Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
huɗu ne fa a wajen,ka bamu akwati huɗu mana.) Wata hargitsattsiyar dariya mutumin da suke yi wa magana ya saki wadda ta sanya wuta kunnuwa da kanta a jajayen candles ɗin dake kewaye a ɗakin,duk da cewa har a wannan lokacin ba a ganinsa hakan bai hana su Emma sake risinar da kawunan su ba cike da ladabi. Ƙatuwar muryar nan ce ta ce. "Oya make una carry four boxes and go." (To ku ɗauki akwati huɗun ku tafi) Kwantawa suka yi a ƙasa cike da murna suna faɗin. "Oshe boss,thank you so much." Suna kammala godiya suka miƙe jiki na rawa suka bar ɗakin,wata ƙofar suka buɗe suka ɗauki wasu madaidaitan akwatina,kowannen su ya ɗauki biyu,ta gaban su El-Hassan suka wuce ba tare da sun ce musu komai ba,hasali ma yi suka yi kamar basu gansu ba. Suna fita Muhammad ya kece da dariyar murna ya ce. "Lallai yaro yaro ne,wato a zaton El-mustapha ba zamu taɓa gano inda ya taskance dukiyarsa ba da yaransa shi ne ya gudo da tarin dukiya mai yawa irin haka ko? To ka yi kuskure ɗan'uwa,gashi mun kashe ka kuma mun biyo bayan dukiyar taka da yaran naka,za mu kwashe komai sannan mu ɗauki yaranka mu gana masu azaba mafi muni." Dariya suka bushe da ita sannan Zaid ya ce. "Ashe kai ma ka ga uwar dukiyar da ta basu a matsayin tukuicin kawo ƴan'uwan mahaifinta ko? Lallai yaro yaro ne." Haka suka dinga tattaunawa har aka kawo musu abun sha,basu ɓata lokaci ba wajen kafa kai suka sha lemo me sanyi da me aiki ya dinga tsiyaya musu a glass cups. Suna nan suna kurɓar lemo suka ga wannan ƙatuwar ƙofar ta buɗe,maza ne guda huɗu suka tsaya a jere da uniform ɗin su kawunan su a duƙe,yarabanci guda ɗaya yake ta zabgawa wanda da ka ji za ka san kirari ake yi. Wata ƙatuwar ƙafa ce ta fara fitowa wadda ta fi kama da a kira ta da ta samudawa kafin hannunsa ya bayyana,sai kuma gangar jikinsa ta fito gaba ɗaya,ɗaure ƙaton mutumin yake da wani lafcecen zani,kai ka ce da atampa guda da ɗori aka yi shi,fuskar sa ta sha bille irin na yarabawan asali,kansa babu gashi ko ƙwalli ɗaya,banda ƙyalli babu abinda kan ke yi,tumbinsa kuwa za a iya yin girki a ƙatuwar tukunyar larabawa a juye masa tass a ciki ba tare da ya rage ko loma ba.Zaid ne ya kalli kansa ya kalli dika mutanen dake wajen,cikin ransa yake ayyana. 'Wannan daga ina kuma,ai ko ni da na fi kowa ƙiba a zuri'ar mu ya yaga min? Idan da za a haɗe mu dika mutanen parlourn nan ba za mu kai girman sa ba,ko dai me gadin yarinyar nan ne? Idan kuwa haka ne lallai za mu sha wahala kafin mu ƙwace dukiyar su.' Abinda yake tinani shi ne cikin zuciyar ƴan'uwansa,don haka sai suka kalli juna suka haɗiyi yawu muƙut,kallon bayan wannan ƙaton mutumin suke yi suna tinanin ta ina Lamyah za ta bayyana ita kuma,sai kawai mutumin ya yi wani surkulle,yana gamawa ya hura wa su Zaid iskar bakinsa,nan take suka zama tsuntsaye suka hau ƙoƙarin tashi sama. Kallon matasan dake tsaye a parlourn ƙaton nan ya yi ba tare da ya ce komai ba suka hau kama tsuntsayen nan suka wuce da su wani ɗaki na musamman. ************************ Bayan kwana tara da tafiyar Layuzah