su kuma suna faman wasan banza, wannan na
tab'a nonon wannan, sunan faɗin.
"La naki yafi girma!" Inji sahiya, takiyah tace.
"A'ah naki akwai guda a cikin shi, tab'a kiji."
Haka suke ta tab'a kukan su, tare da maganar, banza irin na batsa. Zuwan Sidrah yasa suka
zuba mata ido, kafin Zubaina tace musu.
"Laa kuzo mu duba na Sidrah ba ita ba ce amaryan da za ayi aurenta ba."
Daure fuska tayi, cikin tsoron karsu mata. Tsiya, tana jan ruwa ta zuba zata kuma ja,.suka
fincikota tare da yaga mata gaban rigarta, aikuwa ta fasa ihu tana faɗin.
"Wayyo Allah na, ni bana so, Inna Lantana Kinga su ko!"
Buge mata baki Sahiyah tayi tare da barin gurin duk suka watse, ta koma bakin rijiya tana jan
ruwa, tare da share kwalla da ya cika mata idanu.
.. tana gama jan ruwan ta nufi hanyar gida, Allah ya taimaka bata shiga ko ina ba, Cigaba tayi
da aikinta Saratu na ta mata surutu, Lantana tana kwance a dakin sai da Inna Larai ta shigo.
Tana shigowa ta kifawa Sidrah mari, cikin fada tace mata.
"Dan Ubanki bani Naira hamsin dina da kika dauka!"
"Wallahi ban dauki kome ba! Na rantse da Allah, ban dauki kome ba, ki duba ni." Haushi ya
kuma cika zuciyar Larai, ai kuwa ta rufe ta da duka, tare da cewa.
"Bani kudina ko naci iyayen ki da suka karkashin kasa"
Cikin kuka tace.
"Billahil azim, ban dauka ba, idan na dauka Allah ya tsine min!" Ta kuma buge mata baki.
"Kai Larai! Bana son cin fuska. Duk gidan nan kin tab'a jin nace wata Sidrah, ta tab'a daukar
min kudi?
Ko kawai cin zali ta motsa haushin kaza ta sauke kan dami, maza ki nemo wanda ya saukar
miki kuɗin ki."
"Innarmu wallahi ita ta dauka, a duba kayanta mana," inji Sahiyah, ta nufi hanyar dakin aikuwa
Saratu ta bita, tana saka kudin A kwalin Sidrah, Saratu tace.
"Alqur'ani Allah Sahiyah ce barauniyar wallahi, naganki kece kika saka, kudin a cikin kwalinta.
Dan tunda ta dibo ruwa bata shigo daki ba, wallahi kece. Kika ɗauka."
"Kai bani son fitina, Sahiyah dama kece kika dauka?" Lantana ta daka mata tsawa.
Fashewa da kuka, Sahiya tayi tana kallon Saratu, tare da yanko karya ta makawa Sidrah. Huci
kawai Lantana take, fitowa tayi ta mikawa Larai kudinta, sannan ta nufi hanyar kitchen, ta dauko
itaccenta, ta d'aga tare da makawa Sidrah, tsautsayi yasa Sidrah d'ago hannunta zata kare,
aikuwa sai jin wani irin kara suka yi hannun Sidrah yayi.
"Kasss" yana lilo, wata razananniyar kara tayi tare da zuɓewa kasa sumamminya.
Bata san lokacin da tayi wurgi da itaccen ba.
"Innalillahi! Lantana da hankalinki ni da nace ta daukar min kudi bafa cewa nayi ki kashe
marainiya ba, toh wallahi babu ruwa na, can ta matse miki. Ai gaskiyar Saratu ce, domin Sidrah
ta rantse bata dauki kudin ba, amma dake munafukar da ta dauka Yarki ce, kika fito zaki kashe
marainiya.
Toh ba dani ba, domin wallahi bazan yi shaida ba, kuma kina jin rantsuwar da suka yi akan
Sidrah zasu iya sake mace, shine kika mata irin wannan mugun dukar."
Sannan ta fito bakin kofar shashin tace.
"Gudummawa Jama'a, kuzo Lantana da Yarta Sahiyah sun kashe Sidrah, wallahi kuzo kuzo.
