Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai seta fara rera shi
cikin dishashiyar muryan ta da baya fita sosai da sauri Indo ta juya ta wuce ɗakin
ta dan batason ganin Ayrah na kuka haka gashi ba yanda zatayi,Indo ne yau tayi
gyaran ɗakin tass sannan ta ɗaura girki haka Ayrah tayi wuni churr a wajen sede
kuma idan har aka kira Sallah toh tana tashi duk da tana tsoron kar ta tashi Anty
tazo Amma haka take daure wa ta tashi toilet ɗin Indo take shiga tayi alwala ta
zumbuɗa hijab ɗin indo tayi Sallah sannan ta koma har indo ta gama girki har bayan
la'asar tana gurin Sallah kawai ke tada ita seda akayi magrib bayan ta dawo daga
Sallah kaman dama jira Anty take ta dawo kawai sega tanan ta shigo kallon arziki
bata samu daga gurin taba tace ta wuce tabar ɗakin zasu haɗu gobe ne da sauri ta
miƙe ganin Anty na nufi ta tayi waje da gudu tabar ɗakin part ɗin su ta wuce duk
agajiye take koda ta shiga babu kowa a ɗakin duk a wargaje dan yau besamu gyara ba
hakan yasa ta fara gyara ɗakin kafin ta ɗauro alwala dan gabatar da Sallah isha'i
tana cikin yi sega Eshall ta shigo toilet ɗin ta wuce darect alwala tayi ta fito ta
fara sallah la'asar da magrib da isha'i ta haɗa tayi su duk lokaci ɗaya Ayrah kuwa
har ta Idar ta ninke sallayan ta maida shi inda yake kwata kwata batayi mamakin
ganin Eshall na Sallah ba dan haka take yi wani lokacin seta haɗa duka salloli
biyar ɗin nan lokaci ɗaya tayi shi wataran cikin dare take tashi tayi su, ɗale wa
bed nata tayi tasan gobe bata da Time ɗin yin karatu hakan yasa batayi ƙasa a gwiwa
ba wajen ɗaukan books nata ta fara karan tawa abun mamaki Eshall na idar da Sallah
ita ma ta ɗale bed nata school back ɗin ta ta ɗauko ta fito da wasu takardu ta fara
dubawa ga wayanta tana dubawa tana kallon wayan ba komai bane a cikin wayan face
answers na questions ɗin da za'a tambaye su gashi nan wani malamin ta ya tura mata
daga amsan objective har na Essay haka ta gama duba littafin ta kalli questions ɗin
kana ta mayar da littatafan ta ajiye jakan a gefen bed nata Ayrah kam karatun ta
tayi sosai sannan ta rufe book ɗin ta ɗauki wasu ta karanta har seda ta fara jin
baccin ya fara cin ƙarfin ta sannan ta rufe book ɗin ta tasi taje tayi alwala tazo
tayi addu'an bacci se kawai ta kwanta se bacci kuma dan dama a gajiye take sosai,
Eshalla kuwa se dudduba answers ɗin da sir Emanueler ya turo mata take yi rants
fess ko yanzu a shiga Exams bata damu ba, sir Emanuel shine best teacher ta suna
shiri sosai sabida tana cika mai aljihu da ƙuɗi ba kaɗan ba kuma sonta yake yi shi
yasa can wurin past 10 Marwa ta shigo ko sallama babu ko wanka bata yiba tana zuwa
ta baje kan bed wani irin kallon banza Eshall ta watsa mata taja tsaki dan basa
shiri ko ƙaɗan duk da suke uwa ɗaya uba ɗaya abun yana ɓatawa Mama rai sede kawai
tana danne wa ne kuma tafi son Marwa sosai duk inda zasu tare suke zuwa tafiyin
abubuwan ta da Marwa yanzu ma tare suka dawo sun fita tun safe, itama Marwa tsaki
taja kana ta fara shirin kwanciya duk hatta kayan da ta tuɓe anan ta barshi ga
takalmin da ta shigo dashi har cikin ɗakin yana gurin shima wayanta ta ɗauka yau
tayi matuƙar gajiya tana buɗe data itama taga an turo mata answers questions nasu
duka subject ɗin shiga tayi ta gani sanna ta fita dan ita bama shi band a gaban ta
tasan sir Samuel ne ya turo mata malamin ya matsa mata sosai kawai tana biye masa
ne Amma ita baya gaban ta shine de dayake son shishige mata nan tafara danne danne
da wayan duk kowa yayi bacci ya barta se kusan 2 na dare ta kwanta wani bacci ya
ɗauke tana sawa a ranta gob dole Ayrah ta mata wanki dan ta tara sosai kuma tana
buƙatar su, washe gari...

