zaran an gaya maka yayi kaza
ranka a b'ace zaka hukunta shi. Sabida zunzurutun son kai.
... Toh wallahi matukar ka ɗore a haka Tabbas akwai matsala, domin kuwa za a wayi gari
yana adawa da duk wani abun cigaba da zaka kawo mishi kayi nazari da magabata, kayi dubi
da abinda na gaya maka. Matsalar Aamil daga cikin gidan ka aka faro shi. Ba wai daga ko ina
bane laifin uwar shi ya shafe shi. A wannan duniya kowa son ka shi yake kowa na shi yake
so.
Kai kuwa kayi watsi da naka, lokacin da ake bukatar ka more shi ya juya maka baya, sannan
maganar gaskiya indai yadda ya kawo korafin Yarinyar bata mishi ba, mishi ba hakura da auren
nan haka."
"Ba zai yiwu ba! Yarinyar zai aura, naji nayi laifi batun auren Sidrah ko Aamil yana
mutuwa ya dawo sai ya aureta. Balle kuma babu abinda zai faru, aure ne sai yayi shi. Indai Ni
na haife shi." Duk wannan musayar yawun da suke, Alhaji Abubakar yana jin su. Gyara zama
yayi bayan ya kalli Alhaji Ma'aruf, ya sauke numfashi sannan yace musu.
"Wato wani kuskuren da muke aikatawa, bamu sani ba, shine hada iyayen mu mata da matan
auren mu, ba dan kome ba sai dan babu wata uwar da zata jure ganin wata ta juya Mata D'anta,
musamman iyayen mu da suke da duhun kai! Gani suke sun gama wahalar su, lokaci guda
kinzo kin juya mata hankalin D'anta, sannan suma matan mu, basu iya hakuri ganin an juya
musu akalar mazajen su. Sabida ai su, suka fi dacewa da juya mazajen su ba iyayen mazan ba.
Kaga irin wannan al'amarin. Ya sani raba gidana biyu, mahaifina tana can bayan layin mu, har
da yan aikinta da duk wani abun da take bukata na tura mata, har mota nata na kanta, na saya
mata. Da driven ta, gudana kuwa nayi kokarin tsayawa namijin duniya, babu macen da zata
rena min uwa, kuma naki yarda na dauki damuwata da Matana na kai na gayawa Mahaifiyata.
Badan kome ba, sai dan kawai na tsira da kwanciyar hankali na, ka nutsu da kyau, taya za
ayi a ce da kome sai Mahaifiyar ka ta sani, wannan shine dalilin da ya rabaka da matar ka!
Shine dalilin da ya rabaka da Yaronka. Babu wani wanda zai gaya maka gaskiyar da muka gaya
maka.
Kayi ƙoƙarin raba gidan ka, koda mahaifiyarka bata da matsala akwai me kaiwa da komowa,
dan haka kayiwa kanka Adalci wallahi wata rana zaka ji kunyar wofantar da shi da kayi fa."
Shiru yayi yana nazarin abinda suka gaya mishi maganar gaskiya haka ne, babu karya a
cikin maganar su, amma kuma ta ina matsalar take?
"Na rasa fahimtar kome? Wallahi sai naji kamar bani ba."
.... "Eh mana! Sabida baka nazarin abinda kake kawai zartarwa kake da umarnin mata, su kuma
nazarin su bai da tsawo kamar namu, sannan ka nazarci,maganar Auren nan mana."
"Alhaji Ahmed, ba naki maka bane Yarinyar tana bukatar Aamil a rayuwarta, mareniya ce yar
kanin mu da aka kashe a rikicin kabilanci na garin jos, shine aka dawo da ita, Hadeja, toh
yarinyar tana fama da gallazawar jama'a gidan da take shi yasa nake son aura mishi ita, yayi
renonta dan bata wuce shekara goma sha daya ba"
... Sake baki suka yi suna kallon shi, ganin da gaske yake yasa su mik'ewa suna faɗin.
"Amma baka da mutunci, wallahi ba dani za a fara batun child abuse ba, kawai ka nima mishi
manyan yan mata, amma yar sha daya, ina magidabci irin shi zai hakura da ita, idan ba so kake
a bugaka a jaridar Daily trust ba."
Inji Alhaji Abubakar,
Murmushi Alhaji Ma'aruf yayi sannan yace musu.
"Babu abinda zai yi mata koda anyi auren karatu zasu tafi shi zai tafi masters ita kuma zata
karasa primary zuwa secondry, kafin ya dawo tana secondry."
