Shigowa tayi zaratan maza masu kula da lafiyar ta, suna biye da ita, suka ja tunga
daga bakin falon farko. Sabida idan ka nufi falo na biyu, akwai masu tsaron kofar. Suna tana
isa aka bude mata, sanye take da doguwar rigar, wuyarta sakale da karamin gyale, gashinta da
ya kasance ja me dauke da ratsin fari, ya kuma fitar da fuskarta. Ba zaka tab'a yarda ba idan
aka ce tabawa Hamsin da shida baya ba.
Sabida yadda take kula da jikinta, ya sanya tsofarta boya, sannan ko akan fuskarta yar
karamar ce mara nuna girma, mace ce mai tsumammen fuska.
Domin kuwa, ba zaka tab'a ganin dariya akan fuskarta ba. Amma baka raba fuskar da
murmushi ba, sabida yanayinta mace ce mai yawan Alkhairi.
Tana isa falon Allison yana mik'ewa, ta rike kunnen shi, suka nufi wani kofa, zata bude ya
riko hannunta.
"Kiyi hakuri! Na fita, ba sai kin duba ba, kuma ba laifin su bane nawa ne! Mom yaushe zan
daina b'oya? Yaushe zan zama me tsayawa da kafarshi?
Mom sabida Rio Lucifa kike boye ni? Sabida shi kika hanani sukuni? Toh ni Mom ba zan
iya wannan rayuwar ba? Sabida bata dace dani ba.
Mom ina son nayi rayuwa kamar sakakkun tsuntsaye masu yanci, Mom duniya da girma
take me zai sanya ki takura ni ki turani wani gurin nayi rawa wannan duniyar da kika tara, basa
gaba na."
Daga hannu tayi zata mare shi,
"Madam!"
"Mark! Na manta baya, me yasa Allison yake kokarin dawo min da kome?"
"Mom ni bana son wannan dukiyar ki bar ni na zab'i rayuwar da ta dace dani. Mom ko Emily,
zan amsheta ne saboda bani da zab'in kome a rayuwata,
Mom ni zan amshi Emily amma ki bar ni nayi rayuwa da duniyar da nake so! Kudi motoci,
Industries, companies, Mom ni basu ne nake bukata ba, ga guard sama da dubu biyar a gidan
nan, kai ne ban isa nayi rayuwar yancin ba. Gaskiya gwara na fita Su rio su kamani ke ma..."
"Allison!!!" Ta daka mishi tsawa, juyawa yayi da sauri ya haura sama, cikin jin haushi.
"Barka dai Mom! Ko zan iya zuwa gare shi."
Nuna mata saman tayi, tabi bayan shi, zama Tayi idanunta nakan zoben aurenta, hawaye na
zuba daga idanun ta. Kukan da take rike wane na tsawon shekaru yau take yin shi, kuka me
mugun cin rai, bude jakarta tayi tare da zaro inhelarta, ta shaka. Tare da zubawa hoton
mahaifinta idanu.
Mss William mace ce, da take da sa'a a Rayuwarta, mace ce da ake kiran ta, Alkhairi a cikin
biliyoyin mata, ita kadanta alumma ce, balle kuma an hada da halayyarta duk da kasancewar ta,
Christianity amma kuma tana da zuciya mai kyau da taushi.
Tana cikin mutanen da Allah ya basu kwarjinin sosai, domin tana da irin Immunity bata
cika shiga hatsari ba, sai ta bar guri sharri yake wanzuwa. Kowani dan Adam tara ne haka
itama tana cikin tara.
Idan za a kira ta mace mai Alkhairi da Alfarma toh Mss William ta kai haka, shi yasa ake mata
sha'awar shiga siyasar U.S,
Amma saboda Allison ta hakura da wannan matsayin ta gwammace shi ya tsaya, amma
yaki sabida kasancewar shi mutum mai raunin zuciya, yana da hali irin nata, amma bai da karfin
zuciya da rashin tsoro.
Abokan gabar Mss William, har yau basu tab'a nasarar , cutar da ita ba koda kuwa
kwarzane ce.
Har yau suna ka na bakin cikin rashin cutar da ita, ansha kawo mata Mutanen da suke
harinta, tace a sake su, su tafi sabida suna da tasu rayuwar da zuri'ar su.
