Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 12 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsabar yanda take buzuma da ita,jin wani zafi ya ziyar ci
ƙafan nata yasa ta bangaje Ayrah da tayi muguwar tsorata jikin ta har ya fara rawa
bowl na ruwan ma ya zube kan carpet ɗin ga towel ɗin ma yayi nashi ɓangaren sabida
yanda ta wuntsila ƙafan nata kaman wanda aka sara mata wuka wai ita a dole taji
zafi da sauri Abdull ya miƙe Amma ko me ya tuna kawai se yayi sauri komawa Ayrah
kuwa cikin ranta se addu'a take yi dan tasan yau kam nata ya ƙare towel ɗin ta
ɗauka da bowl ta fara goge carpet ɗin koma cikin sauri take yi ta ruɗe sosai hakan
yasa ta rasa abunda zata fara yi First ta matse towel ɗin cikin dan roban sannan ta
cigaba da goge carpet ɗin, wani irin tsawa Mama ta daka mata har Abdull seda yaji
shi har kansa da wani irin voice nata that resemble na maza tsaf da tayi tsawan nan
zaka ɗauka namiji ne yayi sosai Ayrah ta tsorata ta miƙe tsaye jikin ta na
trembling ta sake towel ɗin hanun ta ya faɗa cikin bowl ɗin ɗan sauran ruwan ya
ƙara zubewa a gurin ita bata ma lura da hakan ba dan sosai jikin ta ke rawa,kallon
Abdull Mama tayi sannan tace ''kai tashi ka ƙira min yayan ka'' miƙewa yayi ya fita
a ranshi yana ayyana yarinyar nan yau ta gama inde har ya samu FA'IZ yana nan AYRAH
jin Mama ta ambaci a ƙira mata Fa'iz seda cikin ta ya bada wani sauti na matuƙar
tsoron da ya ƙara cika fal ranta ba'a jima ba sega Abdull ya shigo yana cewa ''Mama
yana bacci'' wani mugun kallo Mama ta wurga mai tace ''jeka tada shi maza maza
yanzu yazo nan'' juya wa yayi ya ƙara fita ba'a jima ba se gasu nan sun shigo tare
sanye Fa'iz yake da boxes brown se vest hanun shi na ɗaure da sarka wuyan shi wani
chen ne guda biyu na zallan diamond haka hanun ma na diamond ne se wani bracelet
dake ɗaure a ɗayan hanun wanda daka ganshi kasan ba ƙaramin kuɗi bane yayi aiki a
gurin yana tafiya yana bubbuɗawa irin tacaccun ƴan iskan nan gashi da halamun maye
a tattare dashi dan be gama sakin sa ba haka ya ƙaraso zama yayi kan kujera yayi
balancing sosai sannan ya kalli Mama da jajayen idanun sa beyi magana ba, Mama ne
ta gaya mai abunda Ayrah ta mata harda ƙara manda akai tace wai ta ƙone sosai after
that she pour water on her expensive carpet, Abdull de shiru kawai yayi haka ma
Ayrah Fa'iz da Mama ta gama gaya masa abunda Ayrah tayi kallon ta yayi a walaƙance
sannan ya miƙe cikin husky Voice irin na ƴan iska yace ''ke biyo ni'' kana ya fita
binshi tayi suka fita Mama ta ƙira me aikin ta dan ta gyara wajen shima Abdull fita
yayi ya wuce masallaci....


*Se bayan Sallah idan me duka ya kaimu*


*Kada fa ku manta littafin nan na kuɗin ne kuma a halin yanzu Free Page ya kusa
ƙare wa dan haka duk me buƙatan biyan ƙuɗin Wannan littafin 300 ne kacal ze iya
tuntuɓa na ta wannan number 09060413321don samu biyan nashi sabida a fara daku kar
ku bari ayi wannan tafiyan baku*


COMMENTS
LIKES
SHARE
FISABILILLAH👏

✍️
Mhizz teemah



💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa, ilmantarwa, harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