*DAN GIRMAN ALLAH KU DIN GA TAYANI SHARING FISABILILLAHI 🙏🏼☺️
☺️☺️
☺️*

COMMENT
LIKE
SHARE
FISABILILLAH

🌹Mhizz teemah🌹

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa ilmantarwa harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


Page 24_25

Washe gari bayan ta tashi tayi Sallah wanka ta shiga tass tayi ta fito kullum
kanta da hula bata buɗe shi se idan zata yi wanka itade batasan yanda zata yi da
gashin ba dan bazata iya wanke kan nata ba gashin ya mata yawa shiyasa kullum kan
yake a kulle kitson kanta ba ƙaramin jimawa yayi ba har kitson ya saje da gashin
kaman ba kitso ne akan ba se wanda ya lura ne ze gane toh bama barin kan takeyi a
buɗe ba kullum kai yana cikin hijabi ɗan ƙarami zuwa cikin ta, tsaf ta shirya cikin
doguwar rigar material me ratsin fari da baƙi tayi kyau ga shatin bulala raɗas a
fiskanta da shatin tafin hannun Anty data mare ta idonta ya faɗa sosai duk wannan
uban ayyukan da take sha bata rame sosai ba se wanda ya lura ne zega yanda taɗan
rame a fiska ba sosai ba nan ma,


fita tayi daga part ɗin nasu ta wuce na mama jiya bata shiga ta gyara mata ba hakan
yasa yau ta fara shiga nan tsaf ta gyara ɗakin ko ina yayi tsaff Mama tana bacci
har ta gama ta wuce part ɗin Anty bakin ta ɗauke da sallama kaman de yanda ta saba
ƙasa ƙasa a falo ta taras da Anty tana daddana waya kaman yanda ta saba har ƙasa
Ayrah ta tsuguna ta gaishe ta Amma bata amsa ba kuma bata kalle taba tashi tayi
simi simi ta fara gyara ɗakin tsaf har kitchen bata samu Indo a kitchen ɗin ba ta
leƙa ɗakin ta bata ganta ba sede taji ƙaran ruwa a banɗaki wanka take yi fita tayi
ta cigaba da gyaran ɗakin ta tsaf tayi shara da mopping da goge goge ɗakin munib ta
shiga yana bacci nan ta gyara har da banɗakin sa ta wanke


tana fitowa Anty ta miƙe ta shige ɗakin ta bin bayan ta tayi dan tasan abinda take
nufi kenan yau kusan kwanan ta huɗu ko fiye da haka ma bata gyara ɗakin ba tun
kafin dad ya dawo,ya ilahi ɗakin yayi datti ba kaɗan ba ga kayayyaki nan a baje a
kan bed ɗin ita Ayrah har yau tsoron ɗakin take yi tun ranan da tayi mummunan gamo
har yau abun be fita daga ƙwaƙwalwan taba,wajen mirror nan duk yayi datti ko ina ba
kyan gani ga wani ɗan banzan warin da ɗakin yake yi me hargitsa hanjin ciki kunsan
idan wari yayi yawa a guri yana saka murɗan ciki mutum ya rasa gane kansa toh haka
yake a gurin Ayrah ma warin yanzu ya fara fin ƙarfin tunanin ta yayi yawa over tun
tana danne wa bata toshe hancin ta har ta fara toshe wa, gyaran ɗakin ta fara tana
tottoshe hanci duk abinda take Anty na kallon ta hakan kuma ba karamin ɓata mata
rai yake yiba ganin yanda Ayrah take toshe hanci ita de Anty bajin warin ɗakin take
yiba shi yasa take ganin kaman toshe hancin da Ayrah take yi ta raina tane ko kuma
ita ɗince me wari,

