Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

teemah🌹

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_________________________________________________________*
Dedicated to my beloved 💔Mom💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵

Free Page 6_7

Sunɗa taba hira kadan kafin Ruma ta mike sabida tanaso suyi waya da ashfat
shiyasa tace mata zata tafi cike da fara'a Ammii ta rakata har bakin kofa tana
tambayan ta yaushe zata dawo cewa kawai tayi idan tagama abinda zatayi zata dawo
aikuwa Ammii tace seta dawo haka ta wuce part ɗin su Ammii ma ta koma dakinta koda
ta koma part ɗin su a falo taga Mom kaman dama jiranta takeyi tana shiga dakin mom
ta mike tafara tambayan ta ina taje duk da tasan gurin Ammii taje hakan kuwa tace
mata daga gurin Ammii take girgiza kai kawai Ammii tayi tana taune labbanta na kasa
sannan ta wuce tabar Ruma tsaye tana kallon reaction ɗin mommyn nata, basar wa tayi
kawai ta wuce dakin ta wayanta ta daga ta kira Ashfat hira sukayi sosai kana daga
ƙarshe Ruma tace wa Ashfat ta gaishe mata da Mimi wato Mahaifiyar Ashfat ɗin kenan
sukayi sallama ta katse kiran tunani ta fara yi ko takira ya Ammar ko ya Ajeeb
tasan duk inda aka samu ya Ammar to ya Ajeeb ma yana gurin se kawai ta yanke
shawaran kiran ya Ammar ɗin inyaso se su gaisa gaba dayan su cikin sa'a kuwa tana
kiran number ya Ammar ya shiga har murna tayi domin kuwa idan basu suka ƙira ba
yana wahala a same su seda tayi ringing har takusa katse wa sannan taji an ɗaga ai
kuwa murna sosai tayi kafun ma tayi sallama wata murya me daɗi da sanyi tayi
sallama amsawa tayi dan tundaga jin yanayin muryan tasan ya Ammar ne gaishe shi
tayi cike da girma mawa kaman yana ganinta domin kuwa gaba ɗaya nutsuwanta ta haɗa
lokaci ɗaya sunɗan taba hira tana tambayan shi ya aiki amsa mata yayi shima yana
tambyan ta ina Mommy nan tace mai tana ɗakin ta a kaimata ne a'a yace sannan ya
ɗaura da faɗin ya makaranta dafatan de tana karatu alhamdulillah tace mai tana
tambayan shi ina ya Ajeeb mika wa Ajeeb wayan kawai yayi aikuwa yana karba
''Assalamu alaiki 'yar ƙanwata ta kaina'' yayi magana yana ɗan dariya aikuwa kaman
jira take suka shiga hira suna dariya ya Ajeeb akwai shi da abun ban dariya seda ya
tabbatar ya sata farin ciki Sannan ya tambaye ta ya mom take aikuwa tace tana nan
lafiya qlau ta ɗaura da cewa ''ya Ajeeb yaushe zaku dawo ina yaya Deen'' duk tahada
masa tambayoyin lokaci daya sautin dariyan shine ke fita daga cikin wayan itama
dariyan takeyi seda yaɗan tsagaita sannan yace ''zamu dawo soon inshallah ina fatan
kina mana addu'a?'' aikuwa cike da murnar sunkusa dawowa tace ''ina muku my
brothers'' toh kawai yace sake tambayan shi tayi ina yaya Deen yana dariya yace
''kai 'yar kan wata toh baya nan wani abu ne'' ya tambaya cike da neman tsokana
aikuwa nan take yanayin ta ya sauya tace ''babu komai kawai dama zamu gaisa ne''
haka suka cigaba da hiran su kana sukayi sallama ta katse kiran tana mejin kewan
yayun nata don harga Allah tayi missing draman su da ya Ajeeb ɗin nata dailing
number ya Deen tayi da tayi saving da Best Brother ringing yayi har ya katse ba'a
ɗaga ba kara kiran shi tayi nan ma yayi ringing ɗin shi harya katse ba'a ɗaga ba se
ana ukun ne nan ma seda ya kusa katsewa sannan aka ɗaga shiru akayi ba'ayi magana
ba sallama tayi seda tayi kusan minti biyu chan se wani daddaɗan cool Voice me
tafiya da hankalin duk wata Mace voice ɗin very Cool a kuma sanyaye cikin nutsuwa
yace ''wa'alaiki Salam'' gaida shi tayi bata ko jira amsan saba ta cigaba da tam
bayan shi ya aiki seda ya kara yin shiru kafun nan yace alhamdulillah shiru ne ya
biyo baya ta rasa me zata ce masa secan taji zazzaƙar voice nashi yana cewa wani
abu ne a'a kawai tace masa ba komai Mommy ya tambaye ta nan tace tana nan Lafiya da
alama de wannan ya Deen ɗin akwai shi da izza da jan aji,taƙama dan daga yanayin
maganan shima abun a bayyane yake da tarasa mezata ce kawai setace ''yaya yaushe
zaka dawo'' shiru be bata amsa ba hakan yasa ta kalli screen ɗin wayan gani tayi
yana jinta dan be katse kiran ba se kawai tamai sallama tareda katse wayan ta a
ranta tana cewa ya Deen ɗin nan ɗan rainin wayo ne wallahi shi idan beyi niyyan
bada amsa ba shiru yake yi gashi bala'in tsoron shi take yi haka ta fara danna
wayan tama rasa me zata yi se ɗaukan books nata tayi tafara dubawa se a lokacin ne
ma tatuna da zasuyi presentations a school ɗin nasu gashi za'a yaye su su wuce
jss 1 ga Exams da zasuyi yanxu kwata kwata bai wuce 2weeeks ya rage musu ba

