Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ku a yau baki ɗaya?" Kunya ce ta sanya Lamyah tashi daga gaban madubi da gudu ta nufi wajen kayan ta ta ɗauki wata doguwar riga ta zira,Tani kuwa dariya ta dinga yi mata har ta bar ɗakin,ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin. "Allah na gode maka da ban taka sawun ɓarauniya Kulu ba,Ya Allah ka kare wannan yarinya mai zuciyar da bata nufin kowa da sharri,yarinyar da take son kyautatawa duk wanda zama ya haɗa ta da shi,yarinyar da take da kamewa da yawan ibada,Allah ka sa duk inda ta sanya ƙafarta ta kasance cikin kariyar ka da amincin ka." Da ire-iren wannan addu'ar Tani ta kammala gyara ɗakin,wanda a nan ne su Afrah za su tare da angon nata Bala. Parlour ta koma shima ta yi masa gyara na musamman kafin ta shiga ɗakin Afrah ta tarar da su suna gwada kayan da suka siyo jiya da Abii. Gaba ɗaya kayan sun yi musu daidai kamar sai da aka gwada su aka ɗinka su,kwalliya sosai Afrah ta yi, Lamyah na taya ta,sai gata ta fito tsaf da ita,suna fitowa parlour suka tarar da Mama Tani na gaisawa da wasu matan layin nasu,mamaki ne ya kama Afrah dan dai ita ta san bata gayyaci kowa ba,haka ma Tani,cikin washe baki ɗaya daga cikin matan ta ce. "Ai Kulu ke sanar damu auren ɗanta da Afrah ƳAR RAWA,shi ne muka shigo mu sa albarka,Allah Ya sa mutu ka raba ne." Yatsina fuska Afrah ta yi kafin ta buɗe baki za ta yi magana Lamyah ta riga ta da faɗin, "Amin Ya Allah mun gode,bismillah ku zauna,bari a kawo muku ruwa,Mama Tani ɗakko musu lemo dan Allah,a buɗe kwalin cake ɗin nan da biscuits a ɗebo musu." "To Hajiya." Shine abinda Mama Tani ta ce ta juya zuwa kitchen,zuciyarta cike ƙaunar halayen Lamyah da take jinta tamkar ƴar cikinta,har abada ba za su taɓa mantawa da karamci da mutuncin yarinyar ba a gare su. Babban faranti ta ɗauka ta saka kofuna ta tsiyaya lemon kwalayen da ta bubbuɗe sannan ta kwashi cake irin na ledar nan ta zuba da biscuits da yawa ta kai wa matan,babu kunya ko jin nauyin idanun Afrah da ta ke bin su da kallon mamaki suka fara shan lemo suna cin cake ɗin,sai surutu suke zubawa suna kurɓar lemo,anan ne Afrah ta ji cewar Kulu ta bar gidan ta koma inda ta fito,cike da mamaki ta miƙe ta fita daga gidan,ƙofar ɗakin su Baba Musa ta nufa ta hau buga ƙofar,Baba Musa ne ya fito ya na naɗe kansa da rawanin da yake sakawa ya ce. "Yauwa Tanina har kin mayar da kuɗin? Allah dai yasa yarinyar nan bata gan ki ba ki taka sawun ɓarawo? A kaf halayyar Kulu da na sani ban san tana....." Yana juyowa ya ga Afrah tsaye ta na haɗe gira alamun tambaya ƙarara ya bayyana a saman fuskarta,kafin ta yi tambayar da ke danƙare a ranta Baba Musa ya ce. "Dan girman Allah Afrah kar ki yi min tambayar da ba zan iya baki amsa ba,yanda kika ga Kulu ta zo babu sanarwa,to gashi an wayi gari ta tafi babu sanarwa,mu bar zancen a haka." "To Baba na bar maganar,amma kuma wanne sawun ɓarawon ka ke tsoron kar Mama Tani ta taka?" "Ki manta da kin ji na faɗi wannan maganar,tinda da na san ke ce ba Tani ba ba zan yi ta ba. Alhajin ya kusa zuwa ne naga amarya