gida ne Kawunta Sale ya je gidan,wanda ya na zuwa ya tarar da Hajiya ta tasa Layuzah a gaba ta na faɗin. "Yanzu da ki ka ɗakko akwati da kayyakin ki kika tasa a gaba kina kuka me zai rage maki uhum? Na ce miki ki yi haƙuri kawun ki ya zo a je a bawa yaron nan haƙuri,tinda laifi dai mun riga da mun yi masa,amma kin ƙi saurara ta,na yi miki alƙawari ko zan yi yawo tsirara sai mun bi tudu da kwasazzabe,lungu da saƙo na samo miki maganin da za ki yi masa mallakar da baki yi masa ba ma a baya. Ballantana ma na san da an basa haƙuri zai haƙura,tinda yaron kirki ne." Cikin kuka Layuzah ta ce. "Hajiya ni babban tashin hankali na be wuce yanda asibiti suka kasa gano wannan ƙurjin na cikina na menene ba,sannan gashi wanda zai kashe min kuɗi ya kai ni har ƙasar waje a duba lafiya ta ya guje ni,azabar ciwo da raɗaɗi sun ishe ni,ki duba ki ga yanda nake ramewa kamar wadda ake ɗebarwa jini da tsoka. Ina kewar mijina Hajiya,bana jin zan iya sake kwana ɗaya ban gansa ba,kin dai sanni bana iya jure zama babu miji a kusa dani Hajiya." Cike da takaici Kawu Sale ya ce. "To ai sai ki bazama yawon duniya matar ayu. Na ce sai ki bazama yawon duniya,ke yanzu in banda lalacewar zamani mahaifiyarki zaki saka a gaba kina yiwa wannan furucin? Ke kuma Yaya kin zauna kina sauraren shirmen ta?" Hawaye Hajiya ta share ta na jin yanda ciwon hawan jininta ke son tashi,kafin ta ce. "To sale idan ban saurari shirmenta ba na wa zan saurara? Ba za ka gane yanda ake ji ba idan yara suna cikin damuwa, saboda kai dai baka ajiye ba,ballantana ka san zafin da ake ƙunsa a cikin rai. Ni dai taimakon da za ka yi min shine ka je ka bawa mijinta haƙuri ya mayar da ita,tinda ba sakin ta ya yi ba,cewa ta je gida kawai,idan kuma ba haka ba mu sayar da wani abun namu mu bazama nemo hankalinsa a inda ya dace." "Humm na gode Yaya da kika tinatar dani abinda na manta,amma kuma zan iya cewa alhamdulillahi tinda Allah bai bani haihuwar da zan lalata tarbiyar su ba ranar gobe ƙiyama Allah ya yi fushi da ni da su ya hukunta mu baki ɗaya ba. Ko kina zaton dan Allah ya baki haihuwa ba zai tambaye ki akan kiwon da ya baki ba? Misalin mai dabbobi ne da makiyayi,idan kika bada dabbobin ki kiwo aka dawo da su kika ga wani abu da baki so a jikin su ba za ki tambayi makiyayi ba? Idan ya kyautata ki bashi sakamako mai kyau,idan ya munana ki ɗauki mummunan mataki akansa. Lamarin ƴan Adam kenan ballantana mu da muke yin magana akan Allah Yaya,shi fa hukuncinsa ya fi na ƴan Adam daɗi idan an kyautata,sannan idan aka munana aiki mummunan hukuncinsa ya fi na ƴan Adam. Dan haka ki yi tunani da kyau akan abubuwan da kuke aikatawa,Allahn nan da kuka raina kuke yin abinda kuka ga dama shi ke da aljannah kuma shi ne yake da wuta." Shiru Hajiya ta yi ta na ƙifta idanuwa,saboda ta san ƙanin nata gaskiya yake faɗa mata,ganin ya taɓo inda ya dace har jikin su ya fara laushi ne ya sanya shi ci gaba da cewa. "Na shigo na ji kina faɗin kalmar wai ko zaki yi yawo tsirara zaki sama mata kan mijinta,to wai Yaya kin manta Allah ya ce zai gafartawa mai zunubi manya da ƙanana