Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Sahiya ga munafuka, ko kumar uban me take? Shegiya annamimiya, dama nan kika fito ina kudin da ya baki?" Cikin rawan jiki da rashin dabara ta mika musu kuɗin,suka kuwa rufe ta da duka, tare da jan ta a kasa, zuwa cikin gidan. "Lantana! Kizo Kinga abinda Yaya Bature ya bata, Shegiya munafuka take zata haƙa rami ta binne, sabida uwarta da Ubanta sun biyaki kadan renonta. Kai wannan yarinya akwai bakin ciki yar banza me gadon tsiya, ince Ubanki ma da ya tafi cirani, abin arziki bayi wa kan shi ba balle ya ajiye miki. Toh wallahi Lantana sai ki dage domin rijiya ta bada guga ya hana, yarinya da mugun hali, ace a baki wannan makudan kudaden ki fara tunanin b'oyewa Yo Allah na tuba idan aka yi auren ai ruwan gidanki ma sai mun roka ki bamu. Hattara dai Lantana domin kifi na ganin ka me har koma, kinyi renon wahala." Inji Iya Larai, wani irin bakin ciki ne ya turnuke Lantana. Ta kamo Sidrah, ta shiga dukarta tare da kwallon da ita, tana faɗin. "Dan uwaki nan aka kawo min ke, an kashe iyayenki wato bari na gama wahala dake, shine xaki gode min da boye abin da saurayi ya baki yar banza dangin asara toh wallahi bani isa ba, koda zaki mutu dan bakin hali sai nasha arzikin gidan ki, yar banza me mugun nufi, zai kare akanki maha'inci." Tsabar duka ko motsi bata iya yi, sannan ta watsa mata ruwa, wanda ya d'ago da dattin tare da kaikayin ƙarara da Ado ya watsa mata, ihu take na birgima babu wanda ya kuma bin ta kanta, duk suka watse abin su, suka barta a cikin wannan yanayin. Har sai da. Allah ya kawo Sabitu, dan Lantana na uku, ya ga halin da take, nan ya dibo ruwa a rijiya ya zuba yayi mata wanka shima ba ace wanka ba, dan da toka ya mirza mata tayi wanka rabonta da wanka tun auren Atiku. Shima sabida ganin Idanun jama'a yasa Lantana ta bata wata ajiyayyen kaya da aka b'oyewa. Saratu, yar ce Lantana kenan. Itace Sa'ar Sidrah. Komawa gefe tayi tana sauke ajiyar zuciya, shekaru biyar kenan da kawo ta Hadeja, tun bayan rasuwar Iyayen ta, bata kuma samun kulawa ba, wani irin kuka ne ya ke zuwa mata, amma bata da ikon yi. Sabida sanyin da ake busawa yana shiga jikinta, tare da rawan sanyi. Wata riga da skirt na Amintako aka bata, skirt din yayi mata yawa sosai, sai da ta daure k'ugun. Sai rigar shima har gwiwarta, sai wani baƙin pant me shegen datti, ta saka tare da komawa gefe tana ajiyar zuciya. Haƙoran ta yana haduwa da juna. --- Yayi tsaki ya kai sau hamsin zuwa sittin, sabida bakin cikin, haka yake tukin gangancin tare da nazarin al'amarin. Cizon lips d'inshi yayi, tabbas dole ya nemi mafita dan ba zai tab'a sadaukar da Rayuwar shi a tare da yarinyar can ba. ..... Zaune suke a tsakar gida, Hajiya Surayyah, ta mike ta barsu dama sun hadu ana zagin Hajiya Uwani ce, sai Hajiya Surayyah ta mike zuwa ban daki. Kamar jira Ya Hindatu take tace. "Ban da rashin girma da hankali, ai ko cewa Surayyah aka yi ta haihu ba zata yarda ba, dube fa nan da sabon wata za a kan kayan auren Ali da Ghali, ga Yan matan ta nan suma aurar dasu za ayi amma matar nan ta baza zani ta kuma dauko ciki. Gaskiya budurwan zuciya tana damunta." "Hmm! Yaya kenan, ai ita burinta ta tara dukiya, dan ta sami kason gado. Kome zata yi da shi oho, yara goma ina zaki kai su, Ahtoh maji ma gani. Na mu