Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [10\4\2024]•••••Fatima Idris Umar {Mhizz Teemah}
Teemancy

BOOK ONE 1

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar

𝐇𝐀𝐙𝐈𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐔𝐁𝐔𝐓𝐀
🌹(Mhizz teemarh)🌹

*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*

Dedicated to my beloved 💔Mom💔

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sani ne,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘅𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗳𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵

1
1️⃣
Page 1

.............. Sauri sauri takeyi tagama shiri dan takusa latti yarin ya ce da
bazata wuce shekara 11 ba kyakyawa ce ajin farko tanada dara daran idanu masu
daukan hankali farace tas tanada kumatu dan daidai bakinta dan karami pink color
tanada ƙiba Amma bawani sosai ba yanayin jikinta irin na masu saurin girma ne akwai
shape kam ba'a magana duk da yanayin yarin tanta idan ta kara girma bakaramin hip
zatayi ba tandan fara yan ƙirga dangi a tsaye cur ƙana na batada tsayi Amma kuma ba
guntuwa bace tana de da ɗan matsakaicin tsayi Uniform dinta take sakawa riga da
wando se dan karamin hijab sunji guga safan ta farare tas tasaka takalminta
Sneakers fari da ratsin baki ajiki me dan uban kyau jakanta ta goya sauri take
sabida takusa latti.

Tana fita taci karo da wata yarinya da baxa ta wuce 15 years ba itakuma xata shiga
dakin seda taja baya dan tasan masifa xatasha idan ma bataji duka ba tunma kafun
yariyar tayi magana tayi saurin fara magana cikin ɗan ɗari-ɗari sabida wani irin
mugun tsoron yayun nata takeyi da xaxxakar muryarta cikin nutsuwa a sanyaye Amma
daga yanayin yanda tayi maganan aɗan kwai tsoro aciki ta furta '' MARWA nagama
shirin fa''ta fada idonta na cikowa da hawaye tsaki wacce ta kira da marwa taja
tana jefa mata mugun kallo sannan tafara magana a faɗace da masifa''Dan ubanki tun
yaushe muke jiran ki wallahi da baki fito ba tafiya xamuyi mubar ki kije da kafa,
shirya wa kawai sekinsa mutum yayi latti Mwwtsss!!'' taja tsaki ta juya fuuuuu
tawuce abunta, saurin bin bayanta tayi har tana hadawa da gudu tafita a dakin nasu
wanda yake part ne daban na yara matan gidan gaba daya, koda tabita ma ko walkiyar
ta bata gani ba wucewa tayi wani part dayake ta bangaren dama.

