yanda ya koma,saboda gaba ɗaya hoton fuskarsa na yarinta ya ɓace min,na san dai yana da suma mai kyau sannan ya na kishi da ni sosai idan yaga Momma na bani kulawa."
Shiru Iya ta yi tana nazarin shin ta fara sanar da Lamyah halin da ake ciki ne ko ta bari dai masu gidan su sanar da ita,buɗar baki ta yi da zummar yin magana Momma ta shiga ɗakin,fuskarta ɗauke da fara'a ta ce.
"Ƴata kin tashi? To ya gajiyar hanya? Ina fatan babu inda ke yi miki ciwo ko?"
Murmushi Lamyah ta yi sannan ta durƙusa ta gaishe da Momma ta ƙara da cewa.
"Na tashi lafiya ƙalou Mommana,babu inda ke min ciwo,ina Abii ko ya fita?"
"Kamar kin sani,saboda sakacin da Yayan ki ya ke faman yi kwana biyu,dole Abiin naku ya fita zuwa kamfani da kansa ko hutawa bai yi ba. Amma na san zuwa la'asar za ki gan shi,idan kin gama abinda kike yi ki fito wajena mu yi hirar yaushe gamo."
Kallon Iya Momma ta yi da kallon gargaɗin kar ta sake ta sanar da Lamyah abinda ke faruwa,dama ta yi zaton za ta zo ta tarar da Iya na sanar da Lamyah halin da ake ciki,sai kuma ta ga saɓanin haka,ko da ta koma parlour zama ta yi ta zabga tagumi tana tinanin yanda rayuwa ke neman sauya musu a cikin wata ɗaya da auren da Aminullahi ya yi. Anya bata tafka babnan kuskure ba na barin Aminullahi ya auri Layuzah? Zuciyarta ta gama gamsuwa duk halayen da Aminullahi ya tsiro da su ba yin kasa bane,to amma yanda Layuzah ke girmama ta yana sanya ta yin shakkun laifin daga wajenta ne. Ajiyar zuciya ta sake saukewa,duk maitar ta da kallo sai ta ji duk ya fice mata a rai.
Babu jimawa Lamyah ta miƙe ta kwashe kayanta kaf ta zuba a ma'adanar kaya,sannan ta mayar da akwatin ciki ta rufe,jakar da Baaba ya bata ta ɗauka ta saka a cikin wajen itama ta rufe,mayafin rigar jikinta ta ɗauka ta yafa a kanta sannan suka fita parlourn Momma ita da Iya. Suna shiga Momma ta dawo cikin hayyacinta daga dogon tinanin da ta lula,Mubarak a saman cinyarta ya zauna yana mata surutu kamar ya jima da saninta. Kafin su fara hira Afrah ta kira wayar Lamyah,cikin kuka Afrah ta ce.
'Shikenan kin tafi kin barni Bala na ta gana min azaba kala-kala,don Allah ki zo ki gudu dani na dena ganin sa,na dena son sa bana auren.'
Dariyar Bala ce ta sanya Lamyah sakin ajiyar zuciya,dan kuwa har ta ji matsanancin tashin hankali ya dirar mata,a kunnen ta ta ji Bala na cewa.
'Haba Baby Afrah meye kike yi haka? So kike ki tona sirrin auren namu? Ki rufawa bawan Allah asiri ki dena kai karata.'
Murmushi Lamyah ta saki sannan ta ce.
"To ya kike? Ya su Baba da Mama Tani?"
Wata iriyar dariya Afrah ta kece da ita za ta fara tsokanar iyayen mijin nata ya karɓe wayar,cike da murmushi Bala ya ce.
'Suna nan lafiya,ina fatan kun isa gida lafiya kun tarar da kowa kalaou? Dan Allah daga yau ki dena tambayar wannan matsokaniyar su Abbahna,ta saka bawan Allah a gaba kamar a kansa aka fara aure da tsufa.'
Dariya sosai Lamyah take yi tana jin wata matsananciyar kewar Afrah da Bala na taso mata,cikin wata iriyar murya Lamyah tace.
"Ina kewar ku sosai,ji nake yi dama muna nan tare gaba ɗayan mu,don Allah ka gaishe min da Baba Musa da Mama Tani."