Sake baki suka yi suna kallon shi, ya sake murmushi sannan yace musu.
"Ba zan hana shi tafiya da ita ba, amma kuyi nazarin lafiyar shi, kafin ya rabu da ita dole zai so
alaƙa da ita kodan yaji haushin renonta da yayi, sannan dole shakuwa zata shiga tsakanin su.
Kun ga kenan haka ya ishe ni amfani ya sauya halin shi."
Zama Alhaji Ahmed yayi sannan yace mishi.
"Kuma kayi kyakyawan tunani! Domin kuwa, shi zai more kuruciyarta amma mutumina kai fa
mugun kwaro ne." Dariya suka saka abin su. Tare da bin yaran da addu'a.
**
Koda Alhaji Ma'aruf ya koma gida, nan Hajiya da Ya Hindatu, suka kitsa masa kome, murmushi
yayi tare da godewa Allah da ya hada shi da abokan arziki, domin kuwa zai yi wuya ka fahimci
yadda mamaki ya rufe fuskar shi, yanzun da a ce Aamil bai zo ya fadi ra'ayin shi ba toh ba
makawa, laifin Uwani zai gani dan haka da yabar dakin suna tsammanin zai haurawa Uwani ne,
sai suka ji shiru bai kuma bin takan zance ba.
***
Tana tsaye kamar wata Status, sai had'iye yawu take, tana kallon yadda kowa yake diban tuwon
masara miyar karkashi, gashi tayi kyau Koriya shar. Sai wani daukar ido take, har tuwon ya kare
ba ta samu ba, a wulakance. Lantana ta kalle ta, sannan tace mata.
"Toh uwar haladu, kakar Musa. Zaki zo ki dauki sauran mara ki dama ga dandano can a daki ki
saka sai kisha,dan babu miyar ta kare, ni kuma bani da Manja ko mangyada da zaki ci tuwon
dashi, yar banza nan da wasu watanin zaki daina cin cimar mu, zaki koma ta yan birni, ja'ira
kawai."
Jikinta na keerrma ta wuce, inda taga tuwon yayi sanyi, da ta kula sai ta ga ashe najiya ce ma,
dan haka bata da zab'i ta shige cikin dakin ta dauko dandanon ta dama tuwon ta diga ta fara ci,
haka kafin wani lokaci har ta cinye. Hamdala tayi sanan ta koma can gefen kitchen ta zauna,
tana kallon saratu, Sahiya, sannan takiya tazo, sai sauran Yan matan gidan suka shirya suka
nufi maciyar da take kofar gidan su. Ita kuwa bata da ikon fita.
"Sidira!" Da sauri ta mike tare da cewa..
"Na'am Innah"
"Zoki kashe min kwarkwatan nan wallahi sun dame ni."
Da sauri na iso kofar dakin Lantana, ta bude wani dambun kanta, Ya ilahi. Wato tsabar kazamta
gashin har baka hango layin kitso, ga kan a duskure. Lantana irin siraran matan nan ne, gata
baka mai tamushashen fuska. Hancin ta kuwa ba laifi dan yaso zama siriri amma ya koma
babba, jin yan yiririn. Hannun Sidrah akanta tace mata.
"Yar banzan baki dan cewa bakwai mike ce ke ba? Ai ke yar wata bakwai ce shi yasa baki
girma, sai shegen wayo da idanun kamar babanin tsaka,
Wannan aka aurar dake ai daren farkon sai da a fidda gawarki, yar Kwankwanso uwa, Yar
kashi kanwar tusa.". Haka take kallon Sidrah take kare mata tanadi.
**
After few weeks.
Babban taburama aka Baje a tsakar gidan, ana fidda kayan auren da Hajiya Uwani ta hado, tare
da Aminanta matar Alhaji Ahmed da Hajiya Sakinah matar Alhaji Abubakar, da Hajiya Ubaidah
ana Baje kayan a hankali, sai tab'e baki Ya Hindatu take, dan ba haka taso ba. Ita a tunanin ta a
bawa Hajiya Surayyah kudin su shiga kasuwar Dutse a sayo yar ka gudu ka sami lafiya.
