Reading SAKAYYA DAGA ALLAH BOOK ONE BY FATIMA IDRIS UMAR Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matuƙar son musa kaman ransu shi ɗaya Allah
ya basu,sunyi farin ciki samun cikin da matar baba malam tayi ranan da ta haihu ta
samu ɗa namiji lokacin har su Maryam da musa sun koma gidan su da me gari ya basu,
ataƙaice de anyi sunan yaro baba malam ranan suna yaci Abubakar Amma sadiqu suke
kiran sa dashi ita kuma maryam ciki ya fito ɓaro ɓaro ba karamin murna musa yayi ba
tasamu ɗa namiji yaci suna ibrahim haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiqu ya girma
kusan sa'ani suke da Ibrahim shekara 2 ya basa shiyasa suka taso tare
🌹TEN YEARS AGO🌹
Wannan lokacin maryam yaran ta Uku duka su maza Ibrahim shine babba se Usmanu se
Kabiru suna rayuwa cikin kwanciyar hankali ranaku suna komawa kwanaki kwanaki suna
komawa satuttuka haka sati yana komawa wattani watani na komawa shekaru har aka
ɗebe shekaru dayawa Ibrahim yayi aure Usman ma yayi Aure kabiru duk sunyi aure inda
matansu suke zaune a cikin gidan nasu sabida gidan yanada ɗan girma ɗakuna 4 ne
acikin gidan haka suna zama cikin aminci da kwanciyar hankali ba wani matsala
maryam kuma tanada ciki haihuwa yau ko gobe bata aikin komai girki sede suyi su
kawo mata bata komai sadiqu kuwa har a wannan lokacin baiyi aure ba tun baba malam
na magana har ya haƙura yayi shiru inda sadiqu yayi sauƙan Alqur'ani yafi a ƙirga
dan shima yanzu ya koma koyar wa duk wani abubuwa da mahaifin sa ya keyi duk ya iya
su bada magani karya sihiri dade sauran su, ranan kwatsam se Maryam ta haihuwa inda
ta samu yarinya mace malam musa yana gona aka je aka gaya masa duk suna matukar son
yarinya suna kuma ji da ita ranan suna yarinya taci suna A'isha haka rayuwan su ya
cigaba da tafiya cikin jindaɗi da kwanciyar hankali har matan yaran su maza suka
haihu daga nan kuwa sunan su ya canja jikokin nasu suke kiransu da inna (Maryam)
shi kuma Musa suna kiranshi da (Malam) har sunan ya bisu ya zama na kowa ma haka
yake kiransu dashi yau da gobe ba wuya suna nan A'isha de batayi Aure ba har su a
lokacin takai kusan shekara 20
Amma ba Aure iyayen sun shiga damuwa sosai ganin su a kwauye duk wacce takai
wannan shekarun yana wahala tasamu wanda zece yana sonta toh hakane ya faru da
Aisha Amma ita bata ɗaga hankalin taba komai na Allah ne ta barwa Allah komai har
yaran yayinta duk sukayi aure ita ɗaya ta rage a gidan duk yaran sunyi Aure har a
wannan lokacin kuma bata nuna damuwanta ba don ita gani take yi tunda ga kawunta ma
har yau beyi Aure ba kuma be ɗaga hankalin sa ba shida a yanzu yakai kusan shekara
Arba'in da wani abu shiyasa itama tabarwa Allah komai gidan yarage daga ita inna
malam se kuma su hafsatu matar Usman da zainabu matar Kabiru da Maryam matar
Ibrahim
haka suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki baba malam kuwa har a wannan lokacin
yana bada magani sannan yana koyarwa ya tsufa sosai haka me gari duk sun tsufa Ana
haka wata rana kwatsam suka tashi basuga A'isha ba tashin hankalin da ba'a samasa
date sun shiga damuwa marar misaltuwa kuma sunyi neman duniya Basu ganta ba tun
suna tsammanin zata ganin ta tadawo har dare yayi ranan inna seda takusa ɗan
karamin hauka tana matuƙar son ƴar tata su Abu (Zainab) ne masu kwatar mata da
hankali kaf faɗin dukku ba'inda basu zagaya ba Amma shiru basu ganta ba sadiqu ba
ƙaramin tashin hankali ya shiga ba dan harga Allah yana matuƙar son A'isha kawai de
be nuna mata bane tun suna damuwa duk garin Allah idan ya waye sesun zaga nemanta