'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
GOMBE
( DUKKU)
Wata tsohuwa nagani tana tafiya da ɗan sauri yanayin tafiyan su na tsofi da
kyar a haka taketa sauri tana rike da kwarya wani matsakaicin gida na marasa karfi
ta shiga wani dattijo ne tsaye a bakin kofan da alama ita yake jira tana shiga
gidan kwaryan hannunta ya karɓa suka ƙarisa cikin ɗan madaidaicin gidan nasu na
laka wata mata ce kwance akan tabarma kamar me bacci tana da duhu Amma ba sosai ba
da alama bata da lafiya ne siririya ce sosai ba komai ya ramar da itaba face rashin
lafiya dan kowa daya ganta yasan tana wahala, gurinta suka karasa zama Inna
(tsohuwar) tayi a gefen matar da take kwance kamar mataciya ta tallafo kanta ta
daura a saman kafaɗan ta maganin cikin ƙwarya data shigo dashi ta dauka karamin
ludayi irin na shan nono tasa acikin maganin ta ɗiba bakinta ta kaimata har lokacin
idon matar a rufe haka ta tura mata maganin bakinta kanta ta ɗaga sama yanda zata
samu maganin ya wuce tana fara haɗiye maganin kawai tasa wani irin ƙara me firgita
ɗan adam tana jujjuya kanta
Amma haka Inna bata dena tura mata maganin ba da alama ta saba da ƙaran da
matar takeyi ko sauran mutanen gidan ma ba wanda ya fito har seda ta haɗiye wani na
zuba ta gefen bakinta sannan ta sake kan matar duk da haka bata dena jijjiga kanta
ba tana wani irin gurnani me ban tsoro Amma bakinta a rufe idonta ma haka mikewa
Inna tayi ta dage kwaryan shigewa tayi dashi cikin ɗaki gidan yanada ɗan girma da
fili ɗakuna ne kusan guda huɗu tsaka nin kowani ɗaki akwai ɗan tazara kaɗan,koda ta
shiga ɗakin yanada ɗan faɗi dakine kawai baida falo bare banɗaki ban ɗaki ɗaya ne a
wajen babu banɗaki a cikin ɗaki ajiye kwaryan tayi ta kasan gado me rumfa shika
ɗaine a ɗakin se babban tabar ma dayake shumfuɗe a kasan,fitowa tayi ta zauna a
gefen matar tana kallon ta tausayin ta take ji sosai ba ɗan kadan ba ita kuwa a
yanxu tayi shiru a kwacen nan batasan inda kanta yake ba zama baba yayi a gefen
Inna wanda ta lula duniyar tunanin wasu irin marasa imani ne suka yiwa baiwar Allah
nan haka taba ta yayi se asannan ta dawo daga tunanin da takeyi kallon shi tayi
sannan tafara magana da harshen fula tanci tana gaya mai yanda sukayi da me maganin
data karbowa matar nan,suna zaune a gurin Abuu ta fito daga dakinta da kwanon sha a
hanunta tarufe shi da marfin sa babba ce dan aƙalla zata kai shekara talatin da
wasu abubuwan, zama tayi a gefen tabarman ta gaishe su suka amsa suna mata sannu
sannan ta tambayesu ya mejiki nan ma suka amsa da cewa dasauki kwanon shan hanunta
ta ajiye musu sannan tazauna suna ɗan taba hira sauran matan gidan ma duk haka suka
rinƙa fitowa anan suka zauna suna shan hiran su itakuma matar nan tana kwance da
alama bacci ne ya dauketa..