ido.". Hajiya Amarya na dire aya Hajiyar mu na fitowa, hannunta dauke da lakar inyamurai, wato farar kasa. Zama tayi tana leka hanyar waje, suma kuma ba zaka tab'a yarda anyi gulmarta ba. Kallon Agogon wayarta tayi sannan tace. "Karfe biyu! Uwar yan boko an kusan dawowa. Ai matar nan ina kallon ikon Allah, karfi da yaji. Ta hana Alhaji bada cefene fa, amma ai da shi yake bada cefene." Cabewa Hajiya Amarya tayi sannan tace. "Yanzun kayi magana ta nuna maka ita tafi karfin ka, kiga lokacin zuwan mu bikin Atiku hadeja, kin bin motar mu tayi karshe dan bakin munafunci sai gata a motar Alhaji..wai ta tsaya aiki shi yasa ta rasa motar mu. Kuma karki manta nice da girki fa!" Jin hayaniyar Yaran gidan sun taso daga makaranta, yasa su katse hirar, mik'ewa tayi tare da nufar kitchen, tana duba dafuwarta, amma tana tana sauri dan kar su yi gulmarta. Tana barin gurin Ya Hindatu tace. "Ke dai zaki sani, sakarya kome sai kin nuna son a sani, sai kace ba a nan aka hanata Daukar ciki ba, sabida matsala amma dan rashin sanin ciwon kai ta kuma kwaso ciki, yaron da ko shekara daya da da rabi bai yi ba. Ita nan sai tayi goggaya da mutane." "Ai na fahimce ta, ko zani na sauya sai tayi ki duba shekaranjiya nake bawa kafinta sauran kudin kujerun da za a min sabida bikin yaran nan ashe matar nan.". Shiru tayi, sakamakon fitowar Hajiya Amarya tana zare idanu, tare da shan jinin jikin ta, alamun nayi da ita, ganin babu kome a fuskar su, yasa ta karasowa dan a cigaba da zagin Hajiya Uwani. "Ina gaya muku, wallahi badan bana son damuwa ba, ai da sai na nunawa Uwani iyakarta. Domin ranar abun ya bata min rai, taya ni da mijina ke ki makale mishi." Fakon idanunta Ya Hindatu tayi ta mata gatsine ( 😂󰢪󰣸 please don Allah kar mu zama fitinannun a cikin al'umma! Mu zama mutanen kirki wanda duk rintsi zaka ji ana bada shaida akanka, ina dalili a lokaci guda ya Hindatu ta haɗa gulma tayi da Amarya a bayan Hajiyar mu, tayi da Hajiyar Mu bayan Amarya,kuma yanzun ta zauna ana yi da Ummi. Me muke nima? Ace baka da aiki sai gulma, Allah ya kyauta." "Mama kizo ki zuba mana mita wallahi yunwa muke ji." Dake bata son ta tashi ayi da ita, sai ta kasa koda motsine tana son a zagi Hajiya Uwani... #Mai_Dambu... [11/13, 8:05 PM] My Zahrah: 𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔 <𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂> ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆... ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮 Bismillah Rahmani Raheem https://chat.whatsapp.com/GIIFqCembtoD3Bp6yWve7C Don Allah idan kana Groups dina karka shiga wannan na masu bukatar Free Pages ne! Please karku shiga *Masu tambaya akan Sunan Labarin! Kusan zan fada muku cewa aya ce ta Alqur'ani kamar Yadda Allah madaukakin sarki yace. He released the two seas, meeting {Side by side} between them a barrier [so] either of them, transgresses 55:19:20! Da fatan zaku fahimta, and indai ruwa biyun zasu zauna a guri guda daya ba zai shiga daya ba, sannan koda ya shiga zai fita! Toh taya haka zai faru? Labari ne akan Halayyar mutane biyu! Duk wanda ya karanta PROLOGUE zai fahimci ainihin kan labarin! Halayyar mai kyau da Mara Kyau! Shine Ma'anar Ka sayi daya ka samu daya kyauta Shine ruwa biyu! Daya me dad'i daya me gishiri! Taya zamu banbance