Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 14 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

DUKKU

Bari mu koma baya domin kuji abubuwan da suka faru,

Jikin matar nan kullum ƙara tsanani yake yi ga baba Malam jiki duk ya tsanan ta
shima shide yasa abunda yake damu shi Amma ba bakin yayi magana ga kullum idan
megari yazo seya masa karatu har takai idan megari yazo ze fara masa karatu se ya
kasa dan ji yake kaman ana shaƙe masa maƙoƙoro tun hakan baya damun sa har yakai
yanzu ya fara tsorata da lamarin dan fa shima ciwo yake yi a tsaye ya rame sosai
wannan ahalin ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba ga baba sadiq baya nan har
yanzu be dawo ba inna bata bar yiwa matar magani ba kullum seta bata Amma duk a
banza anje har gonan da baba sadiq yake zuwa Amma ba'a ganshi ba jin wanan labarin
kuma ba ƙaramin ɗaga hankalin ahalin yayi ba gade su musa basu gaji uban nasu ba
balle su iya gane abunda yake damun shi su kansu ba ƙaramin tashin hankali suka
shiga ba dama baba sadiq ɗin ne da beyi Aure ba yana zaune da baban nashi toh shine
ya koya masa kuma kunsan gado ba karambani ba se ya zama na kaman baba sadiq ɗin
yafi baba Malam sani sosai a wannan harkan duk ƴaƴan sa sun duƙufa ne wajen kula
dashi kullum se sunje kauyen da baba sadiq yake Amma basa ganin sa,

A yau ne suka tashi da wani kalan tashin hankalin da basuyi tsammani ba dan gaba
ɗayan su majinyatan yau jikin yayi tsanani abun mamaki kuma yau jikin matan nan se
rawa yake yi abunda be taɓa ba, gaba ɗayan su zagaye suke da baba Malam da jikin ra
yake ta ƙarƙarwa gashi yayi wani bala'in zafi dukkan su da ƴaƴan sa harda jikokin
sa suna zagaye dashi duk an rasa wanda ze iya taɓa shi sabida yanda jikin nasa yayi
zafi sosai duk ya rame sosai kuma ya haɗu da jikin tsufa inna ne ta fara magana
cikin tashin hankali take ƙiran sunan baba malam ɗin Amma ina ko idon sa baya iya
buɗe wa nan take jikin sa yayi sanyi kaman ba yanzu jikin yayi zafi sosai ba take
ya fara kafewa take kuma bakin sa ya buɗu kalamar shahada kawai ya iya furta wa
daga nan kuma tsit kake ji ya dena motsi nan take kuma ya sandare kaman wanda ya
jima da mutuwa take kuma suka fara kuka wasu kuma suna faɗin innalillahi wa'innan
ilaihir rajun inna kuwa miƙewa tayi da sauri ta fita a gidan dan bata maso ta ƙara
kallon mahaifin nata ba rai aikuwa tana fita tayi wani mummunan ji ihu ta kurma nan
su Ibrahim suka fito suka nufi gidan nasu dan daga nan suke jin ihun suna shiga
koridon ita kuma tana fito wa da gudu ba kowa bane face wannan matar tunda baba
Malam ya ɗauke ɗipp ta kurma wani ihu se kuma ta miƙe ta fito da gudu toh anan ne
suka gamu da ita kuma se aka rasa wanda ze bita duk se suka tsaya a yanda suke dan
ba ƙaramin shock suka shiga ba ganin matar da suka bari kwance ko motsi bata yine
ta fito kuma harda gudun ta matar da ta kwashe shekaru bata iya motsawa duk se suka
tsaya sun afka duniyar tunani seda inna ta musu magana wanda dawowan ta cikin
hankalin ta kenan sannan suka fita da gudu suk fara neman matar Amma sun zaga ko
ina basu ganta ba kaman wanda ta bace batt haka suka nemeta basu ganta ba suna
cikin haka kuma matar megari tazo hankalin ta a tashe ko magana ta kasa kawai se
jansu tayi suka bita aikuwa suna zuwa cikin gidan megari suka tarar dashi kwance
baya motsi ga sauran matan sa zagaye dashi da sauri musa ya ƙarasa kusa dashi Amma
se gani yayi baya motsi ya rasa ma me zeyi a halin yanzu ga baba Malam ya rasu ga
wannan baiwar Allah ta fita da gudu kuma basu ganta ba ga kuma megari ma ya rasu
shikam yau yana cikin tashin hankali mahaifin sa ya rasu abokin mahaifin nasa kuma
amininsa kuma surkin sa shima ya rasu ga matar da take gurin su ita ma ta gudu
wayyo shi ina zesaka kansa ne ga baba sadiq an neme sa ba'a gansa ba (innalillahi
wa'innan ilaihir rajun nima de wannan tashin hankalin ya ishe bi yau ni ina zan
saka kaina ne gwara de na koma wajen SHEAD maybe kafun mu dawo zamu tarar ya samo
😭
inda matar take ko kuma ya samu solution ɗin yanda zeyi )