gida ne me girman gaske part uku ne se wasu dakuna biyu daban daban a farkon daga
get kuma wani sashene shima na daban me girman gaske nan ne part ɗin Abban su gidan
yanada fili sossai komai ya tsaru iya tsaruwa can cikin gidan kuma lambu ne me
girman gsk wanda ya gaji da haduwa, ba irin kayan alatun da babu aciki ko ina a
gyare tas tas ba datti se kamshin kasa yakeyi sabida albarkatun flowers da suka
cika gurin kala kala.
Part ɗin tashiga da sallama falon ya hadu ba karya ko'ina a gyare yake tas dashi
bakowa a falon karisa shiga tayi cikin dakin da sallama tsaya wa tayi a dede
mashigan dakunan tsayuwanta keda wuya sega wata mata ta fito daga wani ɗaki dayake
ta lungu farace fattt doguwa batada ƙiba siririya ce tanada kwayar ido kam masha
Allah kwala kwala dasu, baxata wuce shekara 28 ba sanye take da doguwar riga na
shan iska zama matar tayi kan daya daga cikin luntsuma luntsuman kujeran falon ta
daura kafa daya kan daya tana girgixa wa tareda danna dan kareriyar wayan ta Note
50 karisawa kusan ta tayi ta tsuguna ''Anty ina kwana'' tafaɗa batareda tunanin
xata amsa mata ba aikuwa kaman tasani domin kuwa ko kallonta batayiba balle ma tasa
ran xata amsa mata mikewa tayi jiki a sanyaye ta ce Anty natafi'' nan ma ko
kallonta batayi ba juyawa yarinyar tayi ta fita a dakin wajen ta wuce gidan get na
biyu inda anan driver sun yake jiran ta sabida sunyi latti Bus ɗin makarantar su
yaxo har yatafi basu fito ba shiyasa driver xe kaisu, ita kawai suke jira tana xuwa
ta bude marfin ta shiga yan mata ne su biyu se yaro karami ajiye jakanta tayi a
gefe ta gaisheda driver su wanda aƙalla xekai 36 years amsa mata yayi cikin raha
yana murmushi motsa bakinta kawai tayi kaman wacce tayi murmushi Amma se wanda ya
kula ze gani kuma hakan da tayi ba karamin kara mata kyau yayi ba har seda dinple
dinta na gefe daya inda tadan motsa ya lotsa bata kara kula kowa ba acikin motan ta
xauna shiru har suka isa suna isa ta fita a motan shiga tayi cikin makarantan
babban makaranta ne kallo daya xaka masa kasan seɗan wane da wane makarantan na
'ya'yan manya ne duk fita sukayi daga cikin motan suka shige makarantan koda suka
shiga makaranta kowa ajinsu ya wuce domin kuwa anriga da anshiga aji, tana kaiwa
kofan ajinsu ta tsaya tana neman ixinin shiga sabida akwai malami a ajin a saman
class ɗin an rubuta primary 6 hakan ya bayyana a primary 6 take, malamin baki ne
dogo baida kiba yana ɗaukan su English crister ne sir Richard suke kiranshi kaf yan
class ɗin dawo da kallon su sukayi kanta gaba daya class ɗin basu wuce 20 ba maxa
goma mata goma kowa da bench dinsa da kuma decks kallon ta malamin yayi from head
to toe sannan ya kalli watch din hanun sa gani yayi almost 8 suna shiga 7:30 kanta
a kasa Amma ita tasan kallonta akeyi sabida yanda ta ji ajikinta, izini shiga ya
bata a hankali cikin nutsuwa ta shiga cikin class ɗin yanda take tafiya se aga
kaman yanga takeyi cikin nutsuwa Amma kuma batada yanga domin kuwa ita haka take
komai cikin sanyi takeyin shi batada hayaniya tanada sanyi hali sosai,tsayawa tayi
ta gefe ta gaisheshi da turanci ya amsa tare da tambayan ta meyesa tayi latti shiru
tayi batace komai ba duk yana kallonta ya kara tambayan ta hakuri kawai tabashi
tace baxata kara ba umarni ya bata da taje ta xauna sannan ya juya ya kalli sauran
student ɗin wucewa tayi sum sum ta nufi gurin xamanta cigaba da koyar da su malamin