3️⃣
2️⃣ page 3️⃣2️⃣
Free

Bayan shigan su ɗakin sa a falo ya sata neel down ta ɗaga hanun ta sama shi kuma ya
wuce cikin ɗaki dan har lokacin bawai ya gama huta wa bane haka yasa yana shiga ya
faɗa bed nasa se bacci ka'idan sa ne baya shan abun maye se idan zeyi bacci ko kuma
idan yaje club nan ma ba wani sha yake yi a cen ba a gida ne yake yawan sha sabida
yafi yarda da tsaron gidan a nan ne kuma ze samu nitsuwa lokaci ɗaya har ya samu
daman yin abubuwan sa, baccin sa ya sha yayin da Ayrah kuwa tun tana kuka har
hawayen ya dena zuba ta matu ƙar gajiya dan wallahi shi wannan neell down ɗin yama
fi wani funishment ɗin wahala ta ɗauki tsawon lokaci a haka shi Fa'iz kam yama
manta da yasa ka wata yarinya wani abun be farka ba se gurin la'asar nan ma ringing
ɗin wayan dane ya tada shi ganin me ƙiran nasa yasa shi saurin ɗauka yana seta
kanshi banji abun da aka faɗa masa ba Amma daga yanayin yanda yake wayan da wani me
girma yake yi dan kanshi a ƙasa kaman wanda yake waya dashi ɗin yana gaban sa can
se yace ''Darrrr ne oga'' yana girgiza kai kana ya muƙe yace ''yanzu zan fito oga''
kana ya katse ƙiran bathroom ya faɗa nan yayi wanka shaf shaf ya fito ya fara shiri
cikin wando jeans da yayi masa yawa gashi da faɗi Amma hakan ma kwaliyya ne jikin
wando akwai aljihunai masu ɗan yawa wanda suka ƙara wa wandon kyau kalan suwan toka
se ya saka riga T-shirt shima ruwan toƙa da ɗan kwalliyan ɓaki a kafaɗan rigan tsaf
ya shirya ya fara haɗa kayan sa cikin trolley ya saka kaya kala biyu se wasu
kwalabe da wani abu kaman hoda an killace sa cikin leda suma sunada waya fari tass
wani abun da ya matuƙar bani mamaki ya kuma sani cikin mugun shock shine yanda naga
ya fito fa bindiga gida biyu ɗaya ya saka cikin trolley ɗayan kuma yasoka si bayan
rigan sa ta ciki se wata ƴar ƙaramar wuƙa wanda idan mutum ya gani baze taɓa cewa
wuka bane dan bakin sa be fito ba se an ja wani guri daga jikin wuƙan sannan bakin
gurin kaifin yake fito wa shi kuma cikin aljihun sa ya saka sa ya saka takalmin sa
me igiya ya ɗaure igiyoyin jikin takalmin cikin minti talatin de ya gama shirin sa
sannan ya fito falo turus ya tsaya ganin Ayrah shi yama manta da ita wallahi ita
kuwa baiwar Allah wannan lokacin ba ƙaramin gajiya tayi ba ga yunwa tana ji ga kuma
Sallah da bata yiba daga azahar har la'asar duka jikin ta har ɓari yake yi gwiwan
ta ya sandare yana ta ɓari dan har layi take kaman zata faɗi sabida wahala batama
san ya fito ba seda taji ya buga kujeran dake kusa dashi ya daka mata tsawa da
sauri ta ankara shikuwa dake sauri yake kawai se ya daka mata tsawa ''keeee dallah
tashi ki fita ko nayi Ball dake'' ai da sauri tayi yunkurin tashi Amma tana miƙewa
