nan take Delu ta ɗora hannu a ka ta kurma uban ihu,sannan ta faɗi ƙasa ta tumu ta na faɗin. "Na shiga uku na lalace ni Delu,shi kenan kun tona min asiri a duniyar nan,yarinyar nan ita ce cina da shana a gidan nan,ita ke kula da jikin girmana,sannan amanarta Abbahnta ya bani,me yasa za ka min haka Malam? Ko da yake ai kai ɗin ma na san dalilin yarda a ɗaura wannan auren da ka yi,kwaɗayi ne da dogon buri ya kai ka da cin amanar abotarku." A tsawace Malam ya ce "Delu kar ki kawo min shirme a wanna karon ki yi zaton zan ƙyale ki,Matana sun jima suna sanar da ni yanda yarinyar nan take azabtuwa a hannunki,a kullum suka sanar da ni sai na basu haƙuri na ce musu watarana sai labari,to gashi lokaci ya yi da Aminee zata bar ƙarƙashin ki ta koma cin gashin kanta a gidan mijinta,dan haka ki kiyaye ni,yanzu ba da bace,babu auren abokina akan ki,kina yi min hauka zan yi maganin ki,shashasha kawai." Kallon Aminee da ke a takure kanta a ƙasa Malam ya yi,gani ya yi ta na ɗagowa ta na satar kallon kowa da ke wajen,da alama ta na so ta samu amsar tambayoyinta daga gare sune. Cikin sanyin murya Malam ya ce. "Ke Amineenee,duba nan ki gani,ki na son sa a matsayin mijin aure? Idan baki so dole ne na kashe auren a yanzun nan,ya tafi ba zan yarda a musguna miki ba." A kunyace Aminee ta saci kallon El-mustapha ta na murmushi,shi ɗin ma an yi sa'a ita yake kallo,yana fatan kar ta ƙi karɓar soyayyar sa,yana ganin murmushinta sai ya mayar mata da martani suka ƙurawa juna ido suna jifan juna da wani tsadadden kallo,hamdala Malam ya yi sannan ya ce. "To da alama fa malam El-mustapha an dace,dan haka sai ku wuce mu tafi,zata kwana a gidana,a duk sanda ka shirya ɗaukar matarka can za ka je ku tafi,dan haka mu je na nuna maka waje." Cike da farin ciki Malam ya saka Aminee a gaba bayan ta shiga ta kimtsa ta fito riƙe da wata jaka da kayanta ke ciki, kai tsaye suka wuce gidan Malam Abubakar,duk yanda El-mustapha ya so ya ɗan zanta da Aminee ƙi ta yi,ta wuce gida,shi kuwa Malam ya ce kar ya matsa mata,idan yana son ɗaukar matarsa ko gobe ya zo ya ɗauketa,dan haka Aminee na shiga gidan matan Malam guda biyu da suke ƙawayen Tabawa ne a baya suka tarbe ta suka hau yi mata gyaran amarya da kayayyakinmu na yau da gobe da muke da su a gidan kamar irin su,kurkur,lalle,zuma,madarar shanu, kabewa,da sauran su. Kafin dare Aminee ta fara yin kyau saboda wankan da aka yi mata mai kyau irin na amare,sannan aka shafe ta da haɗin lalle da kabewa da sauran haɗe-haɗen gyaran jiki,daga ƙarshe suka yi mata wanka da ruwan lalle har saida ya bushe a jikinta,uwar gidan Malam ta na yin man kwakwa na siyarwa,bata jima da yin sabon ba,sai ta zauna ta mulke wa Aminee jiki da shi,nan take fatar ta ta yi kyau kamar ta jima ana yi mata gyaran jiki. A can gidan El-mustapha kuwa tinda suka koma bai zauna ba,ƙoƙari ya dinga yi ya na aiwatar da duk wasu aikace-aikacen da ya san dole sai ya je da kansa,ya duba wajen kasuwancinsa,sannan ya leƙa makarantun da yake taimakawa,da kuma gidajen marayun da ya ga sun aiko takardar