yayi har time nashi yayi ya tambayesu kowa yagane sukace a sannan ya fice a class
ɗin second period ta shigo malamar basic science ɗinsu ta shigo itama crister ce
sunan ta anty Ester kaf malaman makarantan kaɗan ne Musulmai
itama tayi nata koyarwan tafita haka har suka fita break, yan class ɗinne suka fara
fita yarage daga ita se wasu mata biyu zasu ɗan fita kaɗan matsawa sukayi kusa da
ita suka mika mata hanu suka gaisa dayar ta gefen daman ta mesuna Ashfat baxata
wuce shekara 13 tafara magana '' AYRA ya akayi yau baki xo da wuri ba'' shiru kawai
tayi batace komai ba tana duddu ba littafinta ta dayan gefen tane me suna Rumaisa'u
itama de baxata wuce 13 ba dan duk sun girmeta takarbi maganan da cewa ''haba ayra
muna miki magana kinyi shiru'' se a lokacin ne tace dasu babu Ashfat ɗinne tace
''toh shikenan yanxu de kixo muci abinci'' tana maganan tafito musu da kulan
abincin ta Rumaisa'u ma ta fito da nata kallon su ayra tayi sannan tace musu ita
kam ta koshi baxata ciba duk kallonta sukayi suna marai raicewa xasu fara magana
tayi saurin katse su da cewa itakam fa a koshe ta ke Amma a zahirin gaskiya ba
abunda taci haka ta fito sabida tayi latti ko ruwa bata shaba shiru sukayi basu
kara cewa komai ba domin kuwa sun san halinta duk yanda suka saba da ita bata taba
cin abincin su ba abun baya musu dadi Amma haka suke danne wa saide kaf cikin ajin
sukadai take kulawa suɗin ma ba koda yaushe ba bata sakewa da kowa haka take kullum
shiru idan malami ya shigo xata maida hankalinta gaba daya kanshi in yafita kuma
tayi shiru ko ta dauko littafinta tadudduba haka take bata sakewa da kowa suɗinne
kawai take dan magana dasu batada kawaye a makarantan intaxo ko fita batayi se idan
antashi kokuma wani malami ya kira ta, haka suka zauna sukaci abincin su sukadai
duk xuciyoyinsu ba dadi sun so ta sake dasu Amma taki tare suke kullum tun daga
primary 5 suka shigo suka sameta an maidasu bayane Amma da dukansu sunfita aji
Amma duk da haka tafisu ilimi sosai duk da suma ba bayaba tunda suka shiga
makarantan kowane term ita take daukan first position se Rumaisa second Ashfay
third ajere haka suke, Anata bangaren kuwa yunwa takeji Amma baxata iya cin abincin
suba sabida Umminta ta hanata kwadayi tun tana yarinya ita a ganinta idan taci
kaman ai xa'ace tana kwadayi ne, haka suka xauna suna cin abinci suna hira jifa
jifa ita kuma tana duba litattafan ta har suka kammala cin abincin nasu komawa duk
sukayi suka xauna wurin xamansu dake suma bawani fita sukeyi ba seta kama duk kowa
littafinsa ya dauka suka fara karatu Bench ɗin su yana kusa dukansu a waje daya
suke har aka dawo daga break karatun su kayi har lokacin tashi yayi aka tashe su
watsewa daliban suka farayi mikewa sukayi tare itada su Ashfat su xuwa ake a dauke
su ita kuma bus ɗin makarantan ne yake maidata tare suka fita su gaba daya driver
yaxo ɗaukan su haka suka wuce suna mata bye tana shiga bus ɗin da xe maidata gida
gaba daya yanayin ta ya sauya kwata kwata setaji dama ba'a tashi ba wani irin kunci
ne taji yafara ziyartan ta a wannan lokacin shiru tayi tafada duniyar tunani Ummin
ta kawai take tunawa duk da ma lokacin ba tada wayo bazata wuce shekara 4 zuwa 5
years ba Amma har yau tana tuna maganan da mahaifiyar tata take yawan gaya mata
wanda ya zauna a kwakwalwar ta takasa mantashi yana nan a kwakwalwar ta.......
Share fisabilillah 🙏
🖊️
Mhizz teemah 🌹