Kasheta suka yi, akan Sahiyah ta dauki Kudina, daga magana tace min wai ai taga lokacin da
Sidrah ta dauka, shine na biyo amsar kudina, kawai Sahiyah ta shige dakin da gudu wai zata
dauko kayan Sidrah. Daga nan kawai Lantana tana fitowa bamu yi aune ba, sai kawai ta
saukewa Yarinyar da ko bakin mahaifi bata bari ba.
Wannan rashin Imanin har ina, zasu kashe musu Ƴa."
"Ahha lallai. Lantana kin tabo mai tsada, wallahi zaki gaya musu badai kashe ta kika yi ba? Toh
jama'a nayi nan" inji Iyar gida.
"Don Allah ku taimake ni, wallahi ban da wata manufa, kawai tsautsayin ƙaddara ce ta faɗa min,
na rantse da Allah ban tab'a.."
"Wa zai taimake ki? Mu din? Wallahi bamu isa ba, tab dijam. Tunda kika kasheta sai kisan
yadda zaki yi ita, wallahi babu wanda ya isa ya shiga wannan lamari tab kice zawarci ya kama
ki."
Kafin kace me tuni sun watse, sun barta da Sidrah a kwance. Hannu ta daura akai tare da
cewa.
"Wayyo Allah na, na shiga uku na lalace. Saratu bani ruwa."
Duk sun rud'e, ba tare da sanin su ba, sai ga Malam Haliru. Ya iso, an sami munafukin da ya
kira shi a waya, ba shi ba hatta sauran yan uwan shi sun tawo tare. Gabaki daya Lantana ta
rud'e cikin fitar hayaci tace.
"Wallahi kaga itaccen can, shine na buga mata, ban san zata suma ba, Allah shine shaidana,
ban yi da niyyar cutar da ita ba.
Kawai ƙaddara ce ta faɗa min, wallahi babu wata manufa a raina, don Allah karka."
"Lantana ki fita ki bar min gida! Idan muka dawo na same ki a gidan nan wallahi zan sake ki!
Kuma ba zan dawo dake ba."
Ya fada mata yana fidda wani irin huci. Ran shi yana kara b'aci sosai. Dan ji yaƙe kamar ya
rufeta da duka, sai dai ya san cewa. A madadin ya samawa Sidrah yancin sabon k'iyayyar tace
zata kuma samun matsuguni a zukatar mutanen gidan. Shi yasa yake ganin gwara ya kora
Lantana gidan
Itama Larai Mamman yana zuwa yace ta fita ta bar Mishi gidan shi, domin itace silar abinda ya
faru. Wannan abin ya gigita yaran uwaye biyun nan.
Sabon k'iyayyar Sidrah ya kuma samun mafakar siyasa a zuciyar yaran su. Gani suke sabida
Sidrah aka kori iyayen su mata, dan haka Lawali yaci alwashin sai ya gigita rayuwar Sidrah
yadda aka kori Mahaifiyar shi Larai.
Sahiya itace yake kullace da Sidrah dan sauran yaran sunce babu wani abin da zasu yi dan
abin da Innarsu tayi babu wanda zai iya dauka, suna bayan Baban su. Duk hukuncin da ya
yanke duk daya ne, dake maza ne kuma suna da hankali, ba kamar Sahiyah da Altine ba,
wacce take ta ihu innarta ta dawo.
Sauran matan gidan kuwa tsoro ya hana su, shiga cikin lamarin dan suma gani suke za a iya
korasu gidajen su. Tunda ka iya koran Larai da Lantana.
Tunda suka dauke ta, aka wuce da ita Asibiti, sun samu an karb'e su dakyar, sunyi jum. Kafin
likitan ya fito, yana kallon su yace.
"Zaku iya ganinta, amma ba yanzun ba, don Allah ku kula damuwa tayi mata yawa, sannan
kuma akwai karaya kashin hannunta, zaku iya mata daurin gida, dan yafi kyau. Sannan ku kula
da lafiyar ta, zuwa dare zaku iya tafiya gida."
Ajiyar zuciya suka a tare, sannan suka leka dakin ta window, tana barcin wahala. Duk ta lalace,
"Anya Bara mu maida ta gurin dangin Mahaifiyarta ba? Wallahi ina matuƙar tsoron karsu kashe
masu yar mutane, mu shiga uku. Ga Ma'aruf da muka yi maganar auren shima bai kuma."
"Ma'aruf yana fama da kanshi dan ko kwanaki naje na samu yana fama da hawan jini. Kaga
kenan babu batun aure dole mu tsaya a gidajen mu, don wallahi babu macen da zata juya mu
don ranta, dole mu kula da al'amarin...