har cikin Gombe sadiqu ya shiga neman ta Amma babu ita ba labarin ta haka suka
hakura suka miƙa kukan su ga me duka kuma suna mata addu'a kullum duk inda take
Allah ya tsare ta ya kareta da iyawar sa a wannan lokacin ne kuma suka gane sadiqu
na sonta don har rashin lafiya seda ya kwanta ba ƙaramin haushi rashin faɗan da
yayi sukaji ba tun kafin lokaci ya kure musa Amma yanzu kam suma basu san inda take
ba balle har ayi maganan ɗaura musu Aure sun dukufa yi mata addu'a ba dare ba rana
tafiya tayi tafiya har suka dena damuwa suka cire abun ma a ransu gaba ɗaya amma
har lokacin suna mata addu'a wata rana Malam ya tafi gona da maraice yana cikin
aikin sa kawai se yaga wata mata tana ba babba sosai bace dan bazata wuce 30yrs ba
tana tafiya kaman bata cikin hayyacin ta har ya share ta ya cigaba da aikin sa
kawai yaji faduwar abu daga kanda zeyi seyaga ashe wannan matar ne ta faɗi dayake
akwai shi da tausayi se ya karansa inda take ya fara magana ''baiwar Allah lafiya''
Amma me se yaji shiru gashi kuma idonta a rufe haka ya karaci maganan sa dayaga
de kaman bata san ma yanayi ba se kawai ya bar aikin da yake yi ya koma gida anan
ya gayawa su Inna abunda yake faruwa haka suka rufo mayafin su da inna da Abu suka
tafi tare da shi don suga meyake faruwa nan kuwa suka ganta kamar yanda Malam ya
barta a gurin abuda Inna suka kamata da kyar suka daga ta gida suka wuce da ita don
su taimaka mata sabida sude basu santa ba kawai de tausayi da suke dashi ne yasa
zasu taimaka mata suna isa gidan tabarma inna ta shimfida kana suka kwantar da ita
ruwa suka fara yayyafa mata
Amma shiru kake ji bata ko motsaba suka ci-gaba da yayyafa mata ruwa daga karshe
de dasuka ga bata farfaɗo ba se suka ƙara ɗaukan ta se gidan baba Malam koda suka
je gidan kallon farko da yayi mata ya gane sihiri ne a jikin ta haka ya duba ta
Amma yakasa gane komai akan ciwon nata inbanda sihiri kawai da yagane Amma ya rasa
ta hanyar da ze warware domin ba karamin sihiri bane a jikin ta haka ya karaci dube
duben sa Amma ina ba abunda ze iya kawai ya mata ba tareda tunanin ze mata aiki ba
juya kanta tayi seda yayi kara katt kana kuma ta dawo dai-dai daga haka kuma bata
kara motsawa ba tun daga haka baba malam ya gane bafa aiki haya ƙin nan ze mata ba
shiru yayi yana nazari tukkuna ya fara tambayan su a ina suka samo wannan baiwar
Allah malam musa ne ya fara bashi labari daga inda ya ganta har zuwa yanzu da suka
kawota gurin shi kaɗa kai yayi alamun ya fahimta kana ya fara magana kamar haka
''wannan matar asiri a ka mata kuma akwai miyagun aljanu a jikinta nide kam bazan
iya mata komai dan duk abunda zan mata bazeyi tasiri a jikin ta ba Amma inaso ku
zauna da ita ku kula da ita sosai dan yanzu idan kuka barta bakusan ina zata je ba
zata shiga hannun na gari ko na banza dan haka zanyi magana me gari yasan da zaman
ta'' amsa masa kawai sukayi da toh kana suka wuce da ita gidan su a inda suka
kwantar da ita ɗazu anan suka kwantar da ita yanzu ma ba bakin cin abinci bare na
ruwa marabanta da gawa numfashi ne kawai farace kyakyawa tanada ƙiba kaɗan ga tsayi
tana sanye da doguwar rigar atamfa ɗan uban su daga yanayin ta kawai ma kasan ba
ƴar kananan mutane bane Amma batasan ma inda kanta yake ba haka suka cigaba da riƙe
ta a gurin su sun ɗauke ta kamar Aishan su da ta bata basu san inda take ba suna
kula da ita sosai Amma bata cin abinci iya kacinta ruwa shima se an ɗura mata kanta
a sama wani na shiga cikin wani kuma na fita hakade kaman matacciya haka suke
rayuwa.
