Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 13 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️

3️⃣
4️⃣ Page 3️⃣4️⃣
Free

Ɓangaren SHEAD kuwa kwance yake kan bed nasa waya maƙale a kunnen sa ya tattara
gaba ɗaya hankalin sa kan wayan da alama magana me mahimmanci suke yi shida me
ƙiran nashi rabin jikin sa a lulluɓe yake da jifgegen bargo dan yanayin garin yau
akwai sanyi sosai, sede kuma duk wannan sanyin masuburbuɗan sanyi na ɗakin a kunne
suke dumm light ne blue a ɗakin hannun shi a waje zuwa faffaɗar ƙirjin sa face nasa
kuwa gashin sa ya rufe gaba ɗaya face ɗin baka iya ganin komai, shiru yayi yana
sauraren abunda shugaban nasu yake sanar dashi nide banji abunda ya faɗa ba se daga
ƙarshe SHEAD yace ''okay sir'' tare fa katse ƙiran juya wa yayi ya cigaba da
kwanciyar sa dan dama yana bacci ne yaji ringing ɗin wayar tasa sede aka ƙira kusan
sau uku sannan ya ɗauka anan ne suka yi maganar sirri wanda suka saba yi akai akai
sabida tsantsar yadda da Solomon yayi dashi ne yasa dashi kaɗai suke wannan maganar
yanzu de sunyi magana ne akan aikin da shi LG ɗin zeyi dama already ya san cewa
gobe ne zasu je so an gama ajiye lokaci har LG ya tara sojojin ruƙunin sa yanzu
gobe kawai suke jira yayi, miƙewa yayi daga kwance a hankali cikin nutsuwa ya sanye
yake da pjmas launin blue ya maida fashin kansa bayan sa Sannan ya wuce bathroom
wanka yayi ya fito ya shiga closet ya shirya cikin dogon wando jeans da Vneck T-
shirt ya gyara gashin kansa ya fesa turarukan sa masu bala'in kamshi da tafiya da
hankali ya saka wata takalmi sau ciki Amma wannan duk jikin sa gashi gashi ne me
ɗan karan laushi kan sa kafan ka ze lotse ciki sabida tsabar laushin takalmin
sannan ya nufi hanyar fita waje a kwana biyun nan jinshi yake wani kala sabida
tafiyan da su Ajeeb suka yi kwata kwata baiji daɗin hakan ba Amma baza ka taɓa gane
wa ba sabida dakiyar sa da juriya duk da cewa kullum se sunyi waya Amma yayi
missing nasu over sabida yanda suka jima tare duk da shima ya kusa komawa Amma haka
ji yayi ma gidan ya masa girma sosai dan koba komai suna ɗebe masa kewa kuma
atleast yana jin hayaniyan mutane kuma koda baison yin magana zasu zo su saka shi a
gaba da hira kala kala Musamman ma Ajeeb,yana fita soldiers nasa suka fara sara
masa be kula kowa ba da sauri Mash da Byron suka rufa masa baya ganin ya nufi ɗakin
sirri makullin ɗakin Byron ya ciro ya yayi saurin buɗe masa a ƴan kwanakin nan
kullum se sun shiga ɗakin sabida ƙara faɗaɗa bincike akan aikin nasu suna shiga ya
zauna a kujeran su kuma suka tsaya a bayan sa aikuwa yana duba ɗan ƙaramin computer
dake ta gefen sa yaga alamun ƙira na shiga wata layin daya ke sun datsi layin LG ba
komai yasa yayi hakan ba kuma se dan zargin shi da yake yi ga kuma yaga an kwashe
makaman da suke dashi kusan rabi hakan yasa shi tunanin ba kowa ne zeyi hakan ba se
LG,saurin ɗaukan system ɗin yayi ya shiga kan layin ya fara duba da waye ne ake yin
ƙiran sannan ya saka head phone dan ya saurari abinda suke faɗa nan yaga number da
ake wayan da ita bana ƙasar bace daga Nigeria number take yasha ruwan mamakin ganin
hakan Amma da yake ba wannan ne a gaban shiba seya kawar da tunanin kawai yayi
playing dan jin abunda suke faɗa, a ɓangaren LG kuwa ya ƙira Fa'iz ne yana ƙara
jaddada masa yanda kayan ze shigo ƙasan gobe dan yanda komai ze gudana sede kash
sunyi rashin sanin cewa duk abubuwan nan da suke tattaunawa akai MG SHEAD na jinsu
a nan ne kuma ya ƙara shiga mamakin ya akayi LG ya haɗa baki da ƴan kasar sa ashe
duk wannan abun da yake yi ɗin da sa hannu gurɓatattun kasar sa Lallai akwai aiki a
gaban sa ba kaɗan ba dole ma ya koma ƙasar sa domin su haɗa hannu da shugaban su
subawa ƙasar su kariya da wannan tunanin ya tashi yabar ɗakin su MASH suka rufa