Afrah ce ta ce.
'Mu ma muna kewar ku sosai,ina ɗan ƙaramina yake? Ban ji muryarsa ba.'
"Gashi can wajen Momma,ni fa anan gidan sai na ga ma kamar an fi son sa ba a ta ni."
Momma ce ta kama baki tana dariya,Lamyah ma murmushi ta yi a lokacin da ta ji Afrah na cewa.
'In dai kika ga ana miki wariya ki yi dawowar ki nan,mu muna son ki kin sani.'
"To Aunty Afrah na,sai anjima a ci gaba da kular min da Malam Bala,kar in ji ya yi kuka da ke."
Bala ya ji daɗi sosai dan haka har suka kashe wayar yana tsokanar Afrah da ta ce Lamyah ta dena son ta,Bala kawai take so. Momma na ganin ta kashe wayar ta ce.
"Kai amma dai ba ƙaramar shaƙuwa kuka yi da mutanen nan ba,dama haka rayuwa take,wani ya ƙi ka wani kuma ya so ka."
Suna nan zaune suka ji ƙamshi turare tare da takun takalmi mai tsini na takowa zuwa parlourn,karar awarwaron da Lamyah ta ji yana tashi ne ya sanya ta tinanin wa suka samu haka ɗan gaye? Idanu ta baza a ƙofar shiga parlourn,Iya kuwa nan da nan ta yi kicin-kicin da fuska kamar wadda za ta yi arba da tsohon maƙiyi. Babu jimawa Layuzah ta shiga parlourn ta durƙusa kusa da ƙafar Momma ta hau gaishe ta,juya wa ta yi ta gaishe da Iya wadda ta amsa a shaƙe. Momma kuwa sai kallon hanyar shiga parlourn take yi cike da ƙaguwa tare da bege,sai dai kash ! Fuskar da take son gani ba ita ta gani ba,Zahrah ta gani riƙe da jarkar zuma ta ajiye a gaban Momma,cikin sakin fuska Layuzah ta ce.
"Mommana ga fa mutuniyar nan,jiya aka kawo wa Hajiya daga Agadez shi ne ta ce na kawo miki."
Fuska babu yabo babu fallasa Momma ta ce.
"Ai kuwa na gode sosai,ina fatan Hajiyan na nan lafiya? Ya jiki jikin nata?"
"To alhamdulillahi za a ce,amma jiki kam yana nan yana cin dukiya,dan ko jiya ma asibiti na kai ta aka duba ta, gwaje-gwajen da aka ce za a yi mata suna da tsada ƙwarai,jin ba za mu iya biya bane ya sanya mu komawa gida,na so ma na kwana da ita amma Baby ya hana."
Cike da jimanta lamarin Momma ta tashi zaune sosai ta ce.
"Subhanallahi,to ina shi sarkin tsamin ran yake da ba zai je ya kai ku asibitin ya biya duk abinda ya dace ba? Ni na rasa wannan sabon hali da ya ɗauka ya ɗorawa kansa. Allah Ya kyauta,Iya don Allah ki shiga ɗaki ki buɗe wajen nan da nake ajiye kuɗi ki ɗakko min dubu ɗari biyu."
Da "To Hajiya" Iya ta amsa ta tafi cika umarnin uwar ɗakin nata ba dan ranta yana so ba. Iya na dawowa da kuɗin sai ta miƙawa Momma,kallon ta Momma ta yi ta ce.
"Yauwa sannu na gode. To bawa Layuzah,maza ta je yanzun nan ta kai mahaifiyarta asibiti ta ga likita,duk abinda ake buƙata kuma ki zo ki sanar da ni,In Shaa Allahu ba zai gagara ba,ki gaishe ta Allah Ya sa mata kaffara."
Godiya sosai Layuzah ta yi har da kukan munafurci,tana miƙewa za ta tafi ta kalli gefen da Lamyah ke zaune tana danna waya,hankalinta gaba ɗaya yana kansu,sai dai ta ɗauke kanta daga kallon Layuzah ne saboda yanda ta ji ƙirjinta ya yi masifar bugawa a kallon farko da ta yi mata. Itama Layuzah ji ta yi kanta ya sara,zuciyarta ta tsinke,wani irin kyau da kwarjinin bala'i Lamyah ta yi mata,cikin zuciyarta ta ke ayyana.