Toh asalin hada kayan ba ma a gidan Hajiya Uwani ta haɗa ba, dan kaiwa Gidan Abokan shi
tayi, domin turamen atamfofin kwatono suka je suka sayi su. Tsaf lace kuwa Hajiya Ubaidah da
zata tafi Chaina aka bata kuɗin shi da kayan dakin Jamila da mafiya, Safiya da Sidrah. Dan ya
dauki nauyin zai mata kome. Sauran kayan ne da kayan kitchen suka sayo a dubai, dan ya
sake kudi kuma bai tab'a aurar da yara ba, sai wannan karon. Duk a cikin kayan da aka sayo na
Sidrah ne babu bra.. amma ba laifi kayan sun hadu iya haɗuwa.
Kuma Ghali da Aliyu sun bada karin kudin su. Abun gwanin sha'awan. Kallon kayan Alhaji
Ma'aruf yayi sannan yace mata.
"Allah yayi miki albarka Rabi! Nagode sosai, gashi keda Yan team din ku. Kun hada min abinda
ban zata ba." Bayan an gama hada kayan kowa tace musu.
"Ni zan dauki kayan Aamil! Sauran kuma su dauka su kai dakin Iyayen su, Na gama nawa,
sannan ga wannan yan kunnen da sarkokin su, da zobban su. Azurfa ne na saya musu nawa
gudummawar kenan,!
"Hmm!" Inji Amarya, wato bata gamsu ba. Sannan ta mikawa Alhaji Ma'aruf wani karamin
akwati tace ya bude..yana budewa yaga wani kyakyawan zoben arzufa tare da set din shi duk
yafi na sauran haduwa an rubuta A&S. Murmushi yayi sannan yace mata.
"Allah yasa ki gama da duniya lafiya!"
"Mu kuma mu kare da duniya a lalace ko? Alhaji Ma'aruf wallahi kama kai kanka wutar
jahannama? Ko"
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Habbaratu baki da hakuri, kome na duniya dan hakuri ne, kin san nawa kuɗin abin da ta saya
ne? Toh bana son haka!"
Shiru tayi tare da kauda kanta, ita ko Hajiya Uwani ko a jikinta, tace mishi.
"Abban su, kayan kitchen na yan matan na saka musu nawa gudummawar, har da zanin gadon
na kara musu, yadda suma zasu fita rasa."
Jinjina kai yayi tare da jin kaunar ta yana kuma kara hoda zuciyar shi. Matar tasan me take yi.
Bayan ta gama mishi bayani sannan ta ciro sauran canjin shi Naira dubu talatin da biyu ta mika
mishi tace mishi.
"Alhamdulillahi na gama aikin da ka sani, ga sauran canjin ka da fatan kome lafiya, ga list din
abinda muka kashe duk zaka gani anan sai kayi min bayani idan ban rubuta kome ba." Ta faɗa
mishi tare da mika mishi wani dogon takarda, sannan ta shiga kwasar kayan Aamil ita da
yaranta, suka kai d'akinta. Dan tana kokarin danne Zuciyar tane, amma tana jin yadda suke
mata magana kasa kasa, tare da tsaki. Ita ba mutum me son rigima ba. Shi yasa ta bar musu
gurin su cinye kan su, ina dalili.
Bayan ta tashi shima Alhajin ya mike ya bar su a gurin, ai kuwa suka shiga kushe kayan
wasu na cewa. An cuci Abban su ne, zagi irin na rashin da'a haka suka yi, suna cikin haka Oga
Aamil ya shigo, yana jin yadda suke zagin Hajiya Uwani, tare da yaran su. Kawai ya gyara
murya sannsn yace.
"Ku da aka zagi Ummi daku, ku tashi ku fara tsallen kwad'o kafin na shiga dakin na fito."
Sun san tunda yace ba makawa sai sun yi shi, dan haka suka mike tare da fara tsallen, shi
kuma ya bar su a gurin basu isa su koda hutuwa ne sabida halin shi, yana shiga dakin shi ya ga
kayan..kamar wanda aka zage shi ya hau fada da fushi karshe ya bar gidan ma, ba tare da ya
yafewa masu tsallen kwad'o ba.
#Mai_Dambu
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: 𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>
ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮
Bismillah Rahmani Raheem
https://chat.whatsapp.com/GIIFqCembtoD3Bp6yWve7C
Don Allah idan kana Groups dina karka shiga wannan na masu bukatar Free Pages ne! Please
karku shiga
#Juyayi
0⃣7⃣
Babu wanda ya kuma bi ta kan Aamil, sabida sun fahimci fitinar shi yake kawai, dan haka
babu ruwan kowa da damuwar shi auren babu fashi. Ya buga ya buga aure babu fashi.
