Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na,kai ku matsa ku gani." Ma'aikatan wajen ta bawa umarnin su matsa,cikin sauri da rawar jiki suka matsa kuwa,nan fa Hajiya Laure ta fara fitar da wasu kayayyaki wanda suka jima a ajiye a shagon ba a siyar ba,sai loda wa su Layuzah take yi tana bayani,a cewar ta sun tsumu da yawa za su fi yi mata aiki,na sha da shafawa a jiki da matsi da wanda za ta yi masa amfani da shi aka haɗa mata. Ana buga lissafi kuɗi suka kama dubu ɗari biyu da ashirin,transfer Layuzah ta yi mata suka ɗauki kayan masu uban yawa suka saka mata a sabuwar motarta,Hajiya ta shiga gidan gaba ta hakimce suka wuce gida. Sai da ta ajiye Hajiya a gidan ta bata kayan ƙwalamar da suka siyo da dubu hamsin sannan ta juya ta ɗauki hanyar gidan Momma dan ta kai musu gaisuwar Juma'a. Kiɗa ta ware a cikin motar ta na bi ta na rawa,ga waya ta kafe ta na yi wa kanta video za ta ɗora a TikTok,ko babu komai itama ta fara yi wa talauci barazana,a yanzu ƙawayenta na lissafata a cikin manyan matan da ke da ƙumbar susa a cikinsu. Tin daga bakin gate ɗin gidan ta fuskanci akwai wani abu da ke faruwa,ba tare da ta kula masu gaishe ta ba ta shigar da motar ta har cikin gidan,mai gadi ne ya kalli sauran abokan aikinsa dake gidan ya ce. "Itama ba zan rufe mata gate ba,za ku gani muna nan da ku a haukace za ta baro gidan." Dariya suka kwashe da ita suka tafa,sannan suka ci gaba da gulmar Aminullahi da kuma matarsa da ta mallake shi wato Layuzah. Kanta tsaye ta hau takun ƙasaita kamar yanda take yi a kullum ta nufi cikin gidan,ta na shiga ta ci karo da Zahrah ta dawo daga ɗakin Lamyah da ta kai wa tea da snacks tare da maganin ciwon kai,dariya ce ta ƙwacewa Zahrah sai ta saka hannu a bakin ta ta na kare bakin ta ce. "Ah ah ka ga Uwar gida sarautar banza a gidan Alhaji Aminullah,to Allah ya sanya alkhairi ya haɗa kan ku da amaryar ki ya baku zaman lafiya." A yatsine ta kalli Zahrah da ke ta sheƙa dariyar shaƙiyanci,cike da ɓacin rai ta ce. "Da alama dai Zahrah kin fara gajiya da aikin ki ko? Shashasha kawai mara hankali,ko giyar wake Aminullahi ya sha an faɗa maki zai iya ƙara aure ne?" Cak Zahrah ta tsaya daga bakin ƙofar kitchen ta ce. "Ƙwarai ba zai iya ƙara aure ba,saboda ke kaɗai kika san dalilin hakan,amma kuma idan shi ba zai iya ba ai yana da na gaba da shi ko? Ko su ma ba za su iya yi masa auren ba?" Zahrah na gama faɗin haka ta wuce cikin kitchen ta na kwasar dariya,Layuzah kuwa hankalinta ne ya yi mummunan tashi ta juya har ta na harɗewa da doguwar rigar da ke jikinta ta nufi cikin gidan ta na ƙwalawa Momma kira. Iya ce ta fito ta ce. "Haba Layuzah wannan wanne irin kira ne kike yi wa Hajiya babu ladabi a cikinsa?" Wata jahilar harara ta maka wa Iya sannan ta nuna ta da yatsanta manuni ta ce. "Ke tsohuwa ba dake nake ba ! Don haka ki matsa ki bani waje,so nake na san gaskiyar abinda ke faruwa a cikin gidan nan da mai aiki za ta tare ni ta na faɗa min maganar banza." Kallon Layuzah Iya ta yi daga sama har ƙasa,lallai wannan matar da ke gabanta ba ita bace ta dinga neman gindin zama a watannin baya,wannan