matsawar be haɗa shi da kowa ba wajen bauta,kin ga kenan duk girman zunubin ki da kin tuba,ko kuma kin mutu bayan kina a matsayin musulma wadda ta taɓa faɗin La'ilaha'illallah sannan take amsa sunan musuluncin to Allah zai iya yafe miki,amma matsawar kika yi shirka to fa babu ke babu jin ƙamshin aljannah ma balle ki shige ta,to ku faɗa min,miji ya kai matsayin da za ku sarayar da imanin ku ashe ku so shi sama da Allah da zai baku aljannah,amma idan kun yi haƙuri zai sabuntawa mijin naku kyakkyawar halitta ya haɗa ku a aljannah. Ke kuma da kike kiran ba ki iya zama babu namiji,ke kika so,saboda shegen shaye-shayen maganin mata barkatai wanda baki san daga inda aka fito da su ba,ke dai kawai ki sha maganin mata,shi yasa baki iya jure zama babu namijin,idan kuma haka ɗabi'ar ki take sai ki dinga yawan azumi,ki guji kallon duk abinda kika san zai motsa sha'awar ki,sannan ki gujewa karanta littattafan batsa da a yanzu suka zamo ruwan dare ko sauraren su,ki guji kallon finafinan batsa da yaran yanzu har ma da wasu dattawan birin suka maida shi ado wajen kallo. Idan kika yi haka za ki samu lada a wajen Allah,sannan zaki kare kan ki daga zina. Yanzu ki tashi ki tattara kayan ki mayar ɗaki ni zan je har gidan iyayensa mu zauna da magabatansa gemu da gemu na ji me yake faruwa." Hawaye ne suke ta zuba daga idanun Hajiya na nadama da kunya,sai ta kasa ɗaga idanunta ta kalli ƙanin nata har ya fita ya bar musu gidan. Ita kanta Layuzah nadamar abubuwan da ta aikata a baya ne ya sanya ta miƙewa ta wuce ɗaki ba tare da ta kwashe akwatinta ba da sauran kayan da ta watsar a kasa. Hajiya na zaune ta na kukan nadama ta ce. "Lallai na cutar da ke Layuzah saboda ban zamo daga cikin iyayen da ke bawa yaran su tarbiyya a bisa tsarin islama ba,a zato na duk iyayen da ke takura wa yaran su da kai su makarantar islamiyya da tsawatar musu idan sun yi ba daidai ba ba son su suke yi ba,rashin tarbiyyar da na taso ina yi wa mahaifinki kina kallo gashi duk kin kwashe har ma kin fi ni Layuzah,Ohh Allah ka yafe mini laifuka na manya da ƙanana,na ɓoye da na fili,Layuzah ki yafe mini kar na mutu da haƙƙin ki akai na ." Kuka sosai Hajiya take yi wanda ya sanya Layuzah kokawa itama,domin kuwa babu abinda bata ji ba daga bakin Hajiyan,cike da damuwa ta fito daga ɗaki ta duba inda Hajiyan ke ajiye magungunta ta ɓallo mata,sannan ta kawo mata ruwa ta bata ta sha,nan suka zauna Hajiyan ta dinga bata labarai game da irin rayuwar da ta yi a baya lokacin bata haife ta ba,a wancan lokacin suna cikin tsananin talauci da fatara,babu kalar cin mutuncin da bata yi wa mahaifinta ba,har dai ya bazama neman halal babu dare babu rana,ya tara abun duniya,sai da ya dawo dan ya zauna a ci dukiyar ya fara jinya,ciwon zuciya ya kama shi,har aka haife ta ya na fama da mummunan ciwon zuciya,ta na aji biyar a firamare ya rasu saboda bugawa da zuciyarsa ta yi. Kuka sosai suka dinga yi suna yi wa Baban Layuzah addu'a. Yau ma kamar koda yaushe Lamyah da Aminullahi sun shirya tsaf cikin shadda kala ɗaya za su tafi gidan Momma gaisuwar Juma'a,Lamyah