Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su ya bar hotel ɗin a zafafe. Tinda suka kama hanya Lamya ke kuka,cikin ɓacin rai da hargagi Aminullahi ya buɗe baki ya faɗawa Lamyah kalaman da suka tarwatsa zuciyarta suka sanya ta dakatawa da shaƙar numfashi na wucin gadi.......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 21. "Malama kin cika min kunne da wannan kukan munafurcin naki!da kin san baki shirya fita yawon karuwanci ba kika fito? Ke ki ka kai kan ki wajen maza,kuma mazan sun biyo ki kin zo zaki ishi mutane da kukan banza,kina abu kamar wata mutuniyar kirki,an faɗa maki kalmar mutumin kirki a baki kawai take yin aiki? To bari ki ji na faɗa maki kafin a kira mutum na kirki sai imaninsa ya fito fili,ayyukansa sun bayyana halayyarsa,a sannan ne mutane za su kira mutum da na kirki ko da kuwa a baɗininsa mutumin banza ne. Meye amfanin rawa da waƙa da kuka jefa kan ku a cikinta ke da wannan ƙyarmasasshiyar kuna yara mata?" Dukan da kalaman sa suka yiwa zuciyarta ne ya sanya ta ƙamewa,hatta da sautin fitar nufashinta ya daina gilmawa a cikin motar,Aminullahi kuwa bai yi shiru ba har sai da ya isa ƙofar gidanta ya tsayar da motar a fusace ya ce. "Fitar min a mota ƙazamar banza kawai,yara ƙanana daku amma kun dage sai kun lalace kun lalata wasu. Mtsewwww." Hawayen dake ambaliya a kuncin ta ta share domin ta ga hanyar da za ta taka ƙafafunta da kyau,tinda Lamyah take babu wanda ya taɓa yi mata tsawa ballantana faɗa,ballantana kuma a kira ta da miyagun sunaye da kalamai irin yanda Aminullahi ya yi,tana ɗora ƙafafunta a ƙasa sai ta ji jiri yana kwasarta ƙafafunta na rawa,a daidai wannan lokacin kuwa Aminullahi ya gama suƙurewa yana tsananin son ta fita ta bar masa motarsa ya wuce gida,cike da ƙunar zuciya ya buɗe ɓangaren direba ya isa inda take ya buɗe mata motar sannan ya ce. "Za ki fita ne ko kuma wani sharrin irin naku na karuwai za ki yi min a mota?" A daidai wannan lokacin motar Lamyah ta tsaya a gefen ta Aminullahi,Afrah ce ta fito cikin sauri ta nufi inda Lamyah ke zaune tana zubar da hawaye,domin kuwa a tare suka tafi ɗakkota da Bala,suna zuwa kuma Faisal ya labarta musu duk abinda ke faruwa,hannayen Lamyah Afrah ta kama ta ji su sun yi sanyi ƙalau,ga kuma wata iriyar zufa da take yanko mata a goshinta,jikin su na rawa gaba ɗaya suka rungume juna suna kuka,a haka Afrah ta kama Lamyah za su shige gida,Baba Musa na buɗe musu gate Aminullahi ya shiga motarsa zai wuce,a daidai wannan lokacin ne Lamyah ta juya idanunta na zubar da hawaye ta kalle shi da wani irin kallon da ya kasa fassara shi,hasken fitilar motarsa da ya haske masa fuskarta ne ya sanya gabansa yin wata iriyar mummunar bugawa,gaba ɗaya kamanninta sai suka sauya masa,tinanin inda ya san mai kamanninta ya fara yi,ita kuma a daidai wannan lokacin suka shige gida ita da Afrah. Jiki a sanyaye Aminullahi ya ja motarsa ya wuce zuciyarsa fal tunani kala-kala. Su Lamyah na shiga cikin gida ɗaki ta wuce ta faɗa saman gado ta rushe da wani irin azababben kuka mai cike da ciwon kai da zuciya,kalaman Aminullahi ba