Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


33️⃣
00️⃣ Page 3 0
Free


Kyau tuttukan presentations da suka yi aka fara raba wa tun daga wanda yazo na
biyar ha aka zo wanda ya kasance na uku ba kowa bane kuma face Ashfat taje ta karɓa
sannan aka ƙara kiran na biyu Ruma ita ma taje ta karɓa sannan na ɗaya Ayrah taje
ta ƙarɓa haka aka ta ƙira abubuwa ukun da aka yi duk Ayrah ne tazo na ɗaya hakan
kuma ba ƙaramin shiga ran muta ne tayi ba sosai aka jinjina wa ƙoƙarin ta,

Sannan aka zo na jss3 aka basu kyauta su banda ƴan ss3 sabida su weac suke rubuta
wa da neco yanzu haka basu gama ba, bayan an gama raba kyautan wa'inda suka yi
ƙoƙari da kuma faɗan wanda yazo na ɗaya se aka fara na Exams shi kuma daga na Uku
ne zuwa na ɗaya haka aka tayi tun daga ajin ƙasa da aka iso primary 3 Munib ne yaci
na ɗaya (ni kuma nace da taimakon Ayrah dan da nadan ita ba baze yi karatun ba so
da taimakon ta) zo kuga murna gun Anty kaman ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka taji
Dad ma yaji daɗin hakan sosai, haka aka ciga ba har aka zo primary Six anan kuma as
usual Ashfat ta fito a na uku Ruma ta fito na biyu Ayrah ta fito na ɗaya sunyi
murna sosai duk da ba sabon abu bane a gurin su haka be hana su farin ciki ba ita
de Ayrah ko a fuskan ta baza kace taji daɗi ba sede a ƙasan zuciyan ta taji daɗi
sosai kawai ta share ne tabar abun ta iya zuciya,

Koda aka zo ajin su Marwa ita ta zo na ɗaya bawai dan ilimin taba malamin ne yasa
ta haye wasu a cikin ajin nasu sunji haushi sosai sun yi mamaki kuma dan su kansu
sun san ba kullum Marwa take zuwa ba Amma ya aka yi kuma tazo na ɗaya, haka de tayi
ta murna ƴan uwan ta na taya ta har aka gama gaba ɗaya kowa yana zuwa wajen iyayen
sa Amma Ayrah kam zaman ta tayi ga kyaututtukan da aka bata a hanun ta, tawagar dad
de gaba ɗaya suka tashi zasu tafi tunda an gama taron toh daya ke shima babban ɗan
kasuwa ne nan suka fara gaisa wa da mutane wa'inda suka sansa dama wanda ya sani
suna kuma taya shi murna ƴar sa tayi ƙoƙari shi kuwa yake kawai yake musu su Mama
da Anty duk sunyi gaba harda du Marwa da Abdull shi kuma dad bayan sun gama gaggai
sawa da mutane ya juya ze tafi kawai suka yi ido huɗu da Abbu nan da nan kansa ya
wani sara masa da ƙarfi seda ya dafe kan toh shima de Abbu ganin dad da yayi seda
kansa ya juya da sauri dad ya ƙara sa barin wajen kaman zeyi tuntuɓe haka ya fita
suka wuce gida shida tawa gansa,

Ashfat da Ruma ne suka miƙe duk suka haɗa kyaututtukan su kana Ashfat tace ''Ayrah
kizo muje ki gaisa da Abbu na gashi can'' girgiza mata kai Ayrah tayi tare da cewa
''a'a kije kawai nikam base na jeba'' jin haka yasa nan take yana yin ta ya sauya
har zata ƙara magana se Ruma ta riga ta da cewa ''Ayrah ki taso muje mana ga yayu
na ma duk ba se ku gaisa ba'' haka de badan taso ba ta miƙe suka nufi gurin da Abbu
yake tare da su Ammar yana tambayan su yaushe a gari tun kafin ma su basa amsa suka
ga isowan su Ruma Ashfat ne ta faɗa jikin Abbu yayin da Ruma kuma ta fara rungume
ya Ajeeb sannan ya Ammar ita kuwa Ayrah tana tsaye kanta a ƙasa sede suka raba juna
sannan Ayrah tsuguna har ƙasa ta gaishe da Abbu sannan ta gaida su Ammar ma kallon
ta Abbu yayi kana ya amsa mata cikin sakin fuska Ashfat tace masa kawar suce tare
da faɗa musu sunan ta gyaɗa kai Abbu yayi yace ''Allah ya miki Albarka Ayrah ya
ƙara buɗa miki ƙwaƙwalwa'' kanta a ƙasa ta amsa da ''Ameen ngd'' haka suka shiga
hira kaɗan ita de Ayrah tana shiru Abbu ne yace ze tafi badan Ashfat ta gaji ba
haka suka wuce ita da Abbu Amma kafin ya tafi seda ya bawa Ayrah kyautan kuɗi shi
kansa besan nawa bane kawai ya miƙa mata ne Amma taƙi karɓa firr yayi da ita ta
karɓa Amma firr taki karɓa haka ya haƙura ya ringa sa mata Albarka,