masa baya baida wasu amintattu da suka wuce BYRON DA MASH duk da suma bawai ya
yarda dasu 100% bane a'a sede kawai sune yafi sake wa har yana jin idan zebar ƙasan
ze nemi alfarma da a bar masa su ya tafi dasu dan gani yake kaman sun zama ɗaya ya
ɗauke su kaman ƙannen sa kuma yana ji baza su taɓa cutar dashi ba yana koma wa
ɗakin sa ya wuce ya fara haɗa kayan sa dan a yau yake so yayi komai ya gama shirin
sa tunda yanzu kam ya gama sanin shirin su gani yake ko su BYRON ya saka da sauran
yaran shi zasu iya dasu tunda shi LG ba gurin ze jeba kuma a yanzu baida hujja da
zai faɗa wa shugaban su ya yarda dashi akan LG yana da laifuka dade sauran su shi
yasa gwara yayi komai a sannu har ya samu cikkaken hujja daze bayar a kan LG kuma
shi yanzu gaba ɗaya hankalin sa ya karkata ga ƙasar sa dan a cewan sa baze tsaya
yana gyara wata ƙasar ba bayan nasa ƙasar tana da buƙatan irin shi ba so gwara ya
koma tunda already yana da matsayi a can ɗin ma se yasan yanda ze fara tunkarar
abubuwa sannan shima ya kafa ƙungiyar shi masu aldalci wanda zasu temaka masa wajen
gyara ƙasar sa dan shi kansa ya sani baze iya shi kaɗai ba dole seda temakon mutane
bawai kuma ya gaza bane a'a sede ko wani aiki yana buƙatan ƙwaƙwalwa nitsuwa ba wai
karfi shine zesa suyi nasara ba basira ya haɗu da kaifin tunani da karfi su zasu yi
aiki so shi yanzu hankalin sa ya karkata ne izuwa ga ƙasar sa, bawani kaya ya
shirya ba yade haɗa duk wasu abubuwan sa masu mahimmanci daze buƙata komai ya haɗa
sannan ya shiga wanka ya fito se tashin kamshin kayan wankan sa yake yi nan ya
shige closet ya shirya tsaf cikin kayan sa sannan ya ɗaura baƙin jacket akai ya
feshe jikin sa da turarukan sa haba wa nan take ko ina ya ɗau daddaɗan kamshin
turaren sa ya fito yayi kyau sosai masha Allah kawai za'a ce ku kiyasce kyawun da
yayi dan ni kam alkalami na ya kasa rubuta muku adadin kyan da yayi wayan sa da ta
fara neman agaji ya ɗauka ganin sunan da yake ƙiran nasa ya sa shi katse ƙiran BIG
QUEEN haka ya saver sunan ƙira yayi bayan ya katse suka fara magana sosai suka
gaisa duk da shi maganan nasa a hankali yake yi cikin wani kalan sanyi sunyi hira
kaɗan a nan ne kuma ya faɗa mata ze dawo gobe Amma karta gaya wa kowa dan baya son
kowa ya sani ita ɗin ma be kamata ya dawo bata sani bane shiyasa ya faɗa mata tayi
matuƙar murna ba kaɗan ba sannan daga ƙarshe suka yi sallama ya fita zuwa harabar
gidan dan fita zeyi cikin sauri suka fito da mota ya shiga suka ɗau hanya guard
nasa suna biye dasu basu tsaya ko ina ba se bakin wani tamfatsetsen get me girman
gaske suka yi hon already dama sun san da zuwan su sabida me gidan ya sanar dasu
take suka buɗe musu get suka kutsa kan motan gidan ya kawatu ba ƙarya dama MG SHEAD
ya sanar da shugaban nasu yana zuwa zasu yi magana hakan yasa aka barsu suka shiga
seda suka daidaita packing MASH ya fito ya buɗe masa murfin kusa dashi ya zuru
kafan sa dake sanye cikin black takalmi sau ciki sannan ya fito gaba ɗaya suka
wuce cikin sauran suna rufa musu baya kafin ma ya ƙarasa har GAR Solomon ya fito ya
masa iso cikin gidan su kuma suka tsaya daga waje zama suka yi kan kujera suka
gaisa sannan ya fara magana lokacin har an cika masa gaba da kayan ciye ciye Amma
be taɓa komai ba PRETTY kuma jin muradin zuciyan ta yazo haka taje ta tsantsara
kwaliyya tayi shiga irin nasu skirt guntuwa iya cinya se riga ƴar karama da ta
kamata sosai bata rufe cibiyar ta bama,bayan ta gama shiryawa ne ta kalli kan ta a
mirror tana sakin murmushi daukar wayar ta tai ta fice a part din ta nufi
downstairs inda MG SHEAD da GAR Solomon suke zaune har sun fara tattaunawa,tun daga
nesa ta ke binsa da mayataccen kallo cike da kaunar sa har zuwa yanzu wannan
murmushin be gushe akan fuskar ta ba.

