Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙwalla ƙara tana kiran Hajiya,Hajiya na fitowa daga ɗaki ta ga murnar da Layuzah ke yi sai ta washe baki tana faɗin. "Kin ga ɗan albarka masu aiki da maganar iyayensu ko? Maza to ɗauki akwatin ki ki je,sai mun yi waya,Allah ya baku zaman lafiya,kin dai ji wa'azin da Kawun ki ya yi miki ɗazu,kar na ji kin saɓa daga kan abinda aka ɗora ki, in kuwa kika je ki ka yi masa shiririta ya sako ki to ga ɗaki nan,sai ki zo mu jere kamar samira a kwabat." Da ƴan nasihohi suka rabu da Hajiya ta fita tana jan akwati,sai dai ta na zuwa ta yi turus ganin Lamyan zaune a gaban mota tana danna wayarta,wani abu ta ji ya taso ya tokare mata wuya,da sauri ta hau kokawa da shi har ta samu nasarar danna shi cikin cikinta,murmushin yaƙe ta saki sannan ta kalli Lamyah ta ce mata. "Ina wuni?" Cike da mamaki Aminullahi da Lamyah suka hau kallon juna,daga ƙarshe sai suka mayar da kallon nasu kan Layuzah,a kunyace ta sake gaishe su gaba ɗaya,cike da ladabi tana wani wasa da mayafinta. Ajiyar zuciya Lamyah ta sauke ta amsa mata gaisuwarta tare da tambayar mutanen gida. Aminullahi kuwa be buɗe mata mota ba sai da ya kalle ta ya ce. "Kin shirya sauya rayuwar da muka yi a baya ko kuma na wuce gida da matata na barki a naku gidan?" Wani malolon baƙinciki ne ya tokare wuyan Layuzah,idonta na zubar da ruwan hawaye ta durƙusa a saman guiwowinta ta ce. "Na yi alƙawarin duk wani halina mara kyau da ka sani,na tattara shi waje ɗaya na watsa masa fetur na cinna masa wuta na ƙone shi. In Shaa Allahu ba za ka sake samu na da wani mugun hali ba,don Allah ka yafe min,kema kuma Lamyah ki yafe min duk abinda na yi miki." Ganin yanda take kuka cike da nadama ne ya sanya Lamyah zira hannunta ta jikin Aminullahi ta buɗe lock ɗin motar,nan take kofofin suka buɗe,shi kuwa wani numfashi ya sauke saboda yanda ta ke gogar jikinsa,waje ta fita ta ɗaga Layuzah sannan ta kama akwatinta ta buɗe bayan motar ta saka shi ta taimaka wa Layuzah ta shiga motar,komawa mazauninta ta yi tana kiran sunan Allah a cikin ranta domin samun sauƙin kishin dake cin zuciyarta. Sai da Aminullahi ya ga sun zauna gaba ɗaya kowa ya yi shiru sannan ya ja motar suka wuce. A hanya Lamyah addu'a take yi a cikin ranta ta na faɗin. 'Ya Allah mamallakin ruhi da zuƙata tare da gangar jikin bayinsa,Ya Allah mai tasarrufi da juya lamuran bayinsa daga mummuna ya koma kyakkyawa,Allah ina roƙon ka ka sarrafa kishi na ya zamo na alkhairi,Allah ka yaye mana mummunan kishi da ni da abokiyar zamana,Allah ka sanya mana soyayyar junan mu da ƙaunar junan mu. Ya Allah ka sanya wa mijin mu soyayyata a ransa ta fi ta kowacce mace da zai aura a duniyar nan,Allah ka sa ya fi samun gamsuwa da cikakkiyar ni'ima a waje na sama da yanda zai samu a wajen kowacce mace a duniya,Ya Allah ka zaunar damu lafiya ka bamu zuri'a mai albarka,Allah ka bashi ikon yin adalci a tsakanin mu saboda ina son shi bana so ya saɓa maka.' Karar buɗe gate ɗin gidan su ne ya dawo da ita daga doguwar addu'ar da ta tafi yi,mota na tsayawa ta hau ƙoƙarin ɗaukar jakar food flask ɗinta za ta shige gida,ji