Har yau babu wanda zai ce ya ganta cikin damuwa ko bakin cikin, sai dai zaka ga
fuskarta aways keeping smile, sabida ta yarda da cewa. Murmushin kan fuskarta yana kunshe
da abubuwa kamar huษu. Na Farko shudaddiyar duniyar da aka binne shi a cikin kasar zuciya.
Na biyu fuskarta sabuwar duniyar da kake rayuwa cikinta. Na uku, rike sirrin boye da take
bayyane a kan zuciya.
Na huษu, gigita abokin gaba yayinda yake ganinka ya firgita, saboda kwarjininka. Yana ji yana
gani zai ta tsammanin kana shirya mishi wutar kashe kan shi ne, alhalin kai taka manufar da
ban. Ba tashi kake ba. Ta kanka kake. Shi yasa haka ya zame mata kwarin gwiwar ta. Dan da
shi take yakar abokan gabarta.
Wannan dalilin yasata rike sirrin murmushin ta, a duniya babu wanda bai san cewa
Allison shine weakpoint ษinta ba,. Duk abinda take aka ce mata, gashi an kai mishi hari zata
bari. Sau dayawa ta sha saka hannunta akan wasu cantract sabida Allison. A kullum burinta
Allah ya kawo mata ranar da Allison zai zama mutum yadda zai kare dukiyar su. Allison yana
da degree a kasuwanci, yadda yake iya sarrafa dukiya abun burgewa ce. Amma zuciyar shi
bata da karfi ko daya. Zuciyar shi bata iya jure damuwa, shi yasa kullum zaka same shi a study
room, yana nazarin kasuwanci.
A yanzun haka baya fita ko ina, amma duk wani aikin cigaba yana yi a cikin gidan su. Mutum
ne da yake da hakuri da son zaman lafiya, amma a duk lokacin da ran shi zai b'aci kowa sai ya
razana, Mutum ne da zai iya zama na tsawon watanni bai cewa kowa cikanka ba, sabida Izzar
kudin da yake bin jikin shi.
Sam haka baya burgeta, burinta ya zama mutum mai fada aji, amma sam ba haka ba,
lusarancin shi yasa ta hana kowa kusantar inda yake sai Emily, itama sabida Mahaifin yarinyar
shine na kusa da ita, kuma d'an uwan ta na gurin Mahaifiyar ta, idan akwai abinda Mss William
take so, Auren Allison da Emily. Amma Allison yace baya son aure yanzun asalima shi bai
gamsu da soyayyar da take mishi ba. Amma kuma bai hana yarinyar takura mishi da soyayyar
zamani ba, tana fara tab'a shi yake kaucewa. Dan ce mata yake shi mata maza ne (
๐คฃ๐๓ฐข
)
dan karta sanya shi aikata mugun abu. Akwai wani lokaci da ta shirya mishi Birthday party, ta
wurga mishi kwaya, a cikin abin shan shi.
Koda abin yabi jikin shi kallonta yake, tare da riko hannun ta. Yana kallon ta, murmushi
yayi sannan yace mata.
"Bana jin kome akan ki! Ba zaki ji zafi ba idan muka kasance tare? Ni mutum ne da bana son
abiya bashin da naci, dan haka kiyi hakuri soyayyata idan zata nutsu sake zaki fi kowacce mace
Sa'a, idan kuma ba zata nutsu sake ba, zaki fi kowacce mace jin zafin abinda na miki.
Ban damuwa da mace mai kyau ki kyalkyale ba, Ni duniyata bana son ta zama me cike
da ฦawa, kawai SOYAYYA nake bukata a gurin macen da nake bukata, ta zama ni zan daurata
a cikin tsarina da ra'ayina. Ina da buri! Ina da yakinin zan yi farin ciki amma ba ta wannan
hanyar ba, wannan yanayin naki ne, baki san zan cutu ba?
Idan na fara darajar ki, toh ba zan iya tsayawa akanki ba, zan iya samun wata ma na fara
da dajarar ta, don Allah mu mabiya ne masu kamun kai, don Allah karki kuma shayar da ni
abinda zai dame mu, kira min Dr Patrick"
Tun daga ranar bata kuma kuskuren bashi wani ba, sai dai inda taga yana fushi tana ฦoฦarin
kwantar mishi da hankali. Yanzun ma sa ta haura falon shi yana tsaye a jikin window yana
kallon yadda tsuntsaye suke rayuwar su cikin yancin da samun kulawa daga jinsin su.