su koda kuwa sun kasance a kofi biyu! Sai ku tayani duba su* #Taƙaddama 0⃣5⃣ "Wai lafiyarki? Ki tafi ki basu abinci mana, kin wani kasa kin tsare, tare da addabar mu da tsida yawu, sai kace wata farin shigar ciki." Inji Ya Hindatu, cike da jin kunya me hade da jin haushi ta mike, ranta bai so ba, ba dan kome ba sai dan gulmarta da tayi imanin zasu yi. Tana mik'ewa Ya Hindatu ta tab'e baki tana faɗin. "Algunguma, kin iya ta wasa baki son ayi taki, dani kike zancen sakarya." "Hmm! Ita nan mai wayo sai da Jamilah suka je shagon kafin ta aka ganta gurin wai ta kama kame kame, ita gata nan mara gaskiya biris nayi da ita na zubawa gudu ruwanta ido, naga iyakatar." "Assalamun Alaikum!" Inji Hajiya Uwani. "Wa'alaikimun Salam, Uwar biyu kyautar Allah, Barka da zuwa, ya aiki? ". Murmushi tayi sannan tace masu. "Alhamdulillahi ya gida!" "Lafiya lau," "Toh sannunku da aiko!" "Yawwa sannu da dawowa.". "Yawwa sannunku da gida, " Tana wuccewa suka bita da zunɗe, tare da nuna bayanta, da baki. Wato gidan Alhaji Ma'aruf, babban gida ne, domin a sauran jikin gidan ya fidda wasu shashi kusan tara, idan ka cire na Aamil wanda yake ciki. Sauran duk suna wajen gidan ne, amma akwai hanya ta cikin gida. Kowani shashin na wajen gidan flat ne na zaman mutane biyu, Ali da Ghali. Flat din su biyu, kowa da shashin sa.. Faruq da Mujaheed, shashin su suma ɗaya. Kuma dukkan su kusan ginin su irin na Aamil ne. Sulaiman da Ismail suma gidan su daya Mahmoud da Saleh suma haka Bala da Isah. Duk suna zama anyi musu...... Dakin Hajiya Surayyah, yara biyar zata aurar. Ali da Ghali, Jamila Safiya, harirah. Wadannan sune za ayi auren su nan da wata uku. ---- Bayan sallah azhar ya shigo gidan, ya samu ana dambe akan abinci, "Wani wani irin rashin mutunci ne? Dan Ubanku." Sake kwanon suka yi tare da kamewa guri guda, suna rawan sanyin tsoro. Tsaki yayi sannan ya wuce dakin Hajiya Uwani, yana shiga ya zube a kujera, ya kalli Aseed, cikin damuwa yace. "Bani ruwan sanyi!" "Kai wuce kitchen ka dauko mishi ruwa mara sanyi a gora, Son zanga ranar da zaka bar shan ruwan sanyi babu amfani a jikin d'an adam balle ka samu abin yi kullum." Zuba mata rinannun idanun shi yayi cikin damuwa, yace mata. "Wallahi idan ban sha ba, toh ba makawa zan zuki wiwi! Dan ina jin kaina kamar zata yi bindiga, Ummi wai meye yasa sai ni ne zaku hada da wancan halittar? Duk cikin gidan nan a rasa wanda zaku yiwa wannan yankan kaunar sai ni, idan baku sona ku gaya min mana? Wallahi ban tab'a ganin abin da ya d'aga min hankali kamar wancan halittar ba, yarinyar da babu komai a tare da ita sai Warin Datti haba Jama'a." "Shine matsalar ka?" Cizon bakin shi yayi cikin baƙin ciki yace mata. "Wallahi bana sonta, koda kun bani zan iya guduwa na barta, karshe ina nufin zan iya saketa na barta don Allah karku hada ni da ita, kamar yadda nake nan kamata yayi na samu Yarinyar da aka yi ta dan ni ba wacce aka yi ni dan ita ba..kin gane maganar gaskiya nake gaya miki amma tabbas zan gudu na bar auren nan." Kura mishi ido tayi, na wani lokaci kafin ta kauda kanta sannan tace mishi. "Meye matsalar yarinyar?" Gyara zama tayi, sannan yace mata. "Wallahi ba zan boye miki ba, ni bana sonta ne! Ummi ni a rayuwata ina son abu me kyau, ina son abu me daukar ido da hankali. Ina son abinda