ta yi Aminullahi ya kama jakar ya amshe,ba tare da ta ce masa komai ba ta yi gaba,sai da Layuzah ta kwashe kayanta ya kulle motarsa,jan akwatin ta yi ta shiga gida,domin ita bata wani damu da abinda ya yi ba,fatanta bai wuce ta shiga ɗakinta ba ta ɗebe duk wasu ƙulumboton da ta binne,da gaske ta shiryawa zaman auren a wannan karon,babu boka babu malam tsananin biyayya da kulawa za ta bawa Aminullahi,wataƙila ta samu ya dena fushi da ita. A can Lagos kuwa....... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 43. A wani ɗaki mai tsananin duhu aka ajiye su Zaidu. Matashin da ya ɗauki tsuntsu Zaidu na fitowa daga ɗakin ya duƙa ya na haki,kallon sa sauran ƴan'uwansa suka yi suka bushe da dariya,cikin haki ya ce. "This man is too heavy i swear." (Na rantse wannan mutumin na da nauyi.) Dariya sauran suka sake bushewa da ita,a haka kowa ya koma wajen da ya ke aiki a gidan. Mr Ayo bai bi ta kan su Zaidu ba sai da suka yi kwanaki uku ana ciyar da su daga wani irin abinci me warin tsiya babu ruwa. Sun galabaita matuƙa har sun gwammaci mutuwarsu akan halin da suke ciki,gashi basu da ikon yin magana ballantana su bayyana wa junan su halin da suke ciki. El-Hassan ne ya kalli Yanda Zaidu ya maida hankali ya na tsattsagar abincin da ba a jima da ajiye musu ba mai masifar wari,wasu hawayen nadama ne suka sirnano masa,a hankali ya buɗe baki ya na kukan tsuntsaye. Ga mamakinsa sai ya ji Zaidu ya amsa masa,da sauri ya tashi sama fiiirrrr ya isa inda Zaidu yake ya tsaya suna kallon juna,cikin kukan tsuntsaye ya ce. "Ka ji me na ce yanzu ɗan'uwa?" "Ga shi kuwa na baka amsa." "Mun shiga uku ɗan'uwa,ka duba ka ga Muhammad ba ya numfashin kirki,da wannan halin ƙasƙancin da muke ciki da ma guduwa muka yi,ku zo mu yi ƙoƙari mu gudu idan muka zauna anan mutuwa za mu yi na tabbata." A hasale tsuntsu Zaid ya ce. "Ta ina kake ganin zamu iya gujewa mutanen nan? Matsafa ne fa,ko baka ga abinda wannan ɗirkeken ya yi ba a ranar da muka koma haka ? Na tabbata babu ta inda za mu iya guduwa. Idan mutuwa ta riski ɗayan mu a haka bamu tuba akan laifukan da muka aikata ba mun shiga uku." Kuka Zaid ya fara yi,ya matsa daga wajen abincin da yake ci da ƙyar. Muhammad na can kwance rai kwakwai mutu kwakwai,bakinsa na tsuntsu a buɗe ya na shaƙar iska babu ɗigon yawu a ciki.. Lumshe ido ya fara yi a wahalce ya ce. "Wannan alhakin ɗan'uwanmu da muka haɗa kai muka kashe ne ba tare da haƙƙinsa ba yake bibiyar mu, na tabbata anan za mu yi mutuwar wulaƙanci,matan mu da yaran mu basu san ina muke ba. A yanda muka ɗora su akan turbar son abun duniya zai yi wahala mu samu addu'ar rahamar Allah daga wajen su. Kaicon mu da biye wa son zuciya." El-Hussein kallon su kawai yake yi,dan bashi da ƙwarin guiwar furta komai,wani irin matsanancin haushin su yake ji,ji yake yi da yana da iko da ya kashe su da hannayensa,domin su ne suka jawo masa wannan masifa da bala'in. Suna tsaka da tattaunawa a tsakanin su suka ji ƙarar buɗe ƙofa,matasan nan da suka saka su a ɗakin ne suka shiga ɗaure da zannuwa jajaye,kawunan su kuwa sun ɗaura musu jan ƙyalle,kwashe su suka yi gaba ɗaya suka