WANNAN SHINE ABINDA YA HAƊA SU DA MATAR NAN DA KUMA ASALIN SU

'''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''
✨LONDON✨

*SEMUN HADU GOBE IDAN ME DUKA YAKAIMU COMMENTS LIKE AND SHARE FISABILILLAH*
🌹MHIZZ TEEMAH 🌹📝
09060413321

💥SAKAYYA DAGA ALLAH 💥
Story & writing
By
Fatima Idris Umar
🌹(Mhizz teemah)🌹
*______________________________________________________*
💋💋HAZIƘAN MARUBUTA 💋💫
*HAZIƘAN MARUBUTA.*
*Marubuta ne masu tafiya da salon zamani tare da koyarwar addinin musulunci,
haziƙai ne kuma jajirtattu wajen fito da labarin da zasu wa'azantar ya faɗakar,
ilmantar tare da nishaɗantarwa.*
*______________________________________________________*
Dedicated to my beloved💔 Mom 💔
Wannan shine littafina na farko Please idan yayi dede da rayuwar wata ko wani

𝗖𝗼𝗺𝗺𝗲𝗻𝘁𝘀 𝗱𝗶𝗻𝗸𝘂 𝘀𝗵𝗶𝗻𝗲 𝘇𝗲 𝗸𝗮𝗿𝗮𝗺𝗶𝗻 𝗸𝘄𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗴𝘂𝗶𝘄𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗵𝗮𝗻𝘆𝗮𝗿
toh a rashin sanine,sannan idan kunga mistake or typing error kuyi hkr 🙏🥰

𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘅𝗲𝘀𝗮 𝗻𝗮𝗴𝗮 𝘆𝗮𝗻𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗸𝗮 𝗸𝗮𝗿𝗯𝗶 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗵𝗮𝗿𝗲 𝗳𝗶𝘀𝗮𝗯𝗶𝗹𝗶𝗹𝗹𝗮𝗵

GARGAƊI!!!!!!!
*Ban yarda ba, ban amince wata ko wani suyi amfani da wani sashe daga cikin
littafina ba ta kowace siga,ban yarda a karanta min shi a YouTube ba, ko a haɗa min
document duk wacce tayi hakan ko yayi hakan koda Allah nabar mutum se ya bi min
hakki na!!!!

Free page 12_13

*✨LONDON✨*
Tsaye yake a gaban miro ɗaure da towel yana gyara gashin kasa da yake ɗigan
ruwa da alama daga wanka ya fito gshin kansa kaman na wata mace domin kuwa tsayin
gashin shi har kafaɗan sa yana tabawa kuma yanada cika se yalƙi yake yi yana ɗaukar
ido duk da yana ɗan ɗigar ruwa yanada laushi ga santsi cikin nutsuwa yake busar da
gashin da hand dryer yanada faffaɗa kirji duk da be juyo ba ga damtse da yake nuni
da yana gym sosai fari ne tas yana da tsayi sosai kuma tsayin ba karamin kyau yayi
masa ba
daga ƙasa kuwa kafan sa me kwance da kyakyawan suma sun kwanta sunyi luff yana
sanye da slifas irin na ɗaki masu ɗan uban tsada kallo ɗaya zaka musu kasan ba irin
normal wanda wasu ke sawa bane ga farcun kafan sa gwanin burgewa kaman wanda bai
taba taka ƙasa ba
seda ya busar da gashin nasa kana ya ɗauko wasu mayuka masu shegen kamshi ya fara
shafawa gashin nasa ai dama daga ganin yanda gashin nan yake yalƙi ga daukan ido ba
Ƙaramin gyara yake samu ba yana kashe wa gashin nasa maƙudan ƙuɗi tsaf ya gama
shafe shafen sa ya fesa body spray na maza me ɗan karan daɗi kana ya juyo dan ya
wuce dressing room
Subhanallah hakiƙa tsarki ya tabbata ga uban gijin talikai me yin yanda yaso da
bawan sa wannan bawan Allah ko dakan shi akace ya ƙera kansa baze yi kyawun da yake
dashi yanzu ba, yana da dara daran idanu masu ɗaukar hankali da tafiya da hankalin
'yan mata har wani yalƙi maiƙo maiƙo farin cikin idon yake yi kaman wanda hawaye ya
taru a idon gashi daga wanka ya fito se idon ya kara wani irin kyau yana sheƙi
