Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Ammar suna zuwa Amma shi hamshaqin tunda ya tafi sede mujisa ta waya''
Mami tayi magana cikin alhini wannan abun a ranta kuwa tana ganin ƙoƙarin yayar
tata ganin tayi 8yrs ba tare da ganin ɗan nata ba ita kam gsky inde itane bazata
iya ba,dariya Ruma tayi kana tace ''wallahi mami bakisan yanda tayi kewan suba
kullum cikin sawa kanta damuwa takeyi se ta zauna tayi ta tunani kuma nima bani da
masaniyar yaushe zasu dawo'' haka de duka ta hira bayan sun gama cin abinci ma suka
koma cikin falo inda anan ma suka ɗaura daga inda suka tsaya suna cikin haka se ga
ABBU ya shigo da sauri Ruma taje ta rungume sa tana murna shima murmushi yayi
kyakyawa ne ba laifi fari daka gansa kaga Abba wato mahaifin Ruma suna tsananin
kama sosai,

''yau kuma lelen baban ta nake gani a gidan nawa'' ya faɗa yana murmushi da
halamun mamaki akan fuskan sa,Mami ne tayi saurin cafe zancen da cewa

''wallahi fa Abbu nima nayi mamaki dan ta jima bata zoba yan zuma Ashfat ta biyu
daga makaranta'' gyaɗa kai yayi halamun gamsuwa Ashfat da ita ma ta tashi ta
rungume Abbu nata ne ta fara magana a shagwaɓe tace

''Mami Abbu shine ina dan kunga Ruma kuka share ni kaman bana gurin haba Mami haka
ake yi ne nima nasan idan naje gidan Abbi zasu ringa ɗoki kome nake so shi zasu
min'' ta ƙarashe tana yamutsa fuska halamu bata ji daɗi ba,

duk dariya suka saka harda Ruma haushi ya ƙara turniƙe ta ganin yanda suke ta mata
dariya harta miƙe zata wuce ɗaki Abbu ya jawo ta ya tsagaita da dariyan nasa sannan
yace

''haba de tilo na ba wani share kin da mukayi de yanzu de kice kinason zuwa gidan
yaya'' gyaɗa kai tayi,sake ta Abbu yayi kana yace ''toh yanzu ina Exams kuke yi
karki damu da kun gama zaki je kiyi hutu acen'' tsalle ta buga na murna nan da nan
ta fara dariya tana jin daɗi zata je tayi hutu acan da sauri Ruma tace

''a'a wallahi Abbu nine fa nace zanzo nayi hutu anan kaman ya zaka ce zata je idan
nazo dawa zan zauna kenan''

Kallon su Abbu yayi kana yace ''toh nikam yanzu duk yanda kuka yi de daga dawowa na
baku ko bari na zauna ba balle na huta kun zo kun fara damu na da hayaniya ko jakan
hanun nawan ma baku ƙarɓa ba'' da sauri Ruma tasa hanu ta ƙarɓi jakan Mami kuma
dariya tayi tace ''yoo inbanda abun ka ba dole ma su manta ba kana ganin yanda suka
cika ka da surutu kaman ƴaƴan akuu'' dariya shima yayi yana zama kan kujera me
zaman mutum biyu,Ruma ta miƙe ta fita direct wancan ɗayan part ɗin taje ta ajiye
masa jakan nasa kan kujera,dawowan ta tasamu yana kan dining Mami na saving nasa
abinci zama tayi haka suka ta hira cikin farin ciki da ƙaunan juna har Ruma ta
tashi tafiya wajen 5pm driver suka sa ya maida ta sukayi bankwana sa Asfat kan se
sun haɗu gobe a school,