se ta zube dan ƙafan ta rawa yake sosai more expecially gwiwan ta wani mugun tsaki
yaja yana zuwa yayi ball da ita ya bude kofan har waje yayi ball da ita kana ya
rufe kofan sa be ƙara bi ta kanta ba sabida saurin da yake yi ga kuma jiran sa da
ogan sa yake yi ba wanda yayi wa sallama ya fita a gidan ya shiga motan sa yaja shi
da mugun gudu, Ayrah kuwa tunda ya wurga ta waje bata ƙara motsi ba da alamu de
suma tayi a kuma dede wannan lokacin ne Abdull ya shigo gidan dan dawowan sa daga
masjid kenan shi yaga fitan Fa'iz ɗin Amma shi be gansa ba ganin ta kwance yasa shi
saurin ƙarasawa inda take ya fara ƙiran sunan ta Amma shiru kaman ma bata numfashi
fahimtar hakan da yayi ne yasa shi shiga ɗakin sa ya dauko ruwan gora a fright ya
dawo inda take buɗe marfin yayi ya tarfa ruwan a hanun sa sannan ya yarfa mata nan
da nan se gashi ta ja dogon numfashi Amma bata buɗe idon taba sabida bata ma son
ganin wanda yake kanta shi kuwa Abdull ganin numfashin ta ya dawo yace ''ke tashi
ki bar nan'' da sauri ta miƙe duk yanda take jin kaman baza ta iya tafiya ba haka
de da kyar ta wuce fannin su shi ma ɗakin nasa ya shige yana mamakin meye ya sumar
da ita haka,bayan zuwan ta ɗakin nasu banɗaki ta wuce wanin wankan ta sake yi
sannan ta ɗumama jikin ta kaman yanda taga Indo ta mata kwana kin baya taji daɗin
jikin ta sosai ta ɗauro alwala sannan ta fito ta shunfuɗa abun Sallah sannan ta
kabbara seda tayi azahar da la'asar wanda bata yi ba sannan ta miƙe ta fita zuwa
part ɗin Anty sosai Anty ta mata masifa kan bata shigo ba se lokacin haka de tayi
shiru tana bata haƙuri dan bata da abun cewa harda zunguri ta samu haka ta cigaba
da rayuwa kullum hantara ta ko ina kuma Anty bata yi mata magana kan kyautan da ta
samu ba haka suka cigaba da rayuwa kullum cikin aiki take bata da wani hutu sauƙin
ta ɗaya Fa'iz baya nan yanzu ta rage shan duka sosai Mama de dama ba shiga shirgin
ta take yi ba ita iya kacin ta tazo ta mata aiki shikenan Amma koda su Marwa zasu
mata masifa ko duka a gaban ta baza ta ce dasu cikanku bama itade kawai harkar
gaban ta take yi fitan da take yi kuma bata fasa ba kullum seta fita Dad baya ce
mata komai kullum de suna tare da Anty idan ya fita aiki hankalin sa nakan gida
baya wani jimawa yake dawo wa ya rame sosai kaman me fama da ciwon ƙan jamau haka
kullu yaumin idan Mama zata fita seta kwasa kuɗi a gurin sa kafin ta bar gidan baya
ce mata komai, toh a ɓangaren Fa'iz kuwa tafiya yayi me tsayi har ya doshi wani ɗan
jeji ya kutsa motan sa gudu kawai yake fallawa har yayi nisa cikin jejin sannan ya
iso wani tan gamemen get me ɗan banzan girma beyi hon ba wayan sa kawai ya ciro ya
ƙira wata number suka yi magana yace gashi nan ya iso sannan ya katse ƙiran..