LONDON

Tsaye suke a compound na gidan shirye cikin kayan aikin su duk sunyi shirin fitan
SHEAD ma sanye yake da nashi kayan aikin yana ƙara gaya musu yanda zasu yi yanzu
gurin ƙarfe 3:30 na dare dama haka suka tsara zasu fitan dan lokacin ne mafi
dacewan farmaki gari yayi shiru ba wanda zeyi tsammanin wani abun suna gama magana
kowa ya ɗale mota inda shima ya shige nasa motan shida su BYRON trolley su kuma
yana bayan motan dayake fitan na sirri ne se basu tada jiniya ba shiru suka fita
gudu kawai suke zubawa a titin har suka isa wani ɓoyayyen guri can ta bayan gari
wata hanya ce da bakowa ne ya santa ba tana iya fitar da mutum har yabar ƙasar daga
nesa da gurin suka yi parking dama basu kunna wutan motan ba haka duk suka dira
daga motan suka fara kutsawa wajen a hankali SHEAD ne a gaba kowannen su hanun sa
riƙe da manyan bindigu ga kuma ƙananan a gefe da gefen wandon su ga manyan bullet
da suka rataya a jikin su chan ta baya suka fara hango haske haka suka ta zuwa a
hankali har suka iso gurin nan suka tsaya inda ba wanda ze gansu mutane ne sunkai
su ashirin a filin gurin ga wasu manya manyan kwalaye da suka zuba a gurin kowannen
su hanun sa riƙe da bindiga wasu kuma suna shiga ɗan tamfol ɗin suna fito da sauran
kwalayen sun jima suna tsaye basu da niyyan fita kuma duk umarni ne na SHEAD shi
kaɗai yasan abunda yake shirya wa kallon su kawai yake yi seda suka gama fito da
duka kwalayen sannan suka ɗanyi wani magana kana suka bubbuɗe su kwalaye ne da suke
cike da kayan maye kala kala se kuma wanda yake ɗauke da Guns manya manya da ƙanana
suna gama ganin duka sanna suka rufe kwalayen suka fara shigar dasu babban motan
dake gurin ganin hakan ne yasa SHEAD bawa sojojin sa umarni su fita su zagaye gurin
sannan suyi shirin harbi haka kuwa suka yi seda yaga sun gama shirya kwalayen cikin
babban motan sannan ya fito fili kana yabawa sauran umarni da zasu iya fara harbi
ta hanyar daga hannun sa sama nan fa suka fara musanyar wuta hakan kuma yazo mawa
miyagun mutanen nan a baza tane dan basu taɓa tunanin akwai wanda yasan shirin suba
shiyasa duk sun sakankance shikuma SHEAD dama yasan basu shirya wa hakan ba shiyasa
seda ya bari suka gama shigar da kwalayen cikin motan sannan ya bada umarnin harbi
haka shima ya ringa harbi ba ƙaƙautawa suma suka fara nasu take guri ya hargitse
aka fara musanyar wuta harbi kawai kake ji guri fa ya hargitse sosai inda har wa
lokacin ba'a harbi ko mutum ɗaya daga cikin sojojin ba danfa kwararune wajen iya
harbi suɗin ba ƙananan kwari bane daɗin daɗawa kuma shine bazatan da suka musu basu
shirya ba shi yasa sun samu nasara kashe su kusan daka nan SHEAD ya ɗauki mutane
uku cikin sojojin sa ya basu umarnin shiga cikin babban motan sanna ya basu umarni
su tafi dashi suje su ajiye motan a gurin aikin nasu za'ayi bincike akan shi haka
kuwa akayi suka wuce da motan, seda suka zagay ko ina ganin babu wanda ya rage yasa
SHEAD ɗin juya wa dan subar gurin haka sauran sojojin suka wuce shine na ƙarshe
yana rufa musu baya ba zato ba tsammani kawai yaji an kwala masa ƙira ta hanyar
cewa ''sirrrrrrrrrrrrr'' juyawan da zeyi kawai se ganin bullet yayi daga nesa ta
kusa iso shi kafin ya samu wani dama na kauce mata har ta iso (oh ni ko ina ba
sauƙi kai innalillahi bari mu leƙa AYRAH maybe kafun mu dawo anyi wani abun 🥱)