zan gani na tabbatar me kyau ne, Ummi ki duba lamari na, idan bai min ba taya zan samu dashi." Shiru tayi tana mamakin shi, tabbas ta yarda da batun shi, domin shi din mutum ne mai mugun don kyale kyale, duk abinda zai samu ko zai baka toh zaka samu dangin kyale kyale ne. Sannan abu ne mai matukar kyau da kyale kyale, dan haka ta fahimci abinda yake cewa. Da gaske baya son Yarinyar ne, koda an bashi zai iya wulankata ta, karshe a samu matsalar zumunci. Amma taya zata fahimtar da Alhaji ba tare da ya zarge ta ba? Dan tayi imani da Allah, cewa zai iya take sányan shi botsarewa. Numfashi ta sauke kafin tace mishi. " Amma Ni dai ka Hadani da jagwal domin babu abinda zai hana ace nice na hana ka don kayi hakuri da yarinyar mana, domin zata." "Ummi wallahi ba dai da wancan me zubin halittar mutanen b'oyen ba, domin ni na zan aureta ba Allah ya gani. Duk abinda zai faru sai dai ya faru." Zuba mishi ido tayi, jikinta yayi mugun sanyi tunda ya fadi haka wallahi ba zai zauna da yarinyar ba, dan haka ta shiru. .. wani irin murmushi Ya Hindatu tayi lokacin da taji tattaunawar su, dan haka ta shige dakin su ta fesawa Mahaifiyar ta, suka zauna tare da kitsawa Ummi karya da gaskiya. Wanda zai tashe ta daga fadar Alhaji Ma'aruf, ya kuma bindige Soyayyar Hajiya Uwani. Murmushi Hajiya tayi sannan tace. "Rabu da yar banza dani take batun, wallahi sai tabar min D'ana tunda ba tare na haife su ba, na gaji da makircin Uwani." "Ai Hajiya ba ita kadai ba shima Dan Sarki ya kamata a taka mishi birki ki saka uban y mishi barazana, akan Ya auri Hasnah domin wallahi haka zai kuma hade mana kan shi a ruwan sanyi." "Wannan ifiritun yaron zaki samu kanshi da wuri! Bar mafarkin haka domin kafiyar bala'i ce dashi." Inji Hajiya. Haka suka yi tattaunawa, har zuwa lokacin da yayi musu. Al'adar gidan Alhaji Ma'aruf, abincin da ake dafawa da rana,ana kaiwa Kasuwa..sannan na dare kuma ana juyewa Babban kula ce. Sannan akan ajiye kwando Babba da kulolin samarin gidan, domin diban abinci, haka ya samo asali ne daga Hajiya Uwani, wacce zuwanta ta samu ana b'arnan abincin a gidan, idan aka zuba a kulolin ba lallai bane, suzo su ci. Domin yayi sanyi. Amma idan aka kwashe a cikin babban abu aka saka laidar siga aka rufe, har washi gari da zafin shi. Ka'idar abincin gidan za a dafa kome da rana, da dare kuma ayi tuwo miyar da kika san me gidan yana ci. Nama kuwa ana kawo na dubu biyu daga kasuwa, domin akwai kifi na rana, na dare akwai namar miyar.( Wannan shine kadan daga cikin gidan ɗai-ɗaikun masu kudin mu! Musamman Hausawa! Asalin wannan shine yadda suke tafiyar da gidajen su, amma idan akwai wacce take da sani bayan haka ta min magana, zan gyara sosai 😘🤩 ) Akwai doya, da dankalin Hausa, da na turawa. Akwai taliya wanda koda b'acin rana zai saka a makara, akwai wanda za a dafa sabida gudun b'ata lokaci, wannan tsarin Na Hajiya Uwani ne. Sannan ba kullum ake soya kosai ba, da kunu. Idan girkin Hajiya Uwani ce, har ta fita ba a cin kosai da kunu, dan akan soya dankali turawa rabin buhu ne, na hausa kwata, sai a dafa shayi da kayan kamshi, sannan tayi miyar kifi, wanda yake kasancewa. Miyar da za aci dankalin dashi. Wani lokaci kuma takan gayawa Alhaji Ma'aruf yazo mata da kayan cikin rago ko na saniya, sabida ita gwana ce a girki, kuma baya jin