"Allison!" Ta kira sunan shi a sanyayye, banza yayi da ita, kafin tace mishi.
"Wancan ranar da naga ka tafi tsuhuwar unguwa tana gyaran mota, na zata dan cika farin cikin
ka ne? Daga baya kuma kazo ka mare ni ranar Lahadi zan shiga Church, bai sani jin na rabu da
kai ba.
... Allison rayuwarka Mom take karewa, domin dan itace zata iya tafiya wani gurin tayi rayuwa,
amma sabida kai take zaune anan, kasan iya adadin dukiyar da take kashewa dan baka
kariya?"
"Emily! Bana son dukiyar? Bana son kome! Ta barni nayi rayuwa na fita daga cikin wannan
duniyar da ta kirkiro min shi. Duk abinda yake faruwa itace silar shi. Ta bar haษa kanta da kowa,
tayi rayuwa irinta Yancin. Babu amfanin goggayya da mutanen da basu da kirki.
Ina son Mom ne dukiyar da muke dashi ta haษa su mu koma wani gurin muyi rayuwar mu,sai
Yaushe zan sami Freedom?
Idan zan fita men in Black suit, tare da manyan bindigogi, haba kiyi nazarin rayuwa mana,
talaka yana barci cikin nutsuwa kai kuma dukiya ta hanaka barci cikin nutsuwa. Ko yaushe ka
juya zaka sami mutane sama da goma suna lura da lafiyarka! Idan aka ji ka motsa za a buษe
kofar a ga lafiyarka! Meye akayi da duniyar da zubda jini ya zama kwalliya a cikin shi. Ni mutum
ne mai san zaman lafiya, koda matsayin da take niman zai zama na tashin hankali ba zan amsa
ba, ni kwanciyar hankali nake buta kin fahimce ni...
Wannan book din na kuษi ne akan 300โฆ haka ma katin mtn 300โฆ
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu.
[11/13, 8:06 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/iAhygLXSfbb
๐๐๐๐ ๐๐๐๐
<๐ฒ๐ ๐๐๐๐ ๐ซ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐ฒ๐๐๐๐๐>
โ๐ธโค๐ธ๐๐ธ ๐โ๐๐๐ผโ'๐ ๐ธ๐๐๐...
แด๐๐ข_แด
๐๐ฆ๐๐ฎ
Bismillah Rahmani Raheem
#Inuwa biyu
1โฃ3โฃ
"Babu matar da zata juya mu, dole mu juyata gidan mu ne, ba gidan su ba."
Shiru suka yi, kafin Malam Haliru, ya ce musu zai tafi ya kira mai dauri, amincewa suka yi ya
fita, tare da yin shiru. Kowa da abinda yake sakawa a ranshi.
Bayan mintuna arba'in suka shigo da wani, dattijo yana shigowa ya duba hannun, yace.
"Kashin gefen hannun ne ya karye, Insha Allah zai hade."
Dutse
Aikin abincin dare Hajiya Surayyah take, ita da Ummita wacce ta shigo taya ta, aikin
hankalin su yayi nisa, sosai nan aka Raliyah ta shigo. Tana kallonta. Tare da kura mata ido,
dake idan suka yi abincin rana, zuwa yamma sai su shigo cikin gidan hirar maraici.
"Ummita ya nake jin kamshin turare na a jikinki, kuma yau sati biyu kenan da aka sace?"
Inji Raliyah.
Cikin wani irin tsoro ta kalli Raliyah, sannan tace.
"Wani irin magana ce wannan? Fisabillahi ana zaman lafiya zaki kawo wani irin."
"Kinga dakata! Karki mai dani sakarya, ina kallon ki ne kawai, domin haka kika saka muka
tsangwami matar Isah nan kuwa munafuka kece barauniyar, kina shiga dakin mutane ko, toh
wallahi baki isa.
Domin haka kike kwashe kayan mutane ana miki Hakuri Wallahi bazan yi hakuri ba, kiji
Dakyau, maza tashi ko na kunyata ki."