fitar da su daga ɗaki mai duhun,hasken da ya daki idanuwan su ne ya sanya su ƙyafta idanuwansu da sauri suna kallon hanyar da ake bi da su,suna shiga wani waje suka gane ashe dare ne ba rana ba kamar yanda suka yi zato. Wani ƙaton gunki suka gani a girke kewaye da manyan candles sai wasu ƙwarya guda huɗu da aka jera a jikin gunkin. Mazaje suka gani masu yawa, wasu da manyan tumbi wasu sirara sosai kamar su karye, Mr Ayo kuma na zaune a girke a wata kujerar da za a iya kiranta da ta sarauta. Ana zube su Zaidu a tsakiyar wajen da aka jera candle ya taso,da ƙyar yake takawa har ya isa gaban wannan ƙaton gunkin, mazajen dake wajen ne suka duƙa suna miƙa gaisuwa da jinjina a wajen Mr Ayo,ɗaga musu hannu ya yi sannan ya ɗauki wata sharɓeɓiyar wuƙa da aka ajiye a faranti,kuka Zaidu ya fashe da shi ya na faɗin. "Wayyoo mutuwa...mutuwaa mai azaba...za mu yi mutuwar wulaƙanci a hannun matsafa." A haka Mr Ayo ya yanke kan Zaidu ba tare da ya samu damar tuba ko yin kalmar shahada ba. Ƙwaryar farko wani mutum ya miƙawa Mr Ayo ya tsiyaye jinin Zaidu a ciki,bai tsaya ba sai da jinin Zaidu ya cika ƙwaryar nan sannan ya yi wurgi da gangar jikin a gefe,a hankali tsuntsun ya fara sauya halitta daga tsuntsu zuwa ƙatoton Zaid kwance a ƙasa a wulaƙance babu sutura a jikinsa. Ana gamawa da Zaidu aka bi su El-Hassan aka yi musu abinda aka yi wa Zaid ɗaya bayan ɗaya har aka gama yanke su tasss. Mutanen nan na ganin naman su Zaid a ƙasa yawun su ya fara tsinkewa,kafin su isa gare su a yunwace Mr Ayo ya daka musu tsawar da ta girgiza su tare da firgita su kowa ya ƙame a matsayar shi,cikin yanayin faɗa ya ce. "Wait na make we finish the ritual first." (Ku tsaya mu gama tsafin da zamu yi tukunna.) Jinin su Zaidu Mr Ayo ya zuba a buɗaɗɗen bakin gunkin nan,yana yi ya na surkullen tsafi,ya na gamawa kuɗi suka fara zubowa daga bakin gunkin kamar ruwan fanfo. Ganin an kammala tsafin da ya tara su a wajen ne ya sanya su daka wa naman su Zaid wawa ciki kuwa har da shi kansa uban gayyar,kaca-kaca suka yi wa naman suka cinye ba tare da sun bar ko yatsa ba. ********************** A hankali cikin Layuzah yake girma,ƙurjin nan na sake girma,a duk lokacin da aka matse shi sai ruwa ya ƙara taruwa wanda ya fi na baya yawa da wari,ga uban ƙaiƙayi da yake damunta sosai. Ta rame sosai ta yi duhu saboda babu halin ci gaba da shafe-shafen mayukan bleaching. Lamyah ce ke kula da ita take ɗawainiya da ita kamar ba kishiyarta ba,tin Aminullahi na nuna halin ko in kula da jinyar tata har abun ya zo ya fara damunsa, don haka wata dawowa da ya yi daga Nigeria sai ya yanke hukuncin ɗaukanta ya fitar da ita ƙasar waje domin a duba lafiyarta. Sai da ya kammala haɗa musu komai da ya kamata domin su yi tafiya zuwa India ne sannan ya sanar da su. Hawaye Layuzah ta fara zubarwa ta na tina yanda ta dinga fatan watarana su fita ƙasashen ƙetare ita da Aminullahi su sha soyayya,sai gashi za a je wajen amma kuma tana cikin halin rashin lafiya. A cikin kwanaki huɗu suka kammala komai tare da sallama da ƴan'uwa da abokan arziƙi,jirginsu ya ɗaga zuwa India. Suna isa airport ɗin Delhi suka