ƙaramin ƙona zuciyarta suka yi ba,kalmar karuwa da ya jingina mata ta rusa duk wata sha'awa da ƙaunar rawa da ta taso da shi,kalmar ta sanya ta tinawa da Aminee da take nuna mata illar rawa tin tana ƙarama,amma ta dinga rintse ido,dama idan mace ta zaɓi rawa a matsayin abinda take son yi a rayuwa karuwa ce? Ko dai har yanzu mutane basu fahimci menene rawa da waƙa ba? Wata zuciyar ce ta ce mata,to ai dama rawa da waƙa shagala ne daga barin bautar Allah da gaskiya,rawa da waƙa duk wasanni ne da shaiɗan ya jefowa ɗan Adam dan kawai ya hana shi maida hankali wajen bautawa Allah,cike da tashin hankali ta tashi zaune ta kalli kanta a jikin madubin da ya zagaye ko ina na ɗakin nata ta ce. "Kenan hakan yana nufin ni karuwa ce da gaske kamar yanda ya kira ni? Kallon da kowa yake yi min kenan dama?" Muryar Afrah ta ji cikin kuka tana faɗin. "Ƙwarai kallon da mutane suke yi maki kenan,irin wannan kallon ake yi min shekara da shekaru,sai dai ni na toshe kunne na ne na zaɓi na faranta raina sannan na samarwa kaina abinda zan ci da kuma kula da kaina ba tare da na je na yi zina ba,ban iya sana'ar komai ba da kika ganni,rawa ita ce abinda na iya,ita ce abinda take kawo min manyan kuɗi a lokaci ɗaya,dan haka a lokacin da kowa ya juya min baya,dangi na suka ƙi su ja ni a jiki saboda na hana a saida min da gidan da na gada wajen iyayena,sai kowa ya janye ya dena tallafa min daidai da kuɗin siyan siga,ko kuɗin siyan kokon safe babu mai bani,mutanen unguwa kuwa dama basu taɓa tambayata shin tinda iyayen ki suka rasu kin ci abinci? Da wanne sabulu kike wanka da wanki? Ki na da buƙatar audigar mata ko kina so yau ki ɗan ci wani abu mai daɗi? Kowa ya rungume ɗan sa yana bashi rayuwar da yake so sun watsar da zumunci da haƙƙin maƙotaka,a lokacin da na samu tayin zuwa rawa kuma na karɓa na fara zuwa ina samun kuɗin da nake biyawa kaina buƙata yau da gobe,sai aka fara kirana da karuwa,ni kuma sai na toshe kunnena na bar su da Allah." Kuka ne ya ci ƙarfin Afrah,cikin sauri Lamyah ta sauka a gado ta nufe ta ta rungume ta tana lallashinta,sai da ta yi kuka sosai sannan ta share hawayenta da har a wannan lokacin basu dena zuba ba ta ce. "Ke kina da zaɓi Lamyah,Allah Ya hore maki arziƙin da ba sai kin fita nema ba,na tabbata daga nan har ƙarshen rayuwar ki ba za ki wulaƙanta ba matsawar za ki yi rayuwa babu almubazzaranci,a yanda nake jin mutane na maganar dukiyar mahaifin ki,an ce ko yara kika haifa nan gaba ba za ku kasance cikin babu ba,to kin ga baki da dalilin fita rawa,amma ni fa? Yanzu ko mijin aure na samu to fa dole ni zan yiwa kaina kayan ɗaki da duk wani abu da dangin uwa ko uba za su yi min. Dan haka....." Cikin hanzari Lamyah ta katse ta da faɗin. "Na yanke shawara zuwa Juma'ar nan ta sama zan je dangin Ammi,idan sun karɓe mu ni da Mubarak shikenan nima na huta da amsa tambayoyinsa akan wanene mahaifinsa da yake yi min a koda yaushe. Idan kuma ba su karɓe mu ba zamu dawo mu jira hukuncin Allah tare da fatan Allah Ya bayyana min Abi da Yah Amee ɗina a duk inda suke." Hawaye ta share ta faɗa banɗaki ta