Saukowa tayi ta shigo falon tana fadin " Hey daddy ".

Dakatawa da maganar da suke yi GAR Solomon yayi ya kalli yar ta sa ya ce " hi my
beautiful pretty come and site down ".cike da sangarta ta nufi kusa da daddyn nata
ta zauna tana kallon fuskar MG SHEAD da ko kallon inda take be yi ba balle ta sa
ran ze kulata,se ma wayarsa da ya ɗauka ya soma latsawa.

Idonta akan sa hallau,ta daura kafarta akan daya cike da yanga ta furta " Hi
SHEAD".
Kamar wanda baya wajen ko motsawa beyi ba, balle ya amsa. Tura baki tayi na rashin
jin dadin kulata da beyi ba ta kalli GAR Solomon da duk abinda ya faru akan idonsa.
Amma se ya nuna kamar be ga komai ba.

Miƙewa tsaye ya yi alamar ze tafi ya sara masa yana faɗin " thank you sir ".

Murmushi GAR Solomon yayi ya gyada masa kai " wish You all the best"ya faɗa yana
miƙewa shima domin ya rakasa,ganin sun mike ne yasa itama ta miƙe ta soma bin su a
baya,dan juyowa kadan GAR Solomon yayi ya dubeta cikin harshen su ta turanci ya ce
ta jira sa yana zuwa.
Ko da suka fito suka tarar da MASH da Byron suna tsaye suna ganin fitowar su suka
sara musu.

Se da suka je har bakin motar kafin ya koma ciki,su kuma suka tafi.

Bayan sun dawo gida ne ya wuce part dinsa yana me rage kayan jikinsa ya
yi freshing up ya saka three qurter na sojoji da Black armless ya fito compound din
gidan, sojojin suna ganin shi suka nufo inda yake dama already ya riga da ya haɗa
rukunin mutanen da zasu fita aikin dasu hakan yasa suna ganin shi duk suka nufo
inda yake jeruwa suka yi tare da sara masa sunyi magan ganu akan aikin da zasu fita
dan ya gano cewa da dare ne zasu ɗauki hanyar fitar da kayan kafin gari ya gama
waye wa sun bar ƙasar shiyasa yake so suma su gama shirin su before Lokacin yanda
shima ze shiga ƙasar tasa da safe.

Bayan sun bar wajen se ya tsayar da MASH da BYRON a nan ne ya sanar dasu tare zasu
tafi 9j su zama cikin shiri basu musa masa ba suka sara masa tare da barin wajen
dan su fara shiri shima ya koma bed room nasa.