ta sha kwalliya haka?" Baba Musa ya ƙarasa maganarsa cike da barkwanci,ajiyar zuciya Afrah ta sauke,dan ba yau ta san halin Baba Musa ba,idan bai yi niyyar yin abu ba ba zai taɓa yinsa ba,sai kawai ta samu gefen ɗakin ta jingina jikinta,cikin sanyin murya ta ce. "Wai fa matan unguwar nan ne suka shigo taya mu murnar aure,wai sun samu labari ne a wajen Baba Kulu,har yaushe ma ta haɗu da su ta basu wannan labarin oho?" "Ai mu abinda ta yi na sanar da su ya zame mana alkhairi,kin ga ko nan gaba babu mai zargin zaman banza ne a tsakanin ki da Bala,gwanda mutane su shaida,ba dan abubuwan ma sun zo a ƙurarren lokaci ba ai har goron gayyata za a aika musu har gida." Ajiyar zuciya Afrah ta sake saukewa a karo na babu adadi,gaba ɗaya jin ta take yi wani iri,wataƙila har da kewar rabuwarta da masoyiyarta Lamyah ke damun ta shi yasa take jin ta haka. Suna nan tsaye Bala ya shigo gidan hannunsa ɗauke da wata baƙar leda babba mai layi layin fari a jiki,suna haɗa ido ya sakar mata murmushi,yaƙe Afrah ta yi masa ta kama hanya za ta shige cikin gida,cikin wata iriyar murya Bala ya ce. "Ina za ki je kuma babu gaisuwa?" Hararar shi ta yi ta kasan idanunta ta wuce ba tare da ta ce komai ba,Baba Musa kuwa dariya ya yi ya shige ɗakin shi,Bala ma dariyar ya yi ya bi bayan mahaifinsa,kayan da ya karɓo daga wajen ɗinki suka hau dubawa kowa ya ɗauki nashi. Sai da suka yi wanka sannan suka shirya tsaf cikin farar shaddar da ta fito da su sharr. Kafin azahar gidan ya cika da mutanen unguwa,su na ta taya su Afrah murna da farin cikin auren da za su yi ita da Bala. Sai a wannan lokacin ne Afrah ta ji kewar dangin mahaifanta sosai,Lamyah kuwa ta roƙe ta ta kira ko mutum ɗaya ne ta sanar da shi amma ta ƙi,da ta dame ta ma sai ta fita ta bar mata ɗakin ta koma ɗakin Mama Tani ta kwanta a gado tana kuka. Ganin haka ne ya sa Lamyah ta ƙyale ta,ta ci gaba da kula da baƙin da suke ta shige da fice a gidan. Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bala da Baba Musa suka fita zuwa masallacin unguwar tasu,a can suka tarar da Abii da Malam Isa, Mai Unguwar Rijiyar Lemo, Malam Abubakar da Malam Ayuba,ana idar da sallar Azahar aka ɗaura auren Bala da Afrah tare da Baba Musa da Tani, akan sadaki naira dubu hamsin hamsin, Baba Musa har da hawayen farin ciki ya zubar,godiya kuwa da ya fara yiwa Abii har sai da Abii ya hana shi ya ce ya godewa Allah. Manya da yaran mutanen da suka shaida ɗaurin auren Bala da mahaifinsa duk sun tafi da goro da alewa, sun kuma sanya wa auren albarka. A cikin motar su Abii su Bala suka dawo gida,lokacin da sanarwar ɗaurin aure ta riski su Afrah sai Afrah ta sake rikicewa da kuka Lamyah na taya ta,matan unguwa kuwa sai suka hau tsokanar Tani da ta kama baki tana ta'ajibin jin wai itama an ɗaura auren ta da nata masoyin ba tare da ta san za a yi hakan ba,daga ƙarshe sai ta hau godiya zuwa ga Allah da ya sa zata sake zama a inuwar aure dan bautawa Allah. Haka aka ci gaba da gudanar da shagalin biki,dan kuwa har abinci sai da Lamyah ta ce a dafa saboda mata da yaran da suka taru a