Wannan book din na kuɗi ne akan 300₦ haka ma katin mtn 300₦
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu..
Kuyi hakuri! Weekend ne, kuma Uzuri yayi yawa....
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/UenPpAMydbb
𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>
ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮
Bismillah Rahmani Raheem
#Hali zanen dutse
1⃣1⃣
Sosai jikin Lantana yayi sanyi, dan idan zata nutsu nasiha ce Sabuwa take mata, a fakaice har
sabuwa ta gama zata bar gidan Sidrah da take makale a bango tana shashekar kuka, bata fasa
ba. Riko hannunta Sabuwa tayi sannan tace mata.
"Kiyi hakuri! Zaki ga amfanin haka domin shi Mahakurci mawadaci. Ance karyanka ta kare
amma gaskiyar ka da hakurinka ba sa karewa, sai da akasin haka. Kowa yace zai iya sai
kabarshi da iyawar shi. Insha Allah zaki kasance wacce zata ribanci hakuri a duk inda ta taso
miki. Lantana na barki lafiya."
..... Kamar ance Sidrah ta kalli, Lantana ta zuba mata jajjayen Idanun, tana na nazarin yadda
zata ci uban Sidrah a nutse, yadda babu wanda zai fahimci abinda take aikatawa sai ta gama,
dan haka ta yayi gyalenta sai gidan kawarta Aminiyarta, kuma kawar cin mushenta, tun daga
soron gidan take kwad'a sallama.
"Lale maraba, Lantana shigo mana. Ai gidan ne nan. Karki ji kome" dake a fusace take tana
shiga ta nemi guri ta zauna tana huci. Ruwa ta kawo mata daga randan sanyi, sannan ta kurb'a.
"Mai dan wake! Kinji yadda nake jin bakin ciki kamar zai karni lahira! Kinji yadda kirjina take
wata irin bugawa!
Wai Nice za acima mutunci a cikin gidana"
"Kamar ya? Meke faruwa, ince kome ya wuce akan wancan yar rikon ku?" Mai dan wake ta
tambayeta,
Cikin tsannanin b'acin rai tace mata.
"Hmm! Akanta ne, kuma wallahi sai na dauki mataki akanta." Lantana ta faɗa tana hura hanci,
"Dadi na dake baki da hakuri, me ya faru kin barin a duhu?"
Nan ta gyara zamanta ta shiga mata bayani, wani dogon tsaki taja sannan tace mata.
"Amma wallahi babu sakarya lamba daya. Akan yar da kika haifa zaki zauna kika ihu. Toh bari ki
ji, toh bari na gaya miki, babu duka babu zagi, wai ma Lantana duka duka nawa Sidira take da
ake baki tsoro akanta?
Yarinyar da ke kanki kin san ba kome bace a gurin ki da gurin sauran mutane, dan banten
Ubanta daura mata talla, idan bata sayar ba, a bakin abincin ta, dole ta fara karuwanci naga
yadda za a dauke ta abawa Bature ita bayan ta zama karamar karuwa."
Zaro idanu Lantana tayi tare da cewa..
"Ke ruwa min asiri wasitira wa alaika z rabani da abinda ya turewa buzu nadi, ke kina tsammani
zasu bar ni je dangin Ubanta, bayan basu daurawa yaran su talla, ai zasu cinye ni d'anye. Ke
dai Zan iya zabtar da ita sai ta rasa inda yake mata dad'i."
...."ji sakarci! Haka shine mafita" inji mai danwake,
"Bafa zai yiwu bane! Domin na tab'a kuskuren hakan malam ya kusan sake ni, da girmana gotai
gotai, ban zauna a d'akina ba. Nace sani zawarci gida ai babu tsari, kawai zan a zabtar da ita
dai amma talla kan akan aurena ne dan duk yaran gidan basa talla."
Shiru suka yi suna niman idea, kansu ya kwance,
"Toh kawai ki cigaba da a zabtar da ita domin na lura mutane basu san cewa kina kokari ba, ki a
zabtar da ita a boye a gaban mutane ki sota yadda babu wanda zai fahimci ainihin abinda kike
mata!"
Shiru suka yi kafin suka kuma fashewa da dariya, ana kuma cigaba da hada rigima sosai.
***
Jigawa dutse.