Ɓangaren GAR Solomon kuwa bayan ya koma cikin falon zama yayi kusa da ƴar tasa ita
kuwa tacika ta batse dan ranta ya ɓaci sosai na farko de tayiwa MG SHEAD magana be
kula taba haka kuma ta tashi zata bisu waje DADDYN ta ya dakatar da ita hakan yasa
ranta ya ɓaci sosai koda ya mata magana se turo masa baki da tayi ta fara magana
cikin tsantsan ɓacin rai da ya Bayyana akan fuskan ta cikin harshen turanci tace
''DAD wai meye sa MG yake min haka ne yasan fa ina son sa kawai de ban taɓa gaya
masa bane Amma ai shi kansa yasan da hakan kaima Dad ai kasani Wallahi sonshi nake
yi kuma sena Aure shi kasa baki mana dad kaine fa shugaban sa'' kallon ta kawai GAR
Solomon yake yi ganin yanda take ta wani ɓata fuska tana magana kaman ba da
mahaifinta take yi ba duk da shi ba wannan yake tunani ba sabida su a gurin su
normal ne yana tunanin ta yadda wannan al'amari ze kasance shide yasan inde ba
ra'ayi MG yayi ba toh bame iya mai magana akan life nasa bugu da ƙari kuma ba yadda
hakan ze kasance tunda shi MG ƙasar sa ze koma kuma yasan halin MG ciki da waje
kuma suda suke ba musulmai ba taya ma zata auri wani ba ƙabilan suba kuma harma
tabar ƙasar ta ta koma Nigeria yasan itama baza ta yarda ta koma wata ƙasa daban ba
shima kuma baze iya yin nesa da ita ba maganan tane ya dawo dashi daga duniyar
tunanin da ya afka sanadin ƙiran sunan shi da tayi.cikin kwantar da murya ya soma
mata Magana.

" Pretty ina so ki saurareni ki ji abinda nake son fada miki, SHEAD musulmi ne ke
kuma Christian ce bana tunanin ze yarda da buƙatan ki koda kuwa kine na same shi da
wannan zance...'' kafin ma ya ƙarasa maganan tayi surin dakatar dashi ta hanyar
ƙiran sunan shi cikin ɗaga murya ranta ya ɓaci sosai miƙe wa tayi ta wuce sama da
gudu tabar shi zaune yana tunanin yanda zeyi da ita dan yasan shikam baida yanda
zeyi mata wajen shawo kan SHEAD dan yasan abune mai wuya.


COMMENT
LIKE
SHARE
FISABILILLAHI

Free Page ya kusa ƙarewa fa my people gsky ya kamata Ku hanzarta biya yanzu muka
fara shiga cikin book ɗin fa 😌
🌹Mhizz Teemah 🌹



💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰
Littafi ne me cike da faɗakarwa, ilmantarwa, harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


3️⃣
5️⃣ Free Page 3️⃣5️⃣
Last

ABUJA

AYRAH fa yanzu har wani baƙi tayi sabida wahala Indo ne kaɗai me temaka mata tana
matuƙar shan wahala sosai gashi hutu suke yi bata fita kullum aiki yanzu haka ma
tana ɗakin Anty bayan ta gama mata aikin ta zata fita se Anty ta ƙira ta wani kofi
ta bata sannan tace maza ta shanye abun da ke cikin cup ɗin karɓa tayi tana kallon
abun haka ba yanda ta iya dan fa Anty ta kasa ta tsare so bata da wani zabin da ya
wuce ta shanye ɗin seda tayi bismillah a cikin ranta kana ta kafa cup ɗin a bakin
ta seda ta shaye tas sannan ta sauke cup ɗin daga bakin ta tare da yaƙinin koma
meye ne Allah na tare da ita baze taɓa cutar da ita ba duk abunda ya faru da ita da
sanin sa dashi kaɗai ta dogara a gare shi take bauta kuma a gare shi take neman
temako so duk abunda ya fari da ita tayi tawakali da Allah kuma tana ji a ranta ba
wanda ze mata abunda Allah be mata ba haka ta ajiye cup ɗin ta fita Indo dake laɓe
tana kallon su jikin ta ba ƙaramin sanyi yayi ba tanaji a ranta koma meye ne wannan
ba abu mai kyau bane Anty ta bata haka de ita ma ta juya ta koma ɗakin ta sabida ba
abinda zata iya yi bayan fitan AYRAH part nasu ta wuce dan ji tayi jikin ta baya
mata daɗi har tashin zuciya take ji sabida abinda ta sha gashi wani yauƙi taji yana
dashi kawai ta daure ta sha ne duk da haka bata dena ƙiran sunan Allah a cikin
ranta ba su MARWA da ESHALL duniya sabo ta musu barin ma Marwa kullum tare suke
fita da Mama ita kuwa ESHALL inta kwanta bacci seta wuni ma ba abunda yake damun ta
kuma wani abun da ze baku mamaki shine kwata kwata bata damu da MARWA wai a
matsayin ta kuma na ƙanwar ta uwa ɗaya uba ɗaya ba haka ma basu wani shaƙu sosai da
Mama ba irin shaƙuwan nan na uwa da ƴaƴan ta toh matar da kullum tana hanyar waje
ina ma taga time na yaran ta ita kanta bata damu da su sosai ba har gwara ma MARWA
suna zama har suyi hira kuma suna fita tare Amma ESHALL kam ni kaina bansan meye
hakan yake nufi ba Amma se gaba zamuji koma meye ne kuma wani abu guda har yanzu
MARWA bata bar fita da abokan Dad ba suna fita susha shagalin su sannan su dawo
kuma Mama ta sani bata hana taba sema goye mata baya da tallafi da ta bata ta
hanyar idan sun fita se suzo su ɗauke ta bayan sun gama duk abun da zasu yi kuma se
su maida ta gurin Mama kana su dawo gida akwai wani gidan da suke haɗuwa sannan
insun tashi dawo da ita ma nan suke kaita idan ta riga Mama dawowa toh zata jira ta
idan kuma Mama ta riga ta dawowa se ta jira ta lokaci be bani daman sanar daku inda
suke haɗuwa ba Amma idan lokaci yayi zaku ji gidan da suke zuwa harma da abubuwa da
yawa da baku sani ba komai ze bayyana muku idan lokaci yayi sannan idan kuka cigaba
da haƙuri dani fannin update duk zaku ji komai.