Bayan tafiyan su Ruma tace ''yaya dan Allah yaushe kuka dawo baku faɗa mana ba ina
yaya Deen meya hana Mom da Abba zuwa'' duka wannan tambayoyin ta ringa jero musu
tana ya mutsa fuska kaman zata yi kuka Auren ne yace ''to rigima yanzu duka wannan
tambayoyin da kika jero ɗin wanne kike so a fara amsa miki yanzu de koma meye ne ki
bari semun je gida''ya ƙara sa faɗan hakan shide Ammar shiru yayi ya ƙure Ayrah da
ido gani yake kaman yasan me kama da fiskan nata Amma se yayi saurin kawar da
tunanin,

Ammar ne yace ''to Parrot kina ta zuba kin manta da kawar taki'' juya wa tayi da
sauri ta kama hanun Ayrah tace ''yanzu Ayrah baza mu sake haɗuwa ba se an dawo
hutu'' tun kafin Ayrah ta bata amsa Ajeeb yace ''Ayrah ke in iyayen ki naga banga
kowa ba ko basu zo bane'' ya faɗa fiskan shi ɗauke da tsan tsan mamaki, dajin haka
idon Ayrah ya cika da hawaye kawai seta ƙara yin ƙasa da kanta bata ce komai ba toh
shima ganin bata amsa masa ba yasa shi basar wa Amma a ƙasan zuciyan sa yana son
sanin amsan da zata bashi gashi kuma wani irin shiga ranshi yaji yarinyar tayi nan
da nan to haka yake a gurin Ammar ma nan da nan tun tana karatu yaji ta wani irin
shiga ransa matuƙa kuma yana son jin amsan ta, cikin son share maganan Ayrah tace
''Ruma barin tafi kar Bus ya tafi ya barni se mun dawo hutu bye'' ta faɗa tana juya
wa da sauri Ruma ta riƙo hanun ta juyo wa tayi gani tayi idon Ruma ya cika da
hawaye wai zata yi kewan ta dan har ga Allah tana son Ayrah sosai Allah ma ya sani,
rungume ta tayi sun ɗan jima kana ta sake ta su Ammar ma suka yi suka yi ta karɓi
kuɗin da suke bata Amma taƙi karɓa dan acewan ta ko ta karɓa ma me zata yi dashi
gwara kawai ta bar musu kayan su may be ze musu amfani da haka ta juya ta wuce Bus
da ze maida ta ta shige kusa da window ta zauna Ruma na ɗaga mata hanun ita ma seta
ɗaga mata hanun tare da mata murmushin daya mugun tafiya da imanin su gaba ɗaya dan
Ruma zata iya ƙirga sau nawa ta taɓa ganin murmushin Ayrah ita de baza kaga fuskan
ta a murtuƙe ba Amma kuma baza ka taɓa cewa tana murmushi ba,

Ita kanta Ayrah a ƙasan zuciyan ta zata yi kewan su gaba ɗaya kuma ita harga Allah
bata so bada hutun nan da aka yiba gashi zasu jima kan su dawo seda ta share ɗan
gutun hawayen ta abubuwa da yawa suna mata yawo a kanta,