kwayar idon sa blue color ne kuma ba ƙaramin ƙara masa kyau yayi ba hanci sa yanada
tsayi ɗan daidai gashi a tsaye yanada faɗi kaɗan bakin shi ɗan karami gashi pink
sosai kaman yana shafa wani Abu cikin sa kaman bai taba saka abinci a ciki ba ga
six pack dasuka fito rass sabida gym da yake yi ga suma da yake kwance a faffaɗar
kirjin sa baki wuluk a dede tsakiyan kirjin nasa ɗan kaɗan hakan ba karamin kyau
yayi masa ba gashi suman ɓaki wuluk har Shining yake yi
Duk inda namiji yakai Akira sa cikkaken namiji toh ya kai shi dan yatara komai da
komai na cikakkun maza ba macen da zata ganshi ta kauda kai bata kara kallon saba a
shekaru baze wuce 30 years ba direct ya wuce dressing Room nasa ko fofi biyu ne a
gurin suna manne da juna toilet da dressing Room
se sannan nema naga yanda tsarin ɗakin yake ya haɗu iya haɗuwa yana ɗauke da
tamfatsetsen bed me ɗan karan kyau ga laushi shumfiɗe da milk color bed sheets da
ratsin brown a jiki headboard na gadon ma milk color ne ya haɗu iya haɗuwa shi
kansa ɗakin abun kallo ne ko ina tass tass ba datti da wuya idan za'a samu ko
tsinke a wannan gurin da alama ma mallakin gurin yana da tsafta sosai ɗakin yanada
girma sosai akwai carpet a tsakiya ɗakin haɗe da Center table milk color me ɗan
uban kyau idan nace zan tsaya kayyade muku yanda kyan ɗakin yake se page ɗin nan ya
kare alkalamina be gama rubutun ba ku kiyasce ya kuke tunanin kyawun gurin,
Kofan dressing Room ɗin ya buɗe wani irin daddaɗan kamshi ne me tafiya da hankali
ya karaɗe ɗakin zuro kafan sa na dama ya fara kana ya fito gaba daya masha Allah
sanye yake da kakin sojoji Black color manya manya shugabani na sojoji ne kawai
suke saka black ɗin ba karamin kyau yayi ba ya fito rass baza ka taba tunanin shi
ba ɗan ƙasar bane yasa jacket a saman kayan shima Black yayi kyau sosai se tashin
kamshi yake yi ya ɗaure gashin kansa ta kasa kana yasaka hulan soldiers gashin
yaɗan fito ta ƙasan hulan hanun sa ɗaure da danƙareren agogon Rolex ɗan uban su ya
manna sun glass a idon sa duk wacce tayi arba da wannan kyakyawan halitta seya tafi
da imanin ta maza ma ƴan uwan sa neman hanyar da zasu samu daman magana dashi suke
yi sabida yanda yake da shiga rai zama yayi a bakin bed nasa ya ɗau wayan sa me
masifan kyau ga kuɗi ya fara dannawa turo kofan shiga ɗakin aka yi Amma ko gezau
beyi ba balle har yaga waye ya shigo yana nan a yanda yake wani kyakyawan saurayi
ne ya shigo sanye yake da short iya gwiwa da White T-shirt fari ne tass baze wuce
28 years ba zama yayi a bakin bed ɗin kana ya fara magana
''SHEED wai meyesa kake haka ne kai kaɗai suke jira tun ɗazu MASH yace min by 10
kuna da meeting yau Amma yanzu har kusan 11 Amma baka fito ba kasande jiran ka
ake yi tun ɗazu ko yanzun ma daka gama abunda kake yi seka zauna haba Sheed''
yakara sa maganar yana mikewa tsaye
ko kallon shi Sheed beyi ba kaman ma besan da wanzuwar mutum a gurin ba ya cigaba
da danna wayan sa seda ya gama abunda yake yi kana ya miƙe beyi magana ba niko nace