gidan. Da la'asar sakaliya Abii ya yiwa Lamyah waya ya ce su shirya su fito ita da Mubarak lokacin tafiya ya yi,nan da nan gidan biki ya koma gidan koke-koke,Afrah da ta jima tana kuka sai ta sake rikicewa,ga wani irin zazzaɓi da ya yi mata dirar mikiya,banda karkarwa babu abinda take yi,hawaye da majina duk sun ɓata mata fuska,Mama Tani na kuka ta ɗakko jakunkunan su Lamyah ta miƙawa Bala ya kai motar Abii,Mubarak na rungume a jikin Afrah tana kuka ya hau share mata hawayen da suka ƙi tsayawa saboda ƙunar da zuciyar Afrah ke yi,cikin kuka Yaron ya ce. "Aunty Afrah kema ki ɗakko kayan ki mu tafi dake." Rungume shi Afrah ta sake yi a jikinta tana kuka ta kasa cewa komai,da ƙyar Bala ya karɓi yaron daga wajenta,ya sanya shi a mota,Lamyah ce ta rungume Afrah suka sake fashewa da sabon kuka,Abii sai ya ji kamar bai kyauta ba idan ya raba su,sai dai babu yanda zai yi dole ne dama duk yanda aka shaƙu watarana a rabu,idan rabuwar muhalli bata raba ba wata rana mutuwa ce za ta raba. Suna rungume da junan su Lamyah ta kama Afrah suka shiga cikin gida,bata tsaya a ko ina ba sai a cikin ɗakinta ta zaunar da Afrah da ta koma kamar ƙaramar yarinya saboda rauni da zuciyarta ta yi a bakin gado. Hannu ta sa ta cire sarƙar zinaren da ke wuyanta ta sakawa Afrah a wuyanta sannan ta kalle ta idanunta na zubar da hawaye,ta sanya murmushin ƙarfin hali a fuskarta ta ce. "Inyee Amaryar Bala ta fito fess da ita,Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka,ni dai ina roƙon alfarma haihuwar farko idan mace ce a yi min takwara,in ba a yi min takwara ba ba zan zo suna ba." Dariya Afrah ta yi hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta,a hankali Lamyah ta zare hannunta daga cikin na Afrah ta kama hanya za ta bar ɗakin,wani irin kuka ne me ƙarfi ya taso mata tana danne shi,ta na fita tsakar gida ta sake shi har wani shiɗewa take yi,Mama Tani ce ta yi saurin isa wajenta ta rungume ta,Afrah ma na ɗaki tana nata kukan haka suka shiga mota suna ɗaga wa mutane hannu suka tafi filin jirgi. A wannan ranar masoyan biyu sun rabu zuciyar su cike da kewar junan su mai tsanani. Ta ɓangaren ango Bala kuwa babu zancen angwancewa a daren nan,dan kuwa kwana ya yi jinyar Afrah da ke fama da zazzafan zazzaɓi wanda Mama Tani kanta bata rintsa ba,tinda ba ta san ma a ina zata tare ba,dan har dare ya raba biyu bata keɓe da nata angon ba ballantana ta san tsare-tsarensa. Washegari da safe Bala ya ɗauki Afrah a mota ya kai ta asibiti aka saka mata ruwa,yana ƙarewa aka rubuta musu magunguna,likita ya yi mata gargaɗi sosai akan ta cire damuwa a ranta,domin kuwa jininta ya na gaf da hawa,cike da jimami suka koma gida. Sai da yamma ne ta fara samun ƙwarin jikinta ta samu Bala ta damƙa masa makullin gidanta ta ce ta mallakawa Baba Musa ya tare a ciki shi da Mama Tani,kallonta kawai Bala ya hau yi ya kasa cewa komai saboda mamaki,gidan da ta hana dangin ta na uwa da uba zama a ciki,gidan da take ji da shi take ganin kamar za ta wayi gari a ce iyayenta sun dawo rayuwa a cikin sa shi ta iya ɗauka ta bawa mahaifinsa