wa namijin,.tsaki
yaja mata tare da daka mata tsawa.
Ya nuna mata hanyar fita, da sauri ta bar dakin, tana tura mishi baki.
Koda ta shiga cikin gidan kai tsaye cikin gidan su ta shiga tayi wanka sannan tazo tana
fesawa uwarta, Nan itama ya tashi ta kai gidan su Azumi, daga nan dai magana ya fara yawo
har waje, Lantana bata sani ba, matan gidan sun ninke ta bai bai.
Sai da maganar ta isa gidan mai danwake sannan itama tazo suka saka Sahiyah a gaba sai
Asibitin wani inyamuri mai suna ogomu, ana zuwa aka ce ciki ne dan sati bakwai za a iya cire
mata shi. Aikuwa ta dawo gida ta kwashe kudinta tsaf, sannan ta nufi asibitin. Likita da yaga
Sahiyah ya shiga lashe bakin shi ne an biyan kudin suka shiga cikin dakin da ake burge cikin.
Shegen kwaro, talle yar banza yayi sai da ya darjeta bayan ya zuba mata alluran barci, yayi
yadda yake so da ita, sannan ya tura mata karfen ya ciro dan tayin, ya zuba a wani kawo, sosai
ya burge cikin sannan yayi mata alluran kashe zafi da wanda jini ba zai zuba ba, ya fito tare da
saka wasu Nurse suka fito da ita.
... Cikin tashin hankali Lantana take kallonta, dan ji take kamar Yarinyar ba zata rayu ba, ga
kuma tsoron mijinta kar yasan abin da Sahiyah tayi ya kore
Wannan book din na kuษi ne akan 300โฆ haka ma katin mtn 300โฆ
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu..
[11/13, 8:06 PM] My Zahrah: ๐๐๐๐ ๐๐๐๐
<๐ฒ๐ ๐๐๐๐ ๐ซ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐ฒ๐๐๐๐๐>
https://my.w.tt/aprwHkaoibb
โ๐ธโค๐ธ๐๐ธ ๐โ๐๐๐ผโ'๐ ๐ธ๐๐๐...
แด๐๐ข_แด
๐๐ฆ๐๐ฎ
Bismillah Rahmani Raheem
_Gaskiya kun sanyawa Lantana Idanu. Ba ita daya ba hatta Oga Aamil
Fatan Alkhairi
Team Lantana!_
'''Sadaukarwa gare Black Women na Online baki daya
๓ฐขช
tare Da Jarumar ku! Sidrah
๐
.Yar
baka mummuna Mrs Aamil Insha Allah black and white couple
๐คญ
'''
#ita ce mafarkina
1โฃ6โฃ
"Adama baki tunanin wani abu ya same ta, idan ta mutu da?"
Tsaki mai dan wake tayi sannan ta zauna tare da sauke ajiyar zuciya, tana faษin.
"Da ban yarda da nan ba, ai ba zan kawo ki ba. Wannan yadda take alluran barci aka mata, dan
haka ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru da ita."
Gauron numfashi ta sauke tare da gyara zama tace.
"Mai dan wake, yarinyar nan da ษaukar magana take, ta rasa me zata dauko min sai cikin shege
kuma nasan yanzun haka maganar ya karade cikin gidan mu.
..... Amma zunzurutun bakin ciki da hassada aka min shiru, ana kallona dashi duk sai na ci
kutumar Ubansu dani suke batun."
"Eh mana, ai abun ya jima ya a faruwa sannan maganar gaskiya, yaran gidan ku, duk suna
bin mazan da suke cirani a kofar gidan ku, wanda ya gaya min ba zai musu karya ba, dan haka
ki ja mata kunne kafin wani abu ya kuma lalacewa babu ruwana." Inji Mai dan wake,
Sai da Sahiyah tayi awa uku sannan ta farka, da ciwon ciki. Allura aka kuma mata, sanan
suka sallame ta, suna dawowa gida Duk Lantana tana cike dasu.
Ruwan wanka, ta daura ta gasa yarinyar sosai, sannan ta dauko mangul ta jika mata ta sanye,
bayan ta kwashe kayan jini ta wanke.