''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
ABUJA
🔥(AYRA)🔥
Ayra kuwa ta sha barcin ta a ɗakin indo yayin da indon ma a inda take zaune tana
tunanin anan bacci ya ɗauke ta Ayra ne ta fara tashi tana buɗe idon ta se ta ganta
a ɗakin Indo ai ba shiri ta miƙe zumbur kaman an hanka ɗota ta sauka daga kan bed
ɗin taji sauƙin ƙafan nata sosai dan ya rage mata zafi Amma har yanzu akwai zafin
kaɗan kaɗan tashin indo ma tayi dake dama baccin nata beyi nisa ba se ta buɗe ido
tana ganin Ayran ne ta miƙe da sauri Ayra kuwa da har idon ta ya ciko da hawaye dan
a tunanin ta yanzu kam Anty ta tashi Abincin da indon ta shigo dashi ɗazu ta ɗauko
kana ta zaunar da Ayran kusa da ita ta buɗe mata plate ɗin ita kuma ta miƙe dan ta
leƙa taga ko Anty ta tashi tana tafiya tace da Ayran taci abincin kafun ta dawo
kana ta karasa fita itade Ayra duk cikin ta ya ɗuri ruwa dan duk gani take yau kam
zata sha na jaki

Game buƙata karanta book na daga farko har ƙarshe ze iya nema na via WhatsApp
09060413321
COMMENT LIKE AND SHARE

🔥JUST THE BEGINNING 🔥👌

🌹MHIZZ TEEMAH 🌹 CE

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story& writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*________________________________________________________*

Dedicated to my beloved 💔Mom 💔
Wannan shine littafina na farko idan yayi dede da rayuwar wani ko wata to a
rashin ne 🥰
COMMENTS ƊINKU SHINE ZE KARAMIN KWARIN GUIWA KUMA TA HANYAR HAKANNE ZESA NAGA
YANDA KUKA KARBI LITTAFINA

GARGAƊI!!!
Banyarda wani ko wata ya juya min littafi ta kowani siga ba ko a karanta min
shi a YouTube ko a haɗa min document batare da ya nemi izini daga guri naba!!