ya zauna a ciki? Anya Afrah na cikin hayyacinta kuwa? Ko dai zazzaɓin ƙwaƙwalwa ne ya kama ta? A sanyaye Bala ya ce. "Afrah kin kuwa san me kike yi a yanzu? Gidan ki fa da kika gada a wajen iyayenki da kika hana kowa kika bawa Babana ya zauna a ciki?" Murmushi ta yi,sannan ta gyara kwanciyarta ta ce. "Cewa na yi ka basu su zauna a ciki ai ba cewa na yi na basu gaba ɗaya kyauta ba,ballantana ka yi mamaki." "Na fahimce ki sarai Afrah,na ga ko ƴan haya ƙin sakawa kikai saboda yanda gidan ke da mahimmanci a wajen ki." "Su ma mutane ne masu mahimmanci a wajena Bala,dan Allah ka je ka kai musu makullin ka ga suma fa sabbin aure ne kamar mu." Afrah ta ƙarasa maganarta cike da barkwanci,hararar ta Bala ya yi kafin ya ce. "Ah ah fa Afrah banda tsokana dan zan faɗawa Abbah na me kika ce." Baki ta rufe ta na dariya ƙasa-ƙasa,ta juya masa baya. Cikin sauri ya damƙe makullayen gidan a hannunsa ya nufi wajen Baba Musa ya damƙa masa tare da sanar da shi abinda Afrah ta ce. Baba Musa ya yi murna sosai saboda dama yana tunanin yanda zai ci gaba da zama da Tani a ɗaki ɗaya da banɗaki,shi da yake da burin bata rayuwa mai kyau ya faranta mata har ta manta da ƙuncin da ta shiga a baya. Godiya tare da sanya albarka Baba Musa ya dinga yi wa Afrah,dan kuwa har cikin gidan ya shiga suka haɗu da Mama Tani suka yi ta godiya,daga ƙarshe Afrah ta ce. "Dan Allah ku dena yi min godiya haka kuna sani jin kunya,kar ku manta gaba ɗayan mu nan alfarmar mutum ɗaya muke ci wato Lamyah,ita ce ta yi sanadiyyar shigar mu cikin farinciki har ta koyar dani yanda zan bayar da abu mai mahimmanci a rayuwata ko da kuwa ba kyauta bace ta dindindin. Dan haka mu haɗu mu godewa Allah sannan mu bita da addu'a a duk inda take za ta riske ta." Da wannan kalaman Baba Musa ya taya Tani kwasar kayanta suka nufi gidan Afrah suka gyara shi a tare,da dare Baba Musa da Bala suka kwashe katifu da sauran kayan dake ɗakin da suka yi zama a ciki suka mayar gidan Afrahn. Bayan sun yi wa junan su sallama ne kowa ya saci jiki ya tafi siyowa amaryarsa kazar amarci. *Niger republic.* Da misalin ɗaya na dare jirgin su Lamyah ya sauka a Niger,bayan sun gama duk wani abu da ya dace a airport suka nufi wajen kayan su suka ɗiba,suna fitowa waje suka tarar da drivern gidan Abii yana jiran su,sai da aka loda kayan su a bayan mota sannan suka ɗauki hanyar unguwar su Abii. Har a wannan lokacin Lamyah bata dena sharar ƙwallar kewar su Afrah ba,wani ɓangare na zuciyarta kuma cike yake da son ganin Momma da Iya da Yah Amee ɗinta. Suna dosar gidan Abii Lamyah ta ji ƙirjinta na wata iriyar bugawa kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito waje. Hannunta kuwa ya ɗauki zufa kamar ta yi wasan ruwa. A bakin katafaren gidan Mus'ab direba ya tsayar da motar yana danna oda,babu jimawa mai gadi ya buɗe ƙaton gate ɗin gidan direba ya shigar da mota ciki,hamdala Abii ya yi a bayyane sannan ya kalli Lamyah da ke rarraba idanu tana tunowa da rayuwar su ta baya da ta shuɗe,nan take ta tina yanda suke guje-guje a tsakar gidan ita da Yah Amee ɗinta,wasu irin