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar

𝐇𝐀𝐙𝐈𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐔𝐁𝐔𝐓𝐀
🌹(Mhizz teemah)🌹

*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
Dedicated to my beloved💔 Mom 💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wani ko wata a
rashi ne, idan kunga typing error ko wani mistake kuyi hakuri nima xan kokarta 🙏🥰.

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘅𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 , 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶
𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝗦
. 𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵

2️⃣
Page

........ sauran ɗalibai se taɗin su sukeyi har suka iso bakin get nasu ta sauka
itada sauran yayun ta karamin ya wuce part na maman sa suma matan suka wuce nasu
part ɗin domin su kimtsa koda ta shiga nasu part ɗin falo ne yaji set komai dass a
cikin part ɗin akwai kitchen daga ta gefe wani lungu se ɗaki guda daya Amma babba
ne da gadaje guda 3 kowanne a gefe da drawer shi dukkan su kowa da nashi bed ɗin
dakin ya tsaru se toilet wanda yake ta gefe ko ina tas ba datti bed natane a karshe
dan haka tana xuwa ta wuce bed ɗin nata ajiye jakanta da takalminta tayi a gefen
gadon kusa da drawer sannan ta xauna a bakin bed ɗin tacire safan kafanta farchun
ta kyawawa farare tas mikewa tayi ta cire hijab ɗinta naɗeshi tayi ta bude drawer
tasaka shi a gefe ta dauki doguwar riganta tawuce bandaki sabida ita bata iya saka
kaya a gaban mutane, wanka tayi tareda alwala a bandakin tasaka doguwar rigan
sannan ta fito tanade kayanta na makaranta tasaka acikin drawer dadduma tashumfuɗa
ta tada Sallah duk suna kwance ba wacce tayi haraman tashi harta idar da Sallan
tanaɗe Sallayan fita tayi a dakin dan tasan yanxu haka jiranta Anty takeyi, sukuwa
suna shiga dakin kowacen su ta dale gado ta kwanta ko Hijab ɗin basu cire ba suka
fara danna waya takalman suma suna shiga suka wullashi, kowace ta rike waya tana
dannawa mikewa Marwa tayi ita ayra takebi daga marwa se Ayra, tana da haske Amma
bata kai ayra ba siririya ce batada kiba ko kaɗan daga ita har yayar tasu duk
basuda yalwar ƙiba wuce wa tayi tashige bandaki wanka tayi ta fito ɗaure da towel
iya ƙugu kwata kwata ko shape ɗinma batada shi a tsaye take zololo batada wani
girman breast yanzu ne ma sunfara girma Amma a hakan take saka bra se aukin raini
ga masifa, wucewa tayi xuwa wajen bed nata tabude drawer ta dauki riga da wando
tasaka sannan tawuce ta fita a dakin ya rage babbar yayan su kawai itamade mikewan
tayi tashige wanka tasaka kaya doguwar riga duk kansu daga Marwa har Eshall ɗin se
aukin tsayi Amma duk kashi ne a jikin haka itama ta fice abunta, koda ayra ta fita
direct part ɗin Mama ta wuce wanda itace uwar gida bakinta dauke da sallama
tashiga falon yahadu iya haduwa wata mata shiyar matace xaune akan kujera tadan