Kafin ta daura musu, abincin rana, dan tazo ta samu Sidrah ta haษa mata wuta, tare da
wanke wanke.
Suna shigowa ta bata kuษin kayan miya, yanzun haka ta wanke tana kirbwa a turmin ne.
Tana idarwa ta kwashe a cikin tukunyar, ta d'aga labulen d'akin Lantana tace mata.
"Innah!"
"Uban me kike d'aga mana labule munafuka." Inji Sahiyah,
"Ke bana son hauka, Sidrah juye wancan manjan a cikin miyar ki dauki naira hamsin ki sayo kafi
zabuwa ta Ashirin dunkule talatin."
Gyada kai tayi tare da fita da sauri, tana aiwatar da abinda aka sakata.
"Innarmu! Yanzun kina nufin nan da wata biyu zaku aurar da Sidrah?" Inji Sahiyah,
Kwafa Lantana tayi tare da jin haushin abinda yake shirin faruwa, kallon Sahiya tai sannan tace
mata.
"Wani shegen ne kika bashi kanki ya dirka miki ciki?"
Uwar ta tambayeta tana me hararar ta.
Cikin rashin kunya, wanda ya bi jikinta, tace mata.
"Toh ai bani daya ce, Zabaina da takiya, duk suna tare da Lawali da Karibu,"
Buge mata, baki uwar tayi sannan tace mata.
"Dan Ubanki idan na kuma ganin ki, a soron waje sai na mutsike ki."
"Toh ni wallahi sai dai ayi auren nan dani" ta faษa tare da zubda kwalla, tsaki uwar tayi dan
tasan kome zata yi tunda aka ce auren na Sidrah ce babu wanda zai hana sai Allah. Dan haka
ta shareta bata kuma bin ta kanta ba, karshe ma girkin ranar Sidrah ce tayi sabida idan ta haษa
abu zata gaya mata.
Har ta gama ta ajiye a gefe tana kallon suka ci sannan suka zuba mata jagwale, tare da
kanzo. A binka da wacce ta tayi girkin, tuni taji abincin yayi mata zio (
๐คฃ
Black Girl in kitchen)
Tana gama cin abincin ta wanke tunkuyar aka mai da na dare, nan ma itace tayi kome
tuka tuwon ne, Lantana ta amsa.
.... Cikin gida basu san cewa an cire cikin jikin Sahiya ba, har kusan kwana uku, ana ririta
alamarin. Wasa wasa sai da maganar ta kai sati biyu sannan mazan gidan suka ji labarin, Allah
ya kub'utar da Lantana da Yarta, aikuwa aka kwashe su zuwa asibiti, binciken Sahiyah aka ce
babu ciki.
Da farin cikin ta, ta koma gefe. Sannan aka kuma yiwa Takiya, take aka samu, sai Zubaina Allah
ya sota tana haila, ai kuwa tun asibitin ake dukar Takiya, ta Kum dage ai ba ita daya bace.
Dukkan su uku.
(Ta fashe da
๓ฐข๐๐คฃ
)
Dan haka suna dawowa gida, aka ษauki matakin farko shine koran su Lawali, bayan Mahaifin
Takiya ya sanya shi a kotu, sabida na farko yaci amanar su, na biyu ya lalata tarbiyyar yaran su.
Na uku dole ya amshi auren takiya, ko yana so ko baya so.
Bai yi taurin kai ba, sabida yayi alakari da suna da Yan uwan masu kuษi idan yaja zasu iya rufe
shi. Ita kuma Sahiyah,aka hadata da Karibu, Zubaina kuma wani Yan uwan su ta gurin Uwarta
yace yana sonta dama, shine aka saka bikin da na Sidrah.
Dan haka Lantana ta shiga rashin hankali, sabida basu tab'a tsammanin haka ba, kuma da
tayi magana, Malam yace sai dai ta bar Mishi gidan shi.
Sanadin wannan al'amarin ya sanya suka fita harkan Sidrah, domin basu da ma lokacin ta,
takan su suke ma, gefe guda suka Lantana ta sake mata girkin rana da na karyawa.