Aiki suke na karyawa masu wanke wanke suna aikin shi. Latifah ta kalli. Hajiya Uwani tace
mata.
"Ummin mu! Ko zamu saka curry a wancan kwai din, sabida yana karni kuma kin san bawai kan
agric bane na kazar gida ce!"
"Saka mana In-law, gran Son baya son karni ko? Jiya ma miyar kukar dare an saka curry sabida
karni, girkin rana ma, curry. Za a haifa min yellow miji ko yellow kishiya"
Shiru tayi cike da kunya, tana aikinta, dan Latifah ta ki yarda da gulmar gidan duk abinda ake
bata shiga, wani lokaci ma zaka same ta tana kallon tashar girke girke. Idan kuma Hajiya Uwani
tana gida zasu fito kitchen suna girka abinda zasu ajiyewa bakin su. Dan Latifah bata rabuwa
da baki. Suna cikin haka. Hajiya Uwani ta shige d'akin sabida wayar da ake kiran ta gashi yaran
suna islamiyya, kamar wacce aka kora Latifah, bayan wani lokaci suka dawo a tare abun
mamaki. Sun samu an kwashe fiye da rabin cincin da suke soyawa, kuma ga mutane a tsakar
gidan,. Fitowa Hajiya Uwani tayi tare da tsayawa tace.
"Yau anyi Kuskuren tab'a, wallahi duk ranar da na kuma saka abu ina girki na tashi wata
karamar mara kunya ta shiga ta diba min zan bata mamaki domin sai ta tozarta a cikin gidan
nan. Na gaya muku wannan shine farkon kuma karshen na kuma."
"Latifah! Ina kike tawo kika bar daki a bude an shiga tare da kwashe min kudin ajiyar
mutane da aka bani, wannan wani irin sakarci ne?" Wani irin shiru ne ya gifta a tsakanin su, ran
kowa ya b'aci, dan haka ta nufi cikin gidan su. Ta kalli kofar ta tabbas yanzun aka debi kudin ta
shigo tayi uzurinta tare da manta key a jikin kofar, tana shiga dakin taga har buhun shinkafa,
aka bude sabo dal, aka diba. Abun ya bata haushi dan haka ta zauna tare da fashewa da kuka.
Ta rasa waye yake musu wannan renin hankali.
Shigar ta uwar dakin ta, ta samu har wardrob ɗinta da kuma karamin akwatin kayanta, a tsora
ce ta fara sauke kayan ta, tana duba gold ɗinta, ajiyar zuciya ta sauke tare da kara boye shi,
dan tasan Allah yana sonta ne ya bar mata shi a boye. Tun da ta samu ta boye cikin gidan da
bata koma ba kenan, karshe Ummi ce ta karasa aikin aka kawo mata nata, amma sauran yasha
ruwa..
Wannan abun dake faruwa, ya sanya kowa ya fara kaf kaf da kan shi, cikin gidan ma
basu yarda da kowa ba, musamman Ya Hindatu, dan anfi zargin ta.
"Wallahi Hajiya ban tab'a daukar abun wani ba, kawai ranar ma tsautsayi ne, matar
Ghali naga ta fita da abu a hannunta, kuma nafi zargin itace take musu." Inji Ya Hindatu,
"Ke nima na jima ina zargin Ummita, domin idanu ta,baya zama guri guda, shi kan shi Ghali
jiya ina jin yana Jajjen ana kwashe mishi kudi ko wani abu, jiya suke hira da dan uwan shi na
fito ban dakin."
"Amma babu wanda zai yarda ai! Sabida bata yi kama da Barauniya ba!"
"Aikuwa mama wallahi zaki ja mana koran kare! Ki rufa mana asiri, tunda bamu da gidan da
zamu zauna baban mu ya gudu abin shi." Shiru Hasnah tayi tana kallon uwarta dan iya gaskiyar
kenan. Gyada kai tayi.
Aminah matar Bala ta shigo, suka kafa gulma. Suna haka Raliyah itama ta shigo, dan su
nan dakin su. Hafsah matar Muhmood, ta shige dakin Amarya, suka fito tare, zuwa dakin
Hajiya, wato idan kaga irin gurmin da ake bugawa.
Sai dai muce idan ta fito ta tsaya iyakan su.
***US.
Mika mishi takalmin shi da agogon shi aka yi, yana me b'ata rai kamar an zage shi.