'Wannan kuma wacece? Daga ina Momma ta kwaso ta? Lallai dole na sake nesanta Aminullahina da wannan gidan gudun kar a raina min hankali a nan gaba.'
Ƙwafa ta yi ta sa sauri ta na murguɗa ƙugu cike da yanga ta bar parlourn,bayanta Lamyah ta bi da kallo ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfin da ta bayyana. Shiru wajen ya ɗauka babu wanda ya yi magana akan Layuzah balle a fayyacewa Lamyah ko ita ɗin wacce. Suna nan zaune aka kira sallar la'asar,ɗaki Lamyah ta tafi ta kwanta a gado idanunta lumshe tana ayyana siffar Layuzah a zuciyar ta.
Mace ce gajera mara gaba da baya,sannan bata cikin mata masu dogon gashi sosai,sannan ba za a kira ta da marar gashi ba,farin ta mai ɗaukan ido ne,duk da cewa tana ƙarawa da mai da sabulu,amma wanda bai sani ba zai ce nata ne,domin kuwa ita har irin allurar nan take yi da ke sanya hasken fata saboda kada yatsunta su nuna bleaching ɗin da take yi. Sam ba za a kira Layuzah da mummuna ba,amma fa bata da shahararran kyau. Ajiyar zuciya Lamyah ta sauke sannan ta ce.
"Wacece wannan ɗin?"
"Matar Aminullahi ce ita mai suna Layuzah."
Shine amsar da aka baiwa Lamyah da ke shirin faɗowa daga gado saboda tsabar shiga firgici da tashin hankali da ta yi,cike da zaro idon ta da suka tara ruwan hawaye ta kalli bakin ƙofa ta ce.
"Ina alƙawarin mu ya tsaya kenan idan har Yah Amee na ya yi aure?"............
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 32.
Ƙafafun sa ya fitar daga motar bayan direbansa ya buɗe masa,cikin sakin fuska ya ce.
"Atiku ka ɗakko kayan nan a shigo da su ciki."
"To Alhaji."
Tafiyar ta ce ta ɗauki hankalin su gaba ɗaya, takalminta da ƙarau ɗin dake jikinta sai fitar da sauti suke yi mai ɗaukan hankali, fara'ar sa ce ta ƙaru a daidai lokacin da ya ga Layuzah na ƙarasawa inda yake,cike da shagwaɓa da karairaya ta karanto masa ƙaryar da ta karantawa Momma har ta samu maƙudan kuɗi wajenta,babu ɓata lokaci Abii ya sake bata wasu kuɗaɗen masu kauri ya ce ta je ta kula da mahaifiyarta,idan tana buƙatar taimako ko na menene ta sanar da shi kai tsaye babu shamaki a tsakanin su,godiya ta dinga zabga masa har da hawayen farinciki,domin kuwa kuɗin nan ba ƙananun buƙatu za su kashe musu ba,ko babu komai za ta fara gyara gidan iyayenta,sannan ta ƙaro mayukanta da sabon gashin dokin da ake yayi a dama da ita,cikin farinciki ta bar gidan ta wuce gidan su.
Abii kuwa kai tsaye ɗakin Lamyah ya nufa kasancewar da safe basu haɗu ba ya yi mata ban gajiya,sai dai yana shiga ya ganta cikin ruɗani tare da tambayar kanta shin wacece Layuzah? Bayan ya bata amsa a kiɗime Lamyah ta jefawa Abii tambayar da ta sanya shi murmusawa har ya ƙarasa shiga cikin ɗakin. Sai da ya zauna a kusa da ita suna fuskantar juna sannan ya ce.
"Ke ma kina gab da zamowa matar Yah Amee ɗin ki kamar yanda Layuzah take matarsa. Alƙawarin da muka ƙulla da Ɗan'uwana yana nan zan cika shi,ko da raina ko babu raina na bar wasiyya baki da miji sai Aminullahi."