kunyar a kawo abincinta kasuwa, dan har makotan shi. Tambayar shi suke, "Alhaji Ma'aruf! Girkin Maman tagwaye ne? Dan muna son girkinta.".cikin farin ciki yaƙe gabatar musu da abincin. Shi yasa da ya gaya mata, taji dad'i kuma dama kular da ake kai abincin kasuwa nashi ne shi ya saya, dan haka tafiyarta wani course Lagos, ta shiga kasuwa ta sayo manyan warmes guda hudu, tare da manyan tire na zuba wasu abubuwan dangin salat, dan haka ranar girkinta ta fito dashi ta fara aiki dashi. Haka ya bawa matan gidan haushi, suka shiga gulmar ta, tare da nunawa cewa ta cika iyayi da sanabe.. Bai dame ta, ita abinda ta sani mijinta da yaranta, sai Aamil. Kuma duk da wannan surutun ranar girkin ta, hatta tuwon dare baya kwana, domin idan ya kwana ana sake yin dumamen shi ayi a cikin abincin karyawa toh na Hajiya Uwani baya kwana, idan kayi latin zuwa diban abincin toh zaka kwana ciki. Sannan ita daya ce duk dare sai ta dafawa mijin su shayi. Abin har ya zama Aamil yana zuwa sha. Shima da flast d'inshi. A hankali Ghali shima ya shiga sahu, sannan Aliyu. Duk su ukun nan itace Uwar dakin su. Domin da ita suke sirri ta kuma san sunawa Baban su barna, dan haka take zama tayi musu nasiha, amma sun zama sai addu'a, Aamil tana mishi Uzuri sabida rashin uwa, su kuma Ali da Ghali, asalima uwar su ce take kara bude musu hanyar cutar da mahaifin su. ---- Idan muka duba ta yanayin kasuwancin Alhaji Ma'aruf, yana da shagunan sayar da abinci. Sannan yana da shagunan sayar da babur, wato irin su Bajaj. Sai kuma shafin sayar da magani abinda ya karanta, duk wani kudin da zai shigo daga wandanan shagunan ta Office din Aamil yake shigowa kasancewar shi wanda ya karanci accaunter. Amma abin tausayi, shi ne me rubda ciki akan Dukiyar, dan wai Uban ya gaya mishi gaskiyar dukiyar mahaifiyar shi ce, Aamil yana da almubazzaranci, amma abin yana masifar b'atawa Uban rai, babu yadda ya iya dashi ne sai yake binshi da ido. Faruq da Mujaheed, suna inda ake sayar da Bajaj, Bala da Isah suna inda ake sayar da magani, Ali da Ghali, suna shafi Daya. Na sayar da abincin. Mahmoud da Saleh, suna dayan shagon sayar da kayan aikin gini, idan akayi ciniki misali dare yayi sukan tura gundarin kudin aiki. Office din Aamil. Idan ana niman mutumin da ya fidda hakkin Iyalin shi Alhaji Ma'aruf ne, ana ganin Hajiya Uwani itace yar gaban goshin sa ce, kawai amma kowani zuciya tana son mai kyautatta mata, Hajiya Uwani kuwa bata tab'a jin ko sau daya ta cuci mijin su ba, koda nawa zata kashe idan da zai zo ya tambaye ta, mika mishi takardan take. Bata tab'a jin a ranta ko sau daya ta zalincin abinda yake bata ba. Haka shima ganin tana kokarin kare kimar shi da dukiyar shi sai ya sashi kokarin ganin ya cusa soyayyar ta a zuciyar shi yadda babu wanda ya isa ya faɗa mishi abu akanta, ya dauka.. Toh su sauran matan gani suke ba haka kawai ta bar shi ba, suna ganin kamar ai ta mallake shi. Da wannan tunanin suke kallonta, bayan ita kuwa halayyar yan boko ke bin jikinta,bata da lokacin kowa sai na aiki. Bata da lokacin kome sai na yaranta da mijinta. Wannan kenan. ....... Har Aamil ya bar d'akin, bata daina nazarin abinda zata gayawa Mahaifin shi ba, shi kuwa ganin ya zareta cikin damuwa, kawai ya nufi Ofishin Abban su,ba tare da damuwa da mutanen da suke Office