hawaye ne suka hau zubo mata wanda ta kasa tantance na menene. A hankali ta saukar da ƙafafunta daga cikin motar bayan Abii ya buɗe mata fuskarsa ɗauke da maɗaukakin farinciki. Momma ce ta fito sanye da wani irin yadi mai laushi fari ƙal sai walwali yake yi fuskarta ta sha ƙwalliya bakin ta jawur da shi saboda jan janbakin da ta saka,kyawawan haƙoranta da suka sha haƙorin makka take ta washewa ta nufi inda Lamyah ta ke ta rungumeta,ƙanƙame Momma Lamyah ta yi kamar za ta shige cikin jikinta ta fashe da kukan murna,ita kanta Momma hawaye ne suka fara zubo mata na tsananin farincikin ganin Lamyah da ta ɗauki tsawon shekaru bata ganta ba. Iya na gefe tana sharar hawaye tare da face majina,Abii ne ya ce. "To Shatu a sake ta haka ta shaƙi iska don Allah,ga Iya nan tsaye tana jira itama ki ɗan sammata waje ta rungume jikarta." Dariya suka yi gaba ɗayan su,Lamyah ta tafi da gudu ta rungume Iya da ke kuka wiwi saboda tinawa da Aminee da ta yi,Lamyah gaba ɗaya ta ɗakko sifar jikin Aminee, sai dai hasken fata da ta fi mahaifiyarta. A haka suka rankaya suka shiga cikin gidan Mubarak na ta mitar babu wanda ya kula shi. Abii ne ya ɗauke shi yana lallashinsa tare da cewa. "Rabu da su, za su zo ne suna son ɗaukar ka ni kuma na hana,tinda sun fifita ƴar su akan ka." Momma na dariya ta kama hannun Mubarak tana sumbata ta ce. "Ka yi haƙuri muna son ka sosai,mun jima bamu ga yayarka bane shi yasa." Suna shiga ciki Lamyah ta kalli Momma ta ce. "Momma wai ina Yah Amee ɗina ne har yanzu ban gan shi ya zo tarbona ba?" Cikin sauri Momma ta kalli Abii dan neman agaji,dan kuwa bata san amsar da za ta bawa Lamyah ba a daidai wannan lokacin.........[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 31. Shirun da ta ga sun yi ne ya sanya ta kallon Iya tana neman ƙarin bayani daga wajen ta,da sauri Momma ta ce. "Mu je ki ci abinci ki yi wanka ki huta,da kansa zai shigo ya ga Lamyahnsa." Murmushin jin daɗi Lamyah ta yi,Momma kuwa ta sakarwa Iya kallon gargaɗi,ɗauke kai Iya ta yi kamar bata gani ba,ta ci alwashin sai ta sanar da Lamyah komai,saboda ta fara shirya ta ta yanda za ta karɓe ragamar Aminullahi a hannun Layuzah,dan kuwa Iya ta gama yarda da amincewa duk halayyar da Aminullahi ya tsiro da ita a cikin wata ɗaya da aurensa da Layuzah akwai wani ƙulli a ciki,duba da yanda ya taso zuciyarsa cike da son kowa da ƙaunar iyayensa har da masu yi musu hidima musamman ita,amma ace yanzu baya ganin kowa da gashi,babu kuma wanda ya tsani ya buɗi ido ya gani a gidan sama da ita,to tabbas ba a banza aka barsa ba,kuma sai ta karya alkadarin Layuzah a idanunsa ko ba jima ko ba daɗe. Ɗaki na musamman aka ware saboda Lamyah,ɗaki ne da yake kusa da na Iya wanda ke a parlourn farko na shiga gidan,duk wani kayan alatu da more rayuwa an saka a ɗakin,hatta da fridge madaidaici akwai a ciki,an shaƙe shi da kayan motsa baki kama daga kan chakulan har zuwa kayan marmari an zuba. Makeken gadon da ya ji shimfiɗa ta alfarma Lamyah ta kalla,a hankali ta taka ta isa gaban gadon ta zauna a bakinsa,cike da sha'awar ɗakin take