Wani irin abu ne mai nauyin gaske ya danne zuciyar Lamyah wanda take jin sa kamar zogin cin amana,me yasa za su yi mata haka? Bata taso ta ga mahaifiyarta da kishiya ba,ita kanta Momma ita ɗaya ce a wajen Abii har yau da shekaru suka ja bai taɓa yi mata kishiya ba,sai ita ce za a kai gidan kishiya? Da ta san haka za a ci amanar alƙawari su kasa jiranta tabbas da ta bi duk wata hanya da za ta bi ta nemo soyayyar handsome ɗin da take kwana da son sa ta tashi da son sa a ranta,me yasa za su yi mata haka? Kuka kawai Lamyah take yi har da shessheƙa,cikin sigar lallashi Abii ya kwantar da kanta saman kafaɗarsa ya ce.
"Ki yi haƙuri Lamyah,auren Layuzah ya zo mana a gaggauce a cikin wani irin yanayin da ni kaina ba zan iya ɗorar da faruwarsa ba a yanzu,ki ɗauka cewa haka zanen ƙaddarar ku ya zo da ke da shi da ita kanta Layuzar,In Shaa Allahu da zarar na shawo kan matsalar da muke fuskanta a yanzu zan ɗaura auren ku domin cika alƙawari."
A shagwaɓe Lamyah ta sake kwantawa a kafaɗar Abii ta ce.
"To Amma Abii ai Yah Amii nawa ne ni kaɗai."
Dariya ya yi sannan ya ce.
"Shi yasa ma nake ta gyara maku gidan ku ku kaɗai saboda ku yi rayuwarku kamar ku kaɗai ne a duniyar."
Murmushi ta yi cike da jin kunya ta sunkuyar da kanta,miƙewa Abii ya yi yana tsokanarta sannan ya wuce sashen Momma da ke zaune ta na shan zuma a cikin wani ɗan ƙaramin bowl. Tana ganin Abii ta ajiye ta nufe sa ta rungume sa,da sauri Mubarak ya fito daga cikin ɗakinsa ya nufi wajen Abii ya faɗa jikinsa ta baya,sakin Momma Abii ya yi ya juya ya ɗauki Mubarak ya rungumesa a jikinsa kamar wanda za a ƙwace masa shi,kisses ya dinga showering ɗinsa da su kafin ya riƙe shi a hannu su shiga ɗakinsa. Momma na riƙe da hular Abii da ta cire ta bi bayansu ta na murmushin jin daɗi. Ganin ƙaramin yaro a gidan ba ƙaramin daɗaɗa ranta ya yi,ji take yi ina ma Layuzah ta samu ciki ta ga jikanta? Murmushi ta yi a daidai lokacin da ta ajiye hular Abii a inda take ajiye masa hulunansa,a bakin gado ta zauna ta na leƙen wayar Abii da ya kunnawa Mubarak video na yara a YouTube yana kallo,shi kuwa Abii banɗaki ya shiga ya yi wanka tare da ɗaura alwala ya fito,dan kuwa yana son zama da alwala,shi yasa da ta karye yake zuwa ya sabunta ta. Parlour suka koma Abii ya hau saman dinning Iya ta zo ta yi serving ɗinsa abinci,yana ci suna gaisawa. Sai da ya kammala cin abincinsa ne sannan ya koma parlour ya zauna da Momma da Mubarak suna kallo suna hira,katse shirun nasu ya yi ta hanyar labarta mata abinda ya faru tsakaninsa da Lamyah,wata iriyar faɗuwar gaba ce ta riski Momma,sai ta ji nauyi da kunyar yarinyar sun kama ta a lokaci ɗaya,ji take yi kamar sun ci amanarta basu kyauta mata ba da suka karya alƙawari suka aurawa Aminullahi wata kafin ita,kamata ya yi ace ita ya fara aura daga baya idan zai ƙara da wata ko wasu sai ya ƙara,sai gashi ya ɓige da auren Layuzah kafin Lamyah. Ajiyar zuciya Momma ta sauke sannan ta ce.
"To Allah Ya sa hakan ya zame musu alkhairi,Allah Ya tabbatar mana da abinda ya fi zama alkhairi."