"Yallabai kayi hakuri! Amma an tabbatar kai ne ka duke su, kuma badan Lauy yazo da wuri ba,
tabbas babu abinda ba zai faru ba, dan zasu iya mika ka ga kotun Unguwa. Kai da mahaifiyarka
take kokarin ganin ka samu damar shiga Whiter house, kaga dole a kiyayye abinda zai b'ata
maka suna. Dan ma Mahaifiyarka bata ƙasar."
... A sanyayye yake tafiya yana gyara zaman agogon shi,kawai sai jin kara akayi, tare da nufo
kan shi, dole Maza body guard din shi suka shiga musayar wuta, tsakanin su, tunda aka saka
shi a motar suka bar gurin, domin motar irin wacce bullet baya fasata ce.
Da gudu suka bar gurin, ana cikin haka sai kamar wanda aka hankado shi, juyawan da
maharan suka yi akan shi. Ai kuwa suka sake bude mishi wuta,
Cikin rashin sanin madafa, harbin ya same shi, a kafadar shi. Sai da motar ta nemi kwacewa
a hannun shi me ya kawo shi nan din nan ya faɗa, cikin son tsira da ranshi yana kallon fuskar
mutane, tare da cewa. "Sai na kashe ku!" Yaja motar da gudu kamar wanda kamar a cikin shirin
film fast and furious, take gudu da motar, yayinda Yan sanda suka rufa mishi baya, suna bin shi.
Sai da suka bar cikin garin sannan yan sanda suka daina bin shi.
Domin ya yanki cikin daji, ne zubar jinin da ya dame shi ya sashi kashe motar, tare da hakki.
Zaro wayar shi yayi tare da ya kira layin Max. Nan ya gaya mishi inda yake yazo ya dauke shi.
Bayan wasu mintuna, ya iso yana zuwa ya fitar da Aamil, sannan ya zubawa motar fetur
ya kona ta.
"Me yasa?"
"A'a, akwai matsala domin zamu iya fukarta barazana ga yan sanda, dan haka muje kaga likita,
domin akwai harsheshi a jikin ka, kuma idan ba a cire ba akwai matsala dole za a cire maka
shi."
" Na ga fuskar shi, wanda ya harbe ni, dole na dauki fansa ta. Meye matsalata da su. Waye
yake son ganin bayana,!" Yana magana cike da taurin kai, tare da jin wani irin azaba, amma
taurin zuciya. Da mugun gudu suka bar dajin, kafin su isa yan team din su, sun kira likita. Ana
zuwa suka shige dashi cikin gidan shi.
.... Tun da ya shiga ƙungiyar gyara motocin, ya zama mara mutuncin kamar me, kuma
bai da hakuri na miskala zarratin, kungiyar su a bayyane ta gyaran mota ce amma a zahirance
yan daba ne na bugawa a jarida. Basa kisa amma kuma suna illatar da mutum.
Tunda ya shiga cikin su ya zama masifaffen sama da baya, kangararre wanda babu wanda ya
isa ya lankwasa shi. Kuma idan ya saka kanshi abu ko su basu dakatar dashi.
. Shi yasa yanzun duk wanda yayi Mishi babu yake cin uban shi, a yanzun yake bakin cikin me
yasa tun farko bai ci uban yan gidan su ba, da suke rena mishi hankali, sai yanzun ga damar
yayi abin da yake so babu su a tare dashi. Kallon shi Jerry yayi sannan yace.
"Zan gane shi." Dan haka yana rufe baki ana kiran wani mutum, tsoho, dan kasar China. Aamil
ya shiga gaya mishi kamanin mutumin, ana cire mishi harsheshin cikin masifar zafi tare da
mugun taurin kai yake juya kan shi , zufa na karyo mishi yana fadar kamanin mutumin,ana cire
harsashin, yana sauke ajiyar zuciya bayan ta gama fadar yadda mutumin yake, sannan ya
bingire ya fara barci sabida alluran barcin da aka mishi.
"Lallai Frank ya kwaso bala'in dole mu dauki fansar abokin mu, Duk tabargazar da muke bai
tab'a shiga ba, amma mara mutunci ya harbe shi bari ya tashi.
----
Haka kawai yaji yana son komawa inda ake harbin, juyawar da zai yi ya kama zubda jini ta
bakin shi, tare da rike kafad'arshi, yana cewa.
"Ku mai dani! Inda ake harbin ku mai dani."