Ruma kuwa bayan tafiyan Ayrah suma suka kama hanyan tafiya driver da ya kawo su
Ajeeb ya maida su dukkan su baya suka shiga suka saka Ruma a tsakiya tana tambayan
su yaushe suka zo, abunda ya faru bayan tafiyan Ruma Mom ta ƙira Dad ta faɗa masa
su Ammar jirgin su ya kusa landing toh da yake tun safe da ta tashi aiki take hakan
be bata daman zuwa taro suba Dad ne yaje shida driver bayan jirgin su ya sauka suka
gaggaisa da dad a nan ne yake gaya musu zashi school na Ruma yau suke abubuwan su
toh shi yasa suka ce gwara su wuce kawai,har zasu wuce makarantar su Ruma se aka
ƙira dad suna da meeting shiya sa yace driver ya kaisu shi kuma ya wuce gurin
meeting ɗin su kuwa ko gida basu yiba direct school na su Ruma suka wuce, taji daɗi
sosai da ganin su haka suka isa bakin tamfatse tsen get ɗin driver yayi hon aka
buɗe masa ya kutsa kai cikin gidan parking yayi duk suka fita Ruma ta ɗauka musu
Trolley nasu sauran kuma driver ya bisu dashi a baya, Ruma ce ta fara shiga falon
nasu suna biye da ita a baya ba ƙaramin kyau suka yiba duba da yana yin dressing na
jikin su tun kafin su ƙarasa shiga cikin falon Mom ta tare su side Hug ta basu haka
duk murna fal ransu gaba ɗayan su don sun jima basu ga juna ba sosai suka yi farin
cikin ganin ta har suka shige cikin falon suka zauna suka sata a tsakiya se kallon
su take yi, se a sannan suka gaisa sosai gaisuwa irin na uwa da ƴaƴan ta da kuma na
anjima ba'a haɗu ba take Mom ta ƙwala wa Ladi ƙira ta fara kawo musu abun sha ita
kuma Ruma ta wuce ɗakin ta don ta watsa ruwa ta kuma canza kaya, haka Ladi ta cika
musu gaba da abubuwa Mom da ta kalli bayan su bata ga gogan nasu ba tasan be dawo
bane kuma bata ji daɗin hakan ba ko kaɗan sosai suke shan hira abunsu se tambayan
su abubuwa take yi har da cewa ko zasu je suyi wanka su huta Ajeeb baki yaki rufuwa
yayi matuƙar farin cikin ganin mahaifiyar tasa sosai, miƙewa suka yi don su ɗan
watsa ruwa ga gajiyan hanya duka fita suka yi a part ɗin suka wuce nasu daya
kasance a tsakiya Mom da kanta ta fara jide musu trolleys nasu tana kai musu har
part nasu, su kuwa bayan sun shiga kowa ɗakin sa ya wuce suka watsa ruwa Ajeeb de
yana fitowa bed nasa ya ɗale ya gaji sosai shi yasa ze ɗan huta shi kuwa Ammar falo
ya fito se a Sannan ne ya samu ya ƙira SHEED dan ya sanar dashi sun iso,

🌹 LONDON 🌹

Kafin su Ajeeb su tafi sosai suka yi ban kwana da da su Mash da Byron harma da
sauran Sojojin gidan shi kuwa Deen yana ɗaki yana kwance suka shiga suka same sa
bacci ma yake yi lokacin haka suka ɗale bed nasan seda suka tada shi ya miƙe zauna
kallo ɗaya ya musu ya ja wani siririn tsaki ƙasa ƙasa Amma duk da haka seda suka ji
''whats your problem'' ya faɗa can ƙasan maƙoshi miƙe wa suka yi kana kaman haɗin
baki suka faɗa a tare ''zamu tafi Flight ɗin mu ya kusa tashi'' Okay kawai yace
dasu be ƙara cewa komai ba kallon juna Ajeeb da Ammar suka yi Ajeeb ne yayi ƙarfin
gwiwan cewa ''SHEED kazo mana ka raka mu airport ko haka zamu tafi ba muyi bankwana
ba ne'' ganin suna ɓata lokacin sune kawai yasa su juyawa suka nufi hanyar barin
ɗakin seda suka kusa fita kana ya miƙe sanye yake da pajamas launin Ash gashin
kansa a wargaje ya zubo har ta gefen fuskan sa, bed Room slipas nashi ya saka me
ɗan banzan laushi ya rufa musu baya basu ankara da yana bin su ba seda suka kusa
sauka daga stairs, cikin falon suka tsaya hugging na Ajeeb yayi haka shima Ajeeb
yayi hugging nashi back so tight shafa bayan sa yayi sunyi 1min kana ya raba jikin
su yayi hugging na Ammar same way da yayi na Ajeeb, akwai uzurin da yake dashi
yanzu shi yasa baze raka su ba fita suka yi suka wuce shi kuma ya tsaya a wajen
yana ganin fitan su ya saka hannu ɗaya a aljihu ɗayan kuma yana riƙe da wayan sa
yana dan nawa...