Iya dake kwashe kwanuka duk ta ji abinda ke faruwa,ranta babu daɗi ta kammala kwashewa ta shiga kitchen sannan ta wuce ɗakin Lamyah,kwance ta tarar da ita ta na zubar da hawaye,ita kanta bata san kukan me take yi ba,abubuwa da dama sun taru sun cunkushe a zuciyarta;tinanin iyayenta,tinanin Yah Amee da amaryarsa,tinanin Handsome,tinanin su Afrah da yanda za ta sanar da ita abinda ke faruwa,sannan uwa uba tinanin makomarta anan gaba,ko an raba musu gida da Layuzah ba zai sauya cewa tana da kishiya ba,wata ta riga ta sanin Yah Amee ɗinta. Cikin kuka ta yi juyi tare da gyara pillown da take kai,Iya ce ta ƙarasa shiga ɗakin sannan ta rufe ƙofar,bowl ɗin da ta haɗa mata kunun cuscus da ya ji madarar ruwa da ta gari da kuma inibi,riɗi/kantu, gyaɗa mai gishiri irin manyan nan da strawberry a ciki ta ajiye a gefen gadon sannan ta zauna ta jingina da allon gadon,hannu ta buɗewa Lamyan ta tashi kuwa da sauri tana kuka ta faɗa jikin Iya,rungumeta Iya ta yi itama tana zubar da hawayen kewar Aminee,sai da Lamyah ta yi kukan da ya ishe ta sannan ta ce.
"Yanzu shikenan Yah Amee na ya tashi daga nawa? Ba zan taɓa iya kiransa da Yah Amee na ba? Me yasa ba a jira ni ba?"
Cikin sanyin murya Iya ta ce.
"Saboda shi namiji ne,kuma ya girme ki yana buƙatar mace a kusa da shi,ko kina so Yah Amee ɗin ki ya faɗa saɓon Allah?."
Cikin sauri Lamyah ta girgiza kai alamar ah ah,hamdala Iya ta yi a ranta kafin ta ce.
"Yauwa Lamyahta,to shi yasa aka yi masa aure da wuri saboda kin ga aure shi ne kawai zai kare mutuncin sa,ko baki taɓa kula da cewa idan matashi ya ji shi a cikin kuɗi da wadata ba neman mata yake ko ya fara shaye-shaye? Kin ga ai ba za ki so Yah Amee ɗin ki ya zamo ɗaya daga cikin su ba ko? To dan haka ki ɗauka cewar ajiyarsa kika bayar a kular maki da shi saboda kar ya faɗa saɓon Allah a matsayinsa na namiji mai ƙarfi a jiki da kuma tarin dukiya,yanzu ne zaki karɓi ajiyar ki ki zauna da ita ki bata duk wata kulawa da ta dace. Ni nan zan koya miki duk wani abu da na sani daga wajen mahaifiyarki har ta yi nasarar zama daram a zuciyar mahaifinki,sannan in ƙara miki da na zamani na a lokacin mijina na raye."
Murmushi Lamyah ta yi ta rungume Iya sosai. Hawaye Momma ta share ta juya ta koma parlourn ta. Tinda Abii ya labarta mata abinda ya faru tsakaninsa da Lamyah sannan ya tabbatar mata da ta na can tana kuka ya baro ta,sai ta ji tana da buƙatar ta je ta lallashe ta ta bata baki akan abinda ya faru,sai dai tana dosar ɗakin ta ji maganar su ita da Iya. Tabbas Iya mutuniyar kirki ce,mace ce wadda bata da son zuciya da son abun duniya,mace ce mai son ta da zuri'ar ta,dan haka babu abinda ba zata yi mata ba matsawar zai faranta ran Iyan. Shi yasa har makka suka kai ta wajen sau uku,suka kai yaranta biyu da jikar ta,shi yasa suka ɗauketa kamar jininsu ba wai mai aiki ba.
A ɓangaren Iya kuwa ta ci alwashin sai ta ƙwatarwa Lamyah zuciyar Aminullahi ta yanda zai farfaɗo daga makuwar da ta kama shi akan iyayensa,ba ya ganin kowa a gabansa sai Layuzah,wanda tana zargin ba haka suka bar shi ba. Bowl ɗin da ta shiga mata da kunun cuscus ɗin ta ɗauka ta miƙawa Lamyah,nan take ta hau sha tana santinsa,cikin matuƙar farinciki ƙwalla na zuba daga idanunta ta kalli Iya ta ce.