haɗaɗɗiyar mace ce da ta ji kayan gyaran jiki ta yi ƙiba ta murje,mace ce da ta ke ji da nera saboda ta na auren yaron hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Mus'ab. Sai dai duk da haka ita ɗin surukar gidan ce ba ƴar gidan ba,bata da ikon zuwa ta dinga ɗaga murya tare da yi wa mutane rashin kunya kamar ita ta sanya su aiki a gidan. A harzuƙe Iya ta ce mata. "Duk abinda mai aikin da kika raina ta sanar da ke gaskiya ne,dan haka zaɓi na gare ki,ki zauna da sabuwar kishiyar ki lafiya,ko ki tsinke igiyar auren Aminullahi dake kan ki,ko kuma ki....." Wani irin ihu Layuzah ta saki sannan ta toshe kunnuwanta. "Ya isa haka! Ya she ki haka ke munafukar tsohuwa, ƙarya kike yi babu auren da Aminullahina ya ƙara,ni kaɗai ce matarsa,da ni kaɗai zai zauna har abada,babu wata shegiya da zata raɓi mijina ban kashe ta ba,zan iya ɗaukan ran duk wata mace da ta raɓi mijina !" Kalaman Layuzah ba ƙaramin gigita mutanen gidan suka yi ba,Momma ce ta ƙarasa inda Layuzah ke tsaye ta kama hannayenta,kallon Iya ta yi fuska a haɗe ta ce. "Me yasa kika sanar da ita ta wannan sigar Iya?" Ɗaga hannaye Iya ta yi ta na kyaɓe baki ta ce. "Haram ni ba ni na faɗa mata ba,ban san a ina ta jiyo ba kawai ta shigo tana maganganun banza shine na jaddada mata gaskiyar lamari,laifi ne dan Aminullahi ya ƙara aure? Ko dama an faɗa mata dan ita kaɗai aka haife shi? Allah ne ma ya yi da rabon ki a zama da shi,amma tin fil azal shi ɗin yana da daɗaɗɗan alƙawali akan sa,kuma da ba a aure ba za a aure ki ba,ke kin sani ke kika kawo kan ki da kan ki aka rufa maki asiri aka aure ki,ba domin haka ba babu auren da zai yi har sai alƙawarinsa ta bayyana." "Duk da haka Iya da an bi ta da lalama,babu fa wanda ke son kishiya sai ta zame masa dole,to fa anan ne zai rungume ta ya yi haƙuri a zauna lafiya." Cikin kuka Layuzah ta ɗaga kai ta kalli Momma ta ce. "Kenan da gaske Baby ya ƙara aure? Don Allah Momma ki ƙaryata ni kar ki ce min ya ƙara aure." "Haƙuri za ki yi Layuzah,bawa baya wuce ƙaddararsa,aure ne an riga an ɗaura masa da yarinyar da aka yi alƙawarin zai aura tin suna yara." "Kan uban nan kayyasa,idan na yarda uwata zina ta yi ta haife ni,ke kishiyar ne da ke da zaku ƙulla munafurci a yi wa mijina aure saboda mugunta da baƙin hali? In da ni ƴar ki ce za ki bari a yi min kishiya?" Tsawar da Momma ta sakar mata ne ya sanya ta sake zuba idanunta cikin na Momman ta na yi mata kallon banza,cike da rashin kunya ta ce. "Ki dena ɗaga min murya domin da muryar ki da kukan annoying zakaran asuba duk ɗaya na ɗauke su a yanzu,baki da sauran ƙima ko darajar da zan kalle ki da su,kin ci amana ta,kun cuce ni." A matuƙar hasale Lamyah da ke jinyar tata zuciyar da jikin ta fito ta wanke Layuzah da zazzafan mari,hucin ɓacin ran da take yi ne ya sanya Layuzah ƙamewa cike da tsoro ta hau bin Lamyah da kallo,hannunta Lamyah ta ja ta wurga ta waje ta rufe ƙofar parlourn,ko da ta koma sai ta ga Momma a tsaye ta na zubar da ruwan hawaye,rungume Momma ta yi ba tare da ta ce komai ba. Layuzah kuwa buga ƙofar parlourn ta dinga yi ta na zage-zage da rashin