Manage This


💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa, ilmantarwa, harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


3️⃣
1️⃣ 3️⃣1️⃣
Page


🌹ABUJA🌹

zaune suke a falon Mom dukkan su suna duba kyaututtukan da aka bawa Ruma ga kuma
kuɗaɗen da ta samu lokacin har sunyi wanka sun huta tare suka ci abinci da Mom gaba
ɗayan su dama anjima ba'a haɗu ba yau de zuka tan kowannen su yana cikin farin ciki
Amma Mom a ƙasan zuciyan ta bata ji daɗin rashin dawowan RASHEED ba kawai de ba
yanda zata yi ne shi yasa taɗi suke yi Mom na tambayan su karatun su haka de wunin
ranan ya kasan ce musu duk suna cikin farin ciki suna hira irin na uwa da ƴaƴan ta
haka kuma Mom ce ta musu girki abinci kala kala na dare farin ciki kaman ransu ze
fita idan suna cin abincin suna santi yaushe rabon su da suci girkin mahaifiyar su
toh ita ma de ta jima bata yi girki ba dalilin rashin lafiyan ta se Abba ya nema
mata ƴar aiki Amma before ita take musu girki tunda ta kamu da rashin lafiya se ta
dena sun sha fama a wannan lokacin (koma de meye ne wannan rashin lafiyan zamu ji
daga baya) har Abba ya dawo Sallah ne kawai yake tada su yau ranan na iyayen sune
sallah isha'i suka tashi dukan su harda Abba suka wuce masallaci gwanin burge wa
sun saka shi a tsakiya duk kusan tsayin su ɗaya sede Abba ya ɗan fisu da kaɗan,
suma su Mom tashi duk suka yi domin su gabatar da nasu Sallah, wata mata ce ta
shigo cikin falon tana leke leke kamar mara gaskiya tana tafiya saɗaf saɗaf har ta
karisa wajen dining kulolin ta bu bbuɗe seda taci karo da na miya sanna ta kunce
gefen zanin ta seda ta ƙara lelleka wa ganin bata ga kowa ba yasa tayi saurin
barbaɗa garin data ciro a gefen zanin ta da sauri ta gauraya miyan da yatsan ta ta
gyara kullin ledan ta mayar gefen zanin ta kana ta juya ta fara tafiya saɗaf jin
kaman ƙaran tafiyan mutum yasa ta ɗeba a guje gashi ta kulle fiskan ta ba'a gane
waye ne ai aguje tayi waje Ruma kuwa da ta fito tade ga kaman wulga wan mutum Amma
bata gane waye bane nan ta tsaya a tsakiyan falon tare da rike ƙugu tana tunanin
toh waye ze shigo musu falo dan tabbas taga wulga wan mutum, kuma bata yi tunanin
tabi koma waye ne waje dan taga daga ina yake ba kawai seta share zancen a cewan ta
ai ba wanda yake shigo musu part kawai de idon tane ya nuna mata kaman mutum zama
tayi tana kawar da zancen daga ranta zaman ta bada jima wa ba sega su Abba da Ammar
dukan su suna shigo wa a lokacin ne kuma Mom ma ta fito duk wuce wa suka yi dining
Area dan suci abinci dare zama duk suka yi,