ABUJA

Tunda Anty ta bata wannan abun tasha take jin kanta na sara mata wani kala take ji
bata jin daɗin jikin ta dan ko tsayuwa tayi setaji kaman zata faɗi dan wani kalan
hajijiya take ji shiyasa tana shiga ɗakin su ta ɗale bed nata ta kwanta nan da nan
bacci ya ɗauke ta Anty kuwa AYRAH na fita ta ɗauki wayan ta ta ƙira wani banji
abunda suka tattauna ba se ji kawai da nayi tace nan da 1hr sannan ta kashe wayan
ta, Indo baiwar Allah yau tunda ta tashi bata jin daɗi haka nan take jin kaman wani
abu yana shirin faruwa da ita ko kuwa wani abu ya faru da ita dan haka nan jikin ta
duk ba ƙarfi tunda ta tashi take kwance takasa miƙewa zuciyan ta yana mata zafi
sosai kuma ta rasa dalili duk abunda tayi yau ba ƙarfi a jikin ta haka nan take yi,
bayan 1hr, zaune Anty take kan kujera ta kwala wa Indo ƙira da sauri Indo ta fito
ta tsuguna ƙasa ko kallon Arziƙi bata samu ba Anty tace ''kije ki ƙira min yarinyar
can'' haka take faɗa bata ƙiran sunan AYRAH miƙewa Indo tayi tace ''toh'' sannan ta
fita a ɗakin hanun ta rike da wata ƴar ƙaramar paper da number ta a jiki tana so ta
bawa AYRAH sabida ko basa tare zata iya ƙiranta haka nan yau ta tashi da son bawa
AYRAH number nata dan tana ji a jikin ta kaman akwai abunda ze faru dasu da wannan
tunanin ta shiga part ɗin su har cikin ɗakin su ta shiga kwance taga AYRAH tana ta
sharɓan bacci har bakin bed nata taje ta fara tashin ta da yake bata da nauyin
bacci se kuwa ta farka miƙewa tayi zaune haka nan kanta kuma be dena ciwon ba
''AYRAH kizo Anty tana ƙiran ki'' shine abunda Indo tace miƙewa AYRAH tayi da sauri
bata ko amsa ba tayi hanyar barin ɗakin da sauri Indo ta rufa mata baya seda suka
zo dapp zasu bar ɗakin Indo ta tsayar da AYRAH ta tsuguna sannan tace ''AYRAH ga
number na ki riƙe a gurin ki idan buƙatan ƙiran nawa ya tashi'' cikin sanyi ta
ƙarasa maganan idon ta na cikowa da kwallan da ta rasa na meye ne karɓa AYRAH tayi
itama haka nan se taji wani iri ta rasa meke mata daɗi ''Anty Indo toh a ina zan
ɓoye'' ta faɗa a hankali karɓan paper Indo tayi da sauri dan ƙar Anty tace sun jima
hulan da yake kan AYRAH ta cire ra saka mata paper a ciki tana kallon gashin AYRAH
dan tunda suke da ita bata taɓa ganin gashin taba ganin yanda take da gashi sosai