taimakon su gare shi. Wata ranar asabar da sassafe ya tashi da maganar tafiya Niger,nan take Mus'ab ya ji daɗi ya kama shi,cike da farin ciki ya ce. "Dama a ƙasarmu za ku zauna?" "Kwarai da gaske,ka fara shirin tarbar baƙuwa." A ranar Mus'ab ya yi waya ya sanar da matarsa Aisha za su zo da El-mustapha da amaryarsa. Ita da Iya mai aikinta ne suka yi jagoranci aka gyara gidan El-mustapha aka share,da kanta ta fara girka abinci kala-kala masu daɗi irin na mutanen Niger domin tarbon su. Da yamma El-mustapha ya je ya ɗauki matarsa suka wuce airport da Mus'ab. Suna isa motar drivern Mus'ab ne ya je ya ɗauke su ya kai su gidan El-mustapha kai tsaye. Aminee da bata taɓa barin garin kano ba sai gata a maƙociyar ƙasar Nigeria. Banda kalle-kalle babu abinda take yi,sosai ƙasar ta yi mata kyau tare da bata sha'awa. Mus'ab da kansa ya je gidansa ya kawo musu abincin da Aisha ta dafa wanda ba ƙaramin mamaki ya yi ba saboda yanda ya san halin Aisha da masifar son jiki da lalaci,hatta da ruwan sha idan yana so sai dai Iya ta kai masa ko sauran masu aikin gidan,ballantana kula da gida wannan bai taɓa zama aikinta ba tin farkon auren su,lokacin da ta samu cikin yaron su na farko wato Aminullah kuka ta dinga yi tana roƙon a cire cikin dan ba za ta iya wahalar rainon ciki ba balle kuma goyo,da ƙyar iyayenta da na Mus'ab suka shiga maganar ta haƙura ta bar cikin har ta haifi kyakkyawan buzun ɗanta Aminullah. Tinda ta haife shi rainonsa da duk wata kulawar yaron ta koma hannun Iya,shi yasa ya taso yana son Iya kamar ita ce ta haifesa,hakan kuwa bai taɓa damun Aisha ba,dan ita a wajenta hutu ne ta samu. Duk yanda Mus'ab ke nuna mata illar abinda take yi na ƙin jan yaronta a jiki bata ganewa,hasali ma gani take yi kamar ya daina sonta ne ɗansa kawai yake so da kuma kansa. Dole Mus'ab ya tattara ya zuba mata idanu dan ba zai iya da rikicin shatun nashi ba. Lokacin da Mus'ab ya kaiwa su El-mustapha abincin da Aisha ta dafa ya yi murna sosai tare da godiya mai yawa a garesu,masu aikin gidan El-mustapha maza ne suka shigar da abincin suka ajiye a inda ya dace da kowanne. Aminee na zaune a takure da lulluɓi El-mustapha ya koma ya zauna a kusa da ita ya ce. "Ki saki jikinki Rouh yau ki na a cikin gidan mijinki ne,duk abinda ki ke so shi za ki yi,sannan duk abinda ki ke so shi za ki ci,gobe idan Allah ya kaimu Iya zata zo ta nuna maki duk yanda ake amfani da kayayyakin kitchen da kuma duk wani abu da ya kamata ki sani,yanzu ki tashi mu je mu ci abinci sai mu watsa ruwa mu yi sallah mu kwanta ko?" Cike da jin nauyin El-mustapha Aminee ta gyaɗa masa kai a hankali,sannan ta buɗe siraran laɓɓanta ta ce. "Na gode,Allah Ya saka maka da alkhairi,Allah Ya jiƙan iyayenka." Ba ƙaramin daɗi addu'ar Aminee El-mustapha ya ji ba,ta tina masa da iyayensa da suka rasu,sannan ta tuna masa da ƴan'uwan sa da suka juya masa baya,ta tabbata yanzu bashi da kowa sai Aminee,dan haka cikin zuciyarsa ya yi alƙawarin kula da ita har ƙarshen numfashinsa,komai nasa nata ne. Cikin wani irin yanayin da ya