haka Ayrah ta naɗe kayan kan bed ɗin nan tass ta buɗe drawer ta saka su sannan ta
fara shara tsaf ta share ɗaki ta dauko mopper ta haɗa ruwan mopping nan ma tayi ta
goggoge jikin drawers ɗin da suke ɗakin na jikin mirror dana gado duka tsaf ta gama
gyaran bata leƙa toilet bama balle taga abubuwan da suka fi ƙarfin idon ta har
tasaka su air freshener na ɗakin tazo zata fita har ta riƙe handle ɗin kofan Anty
da tun dazu haushi take bata jira kawai take tayi laifi dama ga kuma yanda ta ƙular
da ita ganin tana toshe hanci,ta daka mata tsawa tana miƙewa daga kwanciya da tayi
kan bed ɗin ta ƙara sa gurin kofan batai aune ba kawai taji wani masifaffen zafi a
bayan ta na dundun da Anty ta ɗirma mata sannan ta fara magana


''dan uwarki ni kika barwa toilet ɗin na wanke miki da bed ɗin da zaki kama hanyar
fita? wato raini ya fara shiga tsakanin mu kenan ki kiyaye ni ki fita a idona inba
so kike na nakasa kiba tamm!!!!'' da sauri Ayrah da ta sunkuya tana sosa bayan ta
tsabar yanda dundun ya shige ta ta miƙe bed ɗin ta fara shumfuɗa wa tsaf sannan ta
wuce banɗakin ta riƙe handle na ƙofan toilet ɗin ta tsaya tayi addu'a sannan ta
buɗe wani irin wari ne ya daki hancin ta seda ta ja baya se kuma ta daure ta shiga,
banɗakin ba kyan gani,ya ilahi wannan banɗakin se me ƙarfin imani ne ze iya shiga
wani irin wari yake yi me ɗaga hankali as usual datti ya manne a jikin farin tiles
ɗin yayi brown sosai cikin toilet (wajen yin kashi) wani kalan Maroon da Brown ya
haɗu ya bada wani kalan ruwan cikin,ruwa ta fara tara a bocket sannan tayi flushing
na wannan ruwan cikin toilet ɗin duk da haka jikin shi ya canza color seda ta tari
ruwa me ɗan yawa ta kwara a kasan banɗakin ta ƙara taran wani nan ta saka su hypo,
detol, morning fresh, duk wasu detergent na wanke banɗaki


seda ta saka ta fara wanke cikin toilet ɗin bayan tayi flushing sannan ta wanke
mirror da sink na cikin banɗakin seda ta gama tsaf sannan ta dawo kasan tiles na
banɗakin nan ma tafara wanke wa,ba ƙaramin wahala tasha ba wajen wanke banɗakin
tsaff ta wanke sa ya fita har wani shining yake yi warin yaɗan ragu sosai Amma be
fita duka ba baiwar Allah nan harda hawaye tayi wajen wanke toilet ɗin tana haƙi
kaman wacce tayi tsere da doki haka ta fito duk ta jiƙe da uban zufa,

miƙewa Anty tayi tace ta biyo ta haka ta bita simi simi fita suka yi daga part ɗin
wasu ɗakuna guda biyu wanda suke manne da juna ta ɓangaren Mama suka je ganin haka
seda cikin ta ya ƙulle ta fara tunanin karde a ce su ya Abdull ne zasu dawo,bata
gama tunani ba taga Anty ta ciro key ɗakin farko buɗe ɗakin tayi duk yayi ƙura
sabida ya jima ba'a shiga ba falo ne ɗan daidai se ɗaki haɗe da banɗakin sa kujerun
an rufe su da fararen abubuwan da ake rufe kujeru,nuna mata ɗakin Anty da ta tsaya
a bakin ƙofa bata shiga ɗakin ba tayi sannan ta fara magana cike da izza da halin
ko inkula