sai yaba kyawun Yah Amee take yi shima yana yaba nata,ganinta yake yi kamar ba yarinyar da aka haifa baƙa ba,har hakan ya yi sanadiyyar sanya mata suna Lamyah da ya yi. Suna tsaka da shan soyayyar su wayar Aminullahi ta ɗauki ringing. Cikin sauri ya ɗauka domin ya gane ringing tone ɗin,kallon Lamyah ya yi ya ce. "Abii ne yake kira." Ɗagawa ya yi ya kara a kunnensa,cike da ladabi ya ce. "Dama yanzu za mu zo gidan...to shikenan gamu nan zuwa yanzun nan." Yana kashewa ya kalli Lamyah ya ce. "Abii ne yake kirana,ya ce duk abinda nake yi na bari na zo yanzu." "To yalla mu je tinda mun gama komai ko? Ohh jira ni na ɗakko abu a kitchen na zo." "Ki same ni a mota." Gaba ya yi Lamyah kuma ta wuce kitchen ta ɗakko abincin da ta dafawa Abii na musamman a jakar saka abinci ta kulle gidan bayan ta kashe kayan wuta ta bi bayansa...... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 42. Motar su na gama tsayawa a cikin gidan Azizah da Zahrah suka fito fuskokin su ɗauke da fara'a. Aminullahi kuwa zagayawa ya yi ya buɗe wa Lamyah ƙofa ta fito,sai da suka gaisa da masu aikin gidan sannan ya buɗe bayan motar Zahrah da Azizah suka taya ta ɗiban abincin da ta zo da shi suka shiga gidan suna hira,banda yaba kyawun da Lamyah ta ƙara yi babu abinda suke yi,ita kuwa murmushi kawai take zabgawa wanda ke nuni da kwanciyar hankali da natsuwar da ta samu a gidan aurenta. A babban parlourn gidan Aminullahi ya tarar da Abii da Kawu Sule suna tattaunawa akan matsalar dake a tsakaninsa da Layuzah. Sallamarsa ce ta katse su suka amsa masa a tare sannan ya durƙusa har ƙasa ya gaishe su. Bayan sun amsa masa ne Abii ya gyara zamansa sannan ya kalli Aminullahi ya ce. "Ashe abinda ya faru a gidan naka kenan bamu da labari Aminullah? Yaushe za ka tura yarinya gida ka barta ba tare da wani bayani ba,sannan mu nan baka sanar damu abinda ke faruwa ba? Muna jin ka yanzu ka yi mana bayanin abinda ke faruwa a gidan naka." Sosa kai Aminullahi ya yi sannan ya basu haƙuri akan hukuncin da ya yanke ba tare da sa hannun manya ba,daga baya kuma ya soma zayyana musu abubuwan suka faru tin daga farkon zamansa da Layuzah,cikin ɓacin rai ya ce. "Bata taɓa kallo na a matsayin mijinta ba sai idan tana da buƙatata ko kuma buƙatar kuɗi,ga baƙar ƙazanta,a duk lokacin da nake son na ga gidan nan da haske sai dai ni na gyara ko na kira daga nan aje a gyara mana. Bata girmamani ta raina ni ta yanda ban isa na sa ta ba ballantana na hana ta,idan za ta fita kuwa umarni take bani na yi kaza da kaza kafin ta dawo ba wai neman izinina take ba. Lokacin da aka ɗaura auren mu da Lamyah kuwa a daren da aka kaita ba domin Allah ya kare ba da yanzu ba da ni kuke magana ba zaman makokina ake yi ko na Lamyah. Shi yasa na yanke shawarar kawai ta koma gida,idan ta koyo tarbiyya da girki tare da tsafta sannan ta shirya zama da matata sai ta dawo." Ajiyar zuciya Kawu Sale ya sauke mai ƙarfi,domin a yanda ma ya ji maganganu daga bakin su Layuzah laifin su ya shallake tinanin Aminullahi,dan dai kawai ba zai yi kirari ya daɓawa kansa wuƙa bane,dan haka sai kawai