mutunci,ganin babu wanda ya kula ta ne ya sanya ta barin jikin ƙofar ta nufi motar ta a guje,buɗewa ta yi ta shige ta tashe ta ta bar gidan da matsiyacin gudu. Mai gadi da masu aikin gidan na ganin haka suka bushe da dariya tare da ci gaba da gulmammakin da suke yi tin bayan da aka ɗaura auren Aminullahi da Lamyah. Kuka kawai take yi tana buga kanta a jikin kujerar motar har ta isa gida,horn ta dinga bugawa kamar za ta tsaga kunnuwan mutanen unguwar,a guje mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga gidan. Aminullahi na kwance zazzaɓi ya yi masa kamun kazar kuku Layuzah ta isa gidan ta na ƙwala masa kiran mafarauta. Yana jin ta ya kasa amsawa sai rawar sanyi yake yi,wani irin tsalle ta yi kamar a china ta dira a kansa ta hau duka,kuka take ta na ɗura masa ashar,cikin matsanancin kuka ta ce. "Ashe dama kai munafuki ne ban sani ba? Ka shirya cin amanata shi yasa ka siya min sabuwar mota ka zuba min manyan kuɗi a account ɗina,sannan ka yi min alƙawarin zuwa makka ni da Hajiyata dan mu yi ibada,to ba zan je makkan ba na fasa,dan ba zan tafi na barka ka ji daɗin zama da wata ba a rayuwar ka har abada." Haka ta dinga zazzaga masa masifa tana zagin sa tare da cin alwashin sai ta kashe su gaba ɗayan su,idan ya so sai ta ga yanda za a yi ya rayu har ya kawo mata wata mace cikin gidanta,a guje ta sauka daga gadon ta nufi parlour ta bar Amunullahi kwance ya na fitar da ƙwallar azabar jiki da ta zuciya.......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️ ✨ PAGE 35. Ƙarar ƙarafan da Aminullahi ya jiyo daga kitchen tare da ihu da zage-zagen Layuzah ne suka firgita shi,lallai babu abinda ba za ta iya aikatawa ba a irin wannan lokacin da take cikin matsanancin fushin da kishi ya dasa mata,dan haka a daddafe ya miƙe ya isa jikin ƙofar ɗakin ya rufe ya murza makulli tare da barin makullin a jikin ƙofar. Riƙe kansa ya yi yana layi ya koma ya kwanta ya na fitar da numfarfashi. Zaman shi da kimanin mituna uku ta ƙaraso ɗakin a guje da wuƙaƙe a hannunta sai ka ce ƴar mahauta,jijjiga ƙofar ta fara yi tana ci gaba da zagin sa kamar ba mijinta ba,wani zagin ma idan ta danna masa sai ya girgiza kai saboda takaici,yau ko a bariki suka haɗu ai ya kamata ta rangwanta masa tinda babu abinda baya yi mata na kyautatawa. Gajiya ta yi da iface-ifacen ta koma parlour inda ta yi watsi da jakarta da mayafinta ta ɗauki jakar,wayarta ta zaro a cikin jakarta ta hau kiran Hajiyanta,bata wani jima tana ringing ba Hajiyan ta ɗauki kiran,fashewa da kuka mai tsanani Layuzah ta yi,wanda ya sanya Hajiya da ke yagar naman kaza dakatawa ta hau siɗe hannu ta ce. "Na shiga Uku ni Mardhiyya me ya samu Aminullahin Layuzah? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,don Allah ki dena kuka ki yi min bayani." Cikin kuka Layuzah ta ce. "Ni ba gwanda ma wani mummunan abun ya same shi ba,ko ya mutu da abinda ya yi min Hajiya." Zabura Hajiya ta yi ta daddafa kujera ta tsaya a kan ƙafafunta tana ƙyafta idanuwa kafin ta ce. "Ke ƴannan rufa mana asiri,idan ya mutu uban wa zai dinga bamu kuɗin da za mu dinga wadaƙa kamar haka? Kin kuwa san me nake ci yanzu? Kaza ce fa sukutum da guda na ɗakko a firinji jiya na soye ban samu na ci ba sai yanzu da kika aje ni gida,sannan ki duba ki ga siturun da nake sakawa yanzu,dan haka ki dena ma wannan maganganun mutuwar bana so. Yanzu faɗa min abinda ya yi miki mu ga ta inda za mu kamo bakin zaren." "Hajiya aure fa Aminullahi ya yi ba tare da ya sanar dani ba,da haɗin bakin munafukan iyayensa akai komai,ina zuwa gaishe su shegiyar Zahrahn nan ke mini fatan sharri wai Allah Ya bamu zaman lafiya." "La'ilaha'illallahu Muhammadur-rasulillahi sallahu alaihi wa sallam,keee Layuzah ko dai baki ji da kyau bane? Da bakin ki fa kika faɗa min yanda Zahrah ke hassadar ki,dan haka kar ki wani damu ƙarya take yi ja'irar me rai (In Aunty Asma'u's voice)" Kuka Layuzah ta sake fashewa da shi sannan ta ce. "Don Allah Hajiya ki dena magana haka,ya ina sanar dake magana ta tabbata an ɗaura auren Aminuna da wata banza wai da sunan cika alƙawari kina ƙaryata ni,da gaske nake miki munafukar uwarsa ce ta jaddada min faruwar hakan,wai ƙaddara ne,ke ki ji fa,se kace ita ƙaddarar manta ta tayi da ba a yi mata kishiya ba tin da ƙuruciyarta har yanzu da tsufa ya kama ta." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,lallai waɗannan mutane akwai annamimai munafukai,kuma azzalumai,Allah Ya saka miki abinda suka yi miki. Kar ki damu kin ji? Maza share hawayen ki,idan sun san wata ai basu san wata ba kina ji na ko?" Ɗaga kai Layuzah ta yi kamar Hajiya na ganin ta,ita kuwa Hajiya sai ta ci gaba da sanar da Layuzah duk wasu shawarwarin yanda za ta mallake Aminullahi,kuma ta muzgunawa Lamyah har sai zaman gidan ya gagare ta ta gudu da ƙafafunta,sun jima suna waya sosai har sai da zuciyar Layuzah ta ɗan risina sannan suka yi sallama. Cikin jimanta lamarin Hajiya da ta ajiye wayarta ta koma saman naman kazarta ta yago ƙirji ta kai baki ta ce. "Ina zan yarda ki ɓallo auren ki dawo mu koma gidan jiya? Waɗanda aka cuta ma a gidan miji haƙuri ake basu,su zauna su yi ibadar aure ballantana ke da kike cin uban ɗan mutane,dan haka ki zauna ki baza mulki son ran ki,kuɗi na ci gaba da shigo mana." Ita kuwa Layuzah har ta kwanta a ɗakinta ta na jujjuya maganganun Hajiya,ji take yi kamar ba za ta iya ba,saboda yanda take jin raɗaɗi da ƙuna a cikin ranta game da auren da mijinta ya yi ba tare da ya sanar da ita ba,ta manta cewa shi kanshi bai san za a yi masa auren ba a daidai wannan lokacin,bata damu da halin da ya shiga ciki ba fatanta kawai nata ran ya zama fari,ta yi ta samun abinda duk take so a gidan miji. Ta ɓangaren Aminullahi ma yanda yaga rana haka ya ga dare cike da azabar ciwon jiki da na zuciya,a wannan dare haka ya kwana yana sheƙa amai da zawo,daga ƙarshe ma jan jiki yake yi idan zai zaga,ganin zai mutu shi kaɗai ne ya sanya shi kiran mai gadi a waya,da goshin asuba ya lallaɓa ya buɗe masa ƙofa ya kama shi suka wuce asibiti. Layuzah na can na bacci bata san abinda ke wakana ba. Sai da ta tashi da misalin ƙarfe sha biyu na rana ta shiga banɗaki ta yi wanka,sannan ta yi brush ta fito,dan a tsarin ta sallah ma sai ta ga dama take yi,ko ta