🎀AYRAH🎀

Bayan ta koma gida part nasu ta wuce ta cire uniform nata tayi wanka ta shirya
cikin doguwar riga ta shimfiɗa darduma tayi Sallah bayan ta idar ta naɗe komai ta
maidashi inda yake sannan ta saka ƙaramin Hijab ɗin ta direct ta nufi part ɗin
Anty,bakin ta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa kaman yanda ta saba haka ta shiga bata
samu kowa a falon ba hakan yasa ta shige wa ɗakin Indo,tana zaune tayi tagumi ita
kaɗai tasan abun da yake damun ta tayi nisa cikin tunanin nata bata san ma da
shigowan Ayrah ba, Ayrah kuwa tsaya wa tayi tana kallon ta na wasu sakkani kafin
kuma ta taɓa ta tare da ƙiran sunan ta, fisgitgit tayi da alama ta firgita dan
kwata kwata bata ji motsin mutum ba,ganin Ayrah ne yasa ta sauƙe wani gwaron
numfashi kana ta miƙe ta fita Ayrah bata ce mata komai ba sema guri da ta samu ta
zauna gefen gadon fitan Indo ba jima wa ta dawo hanun ta ɗauke da plate na abinci
zama tayi ta miƙa mata abincin karɓa ta fara ci ita kuma Indo ta zauna a gefen ta
tana kallon ta haka kawai rayuwar yarinyar yake bata tausayi sosai seda taga ma ta
miƙe ne Indo ke faɗa mata ai su Fa'iz sun dawo jin haka seda hanjin cikin ta ya
juya ta ruɗe, nan de Indo ta kwantar mata da hankali sosai kana ta fita ta zauna a
falo,zaman ta keda wuya sega Anty ma ta shigo ko kallon Ayrah bata yiba ta wuce
wurin dining ganin komai a jere seta saka Ayrah ɗaukan kulolin ta wuce dasu ɗakin
yayun nata kowa abin da yafi so aka masa ɗakin ya Abdull ta fara shiga bakin ta
ɗauke da sallama a falo ta tsaya ganin ba kowa yasa ta ajiye kulolin a tsakiyan
falon ta wuce ɗakin, zaune yake yana riƙe da wayan sa yana danna wa yanzun dawowan
sa daga part ɗin Mama dan tun daya tashi daga bacci yawuce can ya same ta a falo
suka gaisa sama sama Mama take amsa masa shima kuma be wani damu da yanayin da take
amsawan ba dan yasan dama ita haka take bata fiye son magana ba kai ita idan da
zata samu ma zata iya jima wa bata kula kowa ba tana harkan gaban ta kawai kuma
tafi sake wa da Fa'iz ma dan ko acikin ƴaƴan ta tafi son sa shida Marwa,

Durƙusawa Ayrah tayi har ƙasa kanta a ƙasa ta gaida shi ba yabo ba fallasa ya amsa
yana kallon ta ganin yanda ta ƙara girma a idon shi, sannan tace masa ga abincin sa
a falo umarni ya bata kan ta ɗauko ta kawo masa ɗakin miƙewa tayi ta fita ta ɗauko
abincin har gaban sa ta kai ta ajiye sannan ta fara serving nasa ta miƙe ta fita a
ɗakin dan ta kaiwa ya Fai'iz nasa haka kuwa ta shiga ɗakin sa baya falo kawai seta
wuce ɗakin nan ma baya nan ga computer da ƙaramin book dayake rubutu a ciki ajiye
wa tayi ta koma falo dan tasan ƙa'idan sa, haka har ya fito tayi serving nasa nan
yasa ta shirya masa kayan sa gaba ɗaya seda ta naɗe su ta shirya masa cikin drawer
ta gyara ko ina ta fita da kwanukan daya gama cin abinci bayan takai ta ƙara dawowa
ta shiga ɗakin ya Abdull nan ma ta kwashe kulolin abincin ta jera masa kayan sa
cikin drawer daga nan ta fita haka rayuwa ta cigaba da tafiya

Kullum abubuwa suna ƙara caɓe wa Exams nasu se tafiya yake yi yayin da idan har
dare yayi Fa'iz baya kwana a gida idan yau kaji shi a club se gobe kajishi a hotel
ba inda baya zuwa shi kuma Abdull ya maida hankali kan ayyukan sa na Business a
zahirin gsky Abdull baida matsala gashi yana da sakin fuska dede gwargwado inda
Ayrah kuwa kullum cikin aiki take yi itace wankin inners ɗin Anty tayi na Mama tayi
na Eshall da Marwa tayi na yayyin nata Abdull da Fa'iz in be fita ba ko kuma aka
samu wani akasi tasha duka kullum cikin jibgarta suke yi barin ma Fa'iz ko magana
ya mata bata jiba nan da nan ranshi ze ɓaci ya cire belt ya mata ɗan banzan duka ta
inda Allah ya temake ta ma yanzu Exams suke yi zasu samu hutu toh abun zezo mata da
sauƙi dan ba zuwa makaranta Amma kuma ta wani gurin ba taso su sami hutun dan tasan
ba ƙaramin wahala zata shaba, yanzu Anty ta rage shishige wa dad tunda su Abdull
suka dawo tama fita a harkan sa gaba ɗaya Mama ne take ƙiɗan ta kuma ta taka rawa
dan kullum seta karɓi kuɗa ɗe masu mahaukacin yawa a gurin Dad kuma ya bata inta
fita tun safe kuma se dare take dawowa ba wanda yasan inda take zuwa dad baya taɓa
tam bayan ta ina ta je abunda taga dama shi take yi Anty ma sabgar gaban ta take yi
kullum tana ɗaki idan ta fito falo toh suna hira da Abdull da Fa'iz wanda suka fi
shige mata akan mahaifiyar su sun shaƙu da Anty sosai kome suke so jikin ta har
ɓari yake ta basu Eshall da Marwa tunda suka ga yayun su sun dawo suka nitsu Marwa
ta dena fitan da take yi dan tasan idan Abdull ya sani zata ji ajikin ta Amma duk
da haka seta nemi yanda zata yi su haɗu da abokan dad ko kuma idan sunzo zasu tafi
ta shige motan su gama masha ansu sannan ta fito Eshall de bata da wani magana
wayan ta kullum shine abokin hiran ta Marwa nema idan ta gaji da zama wataran take
bin Mama inda take zuwa, munib ma kullum se sunyi karatu da Ayrah da dare sannan
suke bacci,