ya ce. "Aminullahi babu abinda zan ce maka sai dai na ce ka yi haƙuri,ka sani duk wanda aka cuta shi ake bawa haƙuri,tabbas an cutar da kai,an zalunce ka. Babu amfanin zama da macen da ba zata zame maka wajen da hankalinka zai kwanta ba,babu amfanin zama da macen da zata dinga tada maka da fitina tare da tashin hankali a cikin gida,kai baka huta ba itama bata huta ba. Ni ba zan matsa maka ba akan ka mayar da ita ɗakinta,amma dai zan baka haƙuri akan laifukan da ta yi maka." Murmushi Abii ya yi,domin kuwa ya ji daɗin yanda Kawu Sale ya nuna dattako a lamarin,tabbas ya nuna shi ɗin dattijon azziƙi ne,shi yasa ya cewa Aminullahi. "Aminullahi ka tabbata yau ka je ka ɗakko matarka ka mayar da ita gida,bana son na ji wasu ƙananan maganganu akan hukuncin da na yanke. Allah Ya yi maka albarka ya daidaita tsakanin ku,Allah Ya zaunar da ku lafiya ya kare ku daga sharrin shaiɗan,Allah ya baka ikon tsayar da adalci a tsakanin matanka. Malam Sale ita kuma a ja mata kunne sosai,saboda ko mu ta nan babu irin zagi da cin mutuncin da bata yi wa mai ɗakina ba,kawai dai mun bari ne akan zafin kishi ne ya sanyata yin abinda ta yi,dan haka a nuna mata kuskuren abinda take yi wanda ba daidai bane,ta kuma shirya zuwa dare idan sun kammala ziyarar da suke yi duk Juma'a za su shiga gidan ya ɗakko matarsa ta koma ɗakinta." Lamyah ce ta daskare a inda take a tsaye jin kalaman Abii,wani irin abu ne mai tsinin da ya fi mashi tsini,mai kaifin da ya fi takobi kaifi,mai zafin da ya fi wutar maƙera zafi,mai raɗaɗi da azabar da ta fi ta gulandon da aka fama ciwo ya soki zuciyarta,numfashinta ta ji ya na kaiwa da komowa,da sauri ta juya zata koma inda ta fito,domin bata san abinda ke faruwa ba,suna tsaka da hira da su Momma ta miƙe dan ta je gaishe da Abii da Mubarak ya ce mata yana babban parlour,sai kuma ta ci karo da wannan tashin hankalin. Aminullahi wanda ya ga gilmawarta da sassarfa ne ya miƙe cikin sauri ya ce. "Abii ina zuwa don Allah." Kusan da gudu ya ƙarasa fita ya bi bayan Lamyah dan kar ta ɓace masa,a ɗakin Iya ya tarar da ita tana kwance saman cinyar Iya ta na risgar kuka mai matuƙar ƙuna a zuciya. Lamyah bata taɓa sanin zafin kishi haka yake ba,ashe idan kana son mutum da yawa haka zuciyar ka ke tafarfasa idan ka gansa da wata? Me yasa a baya bata jin haka a game da shi sai yanzu? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa. 'Saboda a baya soyayya kike yi masa tin ta yarinta,baki san garɗi da zaƙin dake cikin soyayyar aure ba,sai da kuka zamo abu guda.' Kuka ta sake rushewa da shi wanda ke sake ɗaga hankalin Iya,cike da damuwa Iya ke ta tambayarta abinda ya sameta. Ganin Aminullahi ya shiga a hargitse ne ya sanya Iya haɗe fuska ta na kallon sa ta ce. "Masoyi me ka yi mata? Yanzu ashe ba za ka bar zuciyar yarinyar nan ta huta ba?" Cikin marairace fuska ya ce. "Bani da laifi Iya,umarni Abii ya bani akan na mayar da Layuzah ɗakinta,da aso na ne ba zan taɓa mayar da ita ba na gama zama da ita kenan,amma ke kin sani ba zan taɓa tsallake umarnin Abii ba,ko da kuwa bana so." Jikin Iya ne ya yi sanyi ta