Tun tana shirme har ta kai idan tayi zai ciwu, sabida tana daukar gyaran idan tayi na yau ya
samu matsala dukarta Lantana take tare da gaya mata gidan da zata shiga ba karamin gida
bane kuma abincin su ya ci kaniyar na gidan da take yi yanzun.
.idan da wuya da azaba. Zata yi kisa, toh da gawar Sidrah ta tube, amma sai Allah ya daura
mata wani irin juriya da hakuri, a da idan suka mata kuka take, a yanzun babu kukan sai dai
kuma. Bata tab'a faraa ko wani abun farin ciki kaga dariya ko murmushi.
Bata cika shiga damuwar kowa ba, nata ya ishe ta kuma bata tab'a kawo karar kowa, balle
yanzun da gidan kowa yake kokarin b'oye damuwar shi. Gefen Lantana kuwa, tana hada
Sahiyah da magungunan mata, tare da wanda zai matseta.
... Gyara sosai takewa yar nata, tare da mantawa da wata Sidrah, sabida tace, ba zata bata
kudinta a koro ta ba.
(
๐ค
Ni kuma nace haka yafi ko? Domin idan aka dura mata an san ranar da Oga Aamil zai zo
ne?).
***
"Ranka shi dad'e! Ga me zanen yazo!" Kallon shi Allison yayi tare da nuna mishi guri ya zauna,
sannan yace mishi.
"Ga hoton ka cire min ita!"
Gyada kai yayi, mutumin ya fara fitar da kayan aikin shi, ya ajiye katakon da kuma kayan
zanen. Lumshe idanun shi yayi tare da cewa.
"Ka fara!"
Bude idanu yayi yana kallon mutumin yana zana hoton laptop din, ganin yayi kamar ya
rage mata, wasu abubuwan rufe laptop din yayi. Mutumin ya kalle shi.
"Me yasa kuma?" Inji Mom tana saukowa daga sama.
"Mom ya rage mata abubuwa dayawa, ita baka ce haka kwayar idanun ta, tsakiyar baki ne mai
dauke da farin digo, gefen idanunta fari ne kal, Mom nayi mafarkin ta. Baka ce Sosai. Hakorinta
farare ne. Mom yarinya ce, karama tana da gashi bak'ikirin, dube yadda ya zanata."
D'ago kansa yayi, sai yanzun ya fahimci, wacce aka zana, Emily ce, haushi ya kama shi.
"Kuyi waje da dan banza, ku bashi ladan aikin shi."
"Son ka bar wannan shirmen, mafarki ba gaskiya bane, kuma yadda kake rayuwarka da
yadda kake tunanin zaka iya zanata a same ta, ba zai yiwu ba. Sabida ita kirkira ce, kai kuma
kana raye."
Kallon Mahaifiyar shi yayi, sannan ya mai da idanun shi kan laptop din shi, ya dauki inda
yake aikin zanen ya fara zana hotonta, yana faษin.
"Zuciyata ta ce min kar na bari, ba soyayya bace, kawai tausayi ne. Kukanta yana hanani barci,
damuwarta kullum kara ta'azara yake, ina ganin ta a tunanina na, ina jinta a cikin jini na, tana
yawo a fitar numfashi na, koda banyi katarin haduwa da ita ba, naji a jikina zan so Yesu christ
ya kawo mata dauki."
Yana gama fadar haka yayi daidai da gama zanata,tana zaune ta kifa kanta tana kuka, tare da
rungume kafarta.
Abinda ya rubuta a kasar hotonta *_Ke ba mafarki bace gaskiya ce ke_* , ya sanya Emily
wurgi da Laptop din, tare da fashewa da kuka tana fadin.
"Allison! Meye amfanin rayuwata!"
Riko hannunta yayi cikin sigar rarrashin ta yace mata.
"Ke ni fa wasa nake ita yarinyar ai kirkira ce inji Mom, ke kuma ba gaki a gabana ba, dole dai ai
zan aure ki, kuma muyi Shagali me dadi..bar damun kanki da wata zanen hoto."
Da haka ya lallabata, suka rabu lafiya, Mahaifiyarshi sai dariya take, tare da jinjina mishi
sabida lokaci guda ya tsarata kuma ta tsaru, kuma suka ci-gaba da hidimar su.