COMMENT
LIKE
SHARE
FISABILILLAHI
🌹Mhizz Teemah🌹



💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa, ilmantarwa, harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️

3️⃣
3️⃣ Page 3️⃣3️⃣
Free

Yana katse ƙiran be wuce da minti biyar ba aka buɗe get ɗin ya kutsa kan motan ciki
fili ne sosai a gurin daga can nesa kuma gida ne a tsakiya gurin yana da matuƙar
girma sosai ginin ya tsaru ga an kewaye gurin da matakan tsaro yanda gurin yake de
kaman gidan gona,fitowa yayi daga motan wasu mutane sanye da baƙin kaya da glass
shima baƙi suka ƙara sa gurin nasa ɗaya ya karɓi trolley sa ya fara tafiya suka
rufa masa baya kuma gaba ɗayan su da bindiga a hanun su hanyar gidan suka nufa ba
wanda yace da wani ƙala har suka isa Amma basu shiga ba a nan bakin ƙofan suka
tsaya har da shi Fa'iz ɗin ma wani madani da yake gefen ƙofan ya danna sau ɗaya be
ƙara danna wa ba can se aka buɗe kofan wani matashin Baturen saurayi ne da baza su
wuce Sa'annan juna ba ya buɗe ƙofan fari tas da ka ganshi kaga Bature fiskan nan ba
halamun Rahama a tattare da shi sanye da wasu arnayen kaya shiga cikin falon suka
yi inda kafin su shiga Fa'iz ya karɓi trolley sa ba karamin haɗuwa falon yayi ba
wasu mutane ne zaune su kusan biyar dukan su Turawa ne zama yayi ya gaishe su yana
wani babbatse wa yana cin magani irin nasu na riƙakkun ƴan iska shugaban cikin su
ne ya fara magana cikin harshen turanci yace ''yanzu de abun da yasa na ƙira ka
shine akan aikin nan dan a yau zamu koma kuma ina saran wannan ban zan ya kusa
dawowa so kawai nake daga an gama aikin nan se a gama dashi dan naga yana samu guri
da yawa yana abun da ya ga dama ya kamata tun yanzu mu taka masa birki dan wancan
tsohon ya ɗaure masa gindi'' ya karasa a harzuƙe abun mamaki kuma ba kowa bane yayi
magana nan face L.G DANIEL wato LEAUTENANT GENERAL (abokin aikin SHEAD) shiru
gurin ya ɗauka na wasu mintuna kafin saurayin da ya buɗe wa Fa'iz ƙofa ɗazu yace
''LG ni bansan me Dad yake nufi da wannan yaron ba wallahi ni tun farkon ganin sa
naji na tsane sa wato yanzu kuma harda ƙara masa matsayi ma yayi nan gaba sede kuji
shi a matsayin Dad nawan ma gaba ɗaya nide kawai dan banda ra'ayin aikin nan ne
Amma da sena koya masa hankali shima tsohon nan ya riga da ya tsufa idan akwai
wanda ya kamata ya ƙara wa matsayi toh kaine LG'' cikin ƙunan rai ya ƙarasa maganan
se a sannan Fa'iz ya fara magana ''oga ni duk ba wannan ba ya maganan kayan da za'a
shigo dasu ne na guri na fa duk sun ƙare kuma kace suna hanya Amma naji shiru kuma
yanzu haka bullet ɗin hanun mu nida mutane na sunyi ƙasa'' a yatsine ya karasa
magana sannan ya ɗaura da faɗin ''kuma gaskiya ya kamata naji alert ɗin nan dan
yanzu ina buƙatan yin wasu abubuwan akwai wata ma da take so a ɓatar mata da wata
yarinya Amma RAMBO na saka wannan aikin dan shi ya santa ni banma santa ba Amma a
yanda ya faɗa min yarinyar ƙarama ce baza ta wuce 13yrs ba ko 14 na manta de'' ya
ƙarasa ko ajikin sa irin ko ohon nan shide yanzu buƙatan sa shine yaji alert dan
yana da abubuwa da yawa da yake son yi,da sauri LG yace ''no problem yaro na zaka
ji alert yanzu yanzu ma kuwa zansa ALEX ya maka kaya kuma gobe zuwa jibi nake sa
ran shigo wan su yanzu haka suna ready abu ɗaya kawai nake jira kuma kasan se da
taka tsantsan inba hak ba za'a gane ta wannan hanyar za'a shigo dashi, maganar
yarinya kuma toh idan an ɗauko ta ina za'a kaita kenan dan kaga bama harka da mata
duk da naji ƙarancin shekarun ta Amma baza mu ƙarɓe taba sede kawai ya kaita wani
guri can daji ya jefar'' gyaɗa kai Fa'iz yayi yace ''okay oga'' kallon ALEX LG yayi
sannan yace ''ka tura masa wannan kuɗin'' gyaɗa kai kawai yayi beyi magana ba
sauran maza biyu da suke wajen basu ce komai ba suma de dattijai ne sun hakimce kan
kujera haka suka cigaba da shawarar su a tsakanin su daga ƙarshe suka tsayar da
gobe ko jibi kaya zasu shigo sannan suka tura wa Fa'iz kuɗin a lokacin daga haka
tattaunawan nasu ya tashi inda LG yace Fa'iz ya zauna a gidan gonan har kayan su
shigo se su raba shi wa mutanen su harda su cocain da duk wani kayan maye suna da
masu karɓa ba ƙaramin kaya suke samu ba ta wannan hanyar hatta club suna karɓan abu
daga gurin su Guns kuma su suke amfani dashi sabida tsaro gasu dama ƴan iska daga
an musu abu kaɗan zasu fito da bindiga ko kuma su nemi halaka mutum, haka de suka
bi jirgi suka koma London yayin da shi kuma Fa'iz ya ƙira RAMBO sa yana tambayan sa
yaushe ne matar tace masa ze ɓatar da yarinyar nan yake sanan masa jibi ne jinjina
kai kawai yayi ya katse ƙiran sa yana tunanin ko yasa shi kawo masa yarinyar ne
kawai dan gwara ta ringa musu aiki a gidan gonan nasu idan ta masa kuma yayi me
afkuwa ya wurgar da ita 🫢 da wannan tunanin ya fita daga ɗakin ya fara duba gidan
dan ya kwan biyu be zo ba lokacin da suke Amerca baya samun daman zuwa sabida yanda
yayi busy ya buga tashan ci a can ba kaɗan ba dan shi ko karatun ma baya yi Abdull
ne kawai yake karatu shi de sede kawai azo a basa mark kuma yana da ilimi ga
ƙwaƙwalwa kawai baze yi bane sabida isa da jin kai, da haka ya koma ya kwanta yana
ɗauka chargy da kayan maye har bacci ya ɗauke sa.

