koma gidan ita Afrah ne da zama,idan ya so Baba Musa ya ci gaba da gadin gidan duk sanda na zo ziyara zan sami gidana ba tare da takura ba."
"Ah ah ba za a yi haka ba,ina roƙon alfarma bayan auren ku ku yi zaman ku anan don Allah,ai an zama ɗaya damu da ku yanzu."
Haka suka yi ta tattaunawa Abii na basu shawara a inda ya kamata,wajen da ya kamata ya basu tallafi sai ya yi musu alƙawarin ɗaukar nauyin yi musu abun dan sauƙaƙa musu lamuran su. Godiya sosai Bala ya yi har da kukan sa,ƙarshe ya je ya sanar da Baba Musa duk abinda ake ciki,shi ma ya shiga ya zube a ƙasa ya na ta zabga godiya. Abii bai bar wajen su Lamyah ba sai bayan Isha'i,anan ya ci abincin da Mama Tani ta dafa musu tare da Lamyah da Afrah da Mubarak,suna ci suna hira cike da maɗaukakin farinciki. Abii bai taba zaton Lamyah za ta rikice ta birkice masa ba a lokacin da ya ce zai tafi,kuka sosai ta dinga yi har da faɗuwa a ƙasa tana birgima kamar ƙaramar yarinya,ita a zaton ta idan ya tafi ba zai sake dawowa ba,da ƙyar da siɗin goshi Afrah ta bata baki suka tsaya suna kallon motar Abii da ke danne ƙwallar da ta cika masa idanu har ya tafi. Da gudu Lamyah ta shiga ɗakin ta ta rufe ƙofa ta faɗa gado ta na kuka,duk lallashin da Afrah ke yi mata bata ji ba balle ta tsagaita da kukanta,har sai da bacci ya ɗauketa sannan suka daina jin kukan nata.
Hamdala Afrah ta yi ta ɗauki Mubarak dake kuka yana bugawa Lamyah ƙofa suka bar wajen,lallashinsa ta yi kafin su je su kwanta suma. Cikin dare Lamyah ta farka ta yi alwala ta yi nafila,tare da roƙon Allah ya dawo da Abii ya ɗauke su ya kai su gidan sa kar su yi ta zama a Kano basu da wani makusanci. Ta na idarwa ta ɗakko akwatunan su ta hau loda kayan Mubarak,sai da ta kwashe kayan sa tas,sannan ta ɗan ɗebi nata kaɗan,sauran kuma ta barwa Afrah ta yi gayen ta da su itama.
Jakar da mahaifinta ya bata ta ɗakko ta buɗe ta ga komai na nan kamar a lokacin ya bata ita,nan take kewar mahaifinta ta kama ta,ko ya ƴan'uwansa suke a can Dubai ɗin? Ko an gano kaidin su an ɗauki mataki akan su oho. Da wannan tunanin Lamyah ta tarkata komai ta aje a gefe ta haye gado ta kwanta.
Washegari da safe sai ga Abii ya zo shi kaɗai, abincin da ya yi musu take away ɗin sa ya sa Bala ya ɗauki nasu ya kai musu ɗaki,sannan ya koma ya taya Abii ɗaukan na su Lamyah ya bi bayan sa. Ko da suka je ƙofar shiga gidan a kulle yake dan kuwa basu tashi daga bacci ba, ƙwanƙwasa wa Bala ya yi,Mama Tani ta je ta buɗe idanunta basu gama washewa ba,tana ganin Abii ta murtsike idanunta ta koma baya tana yi masa sannu da zuwa. Shiga ciki ya yi ya zauna a kujera yana danna wayarsa,saƙo yake turawa Momma akan su fara shirin tarbon sa yana nan tafe gobe da wani surprise da yake so ya yi musu. Tani kuwa ɗakin Lamyah ta je ta tada ita ta sanar da ita zuwan Abii,da sauri ta sauka daga gado ta faɗa banɗaki,brush ta yi ta wanke fuskarta, sannan ta sanya mayafin doguwar rigar da ta yi sallar asuba da ita ta nufi parlour,tana ganin Abii ta isa wajen sa da sauri ta zauna a gefensa tana gaida shi,cike da fara'a ya ce.