shiga mara fassara ya kama hannunta ya ɗagata tsaye ya rungumeta,sun jima a haka kafin ya yi musu jagora su zauna su ci abinci,ya kula da yanda ta ƙi sakin jiki ta ci abinci sosai,dan haka da kansa ya dinga bata a baki har sai da ta ƙoshi. Suna gamawa El-mustapha ya gyara wajen ya maida sauran abincin cikin fridge sannan ya wuce ya fesa wanka,Aminee na zaune a bakin gado inda El-mustapha ya ajiye ta kafin ya shiga wanka,sai kalle-kalle take yi tana hamdala acikin zuciyarta. Ya na fitowa ta shiga itama ta yi wankan ta sauya kayan da ta ga ya ajiye mata a banɗakin,doguwar riga ce mai karan muski ruwan makuba,ba kaɗan ba ta yiwa Aminee kyau sai wani sheƙi take yi a cikinta,a haka ta fito yafe da ƙaton mayafi,a saman abun sallah ta tarar da shi bayansa wata sallayar ce,bata ɓata lokaci ba wajen zuwa ta hau abun sallar,kan El-mustapha na ƙasa tin kallon farko da ya yi mata bai sake kallonta ba har sai da suka idar da sallah suka yi addu'o'in su sannan ya jata jikinsa,kunya duk ta hana Aminee sakewa,a haka El-mustapha ya ɗaga ta ya tsaida ita a gabansa yana juyata,sai da ya gama kallon yanda doguwar rigar ta yi mata kyau a jikinta,ta fidda kowanne saƙo da lungu na jikinta sannan ya rungume ta,daga haka El-mustapha ya miƙa dogon hannunsa ya kashe fitilar ɗakin ya fara aikawa Aminee da saƙon da ta jima tana koyarwa a makarantar Islamiyya........ [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA RUBUTAWA: HAMIDAH SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAERH) PAGE 5: Washegari da safe El-mustapha sai nan-nan yake yi da Aminee yana bata kulawa ta musamman kamar ƙwan kazar bature. A ɓangaren Aminee kuwa duk wani motsin da za ta yi,yin shi take cikin raki da shagwaɓar da bata san ta na yi ba,hakan da take yi ba ƙaramin burge El-mustapha yake yi ba,sosai yake jin kansa a matsayin wata katanga,kuma majinginar da Aminee za ta jingina da shi ta samu jin daɗi da gushewar damuwa. Da misalin goma da rabi na safe Iya ta iso gidan riƙe da ƙullin kayan gyaran da Aisha ta bayar ta ce ta zo ta gyare Aminee da su. A parlour ta tarar da Aminee zaune, El-mustapha ya shiga kitchen yana haɗo mata abinda za ta ci bayan dogon baccin safen da suka yi. Aminee na ganin dattijuwar matar da ta yi sa'a da Tabawanta sai ta zube guiwowinta a ƙasa ta fara kwasar gaisuwa,Iya ma na ganin haka sai ta durƙusa suka hau gaishe-gaishe kamar surukan ƙauye a gona. El-mustapha na shigowa ya tarar da su a wannan yanayin,sai ya fashe da dariya,cikin zolaya ya ce. "Haba Iya,ke da ƴar ki me yasa zaki durƙusa mata haka? Amineena tashi ki zauna da kyau,kin san ba kya jin daɗin jikin ki bai kamata ki zauna haka ba." Cike da wata iriyar kunya Aminee ta sake sadda kanta ƙasa ta ƙi ɗagawa daga inda take,cikin ranta take ayyana. 