kallon ko ina,kayan ta Zahrah ta shigar mata sannan ta gaishe ta cikin washe baki,murmushi Lamyah ta yi mata tana son tina inda ta san fuskar ta amma ta kasa tinawa,dake Zahrah ta girme ta sosai sai ta samu kasan carpet ta zauna ta na cewa. "Baki gane ni ba ko?" Ɗaga kai Lamyah ta yi tana murmushi. "Allah sarki,ai dake lokacin da kuka bar nan kina da shekaru biyar shi yasa ba za ki tuna ni ba. Suna na Zahrah ɗaya daga cikin yaran wanda suka yi aiki a ƙarƙashin mahaifinki balarabe,na ji labarin rasuwar sa a wajen Hajiya,Allah Ya jiƙansa ya sa aljannace makomar su baki ɗaya." "Amin Ya Allah Aunty Zahrah,na gode." Cikin sauri Zahrah ta kalli ƙofar shiga ɗakin ta kama baki sannan ta ce. "Rufa min asiri ki daina kirana da Aunty,ki kira ni da Zahrah kawai. Ni zan wuce idan kina buƙatar a yi miki wani aikin ki kira ni. Ki huta gajiya." Godiya Lamyah ta yi mata sannan Zahrah ta bar ɗakin,ta na yabawa da sauƙin kai irin na Lamyah, cikin jin haushin halayen da Layuzah ke yi a yanzu ta ce. "Humm shi dama wanda ya gaji arziƙi daban yake da wanda ya same shi a sama,matsiyaciyar nan duk ta manta alkhairin da na yi mata a rayuwarta har ta aure ɗan masu gida,amma yanzu ta haɗe da ni ɗin da masu gidan duk tana gara su yanda ta so,a juri zuwa rafi dai..." A tsaye ta ga Iya riƙe da ƙaton faranti ta ɗoro abinci da abun sha a kai za ta kai wa Lamyah,cikin sauri Zahrah ta karɓa ta na yi wa Iya sannu,godiya Iya ta yi wa Zahrah sannan ta wuce ta yi sallama a bakin ƙofar ɗakin Lamyah,jin ba a amsa mata bane ya bata tabbacin ta shiga wanka. Tura ƙofar ɗakin ta yi sannan ta ajiye abincin,har za ta bar ɗakin Lamyah ta fito ɗaure towel a jikinta fuskarta da hannayenta da ruwa da alama alwala ta yi,kallon uban abincin da aka kawo mata ta yi ta zaro ido waje. Cikin sauri ta ce. "Wannan abincin duk ni aka kawowa a wannan tsohon daren? Ƙarfe ɗaya da rabi fa,noo ya yi yawa please." Takawa ta yi zuwa wajen farantin ta hau buɗe abinda ke ciki,abinci ta gani kala wajen huɗu,sai fruit salad da farfesun naman kaza,ɗaukan fruit salad da farfesun ta yi,sai ta ɗauki juice ɗin da Iya ta haɗa mata na musamman a jug da cup ɗaya,ɗaukan farantin ta yi ta miƙawa Zahrah ta ce. "Wannan ma sun ishe ni,na gode,a ajiye min sauran da safe a ɗumama min zan ci,ina Mubarak?." "To za a yi yanda kika ce,ya na can ɗakinsa Hajiya ta na basa abinci." Zahra ta amsa mata ta bar dakin cike da sha'awar halayen Lamyah na rashin girman kai da girmama na gaba da ita. Kitchen ta nufa kai tsaye ta ajiye komai cikin fridge da niyyar gobe ta ɗumama wa Lamyah kamar yanda ta buƙata,ɗaki ta wuce ta kwanta tana hamma,lallai ta sha aiki a wannan rana,amma bata damu ba saboda wadda ta yi domin ta ta yaba. Iya ma ta so ta shiga ɗakin ta kwanta da Lamyah kamar yanda suke yi a baya lokaci zuwa lokaci,sai dai sam ta kasa ko da zuwa ƙofar ɗakin ta saboda tsoron kar Lamyah ta ƙi hakan,bata da tabbas akan sauyawar halayyarta,amma dai tana kyautata mata zato. Ɗakinta ta shiga ta kwanta tana miƙe ƙasusuwan bayanta,zuciyarta fal tinanin abinda zai je ya dawo har bacci