kode kurma ne kam ko kuma yana ciwon baki,wuce wa yayi ya fita daga ɗakin wayan sa
kawai ya ɗauka girgiza kai kawai Ammar yayi kana yabi bayan sa a ranshi yana cewa
inde sheed ne baze taba canzawa ba,
gidan yana da girma sosai ya tsaru ba laifi yana ɗauke da 3 bedroom a sama 3 a
kasa, koda ya fita be ganshi a falon sama ba hakan yasa shi sauƙa kasa anan ya
ganshi a tsaye waya manne a kunnen sa da alama waya yake yi ga kuma wani saurayi
zaune kan daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun ɗakin a shekaru baze wuce 26
to 27 ba kyakyawa ne yana sanye da short shima su biyun duk ƙwayar idon su baƙi ne
Sheed ne kawai yake da kwayar ido blue hakan yasa ya kara fitowa kaman ba bahaushe
dan Nigeria ba,
computer yake danna wa yaji saukowan mutum ɗago kanshi yayi ganin Ammar ne yake
sauko wa se yace ''kasamu ya fito kenan'' yayi maganar yana dariya ba ƙaramin kyau
ya kara ba da yayi dariyan wanda ya kira da Ammar ɗin yana karaso wa cikin falon
zama yayi kusa shi yana hara ran sa yace ''ai kabar yaya Deen ɗin nan wallahi kana
gani tun ɗazu Mash yake ta zirya daga falon nan zuwa waje'' daga yanayin yanda yayi
maganar kasan ransa ya ɗan ɓaci ƙara tun tsurewa Ajeeb yayi da dariya yace ''can
muku nide ba ruwa na''
gyara zaman sa Ammar yayi a cikin kujeran kana yace ''ni wallahi ma na gaji da
zaman ƙasar nan nayi kewan Mom over'' ya faɗa yana ya mutsa fuskan shi ''seriously
nima nayi kewan ta sosai'' ai Ammar yana jin haka ya miƙe zaune cikin zumuɗi ya
fara magana ''toh kaga kawai se mu tafi mu bar shi tunda mukam mun gama namu
karatun har kuma mun samu aiki a 9j'' gyaɗa kai Ajeeb yayi kana yace ''hakane kuma
kaga Already ni dama computer na karanta kuma nayi komai har na samu aiki a kaima
kuma kasuwanci kake ko yanzu kake so zaka iya tada naka inde kamawa Dad magana''
haka suka ta hiran su suna muhawara akan yaushe zasu koma,
Sheed kuwa seda ya gama wayan sa kana ya fice shima ko kallon su beyi ba yayi wuce
wansa beyi sojojine a zagaye da gidan ta ko ina yana fita suka fara sara mishi ko
sannu bece musu ba Mash kuwa da shima tsaye yake yana jiran fitowan sheed ɗin ganin
sa yasa ya buɗe masa marfin wata dan kareriyar mota me numfashi launin baƙi na
tsakiya mota biyu a gaba biyu a baya wanda ya buɗe masa kuma na tsakiya sauran na
sojoji ne,
yana zuwa shiga kawai yayi bece komai ba sauran sojoji ma duk shiga motocin su suka
yi kana sukayi gaba motar daya shiga kuma tana tsakiya Mash ne a seat ɗin gaba kusa
da Byron da yake driver seat shima da kakin sojoji a jikin sa get man ya buɗe musu
get suka fita da wani irin speed suna sakin jiniya,
Ajeeb da Ammar ne kawai suka rage a gidan se get man dakuma masu kula da gidan da
suka kasance suma duk sojojin ne masu jini a jika sunkai 7 fararen fata,
Sheed kuwa koda suka fara tafiya Mash ya juyo kyakyawan bature ne fari tass baze
wuce 25yrs ba barka da safiya ya masa be amsa ba hasali ma kwantar da kansa yayi
ya lumshe idonsa masu ɗauke da zara zaran gashin ido ya nutsa cikin kujeran sanyin