LONDON

GAR wato general of the Army be san ALEX baya ƙasar ba se dawowan sa kawai ya gani
wajen 8 na dare dan bayan sauƙan su seda suka wuce gidan LG suka ƙara wasu
shawarwarin game da fitar da kayan da za suyi jibi sannan ya wuce gida kuma dama
Dad nasa be san baya nan ba wani tamfatsetsen gida ne na gani na faɗa dan ya haɗu
iya haɗuwa yanda baki na baze iya misalta haɗuwar shi ba kawai kuyi imagination na
gidan shugaban sojoji na ƙasar LONDON ya kuke tunanin ze kasance ai kuma kunsan
baki baze misalta haɗuwar shi ba,yana shiga cikin gidan ya wuce falon su na kasa
wata matashiyar mata na hakimce kan luntsuma luntsuman kujerun falon hamshaƙiyar
baturiya fara fatt yanayin fuskan ta taɗan manyan ta Amma bawai ta tsofe ba se wata
matashiyar baturiyar budurwa zaune kusa da ita ta tada kai da cinyar matar ga Dad
(solomon) ɗin su yana zaune shima kujeran gefen su dama yanzu suke maganan ALEX ɗin
be dawo ba se gashi ya shigo ba wanda ya kalla a cikin su se cewa da yayi ''Hi Dad
Hi Mom'' yayi wuce war sa sama abun sa dukan su binshi da kallo suka yi yayin da
Dad bejin daɗin halin yaron nasa miƙewa PRETTY tayi ta wuce sama tana musu seda
safe, toh suma de dama jiran ɗan nasu suke yi ganin ya dawo kawai suka tashi suka
shiga nasu ɗakin..ASALIN SU Solomon Joshua babban mutum ne wanda ya kasance
bayahude yana da matar sa me suna SARAH DAVID sunyi Aure ba jima wa suka samu ɗan
su namiji me suna ALEXZENDRA JOSHUA suna ƙiran sa ALEX suna matuƙar son ɗan nasu
besan babu ba duk abun da yace yana so shi za'ayi, yana me Shekara 18 mahaifinsa ya
samu muƙamin THE GENERAL OF THE ARMY wato shugaban sojoji wannan muƙami ya ƙara
sauya ALEX yana abunda yaso kuma ba wanda ya isa ya taka shi yana taka duk wanda
yaso daga ɓangaren mahaifinsa kuwa ya fuskanci abubuwa daya wa daga ɓangaren abokan
gaba har hakan ya haifar masa da matsala sabida yawan tunani da yake yi ga kuma
makiya da suka sashi a gaba har abun ya lafa bayan wani lokaci duk a tunanin su
komai ya lafa hankalin su ya kwanta sun sakan kance se kuma sauya wan ɗan nasu dan
ganin farat ɗaya ya sauya ba'a gane kanshi ya koma riƙekken ɗan iska ga kuma SARAH
na ɗauke da wani cikin haihuwa yau ko gobe haka de suka cigaba da zama toh a
ɓangaren ALEX ya ƙara lalacewa ne da taimakon LG DANIEL sabida samun muƙami da
mahaifin sa yayi shi ya ɗarsa wa LG mugun ƙuduri a ransa na son ganin ya kawar da
shi ya kuma maye gurbin sa toh hakan bata yiwu ba kawai se ya yanke shawarar janyo
ɗan sa a jiki ya kuma ɗaura shi kan wata hanyar daban har ya samu daman cimma
ƙudurin sa toh kuma be wani sha wahala ba wajen janye ALEX ya kuma fara hangen
nasara a tattare da tafiyan sa har takai takawo sun fara yawo da makami wanda LG ne
yake basa a wannan lokacin ne kuma mahaifiyarsa ta samu yarinya Mace me suna PRETTY
tun daga nan basu ƙara haihuwa ba sun taso cikin gata se abinda suke so suke yi Mom
nasu ita ta ƙara sangarta su kuma kunsan yaran turawa se abund suke so suke yi ba'a
saka su dole yin abun da basu yi niyya ba inde har yaro ya kai 19years toh abunda
yake so shi yake yi ko iyayen sa ne suka masa laifi ze iya maka su a kotu toh haka
Rayuwa su yake kunji waye ALEX da Solomon the general yanzu zamu cigaba da labari..


Comments
LIKE
SHARE
fisabilillahi
🌹Mhizz Teemah 🌹
(💋 Teemancy 💋)



💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa, ilmantarwa, harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi

Please Login or Register in order to submit comment