''gobe yayun ki zasu dawo sun ce ki gyara musu dakin su dan haka ki musu gyara me
kyau idan be fita da kema kinsan sauran ki gama wannan sannan ki shiga wancen duk
ki gyara su'' tana gama faɗan haka ta wuce ta koma part ɗin ta tabar Ayrah da tayi
suman wucin gadi tana tunani watan cin ubanta yayi kenan dan wallahi tana mugun
mugun tsoron yayyen nata, taɗau kusan minti biyar tana tsaye a gurin kafin kuma
kaman wanda aka tsikara tayi saurin dawowa tunanin ta shiga ɗakin tayi ganin yanda
duk yayi ƙura haka ta shige cikin ɗakin ko ina yayi ƙura ga datti ga kuma wasu daga
cikin kayayyakin su a zube a ƙasa wanda suka tafi suka barshi a gurin banɗakin ma
duk yayi kura ga datti tana nan de maƙale da hijabin nan nata kaman na gado dashi
take kwana dashi take tashi kullum ga zufa tana haɗa wa ba halin ta kunna fanka ko
AC tunda gyara zata yi ga ƙura zena dawo mata da aki baya ne tattare ɗakin ta fara
yi kayayyakin da suke zube a ɗakin duk tasa su cikin wash machine anan taga wani
hanky cikin drawer ɗauka tayi ta ƙulle hancin ta sabida protection ga kuma ƙura
aiki ta fara ba kama hannun yaro ta ɗauki kusan past 2hr tana gyara ɗakin ɗaya
kawai yayi ƙura ne na wuce misali sunyi kusan 2yrs basa nan shiyasa tsaf ta gyara
nan da nan sega ɗakin yayi kyau


ta gyara ko ina harda canza bed sheets ta wanke banɗakin nan tass har jikin bango
komai yayi clean seda ta gama sannan ta kunna washing machine ɗin tana tsaye a
gurin tsaf seda ya gama ta fito da kayan taje ta shanya su ta kunna AC falo dana
ɗakin duka ta saka Air freshener ɗakin ya ɗauki kamshi ba ƙaramin kyau ɗakin yake
dashi ba yayi tsaf tsaf kaman ba'a taɓa shiga ba ita kanta seda taji ina ma ta
kwanta ta huta Amma ba hali tunda bata gama ba saura ɗayan ɗakin lokacin azahar ma
tayi ta kashe wutan ɗakin AC kawai ta bari sabida ɗakin yayi sanyi Amma ta rage
power sa sannan ta fito daga ɗakin ta rufe harda key ta zare key ɗin ɗayan ɗakin ta
buɗe da ɗayan key ɗin dayake duk ajiki suke,shiga ɗakin tayi ta buɗe ko ina already
ta cire hanky data ɗaura tun a ɗakin chan ɗin ta wanke sa,bata taɓa komai a cikin
ɗakin ba kawai ta buɗe ne se tace bari taje tayi Sallah ta dawo seta ƙarasa gyaran,

part ɗin su ta wuce her heart is racing tana addu'a Allah yasa kar Anty ta leƙa
bata ganta ba dan tasan shima wani laifi ne da wannan tunanin ta shiga ɗakin su
direct ta wuce toilet alwala ta ɗauro ta shumfuɗa abun Sallah ta zumbuɗa katuwar
Hijab ɗin ta har ƙasa ta cire ƙaramin ta fara Sallah, Marwa da Eshall har lokacin
bacci suke yi tana idar wa ta miƙe ta cire hijab ɗin tasa ƙaramin naɗe darduman
tayi ta ajiye sa tare da hijab ɗin nata bata ko kalla inda su Eshall suke ba ta
fita a ɗakin tana sauri kar tayi wani laifin kuma,


seda taji sanyi a ranta ganin Anty bata zoba ƙarasa shiga cikin dakin tayi nan ta
fara aiki tattare kayan ta fara yi ta share ta kaɗe ƙuran tahau share share ta kaɗe
kujerun ba wani datti bane ajikin su kawai ta kaɗe ne dan a rufe suke gyara dakin
tayi tass ta shiga banɗaki ma ta wanke shi seda ta gama gyara ko ina ta saka kayan
datti a washing machine ya gama ta shanya ɗakin yayi fresh kaman ba'a taɓa shiga ba
air freshener ta sakawa ɗakin ta kunna AC nan da nan ɗakin ya ɗau sanyi ga ƙamshi
zama tayi tana hutawa har ta fara gyangyaɗi taji sanyi AC miƙewa tayi ta kulle
ɗakin da key bayan ta kashe wutan dakin tabar AC kaɗai ta rage power sa bata wuce
part ɗin Anty ba se ta wuce nasu lokacin su Marwa sun tashi basa ma dakin ajiye
keys ɗin tayi kan bed nata ta ɗauki wasu kayan duguwar riga shima ta wuce banɗaki
wanka tayi tana son wanke kanta Amma ba zata iya ba kayan da ta ɗauka ta saka ta
fito hijab ɗin ɗazu ta maida kana tayi Sallah la'asar dan ta ɗauro alwala tun a
bandakin tana idar wa ta ɗauki keys ɗin ta fita direct se part ɗin Anty bata same
ta ba dan haka se ta wuce ɗakin Indo yunwa take ji kuma tasan Indo ta ajiye mata
abincin tana shiga ta zauna gefen Indo abincin da ta ajiye mata ta bata karɓa tayi
ta fara ci indo kuma na mata sannu dan tasan aiki tayi,