.... Dan haka ya shiga daki ya zauna na wuni guda yana nazarin abinda zai aikata. Bayan
kwana biyu, Hajiya Uwani da Kawayenta tare da Ya Hindatu suka kai kayan auren Aamil
Hadeja, bayan an Baje kayan. Tana can bakin rijiya, tana jan ruwa, da wani mummunan kayan
jikinta, riga da zani ce, zanin an mata sanda, amma bai hana tsakiyar zanin darewa na.
Gashi kwana biyu tana fama da kasuwa, dan haka idan ruwa ya tab'a jikinta susa take har
tana zubda kwallar dad'i, gashi ciwon ya kama duk wani gabb'a na jikinta, sosawa take kawai.
Bata san me ake ba, dan haka ta tsayar da Mati ya daura mata bokitin paint. Ta nufi hanyar
shiga shashin su, taga mutane, dan haka ta karasa da sauri, tacewa.
"Altine sauke ni don Allah!"
Tsaki yarinyar ta mata tare da cewa.
"Toh ki dawamma da ruwan a kanki, banza kawai."ta fadi haka cikin jin haushin Sidrah,
"Toh don Allah ku sauke ni, wuya na!" Ta faɗa tare da fashewa da kuka, mik'ewa Hajiya Uwani
tayi ta hango ta kanta yana rawa zata sake bokitin.
"Lantana Sirikar tawa aka bawa wannan katon bokitin, baku san yana maida mace baya ba?
Yarinya karama an daura mata wannan bokitin, ku matsa min na wuce, baku da amfani" haka
ya bangaje yaranta yi ta saukewa Sidrah bokitin, a ranta tana cewa.
*Insha Allah ƙarshen wahalar ki tazo!* Yanzun ta kuma yarda da hadin domin ko babu kome
yarinyar zata samu kulawa.
"Hajiya Uwani! Ina in-law din mu take?" Inji Hajiya Ubaidah, murmushi tayi sannan tace musu.
"In-law na me tsada ce, idan kuka ganta prize d'inta ya sauka ku bari sai nan da wani lokaci
zaku ganta! Idan kun gama kuyi min magana."
Riko hannunta tayi suka fita, tare da nufar shashin Baba Mamman, tana kallon Yadda matan
gidan suke hararar Sidrah, shimfid'a mata taburama aka yi, ta zauna tana murmushi. Tana
kallon yarinyar tare da tausaya mata, a ranta. Tabbas idan Sidrah ta samu kulawa, mace ce
sosai ta bugawa a jarida.
"Shekarunki nawa?"
Ware idanun tayi tare da d'aga kanta tace mata.
"Ban sani ba"
"Yayanku Aamil ya? Me yace miki?"
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace mata.
"Bai ce min kome ba!"
"Bai miki barazana ba?"
Sunkuyar da kai tayi kasa, sannan tace mata.
"A'a bai ce min kome ba!"
D'ago kan yarinyar tayi, tana yabawa da zurfin cikin ta, tace mata.
"Toh babu damuwa! Kina zuwa boko?" Ta kuma tambayarta.
"Eh kafin kayan makaranta na su yage, ina zuwa amma yanzun Baba yace min ba zan
kuma zuwa ba." Ta fada a sanyayye,
"Toh!" Kar'ar wayar ta ya katse mata maganar da zata yi, ta dauki wayar a sanyayye ta saka a
kunne, "ok!" Mik'ewa tayi sannan ta fito ta samu har sun fito.
"Uwani wai boye mana Sidrah kike?" Inji Ya Hindatu,
"Sidrah!" Ta kira sunanta, a sanyayye yarinyar ta fito tana rab'ewa da bango, har ta iso
gabansu, cikin wani irin soyayyar da ita kanta Hajiya Uwani bata kawo Kawayenta zasu yiwa
Yarinyar ba, wanda tafi zaton tausayi ne.
"Zo nan Ƴa guda ba bari ba, sannunki Yar mu!" Nan suka shiga janta a jiki kamar babu wani
abu a tare da ita, nan bakin cikin ya kuma rufe yan gidan, suna jin ina ma da Yar su ce ta samu
kanta a cikin surukar Alhaji Ma'aruf, sunyi imani za a fifita ta sama da yadda ake fifita kowa, sai
wancan bakar me munin kamar zunubin. Haka suka mata kyaututtuka masu yawa, sannan suka
fita daga gidan.
Kamar jira ake subar gidan, kuwa aka kwace kome tare da mata shegen duka. Sannan aka
korata sai kallon kayan suke.