zauna a bakin kwamin wankan dake ciki ta hau rusa kukan baƙin cikin kalaman Handsome ɗin da ya gama nakasa zuciyarta da zazzafar soyayyarsa da bata san sanda ta yi mata mummunan kamu irin wannan ba,wani irin yanayi take ji mai cuɗanya da juna,yanayi ne mai matuƙar zafi da ƙuna. Yaushe ta yi sakaci har ta kamu da son wani namijin bayan Yah Amee ɗinta da take fatan ya zame mata miji har ƙarshen rayuwarta? Ya za ta yi da kallon karuwa da mutumin da ta fara so a ranta yake yi mata? Kayanta ta cire ta haɗa ruwan wanka ta shige,sai da ta gasa jikinta sannan ta cuɗa jikin nata sama-sama saboda rashin ƙarfin jiki da ke damunta,sannan ta fito ta ɗaura alwala ta yi brush. Tana fitowa ta ga Afrah ta fito mata da kayan da za ta saka har da hijabi,tare da shimfiɗa mata abun sallah,murmushi ta yi hawaye na sake zuba a idanunta da suka kumbura suka yi jawur. Tana gama shiryawa cikin doguwar rigar baccinta mara nauyi,sai ta fesa turarukanta masu ƙamshi sannan ta tada sallah,ta jima tana addu'o'i a cikin sallar ta kafin ta naɗe abun sallar ta tashi, addu'ar bacci ta yi ta haye gado,dan ko abinci ba za ta iya ci ba. Afrah kuwa na can ɗakinta itama tana tina yanda rayuwa ke garata ta kowanne ɓangare,shin laifi ne ka zamo maraya? Me yasa mutane yanzu kansu kawai suka sani da iyalansu? Me yasa idan sun ƙi taimakon mutum ya samarwa kansa mafita sai kuma su dawo suna zagin sa? Ta tabbata ko da sana'ar arziƙi take yi a cikin gida matsawar za a shiga za a fita a gidanta to fa sai an samu masu zargi da zagin ta, to wai shi ɗan Adam me za a yi masa a burge sa? Da waɗannan tarin tambayoyin bacci ya ɗauke ta. Ta ɓangaren Aminullahi kuwa tinda ya koma gida hankalinsa yake a tashe,saboda ganin kukan da Lamyah ke yi ba iya na abinda ya sameta bane,har da maganganun da ya gasa mata,to ai ba ƙarya ya yi ba karuwa ce,karuwa ita ce kaɗai za ta je gaban maza tana girgiza jikinta tana lanƙwashewa kamar yanda suke yi. Wani irin raɗaɗi zuciyarsa ke yi masa,ya rasa yanda zai yi ya cire yarinyar daga ran sa,saboda yawan tinaninta da yake yi ne ya sanya shi yin bincike akan ta a wajen Faisal,Faisal kuwa ya tabbatar masa da cewa ita da Afrah uwar su ɗaya uban su ɗaya kuma duk sun rasu,shi yasa ma da ya yi ƙoƙarin zurfafawa a tinanin inda ya santa yake kawarwa,sai ya ɗauka kawai wataƙila tana kama da wata customer ɗinsa ce shi yasa yake yi mata kallon sani. Washegari da safe gaba ɗaya mutane ukun nan sun tashi zuciyoyin su babu daɗi,Afrah ma ko parlour bata fito ba saboda tinawa da mahaifanta da ta yi,Bala shine wanda ya fita ya samo musu abin karyawa kafin ya wuce makaranta dan ya kula har wannan lokacin Mama Tani bata tashi ba itama. Yanayin yanda Mubarak ya damu ne ya sanya Lamyah sakkowa daga gado suka je parlour ta haɗa masa abinci ta basa,ƙin ci ya yi ya dage tare za su ci,gani ya yi ta fara zubar da hawaye sai kawai shima ya fashe mata da kuka,jin kukan da suke yi ne ya sanya Afrah fitowa a rikice,ganin su a wannan halin ya yi matuƙar karya zuciyarta, dika-dika shekarar Lamyah sha takwas ko sha taran bata ƙarasa ba,ita