Bangaren Ruma da Ashfat ma karatu suke ba kama hanun yaro tunda Ruma ta baro gidan
su Ashfat ta dawo Mom bata mata maganan meye sa taje ba haka de suka cigaba da
rayuwar su cikin farin ciki da jin daɗi soyayya tsakanin iyaye da ƴar tasu kullum
karuwa yake yi, inda a makaranta ma mu'amalan su da Ayrah yake ƙara ƙaruwa suna
ƙara samun relation da juna har ranan da suka gama Exams nasu aka basu hutu na ƴan
kwanaki kafun suje ƙaraban result da kuma abubuwan da zasu yi wa'inda zasu yi
abubuwa ne kawai suke zuwa a hutun kwana biyar ɗin da aka bayar suna yin reahersal
na speech nasu ciki kuwa harda Ayrah da Ashfat da kuma Ruma gaba ɗayan su,

🌹LONDON🌹
Shirye shiryen koma wansu 9j ya kan kama inda a yanzu suke lissafin saura 5days
sunyi booking Flight izuwa yanzu sun gama komai kawai jiran rana suke yi yayin da a
ɓangaren SHEED shima ya samu nasarar gane location da wa'inda yake hari suke tare
da taimakon ƴan leƙen asiri da ya saka a gurare daban daban inda suka yi normal
dressing na gida ba zaka taba gane suba sabida sunyi basaja anan ɗaya daga cikin su
yake sanar dashi inda suke hakan yasa suke zaune cikin shiri dan yana gama wannan
aikin ze koma ƙasar sa domin kuwa suma suna da buƙatan sa duk da kuwa ba ogan nasu
bane a gurin yaran shine da ya saka aiki, yanzu haka suna shirin zuwa gurin nan da
kwana biyar dan har yanzu ana bi biyan sune da take taken su ne dirar bazata suke
so suyi musu, ba wanda yakai Ajeeb son ko mawa sabida shifa harga Allah ya matsu
yagan shi a ƙasar sa yana missing Mom nasa sosai da kuma Ruma kaf cikin yayun ta
tafi shaquwa dashi haka shima yafi shaƙuwa da ita a haka suka cigaba da abubuwa
inda Ajeeb ba ƙara min sayyaya ya musu ba ita da Mom da Ashfat ƴar baffan su dukkan
su sunyi musu tsaraba sosai shide gogan kallon su kawai yake suna ɗan zama suyi
hira yanzu sosai harda dariya ma shide kawai raini ne baya so ga kuma izza da yake
dashi ko magana yake cike da izza yake yinta tafiya shima haka shifa komai nasa ma
haka yake yinsa cike da izza Amma kuma cikin nutsuwa, haka suka ci-gaba da shirya
wa daga ɓangarori daban daban..