gashi ya tsufa sosai har ba'a gane kitso ne akan nata ko meye ne da sauri ta kawar
da tunanin da take yi ta mayar mata da hulan sannan ta maida mata da hijab ɗin da
yake jikin nata suka fita tana ce mata ''idan na samu Lokaci zan gyara miki gashin
kanki sannan karki yarda wani yaga paper nan kinga na samiki shi cikin hulan ki''
da ''tohm'' kawai ta amsa a haka har suka shiga ɗakin Anty aikuwa sun gudu basu
tsira ba dan seda Anty tayi masifan ta son ranta sannan ta miƙe ta shige ɗakin ta
ita ma Indo wuce wa tayi nata ɗakin can ba jimawa sega Anty ta fito hanun ta riƙe
da kuɗi ta miƙawa AYRAH sannan tace ''kije waje zaki ga wasu a mota ki basu kuɗin''
a fisge tayi maganan kaman ba ita tayi ba ko kallon inda AYRAH take bata
yiba,karɓan kuɗin AYRAH tayi tace ''toh''sannan ta fita haka nan da zuciya ɗaya ta
fita inda tunda take ba'a taɓa aikan ta waje ko wai ta fita haka kawai bata taɓa ba
se idan Bus ya dawo da ita daga makaranta nan ma bata taɓa tsaya wa ta ƙare wa
anguwan nasu kallo ba, tana fita taga wata mota baƙa tintek ce ba'a ganin wanda
yake a gaban gidan nasu tana zuwa ta tsaya a gurin ta rasa ma ya zata yi ta musu
magana gashi kuma hajijiya take ji daure kawai take yi idon ta har ja yayi kana
ganin ta kasan ba lafiya tana tsaye se lumshe wa idon ta yake yi saboda hajijiya da
take ji, buɗe marfin motan gidan baya akayi wani saurayi baƙi ya fito kuɗin kawai
ta mika masa bata ce komai ba maimakon ya amshi kuɗin se ya jawo ta ta faɗa cikin
motan ya rufe da sauri na gaban mota ya ja ta da mugun gudu,anguwa dama shiru ne ba
kowa a layin haka suka ɗauki titi suka fara gudu ita kuwa suna jefa ta cikin motan
ɗayan na gefe ya shaƙa mata cocain take ta suma dama hajijiya take ji gudu kawai
suke yi a titi lokacin wurin ƙarfe 9:00 na dare suna cikin gudu kuwa sun sha wata
kwana sega wata danƙareriyar mota ita ma zata shawo kwana kawai suka gwaru wancen
motan ya buge wanda AYRAH take ciki ai take motan da AYRAH take ciki yayi sama
sannan ta faɗo ƙasa yata gangarawa sannan ya kife.

TOH FA MY PEOPLE FREE PAGE YA ƘARE KUYI MAZA KU HANZARTA BIYA KAR AYI BAKU 😌


SE MUN HAƊU A BOOK TWO 2 MY PEOPLE

GAME BUKATAN BIYA ZE IYA TUNTUƁA NA TA WANNA NUMBER09060413321

Semun haɗu a BOOK TWO 2
️️️️️

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment