Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manyan mutane suka
tsaya ogan nasu ne ya fara magana duk sun ƙame wuri ɗaya gaba ɗaya hankulan su sun
maida shi kan ogan nasu sanar da su ƙarin matsayin da Sheed ya samu yayi kana ya
umurci Rasheed ɗin daya zo yayi jawabi akan karin matsayin da aka basa beyi musu ba
kuwa haka ya karaso wurin ya fara magana cikin nutsuwa kaf gurin shiru ya kara
ɗauka daddaɗan kuma sassanyar Muryar sa ne kawai ke tashi cikin nutsuwa yayi godiya
da karin matsayin da ya samu kana ya ɗau alkawarin yin aiki tuƙuru don kare kasar
ya karasa maganan sa da in sha Allah duk gurin tafi suka ɗauka raf raf raf a tare
kana suka fara rera taken kasar nasu duk sun kara nutsuwa ko motsi basu yi seda
suka gama wucewa ogan su yayi wasu daga cikin sojojin suna mara masa baya haka
shima MG Sheed ya mara masa baya sabida idan baku manta ba kafun su fara taron nasu
ya umurce shi da idan sungama yana son ganin sa haka suka wuce koda suka karasa
Office na oga nasu a bakin kofan sauran sojojin suka tsaya shi kuma MG shigewa yayi
bakin shi ɗauke da excuse can kasan makoshi tsaya wa yayi ya sara masa kana ya ƙame
a tsayen da yake gurin zama ya nuna masa seda ya kara sara masa kana ya zauna
kallon sa the general of the army SOLOMON JOSHUA yayi kana yace ''Yaushe kake so ka
koma ƙasar ka'' ya tambaye shi tare da kawar da zancen ɓata musu lokaci da yayi
ɗazu dama kawai yayi magana ne dan kar sauran suga be ɗau mataki akan hakan ba Amma
shi kansa wannan bawan Allah yana masa mugun kwarjini, numfashi MG Sheed yaja kana
ya fara magana cikin tsantsan natsuwa da kuma girmama na gaba da shi cikin harshen
Turanci yace '' nan da 1 month in sha Allah sabida akwai ɗan abunda nakeso na kara
sa kafin na koma'' gyaɗa kai yayi kana yace '' abunda yasa na baka Wannan muƙamin
ba komai bane se yanda naga kake da ƙokari duk da nasan zaka koma ƙasar ka Amma
zakana zuwa sannan idan wani aiki ya taso zan iya kiran ka sannan kuma ina so yanda
zaka yi aiki tuƙuru wa ƙasar ka nan ma kayi hakan'' haka de yaci gaba da masa
bayani da kuma shawarwari kana yace zeyi magana da his Excellency wato shugaban
kasa nasu akan ƙarin girman da yaba shi shikuwa ba abunda yake yi in banda gyaɗa
kai kurum sun yi magana sosai kana ya miƙe tareda kara sara masa kafin ya nemi
izinin tafiya shi kansa ogan nasu ma tafiya zeyi dan dama taron ƙarin girman ne ya
kawo sa Amma be cika zuwa ba tare suka fito kaman ɗa da Uba gasu duka farare tass
seda ya rakashi har motan sa ya buɗe masa ya shiga kana shima ya juya wuce wa yayi
can inda suka yi packing dan shima ba abunda ze tsaya yi wucewa gida kawai zeyi
seda ya kusa isa wurin motocin sauran sojojin suka farga da shi wasu daga cikin su
sun taya shi murna sosai wasu kuma ko kallon inda yake ma basu yi ba irin su LG
DANIEL da mu karaban sa da suke tsaye da alama suna tattaunawa ne a tsaka nin su
Mash ne yayi maza ya karasa inda MG Sheed yake a tsaye da su GENERAL da BRIADERL
GENERAL suma suna ɗaya daga cikin wa'inda aka gabatar da taron tare da su sabida
matsayin su suma yanada girma suna taya shi murna tsaya wa yayi daga gefe bece
komai ba har suka gama kana duk suka wuce shima de wucewan yayi da sauri Mash ya
buɗe masa marfin mota ya shiga kana ya rufe zagaya wa yayi ya buɗe marfin gaba ya
shiga ya kalli BYRON da yake sanye shima da kayan sojojin shine yake zaune a
mazaunin driver kana yace ''lets go'' tada motan yayi suka fita daga wajen sauran
sojojin da suka taho dasu suna mara musu baya haka suka ɗauki hanyar gida

*________________________________*

💋ABUJA💋

❤️(AYRA)❤️

SE MUN HAƊU GOBE IDAN ME DUKA YA KAIMU COMMENTS LIKE AND SHARE FISABILILLAH
GARGAƊI!!!
Ban yarda wani ko wata su karan tamin book a YouTube ko wani guri ba tare da
izini na ba kuma kar wanda ya haɗa min document a bar min kayana yanda na rubuta
shi da kaina na haɗa document ɗina da kaina sannan banyarda wani ko wata su juya
min littafi ta kowani irin siga ba idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar
mutum zebimin hakki na!!!!!!!!
Don neman karin bayani zaku iya nema na ta wannan number 09060413321

🌹MHIZZ TEEMAH🌹CE TAKU HAR KULLUM🥰
🔥THE BEGINNING 🔥

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵
GARGAƊI!!!!!!!
*Ban yarda ba, ban amince wata ko wani suyi amfani da wani sashe daga cikin
littafina ba ta kowace siga,ban yarda a karanta min shi a YouTube ba, ko a haɗa min
document duk wacce tayi hakan ko yayi hakan koda Allah nabar mutum se ya bi min
hakki na!!!!*

Free page 14_15

💋ABUJA 💋
❤️(AYRA)❤️
Ayra na fita daga ɗakin Anty tayi wani irin juyi kaman guguwa sega ta akan gado gif
kaman an wullata,Ayra kuwa tayi matuƙar razana da ganin wannan abun ba kaɗan ba ta
ruɗe tana fita daga ɗakin wani irin rawa jikin ta keyi tsaya wa tayi a inda take
zama tama kasa zaman sabida abunda ta gani yafi ƙarfin Brain ɗin ta jikin ta har wa
lokacin rawa yake yi rasa abunda zatayi tayi tama rasa wani irin tunani zata yi dan
duk yanda kuke tunani to ya wuce nan ta razana sosai,
Indo ne ta fito daga ɗakin ta da idan ta gama aikin da zata yi bata ƙara fitowa
Amma yanzu sabida Ayra ta fito dan ta duba ta taga me take yi ko ta tafi ganin ta a
tsaye jikin ta se rawa yake yi yasa ta kara sa gurin da take dan ita duk a tunanin
ta Anty dukan Ayra tayi kama hanun ta tayi hakan yasa Ayra kara razana tana shirin
sakin ƙara sabida kwata kwata tunanin ta baya jikin ta hankalin ta ma gaba daya
yayi nisan zango sake ta tayi tana ambaton sunan ta jin an ambaci sunan ta ne yasa
ta dawo hayyacin ta ai cikin sauri ta faɗa jikin Indo ta ƙanƙame ta sosai hawaye na
gangaro mata itama indo bubbuga bayan ta ta fara yi a hankali kana ta zaunar da ita
a gurin duk da ta dawo daidai Amma jikin ta be bar karkarwa ba shiru indo tayi tana
nazarin ta kana ta fara tambayan ta meya faru shiru Ayra tayi tana tunano abunda ta
kalla a ɗakin Anty cikin sauri ta runtse idon ta da mugun ƙarfi tana girgiza kanta
da kyar ta tsaya nan ma seda Indo ta riƙe hannun ta shiru tayi batace komai ba
ganin hakan se Indo ma bata ƙara tambayan ta meya faru ba ta miƙe ta wuce ɗakin ta
a cikin ranta haka kawai taji cewa da akwai matsala Amma ta share kawai dan a ganin
ta bawai dan tafara temaka wa Ayra ze zama na duk abunda ya faru seta sani ba
wannan duk ba shirgin ta bane Anty kuwa yanda ta kifu akan bed ɗin bata kara
motsawa ba kanta a kife haka tayi ta sauƙe ajiyan numfashi kamar wacce tayi tsere
da doki can kuma setayi shiru kamar me bacci seda ta nitsu tukkuna ta miƙe idonta
sun kaɗa sunyi jawur fiskan ta ya sauya wayan ta kawai ta ɗauka kana ta fito falon
ko kallon inda Ayra take bata yi ba
Ayra ganin Anty se ta fara ƴan kame kame tama rasa abunyi gaba ɗaya seta takure
guri ɗaya ita duk a tunanin ta Anty zata ɗauki mata ki a kanta ne ko zata dake ta
duk se tabi tayi wani iri shigewa cikin falon Anty tayi ta zauna kan kujeran da ta
tashi tafara aikin danna waya saƙo ta gani na yaron Mama me suna Abdul ya turo mata
saƙo akan ranan Monday zasu dawo tasa Ayra ta gyara musu ɗakunan su ai tana ganin
haka wani irin farin ciki ne ya mamaye ta duk da ranta a ɓace yake Amma taji daɗi
Ayra kuwa da duk tabi ta takure guri ɗaya ta ƙanƙame jikin ta kanta a ƙasa baiwar
Allah batasan me yake shirin faruwa da ita ba dan wallahi dawowan yayyen ta ba
ƙaramin barazana bane a gare ta, ba abunda Anty ta mata se cewa ma da tayi ta tashi
tabar mata ɗaki ba karamin mamaki jin abinda Anty tace tayi ba haka ta mike sum sum
tabar ɗakin
direct part ɗinsu ta wuce yau duniya sabo zata samu tayi abubuwan dake gabanta
tunda bata samu zuwa makaranta ba lokacin sha biyu ya wuce tana shiga ɗakin gyara
shi tayi tass ta wanke toilet tayi wanka kana ta fito karatu ta fara yi seda taji
kiran sallah sanna ta tashi tayi ta roki Allah sosai haka ta koma bed nata ta cigba
da karatun bata ko san inasu Eshall suke ba ko sunje makaranta ko basu je ba
karatun ta kawai take yi har seda taji ta gaji sannan ta kwanta gurin daga nan
bacci yayi gaba da ita
Marwa da Eshall yau ma basu je school ba Eshall ta tafi gidan su kawar ta Christer
ƴar class nasu ne ita ma sunan ta Joseca ita ce best friend ɗin ta har rashin
Sallah da batayi ma duk Joseca ce take zuga ta sabida ita dama ba religion nata
bane a takaice de maraban Eshall da arna suna ne kawai dan tana saka farce da gashi
kai duk wani abunda arna suke yi duk tana yi church ne kawai bata zuwa shima kuma
tana son zuwa kawai de tana tsoron Dad ɗin ta ne shiyasa badan ze hana taba se dan
kawai tasan baze ji daɗin hakan ba dama kuma bawani Addini suke da shiba tunda haka
suka taso suka ga iyayen su ko iyayen nasu ma basa musu magana akan rashin sallan
su ko kuma akan wani abun da suke yi ita Marwa kam ma ba'a magana dan ba ƙaramar
yar duniya bace duk makaran ta ya kara lalata su ga kuma haɗuwar da suka yi da wasu
ƙabilun hakan ya kara wargaza musu rayuwa kuma iyayen su basu bibiyan rayuwan su
waya ma ba ƙaramin ƙara lalata su yayi ba Marwa yanzu haka ma fita sukayi ita da
kawayen ta maza da mata sun tafi yawon su (hmm Allah ya shiryar mana da yaran mu a
wannan zamani da muke ciki wasu iyayen basa bibiyan halin da yaran su suke ciki da
haka ne kuma yara suke yin duk a bunda suka ga dama a nasu ganin ba abunda za'a
musu a gida daga haka kuma se su faɗa wani mummunan abun Allah ya tsare mana ƴaƴan
mu daga mummunan abubuwa suma iyaye ya kamata ku ringa bibiyan halin da yaran ku
suke ciki Please)
*::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::*
🌹DUKKU🌹
Haka suka ci-gaba da riƙe baiwar Allah nan kullum ba suƙi kullum Sadiq yana zuw
yayi mata karatu betaba gwada duba ta ba daga yaje karatu kawai yake mata duk
karatun da ze mata bata ko motsi ko ihun da take yi ma yanzu ta dena shi idan za'a
bata maganin ludayi haka ba abinda take Yi shiru haka zasu gama bata duk abinda
zasu mata yanzu ta dena ihu ko motsi ma ta dena kwata kwata tun abun yana basu
mamaki har suka dena mamaki ma gaba ɗaya sauƙi de kam yaƙi samuwa haka zasu ta ɗura
mata magunguna ana mata karatu kuma abun fa yanzu yafi ƙarfin tunanin baba Malam
dan duk yanda yake hasashen idan ana mata karatu dade sauran su zata samu sauƙi duk
abun yaƙi yiwuwa duk wani tunani da basiran sa ya ƙure shi akan ta shi tunda yake
ma be taba ganin sihiri irin wannan da yaƙi cin magani ba duk abunda zasu mata baya
aiki shide baiwar Allah se ƙara ramewa take yi tana bushewa sauki dekam shiru harwa
lokacin,

🌹🌹🌹🌹 LONDON 🌹🌹🌹🌹

A bakin get na gidan suka tsaya hon motan sojojin farkon tayi da gudu get Man ɗin
ya tashi ya wangale musu get na gidan cilla kan motan suka yi cikn gidan direct a
dede bakin kofan shiga falon ƙasa suka tsaya Mash ne ya fito daga bangaren sa ya
buɗewa ogan nasa mota shikuwa gogan da tunda ya shiga motan ya lumshe idon sa buɗe
blue eyes nasa yayi direct se cikin na Mash da yake ta kallon sa a sace karaf ya
ɗago se suka haɗa ido da wani irin sauri Mash yayi ƙasa da nasa idon shikuwa wani
mugun kallo ya aika wa Mash ɗin dan ya tsani kallo idan de har ana kallon sa toh
seya gane koda by mistake ne mutum ya ɗago to seyaji a jikin sa zuro ƙafan sa na
dama ya fara yi kana ya fito duka ai take a gurin duk suka ƙara kame wa suna sara
masa ko kallon su beyi ba ya wuce cikin falon bakin sa ɗauke da sallama ƙasa ƙasa
ba kowa a falon direct sama ya haura se ɗakin sa nan ya shiga rage kayan jikin sa
ya rage daga shi se short sannan ya wuce toilet ruwa ya watsa ya fito gaban mirror
ya tsaya ya fara shafe shafen sa yana gama wa ya wuce dressing Room gajeren wando
ya saka da T-shirt fari tass kana ya fito se baza kamshi yake yi zama yayi bakin
bed nasa yana zama sega Ammar da Ajeeb sun shigo a tare suma zama suka yi kusa da
shi Ammar ne ya fara cewa ''bro ina tayaka murna ɗazu muka ga an ƙara maka matsayi
kai Amma nataya ka murna'' ya karashe magana cikin matsakaicin farin ciki kaman
shine aka mawa karin matsayin haka shima Ajeeb suka taya shi murn sosai kai kawai
ya kaɗa musu be kara cewa komai ba mikewa suka yi tare da ce masa ya fito suci
abinci kaɗa musu kai kawai yayi fita duk suka yi shikuwa seda ya gama danna wayan
sa kana ya mike ya fita a ɗakin cikin tafiyan shi na izza da taƙama kaman wani
jinin sarauta haka yake taka step ɗin yana sauƙa seda ya karasa dining ɗin kana ya
tsaya jan kujera yayi ya zauna duk suna zaune basu fara cin abincin ba da alama shi
suke jira Ajeeb ne ya fara saving nasu abincin dayake su kaɗaine a gidan ɗaya daga
cikin Sojojin ne yake musu girki saving nasu yayi duk suka fara ci Amma Sheed kam
danna wayan sa kawai yake yi ko kallon plate ɗin beyi ba seda ya mula kana yaɗan
tsakuri abincin kaɗan ya ɗauki cup na coppee ya koma cikin falon anan ya zauna ya
fara kurɓan kaɗan kaɗan yana sha yana danna waya kaman meyin wani abin har suka
gama suma suka dawo cikin falon nan suke gaya masa suna son komawa nan da 2 weeks
kallon su yayi sau ɗaya ya kauda kai bece komai ba har sun cire rai da ze basu amsa
kawai suka ji muryanshi can ƙasa yana tambaya su akan meyesa zasu koma baza su jira
sa ba shiru suka yi suna kallon juna Ajeeb ne yayi saurin cewa ''bro wallahi
mingaji kuma kaga inada aiki na ga Ammar ma yana da nasa gwara kawai mu koma idan
yaso kai seka biyo mu daga baya'' yafaɗa yana marai rai cewa ko kallon shi beyi ba
gyaɗa musu kai kawai yayi ai suna ganin haka sunsan ya amince kenan shima dan yana
da ɗan wani abu da yakeso ya karasa ne shi yasa da tare zasu tafi wani irin daɗi ne
ya lulluɓe su Amma tuna cewa shi kaɗai zasu bari se suka ji wani iri ba daɗi sunyi
kusan shekara Uku a London ɗin nan suna tare Amma yanzu zasu tafi su biyu su barshi
duk se murnan nasu ya koma ciki mike wa yayi ya haura sama cikin yanayin tafiyansa
me jan hankali da nitsuwa nan ya barsu suna hira cikin nishaɗi haka rayuwan su tayi
ta tafiya cikin kwanciyar hankali da kaunan junan su sun zama kaman ƴan uwa da
sojojin gidan duka suna fita suje suta hira, BARI MU LEKA AYRA KO TA TASHI DAGA
BACCIN
*ANAN NACE SEMUN HAƊU GOBE IDAN ME DUKA YA KAIMU COMMENTS LIKE AND SHARE
FISABILILLAH*
~*GARGAƊI!!!*~
BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYA MIN LITTAFI TA KOWANI IRIN SIGA BATARE DA IZINI
NA BA BANYARDA KUMA A HADA MIN DOCUMENT KO A KARANTA MIN BOOK A YOUTUBE KO YANAR
GIZO BA IDAN KUMA WANI YAYI KUSKUREN YIN HAKAN KODA ALLAH NABARSHI SEYA BIMIN HAKKI
NA TAM.
GAME BUƘATAN KARANTA BOOK NAN DAGA FAKO HAR KARSHE ZE IYA SAMU NA TA WANNAN NUMBER
09060413321
🔥THE BEGINNING 🔥