yi dan ganin idon mutane kar a ce bata sallah,idan tana sallah a gaban mutane har jimawa take tana mui-mui da baki kamar tsohuwar da ke mamular goro. Cikin wata shadda mai yauƙi da tsada ta shirya kanta sai baza ƙamshi take yi,gidan kaca-kaca babu shara ballantana gyara haka ta tsallake ta wuce ɗakin Aminullahi zuciyarta na turiri,wani abu ta haɗiya ta mayar da baƙin cikin dake taso mata ta ƙwanƙwasa ƙofar sai ta ji ta buɗe,tana leƙa ɗakin ta ga kayan sa a zube a ƙasa, ƙofar banɗaki a buɗe,leƙawa ta yi ko yana ciki,sai ta ji wari,da sauri ta baro ɗakin ta fito waje,wayarsa ta hau kira sai ta ji an amsa amma ba muryarsa bace,a rikice ta ce. "Waye kai? Me wayar mijina take yi a hannunka? Don Allah ka dawo min da shi kar ka cutar min da mijina." Hawaye ne suka fara gudu a kuncinta,ajiyar zuciya mai gadi ya sauke ya ce. "Hajiya ni ne fa,na kawo Alhaji asibiti ne saboda amai da gudawa da ya ƙwace masa,gamu nan likita ya duba sa an rubuta magunguna,dama ina da niyyar kiran ki na sanar da ke ya hana." "Na shiga uku ni Layuzah,a wanne asibitin kuke? Gani nan zuwa yanzu me aka ce yana damunsa?" "Muna nan asibitin da iyalan gidan su suke zuwa,likita ya ce akwai alamun damuwa a tattare da shi,shi yasa ma aka yi masa allurar bacci dan ya huta." "Gani nan zuwa." Kashe wayar ta yi sannan ta bazama zuwa ɗaki ta ɗakko jakarta da mayafi tare da makullin mota ta fita,sai da ta rufe gidan sannan ta wuce private hospital ɗin da ahalin gidan Abii ke ganin likita,waya ta yi wa mai gadi ya sanar da ita ɗakin da suke,a rikice ta isa ɗakin,ta na zuwa ta kwanta a jikin Aminullahi da ke bacci ta fashe da kuka,cikin kuka take faɗin. "Baby don Allah ka tashi kar ka tafi ka barni,idan ka barni nima mutuwa zan yi,don Allah Baby ka tashi na yafe maka duk abinda ka yi min,Allah Ya bamu zaman lafiya." Wata nurse ce ta shigo ranta a haɗe ta ce. "Malama tashi ki fita, wannan mara lafiyan yana buƙatar hutu saboda damuwar da ta yi masa yawa,ku je waje ku barshi ya huta please." A yatsine Layuzah ta kalle ta tin daga sama zuwa kasa,majina da hawayen da ke fuskarta ta share sannan ta ce. "Ke ƴar biɗar a sani jaki da haurin walƙiya ! Ina ruwanki da ni? To mijina ne dan haka ki sa min ido babu ruwanki da ni." Kafe ta da ido matar ta yi,can kuma ta saki murmushin da ita kaɗai ta barwa kanta sanin abinda ya ƙunsa,fita ta yi daga ɗakin ta bar Layuzah na ci gaba da naniƙar Amunullahi. Tana nan zaune har ƙarfe biyar na yamma sannan ya farka,ya na ɗora idanunsa akanta gabansa ya faɗi rasss,cikin ransa yake ayyana. 'Na shiga uku ni Aminullahi,me ya kawo wannan masifaffiyar kuma?' Ita kuwa ta na ganin ya farka ta rungumesa ta na sumbatarsa,daga baya kuma idanunta suka kawo ruwa ta shagwaɓe fuska ta ce. "Babyna don Allah kar ka sake kwantawa jinya irin haka,idan na rasa ka mutuwa zan yi,gashi yanzu komai naka baka sanar dani,ka yi aure ban sani ba,baka da lafiya ma an kawo ka asibiti ban sani ba,ba domin na shiga ɗakin ka dan na baka haƙuri akan abinda na yi maka jiya ba,ai da ba zan san baka da lafiya ba." Hamdala Aminullahi ya saki a ransa,tabbas ya ji daɗin yanda ta sakko da wuri,murmushin yaƙe ya yi mata kafin ya ce. "Ki yi haƙuri matata,ni kaina ban san za a yi...." Dogon yatsanta da ya sha farce da jan farce kalar pink ta saka masa a laɓɓansa ta ce. "Shiiii masoyina,magana ta wuce,Allah ya bamu zaman lafiya,ai ita kishiya kafin a yi ta ne tashin hankalin yake,amma tinda an riga an yi ai dole mutum ya haƙura a fuskanci gaba kuma." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Amunullahi ya sauke,a hankali ya ce. "Ki yi waya gida a je a gyara mana gidan nan please,ban san me ya same ni ba na yi amai da zawo,wataƙila yana da nasaba da yanda komai ya yi datti a gidan nan." Harara ta bankawa saman kan shi,kafin ta zaro waya ta kira Momma. Momma kuwa na can abin duniya ya ishe ta,Lamyah babu lafiya,gashi tana tunanin halin da Aminullahinta ke ciki da masifaffiyar matarsa,tana nan zaune ta zuba uban tagumi Iya ta shiga parlourn ta riƙe da wayarta ta miƙa mata,karɓa ta yi tana duba sunan mai kiran,tana ganin sunan Layuzah gabanta ya faɗi,kar dai kira ta yi ta ƙarasa ci mata sauran mutuncin da ya rage a tsakanin su. Wayar na yankewa ta bi kiran,Layuzah na ɗauka ta fashe da kukan munafurci ta na bawa Momma haƙuri akan abinda ta yi jiyan,ajiyar zuciya Momma ta sauke tare da lallashin Layuzah,baki sake Iya ke kallon Momma da ke ta bata haƙuri,cike da takaici ta bar gaban Momma ta koma ɗakin Lamyah da ke kwance ta na rawar sanyi. Momma kuwa na gama waya da Layuzah ta shiga ɗaki ta ɗakko mayafi da jakarta,parlour ta fito ta kira Aziza ta bata umarnin zuwa gidan Aminullahi ta gyara musu,makullin gidan da ke wajenta ta bata da ƴan kuɗi ko da za ta buƙaci sayan wani abun. Ɗakin Lamyah ta kalla kamar ta leƙa,sai kuma ta wuce saboda ta kula Iya ta ji haushin yanda ta sakarwa Layuzah fuska a waya,driver ne ya kai ta ta ga jikin Aminullahin,ta jima a wajensa ya na jin ta ya ƙi buɗe idanunsa ballantana ya amsa gaisuwar da take yi masa,da ƙyar Layuzah ta lallashe shi ya kalle ta ya gaishe ta a daƙile,mamakin halayyar ɗan nata ne ya sanya ta barin asibitin bata shiryawa hakan ba,anya kanshi ɗaya kuwa? Tinda take da shi bai taɓa nuna mata ƙiyayya ba a matsayinta na mahaifiyarsa,duk kuwa da rashin sauke nauyi da haƙƙin sa da ya rataya a wuyanta da bata yi ba a baya,a kullum nuna mata so da ƙauna yake,amma a yanzu a cikin ƙwayar idanunsa take hango ƙiyayyarta kwance. Ƙwalla ta share ta kalli gefen titi,har suka isa gida zuciyarta bata dena suya ba. Kwanan Aminullahi huɗu a asibiti aka sallame su suka koma gida,masu dubiya na ta zuwa ana yi masa ya jiki,cikin su kuwa har da Hajiyan Layuzah wadda ta ƙunso mata wasu magungunan mallaka ta kawo mata a ɓoye. Iya kuwa bata zo ba sai da ya kwana biyu da dawowa gida,ita ma bata samu kallon arziƙi ba ballantana ya amsa mata gaisuwarta,daga ƙarshe ma bar mata parlourn ya yi ya shige ɗakinsa, cike da rashin kunya Layuzah ta harare ta ta ja tsaki ta bi bayan mijinta ta na faɗin. "Don Allah idan kin fita ki jawo mana ƙofa saboda sauro,kuma a ji tsoron Allah dai kar na fito na ga ban ga wani abun ba,ah toh,dan yanzu duniya babu yarda." Da