samu taxi ta kai su hotel ɗin da za su sauka,wanda yake mafi kusa da babban asibitin da za su ga likita. Washegari da safe suka yi wanka suka shirya,Lamyah ta taya Layuzah yin wanka ta shirya ta,Aminullahi ya ɗauke ta a hannu suka fito daga ɗakin su za su tafi asibiti. A reception suka haɗu da wani mutumin ƙasar india ya na zaune a kujera hannunsa riƙe da carbi irin na mabiya addinin bhuda. Kallon Layuzah ya yi sosai kamar wanda aka kunnawa talabijin,ba tare da ya ce komai ba ya ɗauke kansa ya ci gaba da motsa bakinsa. Su Aminullahi kuwa ba su gan shi ba ma ballantana su san yana yi. Sai da suka ziyarci asibiti aka fara duba Layuzah sannan Aminullahi ya kira gida suka gaisa da su Momma, fatan alkhairi suka yi musu sannan suka zauna jiran tsammani. Yunwar da Lamyah ta fara ji ne ta sanya Aminullahi fita ya samo musu abinci suka ci suka ƙoshi a wajen. Tinda aka shiga da Layuzah tin safe ba a fito da ita ba sai yamma,a wajen suka samu waje suka yi sallar azahar da la'asar,bayan sun idar ne suka koma cikin asibitin,kai tsaye ɗakin da aka kwantar da ita suka shiga,Layuzah na kwance ta na bacci bata san me duniyar ke ciki ba,sun wanke ƙurjin an naɗe shi da bandeji. Aminullahi likita ya hau yi wa bayani cikin harshen turanci,gyaɗa kai kawai Aminullahi yake yi cike da aljabi da mamaki,Lamyah kuwa kasa jurewa ta yi sai da ta shiga banɗaki ta dinga kelaya amai tsabar jin tashin hankalin da aka fitar a cikin ƙurjin Layuzah,cike da damuwa Aminullahi ya riƙo Lamyah suka dawo ɗakin,likitan ne ya yi mata sannu sannan ya ce. "Yanzu za mu jira mu gani zuwa gobe a kawo sauran results ɗin gwaje-gwajen da aka yi mata,idan akwai cancer ko wani ciwon za mu yi ƙoƙarin yi mata maganin da ya dace da ita." Godiya sosai Aminullahi ya yi wa likitan sannan suka tattara suka tafi waje,abinci da abubuwan sha Aminullahi ya siyo wa Layuzah sannan ya ajiye suka koma hotel,dan su asibitin ba a barin kowa a wajen mara lafiya,nurses ke kula da mara lafiya su yi masa komai. A daren ranar Aminullah da Lamyah suka sha soyayyar da suka kwana biyu ba su sha ba sabida jinyar Layuzah da ta sha kansu. Cikin dare suka tashi suka yi wanka suka yi nafila tare da addu'o'i masu yawa sannan suka koma suka kwanta bacci. Da asuba bayan sun gabatar da sallar asuba sai suka shiga wanka a tare,suka yi wanka sannan suka shirya suka fita zuwa reception,suna sauka wannan mutumin ya kalli Aminullahi cikin harshen turanci ya ce masa. "Yau ina majinyaciyar da na gan ku da ita jiya? Cike da mamaki Aminullahi ya juya ya na kallon mutumin,kamar ba zai basa amsa ba,sai ya daure ya ce masa. "Ta na asibiti yanzu ma wajen ta zamu je." Murmushi mutumin ya yi sannan ya ce. "Ka ɗauke ta ka mayar da ita ƙasar ku,maganinta na can,anan ɗin kashe kuɗi kawai za ka yi ta yi ba tare da biyan buƙata ba,domin ciwon ta ba na asibiti bane,ta koma ta nemi gafarar wanda ta wulaƙanta,idan sun ga dama za su barta,idan kuma basu ga dama ba haka zata dawwama da wannan ciwo ba za ta warke ba har abada,ko da kuwa za ka zagaye duniya da ita ne kana nema mata magani." Lamyah na jin furucin mutumin sai ta koma