Abdull ya fara fita kasuwa shida Dad a halin yanzu kusan komai shine yake jagoranci
akai sabida Dad ba kullum yake fita ba gashi ko yaje hankalin sa yana wani gurin a
ƴan kwana kin nan ma abun yafi yin worst dan kwata kwata an dena gane kanshi shi
kansa yanzu ba gane kansa yake yi ba haka kawai yake ji kaman akwai abunda ya rasa
me mahimmanci a rayuwar sa Sannan kuma yana ji ajikin sa akwai wasu abubuwa da suke
shirin faruwa dashi gashi kullum fama yake da ciwon kai abunde ba sauƙi.
Kwance Mommy take kan kujera me zaman mutum uku tayi shiru kanta na kallon sama
idon ta a buɗe da alama wani tunanin take yi Ammar ne ya shigo bakin sa ɗauke da
sallama yayi matukar kyau cikin wata yadi baƙa da layi layin fari Amma farin beje
har can ba ɗinki half jamfa da gani base an faɗa maka ba kasan yadin me tsada ne
kanshi ba hula gashin kan yasha gyara sosai normal aski ne da gyaran fuska gashin
yayi kyau se sheƙi yake yi zama yayi kujeran dake kusa da Mom ɗin ganin yayi
sallama kamar bata jiba gashi yanzu se ƙiran sunan ta yake yi Amma ina tayi nisa
cikin tunanin da take yi seda ya ƙira ta da ƙarfi sannan ta farga miƙe wa tayi daga
kwancen da take ta zauna ta jingina da jikin kujeran kallon ta yayi cikin nutsuwa
yace ''Mommy Please me yake damun kine kwana biyun nan duk kin canza kaman kina
cikin damuwa Amma idan na tambaye ki se kice ba komai kinsan bama jin daɗin ganin
ki cikin damuwa ko'' ya ƙarasa fiskan sa da alamun damuwa tattare dashi shiru tayi
kaɗan

kafin ta fara magana sega Ajeeb ma ya shigo bakin sa ɗauke da sallama kayan su iri
ɗaya sak da Ammar komai iri ɗaya shima zama yayi kusa da Ammar ɗin bayan ya gaishe
da Mom ɗin magana ta fara kamar haka

''ba komai kawai de ina kewar Ruma ne kaga ta tafi gidan baffan ku acen zata yi
hutun ta tare da ƴar uwar ta Ashfat gashi kuma yanzu zaku tafi can Meduguri wajen
kakan ku nasan kuma zaku ɗan yi kwana biyu tunda kun jima baku jeba ai dole na
shiga damuwa dama kukam baku jima da dawowa ba bayanda zanyi ne tunda Abban kune
yace kuje Amma ni bason zuwan naku nake ba''

Shiru suka yi shide Ammar be yadda wannan shine yasata cikin damuwa ba tunda ai
idan tana so zata ce Ruma ta dawo inyaso ko ita da Ashfat ɗin base su dawo tare ba
yasan ta faɗa ne kawai dan ta kawar masa da wannan tunanin shi kuma Ajeeb daya ke
bada shi aka fara maganan ba se ya yarda kewan su da zata yi ne yasa.