"Wannan abun Ammi na yi mana shi,sai dai ita bata saka riɗi/kantu, da kuma gyaɗa a ciki."
Murmushi Iya ta yi sannan ta ce.
"Ashe za ki iya tinawa da shi?"
"Ban manta duk wani abu da Ammi take yi ba,bana jin zan manta har abada Iya,ina tsananin kewar su."
"Ki dinga yawaita yi musu addu'a,In Shaa Allahu suna inda ya fi nan duniya da abinda ke cikinta."
"In Shaa Allah."
Haka su Lamyah suka ci gaba da hira tare da tunawa da su Aminee. A can gidan Aminullahi kuwa tinda ta koma ta tarar da shi yana baccin gajiyar da ta tara masa kafin ta fito daga gidan,sai ta yi cilli da mayafinta a parlour ta kunna kiɗa a wayarta ta hau rawa tana murnar samun manyan kuɗi a wajen surukan nata,wannan shine burinta da na mahaifiyarta dama,su tatsi kuɗi wajen surukanta da mijinta, tinda dai su ɗin masu kuɗi ne. Idan million biyar suka bata ba za su ji komai ba,to dan sun bata waɗannan ƴan kuɗaɗen ne take wani murna? Zama ta yi ta baje ƙafafu tana maida numfashi,kallon kuɗin ta yi sai kuma ta miƙe da sauri ta kwashe su ta kai su ɗaya ɗakin nata ta zuba a jaka ta rufe,parlour ta dawo ƙafafunta sai taka datti yake,kallon yanda ƙasan parlourn nata ya yi ƙura da datti ta yi,kawar da kai gefe ta yi ta wuce kitchen,tsamin kayan wanke-wanke ne ya yi mata lale maraba,ji ta yi kamar kar ta wanke su saboda ƙiwar dake damunta,sai wata zuciyar ta bata shawarar ta wanke su ta gyara gidan ta sake ƙwalƙwalar wasu kuɗaɗen wajen Aminullahi,ko kayan matan da take ɗan sha da na gyaran jiki ai ta samu. Da sauri ta ajiye ƙiwa a gefe ta toshe hancinta da ɗankwalinta ta hau wanke kwanukan da suka kusan sati a kime. Ta jima tana aiki sosai kafin ta kammala ta zube a kujera tana maida numfashi,a kasalance ta ce.
"Anya ba zan danne kishina ba na samo me aiki ko tsohuwa ce irin Iya? Wahalar ta isa haka,na gaji gaskiya."
Tana nan zaune Aminullahi ya fito daga ɗaki yana hamma,zama ya yi a nesa da ita yana bin parlourn da kallo,ya ji daɗi sosai da ya ga wajen a gyare dan haka sai ya ce.
"Inyee yau shara muka samu haka har da goge waje? Masha Allahu Allah Ya sa a ɗore."
Cikin sauri Layuzah ta ce.
"Ba amin ba mugu,kai bari ma ka ji ni fa yanzu mai aiki nake so, tsohuwa irin Iya,dan ba zan jure wannan aikin wahalar ba."
Shiru ya yi yana jin babu daɗi a ransa,shi matar auren sa ke kira da Mugu? To muguntar me ya yi mata? Kasa yi mata musu ya yi sai ya ce.
"To ina abinci? Allah ya sa ba irin na jiya ki ka yi mana ba kin dafa mana abinci da kyau."
Hararar sa ta yi sannan ta ce.
"Ni babu abinda na dafa,a gajiye nake nan da ka ganni,kuma ni ɗin ma yunwa nake ji sai ka san yanda za kai da ni."
"Ba gida kika ce min za ki je ba? Na san dai baki zuwa gida ki dawo da yunwa,ni dai don Allah sama min abinda zan ci,gaba ɗaya jina nake kamar iska za ta tashi sama da ni."
Kallon shi ta yi kamar za ta cinye shi dan masifa,ko me ta tina kuma sai ta miƙe cikin kwarkwasa ta ce.
"Amma dai Baby ka bani aiki gaskiya,kuma sai ka biya dan ba zan yi wahala a banza ba."
"Ladan da za ki samu fa?"