Ruma tana kujeran kusa da Ajeeb Ammar yana kusa da Mom ita kuma Mom tana kusa da
Abba haka suka yi zaman nasu Mom ne ta tashi ta fara serving nasu duk ta saka musu
ita ma ta saka zama tayi Ruma de kwata kwata bata jin daɗi haka kawai taji abincin
be kwanta mata ba se taji ma duk ta koshi hakan yasa ko spoon bata ɗauka ba dad ne
ya fara cin abinci se yaga duk sunyi shiru basu fara ci ba ɗago kai yayi yana
kallon su fuskan sa da halamun mamaki yake cewa ''meya faru kuma baku fara cin
abincin ba'' Ajeeb ne ya tashi saka makon ringing na wayan sa da yaji ya nemi
excuse daga gurin su ya fita a falon ma gaba ɗaya shi kuma Ammar cewa yayi
''wallahi dad haka kawai naji na koshi kasan yau nayi ɗuri da yawa bana jin zan iya
saka wani abu a ciki na idan nasa toh cikin ze iya fashe wa'' ya ƙara sa faɗa yana
dariya suma dukan su dariya suka yi Ruma tace ''nima wallahi a ƙoshe nake'' ta faɗa
tana ya mutsa fiska miƙewa Ammar yayi sannan yayi wa iyayen nasa seda safe kana ya
fice daga falon ya wuce sashen su, kallon Mom Abba yayi yace ''toh kefa lafiya dai
ko kode kema kin ƙoshi ne'' ya mutsa fuska tayi tace ''wallahi ji nayi kwata kwata
abincin ya fita a raina har wani Amai ma nake ji kam....'' ai bata ƙarasa maganan
bama taji aman ya taho da sauri ta tashi ta isa wajen sink ɗin dayake wajen dining
ɗin na wanke hanun nan ta fara kwara amai da sauri duk suka tashi Abba yana mata
sannu seda ya tsagaita sannan ta zauna tana maida numfashi miƙewa tayi ta wuce
dakin ta tace bari ta huta, gurin ya rage daga Ruma sai Abba sun ɗan taɓa hira
kaɗan Ruma ta tashi tamai seda safe shima bayan yaɗan ci abinci Amma ba daya wa ba
ya miƙe ya wuce sama inda Mom tayi,(sede nace musu good night).
🌹AYRAH🌹