ya ɗauke ta. Lamyah kuwa sai da ta yi sallah sannan ta zauna ta hau shan fruit salad tana cin farfesun naman tana lumshe ido,Afrah ce ta faɗo mata a rai,za ta so ta sha irin haɗin nan na musamman wanda madarar har wani kauri take yi saboda yanda aka zuba ta da yawa,da alama madarar da aka zuba suna da yawa,dan duk yanda madara take tana gane ɗanɗanonta tsabar yanda take son harkar madara. Wayarta ta ɗakko ta yi masa video sannan ta turawa Afrah ta WhatsApp tare da yi mata dogon rubutu na yanda take kewarta da kuma fatan da take a ranta dama suna tare a wannan lokacin. Tana gamawa ta kashe data ta kwanta bakinta ɗauke da addu'ar bacci. Washegari da asuba tana yin sallah ta sake komawa bacci,ba ita ta farka ba sai ɗaya na rana,shima saboda ta riga ta saba ko period take yi idan lokacin sallah ya yi sai ta farka. Banɗaki ta shiga ta yi wanka tare da wanke bakinta ta kurkure da mouth wash sannan ta fito,duba lokaci ta yi ta ga ƙarfe biyu ta kusa,da sauri ta zira doguwar riga ta yi sallah,tana idarwa ta yi addu'a sannan ta hau ninke sallayar. Ta na nan tsaye ta ji an buɗe ƙofa,ta na juyawa ta ga Mubarak ya tafi da gudu ya rungume ta,cikin jin daɗi da murna ya ce. "Mommy na zo wajen ki sau sha goma na ga kina ta bacci,Momma ta ce kar na tashe ki kin gaji." "Hhhh sau sha goma fa yana nufin sau ashirin Mubarak,to gani na tashi me ka tanadar min?" Sallamar Iya da Zahrah ce ta sanya ta ɗaga kai ta kalle su fuskarta cike da murmushi. Kafin su gaishe ta ta yi saurin gaishe su,amsawa suka yi Zahrah ta ajiye mata abinci a saman center table ɗin da ke da kujera a gabansa,sannan ta ce. "Idan kin gama cin abincin zan zo na taya ki gyara kayan ki idan babu damuwa." "Ah ah kar ki ji komai,zan gyara da kaina,ai ba su da wani yawa ma,dama kayan wannan yaron ne suka fi yawa." "To idan haka ne ki bata kayan nasa ta je ta jera masa a ɗakin sa,dan kuwa tin jiya Hajiya ta gyara masa ɗakin aka zuba kayan wasa da duk abinda zai buƙata." Wani irin farinciki ne ya lulluɓe Lamyah,irin wannan gatan take so take fatan samu,ba dole sai an wadata su da dukiya ba,ah ah kulawa da soyayya kawai suke so a matsayin su na waɗanda suka rasa iyayen su,musamman Mubarak da ba zai iya ɗorar da komai ba a kan su. Akwatinan kayan sa ta nuna wa Zahrah,ita kuwa ta kashe ta kai can ɗakin dake ɓangaren su Momma ta fara gyara masa kayan. Lamyah kuwa tana cin abinci ta na ta yi wa Iya tambayoyi,dan kuwa abubuwan da take iya tinawa a rayuwar da suka yi a baya ba wasu masu yawa bane sosai,Iya ce ke ta tina mata abubuwa,ita kuwa tana ta dariya saboda yanda ta ji abubuwan rashin jin da ta yi a baya. Shiru Iya ta yi tana kallon ta cike da ƙauna ta ce. "Na ji daɗi da kika dawo gida Lamyah,Momman ku ma zuwanta nan uku dan ta ga ko kin tashi? Sai ta ga kina bacci,sai ta ce kar a tashe ki a barki ki ki huta har sai kin tashi da kan ki." "Allah sarki Iya,ni ma na ji daɗin dawowa ta inda ake ƙaunarmu aka sam darajarmu ni da Ɗan'uwana,yanzu babban fata na da buri na bai wuce na sanya Yah Amee ɗina a ido na ba,ina so in ga

Chapter 18 of 30