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵

*GARGAƊI!!!*
*BAN YARDA WANI KO WATA SU SAUYA MIN LABARI BA TARE DA IZINI NA BA KO SUYI AMFANI
DA WANI SASHE NA BOOK NA KO A KARANTA MIN A YOUTUBE KO WANI GURIN BA TARE DA IZINI
NA BA DUK WANDA KUMA YAYI HAKAN KODA ALLAH NA BARSHI ZEBI MIN HAKKI NA IDAN KUNNE
YAJI JIKI YA TSIRA*

T̶S̶O̶K̶A̶C̶I̶: ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟɪᴛᴛᴀɪ ᴋɪʀᴋɪʀᴇ ʀᴇɴ ʟᴀʙᴀʀɪ ɴᴇ ʙᴀɴʏɪ sʜɪ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴡᴀᴛᴀ
ʙᴀ ɪᴅᴀ ʏᴀᴢᴏ ᴅᴀʏᴀ ᴅᴀ ʀᴀʏᴜᴡᴀʀ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴡᴀᴛᴀ ᴛᴏ ᴀ ʀᴀsʜɪ ɴᴇ .

free page 16_17

🌹🌹ABUJA🌹🌹

Ayra baccin ta tasha bata farka ba se gurin ƙarfe 3:00 Sallah ta gabatar haka ta
ƙara komawa ta ci-gaba da karatun ta yunwa take ji kuma tana tsoron zuwa ɗakin Anty
kar tace meya kai ta duk se taji wani iri dan tunda ta tashi tayi wayo bata taɓa
zama a ƙalla na awa biyu bata komai ba hakan yasa taji duk ina ma ace yanzu Anty ta
kira ta tazo ta mata wani aikin dade taji ta gaji da zaman kawai seta mike ta wuce
part ɗin Anty bata same ta a falo ba
direct wurin Indo ta nufa tana shirin shiga ɗakin ita kuma Indo tana shirin fitowa
karo suka ci da sauri Ayra tayi baya kanta a ƙasa kama hanun ta Indo tayi suka wuce
kitchen bata ce mata komai ba suna shiga ta zaunar da Ayra kana ta bata abinci anan
gurin dan tasan de Anty bata shigo wa kitchen ɗin zata iya rantse wa bata taɓa
ganin Anty ta leƙa koda bakin ƙofan kitchen ɗinne aikuwa haka Ayra taci abincin ta
koshi kana suka fara Aiki yau kam Indo tana nuna mata komai ita kuma tana sakawa
haka suka yi komai suka gama wanke wanken ma Ayra ne tayi nan ma ita ta matsa kan
cewa zata yi haka suka gama komai kaman uwa da ƴar ta nan ma seda Indo ta ƙara saka
mata abincin taci ta koshi dan haka kawai take ji a jikin ta akwai wani abun da
yake shirin faruwa da Ayrah ita kuwa bata wani damu ba haka taci ta koshi kana tace
mata zata je gurin Mama ko tana da wani abun da za'a mata kaman tace Mata karta je
haka
Indo taji dan haka kawai taji a jikin ta zuwan ta ba alkairi bane sede kawai tayi
shiru bata ce komai ba Ayrah kuwa wuce wa tayi ta fita a ɗakin itade Anty tun
abunda ya faru da safe bata ƙara fito wa falo ba Amma da kullum tana falo se dare
ne kawai take komawa ɗaki Indo har mamaki take a ranta tana cewa kode akwai abinda
yake damun Anty ne ko batada lafiya ne ita kaɗan ta de tana ta saƙe saƙe a ranta
wuce wa ita ma tayi nata ɗakin yaude sun samu free daga Indo har Ayran
Koda Ayrah ta shiga ɗakin Mama tasha Ruwan mamakin ganin su Eshall da Marwa Amma
bata nuna hakan a face nata ba duk suna zaune a falon ɗakin ya cika da kamshi itade
Ayra yau tana ganin abubuwan mamaki ga mama taci uban wanka kaman zata gasan wanka