"Ke bana ciki da rashin kunya, gidanku ba a koya miki girmama manya bane, da kike wannan
rashin kunyar wuce ki bani guri."
Cikin rashin mutunci, tace mata.
"Hajiya babu inda zani, haka kawai yarinya tana mana sata ace na wuce wallahi sai ta bani
turare na ko kuma nayi rashin mutunci a gidan nan"
"Yanzun don Allah ba zaki tashi a kaina ba, yau naga rashin hankali, ke Ummita kin daukar
mata turaren ta ne?" Cikin tsannanin tsoro tace.
"Me zan mata tunda part din mu ba d'aya ba, sannan ga masu ษaukar abu bata bincike su ba
sai ni, dan turaren yayi kamshin turaren ta, sai tace nata ne. Wallahi ba nata bane!" Ummi ta
faษa tana kuka, kafin kace me gidan ya cika sabida yadda Raliyah take ihu shi ya janyo
hankulan mutanen gidan.
Ga kuma Kukan da Ummita take wanda ya sanya da yawa ganin kamar sharri tayi mata,
musamman da uwar mijin Ummita ta amshi rigimar ya zama nata, wannan al'amarin ya masifar
b'atawa Raliyah rai.
Dole Hajiya Uwani ta fito ta kashe rigimar Raliyah tace.
"Wallahi na kyale ki ne..sabida Maman su Abdus Samad, amma na rantse da Allah, sai na baki
mamaki. Mara kunya kuma zaki kuma ai ba yau kika fara ba."
Tayi ficewarta, ta bar Ummita tana kuka sosai,sabida tana kiran abinda Raliyah tayi mata da cin
fuska.. ---
"Hmm!" Inji Ya Hindatu, tsabar gulma na cinta, ta kalli waje, a ranta tana jin ciwon sharrin da
Aka mata, tab'e baki tayi sanan tace.
"Insha Allah, sai na rama nima, baki yi kuka ba, yar banza muguwa karfi da yaji, kin sani na
koma mujiya a cikin gida. Ni dake ne sai na rama."
Wannan shine abinda take fada tana kuma shan rantsuwa..
**US
"Rio Lucifa, shine mutum na gaba da ake tsamanin zai zama sakataren na musamman a
fadar Whiter house, toh amma matsalar da aka samu. Manyan mutane da yawa suna niman
wannan mukamin, a cikin su kuwa akwai shahararriyar attajiran nan Mss William! Dattijuwar
kirki mace mai mutunci da kima."
Kallon Jerry Aamil yayi sosai, kafin yayi shiru idanun shi yana rawa, kafin ya mai da gefen shi
yana cewa.
"Ina jinka."
"Kasancewar Mss William, matar sau uku tana fitowa takarar shugaban kasa, kasar nan amma
bata samu ba. Duk da mahaifinta mutum ne da kasar nan babu wanda bai san shi ba,
Haka yaja mata farin jini, sosai kuma mace ce da take ฦyamar auren jinsi, haka ya saka
kowa yaji a ran shi ya zab'e ta, sai dai wani abun da na kasa fahimta. Shine a lokacin da ta fito
takarar sai Mr Rio ya dawo da ita kasa koda kuwa tana dab da cin nasara ne, haka yasa ta
hakura, shima kuma bai yi nasara a nashi hankoron ba.
Sai ya kullace ta, har yana iya kai mata hari a ko ina, Mss William tana da Yaro daya tal,
kuma bata kaunar ya fita koda kofar gida ne, sai ya zama dole.
Ya hada degree din shi na farko a fannin binciken kimiyya, daga baya tasa shi ya koma
kasuwanci, inda ya koma jami'ar havart, inda ya karanci kasuwanci a degree na biyu, yana
gamawa ne, ya fara harkokin kasuwancin shi da nata, dan tace tana son ya gaji iyayenta ne
musamman mahaifin ta.
Gabar da ta kullu a tsakanin mutane biyu, sabida muradun siyasa da cigaban ฦasa. Ita Mss
William tana kokarin kiyayye wasu abubuwan, domin dayawa kungiyoyin mafiya, sun nemi ta
shiga cikin su. Tace musu dukiyarta tsarkake ne. Ita kuma tsarkakkiya ce, ba zata iya hada
wannan kazamtar da dukiyarta da rayuwarta ba.