'Na shiga uku,Allah yasa wannan dattijuwar bata gane me ya shiga tsakaninmu ba,Allah ka rufa min asiri.' Wani siririn hawaye ne ya gangaro a idanun Aminee dake duƙe kamar mai neman gafara,cikin sauri El-mustapha ya isa gareta ya ɗagata ya rungume a ƙirjinsa,kallon Iya yayi ya ce. "Ina mutumin naki na gan ki ke kaɗai?" Murmushi Iya ta saki har sai da haƙoranta suka bayyana,kafin ta ce. "Ai da ƙyar mu ka rabu da shi,tare da alƙawarin gobe zan koma na ɗakkosa mu dawo nan tare,Aminullahi ba dai rikici ba." "Ai kuwa yana da kyau ki cika alƙawarin ki,dan in ba haka ba damunta zai yi da kuka,ita kuwa ba ƙyale sa za ta yi ya dame ta ba duka zai sha." "Dole na ai na ɗakkosa goben In Shaa Allahu." "Allah Ya kai mu." Cikin dabara El-mustapha ya janye matarsa suka koma ɗaki,abinci ya bata a baki yana lallashinta, suna gama cin abinci ya fitar da kwanukan,ya koma ɗakin,zaune ya ganta ta rakuɓe a jikin gado ta na tunani,cikin sanyin jiki ya isa gabanta ya tsugunna ya kama hannayenta ya ce. "Dan Allah Rouh ki daina yawan tunani,ina son ki, kema kuma na tabbata ki na so na yanzu,ko dai ba kya so na?" Cikin sauri da jin kunya Aminee ta rufe fuskarta ta na dariya ƙasa-ƙasa,murmushi El-mustapha yayi cike da jin daɗi ya ce. "To kin ga ni? Dan haka ki daina ɓata min ran ki da tunanin duniya,tunani na kaɗai na yarda ki yi kin ji? Ina so da ni da ke mu riƙe juna amana,kar ki rabu dani komai wuya komai rintsi,bani da kowa a duniyar nan bayan ke,ke kaɗai ce dangi na tinda nawa basu da amfani a gare ni,ke kaɗai nake so,ki so ni kamar yanda nake sonki,mu zama masu tallafawa juna ta kowanne fanni a rayuwa,ki yi min alƙawari babu abinda zai raba mu har abada." Cike da murmushi Aminee ta kalle shi ido cikin ido ta ce. "Na yi maka alƙawari ba zan taɓa barin ka ba har abada,kai ne majinginar jin daɗin rayuwata,bani da kowa bani da komai,amma ka ɗauke ni ka bani kan ka da rayuwarka,to sun ishe ni zaman duniya,ina fata su zamo abokan rayuwata har a ƙiyama." Rungumeta El-mustapha yayi yana jin wata iriyar soyayyar Aminee na shiga cikin ruhi da ɓargon ƙashinsa,ji yake yi kamar ya maida ita cikin jikinsa ta zauna daram. Wasanni ya fara yi da sassan jikinta wanda suka haifar mata da wani irin tsoro saboda tunawa da daren jiya da ta yi, El-mustapha bai kula da yanayinta ba saboda gushewar nasa hankalin har sai da ya gama cimma burinsa akanta,a matuƙar gajiye Aminee take fitar da numfashi cike da wahala da azabar da ta ke ji a jikinta,kallonta El-mustapha yayi ya na shafar fuskarta,albarka ya sanya mata kamar yanda yayi a daren jiya,cike da kulawa ya jata jikinsa ya rungumeta,hawayen azaba Aminee take fitarwa El-mustapha na aikin rarrashi. Suna nan kwance suka ji Iya na ƙwanƙwasa musu ƙofa tare da yin sallama,a gajiye El-mustapha ya miƙe ya zura kayansa sannan ya isa bakin ƙofa ya tsaya,Iya ce ta miƙa masa wani ruwa a bokiti yana tururin zafi,sai tashin ƙamshi yake yi,kanta na kallon ruwan ta ce. "Ga wannan ruwa ne da aka tafasa da kaninfari,ƙaro, musk,ganyen magarya da na lalle,sai kuma ƴar ɗanyar citta kaɗan da bagaruwa da na saka ba mai yawa ba,ka sa ta zauna a ciki har sai ya huce salam,sai a zubar." (Wannan haɗin yana matsi sosai,sannan kuma yana maganin cutar sanyi,zai kuma ƙamsasa jikin mace sosai ya zamana ba za a dinga jin wari a tattare da