"Wallahi idan nice sayar da kayan zanyi, makira ai ta samu"
" Amma baki da hankali, Lamiyo, waye ya aike ki, baki ga sun tafi da wasu abubuwan a cikin yar
karamar akwati ba, toh wallahi, kome na su a kirge yake babu ruwa na."inji Lantana, sanan
suka kwashe kayan aka kai dakin ta.
A hanya suke jajjanta yanayin da suka ga Yarinyar, cikin jin haushi haushi Hajiya Sakina tace
musu.
"Wallahi yana cikin dalilan da yasa bana son family house, ina dalili yarinya mareniya an maida
ita baiwa, wallahi ta bani tausayi sosai, aurenta da Aamil shine mafita a rayuwata."
"Mhh! My dear, shi yasa bana kaunar Nadrah tayi auren a family house, domin yarinyar bata da
sittings yanzun wani ya kai ni ya baro ni, tunda kome kika gaya mata dauka take." Ganin zasu
sake baki Hajiya Uwani ta juya musu harshe take suka an kara da Ya Hindatu, suka ci-gaba da
tattaunawa da harshen turanci. Har suka iso gida.
***
A hankali kome yake tafiya sauran ma an kai kayan su, tare da kawo nasu Jamila, bikin na
karatowa, ana musu gyaran na musamman yaran da ake so fa. Ita kan Sidrah me ta sani da za
a mata gyara mata.
... Ana saura wata guda bikin yana kallon kowa da ido, gashi Alhaji Ma'aruf ya kuma basu
kyautar mota, inda yace zasu biya rabi shi ya biya musu rabi. A gurin Alhaji Abubakar ya saya
musu, amma na Aamil duk yafi nasu kyau datsa. Duk da haka bai hana wasu jin haushin Aamil
ba.
Sannan wani adalci da yayiwa mazan haka yayiwa matan, inda matan dukkan su ya biya
musu Umrah har da Sidrah dole aka tura Aamil yaje ya dauke ta a hoto wanda za a musu
passport, tana can gidan bishiya a kofar gidan yazo, tayi shiru tana kallon masu carafke, dan
wasan yana nishadantar da ita, sai dariya take, yau karon farko ta samu farin ciki sakamakon,
Lantana basa gari sun tafi Auyo, kusan ma duk matan gidan. Kallon yadda take ware yalon
hakorinta ya sashi jin haushin yana zuwa inda take ya suri kafarta tare da watsa mata kayan
hannun shi.
"Na baki nan da minti talatin kiyi wanka ki fito muje wani guri." Kamar mara gaskiya haka ta
tashi ta nufi hanyar cikin gidan, taje taja ruwa a tsorace tana zare idanunta, tare da niman soson
danga, dan shine nata, sannan ta nufi ban daki tayi wanka da ruwan sanyi, bawai tana jin daɗin
shi bane kawai bata da yadda ta iya, gashi Kazuwa ya rike mata wandonta, a hankali tayi ta
zuba ruwa har ciwon ya jike ta cire wandon. Ta fita a hankali sabida ba wai ta yarda da kanta
bane, kayan da ya kawo mata ta dauka riga da skirt ne yan kanti, sai wata fashion hijab iya
wuya,me hade da hular shi. Ta shafa man shafawar ta, dangwali yabe. Sannan ta fito fuskar
nan kamar anyi barin mangyada a cikin dan wake. Kauda kai yayi dan duk wani dakika kara
tsanar yarinyar yake ji. Ta shigo kaddarar shi ta lalata mishi goben shi.
Ta lalata mishi farin cikin shi, ta mai dashi abin b'oye kai a cikin abokan shi, ko jiya da dare
sai da aka yi ta mishi dariya a club. Sabida zai auri yarinya karama wacce bata fi hanjin cikin shi
ba, kauda kai yayi lokacin da yayi tozali da katon makeron fuskarta.
Wanda yake kan cin jikinta, daga nan suka wuce wani shagon hoto, suka je aka mata
passport. Daga nan ya dawo da ita, gida Allah cikin iko. Shi basu dawo ba, dan haka ta cire
kayan ta ninke ta ajiye a bakin kofar Lantana.
Koda ya juya ji yayi motar shi tana kamshin manda tashafa me warin kalanzir bude glass din
motar yayi iska na shiga. Har ya iso garin dutse.
...
Ran shi a b'ace yake sosai, dan haka yana shiga gidan yaji Harira tana yiwa Ummin shi rashin
kunya dan tace mata wanke wanken da wuri zata fita, shine take cewa.