"Sarkin kuka kin tashi lafiya?"
Ɗaga masa kai kawai ta yi tana dariya ƙasa-ƙasa,murmushi ya yi sannan ya ce.
"Anya kuwa kan ki baya ciwo Lamyah? Dan ni na tsorata sosai da kukan da ki ka yi jiya."
"Gaskiya dai kam Abii kaina na yi min ciwo sosai,amma na san zai dena tinda ga ka a gabana ina kallon ka."
Murmushi ya sakar mata sannan ya ce.
"To ɗakko mana plate da spoon mu ci abinci,dan ni yunwa nake ji sosai,kin san Abiin naki ba ɗan gayu bane,ƙarfe takwas nake karyawa."
Dariya Lamyah ta yi,kafin ta tashi Mama Tani ta nufi hanyar kitchen,da sauri Lamyah ta miƙe ta ce.
"Ah ah Mama bari na ɗakko da kaina,wannan aiken Abii na ne bana so a taya ni."
Cike da matsananciyar ƙaunar yarinyar Mus'ab ke kallon ta har ta je ta dawo,tare suka ci abinci su Afrah na can yawon bacci. Suna gamawa suka zauna suna kallo,Abii na bata labarin kasuwancin mahaifinta da yanda dukiyar su take ta haɓaka,cikin farinciki Lamyah ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce.
"Babu abinda ke faranta min rai a yanzu Abii sama da haɗuwata da kai,idan zan dawwama tare da ku bana buƙatar dukiya da duk wani abu da ya shafe ta,ganin ku kaɗai ya wadatar da ni Abii."
Murmushi ya yi yana jin ƙaunarta na sake kama zuciyarsa,lallai ɗan'uwansa ya yi ƙoƙari wajen bawa ƴar tasa tarbiyya duk da cewa sun taso a wruraren da tarbiyyar ta yi ƙaranci. Hamdala ya sake yi ga Allah a karo na babu adadi saboda haɗuwa da ta yi da yaran Amininsa da yake jin sa kamar ɗan'uwansa na jini. Kallon ta ya yi sannan ya duba agogon hannunsa ya ce.
"Je ki ki taso waccan kasar,ta zo ta karya zan fita da ku shopping ku siyo duk abinda babu a gidan nan wanda ango da amarya za su buƙata,gobe ana gama ɗaura auren su za mu wuce."
Cikin tsallen murna Lamyah ta tashi ta shiga ɗakin Afrah,gani ta yi bata gado sai ta ɗaga murya ta ce.
"Afrah ki zo Abiina ya zo,ya ce ki shirya mu wuce shopping. Kai Muba taso mu je ka yi brush Mama ta yi maka wanka mu tafi shopping."
Tashi ya yi yana miƙa ya kwanta a jikinta,da ƙyar ta ƙarasa tada shi ta tura ƙeyarsa zuwa wajen Tani dan ta yi masa wanka ta shirya sa. Shirun da ta ji a banɗaki ne ya sanya ta tashi ta isa bakin ƙofar ta tsaya tana yi wa Afrah magana,shirun da ta ji ne ya sanya ta ƙoƙarin murɗa hannun ƙofar,sai dai Afrah ta riga ta buɗewa,idanunta sun yi luhu-luhu alamar ta sha kuka ta ce.
"Malama gani nan,ai na jiki,ko da afka min cikin banɗakin za ki yi ina wanka?"
Jikin Lamyah ne ya yi sanyi,dan ta gane Afrah na kukan rabuwa da ita ne,murya na rawa ta ce.
"Ki yi haƙuri,dama Abii ne ya ce na kirawo ki. Yauwa ya maganar sanar da dangin Ummahn ki da Abbahn ki maganar auren ki? A gani na yana da matuƙar mahimmanci su sani,dan bai kamata kuna gari ɗaya a yi miki aure basu sani ba."