bayan Aminullahi a tsorace ta na rarraba idanu. Murmushi mutumin ya sakar mata sannan ya ce. "Madalla da zuciya mai tsafta da karamci. Adalci ya tabbata akan azzaluman da suka kashe miki mahaifinki,ki yi rayuwa cikin salama da aminci." Ya na gama faɗin haka ya tashi daga inda yake zaune ya shige wata kwana,jikin Lamyah ne ya ɗauki rawa ta fara kuka kamar ranta zai fita,ganin haka ne ya sanya Aminullahi mayar da ita ɗakin da suka sauka ya hau rarrashinta tare da bata baki,cikin tsananin damuwa da son kaucewa yarda da abinda mutumin nan ya sanar da su ya ce mata. "Kar ki yarda ki aminta da wannan mutumin,domin na jima da sanin ƙasar nan akwai matsafa da masu wankin ido,wataƙila ya faɗi hakan ne kawai domin mu yarda da shi imanin mu ya yi rauni,ki kwanta ki huta zan je na ganta na dawo. Allah Ya jiƙan Baaba da Ammiin mu,ki yi bacci ki huta kin ji babyna zan sa a kawo miki abinci nan." Da ƙyar Lamyah ta bar shi ya tafi,saboda wani irin tsoro ta ji yana shigarta,ya aka yi mutumin ya san kashe mata mahaifinta aka yi? A ina ya san su har ya yi magana akan jinyar Layuzah? Aminullahi na fita ya sa akai wa Lamyah abinci irin wanda take so har ɗaki,sannan ya wuce asibiti cike da zullumin kada maganar mutumin nan ta tabbata. Ya na zuwa asibiti ya samu likitoci suna duba ta,kowa na faɗin albarkacin bakinsa akan result ɗinta da aka kawo daga lab. Duk wani bincike da ya kamata su yi sun yi shi sun gano bata ɗauke da duk wani ciwo da suke tsammani,domin kuwa hatta da infection da suka tsammata za a samu a jikin ciwon ba a samu a ba,kansu ya ɗaure da wannan lamarin shi yasa suke ta tattaunawa a tsakanin su. Gashi ba su son Aminullahi ya ga gazawar ƙwarewar asibitin su. Sai dai duk da haka dole ne su sanar da shi gaskiyar abinda yake faruwa. Babban likitan ne ya kira shi har ofishinsa ya zaunar da shi tare da yi masa bayanin sun yi iya binciken da za su yi amma ba su gano komai ba game da ƙurjin nata,domin kuwa da safe da aka kunce ciwon za a wanke sun tarar ya ƙara girma ne ya ɗuri ruwa kamar ba a matse ba jiya. Cikin tsananin damuwa da tashin hankali Aminullahi ya ce zai ɗauki matarsa za su koma ƙasar su,nan take likitan ya bashi shawarar su jinkirta tafiya su ci gaba da bincike akan ciwon nata,sai dai sam Aminullahi ya ƙi amincewa da hakan,a yanzu zuciyarsa ta yarda da maganar da mutumin nan ya yi,ya tabbata akwai wani zunubin da Layuzah ta aikata har hakan ta kasance da ita. Da ƙyar ya yi musu bayanin da suka gamsu suka sallame su,Layuzah na kwance saboda azaba ko wanda ke kanta bata sani ba,saboda yawan taɓa ciwon na sake ruruta mata shi ne a jikinta har ya dasa mata ficewar hayyaci. Cikin kwana biyu Aminullahi ya ɗauki iyalinsa suka koma Nigeria,maganin gargajiya aka durfafa,duk wani malami da Aminullahi ya ji yana bada magani akan tsarin musulunci sai da ya kai Layuzah,sai dai har a wannan lokacin ƙurji na nan,sai raguwar raɗaɗi da zogi da ta ke samu a hankali. Yau ma kamar ko da yaushe Lamyah ta gama shirya Layuzah ta fito daga ɗakin nata ta na yarfe gumi,hannunta riƙe da kayan da ta cire wa Layuzah za ta saka a washing machine ta