Free page 8_9

Koda Indo ta fita ta leƙa falo bata ga kowa ba hakan yasa taji sanyi sosai a
ranta dan wallahi yanzu kam ta ɗaura ɗamaran jan Ayra a jiki sosai ta kuma ringa
taimaka mata da wasu abu buwa juyawa tayi ta koma ɗaki nan tasamu Ayran ta fara cin
abinci sauri sauri tace tayi ta gama idan yaso seta koma falo ta zauna kaman yadda
take yi idan ta gama aiki kafun Anty ta fito hakan kuwa aka yi tana gama tura
abincin ta fito falo kaman jiran ta Anty take yi tana fitowa ko zama batayi ba sega
Anty ta fito idon ta da halamun yanzu ta tashi daga baccin koma be ishe taba da
alama yunwa ne yatada ta kuma jiya bata samu bacci da wuri ba ko kallon Ayra da
take gaishe ta batayi ba ta wuce dining ko wanke fuska batayi ba bare baki haka ta
zauna da sauri Ayra ta ƙarasa tana saving ɗin ta tana kuma mamaki yanda yau Anty
bata tashi da wuri ba dan wannan lokacin kusan karfe 11:30 ta agogon da yake manne
jikin bango ta gani tana gama saving nata to koma ta zauna a inda take zama tayi
shiru seda Anty ta gama cin abinci kana ta mike ta koma kan kujera me zaman mutum
biyu seda ta zauna kana ta tuna bata fito da wayan taba gashi batason tashi hakan
yasa ta aika Ayra akan ta ɗauko mata wayan ta a cikin ɗakin ta ba ƙaramin mamaki
Ayra ta shiga ba Amma bata musa ba ta miƙe ta wuce ɗakin ita kuwa Anty kwata kwata
ma ta manta da ta hana Ayra shiga ɗakin idan bata ciki sabida yanayin da take ciki
ga kuma halamun bacci a idon ta Ayra kuwa tana shiga wani mahaukacin birki taci a
bakin kofan gashi dama da tashigo seda ta rufe kofan sabida ƙa idan Anty kenan
jikin tane ya fara rawa ta tsurawa waje ɗaya ido gakuma yanayin ɗakin da yake kaman
anyi dambe a ciki komai a hargitse kan bed kawai take kallo ta kasa koda ɗaga kafan
ta kai kallo na nayi kan bed ɗin dan naga meye ne take kallo haka gashi ta kasa ihu
ta kafe a guri ɗaya innalillahi subhanallah jini ne a mala le akan bed ɗinnan kaman
wanda aka yanka mutum dan wannan jinin yafi ƙarfin na dabba ga wasu irin miyagun
halittu sun zagaye jinin suna lashe wa harda wasu kaman tsutsotsi Amma manya manya
buɗe kofan da tayi yasa duk suka juyo gare ta kaman wasu zakuna dan tun daga
yanayin buɗe kofan sun san ba wacce ta kawo su bane ita kuwa Ayra ta kafe waje ɗaya
ba abin da bakinta yake iya furta wa se a'uzu bi kali matillahi tammat min kulli
shaiɗanin wa hammat wamin kulli ainin lammat, sabida shine kawai addi'an da tafi
iyawa kuma ya zauna a bakinta kaman dan ita aka yi shi sabida yanda ta iya shi
sosai kanta suka yiyo a wani irin yanayi suna wani irin gurnani kaman na mutum Amma
suna isowa kusa da ita wani baya suka ja da mugun sauri ita kuwa datse idon ta tayi
da iya ƙarfin ta dan harga Allah ta saddaƙar yaukam kwanan ta ya ƙare Amma seta ji
shiru duk da haka bata buɗe idon taba, bayan tafiyan Ayra daga falo kuwa Anty ta
kwanta zumbur ta miƙe da wani irin sauri ta nufi ɗakin ta tana buɗe kofan taga Ayra
tsaye ta datse idon ta wani irin tsawa ta daka mata me hargitsa 'ya'yan ciki ai ba
shiri ta buɗe idon ta bataga wa'inna miya gun abubuwan ba kai harma da jinin yanzu
duk babu su kara daka mata tsawa Anty tayi akan ta fita daga ɗakin ai kaman jira
take a ɗari tayi waje ita kuma Anty wani irin