*SE MUN HAƊU GOBE IDAN ME DUKA YA KAI MU*

*KADA FA KU MANTA WANNAN LITTAFI NA KUƊI NE AKAN NERA 300 KACAL SANNAN KAR KU BARI
A BAKU LABARI DAN BA'AYI KOMAI BA MA TUKKUNA YANZU NE ZA'A FARA AKWAI SAURAN ƘURA A
GABA, INA ME FARIN CIKIN SANAR DAKU KUMA FREE PAGE YA KUSA ƘAREWA DAN HAKA KU
HANZARTA BIYA DOMIN SAMUN CIGABAN LABARI*😊

🌹Mhizz teemah🌹


💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*
Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa ilmantarwa harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba


Wannan littafi na ƙuɗi ne akan nera 300 kacal game buƙatan karanta shi daga
farko har ƙarshe ze tura ƙuɗin ta wannan account number Hajara Abdullahi Dala
2759142010 FCMB sannan ya turo da shaidar biya ta wannan number 09060413321

Kada ku bari abaku labari wannan tafiya tazo da kafce ma banbanta masu rikita
ƙwaƙwalwa labari ne me cike da abubuwan mamaki da ban al'ajabi zallan soyayya me
ɗauke da ƙalubale kala kala makirci uwa Uba faɗakarwa ☺️
🤫gwara nayi shiru dan se
wanda ya karanta ne kawai ze gane muje zuwa ✌️✍️


Page 28_29

A yau ne su Ayrah zasu je karɓan result a kuma yaune jirgin su Ammar ya ɗaga zuwa
ƙasar su ta gado 9j, tun safe da Ayrah ta tashi aiki take yi kaman yanda ta saba
bayan ta idar da Sallah asuba ta fara gyare-gyaren ɗakunan gaba ɗaya kaman de yanda
take yi seda ta gyara part ɗin Anty tayi na Mama tayi na yayun ta maza part ɗin Dad
ne kawai bata gyara ba shi ma Mama tana can shi yasa gurin 7:50 ta gama komai nan
taje ta fara shiri zuwa school inda ta shirya cikin wata doguwar rigar les me ɗan
banzan kyau da tsada saboda abubuwa da za suyi da kuma Exams ne da suka yi na gama
primary zuwa secondary, ba tayi kwaliya ba kaman yanda ta saba sede ta saka kwali
da lipstick ƙaramin Hijab ta ɗauka launin ja kalan les nata ta saka kaman baby
hijab yake sede yafi shi girma, tayi masifan kyau pink lips nata se Shining yake yi
idon ta da ya kasan ce fari tas me ɗauke da kwayar ido baki wuluk ya yi mugun ƙara
haska mata fuska inka ganta baza ka taba cewa ita ce me shan wahala nan ba sede
kuma wani abu ɗaya har yanzu fuskan ta akwai tabon duka ga kuma shatin yatsu, tayi
kyau kaman ka sace ta ka gudu, su Eshall da Marwa sunyi wanka cire raini ba ƙaramin
kyau suka yi ba sede duk kyan su ko kwatan na Ayrah basu yi ba, sunci uban kwaliya
sun mammatse kaman sabbin arna,

Bus nasu yana zuwa Ayrah tafita cikin takun ta normal yanda take yi ta shiga a ciki
ta isko munib su kuwa su Marwa driver ze kaisu dan acewan su duk wannan wanka da
suka yi baza su shiga bus ba dan haka kaisu za'ayi, hakan kuwa aka yi domin driver
ya kaisu Time da Ayrah ta isa Ruma da Ashfat ma sun iso duk sunyi shigan su masu
kyau ba ƙaramin kyau suka yi ba haka suka jera a tare hakan kuma ya ƙara bada kala
kuma kaman abun haɗin baki dukkan su kayan su akwai ja aciki sede nata jan yafi
yawa kansu ma kusan ɗaya sede duk sun fita tsayi ita de daga yana yin halittar ta
ma baza a kira ta guntuwa ba haka baza ace mata doguwa ba, haka suka wuce har cikin
class nasu duk inda suka gifta se'an bisu da ido sabida yanda suka yi kyau over,

A cikin class ɗin suka tarar da Mr Richard su kawai ake jira duk wa'inda zasu yi
abun suna class ɗin, zuba musu ido yayi yana ganin baiwar kyau da suke dashi yanda
ya ƙure Ayrah da ido duk se taji wani iri seda suka fara gyashe sa sannan ya an
kare fita yayi daga class ɗin su kuma suka rufa masa baya duk cikin su ba wanda
yazo da jaka iya karami suka riƙe kowa kalan kayan sa, filin makarantar suka nufa
inda izuwa yanzu har an fara cika anyi decorating gurin yayi masifan kyau kujeru
sunfi ɗari a gurin, gurin da aka tana da dan masu presentations ya kaisu duk suka
zauna ga sauran ɗaliban ajin su a gefe guda wa'inda ba abunda zasu yi gurin 9 aka
fara taron


time ɗin su Marwa sun zo tare da Anty da Mama harda Dad da Abdull Fa'iz de bezo ba
duk da kasancewar Ayrah ta gansu Amma bata nuna ba dan tasan cewa ba zuwan ta suka
yi ba shiya sa ko kaɗan bata damu ba ko su Ruma bata faɗa wa ba,