wanke su,sai ta ji sallamar Hajiyan Layuzah a parlour,cikin fara'a ta amsa mata tare da faɗin. "Bismillah Hajiya shigo ciki,mu kaɗai ne me gidan baya nan,ya tafi Nigeria shekaran jiya." Fuskarta ɗauke da damuwa Hajiya ta ƙarasa ciki ta na faɗin. "Ai dole ne na jinkirta shigowa kar na je na ci karo da wannan yaron a gida. Sannu da ƙoƙari kin ji? Allah ya saka miki da gidan aljannah,Allah ya bada lada,na gode na gode da ɗawainiyar da kike yi da Layuzah,Allah ya baki yara masu albarka." Kuka Hajiya ta fashe da shi sosai har da majina,a haka suka shiga ɗakin da Layuzah ke kwance ta na shan fruits,ta na ganin Hajiyan ta sai ta saki murmushi ta ce. "Ah Hajiya ku ne tafe? Bismillah shigo mana." Hajiya shiga ta yi ta zauna ta na share hawayenta,ciwon Layuzah ya yi duhu kamar wanda ake barbaɗawa gawayi,hawaye ne suka sake zubowa Hajiya ta ce. "Kwana nake ina tinanin wanda kika wulaƙanta har ya yi miki wannan mugun abu Layuzah,don Allah ki zurfafa tinani wataƙila ki gano ko wanene mu je har da ni na durƙusa na nemi yafiyarsa,ba zan iya jure ganin ki cikin wannan mawuyacin halin ba." Damuwar da Layuzah ke ta ƙoƙarin dannewa ce ta kau,nan take kuka mai tsanani ya ƙwace mata,Lamyah na ganin haka sai ta saci jiki ta fita ta basu waje,ta na fita Layuzah ta ce. "Kin san halina Hajiya,bana raga wa duk wanda na ke ganin na fi shi,ba kuma na ɗaukan mutane da ƙima da daraja sai idan na san zan mori mutum,kin ga kuwa fita neman wanda na ɓatawa ba ƙaramin aiki bane,domin ban san adadin mutanen da na ɓatawa ba,ta ina zan fara neman su?" Kuka suka dinga yi a tare babu wanda yake iya rarrashin wani a cikin su,da ƙyar suka samu suka tsagaita tare da kawo shawarwarin yanda za su samu mafita akan wannan lamarin. A haka Hajiya ta wuni ta na kallon yanda Lamyah ke kula da Layuzah kamar wata ƴar'uwata ta jini,nadama tare da danasanin abubuwan da suka dinga yi a baya ne ya mamaye ta. Da yamma liƙis da ta tashi tafiya Lamyah ta bada mota ta ce me gadi ya kai ta gida,tare da haɗa mata sha tara ta arziƙi,cikin ranta Hajiya ke faɗin. 'Allah sarki kamar ta san bani da ko ƙwayar hatsi a gidan,tinda yarinyar nan ta koma yaron nan ya dena zuwa inda nake,girmamawar dake tsakanin mu ta kau,ita kuma da take kai min abinci da kuɗaɗe ga ta nan ta na fama da kanta. Allah na tuba ka yafe ni,Allah ka saka wa yarinyar nan Lamyah da alkhairi ka tsare gabanta da bayanta.' A haka direba ya ajiye ta a gida bayan ya taya ta shigar da kayan abincinta cikin gidan,ƴan kuɗaɗenta kuma suna ƙulle a ƙugunta,sai da ta rufe gidan sannan ta nufi ɗaki ta kwanta. Bayan kwana uku Lamyah ta shirya Layuzah za ta kai ta asibiti domin a wanke mata ciwo kamar yanda suka saba yi,rasa yanda zata yi ta ɗaga Layuzah Lamyah ta yi saboda Aminullahi da ke yin hakan baya nan. Waya Lamyah ta sa ta kira su Zahrah dan su taimaka mata su sanya ta a mota. Ta na nan zaune suka iso ita da Azizah,bayan sun gaisa ne Lamyah ta sanar da su abinda take so su yi mata. Zahrah ce ta miƙe tsaye ta kalli Lamyah ta ce. "A matsayin umarni kike faɗa mana mu taimaka mata mu saka ta a mota,tinda mu ma'aikata ne a ƙarƙashin ku,ko kuma kina neman alfarma mu taimaka mu saka ta a mota ne?" Nan take Lamyah ta tina menene a tsakanin Layuzah da Zahrah,wata iriyar faɗuwa gabanta ya yi,baki na rawa Lamyah ta ce. " Zahrah ko dai ke ce kika mayar da Layuzah haka saboda wulaƙancin da ta yi miki a rayuwa?" Wani irin kallo Zahrah ta yiwa Lamyah kafin ta ce......