kullum tana son tambayan Indo wai bata da waya ne Amma se ta manta yau ko tana
cikin cin abinci ta tuna ɗagowa tayi ta kalli indo da dara daran idanun ta se kuma
ta sauƙe kanta ƙasa ta buɗe baki cikin sanyi hali irin nata da zazzaƙar muryan ta a
kuma hankali cike da nutsuwa tace ''Anty Indo ina wayan ki ne ni ban taba ganin ki
da waya ba naga bakya ƙiran ƴan uwan ki da maman ki'' kallon ta Indo tayi cikin
basar da magana tace ''bani da waya'' se tayi shiru bata ƙara cewa komai ba kallon
ta Ayrah tayi ganin kaman bata son maganan se kawai tayi shiru dama ita ba gwanar
magana bace,har ta kare abincin tass ta wanke hannun ta miƙewa tayi ta fita a ɗakin
falo ta wuce ta zauna inda take zama tana jiran Anty ta shigo tayi kusan 30min
sannan Anty ta shigo tana ganin ta tayi ƙasa da kanta tace ''Anty na gama'' miƙa
mata hanu Anty tayi ganin hakan yasa ta gane key zata bata samata key tayi a hanun
seda ta juya ta fara tafiya sannan tace ''biyo ni'' binta tayi kaman yanda ta faɗa
ɗin hanya ɗakunan suka yi ta buɗe duk taga yanda tayi gyaran seda ta duba duka
ɗakunan duk Ayrah na biye da ita gyaɗa kai kawai tayi ta fito ta rufe ɗakunan bata
ce komai ba tayi hanyar part ɗin baba ganin hakan se Ayrah ta juya zata yi part ɗin
Anty,


har tayi gaba se taji kaman ba'a biyo ta juya wa tayi se taga Ayrah kam har ta kusa
shiga ɗakin ta,wani mahaukacin tsawa ta daka mata ''ke ina zaki ba cewa nayi ki
biyo niba'' da sauri Ayrah da har ta taka step zata taka na biyu ta juyo ta biyo ta
harda gudun ta part ɗin Dad suka ƙarasa nan ma wani sabon aiki ne dan seda ta gyara
ɗakin nan tas gaba dayan shi yayi part ɗin Mama da na Anty tsabar girman sa Amma
haka ta gyara shi ba ƙaramin gajiya tayi ba, ta aikatu iya aikatuwa yau ɗinnan ko
iya gyaran part ɗin Dad aka barta dashi ma aiki ne ballan tana tun safe bata huta
ba ta gyara part ɗin Anty tayi na, Mama, tazo tayi na yayyun ta wanda yaji ma a
rufe duk yayi ƙura,after that tazo tayi na dad ɗin ta, haba dole ma duk wanda yaji
irin aikin da tayi ya tausaya mata ta aikatu ta kuma gaji duk me zuciyar imani seya
ji tausayin ta a ƴan kananun shekarunta nan,


magrib aka ƙira hakan yasa ta baro part ɗin Anty wanda bayan ta gama gyaran part
ɗin Dad nan ta wuce munib kullum bacci yake sha abunsa kaman kasa baya wani wasa
toh ma dawa zeyi wasan bayan shikaɗai ne daga yaci abinci se bacci se kuma idan
yanada karatu yayi ko yaje gurin Ayrah suyi tare shi yasa bayan ta gama gyara part
ɗin Dad ta koma na Anty suka yi karatu da munib dan tasan idan ba ita ba bawanda ze
koya masa kuma gobe suna da Exams,