kanta tana buƙatar wanda zai zame mata garkuwa a duk sanda ta shiga ƙunci,tinawa da hakan ne ya sanya Afrah ƙwarara kanta ta isa gare su ta haɗe su ta rungume,a haka Tani ta same su,cike da damuwa ta hau tambayar abinda ya faru,dan duk abinda ake yi jiyan tana ɗaki tana sharar baccin gajiyar ayyuka. Afrah bata ce mata komai ba sai kawai ta miƙa mata Mubarak ta wuce kitchen,abinci ta zubawa kowa har Mama Tani ta miƙa mata sannan ta kalli Mubarak ta ce. "Kai ɗan ƙundale sakko ka ci abinci in ba haka ba na yi maka ɗura." Yana jin ta kirasa da sunan tsokanar da take kiransa da shi sai ya yi murmushi idanunsa taf hawaye,cikin dariya irin ta yara shima ya rama da sunan da Bala ya ce masa ya dinga kiranta da shi a duk sanda ta ce masa ɗan ƙundale. "To falwaya." Duka ta kai masa ya gudu wajen Lamyah yana ƙyalƙyala dariya,ganin dariyar yaron ce ta sanya Lamyah murmusawa,haka suka dinga zagaye parlour shi da Afrah har sai da suka gaji sannan suka zauna suka hau cin abinci. A ranar suka fara haɗa kayan su da za su yi tafiya Rijiyar Lemo da su. Ranar Juma'a na zuwa Afrah ta tada Mama Tani da wuri ta ɗora abincin karyawa,ita kuma ta yiwa Mubarak wanka ta shirya sa tsaf suka fito hannunsa cikin nata sai murna yake yi,dan kuwa Lamyah ta sanar da shi inda za su je. Suna kammala shiri Lamyah ta yi wa kowa sallama ta shiga mota ita da Mubarak,Bala ya ja su suka wuce Rijiyar Lemo. Sun isa da misalin tara da rabi na safe,a lokacin wasu daga mazajen unguwar na wajen Mai Unguwa,motar su na tsayawa Bala ya fita da sauri ya buɗewa Lamyah ta fito,sanye take cikin doguwar riga ƙirar Dubai ruwan makuba sai zabga sassanyan ƙamshi take,hannun Mubarak ta riƙe suka tako zuwa fada. Yanda ta ga Bala ya durƙusa itama sai ta samu waje ta durƙusa a gefe. Ido Mai Unguwa ya kafe ta da shi yana so ya gano da wa yarinyar ke yi masa kama. A hankali Bala ya buɗe baki ya gaishe su tare da gabatar da Lamyah a gare su,nan take Mai Unguwa Haladu ya kalle ta da sauri idanunsa na tara ƙwalla,cike da jimamin labarin rasuwar El-mustapha da Aminee da ya gama ji ya ce. "Tabbas ! Waɗannan yara jinin El-mustapha da Aminatu ne babu ja,ga kamanni nan sun bayyana hakan,tin kafin ka faɗa na ga ta yi min kama da wanda na sani amma na kasa tina waye,ashe jikata ce,kai Malam Ayuba a je a kirawo Malam Abubakar da Lado da Ɗantiye,su zo ga ɗiyar ɗan'uwansu ta dawo,sannan ka biya gidan Delu ka sanar da su abinda ake ciki,idan da hali dika su zo nan ina da buƙatar ganawa da su kafin in miƙa musu riƙon wannan yarinya da ɗan'uwanta." Cikin sauri Malam Ayuba ya miƙe ya nufi cikin unguwa dan isar da saƙon Mai Unguwa zuwa ga dangin Lamyah........... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 22. Bala ne ya yi wa Lamyah da mutanen wajen sallama ya koma saboda yana da jarabawa 12-2pm,Lamyah ji tayi kamar ta bisa su koma musamman da ta waiga ko ina ta ga ita ɗaya ce sai Mubarak babu Afrah a tare da ita,sai take jin wani irin tsoro da fargaba na mamayarta. Gidan Malam Muhammadu shi ne a kusa,dan haka a ƙofar gidan Malam Ayuba ya tsaya tare da sallamawa masu gidan,ya jima yana kwaɗa sallama babu wanda ya amsa masa. Yana nan tsaye saddiƙa ta dawo daga talla hannunta riƙe da bokitin nan da ake kira kande tsirara,wasu kuma su kira shi da fallasa talla,fuskar ta cike take da kwalliya sai tauna chewing gum take yi tana ƙas tare da ƙwai,kallon Malam Ayuba ta yi daga sama har ƙasa ta watsar za ta shige cikin gidan nasu,cikin sauri ya dakatar da ita da faɗin. "Ko gaisuwa ma ba zan samu ba ko Saddiƙa? To in kin shiga ki turo min uban naki da Delu,saƙo ne daga mai unguwa yana neman su." Murguɗa masa baki ta yi ta shige cikin gidan cike da karya ƙugu da rashin kunya. Kaɗa kai kawai Malam Ayuba ya yi,dan kuwa ba yau ya san Saddiƙa ba wajen rashin ɗa'a da tarbiyya. Ya jima sosai a tsaye kafin Delu ta leƙo ta same shi yana ta yarte zufa. A sheƙe ta kalle shi sannan ta ce. "Lafiya ka ke ta banka mana sallama tin ɗazu kamar ka na bin mu bashi?." Baki ya saki cike da takaici,ashe ma sun ji sallamar tasa amma aka rasa wanda zai amsa masa,dan ya tabbata Hamzah na gida tinda shi dai ya kashe zuciyarsa da zaman banza,komai sai Delu ta yi masa,idan kuwa ya samo na kansa daga shi sai ƙananan yaran da yake lalatawa yake kashewa. Cike da ɓacin rai Malam Ayuba ya kalli Delu ya ce. "Mai Unguwa na son ganin ku ke da Hamzah." Gyara tsayuwa ta yi cikinta na ɗan kaɗawa,saboda tsoron ko ɗaya daga cikin ƴaƴan nata ko jikarta da take yiwa tsananin so ne suka jawo mata magana. Cikin ɓoye halin da zuciyarta ke ciki ta yatsina fuska sannan ta ce. "Akan wanne dalili ake son ganin mu? Ko kuwa dan yana taƙamar shi mai Unguwa ne sai kawai ya hau kiran mu fada babu bayani?" Murmushin takaici Malam Ayuba ya yi sannan ya ce mata. "Yarinyar wajen Aminee ce ta bayyana ita da ƙaninta,shi yasa ake neman ku,daga nan ma gidan su Lado da Ɗantiye zan je na sanar da su kiran Mai Unguwa." Gyaɗa kai kawai Delu ta yi ta koma ciki ba tare da ta ce masa komai ba. Malam Ayuba kuwa gaba ya yi yana Allah wadai da halayya irin ta Delu da ahalinta. Delu kuwa tana shiga cikin gida sai ta hau ƙwalawa Saddiƙa da Hamzah kira,a tare suka fito suna tambayar dalilin kiran,cikin sauri Delu ta ce wa Saddiƙa. "Maza kira min Lado a wayar ki,hanzarta kafin wancan ɗan iyan ya isa gidan sa,dan na san daga nan can ya nufa." Cikin gaggawa kuwa Saddiƙa ta kira mata Lado,yana ɗauka babu sallama ballantana gaisuwa ta ce masa. "Kai Lado kana nan gida ne ko ka fita?" 'Eh ina gida amma yanzu nake shirin tafiya kasuwa,dan har na sallami iyali ma.' "To maza ka gaggauta ka fita,ga ɗan aike nan daga fada ana neman mu,wai yaran wannan gantalalliyar ne Aminee suka zo neman dangin uwar su, shi ne ake neman mu,ni dai bani da wajen ajiye su balle abinda zan ciyar da su,idan kuma kai kana da yanda za ka riƙe su to sai ka tsaya har a same ka a gida." Delu na gama sanar da Lado ta kashe wayar sannan ta sa aka kira mata Ɗantiye ta sanar da shi abinda ta faɗawa Lado,ashar ya banka tare da faɗin. 