miƙe tsaye ta bar musu ɗakin,ita kanta bata ji daɗin hukuncin da Abii ya yanke ba,sai dai babu yanda za su yi da abinda ya fi ƙarfin su. Aminullahi kuwa zaman lallashi da ban baki tare da bada haƙuri ya yi,nan da nan kishin larabawa ya haɗe da na mutanen kano ya fara taratsatsi. Tun Aminullahi na damuwa har ya dawo dariya tare da jin daɗi a ransa,cikin tsokana ya ce. "Ashe dai Babyn Yah Amee na son shi har haka,lallai yau sai na taka rawa na juya,wataƙila ma DJ zan kirawo na shelanta yanda Babyna ke so na kuma take kishi na,wanda ba kowanne namiji bane Allah ke yi masa baiwar samun mace kamar ki ba." Yanda yake kwarzanta ta da kambama soyayyarsa a gareta ne ya sanya ta murmusawa hawaye na ci gaba da zuba daga idanunta,ɗaukanta ya yi gaba ɗayanta ya ɗora ta saman cinyarsa,lallashinta ya ci gaba da yi da zazzafar soyayyarsa da ke ƙara mata kishinsa a ranta. Ganin ba za ta dena kuka bane ya sanya shi fara share mata hawayen ya na cewa. "Ki yi haƙuri haka ki dena yi min asarar hawayen ki don Allah, kin sani ke ce mace ta farko da na fara so,kuma har yanzu ke nake so,ban taɓa jin son kowa ba a cikin raina,ban sani ba ko anan gaba,amma dai na san cewa zuciyata da soyayyar Lamyah ta ginu,a lokacin yarinta da kuma girma." Dukan ƙirjinsa ta yi a shagwaɓe ta ce. "A lokacin yarinta dai,a lokacin girmanka ba Lailah ka ke so baa." Dariya ya yi kafin ya kama yatsunta ya na cizawa a hankali,cikin lumshe idannuwansa tare da tinano ranar da ya fara ganinta ya ce. "Sai kuma Allah ya taimake ni Lailahn ce dai Lamyah ta ba. Ina son ki A'ishatu,ina son ki sosai son da ba zan iya misalta miki shi ba,da ace so kogi ne da sai na ce maki wanda nake yi maki yafi kogin maliya girma,da kuma a ce so ƙasa ce,lallai da na ce maki son da nake yi maki ya fi saharar dake cikin ƙasashen larabawa yawa. Lamyah da ace so iskar da ake shaƙa ne to fa tabbas da iskar duniyar nan gaba ɗaya ta yi kaɗan ta haɗa kanta da soyayyar da nake yi miki,Lamyah ke ce farko a zuciyata,kuma ina fatan kowacce mace ta biyo bayanki." Tsabar farinciki da jin daɗin kalaman Aminullahi da Lamyah ta ji ne suka sanya ta rungumesa tare da sanya bakinta cikin nasa kamar yanda ya sabar mata. Ba tare da ɓata lokaci ba Aminullahi ya saki jikinsa ya na amsar saƙon da Lamyah ke aika masa da shi. A haka Iya ta sallama ta riske su,salati ta saka sannan ta ɗauki pillown ta da aka wurgar ƙasa ta jefa wa Aminullahi ta na faɗin. "Tashi ka fita ka bani waje mara kunya,a ɗakin nawa za ka kanainaye yarinya Aminullahi?." Dariya sosai Aminullahi ya fara yi cike da kasala ya miƙe,kallon Lamyah ya yi wadda tai tsuru-tsuru ta na zare ido,kanta a ƙasa kamar mara gaskiya,murmushi ya yi sannan ya ce. "Lallai Iya na yarda yanzu wannan ɓakar yarinyar ta ƙwace min fada a wajen ki,ita fa kika gani zaune a saman...." A guje Lamyah ta ratsa ta tsakaninsu ta fita da gudu ta na rufe fuska don kunya,ɗakin Momma ta gudu ta faɗa gado ta na dariya. Momma kuwa da ta ga wucewar ta ta na dariya sai itama ta yi dariya,duk da cewa bata san abinda ya sanya ƴar tata farinciki ba,amma ganin