tasa kadan xatakai 40 to above kallo take a tam fatsetsen plasma tv tashar
Bollywood suna film ɗin ruhil habbul maksumat duk da bajin yaren take yi ba Amma
haka de tana zaune tana kallon gaida ta Ayra tayi Sannan ta fara aikinta wanda
already dama tasan dashi ba se'an tuna mata ba gyaran ɗakin ta soma yi duk da
bawani datti ne dashi ba Amma haka ta kara gyarawa Mama ta hana 'yan aikinta gyaran
ɗaki iya girki kawai suke yi duk sauran ayyukan ita ce me gyara mata ko ina wani
sa'in setayi kusan sau biyar kafun nan tace ya fita bata daga ko tsinke a gidan
Amma haka take kullum se jiki da take ta ajiyewa yaranta kuwa kaman ba abinci suke
ciba duk arame suke se iyayi kuma yaran ta 4 biyu mata biyu maza tana gama aikin
gaba daya tafito duk ta gaji gashi bata ci abinci ba wucewa tayi danufin tabar
dakin mama ta katseta da cewa ''ke ina xakije kingama aikin dana sakine'' A tace
sannan ta fita a ɗakin dan lokacin kusan karfe 3:00
wucewa tayi ɗakin Anty tashiga itace marikiyar ta agurinta ta tashi tasameta
zaune itada muhibban ta wanda kwata kwata bata wuce 2years ba fara ce dan duk yaran
gidan farare ne xaune take akan carpet din tana ta wasa ita kuma maman ta tana
kwance akan kujera tana danna wayan ta bawata babba bace dan ashekaru baxata wuce
28 ba ɗan ta babba shekaran sa 7 yana primary 3 gaisheda antyn tayi bata damu da ta
amsa ba dan tasan ba amsawan xatayi ba tsakiyan falon duk bawon biscuits na minti
da abubuwa de duk sunci sun barshi a guri haka ta fara share share seda ta gama
kana tahada ruwan mopping ma duk tati komai ta wanke bandakin da munib ke shiga
tana gamawa ta sanar da Anty ita kuwa jin taga ma seta kwalawa Munib kira wanda
shine ɗan ta nafari daga can cikin daki ya amsa mata sanna yafito yaro ne ɗan fari
dashi yana xuwa tace ya dauko uniform ɗinsa ya kawo mata aikuwa haka yawuce ya
dauko su ya ajiye mata a gaban ta sannan ya kalli Ayra da har yanxu tana tsaye yace
'' Ayra uncle ɗinmu yabamu assignment zankawo kikoya min''toh ta amsa masa dashi
Anty kuwa banda kallon banxa ba abunda take aika musu gaba dayan su don ta tsani
taga munib yana kula Ayra
ko assignment ne tafiso ya kaiwa su Eshall toh Amma suɗinne koya kaimusu bayi
masa xasuyi ba sede ma su zagesa ita kuma ba karatun tayi ba kuma tanaso munib ɗin
yayi karatu dan tana matukar son yaron Amma shikuma duk abunda bataso shiyake so
kullum inta zauna banda hanashi kula Ayra ba abunda takeyi Amma inaa shikuma jinin
su yaxo daya yana matukar son Ayran kuma yana tausayin ta ganin yanda takeshan
wahala a gurin maman nasa, juyawa yayi ya koma ɗakin da yafito ita kuma Anty nuna
mata kayan tayi tace '' kije kici abinci sanna ki wanke min kayan nan'' kwashe
kayan tayi ta wuce wurin abincin ta tadauka zama tayi ta fara cin abincin seda ta
gama ci Sannan ta kwashe kayan ta wuce toilet din munib idan harde wanki baida yawa
anan takeyi Anty ta hana ta shiga dakin ta bataso kowa yana shiga mata daki inde