'Sisina ba zai yi ciwon kai ba wajen kula da wasu yaran bayan nawa,su maida su can dangin uban su a riƙe su,mu dai ba masu ƙarfi bane.' Cike da farin ciki Delu ta kashe wayar ta samu waje ta zauna ta na yiwa Hamzah bayanin abinda Malam Ayuba ya sanar da ita. Ita fa a duniya babu wanda ta tsana sama da Tabawa da zuri'ar ta,ta jima tana murna da Aminee ta bar gida,tare da fatan Allah Ya sa ba za ta dawo ba har abada,kwatsam kuma sai a ce zuri'ar ta sun zo ganin dangi? Inaa hakan ba za ta taɓa yuwa ba,wa ma ya sani ko talauci da babu ce ta ishe su shi yasa suke neman dangin uwarsu? Shima bayan mahaifiyarsa ya bi,dan ba zai yarda wasu su zo su takurawa yarinyarsa da yake ji da ita ba. Malam Ayuba na isa gidan Lado sai ya tarar da shi a ƙofar gida faram-faram zai tafi kasuwa,cikin sauri ya ƙwala masa kira ya juya fuskar nan a murtuke kamar hadari,cikin tsananin ɓacin rai ya tari numfashin Malam Ayuba ya ce. "Ka ga Ayuba,ni fa babu yaran da zan iya riƙewa a wannan marra da muke ciki ta hannu baka hannu ƙwarya,kai bari na fito maka a mutum idan ita Delun ta kasa yi maka bayani,mu ba za mu riƙe mata yara ba,idan tana so a riƙe mata yara sai dai ta dawo cikin danginta ta baro duk inda ta tafi,shi kanshi Ɗantiye ba iya riƙon su zai ba,dan ka fi kowa sanin yanda yake fama da rayuwa tinda abokin ka ne,to a ina zai samo abinda zai ci da yara har biyu? Ko kuwa Delun da ke zawarci take ci da gidanta da ƙyar za a ɗorawa nauyi? Ai dama mun faɗa muku har mai Unguwar idan har ta auri wannan balaraben to babu mu babu ita,ballantana wata zuri'ar ta,dan haka kar ka matsa mana yin abinda bamu da niyya,ka koma ka sanar da Mai Unguwa ba za mu samu damar zuwa ba dan bamu da buƙatar su a cikin zuri'ar mu." Yana gama zazzaga rashin mutuncin da zai yi ya sa kanshi kudu ya wuce kasuwa yana ta surutai shi kaɗai. Jiki babu ƙwari ya wuce gidan Ɗantiye dan ba zai biye wa Lado ba,dole sai ya je da ƙafarsa ya isar da saƙon Mai unguwa,rashin mutuncin da Ɗantiye ya yi wa Malam Ayuba ya fi ƙona masa rai a matsayinsa na babban abokinsa,dan haka cike da ɓacin ran su ya koma fada ya sanar da Mai Unguwa da su Malam Abubakar abinda suka ce,hawaye Lamyah ta fara zubarwa ta na shessheƙar kuka,cikin tsananin tausayawa da jimanta lamarin Mai unguwa da su Malam Ayuba suka dinga bata haƙuri tare da bata labarin zuwan su Mus'ab neman su,itama sai ta basu labarin abinda mahaifinta ya ce kafin su rabu,ganin tana kuka tana magana ne ya sanya Mubarak ɓara baki shima ya hau kuka tare da ce mata su tashi su bar wajen su koma gida,rungume sa ta yi a ƙirjinta tana sake fashewa da wani sabon kukan,a ganinta ai ya kamata a ce kafin dangin mahaifiyarta su ƙi karɓar su sun zo sun gan su ko da sau ɗaya ne,sannan ita babu nauyin da za ta ɗorawa kowa,hasali ma so take yi ta basu wani kaso na daga dukiyar ta tinda Allah ya hore musu,sai gashi sun juya musu baya tin kafin su ɗora ido akan su. Suna tsaka da lallashin Lamyah ne wani ɗan acaɓa ya tsaya a fadar ɗauke da wani kyakkyawan matashi baƙi,matashin ne ya sauka a saman machine ɗin yana murmushi ya sauke jakarsa ƙasa,kayan bautar ƙasar da ya sanya ba ƙaramin kyau suka yi masa ba,hular shi ya cire ya ɗauki jakarsa ya ƙaraso