Tunda ta sauƙa daga Bus nasu ta nufi get na biyu wanda ze sada ka da cikin gidan
hankalin ta yabar jikin ta dan confirm tasan duk wani abun da aka bata Mama ne zata
kwace ko Anty duk wanda ya riga ganin ta idan basu karɓa ba kuma toh ko Marwa ko
Eshall ɗayan su ne ze karɓe dan tasan halin su da ɗan banzan kishi yanzu zasu ce
ita ta samu kyauta su basu samu ba barin ma Marwa da haka kawai ma mugun ta ke
cinta haka de ta danne ta shiga part nasu ta wuce direct tun a falo taci karo da
marwa zaune ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yi tayi kaman bata ganta ba tayi wuce wanta
har ta ɗaura hanun ta kan handle na kofan ɗakin Marwa ta ƙira ta a tsiya ce tana
cigaba da taunar cin gum dake bakin ta tana yatsina fuska,dawo wa baya Ayrah tayi
nan ma bata yi magana ba tsaya wa kawai tayi,kallon ta Marwa tayi daga sama har
ƙasa a yatsine taja wani mugin tsaki ji kake Mmmwwwtttttss tsabar sautin shi
''dalla banza ki ban kuɗin da kika samu zonan ban abun nan'' ta wacce ledan kautan
da ta samu ɗin ta fara ɓalle sa tana mata masifa kaman uwar ta tana cewa ina kuɗin
kuma, haka Ayrah tana ji tana gani Marwa ta kwace kuɗaɗen duka haɗe da gift ɗin
nata ta ɓalla mata harara kana tace ''banza jaka dalla kibar kallo na ida nuwa
kaman wata mayya zaki bar nan gurin ne ko sena yi ball dake'' da sauri Ayrah da
kuka yake shirin subuce mata tayi cikin ɗakin su da mugun gudu ita kuma Marwa ta ja
wani dogon tsaki again tabi bayan hanyar da Ayrah tabi da harara kaman idon zasu
faɗo ƙasa sannan ta cigaba da abinda take yi, Ayrah kuwa tana shige wa cikin ɗakin
ajiye hand bag ɗin ta tayi wardrobe nata ta buɗe ta ɗauki wata plain doguwar Riga
marar nauyi na material ta wuce bathroom wanka tayi ta saka doguwar rigar sannan ta
fito hanun ta riƙe da rigar da ta cire naɗe shi tayi ta saka a fannin kayan datti
ta tattare ɗakin sannan ta fita as usual tana sanye da ƙaramin hijab nata part ɗin
Mama,tana zaune kan kujera me zaman mutum biyu se Abdull dake zaune a kujera me
zaman mutum ɗaya suna ɗan magana sama sama yana riƙe da wayan sa ba wani abun yake
ba kawai de yana riƙe da shi ne shigowar Ayrah ne yaja hankalin su gaba ɗaya ita
kuwa tana shiga tayi ƙasa da kanta ta gaida su cikin ladabi Abdull ne kawai ya amsa
mata gaisuwan nata daga haka be ƙara cewa komai ba Amma harga Allah cikin ransa
baya jin daɗin halin da ƙanwar tasa take ciki shi ze iya cewa ma duk cikin ƙannen
sa yafi sonta Amma ya rasa dalilin da yasa baya iya nuna mata kula wa gashi yana
ganin yanda take shan wahala daga dawowan sa zuwa yanzu ga kuma yanda FA'IZ yake
wahalar da ita shima shide ba abunda yake mata Amma kuma baya shiga safgar ta kuma
yana gani ana mata abu baya iya magana akan hakan, saurin share tunanin da yake yi
yayi sakamakon yanda yaji kansa na sara masa sosai ita kuwa Ayrah gefe ta samu ta
zauna kanta a ƙasa ta fara magana ''Mm..Maaaa...ma da..dama na..nace ko akwai
a...aikin da....da zan...yi mi....ki'' ta ƙarasa maga nan tana in'ina tana harhaɗa
word ɗin bakin ta sabida tsannin tsoron da take ji ita fa bata tsoron Anty da
shakkan ta kaman yanda take tsoron Mama in tace takk toh haka za'ayi ba canji hakan
yasan ko magana zata mata take tsoro kai ko haɗa ido bata iyayi da ita, Mama da ko
kallon inda take bata yi ba tana ci-gaba da kallon ta se sannan ta juyo ta kalle ta
daga sama har ƙasa kana tace ''ki debo ruwa a bowl da towel kizo ki matsa min
ƙafa'' a yatsine tayi maganan tana juya kallon ta kan TV dan harga Allah yau ta
gaji sosai sabida zuwa makarantar su da tayi daɗin daɗawa ga ranta mugun ɓace yake
dan ita a cewan ta bata taɓa fita haka ba ga zaman kujera ga kuma tunda ta zauna
bata tashi ba haka bata yi magana ba (toh abun mamaki meye Mama take nufi da hakan
kenan? Bayan duk fitan da take yi kullum shine kuma zata ce bata taɓa fita haka ba
gsky abun de akwai ruɗa kai toh wai ma ina take zuwa ne?) Miƙewa Ayrah tayi ruwan
zafi ta ɗiba tayi mix da normal ruwa mara zafi ta ɗauko towel daga bathroom na
Maman sannan ta dawo a ranta kuwa mamaki take yi dan Mama bata taɓa sata maka
mancin wannan aikin ba se yau shi yasa take ta mamaki kuma hakan ya mata wani iri a
ganin ta mutum babba dashi yace a masa messaging na kafafun sa ai dole ma tayi
mamaki Amma tuno lokacin da Anty ta dake ta har ƙafan ta ya ƙumbura Indo ta matsa
mata shi da ruwa da towel yasa ta tunanin toh kode ita ma Mama taji ciwo ne,duk
wannan tunanin a seconds da baza su wuce goma ba tayi su,zama tayi a ƙasan carpet
ɗin kusa da ƙafafuwan Mama ta ɗauki towel ɗin ta matse shi ba sosai ba ga ruwan da
ɗan zafi Amma ba sosai ba,ɗaura towel ɗin tayi kan ƙafan Mama haba wa Mama kuwa da
ta miƙe ƙafa har gurin gwiwan ta a waje singalalen kafanta kaɗai yayi cinyan Marwa
idan ma befi ba sabida

Please Login or Register in order to submit comment