su Marwa ma duk sunyi uban kwalliya da alama akwai abinda yake faruwa a gidan ne
ɗakin mama tsaf dashi an bul bula masa turare har hawa kai yake yi tsabar yanda
yayi yawa
Sauƙe kanta tayi ƙasa ganin yanda suke jifan ta da wani mugun kallo haka ta karasa
shiga ɗakin sum sum kamar muna fuka tsugunawa tayi ta gaida Mama harda su Eshall
ɗin duka ta gaida Amma ba wanda ma yayi mata kallon arziki balle har ta samu su
amsa gaisuwan nata gefe ta koma kan tiles ta zauna duk ma setaji dama bata shigo
ɗakin ba duk ta takure a wuri ɗaya wani irin dogon tsaki Marwa taja kana ta daka
mata wani mugun tsawa me hargitsa ƴaƴan ciki '' ke dan ubanki waya kira ki da zaki
wani shigowa mutane ɗaki kaman ɗakin jatumar ki!!''
Ai da sauri Ayrah ta miƙe tsaye duk tabi ta birkice tama rasa abunda zata ce kawai
se tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hanun ta hakan da tayi kuma ba ƙaramin
ƙara batawa Marwa rai yayi ba miƙe wa tayi a harzuƙe tayi kan Ayrah Mama tana
kallon ta bata ce mata uffan ba tana zuwa ta ɗebe marwa da wani bahagon mari bata
hakura ba dama gashi a tsaye Ayrah take kwashe ta tayi se gata rigijib a ƙasa ita
kanta Marwa da ta kwashe ta seda taji zafin ƙafan ta dama kuma ƙashi ne tazo ta
haɗa shi da tsoka ai dole ne ma taji zafi ga masifa na cinta juyawa tayi fuuu ta
koma inda ta tashi ita kwata kwata a rayuwan ta bata tafiya a nitse komai ɗinta
cikin sauri take yin sa ga faɗa masifa kam ai gidan ta aka zo seda ta zauna sanna
ta ɗago ganin har lokacin Ayra na gurin ta ƙara tunzura masifa na cinta ta daka
mata tsawa ''dan uban ki baza ki fita daga ɗakin nan bane wallahi karki yarda na
ganki a waje yau jaka ƴar matsiya ciya!!!''
Miƙewa tayi da kyar dan fa taji jiki faɗuwa kan tiles ba wasa ba haka ta fice a
ɗakin tana dana sanin shingan ta part ɗinsu ta wuce a ranta de tasan dole wani abun
ne zasu yi shi yasa duk daga Anty har Mama suka ce ta koma ɗaki ko wani ne ze zo
dan haka kawai dekam baza su ce taje ɗaki ba suda basu so sugan ta tana hutawa da
wannan saƙe saƙen ta ɗale kan bed nata bata wani cika yin karatu sosai ba idan
harde ta gane explanation toh duk sauran me sauƙi ne shi yasa ko yanzu ma kwanciyan
ta kawai tayi kuma ba bacci ma take jiba tana nan a kwance
kaman daga sama ta fara jin diran motoci da sauri ta miƙe karisawa tayi kusan
window ta ɗan yaye labulen tana leƙa wa motoci ne masu numfashi guda biyu suka
shigo buɗe marafan motan farkon aka yi wasu alhazawa suka fito su biyu suna da
haske sunɗan tasa baza su wuce 40 years ba ko fiye da haka dan sun ɗan manyan ta
Sannan kuma aka buɗe na bayan nan ma wasu mutanen ne su biyu fara re ne tass Amma
ɗaya daga cikin su duk ya fisu haske baida ƙiba yana sanye da farar shadda ƴar uban
su kyakyawa ne

Please Login or Register in order to submit comment