Be nuna mata be yarda da abunda ta faɗa ba sema cewa da yayi ''Mommy Please ki
kwantar da hankalin ki ko munje baza mu wuce sati ɗaya ba zamu dawo kinga ai a
satin zamu zazzaga dangi kidena damuwa Please''

Ajiyar zuciya ta sauke kawai ba tare da tace komai ba har ga Allah a cikin ranta ba
wannan bane yafi damun ta abunda yake damunta yanzu be wuce canzawan da Abba yayi
ba ko tana masa magana sama sama yake amsawa yanzu wani kalan canza wa yayi in
magana ze mata haka zena basarwa baya dawo wa gida se dare yayi sosai baya dawowa
da rana ma don cin abinci kwata kwata ta dena gane kanshi duk daren da yake kaiwa
kuwa baiwar Allah tana zaune a falo zaman jiran shigo wan sa Amma daya ganta se
yayi kaman be ganta ba idan kuma a gaban yaran nasu ne baya nuna mata komai shi ya
tada tafiyan su Ammar wai suje su zaga dangin su na Meduguri mahaifiyar sa ma tana
can shi da kanin sa ne kawai anan Abuja suma kuma aiki ne ya kawo su nan se kuma
ɗan matsaloli da suka ringa fuskanta a can ɗin yaso ɗaukan mahaifiyar tasa ma su
dawo tare Amma se taƙi fir tace baza tabar tushen taba ya barta anan hakan yasa ya
barta.

Wani hanzari ba gudu ba anan shine ƙanin Dad ɗin ba kowa bane se baban Ashfat
sannan Maman Ashfat ɗin kuma ƙanwar Mommy ne a taƙaice de Auren dangi suka yi da
Abba da Mommy dan mahaifiyar Mommy ƙanwa ce ga mahaifiyar Abba Amma ta rasu a hanun
mahaifiyar Abba Mommy ta girma wannan a taƙaice kenan se lokaci yayi zaku ji komai
dan gane da su Abba.

Sun gama shirin su dama already driver ne ze kaisu so sun shigo ne domin su yiwa
Mommy sallama kayan jikin su kuwa mussaman Abba yasa aka ɗinka musu dan acewar shi
baza suje da ƙananan kaya ba haka yasa aka yi musu ɗinki masu yawa kuma duk kala
ɗaya kaman wasu ƴan biyu komai kala ɗaya hatta takalma sabbi Abba ya saya musu su
kansu da suka saka kayan seda suka ga ya musu kyau dan kwata kwata basu da irin su
gashin kansu ma Abba yayi magana har ya gaji kan su rage yawan shi Amma suka ce ya
bar musu shi haka yayi shiru ya kyale su (niko nace ai bega na oga SHEAD bane shi
yasa).

Addu'a Mom ta musu sosai da fatan isa lafiya sannan ta basu saƙon gaisuwa su kaiwa
dangi har baƙin mota ta raka su inda driver yake jiran su dan har ya zuba trolley
nasu a bayan motan haka ta musu addu'a sosai irin wanda uwa take wa ƴaƴanta sanna
ta kuma ce musu su tsaya a hanya su sayi kayan abinci wanda zasu kaiwa ƴan uwan da
toh kawai suka amsa sannan suka shige motan driver ya tada ita suka kama hanyan
Meduguri yayin da ita kuma Mommy ta koma part ɗin ta duk abunda suke yi Ammii tana
kallon su ta window ɗakin ta wani irin daɗi taji ganin sun tafi yanzu plan ɗinta ze
fara aiki cije leɓen ta na ƙasa tayi tana girgiza kai haɗe da yin wani shu'umin
murmushin da ita kaɗai tasan ma'anar sa sake labulen tayi ta zauna bakin gadon nata
dama ita ta bawa Abba shawarar ya tura su suga ƴan uwan su sabida ta samu abunda
take shirya wa ya tafi yanda taso hmmm Amma fa bata san da dawowan SHEAD bane shi
yasa take wanga zance muje de zuwa .

GOMBE


Please Login or Register in order to submit comment