"Kina so nima su sake gudu na ne kamar yanda naki suka yi miki? Lamyah ɓacin ran ya isa haka dan Allah,idan ke kin manta to ni har yanzu ina jin zafin abinda aka yi miki,a duk sanda na tina ina jin kamar na koma na hallaka mutanen unguwar gaba ɗaya kowa ya huta tinda mugaye aka tara a cikinta,dan haka suma waɗannan babu wanda zan nema a cikin su,su da duke manya suka iya ƙyale rayuwata sai ni ce ba zan iya ƙyale tasu ba? Mutanen da basu damu da karuwanci zan yi na haifi ƴaƴan shegu ba ko aure zan yi na zauna inuwar raya sunnar ma'aiki ba to me zai kaini wajen su?"
"Yi haƙuri Afrah mita,mu je ki ci abinci,duk abinda kike so shi zan yi miki,a gaskiya zan yi kewar ki matuƙa masoyiya."
"Nima zan yi kewar ki masoyiya."
Rungume da junan su suka isa parlour,Afrah durƙusawa ta yi ta gaishe da Abii sannan ta karɓi abincin da Lamyah ta bata ta fara ci,suna kammalawa Bala ya karɓi tuƙin mota suka tafi siyayya.
Sai da suka sai duk wani abu da suke buƙata sannan suka dawo gida a gajiye. Suna shiga cikin gidan Bala ya yi arba da abinda ya sanya motar kusan ƙwacewa daga hannunsa,ikon Allah ne ya tsaida su suka firfita suka nufi wajen Baba Musa......
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 29.
"Me ya kawo ki gidan nan? Ya aka yi kika san muna nan?"
Washe baki kyakkyawar bafulatanar ta yi kafin ta kama hannun Bala ta ce.
"Allah sarki Babana,kai ne ka girma haka? Allah na gode maka da ban mutu ba na sake sanya ka a ido na."
Bakin mayafinta ta kama ta na fyace majinar da babu ita,a hasale Bala ya ƙwace hannunsa da ta riƙe sannan ya sake maimaita tambayarsa a gare ta.
"Ya akai kika san muna nan? Sannan me ya kawo ki? "
"Haba Babana ka bari ma mu shiga ciki na ci abinci na huta mana."
"Cikin ina? An faɗa miki nan ɗin baitil mali ne? Nan gidan aikin mu ne ba mallakin mu bane idan ma dan haka kika waiwaye mu to ki koma inda kika dito, Abbah kai ne ka gayyace ta gidan mutane?"
Sunkuyar da kai Baba Musa ya yi kafin ya ce.
"Ka gafarce ni Bala,wai na ga an saka bikin ka a ƙurarran lokaci ne shi yasa na kirata na sanar da ita,saboda komai lalacewarta mahaifiyarka ce,ban taɓa zaton za ta zo ba,a zato na albarka kawai za ta saka muku,sai gashi ta zo babu sanarwa."
"Ta yaya za ta sanar da kai tinda ka sanar da ita kana zaune gidan mutane masu karamci ka na walwala babu takura? Tinda ta ji inda za ta sha jar miya ai dole ta dawo gare ka."
Juyawa ya yi da sauri ya bar wajen,ɗakin su ya shige ya kulle kansa ya kifa kai a jikin ƙofar ɗakin ya na kwararar da ruwan hawaye masu mugun zafi. Cikin kuka ya ce.
"Ita da kanta ta tsallake mu ta tafi tin ban gama mallakar hankalin kaina ba,ta yi aure sama da huɗu saboda tsabar son abun duniya,wanne irin cin mutunci ne bata yi maka ba Abbah? Wacce iriyar tsinuwa da tozarci ne bata yi mana ba a lokacin da muke binta gida gida lungu da saƙo dan kawai ta haƙura ta zauna da mu? Baki ta yi maka ta ce ba za ka taɓa yin arziƙi ba,za ka mutu ne cikin talauci da uƙubar rayuwa,sai yanzu da ta ji mun fara fita daga ƙangin babu da talaucin da ya yi mana katutu shine za ta dawo cikin rayuwarmu?"
A hankali muryar Baba Musa da ya biyo bayan ɗan nasa ya dafa marfin ƙofar ɗakin ya ce.
"Ban manta dika waɗannan abubuwan da ta yi mana ba,sai dai riƙe su a rai ba shi da amfani ɗana,na yafe mata duk abinda ta yi min a rayuwa,ba zan taɓa manta sanadin Kulu na samu ciwon hawan jini ba,ba zan manta Kulu ta taɓa watsa min ruwan kwata ba ta ce ya fini daraja kuma a cikinsa zan dawwama,haka zalika ba zan taɓa manta ita ce macen da ta haifa min kai ba,ita ce macen da ta yi wahalar rainon cikin ka watanni tara ta haife ka ko rigar da za a sanya maka bamu da ita tsabar babu, bayan haihuwar ka Kulu ita ce ta yi ta faɗi tashi har ta ga na samu ragon sunan da na yanka maka,kar ka manta alkhairin da ta yi maka kafin sharri ya biyo baya,kar ka manta a koda yaushe su mata suna da rauni,musamman akan abun duniya,wasu ana iya amfani da abun duniya a yaudare su,wasu kuma su ne suke da son abun duniyar,kafin Kulu ta guje mu ta ɗanɗana zaman talauci tare da mu,dan haka ka yi haƙuri a gama ɗaurin auren ka gobe tinda ba taro za a yi ba ta tafi inda ta fito."
A hankali Bala ya buɗe ƙofar ya fito yana wani ɗaɗɗaga kafaɗa yana shessheƙar kuka,rungume shi Baba Musa ya yi yana murmushi,bayan ya share hawayensa ne ya ce.
"Na zaci ai auren ta za ka sake yi,sanda arziƙin da ka ɗan tara ya ƙare sai ta gudu ta barka again."
"Allah Ya yi min tsari da sake auren Kulu Bala,ai an yi an gama kuma har abada ba zan sake zaman aure da ita ba,ni ma fa na san menene kishi Bala,ta ya zan auri matar da ta gama auren mazaje da yawa? Allah ya tsare ni."
Dariya Bala ya yi sannan ya koma wajen da su Afrah ke tsaye har a wannan lokacin suna lallashin Kulu dake ta matsar ƙwalla. Cikin haɗe fuska Bala ya ce.
"Ana gama biki za ki koma inda kika fito,tinda dai ke da kan ki kika nesanta kan ki da mu."
Shiru ta yi tana ƙissima abubuwa da yawa a cikin ranta,hannu Bala ya sa ya karɓi kayan dake hannun Abii wanda ya gama haɗa zaren labarin waje ɗaya har ya bashi ma'anar da ta dace.
Sai da suka gama shigar da kayan da suka siyo kaf sannan Abii ya tsaya ya ci abinci ya ƙoshi,ana yin sallar magariba ya wuce gida tare da alƙawarin gobe zai dawo,ana ɗaura aure za su wuce Niger.
Tinda suka shiga cikin gidan Kulu ke kallon ko wacce kusurwa ta gidan kamar idanunta za su faɗi,cikin zuciyarta ta ce.
'Talauci na gudarwa a baya saboda jikina bai yi kalar sa ba,tinda na ga irin wannan dukiyar kuwa yanzu babu shegen da ya isa ya raba ni da gidan nan alƙur'an,kan uban nan ji wasu kujeru kamar a ƙasar waje? Yo ni ko wanke wanke da shara zan yi Musa ya ci gaba da gadi ai ba zan damu ba.'
A firgice ta waiga ta kalli Afrah da ta kasa gane inda yanayin fuskar ta ya dosa,kayanta Afrah ta karɓa ta kai ta ɗakin Tani ta ce.
"Bismillah ga inda za ki kwana zuwa gobe a gama ɗaura aure."
"Me kike nufi da zuwa gobe a gama ɗaura aure? Ke wacece da zaki gaya min haka?"
Murmushi Afrah ta sakar mata mai ma'anoni da yawa kafin ta ce.
"Ni ce nan zan zamo matar ɗan ki da yardar Allah gobe,babu kalar labarin ki da ban samu ba a wajen sa,dan haka dan girman Allah mu mutunta junan mu da ni da ke,kar ki bari azo ana wallahi tallahi a tsakanin mu,abun ba zai yi mana kyau ba."