'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
GOMBE
(DUKKU)
Baabaa tana zaune tana yiwa baiwar Allah nan fifita sabida yanda taga jikinta se
haɗa zufa yake yi gashi yayi zafi jauuu har a wannan lokacin kuma idonta a rufe ga
malam nan shima a kusa da baabaa ya zabga uban tagumi yana kallon wannan baiwar
Allah wacce duk wanda ya kalleta seta bashi tausayi sabida ko ba'a faɗawa mutum ba
daya ganta yasan tana shan jiki ba kaɗan ba, baabaa ce ta ɗago tana kallon shi kana
tafara magana tana nuna tsananin damuwarta a kan wannan baiwar Allah tace '' Malam
anya bazamu maida matar nan gurin me magani ba kadubi fa jikin ta sekara ruruta
yakeyi kaman wuta'' takare maganan tana kallon shi ɗan jimm yayi kaɗan kafun ya
girgiza Kai yafara magana kamar haka '' kin manta sanda muka kaita ne tun daga
farko me Malam yace cewa fa yayi asiri aka mata kuma shima bazai iya warware wannan
sihirin ba'' shima yafaɗa yana kallonta itama kallon shi take yi kafun nan tace ''
haba Malam duk da haka gsky ya kamata mu koma tunda ko ba komai idan munje yana ɗan
mata addu'o'i sannan yana bata magani duk da kuma yana kara mana bayani akan rashin
lafiyan nata abunda kawai yace baxe iya ba shine warware sihirin Amma wannan zafin
da jikin ta yake ɗauka da kuma ihun da takeyi wani lokacin ai yana raguwa'' gyaɗa
kai yayi kana yace ''tabbas wannan haka yake yanzu toh tashi muje ki ƙira hafsatu
ta tayaki ɗaukan ta'' yakara she maganan yana mikewa mikewa itama tayi ta kwalawa
hafsatu kira matar ɗanta na biyu itama babbar ce dan harta aurar da 'ya'yanta biyu
fitowa tayi nan take gaya mata ta ɗauko maya finta zasu fita juya wa tayi taje ta
dauko nata anan tasamu baabaa ma harta ɗauko nata kama matar sukayi bawani nauyi ne
da itaba duk a rame take tana wahala ba kaɗan ba haka suka fita da ita malam na
biye dasu wani ɗan madaidaicin gida suka shiga baida nisa da nasu gidan suna shiga
a zauren gidan wani ɗan tsoho ne zaune kan ta barma da carbi a hanun sa yana salati
nan suka zauna suka jingine baiwar Allah nan a jikin bango yanda bayan ta baze gaji
ba ya zamana kaman tana kwance duk yanda sukayi da ita haka take yi bata ko motsi
still kuma idonta a rufe kallon ta tsohon yayi ya girgiza kai kana ya juyo da
kallon sa kan baabaa da Malam da halamum yana bukatan karin bayani nan baabaa ta
fara magana kamar haka ''malam tun dana karbo magani ɗazu a gurinka wanda kace
mubata ludayi ɗaya in anjima ma haka har yakare toh dana bata ne tayi ta wannan
abun da takeyi daga ƙarshe kuma tayi shiru Amma se kuma jikinta yayi zafi sosai
kuma zafin ma karuwa yake yi shiyasa muka kawo ta ka duba ta'' takare maganar ta
tana kallon matar, malam kuwa koda ya gama jin zancen baabaa se ya fara duba matar
jikin ta yayi zafi sosai kaman wuta gata kuma kamar matacciya marabanta da gawa
numfashi ne kawai se yanda akayi da ita, wani hayaki ya dauko ya ceda hassatu ta
shiga cikin gidan ta ɗebo haka kuwa ta mike taje ta ɗebo ta kawo mai kafun yasa
hayaƙin seda yafara umartan su da su danne ta tukunna hayaƙin yasaka nan yafara
tashi a gurin, wani irin jijjiga tafarayi tana fisge jikinta haɗe da wani irin ihuu
me ban tsoro jijiyoyin kanta sun fito raɗo raɗo still idonta a rufe bakinta ma a
rufe duk seda ta watsar da su gaba ɗaya bubbuga kanta tafarayi a bangon da aka
jingina ta dade malam yaga tanaso ta halaka kanta kawai seya sa hassatu ɗage kaskon
hayaƙin ta shige dashi cikin gidan kaf matan gidan sun zagaye zauren gidan suna
ganin ikkon Allah duk da bayau ta fara yin irin haka ba duk inde aka kawo ta aka
mata hayaki seta jiwa kanta rauni sosai, kallon su malam yayi yana jijjiga kai yana
kuma mamakin wani mara imani ne yayi wa baiwar Allah nan haka magana yafara kamar
haka ''wannan baiwar Allah de ba komai bane a jikin ta face sihiri kuma ba ƙaramin
sihiri bane don nide bazan iya warware shiba batasan inda kanta yakeba yanzu haka
inda za'a yankata ba abunda ze faru mugayen aljanu ne ajikinta wanda suka rike
bakinta suka hanata magana da kuma idonta kai harma da gangan jikin ta bazasu taba
barin taba harse tabar duniya sunada matuƙar hatsari ni bazan iya cire su daga
jikin taba idan harde ba wanda ya turo su ne ze warware kayan sa'' ya karasa
maganar yana kallon su da sukayi diɗim kaman ruwa ya cinye su kana ya kara ɗaurawa
da ''shawaran da zan baku kawai shine kuringa yi mata azkar safe da yamma kar ku
bari ta zauna ba alwala kullum tana zama da alwala a jikin ta asamu wanda zena mata
karatu ko kuma a ringa kunna mata karatu a ajiye nesa da ita hakan zeɗan temaka
mata daga azabtar da ita da sukeyi domin kuwa tana azab tuwa sosai'' nufasawa inna
tayi kana tace '' toh shikenan malam in sha Allah zamuyi yadda kace toh Amma abunda
zamusa mata karatun ne babu'' takare nata magana tana jiran amsan da ze bata ɗan
jim yayi kafun yace ''toh wanna kuma sede ko zan mawa ƙanin ki sadiqu magana se
yana zuwa kullum yana mata'' dahaka suka yanke sadiqu zena zuwa yana mata karatu
kana suka dauketa suka koma gida kamar de yanda suka zo da ita mara banta da gawa
numfashi ne kawai....