Zana hoton mafarkin shi ya fara zame mishi jiki, domin har kafaffen sadarwan na intanet
yana daura hotonta, wasa wasa ya samu mutane suna bin kowanne posting din shi, tare da
niman ya dauke su aiki.
***
Jan kunamar bindigar yayi ba tare da damuwa ba, ya sakewa Benni a kafar shi.
"Ba a haife ni domin kawo karshen Labarin ba, an haife ni ne domin farkon labarin, kai waye da
zaka yi yunkurin kashe ni!"
Ya kuma sake motsawa ya sake mishi harbi.
"Toh kai waye?" Inji Benni.
"Ni kake tambaya? Lallai aiki ya same ka, sauka lafiya." Ya zuba mishi harbi a goshi
sannan ya saka kai ya fita abinshi.
..... Bayan mins biyar da faruwan Al'amarin, sai ga Aamil yazo koda ya shigo ya samu ai abin
har ya faru, dukar kasa yayi sannan ya fita kafin a kama shi.
Shiru yayi, bayan ya isa gidan shi. Dan kwana biyu nan baya zama a cikin gari a makarantar
yake zama, sabida karatun shi. Kuma kullum fuskar shi a tushe take, sabida abinda yake
faruwa, dan ana bibiyar shi sosai. Shi yasa yan kungiyar shi suka ce ya bar zaman unguwar ya
koma cikin makaranta, haka zai sama mishi tsaro, tunda mutanen basu san cewa bashi bane.
***
Dutse.
Ana ta hidimar sunan Latifah, wacce ta rike Hajiya Uwani a matsayin uwarta,, duk da surukarta
bata so haka ba, sai dai ta fahimci ba zata tab'a juya Ali da yarinyar ba, sabida ra'ayin su daya
ne.
Tunanin su daya ne, domin daga baya ya sawun matar shi, ya tare a jikin Ummin Abdus
Samad, dake mace ce da bata damu da kowa ba, sai gashi ana mata kallon ta mallake Ali da
matar shi, tun uwar tana dauka karshe dai ta watsar dan kome zata yiwa Hajiya Uwani ba zata
tab'a kulawa ba, dan ko da Hajiya Surayyah ta haihu, Itace akan ta, da farko haihuwar taso
matsala. Itace a kanta har ta haihu karshe babyn bai zo da rai ba, ga zubar jini. Da wasu
abubuwan marasa dad'i, dole Alhaji Ma'aruf ya saka aka juyar da mahaifar, sabida yace bai ga
amfanin wahalar da kai ba, tunda yara goma nan dai sun wadatar da ita me take bukata..
Hajiya Amarya itama ta sauka lafiya, inda ta sami d'a namiji, aka sanya mishi Adam, suna
kiran shi Aasim.
Tun da ta haifi Yaron ta kakkaro rashin mutuncin, kana mata magana zata ce ita ta haife
Uban gida..
Hidimar sunan yayi sosai, Latifah ta haifi mace , sauran matan duk suna da ciki, kuma fatar
su ayi hidimar da taci Uwar na Latifah, kuma dadin dawa, Iyayenta da yayunta suna da rufin
asiri, shi yasa da aka tashi yin abin sai aka yi tuwon girma miyar nama, sai dai kashe a cikin
kayan fitar sunan da aka kawo mata daga gidan su, an sace turmin Super wax..
Wannan book din na kuษi ne akan 300โฆ haka ma katin mtn 300โฆ
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu.
[11/13, 8:06 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/XNggHNp0ibb
๐๐๐ ๐๐๐๐
<๐ฒ๐ ๐๐๐๐ ๐ซ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐ฒ๐๐๐๐๐>
โ๐ธโค๐ธ๐๐ธ ๐โ๐๐๐ผโ'๐ ๐ธ๐๐๐...
แด๐๐ข_แด
๐๐ฆ๐๐ฎ
Bismillah Rahmani Raheem
#Tarzoma
1โฃ7โฃ
Wani irin takaici ne ya kuma kama Raliyah, dan tasan Tabbas Ummita ce ta dauka, amma idan
tayi magana za ace dan basa shiri ne yasa ta share zancen ta cigaba da jajjantawa mai jegon.