Afrah na gama faɗar haka ta bar ɗakin ranta na yi mata zafi,tsananin tausayin Bala da ya taso babu kulawar Uwa ne ke addabar zuciyarta,gefe ɗaya kewar Lamyah da take ji tana mamayarta tin kafin su rabu ya taimaka wajen shigar ta cikin ƙunci da ɓacin rai,shi yasa bata jin za ta ragawa Mahaifiyar Bala ko na sakwan ɗaya. Abinci ta ɗauka ta kai mata ɗakin ta ajiye mata da ruwa,a tsaye ta ganta tana ta safa da marwa a ɗakin,ba tare da sun kula juna ba Afrah ta rufe ɗakin ta koma wajen su Lamyah,hira suka dinga yi tare da yi wa junan su alƙawura kala-kala,Mama Tani ma na zaune a tare da su suna ta hira kamar su ɗaga gidan saboda hayaniyar da suke ta yi,Afrah ce ta ce.
"Ke mun zauna zaman hira tashi mu je mu taya ki parking kaya."
Dariya Lamyah ta yi ta sunne kai a jikin Mama Tani sannan ta ce.
"Ni fa na jima da haɗa kayan mu,lokacin tafiya kawai muke jira,na matsu na je na ga Momma,mace mai karamci da mutunci,tana matuƙar so na da ƙauna ta,lokacin muna Dubai kullum sai mun yi waya,shi yasa na ji matuƙar baƙin ciki a lokacin da na ga sabuwar wayar da Baaba ya bani babu lambobin wayar su."
"Allah sarki, In Shaa Allahu kina gab da haɗuwa da su,idan kin je dai kar ki manta a yo min hoton Yah Amee ɗin nan naki na gansa,Allah Ya sa dai yana da kyau."
Rintse idanu Lamyah ta yi tana hasaso kamannin Handsome a ranta,tare da fatan Allah Ya sa Yah Amee ɗinta ya fi shi kyau da komai,wataƙila ta samu ta cire son wanda bai ma san tana yi ba,mutumin da ya tsane ta yake jin kamar ya kamata ya yi ta bugu. Dukan da Afrah ta ɗasa mata ne ya dawo da ita hayyacinta,nan fa suka hau kokawa suna guje-guje Mubarak na taya su,Mama Tani kuwa banda dariya babu abinda take yi,sai da suka gaji dan kansu sannan suka zube a kujera suka sauya tasha suka fara kallo,abin motsa baki Mama Tani ta tashi ta ɗebo musu,a hanyar ta ta dawowa ne ta ji kamar motsi a ɗakin Lamyah,sai kawai ta kawar da tunanin a ranta tinda ta san gaba ɗayan su suna can babu kowa a ɗakin,gaba ɗaya ta manta da Kulu da ke cikin gidan,dan tinda ta ga Kulun wani irin takaicinta ya kama ta,unguwa ɗaya suka yi zama tin kafin a haifi Bala,dan haka duk sun san juna,bayan haka kuma ita da Baba Musa sun fara daidaita kan su,kwatsam sai Kulun ta dawo cikin rayuwarsa? Shi yasa ta ɗebe ta ta watsar ta nuna mata da ɗai duniya ba ai ruwanta ba ma balle ta kula ta.
Har tsakiyar dare su Afrah na kallo tare da hira,daga ƙarshe a wajen suka kwana gaba ɗayan su. Asubar fari suka farka suka shiga ɗakunan su suka yi sallah,suna idarwa Lamyah ta shiga kitchen ta dafawa Afrah kazar da ta ji kayan ƙamshi da nonon raƙumi tare da riɗi a ciki,sannan ta dafa mata nonon raƙumin ta ƙara mata madarar shanu a ciki da ta gari ta ajiye a gefe,sai ta sake niƙa kantu da kaninfari da citta ta zuba a haɗin madarar ta yanka kankana akai ta markaɗe,ta jima tana ganin Amminta na yin wannan haɗin tana ci,sai yanzu ta gane amfaninsa a kaf gyare-gyaren da take ganin Ammin nata na yi.