Ruma kuwa se zuba ido take tana son taga ta ina Abba da Mom zasu bayyana Amma shiru
har Yana yin ta ya fara sauya wa duk da ba'a iso kansu ba,toh a gurin Ashfat ma
haka yake ta zuba ido Amma shiru har wannan lokacin ita de Ayrah ko ajikin ta,

Can kaman ance Ashfat ta ɗaga kai kawai seta hango Abbu yana shigo wa aikuwa murna
kaman taje ta rungume shi haka taji, gurin da aka tana dar dan iyayen student ya
zauna yana ɗaga kai suka haɗa ido ya sakar mata murmushi ita ma ta mayar masa da
martanin hakan a ƙasan zuciyan ta kuwa tana mawa kanta tambaya ina Mami kode baza
tazo bane, se kawai ta share maganan,

Ruma de se raba ido take Amma bata ga kowa ba har aka kira sunan Ashfat,

ASHFAT HABIB DAULA aiko dajin haka Ashfat tayi saurin tashi da yake ita spelling
zata yi haka ta fito ta tsaya a gurin da ake tsayuwa tayi gaisuwa kaman yanda ake
yi ta kuma ƙara faɗin sunan ta sannan ta faɗi abunda zata yi (duk da Turanci tayi
hakan) sannan ta fara spelling duk wani word da aka tambaye ta ba ƙananun word bane
kuma manya ne jiga jigan ne haka ta ringa amsa su tsaf Amma me tana zuwa na ƙarshe
seta carke inda aka tambaye ta VETERINARIAN (Likitan dabbobi) a gurin Rian ɗin ta
carke tayi tayi ta ɗago shi Amma yaƙi daga ƙarshe de seda ta koma daga farko aka
ƙara maimaita mata nan ne tayi ƙarshen take aka hau mata tafi ita kuma ta koma ta
zauna kuma an mata liƙi sosai saboda tayi ƙoƙari sosai, tana zama ta sauƙe wani nan
nauyan ajiyan zuciya tana hamdala a cikin ranta Abbu ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin
yanda tilon ƴar tasa tayi ƙoƙari sosai dan yana ɗaya daga cikin wanda suka mata
liƙi murna sosai take yi kuma yaji haushin rashin zuwan Mami duk da kuwa cewa aki
take yi shi yasa ya wakilce su duka,

RUMAISA'U SULTHAN DAULA suka ji an faɗa hakan yasa Ruma saurin tashi ta miƙawa
Ayrah hand bag ɗin ta kana ta shiga filin jikin ta a sanyaye dan gani da tayi ba
wanda yazo mata, gabatar da kanta tayi ta kuma faɗi abunda zata yi Sannan tayi
shiru tana jiran a tambaye ta ta bada amsa ɗaga kan ta tayi da nufin ta kalli Abbu
ko zata ji kwarin gwiwa kawai se tayi turus ganin ya Ammar da ya Ajeeb, murmushi
suka sakar mata gaba ɗayan su Ajeeb ya ɗaga mata gira ɗaya irin yane, da sauri ta
kawar da kanta tana jin wani irin ƙwarin gwiwa yana zuwa mata nan da nan aka fara
tambayan ta tana bada amsa har ta gama ta shiga speech tayi ƙoƙari sosai bata carke
ko sau ɗaya ba hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi wa yayin nata ba dama su Ayrah sun
mata liƙi kam sosai kuma sun ji daɗi har ta gama ta koma ta zauna inda take aka
bita da tafi rungume juna suka yi se murmushi take yi dan tunda ta gama seta ji
wani daɗi gashi bata yi mistake ko ɗaya ba,