AC na shigan sa me haɗe da daddaɗan turaren sa daya karaɗe ko ina lokacin kusan
karfe 11 na safe Mash duk yabi ya ɗaga hankalin sa kan suyi sauri tun karfe goma ya
kamata ace sun isa gurin taron nan Amma yanzu har kusan sha ɗaya yasan yanzu su
kawai ake jira shikuwa gogan ko ajikinsa kuma duk shine silan makaran su Amma ko
damuwa beyiba,
Suna isa wajen Aikin nasu packing suka yi kana duk sojojin suka diddiro suka zagaye
motan ogan nasu suna jiran fito wansa fitowa Mash ma yayi ya zagayo ta inda yake ya
buɗe marfin motan Amma beyi magana ba shi kuwa seda ya mula kana ya ware dara daran
blue eyes nashi zuro kafan sa na dama ya fara yi seda ya mula kana ya zuro da ɗayan
ma duk sojojin dake wurin sara masa suka yi harda Mash kana suka yi kasa da kansu
rufe motan Mash yayi kana suka rufa masa baya a bakin hole da suke yin taron na
manyan shugabanin su suka tsaya yayin da shi kuma ya shige hole ɗin bakinsa ɗauke
da excuse can kasan makoshi sauran sojojin kuwa tsaya wa suka yi harda Mash ga
wurin a cike da sojoji da alama wani babban taro suke yi yanda kowa ya halarci
wajen,
Tunda ya shiga wajen kamshin turaren sa ne ya fara kaiwa mutanen gurin hari yana
kuma yi musu sallama duk dagowa suka yi suna kallon sa su biyar ne a gurin se shi
daya shigo yanzu suka zama su shida, shikuwa tunda ya shiga be ɗaga kai ya kalli
kowa ba ya karasa gurin kawai yayi kafun ya zauna seda ya sara musu gaba ɗayan su
kana ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun gurin be damu da cewa akwai wa'inda
yafisu matsayi ba abunda yake gaban sa kawai yake yi wayan sa ya ɗauka ya fara
aikin dannawa tun daga sara musu da yayi be ƙara wani abun ba banda wayan sa da
yake dannawa gyaran murya babban cikin su yayi kana ya fara magana kamar haka ''
tun karfe 10 muka shirya wannan taro Amma se yanzu gurin 11 kake zuwa yanzu de
lokaci ya ƙure mana banda lokacin jin korafin ka Amma idan mun tashi daga taron nan
kasa meni a Office''
duk wannan magana da yayi cikin harshen turanci yayi shi gyaɗa kai kawai Sheed yayi
bece komai ba dan yasan dashi yake kansa a ƙasa Amma yabar danna wayan da yake yi
sauran mutanen gurin ma duk shiru suka yi dukkan su ba musulmai bane shi ɗaya ne
musulmi a cikin su hakan kuma be dame shiba baya shiga shirgin da bana saba ogan su
ne wato THE GENERAL OF THE ARMY tsoho ne ya ɗan manyan ta kaɗan ze kai kusan 50 to
52 years magana ya fara cikin harshen Turanci kaman haka,
''ba komai ne ya tara mu anan ba face karin matsayi da nakeso na yiwa wani daga
cikin ku kuma ba komai yasa hakan ba se jajircewan sa akan aikin sa kuma ba kowa
bane wanna face RASHEED'U'DEEN DAULA'' ya kai ƙarshen maganar sa yana zubawa
mutanen gurin ido sabida yaga yanayin reacting ɗin su,da wani irin sauri duk suka
ɗago kansu zuwa ga ogan nasu suna kallon sa wasu daga cikin su fiskan su a murtuƙe
wasu kuma annuri ne kwance akan fuskan su shi kuwa gogan ko gezau beyi ba kai ko
alamun ma yaji maganan da ake yi be nuna ba, be jira jin abunda zasu ce ba ya ci-