Tana kai wa Afrah ta koma kitchen ɗin ta haɗa body scrub da Afrah za ta yi amfani da shi wajen gyara jikinta,ɗanyen turmeric ta ɗiba wanda suke girki da shi,sai ta ɗauki tumatur manya guda biyu,ta ɗauki lemon tsami ta yanka shi tare da tumatur ɗin duk ta zuba a blender,sai ta ɗebo sugar babban cokali uku ta zuba ƙaramin cokali na gishiri,sannan ta tsiyaya zuma mai ɗan yawa wadda za ta iya kaiwa cokali biyar,sai ta tsiyaya madarar shanu a madadin ruwa,ta zuba ruwan ƙwai farin amma banda yellow ɗin ta markaɗe su waje ɗaya,tana gamawa ta juye a mazubi mai kyau ta wuce ɗakin Afrah da shi,tana zuwa ta tarar da Afrah ta cinye naman nan tas ta shanye madarar sai santi take yi. Afrah bata bawa Lamyah matsala ba dan kuwa tana so ta yi kyau itama,sai dai ta ce dole ne itama Lamyah ta shafa kayan gyaran jikin,a tare suka ɗaura mayafan su suka shafe jikin su da kayan gyaran.
Tani ita ce ta kai wa Kulu abinci,bayan sun gaisa ta bar ɗakin ta koma kitchen ta hau gyara abubuwan da Lamyah ta ɓata,babu wanda ya san lokacin da Kulu ta lallaɓa ta ɗauki kayanta za ta gudu,har ta kai bakin gate Baba Musa baya nan,tana buɗe gate ɗin ta ci karo da Bala a bakin ƙofa yana ƙoƙarin shiga gidan,kallon kallo suka tsaya yiwa juna,a rikice Kulu ta fashe da kukan munafurci ta ce.
"Tafiya zan yi,tinda na kula kamar na takura muku,kowa ya tsane ni baya ƙauna ta saboda kuskuren da na aikata a baya a matsayi na na ƴar adam,naga dai Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana balle mutum,to ni zan tafi Allah Ya baku zaman lafiya,sai watarana."
Jikin Bala ne ya yi sanyi,ko babu komai wannan ɗin mahaifiyarsa ce,kamar yanda Abbahnsa ya ce ita ta ɗauki cikinsa na wata tara,tinda ko ta haife shi ya zo duniya ai dole ta ci wannan albarkacin,jakarta ya duƙa zai ɗauka ta yi saurin zabura ta yi baya,nan take abinda ta ƙudindine a hijabinta ya faɗo ƙasa,maƙudan kuɗaɗe ne irin na ƙasar Dubai a ciki,wanda bai ma san iya adadin su ba,ita kanta Kulun bata san nawa bane,dama niyyar ta in ta je can ƴan canji sai a yi ta ta ƙare.
Wani irin baƙin ciki ne ya kama zuciyar Bala,mugun kallon da yake bin Kulu da shi ne ya sanya ta ajiye dika kuɗaɗen ta ɗauki jakarta ta bar gidan a kunyace,rasa yanda zai yi ya mayar da kuɗin ya yi ba tare da Afrah ko Lamyah sun sani ba,ko babu komai mahaifiyarsa ce Kulu,ba zai so asirin ta ya tonu ba sai Afrah ta sake tsanar ta akan wadda ya riga ya san tana yi mata. Har ɗaki yaje ya samu mahaifinsa ya sanar da shi duk abinda ya faru,cikin sauri Baba Musa ya ce.
"Tani ce kawai mafitar mu a wannan lamarin,idan kuma ba haka ba dole mu sanar da abinda ya faru gudun zargi."
Da sauri Bala ya girgiza kai ya ce.
"Dan Allah Abbah ka san yanda za ka yi a mayar da kuɗaɗen nan kafin Hajiya Lamyah ta gano ɓatan su."
Miƙewa Baba Musa ya yi ya ce.
"Babu komai ina zuwa."