AYRAH BEDARUDEEN KAISAM jin an ƙira sunan ta yasa ta miƙe cikin sanyi da nitsuwan
ta ta isa inde aka tana da domin su toh ita de abu uku zata yi dan kaff abubuwan da
class nasu zasu yi perticipating zata yi, cikin nutsuwa ta gabatar da kanta da
abubuwan da zata yi nan aka fara tambaya tana ansa wa taron dubbani mutanen duk
anyi shiru ana sauraran dadda ɗan muryan ta inda take spelling duk wani word da aka
faɗa mata dalla dalla bako tsoro ballan tana fargaba, haka ta gama sanna ta ƙara
gaba tar da kanta a talk show nan ma ta fara tun ba'aje ko ina ba manyan mutane
suka fara mata kyauta ganin yanda yarinya ƙarama take zubo karatu kuma me amfani
sabida magana take yi akan gomnati da abubuwan da ake fama dasu yanzu idan take
cewa inda ita ce a wannan muƙamin ga abubuwan da zata yi da kuma matakin da zata
ɗauka, nan da nan jikin manyan ƙasan wa'inda yaran su suke makarantar yayi sanyi
wannan abubuwa da take faɗa wanda ita ma sir Richard ne ya bata a rubuce ita kawai
karanta wa take yi already yana kanta ta samu kyau tuttuka da dama kafin ta gama
yarinyar ba ƙaramin burge muta ne tayi ba ciki kuwa harda Ajeeb da Ammar sunji
matuƙar daɗi ta kuma burge su ganin yanda take zuba turanci me ma'ana, Abdull ne
kawai ya tashi ya mata liƙi dama shi ɗan ba ruwan kane ba ruwan sa da abubuwan
mutane sede kuma kowa na ciki na ciki a ƙasan zuciyan sa ji yake dama ace Marwa ne
ko Eshall tayi wannan abun,

Toh a ɓangaren dad da Anty kuwa dad de a ƙasan zuciyan sa ji yake yi kaman ya tashi
ya rungume ƴar tasa Amma kuma baze iya ba yaji daɗin yanda yaga tana ƙoƙari Amma
baze iya nuna hakan ba ( toh ko meye sa dad baze iya nuna hakan ba? Mhizz teemah ce
kawai zata iya warware muku komai) toh Anty ma de haka ne taɗan ji daɗi yanda taga
yarinyar tayi ƙoƙari toh kuma de kunsan dama ita Anty tana son karatu sosai barin
ma daya kasan ce ita bata yi karatun boko ba, shiya sa da taga yanda yaran suke yi
taji ya burge ta har tana jin ina ma ace Munib ne yake wannan karatun toh Amma fa
wani mugun haushin Ayrah ne taji ya ƙara nin kuwa mata a ƙasan zuciya tsanan tane
ya ƙara mamaye zuciyan ta, Mama kuwa ko ajikin ta dan harkan gaban ta ma kawai take
yi kaman bata san me ake yiba, Marwa kuwa da Eshall baƙin ciki kaman su shaƙe ta
suke ji barin ma da suke ga Abdull ya mata liƙi haushi kaman su mutu more
expecially Marwa da ta cika ta batse da baƙin ciki gashi kuma su ba wani abun da
zasu yi nan da nan haushi ya ƙara turnuƙe su take kuma Marwa ta fara dana sanin ta
kura wa su dad akan se sun zo se yanzu nema take ganin shirmen da tayi suda ba wani
abu zasu yi ba toh meye na zuwan su Mama iya result nefa za'a basu tana cikin
tunanin se kuma wani tunani ya faɗi mata toh ai ita ce zata zo na ɗaya a ajinsu
tuna hakan yasa ta yin murmushi Amma duk da haka taji haushi yanda Ayrah take zuba
karatu,

Seda ta gama koma daga ƙarshe tayi musu godiya ta koma inda ta tashi (karku manta
duk abinda tayi da turanci tayi shi) tun kafin ta ƙara sa su Ruma da Ashfat suka
taso da ɗan gudun su suka rungume ta dan su kansu ba ƙaramin burge su tayi ba Abbu
kanshi yarinyar ta matuƙar burge sa, ƙara sawa suka yi suka zauna Ayrah ta faki
idon su ta share ɗan gutun ƙwallan da ya tarun mata a ido tana ji ina ma ace Maman
ta tana raye,

Da sauri ta kawar da tunanin dan yanzu zata iya fara kuka shiru aka yi ana jiran
fito wan sakamako da kuma result da za'a raba dan dama Ayrah ce last daga ita an
gama se raba kyauta wa'inda suka yi ƙoƙari....

Manage This

💥THE BEGINNING 💥

🌹Mhizz teemah🌹


💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*__________________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*

*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*_______________________________________________________*

Dedicated to my beloved ❤️Mom 💋

Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰


Littafi ne me cike da faɗakarwa ilmantarwa harma da nishaɗan tarwa,ƙirƙirarren
labarine

Please Login or Register in order to submit comment