Koda suka nemi Rio ya amince domin abin da yake nima kenan kuma ya samu cikin
kankanin lokaci, dan haka yana samun wannan babbar damar ya kuma dawowa da karfin shi
niman shugaban kasa, haka yasa aka hana shi sai yake ganin kamar ai itace ta saka baki aka
hana shi. Abun ya dame ta.
Ana cikin haka kawai aka tura mata da sakon za a naษa D'anta Allison a matsayin babban
sakataren harkokin ฦasar, dan haka hankalin rio ya tashi. Nan yayi ta shiga da fecce yayitawa
Yaronta baraza, har ya ce baya son matsayin, uwar tayi baฦin cikin mara iyaka, duk da ban san
shi ba, amma naji mutane suna cewa yana da sanyin hali, yana da matukar hakuri, amma kuma
ance mahaukaci ne, domin wani lokaci yana iya juyewa kamar mara lafiya, yayi ta wasu
abubuwan. Lokacin da suka harbeka sun je harbin motar shine. Sun san baya fada kuma bai
da abokin fada shi yasa suke wannan abin, dan ko zasu kashe shi ba zai amsa musu ba.
Shi yasa kwanakin baya mahaifiyar shi ta hana shi kifuta ko ina idan ka ganta, toh
mahaifiyar shi bata gari ne, idan kuma tana gari kuwa ko get na bai isa zuwa ba balle na karshe
sabida yana zaune ne a guri guda, Amma idan aka kama Alexander shi zai yi bayanin inda Mr
Rio yake."
"Toh ni meye nawa a rikincin su, da zasu harbe ni?" Ya tambaya yana huci tare da fisgar da
iska.
....
Haka ya wuni yana nazarin abinda ya faru dan haka ya watsar da al'amarin tunda bai shafe
shi ba, kawai abinda ya Sani. Idan aka kuma mishi gangancin haka toh zai cigaba da cin uban
kowa.
*
Kwanar Lantana biyar a gida, taji kamar ba zata dawo ba, dan haka abin da ta fara shi, kwashe
kayan Sidrah ta kai can dakin wani dakin ne inda kaji da agwagi suke kwana a cikin d'akin, da
babu kowa sai tarkace, , ga uban beraye, suna hanata barci da kusur kusur,..
Wannan abun da ke Lantana take, yayi masifar d'agawa kowa hankalin domin ba iya
yarinyar ka dai takewa wannan mugun halin ba hatta matan gidan, gashi mazan gidan basu
sani ba, kuma bawai tana da hakuri da zata iya daukar nauyin wasu abubuwan bane shi yasa ta
kuma boye mugayen Halayyar ta, yadda babu wanda zai iya dakatar da ita.
Uฦubar da yafi nada, shi take sha, duk yarinyar ta kuma karewa sai uwar hanci da ba
idanu, sannan da tana zuwa gurin dangin Mahaifiyar ta, toh yanzun ta daina zuwa Konace an
hanata, haka ya sa yarinyar ta koma kamar wata sauna, ita ba zuwa makarantar boko ba, ita ba
islamiyya ha, ga tarin kazamta, da rashin kulawa.
Haka yasa Lantana ta rabata da yaranta, sabida kuntatta rayuwar yarinyar, yadda ba zata
mori kanta ba, kuma haka ce ya fara samun rayuwar Yarinyar, gashi karfi da yaji sun cusa mata
tsoron mutanen, bata iya zama cikin su.
..... Zai yi w
uya ka fahimci halin da take ciki, sabida a yanzun ko aiyukan gida bata yi, kome Lantana da
yaranta ne suke. Karka kayi tunanin ko asiri ne a'a kawai tsabar bala'in masifa ce da Allah ya
jarabcin Kanana dashi shi yasa take abubuwan irinta marasa hankalin. Kuma tana rike da
Sidrah a ranta, shi yasa take azabtar da ita fiye da kima. Kuma take jin ba zata yi nadamar abun
da take aikatawa ba.