matancinta ba.) Godiya sosai El-mustapha yayi wa Iya sannan ya karɓi ruwan ya koma ciki,da kansa ya ɗauki Aminee a hannu ya kaita banɗaki yayi mata wankan tsarki sannan ya haɗa mata wannan ruwan ya saka ta a ciki,tin tana raki da shagwaɓa har sai da ta yi shiru ta zauna tana jin daɗin ruwan na ratsa jikinta. Yana hucewa El-mustapha ya kamo ta suka fita daga banɗakin suka koma ɗakinsu,kaya ya sanya mata ya janyo man shafawarsa zai shafa mata,hannunsa ta riƙe kanta a ƙasa ta ce. "Ka na shagwaɓa ni da yawa Balarabena,ka bari zan iya shafawa da kaina,kai ma ka je ka yi wankan." Lakace mata hanci yayi yana dariya sannan ya ce. "Ni dai wannan suna bai yi min daɗi ba,dama kowa ya san ni balarabe ne mana,a samo min mai daɗi na soyayya kafin na fito daga wanka." Gyaɗa masa kai kawai ta yi tana dariya ƙasa-ƙasa. Wanka El-mustapha ya shiga yayi shima,kafin ya fito Aminee ta gudu daga ɗakin,wani ɗaki ta shiga a gidan ta gabatar da sallar azahar sannan ta hau ƙatuwar katifar da ke malale a ɗakin ta kwanta,nan take bacci mai daɗi ya sace ta. Kunya take ji sosai ta haɗa ido da Iya,saboda tinda ta kai mata wannan ruwan ta zauna a ciki ta san me ya faru tsakaninta da El-mustapha kenan,shi kuma gashi ya bata aikin zaɓa masa sunan soyayya wanda bata shiryawa hakan ba,dan ita ɗin ba ma'abociyar soyayya bace,to yaushe ma aka bata damar yin soyayyar? Su waye ma za su so ta a da da tana Aminenen ƙauye? Da wannan tunanin bacci ya ɗauketa. El-mustapha kuwa da ya fito bai ganta ba sai ya saki murmushi,shiryawa yayi ya tafi masallaci,Iya kuwa bata san wainar da ake toyawa ba,aikin gabanta kawai take yi,banda sauri ta samar masu da abinda za su ci da rana babu abinda take yi. A haka El-mustapha ya dawo daga masallaci ya na neman Aminee,da ƙyar ya gano inda take a cikin gidan,zama ya yi a gabanta yana kallon kyakkyawar fuskarta,baya gajiya da ganin kyawunta,gani yake yi kaf duniya babu macen da ta kai masa Amineen sa kyau,duk yanda Mus'ab ke zuzuta kyawun Aisha sai ya ga ba komai bane akan kyawun Amineen sa,anya ba abun nan bane da mutane ke cewa masoyi baya ganin munin abun son sa? Murmushi yayi sannan ya zare jallabiyyarsa ya kwanta a gefenta,tare da rungumeta a jikinsa. Da la'asar El-mustapha ya farka cike da tsamin jiki saboda yanda Aminee ta koma saman jikinsa gaba ɗaya ta ƙanƙamesa tana bacci,a hankali ya janyeta daga jikinsa ya shiga banɗakin dake wajen ya yi alwala ya wuce masallaci,yana fitowa ya kalli inda take ya ga bacci take yi sai ya tafi ya barta,ya tabbata zata tashi ne da kanta. El-mustapha na fita Aminee ta miƙe,dan tun shigarsa bayan gida ta farka,amma sai ta yi bakam bata buɗe idanunta ba,alwala ta ɗaura sannan ta gabatar da sallar la'asar,tana zaune tana azkar ɗin bayan sallah Iya ta shiga da babban faranti ɗauke da abinci da kayan marmari,zama ta yi tana zubawa Aminee sannan ta ce. "Maza ki ci abinci ki ƙoshi,irin mazan nan da suke da jini a jika ba su iya samun waje ba,wuyarta su fara ne su ji ya abun yake,dan haka ki dinga cin abinci ki na ƙoshi sosai,sannan