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 44. Hawaye Zahrah ta share kafin ta sassauta muryarta mai rauni ta ce. "Idan na ce miki abinda Layuzah ta yi min bai yi min ciwo ba ƙarya nake yi. Amma hakan be zame min uziri kuma sanadin da zai kai ni na yi mata mummunan fata ba a rayuwarta ballantana har ni da kaina na cutar da ita. Tinda nake a rayuwata ban taɓa sanin hanyar da zan kai kaina wajen wani mushirikin da zai sa na ɗaukaka a rayuwata ballantana na cutar da wani,ban ji daɗin zargin nan da kika yi min ba,na zaci zaki iya bada kyakkyawar shaida akaina." Cikin ƙasƙantar da kai Lamyah ta riƙe hannayen Zahrah da suka ɗauki wani irin sanyi saboda halin da take ciki na damuwa ta ce. "Don Allah Zahrah ki yafe mini,ban san me ya shiga kaina ba har na yi miki wannan mummunan zargin,a koda yaushe Iya ta na yabon kyakkyawan halin ki,wanda ni da kaina na ganewa idanuwana su har da ƙari,na rasa yanda zan yi ne saboda damuwar halin da Layuzah ke ciki,shi yasa nake ta tunani akan mutanen da na san ta taɓa saɓawa,amma don Allah ki yi haƙuri ki yafe min." Kallon Lamyah Zahrah ta yi cike da so da girmamawa ta ce. "A gaskiya na jima ban ga mace mai kyakkyawar zuciya irin taki ba. Tabbas kin yi gadon kyawawan halayyen mahaifiyarki,har yau ina tina yanda take jan mutanen da ke ƙasa da ita a jiki ta na ɗaukan kanta ba komai ba. Allah Ya jiƙan ta." "Amin Ya Allah, don Allah ku kama min ita mu sanya ta a mota,na kaita asibiti." Haka su Zahrah suka taimaka wa Lamyah ta saka Layuzah a mota,ɗaga mata hannu suka yi ta wuce asibiti,Zahrah kuwa zama ta yi ta taya Lamyah gyara gidan tare da wankin su,sannan ta ɗora musu abinci,Azizah kuma ta koma gida ta kama aikinta. Lamyah na zuwa asibiti ta kira nurses aka zo da gadon ɗaukan marasa lafiya aka shimfiɗe Layuzah akai,sai da aka shiga da ita wajen wanke ciwon sannan Lamyah ta kira Hajiyan Layuzah ta sanar da ita,saboda kar ta je gidan ta tarar ba sa nan,cikin sanyin jiki Hajiya ta ce. 'To gani nan zuwa asibitin,dan kuwa na ɗakko hanyar zuwa wajen naku.' Bayan sun kashe waya ne babu jimawa aka gangaro da Layuzah wadda ta sha kuka saboda azaba,wani ɗaki aka kwantar da ita za a zo a sanya mata ƙarin ruwa. Lamyah na zaune a waje wata nurse ta shige ɗakin ɗauke da kayan aiki,kallon Layuzah ta yi ta na murmushin samun nasara da jin daɗin halin da ta ganta a ciki. Hajiya na zuwa sai suka haɗu da Lamyah suka rankaya cikin ɗakin da aka kwantar da Layuzah,suna shiga suka ji nurse ɗin nan da Layuzah suna magana,cikin kuka da fitar hayyaci Layuzah ta ce. "Ban san abinda na yi miki zai ɓata ranki ba...don Allah ki...yafe mini...ina gab da rasa raina saboda azabar....da nake ciki." Dariya Nurse ɗin ta yi sannan ta ce. "Ba kowa ake wulaƙantawa a zauna lafiya

Chapter 27 of 30