bata ciki ko gyara idan Ayra xata mata sede su shiga dakin tare ita ta xauna Ayran
kuma tayi aikin ta kuma ba ko ina take barin ta tana shiga ba, wanke kayan tayi
tass sanna tafita ta kofan baya na dakin ta shanya a saman igiyan sunada washing
machine Amma haka Anty xata ce wanke wa xatayi da hanun ta, seda ta gama tsaf
sannan tawuce part ɗinsu na yara matan gidan gaba daya wanda daga bacci sekuma idan
xatayi wanka ko wani abun ne yake kaita ɗakin Amma duk da ta dawo daga boko xata
fita se kuma idan xata yi Sallah ko wani abu sekuma dare take komawa duk ko kuma
idan ba wani abun da xatayi, shiga dakin tayi inda tasamu su Eshall duk suna kwance
kowacce da waya a hannunta kawao musu abincin su akeyi har part ɗin nasu basa fita
ita har mamaki suke bata yanda basa gajiya da danna waya wucewa tayi ta dauki kayan
ta tawuce toilet don tayi wanka sabida ta gaji gashi datayi aiki se wanka inde har
tayi aiki batayi wanka ba wani iri takeji a jikinta alwala tayi Ta shimfida Darduma
ta tada Sallah domin kuwa an kira Sallah tayi sannan ta nade sallayan ta maida shi
inda yake nan takara fita ta koma dakin Anty ta dauki wankin muhibba na kayan ta
masu datti duka tafara shi tayi wankin tass sannan ta shanya duk da kananun
shekarunta Amma haka takeyin ayyukan da duk aka sakata dawowa tayi cikin dakin ta
taras indo me aikin Anty zata daura abinci haka nan ma ta tsaya tana taya ta aikin
girkin duk da ba abunda ta'iya Amma de tana yan miko miko dan abunda ba'arasa ba
harsuka gama girkin suka jera komai akan dining table wanke abubuwan da suka bata
sukayi gaba daya suka jera shi inda yake kana ta koma ɗakinsu nan kuwa tasamu su
Marwa basa ɗakin se a lokacin ne tasamu ta gyara ɗakin nasu tashiga bandaki ma ta
wanke shi tass tayi alwala sannan tafito tayi Sallah magriba zama tayi akan salayan
bata tashiba taringa istigfari itama kuma mamanta ne ta koya mata yin hakan idan
tayi Sallah bata tashi akan darduma se tayi isha'i tsakanin magrib da isha'i bawani
rata sosai bane ne a wannan lokacin take samu tayita istigfari tana ambaton Allah
wanda hakan yanada kyau sosai seda tayi sallan isha'i sannan ta tashi ta naɗe
sallayan wuce wa tayi danufin ta kwanta dan tagaji sosai ba kadan ba yau ɗinnan
tayi aiki sosai tunda ta dawo daga makaranta bata huta ba kowani babban mutum iya
kaci ko abincin ma batajin xata iyaci sabida yanda tagaji bacci takeji gashi gobe
ma da wuri xata tashi kuma tanaso ta duba karatunta na makaranta ko xama batayi ba
sega munib ya shigo ita se alokacin ne ma tatuna da xasuyi wani assignment zama
tayi a bakin bed nata tare sukayi assignment ɗin tana nuna mishi har suka gama
sannan ya tashi ya tafi yana mata seda safe dan Anty batasan ya fita ba kwanciya
tayi akan gadon tafara sana'an nata wato tunani sabida inde har zata kebe ita daya
to bawani abun da zatayi face tunani batayi nisa da fara tunanin nata ba bacci yayi
gaba da ita sabida ta gaji sosai.... ASUBA TAGARI AYRA