tana shiga part nasu bata taras da kowa ba alwala tayi tayi sallah as usual ta
zauna har seda tayi isha sannan ta tashi books nata ta ajiye kan bed sannan ta
ɗauki uniform nata da kayan ta da sukayi datti ta wuce toilet ta fara wanke su tana
cikin yi su Marwa suka shigo se a lokacin Marwa ta tuna zata bawa Ayrah wanki jin
ƙaran ruwa a banɗaki yasa ta nufi toilet ɗin ba ruwan ta da ko wanka take ko wani
abu haka ta banka ƙofan toilet ɗin seda Ayrah ta tsorita ta juyo da sauri ganin
Marwa seta cigaba da wankin ta ''ke'' Marwa ta faɗa da masifa miƙewa Ayrah da har
ta kusa gama wankin ta tayi tana kallon Marwa ''biyo ni''shine abinda tace haka ko
akayi ta bita kamn yanda ta faɗa ɗalewa bed nata Marwa tayi ta hakimce sannan tace
''ki haɗa kaya na ki wanke min su yanzu kuma sufita'' gyaɗa mata kai Ayrah tayi
kana ta wuce wajen drawer Marwa buɗe wa tayi a loka na ƙasa kayan suke haka ta ɗibe
su ta wuce toilet dasu seda ta gama wanke nata tass ta shanya su a banɗakin kana
tahau wanke ƙananan kayan Marwa duka su pant ne da bra se vest da underwear duka
haka ta wanke seda ta gama tass wajen past 9 sannan ta fito ta ɗale nata gadon ta
ɗauki books nata ta fara karanta wanda suke dashi gobe, tasha karatu ba kaɗan ba
kafin wani waha lallen bacci ya ɗauke ta already tayi addu'an ta tin kafin ta fara
karatun, su Marwa da Eshall ma duk sunyi bacci da wuri sabida Exams da zasuyi gobe
akwai zuwa school da wuri, washe gari

🌹🌹London 🌹🌹

Zaune suke gaba ɗayan su kan dining suna break fast Ajeeb yace ''wallahi na matsu
na koma nayi missing Mom da baby Ruma'' Ammar yayi sauri caɓe zance da cewa ''nima
na gaji da ƙasar nan like serious i wanna see me at home'' duk wannan magana da
suke yi gogan na jinsu Amma be sa musu baki ba ya cigaba da cin abincin sa kaman be
jisu ba Ammar ne yayi ƙasa da murya yanda daga shi se Ajeeb ne zasu ji magana da
yayi yace ''jibi sheed muna magana yayi kaman be jimu ba Amma yanzu da a gaban Mom
yake haka zasu ta taɗi harda dariya ma sabida mu ya rena wa wayo shi yasa yake
share mu wallahi'' ƙasa da murya sosai Ajeeb yayi yace kyale sa ai kafin mu tafi se
mun tsokano sa wallahi se mun sashi magana ne kaide barshi'' kaf wannan magana da
sukayi rass a cikin kunnen sa duk da haka be nuna musu yaji suba ya cigaba da cin
abincin sa kaman besan dashi suke ba su kuwa duk a zaton su beji suba gya ɗa kai
Ammar yayi yana murmushin da shi kaɗai yasan dalilin yin shi,tissue ya ɗauka ya
goge bakin sa ya haura staircase ya wuce ɗakin sa haka suma suka gama suka koma
cikin falo can bayan mintuna se gashi ya sauƙo sanye da uniform na sojoji yayi ɗan
banzan kyau yana taku cike da izza yayi bala'in kyau kamshin sa ya karaɗe ko ina na
cikin falon kafan sa na sanye black cover shoe gashin kansa ya kwanta luff har
bayan wuyan sa in a stylish way dayayi mugun mugun masa kyau kwayar idon san nan se
ɗaukan ido yake koya mutum yakai ga son haɗa ido dashi baya iya wa sabida kwarjinin
sa ga haiba tattare dashi yana da wani irin shiga rai yanda ko sunan sa mutum yaji
se yaji ya kamu da son me sunan koda kuwa be kalle saba hanun sa na ɗaure da
danƙare riyar agogon Rolex me ɗan uban tsada taka stairs ɗin yake cikin nutsuwa
daka ganshi kaga ƙaƙƙarfar meji da jini a jika har ya ƙarasa sauko wa su Ammar da
suka zuba masa ido suna ganin tsantsar kyau da Allah ya masa ga wani irin baiwa da
Allah ya bashi basu san ya sauka ba su kansu ya tafi da imanin su inaga duk wata
mace da tayi arba dashi kuwa su kansu

Please Login or Register in order to submit comment