"Ai kina da yara Me zai hana kisaka su suyi tunda sauri kike!"
Yana shigowa ya kwashe ta da mari, ya kuwa zaro bulala ya shiga zaneta, Ali ya fito.
"Wai kai Aamil me ka dauki kanka? Ina ruwanka da ita, idan ka ji haushi kayi wanke wanken
mana!"
Sake bulalar, ya kalli Hajiya Surayyah, cikin tsantsar rashin mutunci yace mata..
"Surayyah baki gaya mishi kece kika yi sanadin korar min Uwata a gidan nan ba keda
wadancan algungunman matan. Ko karya na miki? Sarkan da kike alfahari dashi na Uwata ce!
Kome da kike sakawa na kawa keda su Mero da Hindatu, dukiyar Uwata ce, dan haka wallahi
ko tattaro min ko kuma na jininku yayi malala a tsakar gidan nan."
Shiru gidan ya dauka kafin. Hajiya ta fito tana faɗin.
"Toh anamimi, ba zamu bada ba, wato ka zauna ka samu wata ta gaya maka kayan mu na
mahaifiyarka ce toh karya ce da Arzikin Ma'aruf ta same shi idan kuwa ka dage sai na tsinewa
Ubanka,"
"Ji min abin dariya, toh ki tsine mishi mana! Idan zai dame ni, d'anki ne ke ce da...." Tass
Ummin ta wanke shi da mari.
"Hajiya ba sa'arka bace! Girmamawa ita a tsakanin ku!"
"Ummi!" Ya kira sunata a sanyayye, Tabbas bayan ita ta mare shi ba da yau gidan nan sai anyi
bala'in da ba'a ta yin shi ba ko da a yakin duniya.
....juyawa yayi ya bar musu gidan karewa ma, kenan. Ran shi ya kuma b'aci, dan haka ta kalli
Hajiya cikin damuwa tace mata.
"Kuna tunanin na mare shi ne dan kawai na dakatar dashi? Ko daya na nuna muku idan ban isa
da yaran ku ba, shi da ban haife shi ba na isa dashi, yaushe aka haifi harira, shi kuma da
hakoran shi na same shi, Harira sa'ar Muh'd ce, amma kuka baza kune yana min rashin
mutunci.
Ban san me kuka dauki rayuwar gidan nan ba, amma kusani duk abinda kuka shuka a
baya, da sannu zai dawo. Koma yaya kuka boye zai bayyana, Hajiya ke uwace! Ki raba kanki
da shiga rayuwar Aamil tunda babu wani abinda zaki mishi ya burge ki. Idan ba haka ba zai
cigaba da zaginki tare da tozarta ku.
Karki ga yau na dakatar dashi, idan kika tsinewa Ma'aruf kece kika yi asarar bashi ba,
sabida ya rigada ya gama mishi wani amfani ya bashi ilimi da wasu abubuwan, sannan kai Ali
da kake cewa me yake takama dashi dukiyar Uwar sa! Wanda kowa yake kokarin ganin ya
hamdame shi,. Shi yake diban shi a duk lokacin da ya kalle ku yagan ku a matsayin bayin shi
sai yaji kome yazo mishi dai dai, dan haka ka rage tambaya wata rana zaka tambayi abin da zai
dame ka. Hajiya Surayyah kiyi kokarin ganin kin nuna Yaranki tarbiyya, da ace shekarun baya
kin daura Yaron da aka bar miki bisa tarbiyya, da yau Allah ya dubi naki ya baki wanda ba zai ja
miki zagi ba.
Kuna tsammanin dan ya lalace ba zai tankawa kowa bane zuciyarshi bata yi wannan
lalacewar ba, dan haka a kiyayye abin da harshe zai furta, zuciya zata iya fadawa matsala."
Daga haka ta bar musu falon ta koma d'akinta, dama kwana biyu Ya Hindatu ta kora musu
nasu aiki wai kar a dami dan uwanta wanda bai damu da ita ma irin son a sani farkan kusa da
gida.
.... Tun daga ranar suka rage wani tsiyar, gefe guda kuwa Malam Aamil yana shirya musu
tanadi.
Kallon kowa yake bayan yasake ran shi kamar da gaske, abin da ya daurewa Hajiya Uwani
kai yadda yake shige da fice, kamar da gaske, dan makaranta yake zuwa yayi wasu abubuwan
tabi didigin shi amma bata ga kome ba. Dan haka ta share batun shi.
Ga bikin yana kuma karatowa, kuma dan banza shiri
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13