Har yamma ana niman zanin ba a gani ba.
Karshe abin ya zama gulma, kowa ya shigo sai ya san an zabga satar rashin kunya, a cikin
gidan. Dole shakku ya kama shi domin al'amarin sata ba wasa a cikin shi. Yarinya za a kira da
Aafreen.
Ba a kuma mamaki ba, sai da dare yayi aka yanke cinyar Ragon suna, anan ne fa kowa ya
yi caa akan yankar namar, da gari yawaye sai aka tsinci namar a gurin wanke wanke, kamar
abune yaja, dan anyi surutu tare da fatar Allah ya tona asirin barawo.
..... Gidan ya koma ko dan abu ka ajiye kafin zuwa anjima, zaka niman karasa kuma an
rasa waye ke wannan aikin, domin Ummita ta rufe kofar da zaka zarge ka, a hankali har aka
gama hidimar sunan. Ana cikin soya namar ragon Ummita tayi ta shiga da fita, har dai karshe
wata Kanwar Mamar Latifah tace mata.
"Ke! Kar na kuma ganin kafarki ' a nan dan kinyi na farko kinyi na ฦarshe, dan na lura baki da
kunya, ina zaune anan yar banza mara zuciya sai tsame nama kike. Na kuma ganin ki tunda
baki da aiki sai na sata yar banzan mara kunya, ki je can Allah zai tuna miki asiri."
Simi simi tabar dakin, ta koma nata, tare da jin mugun kunya.
..... Kallon takardun gaban shi yayi, sannan ya d'ago kai ya kalli Hajiya Uwani,.kafin ya
saka hannu ya nade takardan yana sauke numfashi,.kafin wani lokaci yace.
"Saura kwanaki ฦalilan, kuma ban san ya zanyi da yan uwana ba, ban me zance musu ba.
Kuma sun gaya min yarinyar tana cikin kunci. Ya zanyi? Su kansu sun matsu da a d'aga
yarinyar daga cikin gidan, ko haka zai sama mata daraja da sukuni.
Ni kuma wannan mutumin banzan ne nake gudun kar yazo ya cutar da yar mutane,
yarinyar da bata tashi a gaban iyayen ta ba,babu amfanin mu hadata da wanda zai
wulakantata."
Murmushi Hajiya Uwani tayi sannan tace mishi.
"Ni kuwa nake ganin kamar zai zo, dan ina jin haka a raina zai dawo da izinin Ubangiji, kawai
abin da zamu mishi Addu'a, shine matakin da ya dace mu dauka. Amma Insha Allah."
Cikin zakuwa yace mata.
"Kuma kina ganin idan yazo zai amshi auren Yarinayr da muka bashi?!"
"Wannan kuma sha'anin Ubangiji ne, amma nayi imani da Allah ba zai ki amsar ta ba,!"
Shiru yayi kafin yace mata.
"Am bored"
"Dame fa?"
Ta tambaye shi, "da halin Aamil, baya gudun zuciyata, duk abinda zai jefa ni cikin damuwa shi
yake aikatawa. Yanzun don Allah meye amfanin haka? Meye ribar abinda ya aikata, duk cikin
y'ay'ana shine ya fita. Zakka ga baki daya abun da ya gadama yake aikatawa kuma ko nayi
mishi magana baya kulani."
"Sabida kai ka bada goyon bayan a cutar da shi." Ta faษa tare da tsare shi da idanu.
Girgiza kai yayi cikin damuwa sannan yace mata.
"Ko kadan bani da hannu akan abin..."
"Me yasa baka nime Mahaifiyar shi ba? Ka tab'a bashi labarin mahaifiyar shi? Ka tab'a gaya
mishi cewa soyayya ya haษa ku ba k'iyayya ba?
Abin da bakin ka ya iya furtawa shine dukiyar ta da yake hannunka, me yasa baka tab'a
tunanin cewa dole wata rana zai bukaci Mahaifiyarshi?"