ta a wannan yanayi ya sanyaya ranta,ba dan komai ba sai dan sanin cewa Abii ya umarci Aminullahi ya mayar da Layuzah. Mubarak ta ɗaga daga cinyarta ta bi bayanta,ta na shiga ta tarar da ita kwance ta dunƙile waje guda ta na sakin murmushi. Kalaman Aminullahi ko da ƙarya ne to fa sun yi gini a zuciyarta,gini da baƙar dalma ma kuwa,dan ta san fitarsu a ranta ba abu bane mai sauƙi. Dafa ta Momma ta yi sannan ta zauna a gefenta. Tashi ta yi zaune ta kwantar da jikinta a na Momma,cikin kalamai masu taushi da sanyaya zuciyar mai saurare Momma ta dinga tausar zuciyar Lamyah akan haƙuri da zama da kishiya. Sannan ta dinga koyar da ita dabarun zama da miji da yanda za ta kafa kanta a cikin zuciyar Aminullahi zama na har abada. Daga ƙarshe tare suka je kitchen duk ƙiwar Momma a ranar ita ta girkawa Lamyah abubuwan da ke ƙarawa mace ni'ima ta haɗa mata na sha na musamman,su Zahrah kuwa ba ƙaramin jinjina lamarin suka yi ba,dan kuwa ko Abii Momma bata yi masa girki,sai gashi ta yi wa surukarta kuma ƴa a wajenta. Suna gamawa suka kwaso komai suka koma parlour,Lamyah kuwa babu kunya haka ta zauna ta lashe komai ta shanye komai,ta na kammalawa suka ɗora da hirar su,sai dai rashin ganin Aminullahi ya sanya ta zargin ko ya wuce wajen Layuzah tin yanzu? Ai Abii cewa ya yi sai dare zai je ya ɗakko ta. Lokaci zuwa lokaci take duba wayarta tana tinanin ko message za ta yi masa ta ji inda yake? Ɗaya daga cikin nasihar da Momma ta yi mata a ɗaki ce ta faɗo mata. 'Ƴata kar ki zamo me yawan binbinin miji da son sanin shin yana wajen kishiyata ne ko ya na ina? Idan yana wajenta ki sa a ranki kawai wani hutu kika samu da kuma mayar da abinda kika rasa na daga ni'imar jikinki,kafin ya dawo wajen ki kin ƙara gyara masa kanki,ta yanda ke da shi za ku samu gamsuwa da junan ku ba tare da gundura ba,idan kuwa kika zamo mai binbini da mita tare da jassasar inda mijinki ya tafi,to za ki gundire sa sannan kuma za ki shiga haƙƙin abokiyar zaman ki.' Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi,a haka suka wuni har dare Aminullahi bai dawo ba,sai da misalin takwas da rabi na dare suka dawo shi da Abii. A sannan ne hankalinta ya kwanta,ba ta tambaye shi inda ya je ba ta fara shirya kayanta da jikinta suka wuce.Ta yi zaton gidan su Layuzah za su tsaya sai ta ga ya wuce. Har ta fara tunanin ko zata ce masa ya fara kaita gida kafin ya ɗakko matarsa,amma ta kasa buɗe baki ta yi magana,saboda gudun kar ya ga ta cika korafi ya fara jin haushinta. Gani ta yi sun ɗauki wata hanyar da bata san ina ne ba,sai da suka yi tafiya mara nisa sannan suka tsaya a wani shago,shiga ciki ya yi ya hau yin siyayyar kayan ƙwalama,sannan suka koma unguwar su Momma,a ƙofar gidan su Layuzah ya tsaida motarsa, wayarsa ya sa ya kira layinta da ya manta rabon da ya kira ta ko ya amsa nataccen kiran da take yi masa a kullum. Layuzah kuwa ta na cikin gidan su ta shirya tin a lokacin da Kawu Sale ya je ya sanar da su hukuncin da Abii ya yanke na komawarta a ranar. Murna da farinciki ne suka baibayeta ta miƙe tsaye da mugun gudu ta

Chapter 26 of 30