gaban jama'ar dake fadar ya durƙusa yana gaishe su,cike da fara'a tare da maɗaukakin farin ciki suke amsa masa gaisuwarsa,Mai Unguwa kuwa ji yake yi kamar ya tashi ya rungume gudan jinin nasa a jikinsa. Murmushi matashin ya sakar masa tare da faɗin. "Allah Ya nufa yau an kammala bauta wa ƙasa Abbah." Addu'o'i masu daɗi mai Unguwa ya hau yiwa ɗan nasa tare da faɗin. "Ka shawo hanya maza ka shiga cikin gida ka huta,gyatumar ka da ƴan'uwanta suna nan sun girka maka kayan daɗi an hana ni saboda zuwan ka,na ce ahaf kwana nawa ne zai jere da mu a ci tuwon dawar da shi kafin Allah ya kawo aikin yi?" Dariya mutanen wajen suka sanya gaba ɗaya,har da Lamyah da ta takure rungume da Mubarak sai da ta yi murmushi. Matashin ma dariya ya yi ya ɗauki jakarsa zai wuce ba tare da ya kula da Lamyah da ke zaune can gefe ba,har ya yi gaba Mai unguwa ya kira sa ya ce. "Musaddiƙ ga baƙuwa nan, ƴar'uwar ka ce itama,ka yi mata jagora ku shiga ciki gani nan zuwa,a bata ruwa da abinci dan Allah." A daidai lokacin da Lamyah ke shirin miƙewa ne ta sanya hannu ta yaye fuskar ta da mayafinta ya rufe,idanun Musaddiƙ na sauka a kan ta ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya,tsananin kyawun da Lamya ta yi masa ne ya kiɗima shi har ta gaishe sa bai san tana yi ba,sai da Malam Abubakar ya zunguri ƙafarsa sannan ya dawo cikin hayyacinsa,a ɗan daburce ya duƙa ya ɗauki akwatinta ya haɗa da jakarsa sannan ya karɓi Mubarak da ke hannunta,gaba ya yi Lamyah na binsa a baya,suna shiga gidan ta ga tsakar gidan fankacece mai yalwa,a share yake tasss kamar babu yara simintin sai ɗaukan ido yake yi kamar ana wanke sa kullum,ɗakuna ne guda biyar a kurkusa da juna,biyu na kallon biyu sai guda ɗaya da suka saka a tsakiya,sai babban madafi da makewayi,tare da wani ɗaki a can gefe guda ɗaya,da kuma ɗakin da yake a matsayin ma'ajiyar abinci wanda yake shaƙe da hatsi kala-kala. Gefen madafin itace ne mai tarin yawa a ƙulle,sai randinan ruwa manya da ƙanana. Matan gidan su biyu suna zaune suna hira tare da cin gyaɗa mai gishiri,sallama suka yi musu,murna matan suka miƙe suna yi tare da zabga guɗar farin cikin ganin Musaddiƙ ya dawo gida lafiya. Suna tsaka da murnar ne Innoh ta ɗaga labulen ɗakinta fuska a tsananin haɗe ta kalli Musaddiƙ ta ce. "Sannu mara hankali,ka dawo yanzu shine ka tsaya ƙannen uwar ka su sa maka albarka ba za ka iso ka ga uwarka ba ko? To da kyau,ita kuma wannan nunar ranar da nake gani tare da kai fa?" "Ki yi haƙuri Innohta ai gani nan yanzu zan shigo,shigo wa ta kenan fa ko minti ɗaya ban yi ba. Wannan kuma Abbah ne ya ce ta biyo ni na kawo muku ita sai ya shigo zai yi muku bayani." Hannu Innoh ta hau tafawa tare da faɗin. "Oh ni Innoh ! Allah ka tsare mu kar watarana Maigida ya ɗakko mana mayya a kawo mana cikin gidan nan ta bi dare duk ta lashe kurwar mu,ke Asabe ai sai ki ɗauki jakar ta ki aje min ta ɗana ki kai ta can ɗakin baƙi ko?" Cikin sauri wadda aka kira da Asabe ta ajiye jakar Musaddiƙ ta kama akwatin Lamyah da jakarta ta nufi ɗakin da aka kira da na baƙi da su,tana zuwa ta

Chapter 12 of 30