Waje ya fita ya lalubo ƴar ƙaramar wayarsa ya kira Tani,babu jimawa ta zagayo ta ƙofar baya kamar yanda suka saba haɗuwa su sha hirar su ta koma babu wanda ya sani,tana zuwa sai ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi,bayan ya amsa ne ya yi mata bayanin abinda Kulu ta yi,cike da damuwa ta miƙe tsaye ta ce.
"Lallai jiya na ji motsi a ɗakin Hajiya Lamyah lokacin duk muna parlour ana ta hira da wasanni,ashe kulu ce take nata aikin,tabɗijam ! yanzu to ya za a yi a mayar ba tare da sun sani ba? Tinda dai wannan abun kunyar idan ya fito sai ita Afrah ta dena ganin mutuncinta."
"Dama can ba gani take yi ba,amma dai sanin ba zai yi wa kowa daɗi ba,ki taimaka na kawo miki su ki mayar ba tare da kowa ya sani ba."
"Shikenan ka kawo su ɗin,na tabbata ba zai wuce a cikin babbar jakar Hajiyan ta kwasa ba,tinda ta taɓa nuna min da kanta."
"Na gode Taninaa,Allah Ya barmu tare,ni fa ina ganin da an gama hidimar bikin yaran nan za mu angwance mu ma,kin ga sai mu yi zaman mu a bakin ƙofa muna zuba soyayyar mu ko?"
Dariya kawai Tani ta yi ta shige ciki,ta ji daɗin abinda Baba Musa ya faɗa,dan kuwa itama tana ra'ayinsa sosai kamar yanda yake ra'ayinta. Wata baƙar leda babba ta ɗakko ta dawo bayan gidan tana jiran dawowarsa,ba jimawa ya dawo hannunsa cike da damin kuɗi,salati Tani ta sanya tana mamakin son zuciya irin na wasu mutanen,a ledar ya saka mata ita kuma ta yi sauri ta shige gidan,ɗakin Lamyah ta shiga da sauri ta zuge jakar ta zuba kuɗin,tana gama zugewa za ta bar wajen Lamyah ta shiga ɗakin dan wanke jikinta,kallon kallo suka tsaya yi ita da Mama Tani wadda zufa ta fara wankewa fuska........
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
*Don Allah idan na manta ban tura page a group ba, ku dinga bin link ɗin channel ku karanta wanda ku ka yi missing a sauƙaƙe,shi yasa yanzu nake sharing haɗe da link ɗin channel,wadda bata yi following ba ta yi saboda gujewa missing pagi.*
PAGE 30.
"Sannu da aiki Mama Tani,ko ki na buƙatar taimako ne idan na wanke jiki na na zo na taya ki sharar? Dan na ga yau aiki kike yi sosai."
Lamyah ta faɗa ta na mai buɗe ƙofar banɗakinta ta shige,wata iriyar ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske Mama Tani ta sauke,cikin dakiya ta ce.
"Ah ah wace ni da saka amare aiki? Ai yau duk inda lungu da saƙo yake a gidan nan sai na sharo shi na goge shi tass,bari ma na ɗebo kayan aiki na,dama na shigo ne na fara ɗaga kaya na gyara gadon ki."
Lamyah bata amsa ta ba kasancewar ta na cikin banɗaki,jin shirun da ta yi ne ya sanya Mama Tani fara gyara gadon,sannan ta kau da akwatunan da Lamyah ta haɗa kayan su a ciki waje ɗaya,sai ta fita daga ɗakin ta nufi inda suke ajiye kayan aikace aikacen gidan ta ɗakko tsintsiya da bokitin mopping da towels ɗin goge-gogen ƙura,tana komawa ɗakin ta tarar da Lamyah har ta fito daga banɗaki tana shafa mai,fatar nan ta yi luwai-luwai kamar ta jarirai. Juyawa ta yi fuskar ta ɗauke da maɗaukakin murmushi ta ce.
"Mama Tani ya kika ganni na yi kyau?"
Murmushi Tani ta sakar mata sannan ta ce.
"Ai dama can ke ɗin mai kyau ce,sai dai na ce yau kin ƙara kyau akan kyan da kike da shi,fatar ki ta yi kyau tana ɗaukan idanu,anya kuwa ba za a kira surukina na Niger ba kema a ɗaura auren
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 30