ANAN NACE SE MUN HAƊU GOBE IDAN ME DUKA YAKAIMU COMMENTS LIKE &SHARE 🥰
🔥 THE BEGINNING 🔥
GA MASU BUƘATAN KARANTA WANNAN BOOK DAGA FARKO HAR KARSHE WHATSAPP ME VIE THIS
NUMBER 09060413321
🌹MHIZZ TEEMAH CE 🌹

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵

Free page 10_11

SU WAYE INNA DA MALAM?WAYE WANNAN MATAR? MEYE HAƊIN TA DA SU?
Inna Asalin sunan ta Maryam Muhammad Bashir hai faffiyar garin Gombe cikin
kwayen dukku haka Malam asalin sunan sa Musa Ibrahim bukar dukkan su an haife su a
local government na Gombe wato dukku mahaifin inna (Maryam) da Mahaifin malam
(Musa) abokanan juna ne tun suna yara tare suka yi makarantar kaman ƴan uwa haka
suka zama komai tare suke yi duk inda aka ga ɗaya to ɗayan ma yana gurin har suka
girma basu rabu ba inda Allah yayiwa me gari rasuwa baban Ibrahim nan aka ɗaura
Ibrahim buƙar me garin dukku gaba ɗayan ta shikuma baban inna malami ne babba yana
da almajirai sosai yana koyar da su shima gada yayi daga gurin Mahaifin sa Allah ya
ji ƙan rai,sunyi rayuwa har sukayi aure ko alokacin auren su tare suka yi akwana a
tashi ba wuya se ga matar me gari da ciki ita ko matar
Malam Muhammad Bashir bata samu ba a wannan lokacin har matar ibrahim bukar ta
haifi ɗa na miji aka yi suna yaro yaci sunan baban matar Musa suna Kiransa da baba
yaro har ya girma Amma shiru de har a wannan lokacin matar Malam ba ciki ba alamun
sa toh dayake malami ne shi se bewani tada hankalin sa ba yayi tawakali da Allah
kullum yana roƙon Allah yabashi masu albarka har Musa yayi shekara Uku kwatsam sega
matar Malam da ciki sunyi matuƙar farin ciki sosai kuma sun gode wa Allah haka suka
reni cikin nan har lokacin haihuwan ta yayi ta haifo santale liyar yarinya ranan
suna taci Maryam mesunan mahaifiyar Malam a lokacin kuwa Musa yanada shekara huɗu
sunyi farin cikin samun yarinya mace akwana a tashi yarinya tana girma kullum Musa
yana cikin gidan malam sabida yanda Allah ya ɗaura masa son yarinyar itama har ta
saba dashi daga ya shigo gidan zata fara washe baki sabida tasan ze ɗauke ta yayi
ta mata wasa tun daga wannan lokacin da matar me gari ta haifi Musa bata kara
haihuwa ba sunyi matuƙar damuwa shide me gari yanason yara mata Amma Allah be bashi
ba
malam ibrahim nema me ɗan kwantar musu da hankali ta hanyar tuna tar dasu akwai
Allah da kuma yi musu nasiha ana haka har Maryam tayi Shekara 3 yayinda shikuma
Musa yakeda shekara bakwai yana zuwa gurin Malam suna karatu sosai yauda gobe ya
wuce wasa inda Maryam ta girma tazama budurwa shima musa ya girma sosai da lokacin
yanada shekara 22 ita kuma tana da shekara 15 a kwaye duk yarinyar da takai koda
kuwa 13 ne takai aure inde har ta girma toh haka yake a gurinta domin soyewan su
suke yi ita da Musa ba kama hannun yaro dama already sun saba daga sabo abun yakoma
soyayya tun iyayen basu gane ba har suka gane haka aka musu aure sunyi matuƙar
farin ciki anan gidan baba malam mahaifin Maryam anan suka zauna akwai ɗakuna da ba
kowa nan aka gyara musu kafun me gari ya gama gyara musu gida dan shine ya ɗauki
nauyin sama musu gida
Auren su befi da wata ba sega mahaifiyar Maryam da ciki itako matar me gari har
lokacin shiru daga kan musa basu ƙara haihuwa ba tun suna damuwa har sukayi
tawakali da Allah suka dena damuwa suna

Please Login or Register in order to submit comment