din ba ya gaya mishi abinda ke ran shi,zai fita Abban shi yace mishi. "Duk abinda zaka yi sai dai kayi amma aure babu fashi, kuma wallahi ni da kai ne,mutumin banza." "Nifa wallahi bana sonta duk abinda zaku yi sai dai kuyi amma wallahi babu abinda ya dame ni!" . Idan ran Uban yayi dubu ya b'aci. Sai da Alhaji Ahmed abokin shi yace mishi. "Tuntuni kayi wannan kuskuren! Yaron nan baka tab'a yunkurin hada shi da Magret ba, gani kake kamar kana kai shi zata kwace shi, da ace tun fil azal ka ja shi a jiki da babu abinda zai tab'a faru. Kaga illar rashin bincike, gashi ya girma ya kai minzalin da za ace yana da yara sama da uku amma ya zama mara kirki a gareka. Baka san wani abu ba. Allah ya bamu dama domin muyi amfani dashi amma kai da kasamu sai kayi watsi dashi, wata uwace zatayi wurgi da d'anta, sannan taki dawowa, kayiwa kanka Adalci, wallahi ba haka kawai Magret tayi fushi ba, karka manta a ranar da abin zai faru diamond ɗinta ta baka, kazo ka sayar ka daina yawon bin neman aiki, amma sabida rashin adalci, da aka ce maka ta gudu baka bi bayanta ba, duk da lokacin na gaya maka kayi maza kabi sawunta kace kai a'a. Yarinyar da ta bar dukiya me tarin yawa tabiyo soyayyarka, me kake tsammaci zata yi wallahi bana raba dayan biyu koranta suka yi gidanka sai kai,.duk wanda yayi yayi yunkurin juyin musu hali zasu bashi mamaki." _Wannan Littafin na kudi ne_ [11/13, 8:05 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/JAgNlnN98ab 𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔 <𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂> ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆... ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮 Bismillah Rahmani Raheem #Kayan aure 0⃣6⃣ "Alhamdulillah! Ya zanyi? Na kasa fahimtar kome akan Hauwa, duk abinda zanyi dan ita nayi amma sabida son kai tayi tafiyarta, shi yasa ban bi bayanta ba. Ba wai!" Katse mishi magana Alhaji Ahmed yayi cikin nutsuwa yace mishi. " Baka da wani excuse! Domin kuwa da saka hannunka kome ya faru, kai da kanka ka gaya min kasha dukarta, amma haka bai sanya ta bar ka ba,karka manta tunda ka saka hannu a jikinta kimarka ta fara raguwa, a hankali tana hakuri da kai baka fahimci tsawon lokacin da ta dauka tana share kwalla ba. Ni da kai Mahaifinta yaƙe gaya mana cewa. Ba zaka iya rike ta ba, dan ya rene ta da SOYAYYA ce,ya rene ta, ta yadda babu abinda ta nima ta rasa, haba Ma'aruf. Wai yaushe ka zama mara kirki ne? A ranar da abin zai faru, kake gaya min baka san tana ajiye da dukiyarta ba, sai da kazo zaka fita niman aiki. Ta ciro ta mika maka, sannan ta kuma ce maka bata jin dadi, kai kanka kayi imanin ba zata iya tafiya ba a rana, yarinyar da muka zo da kayanta sama da kwati bakwai sai da aka wayi gari , rigar da take sawa babu maraban shi da ta almajirai, sannan kace ta gudu ne dan tana da dukiya a hannunta, kai a tunanin ka da tana son guduwa ai da ta tafi, tuntuni amma sabida soyayyar da take maka yasa ta tsayawa. Kayanta da ta dauka ta baka, sannan ta ta tashi gudun da kake fada bata tafi da kome na ta ba,sai wannan duwatsun Haba Ma'aruf idan mai magana wawa ne, ai majiyin shi ba wawa bane. Kayi nazari da kyau shi yaron da ake son yabi ra'ayin ka,. Ka tab'a tambayar shi meke damun shi? Baka tab'a ba, da

Chapter 3 of 13