ki na yiwa kayan marmari irin wannan haɗin ki na sha,da yardar Allah watarana za ki saba." Kunya ce ta hana Aminee ɗagawa ta karɓi abincin da Iya ke bata,da ganin haka sai Iya ta saki murmushi ta miƙe ta fita daga ɗakin,tana fita kuwa Aminee da ke jin hanjinta da tumbinta a matse waje ɗaya saboda yunwa sai ta ɗauka ta hau ci,tana kammalawa ta tattara komai ta fitar kitchen,jayayya suka fara yi akan wanke kayan ita da Iya,a haka El-mustapha ya tarar da su,cikin girmamawa ya kalli Iya ya ce. "Iya bar mata ta yi na yau,amma Aminee ina so ki sani,Iya ta zo gidan nan ne dan ta taya ki ayyuka sannan ta nuna maki duk abinda baki iya ba,ina so ki ci gaba da girmamata. Ke kuma Iya dan Allah ki ɗauketa kamar ƴar cikin ki,duk abinda ya dace ta sani ki nusar da ita,bana so a raina min mata ko a musguna mata,idan haka ta faru ƙarshen zaman mu dake zai zo." "In Shaa Allahu Alhaji za ka same ni fiye da yanda ka yi zato." "To Allah Ya sa. Rouh kawo min abincina yunwa nake ji." Iya ce ta taya ta haɗa masa kayan abincin,suna kammalawa ta ɗauka ta kai masa babban parlourn dake malale da carpet mai laushin gaske,ga wasu kujeru daf da ƙasa sun sha shimfiɗar wani lallausan bargo,Acn data sanyaya wajen sai ci gaba da busa sanyi take yi mai daɗi,ƙamshin turaren wutan da bata san sanda aka kunna shi ba sai tashi yake yi a wajen,a haka El-mustapha ya zaunar da ita ya na cin abinci yana kallon kyakkyawar fuskar matarsa da yake jin babu abinda zai raba su sai dai mutuwa. Wunin ranar El-mustapha bai saurari duk wasu ma'aikatansa ba ko masu neman taimako,a gida yayisa tare da amaryarsa. Washegari da sassafe Iya ta tafi gidan Aisha kamar yanda ta yiwa Aminullahi alƙawari,tana zuwa ta tarar da shi ko brush bai yi ba,gashin kansa irin na buzaye mai laushi da laulayewa kamar wani gashin tinkiyar turawa duk ya sake hargitsewa,jakar shi ta goyo rataye a bayansa ya zuba tarkacensa a ciki yana kuka,rungumesa Iya ta yi tana lallashi,kallon Aisha dake harkokin gabanta ta yi sannan ta ce. "Haba Uwar ɗaki na,kina jin yaron nan yana kuka ba za ki lallasar min shi ba?" Yatsina fuska Aisha ta yi kafin ta ce. "Kin san bana son damuwa,shi kuma ɗan naki akwai son saka mutum ciwon kai,tinda ga ki kin dawo,dan Allah tafi da shi ba zan iya da hayaniya ba." "Ai dama ko baki faɗa ba abinda ya dawo da ni kenan." Ɗakin Aminullah Iya ta shiga ta haɗa masa kayansa da basu da yawa suka wuce gidan El-mustapha,suna zuwa Aminee ta ɗora idanunta akansa,sai ta ji wata iriyar ƙaunar yaron ta shige ta,hannu ta miƙa masa akan yaje gareta,sai ya koma bayan Iya ya maƙale kafaɗa,murmushi Iya ta yi sannan ta ce. "Kar ki damu,na tabbata watarana sai yafi son ki ma akai na,dan kuwa shi Aminullah yana da son kulawa,idan har za ki dinga bashi kulawa to kuwa zaki ƙwace min shi." Murmushi Aminee ta saki,ta na bin yaron da kallo har suka shige ɗakin Iya tare........... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA: HAMIDAH SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAERH)✍️✨ PAGE :6 Aminullahi bai saki jikinsa ba har sai da ya haɗu da El-mustapha. Cike da farin ciki ya tafi da gudu ya faɗa jikin El-mustapha da yake kira da Baaba Musty,wasa suka dinga yi tare kamar wasu abokan juna,sai dai da zarar Aminee ta sanya baki a hirar tasu,ko ta shiga wasan sai Aminullahi ya ɓuya bayan El-mustapha yana kallon ta yana dariya ƙasa-ƙasa irin ta yara masu ƙiwa. Washegari da sassafe Aminee ta tashi daga baccin da ya ɗauketa bayan sallar asubata ta watsa ruwa,tana fitowa ta shirya cikin doguwar riga ƙirar Egypt baƙa mai saƙa da koren zare,ba ƙaramin kyau kayan suka yiwa Aminee ba,turaruka ta fesa masu daɗin ƙamshi,a cikin wanda Aisha ta bayar a kawo mata. Kitchen ta nufa ta hau yin funkason alkama,wanda ta haɗa kwaɓinsa da flour ta zuba madarar shanu,sugar da ɗan gishiri a ciki,sai butter da bata fi cokali ɗaya ba,gefe kuma farfesun naman ƙaramar dabba ta ɗora ta koma kan kwaɓinta,tana dubawa sai ta ga ya tashi yanda za ta iya soyawa, mai ta ɗora a wuta ta yanka albasa,sannan ta fara soyawa,nan da nan gidan ya gauraye da ƙamshin suya. A haka Iya ta shiga kitchen ɗin ta tarar da ita tana aiki,cike da mamaki ta tambaye ta a ina ta iya irin wannan girkin na gidan sarakai? Murmushi Aminee ta yi sannan ta ce. "A gidanmu na iya,tun mahaifiyata na da rai take dafawa Abbah na irin wannan abincin,saboda yana matuƙar son sa,ban sani ba ko ya so sa shima." Murmushi Iya ta yi sannan ta hau taya Aminee duk abinda take da buƙatar a taya ta. Suna tsaka da girki Aminullahi ya tashi, kitchen ɗin ya nufa shima cike da sangarta yake kiran sunan Iya,da sauri Iya ta ajiye farantin da suka jera abinci za ta kai parlour ta nufi wajen Aminullahi,cike da kulawa ta ce. "Yarona ka tashi?" Kai ya ɗaga mata,gashin kansa yana rawa a saman kansa ya ce. "Iya me kike dafa mana mai daɗi yau? Ina so in ci yunwa nake ji." "Ba ni ce na dafa ba Babana,Tanti/Auntyn ka ce ta dafa,mu je ka wanke baki ka yi sallah sai ka ci ko?" Kukan taɓara ya sanya mata yana wani dire-dire shi a dole sai ya fara cin abinci kafin ya je yayi sallah. Aminee na ganin haka sai ta ƙarasa ajiye kofunan shan shayi a babban farantin ta ɗauki funkaso ɗaya ta nufe sa da shi,tana zuwa sai ta rage tsawo a gabansa ta kama hannunsa ta sanya masa funkason sannan ta ce. "Gashi na baka ka ci ka je ka yi sallah ko? Amma kuma da za ka yi haƙuri ka je ka wanke baki ka yi sallah ka zo,zan zuba maka har da nama da man shanu,kana so?" Cikin jin daɗi Aminullahi ya ajiye funkason hannunsa a hannun Aminee da ta buɗe masa,dan kuwa ta san da ya ji abinda ta tanadar masa dole zai mayar mata da wanda ta basa,cikin murna ya wuce ɗaki ya shiga banɗaki ya wanke bakinsa sannan yayi alwala ya koma ɗakin,sallah ya gabatar sannan ya miƙe ya koma wajen su Iya,a parlour ya gansu har El-mustapha,da gudu ya wuce wajen Aminee ya haye cinyarta sannan ya hau tambayar abincinsa,cikin mamaki El-mustapha ya kalli yaron ya ce. "Kai Aminullah yau babu magana? Me yake faruwa ne anan?" Dariya Aminee ta yi cike da jin kunya ta ce. "Ah abinda ke faruwa shine

Chapter 3 of 30