gaba da magana '' Rasheed'u'deen Daula'' ya kira sunan shi se a sannan ne ya ɗago
kansa yana kallon ogan nasu nan ma bece komai ba nisawa yayi kana ya ɗaura da faɗin
''Sabida yanayin jajircewan ka akan aikin ka da kwazon ka da kuma yanda kake aiki
da ƙwaƙwalwa wajen gudanar da duk wani binciken ka yasa nake me farin cikin sanar
da kai cewa daga yau kaine sabon MG MEJOR GENERAL ''
Mikewa Sheed yayi ya juya gare sa ya sara masa kana cikin wani irin Voice me daɗi a
kuma dake camly ya furta ''yes sir'' daga haka be kara cewa komai ba kuma be zauna
ba yana tsaye a kamen da yake gyaɗa masa kai ogan nasu yayi kana yace ya zauna se
sannan ya zauna be kuma ƙara cewa komai ba kallon sauran jama'an hole ɗin ogan yayi
kana yace ''akwai me magana ko karin bayani'' ya tambaya yana kallon su mutum ɗaya
daga cikin sune ya ɗaga hannu kana yace'' inada magana ranka shi daɗe'' gyaɗa masa
kai yayi kana yace ''zaka iya yin maganar ka''
mikewa tsaye yayi babba ne shima ya ɗan tasa kaɗan a shekaru baze wuce 40 years ba
magana ya fara kamar haka ''Sir Amma ni agani na kaman hakan be dace ba sabida
yanayin Aikin sa kasan de yace shi ƙasar sa yake so yayi wa aiki toh akan wani
dalili kuma zaka bashi wannan wannan muƙamin shida ma ya kusa komawa kasar su kuma
ƙabilan sa daban hakan maa ai baze taɓa yiwuwa ba''
ya ƙarasa maganan a ɗan hasale da alama abun ya ɓata masa rai sosai ko kallon shi
Sheed beyi ba dama kuma already yasan hakan zata faru ogan nasu ne ya kalle shi
kana shima ya fara magana kamar haka ''cancanta da naga yayi ne yasa na bashi
wannan matsayin duk da sanin cewa ya kusa barin ƙasar kuma yana da burin sa na
ganin ya temaki Ƙasar sa yayi musu aiki tuƙuru kaman yanda ze yi aiki a Kasar sa
haka zeyi a wannan ƙasar ma kuma wannan muradi nasa shiya ƙara nuna min shiɗin yana
kishin ƙasar sa kuma ze tallafa musu ko ya koma ƙasar sa inaso kasani LG yanada
ikkon yin duk wani abun da yaga dama a wannan ƙasar wannan dama ce nabasa''
ya kai ƙarshen maganan sa ciki nuna tabbacin abunda yake faɗa tsaye LG yayi yana
kallon ogan nasu duk takaici ya lulluɓe sa yanzu kenan wanda ya kasance ba ɗan ƙasa
ba shi za'a bawa muƙami babba har MG kuma ma religion nasu ba ɗaya ba kai ina da
sakel yana can ya tafi duniyar tunani yaji ogan nasu yana cewa ''akwai wani mai
magana kuma ko babu dan sauri nake yi akwai abunda yake gaba na yanzu'' kar ku
manta duk Wannan magana da suke yi da harshen turanci suke yin sa komawa LG yayi ya
zauna yana ta saƙa da warwara a cikin zuciyan sa duk shiru sauran suka yi dan basu
da bakin magana yanda suka ga LG yayi magana Amma ba wani abu masu jin haushi nayi
miƙewa the general of the army yayi wato ogan nasu kana ya umarce su da duk su fito
a gabatar da Sheed a matsayin Mejor General a gaban duka sojojin duk mikewa suka yi
suka mara masa baya
Sheed ne ƙarshen fita komai nasa cike da izza yake yinsa suna fita gaba ɗaya
rundunan sojojin suka fara sara musu wajen da aka tanada dan

Please Login or Register in order to submit comment