"Me yasa kuke zargina da nuna a halin ko in kula akan shi?" Ya tambayeta a gajiye,
Murmushin gefen baki tayi sannan tace mishi.
"Me yasa kake tattalin Hajiyarka? Ka tab'a tuninan shima yana da burin tattalin mahaifiyar shi
haka?
Me yasa baka tab'a cewa Hajiya tabar gidan ka ba, kai ko Hindatu tabar gidanka? Baka
tab'ayin haka ba, amma kana blaming Yaron da ya taso a karkace, tare da tallafawar ka,
sannan kayi tunanin zaka mikar dashi, how? Toh a ajiye a gefe yayi laifi ka hukunta shi sai ka
kashi a jikinka yadda babu wanda zai iya cutar da shi, ka nuna musu shine farin cikin ka, toh ka
nuna wofantar dashi a gaban kowa, ba dole ya wofatan da duk wani abinda ka kawo mishi
domin cigaba ba.
Kana ganin kamar muna takura maka ne, amma ni a tuninan kaine ka lalata mishi
tarbiyya ba kowa ba, da ace ka nuna mishi gata baka iya sakewa da kome amma sakewar da
zaka yi dashi yafi na yadda zaka yi da kowa toh babu wanda ya isa ya raba maka hankalin shi
da kai.
Amma yanzun an gama b'ata kome tsakanin ku, domin babu boka babu malam kawai tsantsar
azabtar dashi da akayi yasanya baya tausayin ka, baya jin kanka.
Ka nutsu da kyau mana, ka tab'a kama shi da laifi? Sai dai ace kama, yayi laifi baka kama
shi dashi ba. Karfi da yaji an mai da shi mai laifi ba tare sanin ka ba, sannan yau kayi tunanin
zai bi ra'ayinka ko sau daya ka tab'a mishi adalci? Baka tab'a ba, wallahi nayi imani da yau
Hauwa zata zo, taga yadda ka wulankata mata d'a zata ce dama sabida dukiyarta ka damu da
ita, gashi bayan bata nan, ka gaza rike abin da tabar ka, kai Hajiyarka bata kaunar wata mace
ta juya ka, amma ta gaza samawa Yaron da aka rabashi da Mahaifiyar shi a tsumar goyo."
Cikin zafin rai ya kalle ta, sannan ya kauda kan shi yace.
"Ba raba ta akayi dashi ba, itace ta gudu tabar shi."
"Ba guduwa tayi ba, koranta akayi tare da barazanar za a kasheta idan ta kuma dawowa
rayuwarka da ta yaron." Cikin rawan jiki ya d'ago zai mata magana, ruwa ta zuba mishi yasha,
sannan ya cigaba da cewa.
"Sam bata da manufar tafiya, sai dai masu gidan sun juya maka akalar rayuwarka, ba tare da ka
fahimci cewa akwai kuskuren da ka tabfka ba.
Zaka iya kallon kowa da ido biyu, amma mafi girman gani da idanun zuci ne, sabida shi
kullum a bude yake asalin idanun mu kuma a rufe suke.
Insha Allah Aamil zai dawo soon."
Daga haka tayi feccewar ta, ta duba yaranta ta kuma musu addu'a, sannan tazo ta kwanta.
Shiru yayi yana kuma yarda da batun ta, tare da jinjina karfin yarda da batun su, itace mutum
na uku da suka bashi damar ya bincika abinda ya faru da shi. Kuma yana shirye ya bincika Sai
dai matsalar, yadda zai shawo kan kome kafin lokaci ya kure mishi.
Hau saman gadon tayi tare da ce mishi.
"Me kake tunawa?"
Furza da iskar yayi daga bakin shi, sannan ya ce mata.
"Toh yanzun idan naje gurin Hauwa ta ce zata dawo fa?"
Dariya ta saka mishi sannan tace mishi.
"Wai? Malam ango, don Allah rabani da batun nan, ai ba wani abu bane dan an gyarota, kawai
sai dai ka rufe idanunka ka shige dakin Babynka!"
Dariya suka saka a lokaci guda, yana kuma kallon ta ya kuma cewa.
"Baki kishina kenan?"
"No a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 13