Wani irin zafi yake ji a cikin ranshi da kafadar shi, ganin yadda yake rike gurin, yasa P.A ya
shiga bude rigar, gurin ya tara jini kamar zai fashe, da bai fita ba shine shi kuma yake aman
jinin, abin da ya kuma firta su kenan, domin a sanin P.A din Maman shi, a duk lokacin da
wannan yanayin ya bayyana, toh akwai matsala a kwayoyin halittar jikinsa, yana aiki kenan bai
cika jin haka ba. Sai dai a cikin shekaru bai fi sau biyu ko uku ba, yake zama haka, amma ko
lokacin da yake yaro sun sha wahala dashi sosai domin sai da suka kai shi India gurin masu
maganin gargajiya....
Akafta
Wannan book din na kuɗi ne akan 300₦ haka ma katin mtn 300₦
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu..
[11/13, 8:06 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/sWKmMfn3gbb
𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>
ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮
Bismillah Rahmani Raheem
Har abada wutsiyar Raƙumi tai nesa da kasa
🤩
#Manta baya
1⃣4⃣
Sake daya harbul yayi a kafa, daya kuma a hannu, dole suka yasar da bindigar, yana zuwa ya
dauke daya da mari, dayan kuma ya dake shi da bakin bindigar din.
Ihu suka saka tare da komawa gefe, jikin su na makarkyata.
Takowa yayi kuma yi dai dai wayar dayan su na kara, yana dauka ya saka a kunne yace.
"Xsezza! Kun kashe shi?" Aka yi tambayar a kagaucce.
"A'a sai dai ni na kashe su, Banza kawai!"
Kawai ya sake musu harbin cikin nutsuwa, dan abun ya bashi haushi. Wato ma so ake lallai a
ga bayan shi, sannan yayi ta dukar su da kafa, kafin ya juya ya bar su a kwance cikin jini.
...... Dawowa yayi ya dauki wayar su ya dauki Numbern da aka kira , sannan ya juya tare da
barin gurin. Yana jin a ranshi yayi ta cin Uban yan iska da suka so kashe shi zai tayi har sai
yaga bayan banzaye.
Bayan tafiyar shi, sai ga Yan sanda. Suna zuwa suka kira motar asibiti, zuwa asibiti.
---
Babbar jirginta wanda ya kasance nata da d'anta ne ya dauke ta a filin tashi da saukar jiragen,
na cikin ƙasar. Sannan suka taka zuwa gaba inda karamin privet jet ya kuma daukarta zuwa
cikin gidan ta, sabida gudun kar a kai mata, farmaki.
Tafiyar minti goma kacal ya isa dasu. Wani katafaren Mansion wanda yake da kusan girman
gari guda, dan yakai girman wata kauyen, gidane a tsakanin wasu tsauni na ciki garin sannan
gidan yana kudu da bakin teku.
Body guard dubu daya da dari biyar ne suke gadin bakin tekun, tare da manyan bindigogi,
sai ta Yamma da tsaunin, (mount wato) shima akwai body guard dubu daya da dari tara, da
musu duba sararin samaniya, sabida kota kwana. Sai ta arewancin gidan, akwai masu gadi
suma sama da ɗari huɗu, sabida akwai karamar gurin shakatawa.
Sai bakin gate din shiga Mansion din, inda aka girke masu tsaro da ta kwana, sannan duk
bayan awa daya ana sauya masu tsaron, sabida kula da abubuwan gidan.
Ta cikin gidan kuwa, gidan sama ne mai dauke da dakuna bakwai, tare da manyan manyan
falo uku, a sama. Sai a kasa dakuna biyar ne dauke da falo hudu. Falon farko mai dauke da
wasu. Wasu kujerun alfarma na royal. Masu matukar kyau da daraja. Sannan wall din falon na
katako ne.
.....falon babba ne na fitan hankalin wanda yake dauke da wasu manyan manyan, frame na
hoton Mss William da Allison William. Gefe guda wani tsohon attajiri ne cikin shigar Alfarma.
Gefen shi wata mace tare da matashiyar budurwa. Wacce ta kasance Mss William. Dan gaba
kadan hotonta ne na aure Ita da wani mutum, suna sanye da Wedding dress. Murmushi suke
baki dayan su.
Gefe da gefen falon cike yake da manyan wall labrary. Me dauke da Littafan. Tare da
wasu tarkacen da ake kawata falo yayi kyau.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 13