**
"Kina can duniya! Niman duniya toh ki kira ki ji shin d'anki yana raye ko ya mutu? Idan yana
raye Alfarma nayi miki, idan kuma ya mutu toh har abada babu wani namijin da zai tab'a
taimaka mishi ba tare da na kashe shi ba.
....kinyi nasarar sakani na rasa matsayina har sau uku, kema zan yi nasarar sakaki rasa tilon
d'anki da kike ji dashi. Idan kuma kinyi kokarin sanar mishi da cewa shi din dan kwaroro ne
babu uba sai kare"
Kashe kiran tayi tare da dafe goshinta, idanunta yana wani irin cika da kwalla, yaushe Allison
zai iya karban kan shi a gaban jama'a? Yaushe zai zama namiji kamar sauran mazan,?
Bata rene shi da kome ba, sai soyayya da fansa. Tayi fatar ya zama me ra'ayin kan shi, amma
ina kawai ya zame mata wani irin mutum me kama da hawainiya ne, duk yadda taso yayi gabar
wani lokaci sai ta karkata yamma, idan tayi dashi arewa sai ya koma kudu. Wannan abun yana
damunta.
Kiran gaggawa tayi. Cikin mintinan ฦalilan, ta kashe wayar, tare da dafe kanta, tabbas akwai
matsala, tunda sunki daukar wayarta haka yana nufin zuwanta Canada bai amfane ta da kome
ba, duk da zuwanta akan taron kasuwanci ne na nahiyar Turai, gashi bai amfane ta ba sai ma
b'ata lokaci da tayi dan haka dole tabar kasan yadda zata isa U.S cikin gaggawa sabida taga
halin da tilon danta yake wanda take jin zata iya bada kome domin shi.
Zata iya sadaukar da Rayuwar ta, dan shi. Ina ba zata iya daukar kasadar zama a Canada.
Ganin nisar komawar ta tayi, domin kuwa haka ya mugun d'aga mata hankali, har ta isa inda
jirgin ta yake, kiran layin P.A take amma yaki d'agawa, haka ya kuma tunzura zuciyarta sosai
dan gani take kamar an kashe mata Yaro ne.
.......
"Gareth kalli gayen wanda aka bamu hoton shi mu kashe shi." Inji wani baฦin fata.
Kallon hoton wayar shi suka yi, "tabbas shine. Mubi shi"
Suka fada tare da bin bayan Aamil.
Shafa bindigar mugun shi yayi, bai taษa kisa ba, kuma baya fatan ya fara, amma dole ya
gano waye yake son kashe shi, sunyi tafiya me dan nisa, suka nime shi suna rasa, juyawa suka
yi zasu bar gurin kawai suka hango shi tsaye, yana saka salansar bindigar, tare da zuba musu
ido. Kafin suja kunamar bin.....
Wannan book din na kuษi ne akan 300โฆ haka ma katin mtn 300โฆ
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu.[11/13, 8:06 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/sWKmMfn3gbb
๐๐๐ ๐๐๐๐
<๐ฒ๐ ๐๐๐๐ ๐ซ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐ฒ๐๐๐๐๐>
โ๐ธโค๐ธ๐๐ธ ๐โ๐๐๐ผโ'๐ ๐ธ๐๐๐...
แด๐๐ข_แด
๐๐ฆ๐๐ฎ
Bismillah Rahmani Raheem
Har abada wutsiyar Raฦumi tai nesa da kasa
๐คฉ
#Manta baya
1โฃ4โฃ
Sake daya harbul yayi a kafa, daya kuma a hannu, dole suka yasar da bindigar, yana zuwa ya
dauke daya da mari, dayan kuma ya dake shi da bakin bindigar din.
Ihu suka saka tare da komawa gefe, jikin su na makarkyata.
Takowa yayi kuma yi dai dai wayar dayan su na kara, yana dauka ya saka a kunne yace.
"Xsezza! Kun kashe shi?" Aka yi tambayar a kagaucce.
"A'a sai dai ni na kashe su, Banza kawai!"
Kawai ya sake musu harbin cikin nutsuwa, dan abun ya bashi haushi. Wato ma so ake lallai a
ga bayan shi, sannan yayi ta dukar su da kafa, kafin ya juya ya bar su a kwance cikin jini.
...... Dawowa yayi ya dauki wayar su ya dauki Numbern da aka kira ,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 13