Tura baki ta yi tana shagwaɓa ta kwanta a jikinsa ta ce.
"Ai wannan Allah ne zai bani,kai ma sai ka bani naka."
Bakin sa ta sumbata sannan ta fara yi masa wasu irin abubuwan da suka sanya shi cewa.
"To zan baki katina ki je shopping shikenan? Maza tashi ki je don Allah ki yi min girki,kuma dole ne a samo mai aiki a gidan nan gaskiya,ina da azziƙin da zan ɗakko mai aiki a kowacce ƙasa nake so amma saboda kishi kin hana."
Murna Layuzah ta dinga yi,sai da ta je bakin kitchen sannan ta leƙo kanta ta ce.
"Kai ma kishin ke damun ka ai tinda ka ƙi ɗakko kuku na miji."
Girgiza kai Aminullahi ya yi ya wuce ɗaki,har ya fara cire singiletinsa ya tsaya yana nazarin maganarta,shin da gaske yana kishin Layuzah? Shi dai a iya saninsa mace ɗaya ya taɓa jin kishinta ya ji kamar ya kashe mazajen da suka sa ta a gaba suna son cimma wani mummunan ƙudirin su akan ta,idan ya ganta ta fito daga wajen rawa kuwa ji yake yi kamar ya kama da wuta saboda masifaffen kishinta da yake yi,shin yaushe zai koma Nigeria ne dan ya ɗora ta a idanunsa? Ya yi kewarta sosai. Tsaki ya ja da sabon tinani ya shige sa akan ta,a hankali ya furta.
"Allah ka yi min tsari da kewar karuwa."
Wanka ya faɗa ya fito ya rama sallar la'asar da ta wuce shi, yana idarwa ko addu'a bai tsaya yi ba ya koma parlour,kamar kullum indomie ce ta dafa masa,sai dai wannan karon ta samu mutuncin naman kaza da dafaffen ƙwai uku,sai kayan lambu da ta zuba mata,ta yi ruwa ta yi tsamo-tsamo abinta tana ta annashuwa a kwanon,ga mai nan sai ƙyalli yake kamar a kalli fuska. Zama ya yi ba dan ya ji sha'awar indomien ba ya fara ci,yajin da ya ziyarci kwanyarsa ya ɗaure masa harshe ne ya sanya shi miƙe wa tsaye da sauri ya nufi fridge ya ɗakko ruwa ya buɗe,ɗaga kai ya yi idanunsa na zubar da hawayen azaba ya shanye ruwan,ya jima yana ci da shan duk wani abu da ya san zai shashe masa baki. Yana dawowa hayyacinsa ya kalli Layuzah da ta ke ta juya ATM card ɗinsa da ya bata tin kafin ya zauna zaman cin abincin,ji ya yi kamar ya ƙwace katinsa sai dai ya riga da ya yi mata alƙawari,cikin haɗe fuska ya ce.
"Gaskiya ba zan iya cin abincin nan ba,gidan Momma zan je na ci abinci yau."
Murmushi ta yi sannan ta ce.
"Ka bani aron motar ka na je na kai Hajiya asibiti a duba ta,dan bata da lafiya dama ka ga idan muka dawo sai ka dawo kai ma ko?"
"Ok babu matsala,ki yi amfani da katina ki kai ta asibitin Allah ya bata lafiya."
"Amin Ya Allah."
Aminullahi ne ya fara fita daga gidan ya wuce gidan su da ƙafa yana zancen zuci,ji yake yi duk wani taku da yake kusanta shi da gidan yana faɗar masa da gaba,ya rasa dalilin da yasa yake jin damuwa da tashin hankali a duk sanda ya nufaci zuwa gidan nasu,ji yake yi kamar ana cusa matsa tsana da jin haushin zuwa gidan nasu,can ƙasan ransa kuwa kewar iyayensa yake ji da Iya tana addabar ransa. A haka ya ƙarasa zuwa gidan nasu tare da ayyana.
'Abinci kawai zan ci na bar gidan,ba dole sai na haɗu da kowa ba.'
Tin daga gate yake amsa gaisuwar masu aikin gidan har ya isa ƙaramin parlourn dake cikin gidan wanda shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 30