kuka Iya ta koma gida tana sharɓen hawaye da majina,babu abinda ya fi damunta sama da kallon tsanar da Aminullahi yake yi mata,yaron da ta taso ta rene shi kamar ita ta haifesa,soyayyar da yake yi mata ko uwar da ta haife shi baya yi mata ita. Da ta zauna tana kuka ta na sanar da Momma abinda ya faru tsakaninta da Aminullahi da matarsa,sai Momma ta ji damuwarta ta ƙaru sosai,idan har Aminullahi zai fito fili ya nuna ƙin Iya a gaban kowa to tabbas abun nashi ba ƙalaou ba,cike da jimanta abun Momma ta ce. "Yanzu menene mafita Iya? Bana so mu rasa Aminullahi mai kyakkyawar zuciya da muka sani,mai son jama'a da kyautata musu,don Allah ki kawo mana mafita Iya." Momma ta ƙarasa maganarta ta na sharar hawaye,murmushi Iya ta yi sannan ta ce. "Ai mafita ɗaya ce Hajiya, mafitar kuwa ita ce a yi ƙoƙari a kai masa matarsa,na tabbata ita ce za ta kawo ƙarshen wannan abubuwan da suke faruwa." Cikin rashin fahimta Momma ta ce. "Iya kar ki manta fa saboda auren da aka yi masa ne ba tare da saninsa ba ya rikice mana haka." "Ah ah,ba ruwan auren da aka yi masa da halayyarsa,ke ce baki fahimci sauyawar halayyarsa ba tin kafin bayyanar Lamyah,ina tsoron abinda nake zargi ya tabbata Hajiya,dan haka maganin matsalar nan ita ce tarewar Lamyah a ɗakinta." Shiru Hajiya A'isha ta yi ta na nazarin maganar Iya,sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "To shikenan Iya a fara shirya amarya,idan Abii ya dawo zan yi masa magana,gaskiya bana so a haɗa su gida ɗaya a cutar da marainiyar Allah,gwanda kawai a basu gidan su su zauna a ciki,ita Layuzah a barta a wanda take ciki yanzu." "Humm idan aka yi haka ai ba a ci riba ba kenan Hajiya,haɗa su waje ɗayan ma yana da nashi amfanin a daidai wannan lokacin." "Wanne amfani kuma zai yi Iya da ya wuce a yi ta tashin hankali da rabon faɗa?" "Ke dai ki nema mana alfarma wajen Alhaji a haɗa su waje ɗaya kawai idan har kina son Aminullahi ya dawo mutum kamar da." Ajiyar zuciya Momma ta sauke kafin ta ce. "To Iya Allah Ya zaɓa mana abinda ya fi alkhairi." "Amin." A daren ranar Momma ta sanar da Abii tattaunawar da suka yi da Iya,shi ma ya goyi bayan a haɗa su gida ɗaya saboda ceto rayuwar ɗansa,daga ƙarshe ya saki bakin aljihu dan a fara gyara ɗiyar tasa da kuma yi mata kayan ɗaki na gani na faɗa. Amarya Lamyah jiki ya yi sauƙi,sai rama da ta yi sosai,ta yi haske sosai ta ƙara kyau kamar ba ita ba. Tinda Iya ta sanar da ita nan da sati ɗaya za ta tare a gidanta ta sanar da su Afrah,babu ɓata lokaci ta turawa Bala kuɗi ta ce su sayi tikiti su hawo jirgi, domin kuwa su kaɗai ne mutanen da take buƙata a wannan lokacin,duk wasu ƴaƴan ƴan'uwan Momma da suke zuwa gidan ta kasa sabawa da kowa a cikin su,saboda rayuwar su daban da tata,kasancewar su farare kyawawa sosai to su suna da ji da kai da ɗaga kai ba kamar Momma ba da ke da sauƙin kai,duk da cewa ita ma Lamyahn ba baya bace wajen kyau,amma fatar ta ba ta kai tasu haske ba,Mubarak ya fi ta haske sosai,shi yasa idan suka zo ta ga suna ɗaga kai suna iyayi sam bata shiga cikin su. Ranar da Afrah za ta zo kuwa tin asuba

Chapter 21 of 30