DAHAKA NIMA NAKE CEWA ASUBAH TAGARI
🌹Mhizz teemah🌹

💥SAKAYYA DAGA ALLAH💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar

𝐇𝐀𝐙𝐈𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐔𝐁𝐔𝐓𝐀
🌹(Mhizz teemah)🌹

*HAZIƘAN MARUBUTA*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
Dedicated to my beloved💔Mom💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wani ko wata a

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘅𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 , 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗸𝗮𝗱𝗮𝗶
rashi ne, idan kunga typing error ko wani mistake kuyi hakuri nima xan kokarta 🙏🥰.

𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝗦 . 𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵


3️⃣
Free Page

Washe gari da asuba ta tashi bawanda ya tashe ta tariga da tasaba ko ba'a
tasheta bama tana tashi toilet tashiga ta dauro alwala tafito dadduma ta shimfiɗa
ta tada sallan asubah koda ta idar ma mikewa tayi ta gyara gadon ta sannan ta fita
a ɗakin direct ɗakin Anty tawuce tana zuwa ta taras indo me aikinta ta ɗaura girkin
safe ganin haka se itakuma ta gyaran dakin seda ta gyara ɗakin tass duk Anty tana
Bacci gashi ba shiga mata cikin daki sukeyi ba kawai seta fita a ɗakin ta wuce part
ɗin mama lokacin har haske ya fara fitowa tana shiga nan ma de kaman dakin Anty
haka ta gyara shi tawuce cikin dakin ma ta gyara komai duk Mama na Bacci koma wa
tayi part ɗin Anty ɗakin da munib yake kwana tashiga nan tasa mesa se bacci yake
sha tashin sa tayi dan yaje ya fara shirin makaranta haka ko akayi mikewa yayi ya
shiga toilet ita kuma ta fito falo lokacin kusan karfe 7:00 fita itama tayi ta wuce
part ɗinsu don tafara shirin makaranta koda ta shiga bakowa a ɗakin duk sun tashi
basa ma part ɗin gaba daya suna tashi suka wuce part ɗin Mama gyara musu bed nasu
tayi duka ta gyara ko'ina sannan ta shige toilet wanka tayi ta wanke bandakin kana
ta fito tafara shirin dan bataso tayi latti Amma tasan yanxu Anty zata iya kiranta
idan munib ya tasheta sauri sauri ta saka uniform ɗin ta tana gama shiri ta fito
tsaf da ita wucewa tayi part ɗin Anty nan tasamu an sakawa munib abincinsa cikin
lunch box zama tayi ta fara cin abincin ta ko Spoon biyu bata yiba Bus ɗin su yazo
haka ta tashi ta bar abincin suka fita tana rike da hanun munib ga lunch box ɗinsa
a ɗayan hanun haka suka fita a cikin gidan tana ta Allah Allah su tafi kafun Anty
ta tashi dan kada tace setayi wani abun Bus suka shiga suka kama hanyar makaranta
suna isa duk suka fita ko wannen su ya wuce ajin su itama nata ajin ta wuce Eshall
bata jeba da Marwa sabida ita Eshall a ss3 take kuma yanxu suna third term sune
za'a yaye Marwa kuma jss 3 zata tafi ss1 shiyasa suke zaman su se Randa suka ga
daman zuwa se suje Ayra kuma zata tafi jss1 duk de abun yazo kusan lokaci daya ne,
kofan ajinsu ta tsaya ba malami a ajin Amma seda ta yi sallama sannan ta shiga su
ashfat duk sunzo kowane harkan gabanshi yakeyi bawanda ma ya kalleta zama tayi
gurin zaman ta suka gaisa da su ashfat daganan bata kara magana ba ta dauko
litattafan ta tana dubawa Karatu suka fara har suka fita break kaman jiya yauma
haka sukaci abincin su sukadai har suka koma class aka cigaba da karatu har aka
tashi tafito tafara duba munib shida yake primary 3 ta kama hanun shi suka wuce Bus
daze maida su gida koda suka isa munib ya wuce part ɗin anty ita kuma tawuce nasu
tana shiga ta taras ɗakin gaba daya ko'ina a hargitse kan bed nasu duk kaya sunfito
dashi basu mayar ba anan bakin kofan ta tsaya tana tausaya wa kanta domin kuwa
tasan yau bakaramin aiki zata sha ba nan take idonta ya ciko da hawaye Amma haka ta
danne ta shige dakin ajiye jakanta da takalmin ta tayi sannan tadauki kayan da zata
saka tawuce toilet dashi murɗa handle ɗin toilet ɗin tayi tana addu'an shiga
bandakin ko karasa addu'an batayiba nan ma ta tsaya cak kaman an tsaida ta toilet
ɗin kota ina a wargaje duk kuma yayi datti soson wankan ta a yashe a kasa kaf
mayuka da sabulun cikin toilet ɗin suna kasa wasu babu marfi ma ga sahun kafan
mutum nan gashi a jike ko'ina yayi kaca kaca komawa dakin tayi ta ajiye kayanta
sannan ta wuce toilet ɗin tafara tattare su sabida tunda taga haka tasan acikin
sune wani yayi wanka yayi duka wannan barnan Amma bayanda zatayi haka ta tattare su
gaba daya se asannan nema ta kalli pant ɗin dayake gefe a yashe a kasa tana gani
tasan na eahall ce sabida dama itake wanke musu kananan kayansu gaba daya su harda
Anty da mama duk ita take wanke musu wanke bandakin tafara

Please Login or Register in order to submit comment